Share this page
ba" kai Asiya ta jinjina har da sakin murmushi tana cewa . "Yauwa d'an albarka je ka da kan ka kar ka yi sanyi ka bud'e murya yadda za ta ji ka sosai ka fad'a mata ba ka son auren dole da take neman 'ka'kaba ma ka" bai tsaya jin 'karshen abin da zata fad'a masa ba ya yi waje kan sa tsaye 'kofar Hajiya ya shiga tana ganin sa ta fara hararar sa shi ma had'e rai ya yi sosai ya tamke fuska ko ina kwana bai ce mata ya fara magana. "Hajiya na ji sa'kon da ki ka baiwa Abban mu ya fad'a min amma ni Zain............. Tun bai fad'i abin da zai fad'a ba ta tare shi da fad'in "eh ba dole na bashi sa'ko ba na ga kun mayar da ni tsohuwar banza wacce ba ta da daraja a idon ku har kamar ni ce zan ce ku yi min abu amma ku 'ki yi kun kyauta kenan a ganin ku saboda rashin tarbiyya"?. "Me ki kace mu yi mu ka 'ki yi? ke ma fa Hajiya ba haka ake rayuwa ba an ta'ba so dole ne da za ki ce sai na so Zainab na aure ta ni ba na son ta kuma ba zan ta'ba son ta ba har abada akwai wasu mazan a gidan nan ki neme su ku tattauna maybe ki samu wanda zai kar6i ta yin ki amma ba dai ni ba" gwalo ido Hajiya tai tana kallon sa tace "au ba za ka aure ta d'in ba kenan ka bujirewa umarni na"?. "Ni fa Hajiya kar ki nemi d'ora min laifi na fad'a miki iya gaskiya ta ne bazan auri Zainab ba kawai bazan aure ta ba ina nufin bazan iya ba, bana son ta bana sha'awar zama da ita" kallon sa sosai Hajiya ke yi daga baya ta jinjina kai tana cewa "shikenan Zaidu ka kyauta kar Allah ya sa ka aure ta d'in tashi ka bani guri marar mutunci fitsararre" tashi Zain ya yi yana nufar 'kofar fita yace "kome za ki ce ta haushi ta biyo aure dai nace bazan aura ba". "Kar ka aura d'in man bankad'add'e Allah ya sa matar da zaka auro ta ri'ka yi wa Asiya dukan tsiya kai kuma tana kwara maka ruwan sanyi idan ka na barci kuma ta mayar da kai mijin tace ta ri'ka saka ka shara da wanke-wanke zan yi ta addu'a in Allah ya yarda ba za ka ji dad'in auren da za ka yi ba tun da ka 6ata min rai" shi kam Zaid ba jin ta yake ba domin ya riga ya yi tafiyar shi. ZUCIYAR ALIYU CE @YUSRAH JIGAWA PAGE 40 Tashi Hajiya ta yi ko takalmi ba ta d'iba ta saka ba ta fita ta shiga 'kofar su Zaid a lokacin Asiya tana waje tana wanki ko sallama babu ta na shiga tace. "Ke Asiya wato ke ce ki ka zuga Zaidu yaje yayi min rashin kunya akan nace ya had'o wani lefen ya auri Zainab ko? Tunda kika hana shi auren ta insha Allahu matar da zai auro miki sai ta zame miki masifa da bala'i sai kin shiga uku a wurin ta yadda ki ka wulakanta ni ki ka raina ni ke abinda za ta yi miki sai ya ninka nawa sau dubu matsiyaciyar mace kawai" tana fadin haka ta juya ta fita baki Adama ta ri'ke bayan fitar Hajiya ta fito daga d'aki tana kallon Asiya wacce ke hararar 'kofar da Hajiyan ta fita tace "amma mu dai mun shiga uku a gidan nan dan masifa uwar miji ta hana ka sukuni tunda na shigo gidan nan ban ta'ba ganin ranar da ta fito ta fad'i Hajiya ba tayi fad'a da surukar ta ba ke ma abun ya juyo miki kamar yadda ta ke takurawa Hauwa" ta6e baki Asiya ta yi tana cewa. "Ai ni kuma nafi 'karfin ta ina daidai da ita duk abinda take ji dashi na fita 'karshe bai wuce ta ce Habibu ya sake ni ba ni kuwa ban damu ba tunda d'ana ya d'ago ya mallaki gidan kansa inda zan zauna dai ba rasawa na yi ba balle ta ce dole sai a inuwar d'an ta kad'ai zan rayu ni ma Allah ya yi min arzikin d'an" kai Adama ta girgiza tana cewa. "A'a in sha Allahu ba za ta ce ya sake ki ba kawai dai bala'i ne ba za ta daina miki ba sai dai idan mutuwa ta yi dan nasan ko ranar d'aurin auren ma sai ta zo ta yi miki ga dangi sun cika gida sannan ko haihuwa matar tayi nan ma sai ta tuna baya ta zage ki ta ce da yanzu Zainab ce ta haihu da shi kece ki ka hana". Mi'kewa Asiya ta yi tana d'iban kayan data d'auraye ta fara shanyawa tana cewa "na hana d'in nima hanau ce ta hana ni kin ga nifa yanzu lamarin Hajiya baya sha mun kai domin tun ina jin shakkar ta yanzu ta saka ko kad'an bana tsoron ta kina gani fa har so take wani abu ya had'o mu da ita nayi min tas to ni ma yanzu ba 'kyale ta zanyi ba jira nake babban abu ya had'o ni da ita na zage ta tas yadda a gaba zata kiyaye ni" jin abin da Asiyan ta ce yafi 'karfin d'auka ya sa Adama cewa. "Uhm mu kam babu abin da za mu ce saidai Allah ya rufa asiri" ta fad'a tana wucewa ta d'auki buta ta shiga band'aki. Batun Hajiya kam tana fita daga 'kofar su Zain 'kofar su Zainab ta wuce nan ma ta soma 'kwallawa Umma kira tun kafin ta 'karasa shiga "Hauwa Hauwa" da sauri Umma ta fito daga d'aki tana zuwa kofar shigowa lungun nasu tare da dur'kusawa ta ce "gani Hajiya" kallon ta Hajiya tai tana cewa. "Duk abinda ya kamata ace na yi matsayi na na kaka a wurin Zainab nayi 'ko'kari akan ta samu mijin aure idan baku gode min ba baza ku tsine min ba yanzun nan daga kofar Habibu nake wancan mitsiyaciyar ta hana Zaidu ya 'karo lefen da zai auri Zainab to yanzu dai ban san yadda zaku yi da 'yar ku ba shawara ta ragewa me shiga rijiya ko ya saka igiya ya shiga ko ya dirga idan kuma zaku je ku fad'awa liman ya cikita muku ko za'a samu mai auren ta nan ma dai ku kuke yi ni na gama iya nawa tashi ki je" tana fad'in haka ta juya ta tafi tashi daga tsungunen da take Umma tai ran ta babu dad'i ta kalli kofar d'akin Zainab ta ga takalmin ta yana nan maybe ta ji wannan maganar kamar zata bud'a ta le'ka ta amma tunanin irin halin da zata riske ta a ciki yasa kawai ta koma d'akin ta jiki a mace. Zainab kam tana kwance a d'aki ta zubawa celling ido tana jin komai abin da Hajiya ta ke cewa numfashi ta sauke ba ta iya aikata komai ba ta rasa me ya kama ta tayi a wannan lokacin kuka ko tunani ko me ta na jin yadda Asabe ke gud'a tana shewa ta na faffad'awa Umma maganganun banza marasa dad'i amma ko kad'an ba ta ji muryar Umman ba cije lips tai lokacin da taji Asaben tace "ai ba lallai Zainab ta samu mijin aure ba watakil a haka zata 'kare rayuwar ta a gida kawai abinda yafi sauki zan ba ku shawara ku siyo mata kayan d'akin ta ta jera abun ta ta ri'ka kallo ko ya rage mata rad'ad'in rashin auren da take ji ko dan ina kud'in kayan d'akin tunda daga ke har shi ba arziki gare ku ba me ku ka tara mu na nan mu na jira za mu ga ta inda mijin na ta zai fito kuturu ne ko makaho ne wa ya sani" ta 'karasa maganar tana she'kewa da dariya ta sake sakin gud'a kamar za ta cire hanci saboda farin cikin abinda ya faru yanzu. Humm Allah sarki duniya mai cike da abubuwan mamaki da al'ajabi duk wadannan maganganun da Asabe ke yi Umma ta na jin ta amma tsabar ha'kuri ko cira kai ta kalle ta ba ta yi ba balle ta mayar da martani sai Zainab dake d'aki hawayen damuwa su na ta zuba mata Allah ya gani ba za ta iya wannan masifar ba in sha Allahu ana yin hutun makaranta za ta tafi D'an Yana ba za ta dawo ba sai hutu ya 'kare idan ba haka tai ba ba'kin ciki sai ya saka zuciyar ta ta buga a gidan nan................... 💓ZUCIYAR ALIYU CE💓 ><°°>< YSRH @JIGAWA STATE PAGE 41 Kamar yadda Hajiya ta ce ba za ta sake magana ba akan auren Zain da Zainab haka ne ya faru duk abin da ake ta na shan kallon su sai dai ta d'au fushi ta cika ta yi dam duk ranar girkin Asiya idan an kai mata ba ta ci sai dai ta kora yaran da ya kawo ya mayar bata huce ba har lokacin bikin ya yi hatta goro da aka bata da ta amsa bayan fitar Habibu ta taso ta zo ta watsawa Asiya a kan ta ta juya ta fitce tana cewa ko ba ta ta'ba cin goro ba baza taci na auren Zain ba. Aunty Murjah ba ta samu damar shigowa ba ranar da aka fara bikin sakamakon can ma wani bikin ne da su shiyasa ta bari sai ranar dinner ta d'an le'ko musu ta wuni a d'akin Zainab su na ta hira da dariya musamman da Aunty Murjah ta ke ce mata Mukhtar ya na neman ta ya kamata ta je su gaisa. Da lokacin tafiya dinner yayi babu yadda Aunty Murjah ba ta yi ba Zainab ta ce ita babu inda za ta je da ta yi wankan ta ma keken ta ta hau take rage d'inkuna Umma ba ta san bata je ba duk zaton ta da taji Aunty Murjah ta na mata sallama tana cewa sun tafi ta d'auka da Zainab d'in ne d'age labulen d'akin ta yi tana le'kawa ta ce. "Zainab ke baza ki je gurin dinner ba naga kinyi wanka na d'auka ma tafiya zaki yi sai kuma naga kin hau keke kina d'inki dama ba tare da Murjanatu za ku tafi ba"? Kai ta d'aga tana cewa "eh Umma gaskiya ba zuwa zan yi ba". "Amma me ya sa kowa fa ya tafi ke kuma ki na gida babu dad'i me ye dalilin da za ki ce baza ki je ba"?. "Wallahi babu komai kawai son zuwan ne bana yi musamman kin ga harkar da ya shafi kid'a ne ba abun burgewa anan". "Amma Zainab wannan rashin zuwan naki baza ki ta'ba fita ba 'yan gidan nan za su yi tunanin ko damuwa ce ta hana ki zuwa ko 'kin amincewa da Zaidu ya yi ya aure ki kishi ya sa ba za ki je ba kodai wani abu ne" murmushi Zainab tai ta na cewa. "Damuwar me ne zai saka har na yi abun da zai takura min in dai ina son zuwa". "Gani za su yi kamar saboda baki yi aure ba ne su kuma suna matsayin 'kannin ki shiyasa kike 'ki zuwa gashi harda Haulat yanzu kowa d'auka zai yi kina daga cikin wad'anda suke yi ba'kin ciki shiyasa baki je d'in ba balle gashi abinda ya faru tsakanin ki da Zaidu ke bakya tsoron hakan ne"? Shiru Zainab tai tana kallon wayar ta da ta kawo haske alamar kira domin ta saka ta a silent *bro S* ne yake kiran ta tasan bazai wuce akan bai ganta a gurin dinner d'in bane ita kuma gaskiya duk wani abu daya shafi harkar kid'e-kid'e ta tsana d'agawa ta yi Umma kuma ta saki labulen tana barin 'kofar d'akin tun kafin Zainab ta yi magana Sameer yace. "Zainab kina ina ne tun d'azu sai neman ki nake yi a gurin amma ban gan ki a ko'ina ba kina ta wajen ina ne na kasa samo ki"? Numfashi ta sauke tana cewa "Yaya Sameer ina gida ban zo ba". "Me ya sa ba ki zo ba"?. "Babu komai". "Bakya ra'ayin zuwan ne ko kuma yaya"?. "A'a kawai dai ba na son jin 'kara ne gashi ta wayar ma ina jin tashin sa balle wanda ya je gurin gara na zauna a gida na yi d'inki na ya fi min alkhairi" ji ta yi yace "ok sai mun dawo mu kam sai mun ga abin da ya turewa buzu nad'i" yana fad'in haka ya kashe wayar yana amsa kira da alama wani ne yake kiran sa a wurin dan ta jiyo sanda aka ce Sameer d'an murmushi tai tana girgiza kai wato sai sun ga abinda ya turewa buzu nad'i kenan rawa Yaya Sameer zai yi ko me? Dariyar da ba shiri tayi tana ci gaba da d'inkin ta kafin ya dawo ta san zai d'auko video ta kar6a ta gani". Kamar mintuna talatin ta ji sallamar Sameer da mamaki ta tsayar da d'inkin da ta ke dan ta ji kunnen ta ne ko kuma shi d'in ne ji ta yi yana magana da Umma a ranta tace "Subanallahi Allah ya sa ba zuwa ya yi mu tafi b........... Tun kafin ta 'karasa addu'ar da ta ke yi ta ji yace "Zainab ki na ina"? Numfashi ta sauke tana cewa "ga ni a d'aki". "Ok fito mu tafi gurin dinner d'in nan" jin abinda yace yasa ta d'an 6ata fuska ta na mi'kewa ta fito waje ya na tsaye a kusa da 'kofar d'akin nata ganin ta fito ya sa yace "koma ki d'auko mayafi da handbag d'in ki mu tafi saboda na d'auke ki na dawo". "Ni fa Yaya Sameer.............. "Kar ki ce min ba za kije ba dan Allah taho mu tafi gashi kin yi wanka ba tsayawa zaman jiran ki zan yi ba kawai sai dai ki saka anko". "Ni ban yi anko ba" . "me ya sa"?. "Saboda ba'a kawo min ba lokacin da Haulat ta siyo atamfar ankon ta shigo ina ji ta zo ta nunawa Bilki ta fita ba tai min magana ba shiyasa nima ban yi ba ni bana abin da ba'a sako da ni ba kuma Atikah ma haka ba wanda ya tambaye ni idan zan yi" kai ya d'aga ya na cewa "ok na gane yanzu dai d'auko mayafin ki mu tafi". "Gaskiya Yaya Sameer sai dai na saka hijab" zaro ido ya yi yana kallon ta da mamaki yace "hijab kuma Zainab ba fa islamiyya za ki je ba gurin dinner za mu je haba ke kuwa yau d'ayan" d'an dafe goshi ta yi kamar za tai magana sai kuma ta fasa ta koma d'aki bisa dolen ta ta d'auko mayafi da handbag d'in na ta kamar yadda ya ce kai ya jinjina ya na murmushi ya ce "yauwa 'yar 'kanwa ta ko ke fa mu je" ita dai Zainab ba dan ran ta ya so ba ta bi bayan sa suka fita ta d'auka mashin d'in sa za ta gani sai kuma ta ga mota a wajen da alamar tambaya ta kalle shi gira ya d'auke yana cewa. "Aboki na ne tare mu ka zo zan d'auko mashin ya ce na barshi mu je a motar sa sunan sa Äl'ämëëñ" kai ta d'aga ba ta yi magana ta ya bud'e gaba ya shiga ita kuma ta shiga baya tana shiga ta zaro Nikaf d'in ta ta d'aura dan ba za ta iya shiga wannan uban taro kowa ya na kallon fuskar ta ba balle wai yau ita ce ta fita da mayafi humm ji ta ke kamar ba ta saka komai ba. Ko kad'an Sameer bai kula ba saida suka je gurin ta fito ya ga fuskar ka rufe da Nikaf baki ya bud'e ya na cewa "kai ke dama kin taho da Nikaf to me akai kenan ai da kin sako hijab d'in ki ma kawai ya fi" ya fad'a suna shiga ita dai ko tari ba ta yi ba da suka shiga ma a can gefe ya nuna mata kujera ta zauna da lallami da'kyar ya samu ta cire Nikaf d'in amma a tsarge ta ke gani ta ke kamar kowa ita ya ke kallo su na zaune suna zance abokin sa da ya raka shi yanzu shine ya zo gurin yana zama a d'ayar kujerar ya kalli Zainab wacce ta yi 'kasa da fuska ganin irin kallon da ya ke mata Sameer ya kalla ya na cewa. "Ya kai Sameer wannan Ladyn fa 'kanwar ka ce"? Kai Sameer ya jinjina ya na kallon yadda ta ke 'kara yin 'kasa da fuskar ta ba ta so Al'ameen ya kalle ta (Bari nayi tsokana Al'ameen A. Prince🤴 nake nufi😃). Sameer ya ce "eh 'kanwa ta ce" gyara zama Al'ameen ya yi yana cewa "amma gidan ku d'aya ko kuma biki ta zo"?. "Uhm gidan mu d'aya". "Ok abin da na yi tunani kenan dan na ga kuna kama da ita cousin sister d'in ka ce"?. "A'a wannan ta fi 'karfin cousin sister uban mu d'aya kawai bari na 'kare maka karshen zance" zaro ido Al'ameen cike da farin ciki ganin shikenan fa'kat 'karshen zance yace "wow alhamdulillah ashe yau na yi tsintsuwa irin wannan kyau da hankali haka fatan zaka ba ni ita Sameer"? Kad'a kai Sameer ya yi yana kallon Zainab wacce tun lokacin da Al'ameen ya zauna ta sunkuyar da kai ta'ki d'agowa ya ce. "Eh to gaskiya ba ni da tabbaci akan haka" da alamun tambaya Al'ameen ya ce "me ya sa kace ba ka da tabbaci"? Kai tsaye Sameer ya ce "saboda tana da wanda za ta aura" yana rufe baki Zainab ta d'ago da sauri ta na kallon shi ganin yana kallon ta yasa ta yi wani irin da fuskar ka kamar za ta yi kuka murmushi yayi kamar bai ga abindm da ta yi ba ya ci gaba. "Da gaske na ke maka Al'ameen wallahi akwai wanda ya ke son ta kuma auren ta zai yi" huci mai zafi Al'ameen ya sha'ki iska ya fitar ya na 'kure Zainab da kallo ya ce "innalillahi wayyo Allah na gaskiya na ji ba'kin ciki ban ji dad'i ba ina ma ace na riga wancan yanzu idan na ro'ke shi zai iya bar min ita"? Kai Sameer ya girgiza ya na cewa. "A'a gaskiya ba zai iya bar maka ba". "Ko na ce zan bashi duk abin da ya ke so yana da sana'a ne ko ya na da fili ka fad'a masa duk abin da ya ke so ni zan ba shi ko jari ya ke nema in dai zai bar min ita ka fad'a masa ka bashi number ta ya kira ni sai mu had'u"? Murmushi Sameer ya yi ya na girgiza kai yace. "Shi ma ba baya bane yana da komai Al'ameen ba abin da ya nema ya rasa duk abin da ka lissafo ya na da su shi ma sai dai ya baiwa wani mu ma a 'karkashin inuwar sa mu ke". "Da gaske Sameer"?. "K'warai na fad'a maka gaskiya ne saboda kai aboki na ne babu rufewa tsakanin mu". "Gaskiya ne na gode Sameer amma ba ta da 'kanwa ka ba ni"?. "Ba ta da wata 'kanwa ita kad'ai ce sai Bilki ita kuwa ba ta da hankali ba zan so ka auri yarinya irin ta ba" murmushi Al'ameen ya yi yana kallon Sameer ya ce. "Humm ko dai hana ni ka ke son yi ba shi ya sa kace haka"? Dariya Sameer ya you yana cewa "kai a'a ba haka ba ne ka yarda da ni da gaske na ke fa". "Na yarda kai Sameer shi ke nan na gode amma kai sai yaushe za mu zo na ka bikin ka ga anan saina za6i matar auren da kai na". "Aure na akwai dogon lokaci domin ko kad'an ba ni da budurwa balle na yi batun auren ka gan ni iya fili na siya ko ginin ban fara ba". "Sai yaushe za ka yi to"?. "Ba rana sai na shirya". "Tom Allah ya kai mu" hankalin sa ya mayar kan Zainab wacce ta ke sauraron duk wata hira da su ke ya ce "big girl sai an jima ina ro'kon Ubangiji ya bani matar aure mai hankali da cikakkiyar nutsuwa irin ki" ya fad'a yana mi'kewa da murmushi akan fuskar sa ya kalli Sameer ya na y "na wuce sai mun sake had'uwa". "Ok Al'ameen na gode" hannu ya mi'ka masa su ka sake gaisawa sannan ya wuce kallon Zainab ya Sameer ya yi bayan wucewar Al'ameen ya ce "ba dan an riga shi ba wannan abokin na wa mutumin kirki ne da shi zan aura miki" kai Zainab ta jinjina tana cewa "waye ya riga shi? Ni fa bani da kowa" ta fad'a ta na had'e rai dariya yayi yana mi'kewa ya ce. "Lokaci ya yi mu je mu tafi gida kar magriba ta yi mu na nan maganar ba ki da kowa kuma bai taso ba domin ki na da kowa ta so mu je" tashi ta yi su na fita daga gurin ya je ya d'auko mashin d'in sa ta hau su ka tafi a hanya Sameer ya ke cewa. "Ki kace baki da kowa Zainab ina ki ka jingine wancan abokin na wa"? D'an yatsina fuska ta yi tana cewa "Yaya Sameer ni kam ban mayar da maganar Aliyu ya na so na komai ba" da mamaki ya ce. "Kai lallai ma saboda me"?. "Saboda ba na jin a raina cewa shi miji na ne". "Au wai akan haka ne dama? Za ki ji daga ranar da aka d'aura miki auren da shi" ya na rufe baki ta ta'be baki ta na cewa "hummm hum'um". "Ya na ji kina jan numfashi me ya faru fad'i man"?. "Me zan fad'a"?. Na ji kin ce humm na san akwai magana a bakin ki shi ya sa na ce fad'i". "Ni ba wani abu zan fad'a ba" daga haka ta sauya zauncen da cewa "Yaya Sameer ka san me wannan mashin d'in na ka idan ka hau yana maka kyau". "Da gaske ai kuwa shi ya sa nake son abu na yanzu addu'a na ke ma Allah ya hore min na yi gini na sai mota ko"?. "Ba aure za ka fara yi ba"?. "Eh zan yi amma ba yanzu ba sai na gama komai na nutsu saboda kar na rame kin san yadda ango ya ke komawa kuwa idan aka kusa aure wani sai kin tausaya masa musamman talakawa irin mu haka za ki gam mu kamar skeleton" ya rufe baki Zainab ta fara dariya Zainab tana cewa. "Kai Yaya Sameer me ne abun ramawa a nan"?. "Akwai ramewa man ka yi wancan ka yi wannan duk lokaci guda ki tuna abubuwan da suke jira na gini lefe sadaki kin ga kuwa ai ni nake da aiki" kai ta jinjina ta na cewa "uhm haka ne gaskiya da aiki Allah ya bud'a maka 'kofofin samu ka yi abubuwan da ba ka yi ba". "Amin" ya ce yana parking a 'kofar gate d'in gidan Zainab ta sauka shi kuma bai sauka ba ta bud'e masa gate d'in ya shigar da mashin d'in cikin gidan saida ya kai shi har 'kofar d'akin sa sannan ya yi alwala ya fita ita ma tana aje handbag d'inta fitowa ta yi ganin lokaci ya na neman fita an jima da yin sallar magriba d'in da sauri ta yi alwala ta je ta yi sallar tana zaune akan sallayar akai kiran sallar isha ta tashi ta yi tayi shafa'i da wutiri sannan ta yi addu'a ta tashi ta cire hijab kenan ta ga Aunty Murjah ta bud'o labule ta shigo ta na sauke numfashi kallon ta Zainab ta yi tana cewa.............. ZUCIYAR ALIYU CE WRITTEN Yusrah Musa. @YUSRAH YMA DUTSE PAGE 42 "Y'an dinner sai yanzu kenan"? Sabon numfashi Aunty Murjah ta sake saukewa tana cewa "uhm ke dai bari ai saida aka tashi sannan mu ka taho da har zan kira Sweet nace yaje mu tafi ta can kuma na tuna da kaya na anan bayan haka ban yi muku sallama ba" juyowa Zainab ta yi tana kallon ta da murmushi ta ce. "Ai da kin tafi ba komai za mu fahimce ki" zama ta yi tana cewa "ai ina son dawowa gidan ne ba dan haka ba sai ranar da mu ka had'u". "Sallah

Chapter 18 of 34