Share this page
Zainab tana jinta bud'e labule tayi ta le'ko waje tare da yiwa Zainab wani tantirin kallo sannan ta sake labulen ta koma tana cewa. "Ya da min irin wannan kallon kar dai kiyi min sharri cewa nice na jefa miki waya dan nasan ku gadon munafirci ne ni nafi 'karfin 'karyar ki" jin abinda tace yasa Zainab kallon kofar kamar zatai magana sai kuma ta fasa ta koma d'akin ta tunda tasan yanzu da tayi magana ko itace mai gaskiya ana zuwa gurin Hajiya zata yi mata tas a gaban kowa sabulu ta d'auko tazo ta d'auki ruwan har ya fara hucewa ta shiga tayo wankan ta ta fito dan ita sai yanzu ta tuna ma su Umma anguwa suka tafi. Sameer kam yana fita yaje bakin chemist d'insa ya d'auko mashin d'insa ya tafi gurin gyara mata yana tsaye me gyaran yana kunce wayar Aliyu ya kira shi gefe ya koma ya zauna akan mashin d'in nasa yana d'agawa yace "hello Marshall ya gari ya kake kwana biyu shiru lafiya dai"? Daga can 6angaren Aliyu dake zaune sanye da uniform d'insa na army ya saka photon Zainab a gaba yana kallo saida ya shafo fuskarta dake jikin photon ya sauke ajiyar zuciya sannan yace. "Alhamdulillah ko kaje wani wuri ne nake jin kamar kana guri me hayaniya"?. "Wallahi nazo wani waje na kawo gyaran waya ne". "Wayar wa"?. "Wayar Zainab ce". "Ok meya samu wayar"?. "Wai ruwa ta fad'a d'azu da safe shine ta d'auke ta'ki kawowa yanzu dai na bar me gyaran yana kuncewa yaga matsalar". "Ruwa kuma yanzun ta gyaru ko a'a dame take yin assignment d'in school"?. "A'a yau ne fa ta lalace ba dad'ewa akai d'azu da safe ne". "Ok amma ta gyaru ne ko ya duba bazata tashi ba"?. "Wallahi ban sani ba yanzu na bada ya kunce ta dai na dawo gefe sakamakon kira na da kayi". "Shikenan kuyi cinikin ta da me gyaran a haka ka siyar da ita zan baka kud'i ka siya mata wata sabuwa saboda aikin school d'inta". "A'a Marshall basai ka siya mata wata ba dan Allah ka barshi wannan d'in ma insha Allahu zata gyaru". "Na riga nayi niyya karka 6ata min niyya ta ba ro'ka tayi ba sannan kome na baiwa Zainab a rayuwa ba fad'uwa nayi ba abun alfahari zai zama gare ni idan naga tana amfani da kaya da na tabbata daga hannu na ya fita yaje gurin ta sannan a yadda nake jinta a zuciya ta ko raina ne zan iya bata indai zatai farin ciki da hakan" murmushi Sameer yayi yana cewa "na sani Marshall amma abubuwan ne sun yi yawa daga wancan kayi wancan shiyasa nace basai ka siya mata ba". "Sameer a gurin ka ne abubuwa sukai yawa amma a gurin Aliyu bai sa hannu akan hidima da Zainab ba tamkar banyi mata komai a rayuwa ba haka nake ji fatan ka gane"? 'yar dariya Sameer yayi yana jinjina kai yace "eh na fahimta ai dole na gane Marshall". "Ok zan turo maka kud'in saika sai mata wata d'in kawai" Sameer baya son yawan jayayya shiyasa da Aliyun ya dage saiya siya matan yace "shikenan ba damuwa ba matsala Marshall Allah ya kara bud'i" "Amin zai shigo yanzu insha Allah" yana fad'in haka ya kashe kiran shiru Sameer yayi kawai yana mamaki har baisan lokacin da yayi murmushi. Bayan sun gama wayar ko minti goma ba'ai ba Sameer yaji alert ya shigo wayarsa yana dubawa yaga Aliyu yayi masa transfer dubu d'ari biyu da hamsin zaro ido yayi a rud'e bai san lokacin daya danna kiran shi ba Aliyu na d'agawa yace. "Marshall wannan kud'in kuma fa sunyi yawa waya fa zan siya mata ba saniya ba" mi'kewa Aliyu yayi daga can 6angaren da yake da photon Zainab a hannunsa yaje ya mayar dashi inda ya d'auko batare daya baiwa Sameer amsa ba wanda Sameer duk zaton sa ko ya kashe kiran ne saida ya duba yaga ba katsewa yayi ba shiyasa ya sake cewa "hello Marshall kana jina"?. "Eh ina jin ka meya faru"?. "Nace wannan kud'in sun yi yawa a siyan waya kud'in me ka turo haka ko duk wayar za'a siya dashi"?. "Da kud'in me na turo maka kud'in wayar ne man ka siya mata me kyau ta dubu d'ari biyu da hamsin d'in nan dan Allah Sameer gara ta ri'ke babba wacce zata fi jin dad'in ta" kai Sameer ya girgiza yana cewa "amma Marshall.................. "Amma me? dan Allah Sameer kayi shiru kar kasa naji ba dad'i kayi abinda nace kawai sai anjima" yana fad'in haka ya katse kiran shiru Sameer yayi ya rasa wanne irin yanayi yake yanzu idan ya koma gida me zai cewa Zainab taya zaiyi mata bayani yadda zata fahimta waya bata 'karamin kud'i ba dole zata nemi jin waye ya siya mata anan ya zaice wacce kalma zai fad'a Aliyu ya jefa shia tunanin ta yadda zai iya kai mata idan ya siya da wacce kalma zaiyi furuci? Ganin bashi da amsa yasa ya tashi daga kan mashin d'in nasa ya koma gurin mutumin ya tambaye shi yaya batun wayar bayan mutumin ya duba wayar yace. "Mai gida saidai ka barta anan fa baza ta gyaru a yau ba da ruwa a cikin ta sosai" kai Sameer ya d'aga yana cewa "ok zan dawo na kar6a daga baya idan nazo saika fad'i kud'in gyaran na baka Allah yasa ta gyaru". "To ba damuwa insha Allahu zata gyaru karka damu". "Ok tom sai na dawo" Sameer ya fad'a yana zuwa ya d'auki mashin d'insa daga gurin me gyaran da ya tafi shagon saida wayoyi ya shiga ya siya mata sannan ya fita ya hau mashin d'in ya tafi gida da tunanuka kala-kala a ransa lokacin daya shiga kofarsu Zainab tana waje ta shimfid'a babbar tabarmar Umma tana yanka kayan d'inki ganin sa yasa ta aje almakashin tana cewa. "Yaya Sameer ta gyaru"? Kaiya girgiza yana karasawa inda take yace "Zainab wayarki baza ta gyaru a yau ba amma ga wata" da mamaki ta d'ago tana kallon ledar da yake mi'ka mata sannan ta kalle shi tana cewa "wata kuma Yaya Sameer ina kaga kud'in siyan wata wayar da ka bari an gyara min wancan d'in" kaiya girgiza yana kallon ta yace "bani na siya miki ba" jin abinda yace yasa Zainab d'agowa a firgice tace. "Waye ya siya"? Kai tsaye ya bata amsa "wanda ya biya miki makaranta ne" mamaki ne 'karara ya bayyana a fuskar ta har bata san lokacin da tace "wai Yaya Sameer waye wannan da yake min abubuwa me yasa baza ka fad'a min shi ba"? Murmushi taga yayi mata yana jinjina kai yace. "Lokaci ne baiyi ba Zainab idan lokacin daya d'iba yayi shi da kansa zai bayyana miki kansa basai na fad'a miki shi ba" shiru tayi zuciyarta na bugawa da 'karfi gaskiya wadannan al'amuran suna mugun bata tsoro taya wani zai ri'ka mata abubuwa na ban mamaki akan wanne dalili gashi Sameer da yasan komai ya'ki ya fad'a mata to waye zai fad'a mata bayan shi................ "Amshi" taji ya katse mata tunanin tsabar yadda ta'ki a gigice har wata 'yar zabura tayi tana kallon sa wayar yake mi'ko mata 'kin kar'ba tayi sai kai da take faman girgizawa muryarta har rawa yake tace "Yaya Sameer ka mayar masa kayarsa gaskiya bazan iya kar'ba ba tafi 'karfi na nagode". "Na mayar masa kuma? kema kinsan abinda bazai yuwa bane ba kyau mai da hannun kyauta baya kiyi hakuri ki kar6a dan Allah haba Zainab so kike wani yaji maganar da muke daga ni har ke mu shiga uku a gurin Hajiya domin sai tayi mana rashin mutuncin da kare bazai lasa ba sannan kinsan Bilkisu tana d'aki ita ma babbar masharranciya ce zata iya zuwa ta fad'awa Hajiya harda 'karin abinda ba'ai ba saita fad'a dan haka ki kar'ba kawai ina son zan koma chemist". Jin abinda yace yasa jiki a sanyaye tasa hannu ta kar6a tare da mi'kewa ta kai d'aki ta fito ta karasa yankan kayan da take yi sannan ta tashi ta koma d'akin kallon ledar wayar kad'ai tayar mata da hankali yake da'kyar ta iya fito da ita tana kallon photon wayar da yake jiki kwalin taga ga kud'in da aka siya nan dubu d'ari biyu da hamsin kamar za ta fasa ihun tsoro da'kyar hannunta na rawa ta bud'e ta ciro ta sai sha'ki take ido ta zuba mata hankalinta in yayi dubu ya tashi waye wannan mutumin wai meye haka ne ita fa ta rasa ganewa wannan al'amarin yaushe ne zata fahimta tasan Sameer bazai mata wasa ba kuma ba tsokanarta yake ba bashi da kud'in dazai ri'ka yi mata wadannan abubuwan tabbas akwai mai yi mata to abun tambayar waye shi a ina yake yaushe zata san shi meyasa yake mata hakan waye zai bata wadannan amsoshin? Ta tabbata ko Sameer ta tambaya bazai fad'a mata ba saidai yace akwai lokacin yaushe lokacin zai zo.............. Sallamar Umma ce ta katse mata tunanin da take yi alamar sun dawo daga anguwar gaba d'ayan matan gidan suka ji tashi tayi da wayar a hannunta ta shiga d'akin Umma a lokacin Umma ta cire hijab ta ajiye ganin ta da yanayin ta kamar bata cikin walwala yasa cikin fargaba tace "Zainab lafiya ko wani abu ne ya faru Hajiya tayi kiran ki ne"? Kaita girgiza a damuwance ta mi'ka mata wayar tana cewa "ga abinda ya d'aga min hankali Umma" kallo Umma tabi wayar dashi ba tare data kar'ba ba tace "wannan wayar kuma fa daga ina"? Jikin a sanyaye Zainab tace. "Yaya Sameer ne ya kawo min". "Sameer kuma ina taki wayar"? Numfashi Zainab ta sauke tana cewa "d'azu bayan fitar ku anguwa ta fad'a ruwa shine na bashi ya gyaro min kuma daya dawo maimakon na ganshi da tawa sai yace wai baza ta gyaru a yau ba amma ga wata" da mamaki Umma tace "ga wata kamar ya siya miki yayi"?. "A'a wai wanda ya siya min makaranta ne ya bashi kud'in ya siya min" zaro ido Umma tai tana cewa "innalillahi wa inna ilaihi raji'un wai dan waye wannan me miki wadannan abubuwan meyasa Sameer bazai fito fili ya fad'a miki ba wannan abun ya zarta hankali bari naje na kaina gurin nasa naji abinda yake faruwa" ta fad'a tana d'aukar hijab ta kar'bi wayar a sanyaye Zainab ta kalle ta tana cewa. "Yana chemist fa" Umma data gama saka hijab tace "eh ai can chemist d'in zanje" fita tayi ta bar Zainab shiru a d'aki ta rasa me yake mata dad'i. Umma kam da saurinta ta fita daga gidan kana ganinta kasan hankalinta ba'a kwance yake ba a lokacin da taje tayi sa'a kuwa shi kad'ai ne ba kowa da sallama ta shiga tana aje masa wayar tace "Sameer waye ya siyawa Zainab wannan wayar? Kace wanda ya siya mata makaranta ne haka ne"? D'an murmushi yayi yana d'aga kai yace "eh Umma haka ne d'azu wayar tace ta fad'a a ruwa na shiga gidan ta bani na kai a gyara mata acan yayi kirana a waya nace na kawo mata gyaran waya ne shine yayi transfer na siya mata wata na kawo mata nima da nasan idan nace wayarta ce ta 6aci zai zaice zai siya mata wata wallahi Umma bazan fad'a masa ba". Da alamar tambaya Umma tace "to wai Sameer waye shi"? Shiru yayi ya rasa me zaice mata domin bai da amsa ita ma Umman ta fahimci hakan sosai shirun ya ratsa gurin can ya d'ago yaga yadda ta 'kure shi da kallon jiran amsa numfashi ya fitar a hankali yace. "Umma aboki na ne kuma yana son Zainab ne amma yace baya so a sani yanzu sai ya tashi zaiyi auren zai zo ya bayyana mata kansa alkawari na d'auka masa cewa bazan ta'ba fad'a mata shi ba sai lokacin daya d'iba da kansa ya cika zuwa da kai yafi sa'ko sannan duk abinda da kika ga yana yi mata yace min bai saka hannu a cikin yi mata hidima ba shiyasa nake rasa abun cewa a duk lokacin da Zainab ta tare ni da tambayar waye shi dan Allah Umma kiyi hakuri bazan iya fad'a miki shi ba saboda alkawarin dana d'auka masa insha Allah yana nan zai zo gare ku" tunda ya fara magana jikin Umma ke rawa har ya kai karshe waye wannan yake son Zainab a ina yake dama sonta yake?.............. Kai ta girgiza tana sau'ke ajiyar zuciya mai 'karfi tace "kuma Sameer idan lokaci yayi ya bayyana tace ba ta son sa fa shine abun damuwar"?. "In sha Allahu Umma Zainab ba za ta 'ki ba saboda ina da tabbacin hakan ba za ta ta'ba juya baya ba za ta amince masa shine ya dace da rayuwar ta" kad'a kai Umma tayi ba tare da sanin abun dafawa ba tace "shikenan Allah ya rufa asiri ubangiji ya za6a mana abinda ya fi alkhairi a rayuwar mu bari na koma kawai" tana fad'in haka ta juya ta bar chemist d'in sansanyan numfashi Sameer ya fitar bayan ta tafi ya kira Aliyu. "Marshall akwai matsala fa dama na fad'a maka in dai na siya mata wayar ne dole zata nemi sanin waye kai kuma gashi hasashe na ya tabbata yanzun nan Umma ta bar chemist d'in nan tazo jin waye ya siya mata". "Kuma ka fad'a mata"?. "A'a taya zan fad'a mata bayan alkawari mu kai dakai cewa kaine da kanka zaka fad'a mata kuma saina karya maka alkawari". "Yanzu ka fad'a mata wani abu ta yadda zata fahimta ne"?. "Eh nayi mata kyakkyawan bayani nasan ta yarda kuma idan ta koma gida zatai wa Zainab bayani ita ma zata fahimta". "Ok yayi ina so ne saita gama school d'in idan ta samu offer ta fara aiki saina fito mata da maganar son ta sannan koma menene sai ayi kawai". "Allah ya yarda Aliyu muna godiya".. "Karka damu kaina nake wa domin ko me Zainab zata zama dai muna tare idan na aure ta sai ranar da kuka ganta idan na 6oye ta duk ranar da tazo gida baza ku gane ta ba saboda yadda kamannin ta zasu canza tayi kyau akan wanda take dashi ta 'kara haske tayi 'kiba sosai" dariya Sameer yayi yana cewa "Allah yasa Marshall zan fi kowa jin dad'in hakan wallahi har na matsu lokacin nan yayi Zainab ta zama matarka". "Na fika damuwa da hakan Sameer yanzu maganar nan da muke da kai ji nake kamar nayi tsuntsuwa nazo na ganta kawai ko zuciya ta zata samu salama daga tafasa da 'kaunarta take yi". "Lokaci ne yana nan zuwa". "Haka ne dalilin da yasa bazan sake zuwa gida pass ba sai ta gama school d'inta". "Ok tom Allah ya dawo da kai lafiya". "Amin na gode Sameer" yana fad'in haka ya katse kiran murmushi Sameer yayi yana aje wayar a gefe daidai wasu mutum biyu sun shigo ya tashi yana kallon a yadda aka ri'ko d'ayan da gani baida lafiya sosai.................. JGW STATE. ZUCIYAR ALIYU CE. @YUSRAH MUSA PAGE 29 Umma tana komawa a yadda ta bar Zainab a d'akinta anan ta dawo ta same ta tayi tagumi ta zubawa guri d'aya ido ko sanin tayi sallama ba tai ba saida ta kira sunanta sannan ta d'ago tana sau'ke ajiyar zuciya mi'ka mata wayar Umma tai tana cire hijab ta aje tare da zama ta kalle ta tana cewa "Zainab naje gurin Sameer yayi min bayani abokinsa ne yake miki wadannan abubuwan sannan yace min sonki yake amma ba yanzu zai bayyana miki kansa ki ganshi ba ni dai da ace akwai abinda zan iya yi gara koma waye ya fito mu ganshi tsoro na nan gaba Zainab kice bakya son shi bayan duk wannan d'awainiyar da yayi miki"? Shiru Zainab tayi ta kasa magana gaba d'aya bata san me zata ce ba waye abokin Sameer a ina yake duk iya zurfafa tunanin ta bata gano ko waye ba............. "Zainab" Numfashi ta fitar tana kallon Umma a sanyaye jikinta ba wani sauran 'karfi tace "na'am" ita ma Umman zuba mata ido tayi tasan tana cikin halin rud'ani ta yadda duk abinda zata fad'a mata ba lallai ta fahimce ta ba shiyasa kawai tace mata "tashi kije koma waye Allah yasa shine mafi alkhairi a rayuwarki idan babu alkhairi Allah kar ya shigo dashi cikin rayuwarki balle har a samu matsala nasan dama bazai wuce hakan ba domin ruwa baya tsami banza duba irin abubuwan da yake miki dole saidai so d'in ni kam Allah yasa kar Hajiya taji labarin siyo miki wayar nan tazo ta d'aga mana hankali" ita dai Zainab tari da bai kama ta ba bata yi ba 'karshe ta mi'ke ta fita daga d'akin tana jin yadda wani zazza'bin fargaba da damuwa ya lullu'be ta lokaci guda. *** ** *** Kwanaki sun sake ja lokaci yana ta tafiya abubuwa suna ta faruwa tun Hajiya tana fad'a da zage zage har tazo ta zuba musu ido taga iya gudun ruwan su so take su kaita bango rana d'aya ta fito tayi musu uwar watsi ta gigita musu lissafi daga iyayen har 'ya'yan nasu zata nuna musu duk abinda suke ji dashi nata yafi nasu idan rashin mutunci ne tun kafin a haife su ta iya idan wula'kanci da fitina ne ma duk saidai su biyo bayan ta. Tana zaune ita kad'ai babu kowa Zain ya shiga gaida ita yana zama ko ina kwana bata bari yace ba tace "Zaidu d'aga idon ka ka kalle ni nan" da yake d'an zamani ne tar ya d'aga idonsa ya zuba mata taci "Zaidu kuna son gani kalata a gidan nan kuna son ganin rashin mutunci na zan gwada muku ni ba tsohuwar kwantu kwan bace" da mamaki Zain yace . "Me kuma ya faru Hajiya"?. "Au meya faru kake tambaya ta"?. "To ya kike so nace Hajiya ke fa kina da d'orawa mutum laifi daga shigowa ta ko bari na gaida ke baki yi ba kin kama balbala min bala'i". "Dan ubanka ni nake balbala maka bala'in"? Shiru yayi bai amsa mata ba taci gaba "batu nake akan maganar aure dana had'a ku kai da Zainab har yanzu tsabar raini banji tsinannan da yazo yace min ya amince a cikin ku ba"? Wani irin kallo yayi mata jin abinda tace lallai ma Hajiyan nan da neman rashin zama lafiya take ta'be baki yayi yana cewa. "Ni dai banda ni a cikin su kiwa sauran dai amma ban da Zaid". "Uban wa ka fi"?. "Me kike nufi ni dai karki saka ni a cikin wannan shirmen banga mai yi min auren had'i ba wallahi". "Sai ni dan ubanka". "Kinsan Allah Hajiya bazan auri kowacce yarinya a gidan nan ba gara ma ki sani". "Ni kuma saina aura maka in yaso ana shafa fatiha ka furta mata kalmar saki". "Ai kuwa zan furta". "Da naci 'kwal ubanka wallahi" kallon mamaki Zaid ya bita dashi ganin tunda ya zauna take masa zagi na tsamar nama yace "wai ke Hajiya dan Allah haka ake rayuwa ne ke haka akai miki auren dole ne ko me da kika matsa sai munyi gadon ki kike so muyi ko me"?. "uban wa ya fad'a maka auren dole a kai min ni auren so nayi da kakan ku". "Kuma mu kike neman 'ka'kaba mana abinda ba mune mukai ra'ayi ba"?. "K'warai kuwa sakawa tace umarni na ne dole ka auri Zainab saina aura maka ita" kaiya jinjina yana she'kewa da dariya yace "waye zaki aurawa Zainab d'in amma dai bani ba"?. "To da ubanka zan d'aura idan ba da kai ba"?. "Caf lallai Hajiya wacce irin magana kike yi wannan mara dad'in ji kema kinsan abunda bazai yuwa bane wallahi. . "Kuma dan ubanka ni kake cewa caf fad'a min dalilin da yasa baza ka auri Zainab d'in ba"?. "Saboda babu soyayya tsakani na da ita kuma bayan haka ni ina da wacce nake so". "Yar gidan uban waye a ina take"?. "Yar gidan baban ta ce a sabuwar 'kofa suke da zama" yana rufe baki Hajiya tace "to wallahi bari kiji ko a gidan uwar wa take ba sabuwar 'kofa ba dole ka barta ka auri Zainab ko kuma ka had'a ka aure su duk su biyun ranar d'aya a cikin biyu ka za'bi d'aya ko rabuwa da wancan ko auren su biyun lokaci guda ina jin ka"? Ta'be baki yayi yana cewa. "Ni bani da 'karfin da zan auri mata biyu rana d'aya dame zan ji da yi musu lefe ko da kud'in sadaki ko kuma gini na da ban 'karasa ba? Gaskiya bazan iya ba". "To tunda haka ne sai ka bar waccan yarinyar ka auri iya Zainab domin gida bai koshi ba kaga ai baka isa ka d'auko mana yar wani gidan ka kawo ta ba so nake suma sauran su shigo nayi musu magana ku taru ku rufawa junan ku asiri idan ku 'ki humm abun bazai muku kyau ba". "To wai Hajiya ni ban gane inda kika dosa ba meye hakan ne wai"?. "Taya kuwa zaka gane abinda nake nufi ka tsaya kana min fitsara mara kunya kawai tashi ka bani guri kafin na buga maka wannan sandan" ta fad'a tana d'ago masa shi yasan ba 'karamin aikin ta bane ta buga masa d'in shiyasa bai sake magana ba ya mi'ke ya fita daga gurin Hajiya kofar su ya shiga a lokacin mamarsa tana d'aki yaje ya same ta. "Lafiya naga ka shigo ranka a 6ace"? Yana daga tsaye ba tare daya zauna ba yace "gaskiya Mama bazai yuwu ba bazan iya wannan masifar ba zan nemi transfer aikina na koma kaduna kawai" jin abinda yace yasa ta kallon sa da mamaki tace. "Saboda me zaka nemi transfer ana zaune 'kalau"? Bud'e hannu yayi cikin fad'a ya fara magana "ba kowa ba saboda Hajiya haka kawai daga na shiga gurin ta na gaisar da ita wai ta tsare ni da maganar aure dole saina had'a lefe na auri Zainab bayan ni ba sonta nake ba sannan tayi min girma sa'ata ce fa shekara ta ashirin da biyar ita da had'u dame na fita haka kawai za'a d'ora min aiki" zaro ido Asiya tai tana cewa. "Meee Hajiyan ce tace kayo lefe ka auri Zainab"?. "Eh man yanzu fa daga gurin ta nake fita zanyi amma wannan maganar data fad'a min yasa bana jin zan iya karyawa idan na fita shiyasa ma na dawo" a masife Asiya tace "kuturun ubancan akan wata shegiya zaka hana kanka sukuni wallahi bazai yuwu ba tashi kayi fitar ka babu wani transfer aiki da zaka yi sannan Zainab tunda baka sonta kar ka yarda su aura maka ita ko tsine maka zatai bazai bika ba dan naga Hajiya niyyar ta kenan idan kaci gaba da jayayya da ita". "Wai taya ma zatai min haka nifa ina da budurwa 'yar sabuwar 'kofa ce kuma ita nake so ba wai Zainab ce bana so ba ni auren had'i ne bana ra'ayi". "Ka daina wani 6ata bakin ka kana maimaita magana tunda baka so ba wani shege da zaiyi maka abi da baka ga dama ba ka manta da wata Hajiya ka daina tada zancen dan Allah yanzu nafi tunanin gigin tsufa ne yasa take yin duk wadannan abubuwan abinda za'ai kawai kayi wa babanku magana akai maka kud'in gaisuwa can sabuwar 'kofan kayi auren ka kawai shine magana ina ruwanka da wata Zainab yadda take ganin tana da ilmi gashi tana da hanyar samun kud'i ai raina naka arzikim zatai ko ka aure ta ba za ta baka daraja ba kayi tafiyar ka kaje ka karya ka manta da batun". "Ok tom shikenan Mama hakan zanyi kawai a wuce gurin nayi maganin ta" yana fad'in haka ya fita Asiya da tabi kofar daya fitan da kallo tsaki taja tana cewa "wallahi indai ina raye babu wanda ya isa ka auri Zainab a gidan nan idan guguwa suke bu'kata ni masifa ce zanyi maganin duk d'an iskan da yake neman saka ka Zainab cikin rayuwar Zaid haba dan jaraba mutum da ransa da lafiyar sa a nemi hana shi ya sha'ki iska me kyau" ta karasa maganar tana jan tsaki ji take kamar ta tashi taje ta yiwa Hajiya magana akam takura Zaid da take sai kuma ta fasa domin tasan sharrin ta yanzu Habibu yana dawowa zata had'a mata bom abinda batai bama saita fad'a. Ko da dare bayan sallar isha da Hajiya taga Habibu bai shigo ya gaida ita ba yasa ta saka akai mata kiran sa lokacin bai jima da dawowa ba ko wanka baiyi ba saboda gudun laifi yasa ya amsa kiran nata yana shiga da'kyar ta bari suka gaisa kamar wani zai riga

Chapter 12 of 34