nayi ta neman ki"? Ta'be baki Zarah tai tana cewa.
"Akan me zan fad'a miki sai kace wata uwata dole sai nace miki na tafi siyan ice-cream yanzu da kika ganni dashi ai ya baki amsar tambayar ki ko"? Kai Nihal ta jinjina tana kallon ta tace "bansan yaushe kika koyi raini ba amma bari muje gidan wallahi saina had'a ki da Yaya Ammar yayi min maganin ki" tana rufe baki Zarah ta murgud'a mata baki tana gatsinin ta ran Nihal a 6ace ta d'aga hannu zata mareta a fuska hannu Zarah ta saka za ta tare marin kawai bata sani ba ta buge glass d'in dake fuskar Nihal ya fad'o kasa da sauri Nihal ta sunkuya tana laluben ta inda zata ji glass d'in ta d'auko jin bata ta'bo shi ba yasa tace.
"Zarah ki d'auko ki bani baza kizo ki mi'ko min ba" tsaye Zarah tai tana gefe tana kallonta ta'ki magana Shareef dake cikin mota tsananin mamaki ne ya kusan sumar dashi ganin da glass d'in ya fad'i tana laluben sa alamar bata gani kenan sai dashi dama ciwon ido take shiyasa yake yawan ganinta a hospital, baki Badiyah dake tsaye ta bud'e tana kallon su ganin yadda Nihal ta gigice yasa tace.
"Ayya Allah sarki ashe bata gani saida glass d'in ni kuma har nayi mata muguwar fassara astagfirllah Allah na tuba bari naje na d'auka na bata wannan 'kanwar tata anyi mara kunyar yarinya" ganin da Baby tayi zata tafi inda Nihal take yasa ta ri'ke ta tana cewa "wallahi baza ki taimake ta ba na tsane ta bana son ganinta da nasan zan had'u da ita bazan zo gurin nan ba" da mamaki tace.
"Haba Baby ke fa musulma ce sannan taimako take nema".
"Ai ba a wajen ki take neman taimakon ba ko ke kad'ai ce mai rai a gurin".
"Ni banyi la'akari da kowa da yake nan ba zanje na taimake ta Allah yana taimakon bawa ne matu'kar bawan yana taimakon d'an uwansa musulmi kin gane"? Kai Baby ta girgiza tana cewa "ban gane ba" zaro ido 'kawar tayi da mamaki zatai magana suka ga Shareef wanda basu san da zuwansa gurin ba sakamakon bada motar sa ya fito ba ta Mami ya d'auko da sauri suka ga ya fito daga cikin motar ya karasa ya d'auka ya saka towel ya goge yace.
"Kar'bi" ya fad'a yana kara Mata a hannunta kar'ba tayi ta mayar dashi idonta tana sauke ajiyar zuciya tace "na gode" kai ya d'aga mata zai juya tace "amma kamar kaine wanda nayi wa laifi a hospital kwanan baya ko"? Jin abinda tace yasa ya kalleta yana girgiza yace.
"No baki min laifi ba ki saka a ranki kece da gaskiya bayan wayarki data 6aci wanne rashin gaskiyar za'a baki".
"Shikenan na gode".
"Karki damu" yana fad'in haka ya koma ya kulle motarsa ya shiga gurin ko lura da baby baiyi ba wacce tsananin rud'ewa ta kama ta ita kam Nihal tana ganin ya bar gurin itama ta juya ta fita domin Zarah tun ganin datai yazo ya d'auki glass d'in da gudu ta bar gurin saboda kar Nihal ta saka glass d'in taga tana nan ta'ki mi'ko mata.
A mota ta samu Zarah sai kallonta take bayan ta shiga bata kula ta ba har driver ya tu'ka motar suka bar gurin suna zuwa kuwa sukai sa'a Daddyn su yana nan a parlor Nihal ta tsaya bayan ta gaisar dashi tace "Daddy daga yau warewa Zarah nata driver da zai ri'ka zuwa d'auko ta domin na gaji da halinta tun ina dannewa yau ta kaini bango".
"Me ya faru"?.
"Wai Daddy yarinyar nan ta buge min glass ya fad'i tana ji ina ta 'kwalla mata kiran tazo ta mi'ko min ta'ki sai wani saurayi ne ya taimaka min".
"Subanallahi ita Zarah d'in"?.
"Eh Daddy wallahi na gaji da halinta na rashin ji bazan iya ba kawai a samar mata wanda zai ri'ka d'aukar tsiyar ta amma bani ba".
"Ok na fahimta ina ita Zaran take"?.
"Ana yin parking da motar ko bari ya kashe batai ba ta bud'e murfi ta fito ta kofar baya ta shigo part d'in mu".
"Shikenan yanzu tashi kuje kuyi wanka da sallah kuzo kuci abinci ita kuma nida ita ne ki rabu da ita zanyi maganinta sannan daga yau driver na shine zai ri'ka kaita" murmushi Nihal tai cikin jin dad'i tasan ko ba komai an wuce gurin tunda har Daddyn yace haka tasan idan zai tafi gurin aiki tare zasu tafi ya sau'ke ta haka idan an tashi zai tura driver ya d'auko ta ya dawo da ita gaskiya bazata taji dad'i ita kad'ai ba amma tunda haka ta za6a shikenan.......................
ZUCIYAR ALIYU CE...............
YMA DUTSE JIGAWA VNTRS.
.................PAGE 26
Su Afifah suna zaune a parlor gaba d'ayan su harda Afif daya dawo daga gurin aiki ko part d'insa bai shiga ba saboda ya d'ebo yunwa yana zaune tare da su Momy ana zance suka ji sallamar Amirah kowa zuba mata ido yayi harta karaso ta zauna Momy ta fara gaisarwa sannan suka gaisa da Afifah sauran ma suka gaishe ta.
"Fati tashi ki d'aukowa Amirah lemo da cup man" to Fati tace tana mi'kewa shiru Amirah tai so take ta tambaye su ina Aliyu kuma tana tunanin ta yadda zata tambaya d'in da kamar a bedroom suke su kad'ai zata iya tambayar Afifah.
Har Fati ta d'auko juice da kofi ta kawo mata bata sani ba saida Momy tayi mata magana sannan ta dawo daidai cikin hayyacinta amma data zuba ma kur6a d'aya tayi ta aje tai shiru kallonta Momy tayi cikin kulawa ganin ta d'an rame kad'an tace.
"Amirah ko baki da lafiya ne"? Kaita d'aga a sanyaye muryarta a hankali tace "wallahi nayi zazza'bi kwanan nan shiyasa yau ma a kwancen nake kawai dai cewa nayi bari nazo na gaishe ki saboda na d'an yi yawo jini na ya tsinke".
"Kin kyauta kuwa ni da naga shiru-shiru ma baki dawo ba nasa Afifah ta kira ki kika ce lafiya kalau kina dawowa shiyasa daga haka na bar batun".
"Eh a lokacin nayi tafiya ne naje Abuja gidan Aunty Fadeelah ban dad'e da dawowar ba na fara zazza'bin kuma asma ta ta tashi".
"Ayya babu wanda ya sani ai da za'a je a dubo ki kuma baki kira Afifah kin fad'a mata ba Allah ya 'kara sau'ki".
"Amin" Amirah tace tana kallon Afifah tayi mata magana da ido kaita d'aga tana mi'kewa suka hau stairs tare bedroom d'insu suka shiga akwatin Amirah dake aje Afifah ta d'auko tana kawo mata zama a gefen gadon Amirah tayi tana zuge zif d'in ta soma fito da kayan tana cewa "dole idan na koma na baiwa mai yi mana wanke ya d'auraye min su saiya goge min sun d'an yi 'kura".
"Wai nikam Afifah ina Aliyu ne naga motarsa a parking space amma kuma naga an rufeta da rigar rufe mota ko ya koma ne"?.
"Eh ya koma bai kira ki ya fad'a miki ba"? Shiru Amirah tai tana kallon waje daya daga baya tace "taya zai fad'a min ban sani ba sai yanzu dana kasa ha'kura na tambaya amma ko ba komai ya kirani kota waya ne ya fad'a min nayi masa fatan alkhairi".
"Maybe zai kira ki daga baya" Afifah ta fad'a tana dariya numfashi Amirah ta sauke tana cewa "wanne irin zai kira ni tun da bai kirani ba sanda ya tafi sai yanzu ya dad'e fa da tafiya ko"?.
"Ya dad'e man dama ai ba wani dogon hutu ya d'auka ba sai ranar daya sake dawowa kuma" kai Amirah ta kad'a tana cewa "Allah ya dawo dashi lafiya" daga haka bata sake cewa komai ba ta fara kad'e kayanta tana linkesu tana mayarwa cikin trolley Afifah kuma ta shiga wanka sakamakon lokacin tafiya islamiyya ya kusa sanda ta fito Amirah harta gama ta rufe akwatin da wayarta a hannunta tana dubawa jiran Afifah tai ta shirya ta saka hijab d'in islamiyyar da nikaf ta d'auki jakarta sannan suka fito tare ganinta da akwati yasa Momy cewa.
"Wai tafiya dashi zakiyi shikenan kuma na d'auka kinzo ki d'an yi mana sati d'aya ne"?.
"A'a wallahi Momy zan dawo nayi muku satin amma ba yanzu ba".
"Ok to mun gode ki gaida maman naki".
"To Momy insha Allahu zata ji" kallon Afifah Momy tayi tana cewa "Afifah kiwa driver magana ya kaita" kai Amirah ta girgiza tana cewa "a'a da mota nazo tana harabar gidan".
"Ok to ba damuwa ki gaida gida" to tace suna fita tare da Afifah ita ta shiga motarta Afifah kuma ta fita daga gidan har tayi tunanin zuwa gidan su Zainab ta gani ko bata taho islamiyyar ba sai kuma ta fasa ta wuce kawai saidai tana shiga ta hangota suna tsaye tare da wata suna zance murmushi tai bayan ta karasa tayi musu sallama d'age nikaf d'in tayi tana kallon Zainab tace.
"Hajiya zee zee ikon Allah kin shigo islamiyyar ma bazaki cire nikaf d'in nan ki d'an huta ba"? Kaita girgiza tana cewa "Afifah bazan iya cire nikaf a ko'ina ba saidai a gidan mu balle nan islamiyyar ba maza ne"? Dariya tai tana cewa "da maza man amma ai ba ruwan su da hakan".
"Waya fad'a miki babu inda shed'an baya zuwa ya haddasa fitina shiyasa nake kokarin kare kaina daga shiga fitinar tasa" kai Afifah ta jinjina daidai ya sayyadi ya shigo da littafai a hannunsa fuskarsa fal da gashi irin na ustazai yasha jallabiyya da rawani a kansa yana karasowa suka dur'kusa suna gaida shi amsa yai yana cewa.
"Malama Zainab Abdullahi ki shiga ajin da kike koyarwa ki kar6i hadda" kaita d'aga cikin ladabi tace "to sayyadi insha Allah" saida ya wuce sannan suka mi'ke da yake ajin su Afifan take koyarwa nan suka shiga duk su ukun saida ta fara kar'bar haddan kowa ya biya tukuna sannan tayi musu sabon d'ori suna biyawa har akai kiran sallar la'asar kowa ya fita zasu yi alwala Afifah dake tsaye bayan ta gama alwalar ta baiwa Zainab butar taje ta d'ebo ruwa a famfo ta dawo ido ta zuba mata taga yadda zatai domin kullum haka ake fama bata son aga fuskarta ko kad'an tsayawa tayi ta duba gabas yamma kudu arewa ganin ba namaji a cikin malaman islamiyyar sai zallar mata yasa ta cire nikaf d'in ta mi'kawa Afifah wacce tayi dariya tana kallon yadda fuskarta tata take dad'a wani irin yellow tsabar sabon saka nikaf kaita jinjina tana cewa.
"Allah mai iko kenan kowa da kiwon daya kar'be shi wai makwafcin mai akuya ya sayi kura" mi'kewa Zainab tai bayan ta shafa addu'a tace "ke kuma dawa kike wannan karin maganar"? Ta fad'a tana kar'bar nikaf d'in ta mayar kai Afifah ta girgiza tana cewa "dawa nake kuwa banda ke"?.
"Ni kuma da nayi me"?.
"Da naga kina wasu abubuwan da suke bani mamaki".
"Haka ne"? Da kyau muje kar a shiga sallar muna nan" Zainab ta fad'a tana d'aukar carbinta data aje a gefe ta mayar shi yadda yake a yatsarta ta zura shi sannan suka wuce bayan an idar da sallar kowa ya koma cikin aji aka ci gaba da karatu sai da rana tayi sanyi sosai jikin magriba daidai lokacin tashi ya sayyadi ya le'ko yace tayi musu addu'a sai gobe kuma.
Addu'ar tayi suka shafa sannan d'aya bayan d'aya suka fara fitowa suna fita daga islamiyyar saida kowa ya tafi ya sayyadi ya tura gate d'in ya rufe shima ya nufi hanyar anguwar su.
AYI HA'KURI IDAN AN SAMU TYPING ERROR MATSALAR KEYBOARD NE.
J.W.A
Yusrah Musa Abubakar
@♠Y♠M♠A♠ DUTSE
PAGE 27
Zainab tana shiga ta tarar da Umman ta a kofar kitchen tana zaune akan kujera tana mulmula tuwon shinkafa shiga d'aki tayi ta aje jakarta ta cire nikaf da hijab d'in sannan ta fito tayi mata sannu da gida ta kama mata aikin ita kuma Umma ta mayar da hankalinta kan miya saboda kar Abba ya dawo daga gurin sana'a bata gama ba lokacin anyi kiran sallar magriba Zainab ta saka dukkan tuwon a cooler ta saka murfin ta rufe ta tashi taje tayi alwala ta shiga d'aki bata sake fitowa ba saida taji sallamar babansu ya dawo ta fito tayi masa sannu da dawowa ta koma bayan isha tana zaune a d'aki Umma ta le'ko tana cewa.
"Zainab kizo ki d'auki abinci man" kaita d'aga mata tana cewa "ina zuwa Umma wannan atamfar nake so na karasa yankawa gobe idan Allah ya tashe mu lafiya dana dawo daga makaranta saina fara d'inkin ta" sakin labulen Umma tai tana cewa "to shikenan gashi nan dai a d'aki ni gurin Hajiya zanje" jin abinda tace yasa Zainab mi'kewa cike da fargaba ta fito tana cewa.
"Me zaki yo acan"? Umma dake kokarin saka hijabi tace "bani kad'ai bace taron matan gidan ne gaba d'aya bansan me ya faru ba" numfashi Zainab ta sauke tana cewa "Allah yasa alkhairi ne" daga haka bata sake cewa komai ba har Umma ta fita ita kuma ta koma d'aki samun kanta tayi da kasa ci gaba da yanka atamfar duk jikinta yayi sanyi tasan kiran nan ba kiran alkhairi bane Allah yasa ba akan Umma ko baban su abun zai 'kare ba shiru ta zauna har Sameer ya shigo ganin kofar ba kowa yasa yace.
"Zainab".
"Na'am Yaya Sameer" ta fad'a tana fitowa kallonta yai ganin yadda fuskarta ta nuna alamun da akwai damuwa yace "ina yan kofar suke"?.
"Suna gurin Hajiya".
"Gurin Hajiya kuma me take musu"?.
"Wallahi Yaya Sameer ban sani ba amma dai naji Umma tace taron na duka gidan ne".
"Na duka gidan har yaran gidan kenan"?.
"A'a nufi iya su matan gidan dasu Abba".
"Ok na fahimta yau me aka dafa"?.
"Tuwon shinkafa ne"?.
"Da wacce kalar miya"?.
"Miyar ganye" "ok" kawai yace yana wucewa ya shiga d'akin sa ita ma nata d'akin ta koma kafin Umman ta dawo.
Batun su Umma suna can sun hallara maza su uku mata su shida Hajiya tana zaune daga kan kujera su kuma suna 'kasa a zaune kowa yayi shiru suna sauraron su ji dalilin da yasa ta tara su kallon su Hajiya ke yi d'aya bayan d'aya kafin tayi gyaran murya tana cewa.
"To jama'a salamu alaikum" amsa mata sukai "wa alaikum salaam" kafin taci gaba "nasan wasu daga cikin zasu yi mamakin me yasa na tara ku anan wasu ransu bai so ba amma ni na zama ciwon ido zama dani sai mai ha'kuri ba wani abu ne yasa na tara ku magana ce akan 'ya'yan ku dama ku kanku wanda yaji hukuncin da zan yanke baiyi masa ba sai yakai ni hukumar kare hakkin d'an adam tunda naga so kuke kuna kallo 'ya'yan ku su maida mana gida gidan karuwai to wallahi baku isa ba 'ya'ya sun kawo mizanin aure sun zama gird'a gird'a kamar shanu kuna kallon su kun 'ki ku tsaresu su fad'a muku gaskiyar samarin su na kwarai yau zan kawo karshen komai ta kanka zan fara kai Habibu kaine babba a gidan nan kuma kana samun kud'in da zakaiwa 'ya'yanka kayan d'aki meyasa ka barsu kara zube ka'ki musu aure"?.
Ajiyar zuciya Habibu ya sauke yana cewa "kiyi hakuri Hajiya ba nine na'ki musu aure ba lokacin sune baiyi ba ina gasu Rafi'atu da Aisha da lokacin su yayi na aurar dasu".
"Au abinda zaka ce kenan? Lallai kuwa naji naka" juyawa tai tana cewa "sai kai Aminu meyasa ka'ki kayi wa Atika da Zakiyyah da Rasheedah aure"? Kai ya girgiza yana cewa "Hajiya bani da amsar tambayar ki domin ban 'ki yi musu aure ba komai nufin Allah ne" kai Hajiya ta jinjina tana kallon Abdullahi ta ce "to masu damar ma anyi musu maganar basu aurar da 'ya'yan su ba sunce lokaci ne baiyi ba ina ga kai Abdullahi saidai kar kaji nace haka zuciyarka tayi fari ka sake baiwa Zainab lasisin zama a gidan ka baka isa ba" mayar da hankalinta kan gaba d'ayan su tayi tana cewa.
"Ku bani hankalin ku nan yanzu zan fad'a muku hukuncin dana yanke tunda ku kun garara kuma kar wanda ya kuskura ya musa min dole ku bi abinda zan fad'a ko ranku baya so sannan ko ba kayan d'aki sai kun aurar da yaran nan in yaso ku kaisu da tabarmi".
"Ban tari numfashin ki ba amma Hajiya ina ganin da kin bari kowa a cikin mu muje munyi magana da yaran idan suna da samari a waje sai musan wanne kalar mataki zamu d'auka" kaita girgiza tana cewa "bakin al'kalami ya riga ya bushe na gama yanke shawara da zuciya ta umarni zan baku ba neman yardar ku nake ba "Isma'il d'an wajen Habibu ya auri Bilkisu Yusuf d'an wajen Habibu na d'akin Mairo ya auri Rasheedah Samar ya auri Zakiyyah Zaidu shi kuma ya auri Zainab Abdul-Razza'k ya auri Safiyyah wadannan yaran dana lissafa su nake so na bud'e ido naga kowa da mijinta tunda Haulat da Atikah su an gama komai na bikin su kun ji abinda nace"?.
Kowa a gurin 'kamewa yayi aka rasa wanda zai fara 'kin yarda ya mayarwa Hajiya magana sai Asabe wacce ta gyara zama tana cewa "Hajiya ina da magana gaskiya hukuncin da kika yanke akan Sameer bai dace ba a rasa wacce za'a 'ka'kaba masa duk yawan yan matan gidan nan sai Zakiyyah yarinyar da ba ganin girma na take ba bata ta'ba gaida ni ba tunda nake gaskiya bazai yuwu ba" caraf Mairo tace "dama uwar me Zakiyyah zatai da d'anki 'yata tafi karfin auren had'i kuma tafi karfin auren talaka irin Sameer" a masife Asabe tace "wallahi 'karya kike Sameer ba talaka bane duk samarin gidan nan ba wanda ya isa ya fad'a masa samun kud'i saidai Zaidu tunda shi yana koyarwa".
"Au ashe dai da wanda ya fishi ai na d'auka shine millionaire gidan"?.
"Dallacan gafara rufe min baki kafin na fasa shi wallahi baki isa jamila ta auri Sameer ba kin ji na rantse".
"Kuma nima sai aka fad'a miki zan amince shi Sameer d'in na bari ya aure ta ne Allah ya tsari gatari da saran shuka yafi karfin wacce taba damu da zuwa islamiyya ba shiba jahila zai aura ba".
"Kece babbar jahila jakar 'kauye" mi'kewa Asabe tai jin tana zaginta ita ma Mairon ta mi'ke zasu fara fad'a Hajiya tace "wallahi duk wacce tsautsayi yasa hannunta ya fara sauka akan d'aya yau saidai ta tafi gidan ubanta sakinta zansa ayi kuma kuyi fad'an na gani" jin abinda tace yasa kowa ta tsaya tana huci suna aikawa da juna mugun kallo.
Ganin guri yayi shiru yasa Adama itama tace "nima fa wallahi ta Asaben Yusuf bazai auri Rasheedah ba" caraf Asiya tace "balle kuma ni wallahi bazai yuwu ba anfi cutar Zaidu a rasa dawa za'a had'a shi sai Zainab kusan sa'ar sa Allah ya sauwake gaskiya a duba wannan al'amarin abar kowa yaje ya nemo matar aurensa da kansa".
"Ban bari kowa yaje ya nemo d'in ba hukunci na riga na gama yankewa babu wanda ya isa karya min ku tashi ku bani guri" ba wanda yayi motsi a cikin su Hajiya ta sake cewa "baku ji bane nace ku tashi ku bani guri" tashi sukai zasu fara tafiya Habibu yace "ku tsaya" kallonsa Hajiya tayi tana cewa "uban me zasu tsaya suyi maka" cikin nutsuwa yace "magana zamuyi ta fahimta Hajiya yadda kowa bai goyi bayan wannan hukuncin naki ba matu'kar akai aurarrakin nan masifa da fitina aka had'a baza su ta'ba zaman lafiya ba tunda kowa ba cewa yayi yana son kowa ba Hajiya mai zai hana ki bamu lokaci kowa ya tara 'ya'yansa muyi musu magana su fitar da mazajen aure suma samarin su fito da matayen aure ina ganin hakan yafi akan wanda kika fad'a ko ya kuka ce"? Duk kaurewa sukai kowa yana cewa "yayi a bamu lokaci gaskiya gara hakan" shiru Hajiya tai tana binsu da kallo daga baya kuma tace.
"Shikenan na baku lokaci amma wallahi gaba bazan yi muku uzuri ba ko kuna so ko bakwa so idan na tashi saidai kuji an d'aura domin zanje gurin liman da kaina na masa bayani ko kuma nasa 'ya'yan naku ayi shelarsu masu son 'yan sadaka suzo su kawo sadaki".
"Insha Allahu Hajiya hakan bazai faru ba".
"Idan Kun kiyaye kenan naji fitsararrun matan naku suna wannan maganar zaka ce hakan bazai faru ba humm ina daidai da kowanne shege ku tashi ku bani guri na gaji da ganin ku" duk mi'kewa sukai kowa yana mata saida safe ko karasa kallon su batai ba balle ta amsa har suka fita karshe da zagi ta raka su daga 'ya'yan nata har surukan.
ZUCIYAR ALIYU CE
@YUSRAH Y♣M♣A
PAGE 28
Washe garin da akai wannan rikicin da yake Zainab bata sani ba taje gaida Hajiya ai kuwa saida tayi dana sanin zuwa saboda irin maganganun data ya6a mata marasa dad'i shiyasa koda ta dawo kofarsu kawai ta shiga d'aki ta kwanta tunda ba school zata je ba gashi zazza'bi na neman rufe ta balle tace zatai d'inki harta lullu'ba barci yana neman d'ebeta ta tuna bataiwa Umma aiki ba da sauri ta tashi tana fita ta kallo gurin wanke-wanke ga sharar kofar ba'ai ba tsintsiya ta d'auka ta fara yin sharar sannan ta had'a kwanukan duka ta kai inda zata wanke ta ta had'a ruwan klin da wanda zata d'auraye ta wanke harda na Asabe da suke gurin takai mata d'aki kamar yadda ta saba sannan ta d'auke nasu ma daga gurin ruwa ta dafa zatai wanka ta zuba shi a bokiti har zata kai band'akin ta fasa ta tafi kofar d'akin ta dashi ta aje ta shiga d'akin sabulun wankanta ta bata ganshi ba dole ta d'auki hijab ta fita zata siyo wayarta na kan window ta kunna wa'azi bata kashe ba ta barta a gurin ta fita jinjina kai Bilki dake tsaye ta window tana le'kenta ta yi ganin ta fita ya sa da gudu ta fito daga d'akin su tana zuwa ta d'auki wayar Zainab d'in ta jefa ta a cikin ruwan bokitin da sauri ta juya ta koma d'aki tana dariya harda tsalle ganin shikenan ta lalata mata wayar tasan duk tsiya wannan wayar ta gama yawo domin kafin taje ta dawo ruwan ya gama ratsa ta.
Da yake shagon kusa da gidan su ta ganshi a rufe yasa ta wuce d'ayan ta siyo tana shigowa gida kawai taga wayarta a cikin ruwan bokitin dake kofar d'akin zaro ido tai da sauri tasa hannu ta d'aukota ta fara gogewa ruwa har tsiyayowa yake ta cikin wayar tsananin mamaki ne ya kama ta taya za'ai wayar ta fad'o ta fad'a ruwa bayan acan cikin window ta d'ora saida idan wani ne ya jefa mata shiru tayi mugun takaici ya gama cika ta har hawaye ne taji suna taruwa mata a ido yaushe ta siya wayar duba sittin da biyar amma har zata lalace gwada kunnawa tayi amma ta rufe ta'ki bud'ewa d'aki ta shiga kawai hawayen ba'kin ciki suna zuba mata ta dad'e tana kukan ta sannan taga kukan ba magani zaiyi mata ba abinda ha'kuri bai baka ba rashin ha'kuri ma bazai baka ba Allah ne ya hore mata ta siya yanzu ma shi zata ro'ka ya sake hore mata duk ta tana zubin adashi a gurin auntyn ta Murjah taso ya kasance ita ce karshen d'auka amma yanzu dole taje ta kar'bo ta siya waya idan ba haka ba dame zata ri'ka assignment..................
"Zainab Zainab".
Taji muryar Sameer yana kiran ta tashi tashi da sauri tana goge fuskarta ta fita yana tsaye a can wajen kofar d'akin sa kallonta yayi yana cewa "ina kika je naga kin wuce d'azu"?.
"Na je siyo sabulu ne kuma na dawo kaga wayata nazo na tarar ta fad'a ruwa".
"Subanallahi a ina kika barta harta fad'a ruwa"?.
"Nidai akan window na tafi na barta dana dawo nazo na same ta a cikin ruwan da zanyi wanka dashi" jin abinda tace yasa Sameer yayi shiru yana kallon kofar d'akin Asabe babu takalminta amma yaga na Bilki zato zunubi koda ya kasance gaskiya amma ya tabbata Bilki ce zata jefa wannan wayar a ruwa saidai baya son data hankali shiyasa ya kalli Zainab d'in yana cewa.
"D'auko min wayar mu gani" juyawa tayi ta koma ta d'auko masa ya kar'ba yana jin har lokacin da sauran d'umin ruwan a jikin wayar kai ya jinjina yana cewa "ok bari na kaita gurin masu gyara su duba miki Allah yasa ta tashi" amin Zainab tace shi kuma ya fita daga kofar yana fita Bilki dake d'aki ta kwashe da dariya wanda
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 34