Share this page
bakai a hankali ba wata rana za'ai bakai dan tuntuni na fahimta wannan talaucin da kake fama dashi sune sila basu da 'kashin arziki kaga fa duk sauran 'yan uwanka kowa aikin gwamnati yake yi kuma kaima kayi karatun nan amma auren dangin tsiya da ba'kin jini ya jawo maka ka 'kare a gaban bencin kayan miya ana mi'ko maka d'ari uku d'ari biyar ka na zubawa a leda kana mi'kawa" sosai ransa ya 6aci ganin yadda Hajiya take masa a gaban 'ya'yansa da 'ya'yan 'yan uwansa bai kamata ba..................... "Tashi ka bani guri kuma ka tabbata sa'ko na yaje gurin wannan uwar gulmar" yaji muryarta ta katse masa tunani mi'kewa yayi yana d'aukar kayan daya shigo dashi a hannunsa yace "saida safe Hajiya" kamar zatace masa kowa ya kwana lafiya shi yaso sai kuma a she'ke tace "toh" fita yayi ya wuce tasa kofar kai tsaye d'akin Umma ya shiga bai shiga d'akinsa ba saboda ranar a d'akinta yake har lokacin tana zaune a yadda take tayi tagumi hatta gurasar da Zainab ta kawo mata bata ko kalli yadda take ba balle ta samu damar ci sallamar dayai ce tasa ta d'ago tana d'an sakin fuskarta saboda karya fahimci halin da take ciki tace. "Sannun da dawowa" zama yai yana sauke numfashi ransa na sake 6aci ganin yadda ta jefasu cikin damuwa yace "kinyi magana da Zainab ne yau"? Kaita d'aga tana kallon sa tunda taji ya tambaya tasan daga kofar Hajiya yake shima yaje ta tsiyata shi kenan............................ "Tunda kinyi magana da ita gobe da sassafe idan kinyi sallar asuba ki kirata kice ta taho a goben karta 'kara kwana saboda Hajiya ta fad'a min wata magana da banji dad'in ta ba kuma tayi rantsuwa akai cewa indai bata dawo a gobe ba kema sai kin bita" yana rufe baki Umma tai murmushin da yafi kuka ciwo tana cewa "Zainab ta dawo tana d'akinta tun d'azu ta shigo". "Au ta dawo"?. "Eh ta dawo tana nan". Jin haka yasa ya mi'ke yana fita 'kofar d'akin Zainab yaje yana cewa "Zainab Zainab" daga d'aki tace "na'am Abba" tashi daga kwancen da take tayi tana zuwa bakin kofar ta bud'e tare da fitowa ta dur'kusa a gabansa tana cewa "ina yini ya aiki fatan ka dawo lafiya"?. "Lafiya kalau Zainab fatan kema kin dawo lafiya ya kika baro su Umman da wajen Alhaji Balaraben duk suna lafiya"? Kaita d'aga tana cewa "eh lafiyarsu kalau". "Masha Allah dama gaisawa kawai zamuyi naga lafiyarki tashi ki koma ki kwanta saida safe" mi'kewa tai tana cewa "Allah ya tashe mu lafiya Abba" Amin yace yana yin wajen kofar d'akinsa ita kuma ta koma d'aki ta kwanta kamar yadda take d'azu. ✍️YUSRAH MUSA ABUBAKAR 💓ZUCIYAR ALIYU CE💓 @YMA DUTSE PAGE 12 Washe gari da asuba bayan Abba ya dawo daga masallaci sanin da yayi Zainab ta riga ta dawo shiyasa ya shiga 6angaren Hajiya zai gaida ita cikin 'kwarin gwiwa ba fargabar fad'an Hajiyan za tai masa daidai ya zauna sun gaisa tun bai sauke numfashi ba ya ji tace "Ina sa'kona Abdullahi" da 'yar alamar tambaya yace "wanne sa'ko ne Hajiya"?. "Au harka manta saboda an shanye ka baka damu da umarni na ba"? Cikin ladabi ya sake du'kawa yana cewa "kiyi hakuri Hajiya sa'kon ne na manta" cikin fad'a tace "ai gara daka manta amma bazaka manta ba daga lokacin dana mi'ko maka biro da takarda nace ka saki wancan matar taka zaka tuna ko"? Jin abinda tace yasa ya sauke ajiyar zuciya yana cewa "kiyi hakuri Hajiya sha'afa nayi Zainab ta dawo tun jiyan anan ta kwana". "Au ta dawo tun jiyan shine saboda rashin arziki data gada a gurin uwarta shine bata zo ta gaida dani ba har yau zata shigo tazo ta sameni sai naci mutuncin ta"?. "Dan Allah Hajiya kiyi hakuri bansan bata zo ta gaida ke ba amma zan mata fad'a karta 'kara" tsaki Hajiya tai tana cewa "tama 'kara d'in man ni dama da ita da babu duk uwarsu d'aya yarinya ta'ki aure kun zuba mata ido babu ruwanku ko saita zama tsohuwa a gida ne ko kuma auren ne baza tai ba ko wanda zata aura ne bata dashi fad'a min naji"?. "A'a tana dashi amma ban sani ba ko basa tare yanzu". "Waye shi d'an waye a ina yake"?. "Ina jin kamar dai anan anguwar yake saidai bansan ta wajen wanne 6angaren ba abinda na sani kawai dai tace min malami ne a islamiyyar su". "Hum yayi kyau Allah ya kawota gurina zata sani ne sai naci mutuncin ta wanda ranta zai 6aci tayi zuciya ta fito da mijin aure inace ga Rafi'atu nan da Ralmat duk sa'annin tane kowacce tayi aure harda yara suke dashi amma ita ta tsaya ruwan ido indai tai za6en tumun dare wallahi a kanka masifa take bani ba kune zaku ri'ka sha'kar ba'kin ciki kuna mata aiken abinci daga Nan kunga babu amfani kenan kun siyar da akuya tazo tana gogar muku katanga" sosai ran Abba ya 6aci baya jin dad'i duk lokacin da Hajiya ta fad'i wani abu akan Zainab saboda shi yasan wace 'yarsa yasan irin hankali da nutsuwarta ya tabbata jinkirin aurenta alkhairi ne saboda kullum yana Mata addu'ar ta samu miji na gari yasan hakan ne yasa lokaci yake 'kara ja addu'ar sa ta kar'bu insha Allah Zainab zatai aure zata bar gidan nan duk daren dad'ewa............ "Na gama magana dakai tashi ka bani gu" yaji muryar Hajiya ta katse masa tunani kaiya girgiza yana mi'kewa zai fita ya aje mata d'ari biyar wanda tun bai gama kai ga ajewar ba tace "me zan gani wacce lalacewar ce wannan"? Ta fad'a tana d'ago da d'ari biyar d'in alamar batai mata ba shiru yayi ya rasa me zaice mata "dakai fa nake ka rasa me zaka bani sai d'ari biyar wadanda ban haifa bama suna min babbar kyauta har dubu goma Allah yayiwa yaron nan Aliyu d'an gidan Alhaji Amadu albarka ranar Samar ya kawo shi dubu goma 'kal-'kal suna walwali a mi'ke ya d'auka ya bani balle kai anya kuwa lafiyarka kalau"?. "Lafiya kalau nake Hajiya kud'in ne na siyo abun karyawa jiya da dare kuma yanzu zanje na bada kud'in abincin rana dana dare shiyasa kud'in suka 'kare babu wani a gurina iya d'ari biyar d'ince tai saura da nayi lissafi saboda jiya na bayar da kud'in sarin kayan miya bani da komai". "Fatara a kanka ta 'kare ne kullum da anyi magana sai kace baka da kud'i wannna kiran babun da kake shiyasa baka gaba abun ma ya shafi 'yarka ta'ki auruwa kowa zai wuce yana kallonka a gaban bencin tumatur kana cinikin naira dari biyu d'ari uku ba albashi kake d'auka ba waye dama zaizo yace yana sonta yasan ko kayan d'akin arziki ba samu zaiyi ba balle kayan gara" rufe ido Abba yayi yana girgiza kai zuciyarsa gaba d'aya ta 6aci da sauri ya fita daga gurin Hajiyan ko sallama baiyi mata ba yasan idan da rikicin tsufa a wadannan maganganun nata tofa akwai 'kiyayya ma yana so yasan meyasa bata son Zainab amma har yau ya kasa ya ganewa shi dai yana son kayarsa domin koda duniya ne suka taru suke 'kin Zainab shi kad'ai zai so abarsa domin cikin 'ya'yansa babu wanda ya shiga ransa kamar Zainab saboda ladabi da biyayyarta ga tarbiyya. Zainab tana d'akin ta bayan datai sallah bata fito ba saida gari yayi haske sannan ta fito ta shiga gurin Umma ta gaida ita saboda gudun laifi yasa tace mata ta tashi taje ta gaisar da Hajiya amma sakamakon ba tafiyar shiri tai ba bata siyo tsarabar komai ba yasa bata jeba ta bari Sameer ya shigo ta tambaye shi idan ya siyo mata idan kuma ya manta saita fita ta siyo da kanta domin da taje gurin Hajiya ba tsaraba gara ta ha'kura da xuwa gaida ita. Shi kam Sameer bai shigo gidan ba har wajen sha biyu sannan yazo mata da takarda a lokacin tana gurin wanke-wanke tana taya Umma ayyuka ya shigo tsayawa yayi daga wajen kofar shigowa yana cewa "Zainab zo nan" kallon inda yai maganar tai tana mi'kewa da fara'ar ta tace "Yaya Sameer ina kwana''? Kaiya d'aga yana cewa "lafiya na tashi akwai biro a gurin ki ne"?. "Eh da akwai baka zanyi"? Zama yai a kan wata farar kujerar roba dake kofar d'akin Zainab din yana cewa "uhm kawo min abu zanyi dashi" shiga tayi tana cewa "to bari na duba maka jakar islamiyya ta" yana zaune ta d'auko masa ta bashi zata koma gurin aikin yace "a'a Zainab dawo nan zo ki cike" jin abinda yace yasa da mamaki ta juyo tana kallon sa tare da nuna kanta tace "nice zan cike"?. "Eh kar6i" ya fad'a yana mi'ka mata 'kure takardar tai da kallo tana cewa "amma Yaya Sameer takardar ta mene zan cike"? Murmushi yai shima yana kallon takardar yace "form ne na makaranta" da sabon mamaki tace "form na makaranta kuma waye ya sai mun makaranta Yaya Sameer"?. "Ba ruwanki kawai kizo ki cike min" dawowa tai tana kar'ba tare da zama akan wata 'yar 'karamar kujera ta aikin gida ta fara cikewa fitowar Asabe kenan daga d'aki ta tashi daga barcin hutu ganinsa zaune ga Zainab na cike paper yasa ta aje butar data d'auka tana cewa "Sameer me kake anan"? D'agowa yayi yana kallon ta yace "ina kwana Umma"?. "Lafiya nace me kake anan"?. "Takarda ce na kawowa Zainab ta cike". "Takarda ta meye ko aikin polio ka samo mata"?. "A'a ba polio bane". "To takardar ta meye"?. "Form ne na makaranta" zaro ido Asabe tai tana cewa "form na makaranta karatu zata d'ora"? Amsa ya bata da "eh" daidai Zainab ta mi'ko masa takardar tana cewa "gashi Yaya Sameer na gode" ta fad'a tana mi'kewa ta koma gurin aikinta da kallo Asabe ta bita cikin takaici kafin ta dawo da hankalinta kan Sameer da shima ya mi'ke yana shirin fita tace "kenan kaine ka biya mata taci gaba da karatun"?. "A'a bani bane ni ina naga kud'in dazan biya mata tai karatun jami'a"? jin abinda yace ta sake jefa masa tambaya "ban gane bakai bane to waye ya biya mata"?. "Wani ne". "Wani kuma Sameer karka raina min hankali fa bana son munafirci uban wa take dashi wanda zai biya mata kud'i tayi karatu a wannan tsadar rayuwar"? Shiru Sameer yai bai sake magana ba taya zai fad'a mata cewa Aliyu ne ya siyawa Zainab makaranta bayan ita kanta Zainab d'in batasan yana sonta ba kawai zaman lafiya ya samu ya fita karma Asabe ta 'kureshi da tambayoyin har yayi 6arin zance juyawa yai zai fita ta ri'ko rigarsa tana cewa. "Sameer ka fad'a min gaskiya kona tsine maka waye ya siya mata makaranta kaine"? Kaiya girgiza yana cewa "wallahi Umma bani bane wani ne" a masife tace "to waye wanin inda kana da gaskiya ka fad'a min wanda ya siya mata munafirta ta kake Sameer wato kafi d'aukar Zainab wacce kuke uba d'aya da muhimmanci akan Bilki da kuke uwa d'aya uba d'aya ko". "Ba haka bane Umma dan Allah ki fahimta wallahi bani na siya mata ba nima d'an sa'ko ne" kallo inda Zainab take zaune Asabe tai tana ta'be baki tace "a iya sanina tunda Zainab ta taso ban ta'ba jin ance ga wani fitaaccen saurayi yazo gurin taba sai wannan fatararran malamin islamiyyar tasu waye sunan nasa"? Murmushin daba shiri Sameer yayi yana d'an girgiza kai yace "a'a bashi bane bansan ma wani Yaa sayyadi yana sonta ba sai yanzu naji a gurinki" yana fad'in haka ya juya ya fita cizon yatsa Asabe tai tana komawa ta d'auki butar da zata shiga band'aki tana cewa "humm zanga wannan munafikin ne ya siya miki makarantar idan tai tsami zamuji basai mun tambaya ba munafikai kawai daga ke har Sameer d'in zai dawo ya same ni ne shashashan yaro" shiru Zainab tai ko tari duk da taji zafin maganar da Asaben ta fad'a saidai ya zatai tunda uwace a gurinta bata da bakin da zata bud'e ta rama damuwarta Allah ya had'ata da alkhairinsa........................ Kwacaff taji 'kara a kusa da ita da sauri ta d'ago a tsorace tana kallon Asabe wacce ke tsaye a kanta tana sake turo mata kwanukan data d'ebo daga d'aki tace "yar aiki ki had'a da nawa kwanukan ki wanke dama hakan ne ya dace dake tunda kin 'ki aure saiki zama baiwar mu ashe ware nawa kwanukan kike saboda baki gaji arziki ba kodan ni ban haife kiba shiyasa kika ware nawa cikin naku kika mayar dasu gefe"? ta tambaye ta tana sake d'ebo su ta watso mata su cike da rashin son zaman lafiya shiru Zainab tai ko d'agowa batai ba balle tace wani abu sai kwanukan data tattara ta saka a kusa da nasu kafin ta gama itama ta wanke mata baki Asabe ta ta'be tana juyawa ta shiga d'aki tana rera wa'ka. Tas Zainab ta wanke mata kamar yadda ta wanke nasu ta d'auka har kofar d'akinta takai mata kamar dai babu abinda ya faru muryarta a daidai tace "gashi Maman Bilkisu na gama" ta fad'a tana ajewa saidai ko juyawa batai ba Asabe tace "shigo ki kawo min kamar yadda kika kaiwa taki uwar ko itama a kofar d'akin kika aje mata ki kace gashi ta fito ta d'auka"? Kai Zainab ta girgiza tana du'kawa ta d'auki kwandon ta shiga da sallama ta aje mata sannan ta fito ta d'auki nasu takai musu shi kitchen ta shiga d'akin Umma ta share ta share nata sannan ta share tsakar gidan ta wanke band'aki saida ta gama komai sannan ta shiga tai wanka ta shirya tana zaune lokacin tana shirin tashi taje gaida Hajiya tunda har yanzu bata samu ta shiga ba hijab d'inta ta d'auka da kayan tsarabar da tasa Sameer ya siyo mata ta koma d'akin Umma ta sanar mata zata shiga gurin Hajiya..................... We will meet again🤝. ZUCIYAR ALIYU CE @YUSRAH DUTSE Chat with me. +234 816 098 3083 PAGE 13 Ta fita daga kofarsu kenan taga Afifah ta fito ita kuma daga 6angaren Hajiya ga Balki da Haulat sun biyota kowacce tana so dole sai Afifah tasan da ita kodan su samu kusancin 'kawance su ri'ka shiga gidansu murmushi Zainab tai wanda ganinta yasa Afifah tahowa da d'an gudu tana rungume ta cikin farin ciki tace "kai Hajiya zee-zee nayi kewarki sosai wallahi matafiya kamar bazaki dawo ba gashi idan na kiraki ko kad'an bana samunki kullum wayarki a rufe meya faru ne"? Har lokacin da murmushi akan fuskar Zainab tace "ayya kiyi hakuri Afifah acan ne kwana biyu da zuwana na cire Sim tsautsayi wallahi shikenan na rasa shi babu inda ban duba ba ya fad'i shiyasa kika jini shiru sai d'ayan sabon Sim d'in da nayi lokacin dana kusa tafiya shi kuma sakamakon babu islamiyya yasa bamu had'u na baki ba" d'an had'e rai Afifah tai tana cewa. "Kuma wato shine kikai tafiya sama da sati hud'u ko sallama baki min ba ko kamar ni Afifan ki guda ko sanarwa saida na gaji nazo na tambayi Yaya Sameer yace min kina D'an Yana na gode" had'e hannunta Zainab tai tana cewa "ina neman afuwa nayi laifi Afifah nasan ban kyauta ba kiyi hakuri gani aina dawo ko kamar banje ko'ina ba yanzu haka zaki ji". "Uhm haka ne mu karasa d'akin naki ko,? dama ke nazowa sannu da zuwa saboda d'azu Yaya Sameer sun shiga gidan tare da Yaya discipline nake tambayar sa ke shine yace min kin dawo" da alamar tambaya Zainab tace "waye discipline kuma a gidan ku"? Dariya Afifah tai tana cewa "humm Yaya Aliyu nake nufi boss me zamani kenan". "Ok ya dawo ne"?. "Eh ya jima da dawowa ma neman komawa yake kwanan nan" numfashi Zainab ta sauke tana cewa "Allah ya taimaka". "Amin Hajiya zee-zee muje ki bani tawa tsarabar mana". "Tab waya fad'a miki na siyo kayan tsaraba nikam ban siyo komai ba saboda ba tafiyar shiri nayi ba kwatsam abun yazo min". "Au nan nufinki nazo miki sannu da dawowa har gida kice min babu kayan sannu da zuwa tab aiko dole ki bani wani abu". "Indai ba kaina zan baki ki tafi dani ba da gaske nake ban zo da komai ba kinga wannan ma klin ne saboda halin tsufa irin na Hajiya na tabbata naje gaida ita babu kayan sannu da zuwa saita maganta min sai d'azu Yaya Sameer ya siyo min a shago yanzu zan kai mata amma tunda kin zo min kawai mu komai nan da la'asar naje gurin nata" kai Afifah ta d'aga tana cewa "ok muje to" juyawa sukai suka koma kofar su Zainab d'in wanda Haulat taja tsaki tana cewa "gaskiya Zainab d'in nan anyi munafika mai mugun hali ji kawai ta ganmu tare maimakon tace mu tafi gurin Hajiyan gaba d'ayan mu sai tawani ce su tafi d'akinta" baki Balki ta ta'be tana juyawa zata koma tace "damuwarta ce ba tawa ba 'kawance ne idan naga damar yi da 'kanwar Aliyu ko bata so sai mun 'kulla kuma saina raba su itama ai zilama ce tasa ta le'ke mata kina gani fa hatta islmaiyya idan muka je suna tare ko'ina suna manne sannan idan an taso ma saidai su ware kansu su taho tare tsabar neman suna" bin bayanta Haulat tai suna komawa gurin Hajiya su Zainab kam suna d'akinta tun daga waje idan ka shiga kofar tasu zaka ri'ka jiwo muryoyinsu suna dariya da zance cikin nishad'i na an dad'e ba'a had'u ba Asabe na jinsu daga d'aki tana aiko musu da zagi wai sun dameta sun cika mata kunne da hayaniya kamar suna kasuwa. Afifah bata bar gidan ba saida akai kiran sallar azhar sannan tai sallah lokacin Umma ta gama abincin rana taiwa Zainab magana tazo ta d'iba musu abinci fur Afifah ta'ki ci saida 'kyar shima baifi loma biyar ba tace ya isheta rufewa Zainab tai tana mi'kewa zata raka Afifan kawai ta d'auki kayan da zata kaiwa Hajiya da nufin idan ta rakata ta dawo saita shiga ta gaishe da ita. Suna tafe suna d'an hirar da basa gajiya da yinta saida sukai nisa d'in har ta kusa rakata kofar gate d'in gidansu cak ta tsaya tare da cewa "Afifah bari na koma gida daga nan" juyowa Afifah tai tana kallon ta da alamar tambaya tace "haba Zainab ina laifin ki 'karasar dani har gida dan Allah tunda munzo nan kinji"? Kaita girgiza tana cewa "a'a daga nan d'in dai zan koma kiyi hakuri". "To saboda me"?. "Saboda bazan iya 'karasawar ba kalli man Yaya Sameer yana rumfar kofar gidan ku ga soldier's sannan kuma ga Yayan ki shima yana gurin" kallo gurin Afifah tai tana girgiza kai kafin ta sake juyowa inda Zainab d'in take tana cewa "me zasu tare miki zasu hanaki wucewa ne ba ruwan su dake sannan ba gurinsu zakije ba mu da zamu wuce kawai". "Nifa bazan 'karasa ba Afifah mu rabu anan na koma" ta fad'a tana kokarin juyawa ri'keta Afifah tai tana cewa "wallahi bazaki juya ba mu karasa". "A'a babu inda zanje fa ina da d'inkuna na mutane dana tafi na bari banyi musu ba kuma suna tambaya kawai jeki abinki sai mun had'u a makaranta" had'e rai Afifah tai tana cewa "kai dan Allah Zainab muje dan Allah wai yanzu na tako nazo gurin ki amma ki kasa rakani"? Shiru Zainab tai tana kallo wajen su Sameer tunanin ta yadda zata fara wucewa ta gurin take shiyasa taso ta juya tun anan duk da sukam hankalin su ba'a inda su Zainab d'in suke yake ba................. "Kawai ki koma kiyi d'inkin ki na tafi sai mun had'u a islamiyyar" Afifah ta fad'a tana yin gaba d'an kallonta Zainab tai tasan bata ji dad'i ba na 'kin raka ta din amma ya zatai bata son hakan saidai data wuce ta wancan majalissar mazan ba nikaf a fuskarta gara ta ha'kura duk muhimmancin abinda take son tayi tana kallo har Afifah taje kofar gate d'in gidansu aka bud'e mata ta shiga numfashi ta sauke tana juyawa ita ta koma gida. Shigar Afifah gida duk suna parlor a zaune wajen Momy shiyasa itama bata wuce ba ta zauna a gurin kallonta Fati tai tana cewa "kai wai harkin dawo daga gurin ta"? "Eh man aina dad'e ma a hakan 'kin rakoni tayi har kusan nan muka zo amma tace saidai na taho ita tana da ayyuka" kai Elham ta jinjina tana cewa "nifa tunda nake ban ta'ba ganinta a gidan nan ba Aunty Afifah meyasa bazata ri'ka shigowa bane"? Kafad'a Afifah ta d'aga alamar oho tana cewa "nima ban sani ba na kasa fahimtar dalili har gobe amma Amirah ta dawo daga gida ne naga kamar ba'kuwar mota a can"?. "A'a bata dawo ba saidai idan motar Yaa Afif kika gani". "Ok yana ciki ne"?. "A'a bai shigo ba tunda ni ban ganshi ba cewa nayi maybe ko tasa ce tunda ni banji Momy tace Daddy ya sayi mota ba balle kuma Yaya boss kinga kuwa ai saidai ta Yaa Afif d'in" mi'kewa Afifah tai zatai stairs harta fara takawa ta tsaya ta juyo tana cewa "Momy meyasa Amirah tun ranar data bar gidan nan bata sake dawowa ba"? Girgiza kai Momy tai tana cewa "taya zan sani tunda ba fad'a min tai ba ni washe garin ma bansan ta tafi gidan nasu ba domin ba had'uwa mukai ba" cikin kokwanto Afifah tace "to kodai hana ta komowa sukai a gidan"? "A'a bazasu hanata ba kawai dai ra'ayin tane ko kuma akwai uzurin da yasa bata dawo d'in ba inace tabar trolley nata anan ko dashi ta tafi"?. "Bata tafi dashi ba yana nan amma nayi mamaki da bata dawo ba tun a ranar ko washe gari ba bayan tasan Yaya discipline yana gari" da alamar tambaya Momy tace "kamar ya yana gari meyasa sai dan yana gari ne kad'ai zata zo gidan nan ta zauna bayan ta riga ta saba hakan ya zame mata jiki"? Dariya Afifah tai tuna abinda ya faru tsakanin ta da Aliyun ranar kamar zata cewa Momy ga dalili saboda Aliyu yace mata yana da wacce yake so sai kuma ta fasa fad'a kawai ta girgiza kai ta wuce. Wucewar ta da kamar mintuna biyar Aliyu shima ya shigo gidan amma ba tsayawa yayi a parlor ba wucewa yayi bayan ya wuce ne Fati ta sake matsawa kusa da Momy sosai tai 'kasa da murya saboda gulmar da zatai tace "Momy Yaya boss yana da budurwa ne"? Jin tambayar datai mata yasa Momy kallonta tana cewa "a ina kenan ni ban sani ba idan ma yana da itan kenan" kallon inda Aliyun ya shiga tai tana cewa "to amma meyasa idan baya nan Amirah ko ziyara bata zuwa gidan nan sai taji labarin ya dawo a ranar zaki ganta ta ciko akwati da kaya tazo meyasa"?. "Taya zan sani tunda ba fad'a min dalilin ta nayin hakan tai ba" numfashi Fati ta sauke tana cewa "alamar karfi dai tana ga mai 'kiba nasan ruwa baya tsami banza dole akwai wani abu a 'kasa bazai wuce tace nan gaba tana son Yaya boss ba" murmushi Momy tai tana kallon Fati datai maganar tace "ke kam kin cika sa ido tunda sun dad'e tare suna karatu sun saba mene damuwarki da tambaya irin haka idan ma soyayya suke naku addu'a ne Allah ya bashi mace ta gari wannan shine fatan mu" hannu Elham ta d'aga tana cewa "Amin Momy dan wallahi nikam haka kawai a raina banji Amirah tayi min ta zama matar Yaya boss ba gara wata dai". "Kuma watan kika san 'yar waye mayya ce ko kuma mai 'kulle 'kullen asiri ce mu shiga uku ba gara auren wacce ka sani ba" Fati tai maganar tana mayar da hankalinta kan Momy taci gaba "Momy koba haka magana ta take ba nasan dai duk tsiya da mutum ya auro macen da baisan halin gidansu ba gara ya auri wacce yasan komai nata"? Kai Momy ta d'aga tana cewa "eh haka abun yake wani lokacin amma fa koda 'yar gidan ya aura itama zata iya yi masa 'kulle 'kullen saboda duniya ba tabbas ba kowa ake yarda dashi ba amma watakil wacce zai auro daga can nisan duniya ya kawota cikin ku saita zame muku garkuwa ta zama silar wani abu naku wanda zaku ji dad'in sa koda ace bata nan zaku ri'ka tunawa da ita kuna alfahari da

Chapter 5 of 34