Share this page
ya sa hajiya tace "kai ku saki juna bana son hauka idan kun je gida kwa yi a can" tura Zaid Sameer yayi yana nuna shi da yatsa yace "wallahi ba 'kyale ka na yi ba sai na nuna maka iyakar ka" tsaki Zaid yayi yana cewa. "Sai mu nunawa juna iyaka kai dai Sameer ko 'kasa ce abinci na ba zan tsaya ka min duka kamar yadda ka ke d'auka a ran ka ba aure kuma nace bazan aure ta ba idan akan haka ka ke jin haushi na ma wallahi ba zan auri Zainab ba" yana fad'in haka ya bar wajen ashar Sameer ya sakar masa ya na cewa "uwar ka Zainab za ta yi da kai wallahi tafi 'karfin auren jaki irin ka zuba ido ka ga irin mijin da za ta aura kaf yaran gidan nan ba wacce zata samu irin sa daga wadanda sukai auren har na bayan ta". Kallon sa Hajiya ta yi bayan wucewar Zaid tace "Samar ba za ka fad'a min gaskiyar a inda ka samo ta ba"?. "Hajiya wallahi Allah kenan kin ji na rantse tare da ni mu ka tafi awara na kara ta ta siyo kin gani" ya fad'a yana nuna mata ledar dake hannun Zainab a ri'ke kallon Zainab Hajiya ta yi tana cewa "amma me ya sa tun da ake maganar ba ta ce komai ba ta yi shiru"?. "To Hajiya me zata ce"?. "Da tana da gaskiya ai za ta yi magana za ta musa zargin da ake mata amma ta yi shiru ta na sauraren mu"?. "Ke dai Hajiya tun da ba'a iya miki Allah ya sauwake kawai shine abinda zan ce amma yadda ku ke d'aukar Zainab ba haka ta ke ba baza ku gane ba sai gaba idan lokaci ya zo muje" ya fad'a yana kallon Zainab jiki a sanyaye ta wuce ta fara yin gaba shi kuma ya juya inda Haulat take tsaye ta gama kukan ta ta share ya ce "zanyi miki gargad'i daf da duka daga yau idan na sake jin kin je kin ce wa Hajiya wai kin ga Zainab ta yi wani layi tare da saurayi hummmm matakin da zan d'auka a kan ki ba zai fad'u ba zaki gani ki ci gaba da mata sharrin" yana fad'in haka yabi bayan Zainab wacce ke tsaye a d'an nesa da su tana jiran sa ya je su fita. Tsaki Hajiya ta yi tana kallon Haulat wacce ta yi shiru ta ce "wai ke dama dan uban ki da Samar ki ka gan ta amma shi ne ki ka ce min wani saurayi ne gashi kin sa a daren nan na fito waje Allah ya 'kara da ya mare ki ina ma dukan tsiya ma ya miki shegiya ma'karyaciya" murgud'a baki Haulat tai tana hararar Hajiya fuuuuu ta wuce tana cewa "duk sharri na ban kai ki ba mutum bai yi abu ba ki ce yayi idan 'karyar ce ma gurin ki na gada" ta fad'a tana nufar hanyar gida d'aga murya Hajiya ta yi yadda za ta ji ta ta ce "Asiya ce ma'karyaciya ba ni ba bankad'add'iyar yarinya kawai" dariya Rasheedat da ke gefe a tsaye ta yi tana cewa "muje gida Hajiya duk sun tafi sun bar mu" juyawa Hajiya ta yi suna tafiya ta ce "ai ba 'yan arziki bane ta ya za su jira mu kowa ya na ji da ba'kin hali". Komawa su kai Hajiya da yake dama a kwance take d'azun ma shiyasa ta koma ta kwanta Rasheedat da Bilki da Zakiyyah suna waje a kofar d'akin ta a zaune suna zance dariya Rasheedat tana cewa "ke Bilki ban ba ku labari ba" cike da son jin me akai Bilki tace "me ya faru bana nan fad'a min"? Sabuwar dariya Rasheedat ta sake yi tuna abinda ya faru da irin gwaramar da akai tace. "Humm ku dai ku bari kawai d'azun nan Haulat ta shigo da gudu ta na cewa Hajiya kiyi sauri mu je wallahi ga Zainab can tare da wani saurayi sun yi bayan layi mu ka tashi Hajiya har da tuntu'be ta ke yi mu ka samu Yaya Zaid a waje shi ma ya bi mu ashe 'karya Haulat take tare da Yaya Sameer su ka je ya raka ta siyan awara tabd'ijan baki ga gwaramar da akai a gurin ba saura kad'an Yaya Sameer ya yi wa Yaya Zaid dukan mutuwa wallahi sannan ya mari Haulat d'in ta yi ta kuka ni kwa ina gefe ina dariya abu na" zaro ido Bilki ta yi tana cewa "ke dan Allah da gaske ki ke Rasheedat"?. "Wallahi da gaske na ke mu ku d'azu ai mun yi kallo ku na nan ba ku sani ba naso ace naje da waya ta na yi musu video". "Me ya sa ba ki zo kin kira mu ba ku ka tafi iya ku ai mu ma da mun yi kallon. "Taya zan tsaya zaman kiran ku ina sauri kar ayi ba ni hum nan gaba nasan Haulat ko da kud'i ba za ta yiwa Zainab ko Yaya Sameer 'karya b............... "To 'yar munafika annamimiya munafirci na ki ke kenan mitsiyaciya," suka ji muryar Haulat wacce ta shigo kofar Hajiya yanzu ta ji abinda Rasheedat ta ke fad'a duk juyawa su kai su na kallon ta daga baya Bilki ta yi dariya ta na cewa. "A'a Hajiya Haulat iyayen 'yan sharri ashe d'azu mari kika sha a gurin Yaya Sameer fatan fuskar ba ta kumbura ba yatsun sa sun fito"? Wata ba'kar harara ta sakar mata tana cewa "ban sani ba ke ma" baki Bilki ta ta'be tana cewa "kar Allah ya sa ki sani ai dama Yaya Sameer d'in su ne maganin munafikai irin ku" a masife Haulat tace "ke kin ga kar ki 'kara fad'a min magana munafirci aka kai ki komai sirrin kofar ku sai kin fad'a hatta jefa wayar Zainab da ki kai a ruwa sai da ki ka fad'a mana dan bana son tashin hankali ne amma wallahi da gobe sai na fad'a mata". "Idan kin fasa fad'a mata Asiya cikin shege tayi ta haife ki" jin abinda Bilki tace mata yasa ta fasa shiga d'akin Hajiya a fusace ta juyo suka hau damen fad'a wanda hatta Hajiya da ta fara barci saida su ka tashe ta da sauri ta bud'o labule ta na cewa "kai kai uban me haka zaku baro iyayen ku ni ku zo ku cika min kunne da fad'a ba za ku bari ba"? ko sauraron ta ba su yi ba ga Rasheedat a gefe sai dariya take ta'ki tashi ta raba su ganin haka yasa Hajiya d'auko sanda tana fitowa ta yo wajen su tana cewa "tselan uwa ku tsinannun yara ina magana shine ku kai kunnen uwar shegu da ni kamar yadda iyayen ku mata su ka raina ni kuma haka" ganin da sukai tana shirin rad'o mu su sandan yasa suka saki juna kowa ya na huci kallon su Hajiya ta yi tana cewa . "Fad'an uban me ku ke yiwa mutane da daren nan"? Ran Haulat a 6ace ta ce "wai tsabar rainin hankali ina shigowa na ji su na munafirci na wai wani d'azu Sameer ya mare ni saboda na yiwa Zainab 'kazafi" "Ba ki yi bane dan uban ki ina ni ma har sani ki kai na sha wahalar fita ki kace zaki raka ni inda kika ga sun yi ashe 'karya ki ke kuma dan su na maimaita zancen shi ne zaki kama ta da kokawa"?. "Bazan kama ta da kokawa ba uban ta ne yace ta ce min Sameer ya mare ni d'azu harda wani ko fuska ta ta kumbura yatsun sa sun fito". "Ta fad'a ya mare ki ni ma na fad'a d'azu Samar ya mare ki dan ubanki ki yi wani abu akai na sake jin kin yi magana a kofar nan wallahi sai na fito na shirga mi ki wannan sandan a bayan ki" tana fad'in haka ta koma d'aki tsaki Haulat ta ja me 'karfi ta na hararar kofar d'akin Hajiya kafin ta juya inda Bilki ta ke tana cewa "ke kuma zamu had'u ne wallahi sai mun fidda rainin da ya ke tsakanin mu" ita ma ta na fad'in haka ta juya fiiii ta fice daga kofar ita dai Rasheedat da take ta yi musu dariya ganin Haulat d'in ta ji haushi ta fice ta ce. "Gaskiya 'yan gidan nan suna burge ni masifa ko gidan haya iyakaci kenan haba ace kullum idan rana ta fito kafin ta fad'i sai an samu wandanda su Kai tashin hankali idan kuwa ba'a yi da rana ba sai anyi da dare kafin a kwanta barci a gidan nan ba'a rasa abun yi" ta'be baki Bilki tai tana cewa "waye zai zauna a raina shi ke yadda 'yan gidan nan ba mutunci ne da su ba daga manyan su har 'kananan su idan su ka ga kai ba mafad'aci bane tuni za'a sakaltar da kai gara ka nuna kai ma masifaffe ne da bala'i ya gan ka saida ya sara maka sai ka nuna haka sannan za ka daidaita da kowa" kai Rasheedat ta jinjina tana cewa "gaskiya ne shiyasa ai mu ka raina Zainab saboda ita ba mai son hayaniya ba ce". "Wannan kuma ita ta so sai kin je 'kofar mu ma kin ga yadda na ke mata rashin mutunci son raina da rashin kunya ko tari ba ta yi min ke ko 'karasa kallo na ba ta yi" kai Rasheedat ta girgiza tana cewa. "Uhm gaskiya dai a gidan nan indai ba sharri za ka yi mata ba bata da wata matsala Allah sarki wallahi har na ji tausayin ta ya kama ni" zaro ido Bilki tai tana cewa "ke Zainab ba abar tausayi ba ce garama kar ki wahalar da kan ki saboda ita" da mamaki Rasheedat ta ce. "Me ya sa ki kace haka"?. "Kina gani a gidan nan ita kad'ai ta ci gaba da makaranta saboda ba kud'in da za'a biya mana mu dora ita kad'ai ce take sana'o'i kusan shida amma ki ce tana baki tausayi hum idan ba ki sani ba bari na sanar da ke kece babbar abun tausayi" dariya Rasheedat ta yi tana cewa "saidai abun taushe ba abun tausayi ba sana'a mu na da hanyar yi dan dai ba mu da jari ne amma ai ke Yaya Sameer ne zai ba ki" zabura Bilki tai tana cewa. "Wanne Yaya Sameer d'in amma dai ba na gidan nan ki ke fad'a ba"?. "Wai da shi". "Cafd'i wallahi ko mutuwa zan yi Yaya Sameer biyar d'in sa baya d'agawa ya bani tunda na ke dashi bai ta'ba min wani abun arziki ba amma ya yiwa Zainab ya fi 'karfin a 'kirga". "Jinin su ne yazo d'aya" cewa Rasheedat tana hamma alamar barci kai Bilki ta girgiza tana cewa "ke ba wani had'uwar jini sai dai had'uwar asiri a banza ba zai ri'ka kulawa da ita yana mata abubuwa ba alhali suna uba d'aya ni da muke uwa d'aya ya ri'ka share ni ki na ganin fa kowacce 'kofa a gidan nan had'e kai 'yan d'aki d'aya su ke yi amma ban da Yaya Sameer shi kam da 'yan uba yake nasa sha'anin domin kwanan baya gidan Murjah yayar Zainab d'in ya je amma bai le'ka gidan Auntyn Aisha ba kin ga ko ta nan ai kinsan ba son Allah ya kewa 'yan d'akin su Zainab ba asiri ne yake yawo a jikin sa a halin yanzu nasan da mutuwa za'a bashi za'bi tsakanin ni da Zainab cewa zaiyi mutuwar ta d'auke ni tunda ba 'kauna ta ya ke ba yafi son ta dad'in abun ma ba aure tsakanin su uban su d'aya amma ba dan haka ba yadda yake mata wannan shishshigin 'karshe ba zai wuce yace yana son ta ba wallahi wani lokacin idan ya yi mata wani abun kamar na yi ta kuka haka na ke ji tsabar ba'kin ciki da takaici" tana rufe baki Rasheedat ta fara dariya tana kallon ta tace. "Hum ai kuwa aiki ne bai ishe ki ba nidai da ace Yaya na ne yake irin wannan abun ko 'karasa kallon sa ba zan yi ba saboda damuwa zan ri'ka d'orawa kai na shi kuma ba tare da ya damu ba maybe ma shi Yaya Sameer d'in bai san kina damuwa da hakan da yaje yiwa Zainab d'in ba". "Uhum wallahi yana sane kawai dan ya 'kuntata min ne ba komai ba shi ya sa nima idan na ga ya fice nake ramawa a kan Zainab d'in tun da ba wata tsiyar ta isa ta min ba". "Akwai ranar da zaki daina ai idan ta yi aure ta bar miki gidan". "Anya Zainab za ta yi aure kuwa? Miji ya'ki fitowa"? Kai Rasheedat ta d'aga tana cewa "daina mata fata za ta yi man akwai lokaci nikam bari kiga na d'aga wannan zancen da mu ke ba 'karewa zai yi ba idan zamu kwana a nan ni kam bari ki ga na tashi ta tafi kofarmu na kwanta barci na ke ji kar na fara gyangyad'i" ta fad'a tana mi'kewa ita ma Bilkin mi'kewar ta yi suka fita tare kowa ta tafi 'kofar su.................. ZUCIYAR ALIYU CE YUSRAH MUSA DUTSE NAJA'AT MUSA ABUBAKAR ✨ SALEEM MUSA ABUBAKAR ✨ FATIMA MUSA ABUBAKAR ✨ AISHAT MUSA ABUBAKAR ✨ ABUBAKAR MUSA ABUBAKAR @YMA DUTSE PAGE 33 Yau Shareef bai je hospital da wuri ba duk irin jiran sa da Baby ta yi amma shiru sai wajen 'karfe tara da rabi ya zo amma sakamakon yana da ayyuka yana zuwa ya wuce a ta'kaice ba ta samu had'uwa dashi ba sai 'karfe d'aya da rabi sannan sun gama komai ya dawo office ta je. "Barka da rana Shareef ya kake"? Bai d'ago ba wayar sa ce a hannun sa yana dubawa ya ba ta amsa. "Lafiya". Numfashi ta sauke tana cewa "fatan ba wata matsala na ga kamar fuskar ka da damuwa"?. "Ni ma fad'a mi ki"? Ta sake ji ya bata gajeruwar amsa cije baki ta yi kamar za tai shiru sai kuma ta sake cewa "ya Mami fatan ta na lafiya"? Jin abinda ta ce yasa ya d'ago ya kalle ta tare da aje wayar yana fuskantar ta sosai yace "dama ina so na kashe miki warning akan zuwa gurin Mami da ki kai ranar Saturday kar ki dad'a zuwa bana so bana bu'katar ki sake zuwa gidan mu" da mamaki Baby ta ke binsa da kallo ta ce. "Amma saboda me"?. "Tambaya ki ke me ya sa"?. "Dole na tambaya Shareef me ye laifi na a ciki dan kawai na je na gaisar da ita"?. "zuwan ne bana bu'katar ki 'kara yi kin gane"? Shiru ta yi ta zuba masa ido ta ma rasa abinda za ta ce masa ba wanda ya sake magana a cikin su tsawon mintuna can tace "Shareef idan har zuwa gidan ku da nayi shine ya 6ata maka rai kayi ha'kuri ba zan sake ba daga yau insha Allahu amma kai ma ya kamata ka yi min adalci ba fa a rayuwa haka kaga yadda ka saka ni a garari kuma dan na yi abun arziki sai ka d'auke shi da fushi"?. "Na fad'a miki a karo na uku kar ki sake zuwa gidan mu balle ki yi min 'karya a gurin mahaifiya ta". "K'arya kuma Shareef"?. "Eh ba ki yi bane kin ce idan na zo hospital bani da zance sai nata kullum idan muna tare ita na ke furta miki yawan ambaton ta da na ke yi yasa ki kace dole sai kin je kin gan ta da yaushe mu kai haka da ke a ina na samu lokacin da zamu zauna har na fad'a miki irin wadannan maganganun? Ya isa haka ki bari bana so idan kina son zama da ni lafiya kar na sake jin labari ko a mafarki ne kin 'kara zuwa gidan mu kin gane"? Rasa abinda za ta ce masa ta yi shi yasa kawai ta yi shiru gabadaya wani irin yanayi ya lullu'be ta ta gaza gane wanne irin mutum ne Shareef ta na so tasan a inda matsalar ta ke ta gyara amma har gobe ta rasa, kai ta girgiza tana sake d'agowa ta kalle shi ta ga ya mayar da hankalin sa kan wayar sa ta tabbata tun da ya yi mata iyaka da gidan su idan ta 'kara zuwa abun bazai mata kyau ba zata yi 'ko'kari ta danne duk wata damuwa ta d'an share shi na tsawon wata guda maybe idan ta cire shi da damuwa da shi a ran ta za ta samu lafiya kar ta je ta jawowa kan ta ciwon da ya fi 'karfin ta ko wanda zai hallakar da ita, mi'kewa ta yi tana d'aukar jakar ta da key d'in motar ta ba tare da ta sake ko da tari ba ta fice ko kad'an bai damu da yanayin da ta shiga ba shi yasa a rayuwa kar ka damu da mutumin da bai damu da kai ba ko dashi ko ba shi za ka iya ingantacciyar rayuwa mai kyau wacce ta fi wadda kake tunanin yi da shi. Afifah yau tana dawowa daga school ta ga sa'kon da Aliyu ya bada a kawo musu ita da Amirah har ya iso cike da murna ta kar6a tana ihu ganin yadda yanayin sa yake daga photon sa na jikin kwalin tun kafin ta bud'a lallai wannan agogon mai mugun tsada ne zata sha wanka da kayan ta. Tana bedroom ta yi wanka da sallah kenan ta saka kaya tana zaune a gaban mirror Aliyu ya kira ta tasan bazai wuce ya tambaye ta ko Amirah ta kawo mata ba shiyasa tana d'agawa ta ce "hello Yaya Aliyu Ina yini naga agogon ya zo". "Eh nace Amirah ta kawo miki ta kawo d'in"?. "Eh ta kawo min lokacin ma ban dawo daga school ba sai yanzu Momy ta bani ita Amiran ta tafi na gode sosai Allah ya 'kara arziki". "Ok kin bud'e shi ne"? Kai ta girgiza tana cewa "a'a ban duba ba". "Yayi kyau gara da baki bud'e ba domin ba naki bane ki kaiwa Sameer yanzun nan kuma wallahi idan yace min kin 6arka gidan agogon nan na dawo sai jikin ki ya fad'a miki" zaro ido waje Afifah tai kamar zata fasa ihun takaici wannan agogon na mata ne akan me zaice ta kaiwa Sameer gaskiya badan babu yadda ta iya ba babu inda zata je amma tasan tunda yace haka zaman lafiyar ta kawai ta kaiwa Sameer d'in............... Ba ki ji abinda na ce bane"? Kamar za tai kuka ta ce "na ji". "Ok ki kai masa" yana fad'in haka ta ji ya kashe kiran cije yatsa ta yi tana sake kallon agogon tace "kan bala'i wai da gaske Yaya discipline ya ke yanzu wannan agogon tsakani da Allah ai na maza ne idan na kai masa shi ma sai dai ya bada kyautar sa innalillahi gaskiya Yaya discipline ya gama da rayuwa t............ Ringtone d'in wayar ta taji da sauri ta duba shi ne ya sake kira kamar kar ta d'aga tsabar takaici bari ta yi saida ta kusa katsewa sannan ta d'aga ji ta yi yace. "Kin tafi ne"? Da sauri ta ce "a'a ban tafi ba ina bedroom" ta d'auka cewa zaiyi ta barshi basai ta kai masa ba idan ya ji ba ta tafi ba sai kuma ta ji yace "baza ki tashi ki Kai masa ba kenan wato dan kin ga bana kusa shi ne za ki min raini ko"? Turo baki tai tana tashi ciki-ciki tace. "Ka yi ha'kuri". "Ban ha'kura ba ki je ki kai masa idan kin dawo ki kira ni ki sanar da ni" d'it d'it taji wayar ta katse d'aukar hijab d'inta ta yi tana tura baki ran ta a had'e sosai ta fita parlor iya Fati da Momy ne Husnah da Elham ba sa gurin ganin yadda ta fito tana cika da batsewa yasa Momy cewa. "Afifah ya haka ke da ki ka shigo ki na murna me ya faru lafiya"? Agogon ta d'agowa Momy tana cewa "ina lafiya Momy haka kawai Yaya discipline tun kafin agogon nan ya zo ya kira ni ya fad'a min Amirah za ta kawo min ina ta saka rai nawa ne sai yanzu da yasa aka kawo min wai ya kira ni yanzu ba nawa bane naje na kaiwa Sameer kuma fa agogon mata ne kin gani" ta fad'a tana mi'kawa Momy kallon agogon Momy ta yi tana cewa. "Ok tun da dai ga wanda yace ki kaiwa kije ki kai masa saiki fad'a masa cewa kema kina son irin sa idan zai dawo ya taho miki da shi". "Uhm uhm nidai daya bar min wannan d'in yafi amma shikenan lamarin Yaya discipline sai shi Fati taso ki raka ni" mi'kewa Fati tai tana cire mayafin da tayi rolling a kanta dashi ta yafa suka fita tana tambayar Afifah "to wai Aunty Afifah ni ban gane ba me yasa zaice ki kaiwa Yaya Sameer bayan shi namiji ne kuma dai wannan agogon mata ne" cike da jin haushi Afifah tace. "Oho masa shima Yaya Sameer d'in wa yasan me zaiyi da shi daina taso min da kayan takaici kar na fara hawaye a layi" murmushi Fati tai tana kallon ta ta ce "ki gwada cewa ya bar miki man nasan Yaya Sameer zai baki" kai Afifah ta girgiza tana cewa. "A'a tunda Momy tace na fad'a masa ya taho min dashi gara hakan da nayi abinda idan ya dawo zai ci ubana duk da nasan Yaya Sameer in dai nace masa ina so zai bar min d'in" ta fad'a daidai sun shiga chemist d'in da sallama ta mi'ka masa tana cewa "Yaya Sameer gashi inji Yaya Aliyu yace a kawo maka" kar6a yayi yana murmushi ya kalli agogon kafin ya d'aga kai yana cewa "ok tom na gode dama yanzu ya kira yace kin kawo min nace a'a ashe kina kan hanya". Jinjina kai Afifah tai tana cewa "ki ji dan Allah Fati wai kafin nazo harya kira yana tambaya"? Dariya Fati ta yi bata ce komai ba Afifah taci gaba "yanzun nan ni d'in ma mukai wayar dashi amma har ya kira ka"?. "Eh Aliyu ne fa kad'an daga cikin aikin sa ne wannan" ya fad'a yana aje agogon d'an ta'be baki Afifah tai tana cewa "ai shikenan na kawo na huta da naci Fati mu je Yaya Sameer sai anjima". "Ok ki gaida Momy kafin na shigo na gaida ita". "Za ta ji insha Allahu" ta fad'a su na fita suka koma ba su samu Momy a parlon ba babu kowa shiyasa Afifah ta wuce dinning taci abincin rana Fati kuma ta shige ciki bata tsaya a parlon ba Afifah ta dad'e sosai kafin ta ji 'karar bud'e 'kofa Momy ce ta dawo ta na zama tace. "Au har kun dawo ke nan"?. "Eh tun d'azu wai nan d'in kafin mu je har ya kira shi yana tambayar sa na kai masa". "Ai kuwa dama zai kira shi kin san waye Aliyu fa shi ya sa na ce miki ki kai masa kawai idan kina so ki fad'a masa ya taho miki dashi idan ya tashi dawowa". "Ni fa na ha'kura Momy kawai ya wuce tun da ban samu wannan d'in ba Yaya Sameer ya ce yana gaida ke kafin ya shigo". "Ina amsawa ai dama ya dad'e bai shigo ba saboda ya ga yanzu ba Aliyu kuma da ya duba ko da ace Aliyu ba ya duniya shi me shigowa gidan nan ne kullum balle yana raye ko dan abinci ma sai dai a bishi chemist d'in da shi ya daina zuwa ya kar6a" kai Afifah ta d'aga tana tasowa daga dinning table dawo parlor gurin Momy tana cewa. "Ai yana da kunya ne shi yasa". "Eh gaskiya kam ya na da kara da wani ne haka zai ri'ka shigowa koda yaushe ba ruwan sa". AYI HA'KURI IDAN AN SAMU TYPING ERROR MATSALAR KEYBOARD NE. @YUSRAH DUTSE PAGE 34 Kiran wayar Afifah da akai shi ya dakatar da zancen da su ke yi ta d'aga daga can 6angaren Amirah dake zaune akan gado ta d'ora pillow akan cinyar ta ta ce "hello Afifah ya kika ga agogon ya yi miki kyau da kika d'aura"? Ta'be baki Afifah tai tana cewa "wanne irin kyau d'in bayan ashe dama ba nawa bane d'azun nan ya kira ni yace na kai wa Sameer". "Sameer kuma shi me zaiyi da abun mata"?. "Oho nima na kasa gane wannan al'amarin". "Kenan

Chapter 15 of 34