ko nan da wata guda ne ko shekara ka zauna kayi nazari a kaina komai kake so nayi alkawari zanyi maka zan gyara halaye na".
Kaiya girgiza yana kallon ta kamar yadda ta kafe shi da ido yace "maganar zaki canza halayen ki wannan ba gaskiya bane domin hali tamkar zanen dutse ne bashi shafuwa koda kinyi kokarin canzawar daga baya zaki koma kan halin ki da ace zaki canza Baby da yanzu kin canza shekara ta nawa dake a hospital d'in nan ina fad'a miki abinda ya kamata ina miki nasiha amma bakya d'auka na gwada ki ta hanyoyi da yawa amma baki iya cinye jarrabawar da nayi miki ba some times nakan yi wani abu saboda naji me zaki ce a kai saina tarar kin 'kalubalancin abun koda ya kasance gyara ne ga rayuwarki sannan idan naga kuskure na nuna miki maimakon ki min godiya saidai ki nuna kinji haushi da tunatarwar da nayi miki yanzu Baby me irin wadannan halayen ce kike so na aura a tunani na ko baki furta min ba ni nazo miki da kalmar soyayya zaki ce a'a baki dace dani ba naje na nemi mace ta gari wacce idan na fad'a mata magana zata ji idan na bata umarni zata yi aiki dashi yanzu tsaya nayi miki misali kamar wannan budurwar da kika bugeta ranar da naje da basket hospital kece da laifi gashi wayarta ya 6aci maimakon ki bata ha'kuri sai bala'i kike mata harda marinta kuma ina miki magana kina dad'a daga muryarki akan tawa hakan gani kike ado ne? Na fad'a miki wani abu da zai baki mamaki kwanan baya mun had'u da ita a wani wuri abinda tace min tana sake bani ha'kuri akan wannan abun daya faru tsakanin ki da ita gashi ke da muka shiga office ina miki fad'a sai kika nuna abinda kikai shine daidai ko"? Hankali tashe ta ce.
"Ban yi tunanin hakan wani abu bane"?.
"Baki tunanin hakan wani abu bane ashe idan yayan ki yana miki fad'a a gidan ku bakya tunanin kiyi shiru ki saurare shi sannan ki bashi ha'kuri ko kece da gaskiya"? Shiru tayi jikinta yana tsumma ta sunkuyar dakai hawaye sai faman zuba mata yake da tasan Shareef yana komai dan ya gwada tane da ta zama cikin mata masu ha'kuri data kame kanki ta danne kowanne irin abu idan ya taso gashi yanzu tana gani duk yadda take son shi ya nuna halinta bazai barshi ya aure ta ba kuka ta fashe dashi tana girgiza kai ta kasa magana.
"Kuka bazai miki amfani ba kamata yayi kije ki zauna kiyi nazari sosai ki gyara halayyarki ki ri'ka kallon mutum da kima domin d'an Adam ba abun wula'kantawa bane kamar yadda ke kika d'auka" sosai ta ke kuka tana girgiza kai cike da tarin nadama tace.
"Wallahi Shareef na tuba daga yanzu na gane na amince ni ce na zalunci kai na kuma zan gyara kamar yadda ka ke bu'kata amma dan Allah kar ka fitar dani a cikin rayuwar ka hakan zai cutar dani kar ka watsar da ni".
"Ai dama bance zan watsar dake ba maganar da kika zo min dashi ne yasa nima na fad'a miki abinda ya kamata ace kin sani game da ni ba zan iya rufe miki gaskiya ba ko dan mutunci da sanayyar da ya ke tsakanin mu" huci mai zafi ke fita daga jikin Baby tsabar irin tafasar da zuciyar ta ke yi ta ce "in dai ba za ka watsar dani ba to Shareef ka kar6i soyayya ta ka ji"?.
"A'a wannan kuma ba zan iya ba kawai ki yi ha'kuri Baby za mu ci gaba da mutunci idan kin bu'kaci hakan amma ba maganar so ba kin gane"? Shiru Baby ta yi ta kasa cewa wani abu daga haka gabadaya hankalin ta neman fita daga jikin ta ya ke yi shi ma daga haka bai sake mata magana akan komai ba sai mi'kewa da ya yi yana cewa.
"Zan tafi ki kula" ya na fad'in haka ya juya ya bud'e 'kofa ya fita hannu Baby ta d'ora a ka ta fasa ihu me 'karfi wanda ba san ta yi ba tsabar rud'ewa da cikin azama ta yi saurin rufe bakin ta tana fatan Allah ya sa kar a jiyo daga cikin gidan su kai ta kifa akan kujera kawai ta yita kuka domin idan ba kukan ta yi ba baza ta ta'ba jin sassauci a zuciyar ta ba..............
ZUCIYAR ALIYU CE
•♣ YSRH ♣•
@YUSRAH YMA
PAGE 53
Yau Zainab ba za ta samu damar zuwa school ba sakamakon tun dare da zazza'bi ta kwana gari ya na wayewa ta soma kwara amai da sauri Umma ta fito ta na zuwa in da take a dur'kushe ta na ta amai kwaaa kwaaa yellow shar alamar malaria ce d'agota ta yi ta jingina ta a jikin ta ta na cewa.
"Sannu Zainab zazza'bi ki ka tashi da shi sannu bari Sameer ya tashi daga barci sai ya duba ki" numfashi kawai Zainab ta ke yi sama-sama kamar minti biyu Umma ta na 'ko'karin mi'kewa ta kai ta d'aki sabon amai ya sake 6alle mata wannan karon har jikin Umman ta 6ata juyi Asabe ta yi daga kwancen da take jin 'karar amai ya sa ta zaro ido ta na tashi zaune tare da dirowa daga kan gado da gudu ta fito waje ta na yin inda ta ga Umma da Zainab d'in a dur'kushe 'karasawa ta yi ta na tafa hannu ta ce.
"Laha'ilah ha'illallahu Zainab amai ki ke wato ciki ne da ke"? Ba wanda ya kula ta ta ci gaba "kan uban nan wallahi ba ku isa ba gara da asirin ku ya tonu yau kowa zai sani ashe dama ke 'yar iska ce? Humm aiko baki Isa ki haifa mana d'an shege a cikin gidan nan ba, ba za ki sa yaran mu su rasa mazajen aure ba sai dai ki tafi D'an Yana can dangin gyatumar ki, ki haifa musu tsiya a can yanzun kuwa zan tara mu ku jama'ar gidan nan kowa ya zo ya gani da idon sa kar a 'karya ta ni daga baya" ta na rufe baki ta d'ame iya 'karfin ta, ta fasa wani uban ihu ta na cewa.
"Yekuwa jama'ar gidan nan kowa ya fito yau ya ga abin da Zainab ta ke aikatawa" ta fad'a ta na fita daga 'kofar ta su ta sake yin sabon ihu ta na cewa "wai ba, mutane a,gidan nan ne ba za ku fito ku yi kallo ba wayyo Allah jama'a ku fito wayyo yau wa su asirin su ya tonu" haka ta yi ta bin 'kofa 'kofa ta na hela tuni kuwa kowa ya fara fitowa yara da manya kowa tambaya ya ke.
"Me ya faru asirin su waye ya tonu"? Nuna 'kofar shiga lungun su Asabe ta yi ta na cewa "cikin shege ne da Zainab tun jiya da dare take amai har yau yanzu ma su na nan a waje tare da munafukar uwar ta tana faman kwara aman kamar ba za ta daina ba" jin abinda Asabe ta ce ya sa kowa ya zaro ido wasu na cewa.
"Ciki? Tabd'ijan dan'kari yau ake bala'i bari mu je" rudududu suka fara gudu su na shiga 'kofar su ka je su ka zagaye Umma da Zainab kowa ya na salati kai Asiya ta jinjina ta na cewa "Allah ya so Zaidu da ya'ki auren yarinyar nan da yanzu an cusa masa d'an wani an d'ora masa bala'i" kai Asabe ta jinjina ta na cewa.
"To kin gani dai gashi nan ciki gare ta da aka so lalla6a ku ki kar'bi jikan da bai fito daga jinin d'an ki ba ni fa dama abun nan yana bani mamaki kwanakin nan na ga yarinyar nan ta yi wani irin fari ta sake ja d'auu idan ta fito rana ka kalle ta har d'auke maka ido ta ke tsabar yalo da haske ashe hasken ciki ne 'kayan kwad'ayin da ake siyowa aci ba'a banza ba kullum ba'kar leda ta na tafe da tofe-tofen yawu".
"To wai tsaya an fad'owa Hajiya ne"? Cewar Mairo wacce ke tsaye ta na dariyar farin ciki kai Asabe ta girgiza ta na cewa "ina za'a fad'o mata idan ba so kike mu ma mu shiga uku ba kina ganin fa laifi ko ba naka bane idan ta ga dama sai ta 'ka'kaba maka dan kawai ta samu hanyar da zata ci maka mutunci".
"Wallahi ko ma meye sai an fad'o mata dole ta sani wannan babbar matsala ce ba abu ne wanda za'ai shiru a rufa asiri a kan su ba".
"Dama wa zai rufawa Hauwa asiri a gidan nan? Sai dai munafiki irin ta amma indai mutum yasan gaskiya bazai yarda da wadannan mutanen ba".
"To yanzu dai kawai aje a fad'owa Hajiya ta zo taga komai da idon ta" cewa Asiya ta na fita daga 'kofar da sauri Umma da ke zaune tare da Zainab a jikin ta bata cewa kowa komai ba sai mi'kewa da ta yi ta na d'ago Zainab ganin yadda su ka zagaye su kamar wanda su kai sata ya sa ran Umma ya yi mugun 6aci ba tare da ta yi magana ba ta hankad'a su gefe za ta wuce caaaa su ka yo kan ta kowa na fad'ar tsiyar da ya d'ebo a bakin sa ya na sauke mata jin hayaniya yasa Sameer tashi ya fito wajen ganin yadda 'kofar take fal da mutane ga Umma a tsakiyar su ta na ri'ke da Zainab wacce idon ta ke rufe hawaye ya na zuba cike da mamaki ya 'kasaro ya na cewa.
"Umma lafiya"? Tun kafin Umma ta yi magana Asabe ta yi caraf ta ce "shashashan banza wato ita zaka tambaya lafiya a tunanin ka zata fada maka gaskiya ne? To yau Allah ya toni asirin mayyar ta ka ciki gare ta gashi nan amai ta ke" a rud'e Sameer ya ce "ciki kuma"? Tsananin mamaki ya gama rufe shi da 'karfi Asabe ta ce "eh cikin shege ma kuwa ga ta nan ai idan kana tunanin 'karya ko sharri akai mata" shiru Sameer ya yi yana kallon Zainab wacce har lokacin hawaye basu daina zuba mata ba kuma ba ta bud'e idon ta ba ya ce.
"Wannan ba gaskiya ba ne hakan ba zai ta'ba faruwa ba har abada wallahi duk wanda ya fad'a muku ma ya yi 'karya".
"Ni ce na fad'a ni ce ma'karyaciyar kenan tun da duk mutanen wajen nan ba wanda ya sani sai da na je na fad'o musu".
"Amma Umma me ya sa za ki yanke hukunci akan abin da baki tabbatar ba babu kyau shedar zurrr" a masife ta ce "kai dan kan uwar ka na yi shedar zurrr d'in sai kasa a yanke min hukunci".
Bai kula zancen da take masa ba sai kallon Umma da ya yi yana cewa "Umma ki mayar da ita d'aki bari na je chemist na d'auko kayan aiki na zo na duba ta" yana fad'in haka ya koma d'akin sa ya d'auko key d'in chemist d'in ya fito ya saka takalmin sa ya fita a hanya ya had'u da Hajiya ta fito za tai 'kofar ta su ganin sa yasa tace.....................
ZUCIYAR ALIYU CE
@YUSRAH MUSA
PAGE 54
"Kai Samar tsaya uban waye ya yiwa Zainab ciki"? Jin tambayar da ita ma take masa ya sa ya ta'be baki ya na wucewa ya ce "ki je ki tambaye ta man" ya na fad'in haka ya fice kai Hajiya ta jinjina ta na ci gaba da tafiya ta ce "za ta ci uban ta ai wallahi yau sai ta fad'a min tsinannan da ta je ya bata kud'i ta bashi kan ta ko na yi mata duka da wannan sandan" 'kofar ta shiga ganin yadda ta ke cike da mutane ya sa tace.
"Ina me cikin ta ke ko na'kuda ta ke yi"? Jin tambayar da ta yi yasa wasu daga cikin 'yan matan gidan su ka rangad'a gud'a a fusace Hajiya ta ce "mitsiyata dan tselan uwa ku da ku ke shewa da farin ciki shashashu ba ku san idan labari ya fita waje ba saurayin da zai sake zuwan gidan nan neman aure ba mahaukatan banza ina magana ku na dariya ai lalacewar har da kowacce sai dai ta zauna a gaban uwar ta ta tsufa ba miji".
"Ni kam aure sai na yi wallahi ko d'an shaye-shaye ne balle ma Allah ya rufa asiri wacce nan idan kin ji ana cewa ta gaban jirgi ta gaban mota ni ce" Rasheedat ta yi maganar ta na nuna kan ta kallon ta Hajiya ta yi ta na cewa "zan ci uban ki ne 'yar marar kunya kawai bari a gama wannan abun wallahi sai na miki duka a gidan nan" hararar ta Rasheedat ta yi tana cewa.
"Allah ya sauwake na bari har na zauna ki dake ni kamar 'kasa ce abinci na" kai Hajiya ta jinjina ta na cewa "wallahi tun da na rantse ba zan yi kaffara ba sai dai ki bar gidan nan har abada amma sai na dake ki" ta na fad'in haka ta shiga d'akin Zainab iya Umma ce a ciki sai Asabe dake tsaye ta ri'ke labulen 'kofar d'akin ta na jijjiga ta na harare-harare zama Hajiya ta yi akan kujerar d'inkin Zainab ta na kallon Umma ta ce.
"Kin zo kin saka yarinya a gaba kin yi tagumi dan munafirci kamar ba ke ce ki ka d'ora ta akan wannan mummunar hanyar ba yau wa gari ya waya wa"? Kan Umma a sunkuye cike da damuwar maganganun 6atancin da 'yan gidan su ke fad'a akan Zainab wanda ba gaskiya ba ne hawaye ne ya ke ta zuba mata takaici ya hana ta iya d'agowa balle ta yi magana har Sameer ya dawo d'akin ya shigo zai fara duba ta Hajiya ta ce.
"Kai Samar ban yarda da kai ba kar ka fara duba ta ba baza ka ta'ba fad'a min gaskiya ba" jin abin da tace yasa Sameer had'e fuska ya na cewa "ai dama ba sai na fad'a miki gaskiya ba ni dai damuwa ta 'yar uwa ta, ta samu lafiya" ya fad'a ya na dur'kusawa a kusa da Zainab ya fara duba ta waje Hajiya ta le'ka ta na kallon Zakiyyah da ke tsaye a 'kofar d'akin ta ce.
"Ke Abdul-Razza'k ya tafi asibiti ne"?.
"Ban sani ba ko ya tafi kira miki shi za'a yi"? Zakiyyah ta fad'a cike da gulma ta na le'ken d'akin ta ga ina Zainab d'in muryar Hajiya ta ji ta ce "eh kira min shi ki ce ya zo ya duba Zainab ya taho da abun gwajin ciki" dariya Bilki ta yi jin abin da Hajiya ta ce harda girgiza ta na cewa "ayuririiiiiiiii wayyo Allah na dad'i kashe ni ashe kwanan nan za mu ci ragon suna" wurgo mata sanda Hajiya ta yi tana cewa "a gidan uban ki za ku ci ragon shegiyar yarinya mara kishin zuci" ta'be baki Bilki ta yi tana cewa.
"Ina ruwa na da ita da zan damu dan ta yi ciki dama ni nace ta je tayi"?.
"Da baki ce ta je tayi ba ina uban ku d'aya kuma yayar ki ce duk tsiya idan ana gulmar za'a ce 'yar gidan Abdullahi ta yi cikin shege abun bai shafe ki ba"?.
"Caf wallahi Hajiya bai shafe ni ba babu had'in hanyar mota data jirgi dan mu na uba d'aya ta yi abun kunya ba dalilin da zai sa na damu kai na akai".
"K'warai kuwa ba abin da yayi miki zafi ai ba ke ce kika sa taje gurin samarin banzan da suke bata kud'in ta na bushasha ba" Asabe ta fad'a tana gyara tsaiwar ta ran Sameer a 6ace ya d'ago ya na cewa "wai dan Allah me ye haka Umma"? Kamar Asabe ta buge shi haka ta ji lokacin da yai maganar ta ce "uban ka ne haka nace uban ka ne ba zan fad'i abin da ya ke raina ba saboda tsoro ko me"?.
"Saidai uban ki ne haka ba uban sa ba" Hajiya ta fad'a ta na aikawa da Asabe harara hannu Asabe ta d'aga ta na cewa "Hajiya ba ruwan ki anan tun da ba dake na ke ba magana ce tsakani na da d'ana" baki Hajiya ta bud'e za ta yi magana sallamar Abdul-Razza'k yasa ta yi shiru shigowa ya yi ya na kallon dukkan su ya ce.
"Me ya faru Hajiya ki ke tura nema na lafiya"?.
"A'a ba lafiya ba ka ga yarinyar nan zaka duba min" kallon Zainab dake kwance ya yi ya kalli Sameer wanda ya ke duba ta yace "kuma Hajiya bayan ga Sameer nan shima fa likita ne gashi ya na duba ta" kai Hajiya ta girgiza ta na cewa "ai ban yarda da shi bane bakin su d'aya ko da matsala zai iya 6oye min shiyasa na sa a kira ka d'auko na ka kayan aikin ka duba ta yanzu" da har zai sake magana amma gudun abin da Hajiyan zata ce yasa ya fita ya koma kofar su ya d'auko kayan aiki shima kallon Sameer Hajiya ta yi tana cewa.
"Kai Samar tashi ka baiwa 'kwararre guri ya bincika min sosai" kai Sameer ya jinjina kamar zai yi magana amma gudun hayaniya ya sa ya matsa kad'an ya barwa Abdul-Razza'k gurin shi ma du'kawa ya yi ya fara duba ta kamar yadda Sameer d'in ya yi sannan ya ce.
"Hajiya ba komai ba ne zazza'bin malaria ne kawai ya ke damun ta" yana rufe baki ta ce "karya ka ke" da mamaki ya juyo inda ta ke ya na cewa "ban gane 'karya na ke ba kamar ya"?.
"K'arya ka ke man naga ka kalli Sameer kafin ka yi min magana" baki ya bud'e cike da mamaki ya na kallon ta yace " da yaushe ki ka ga na kalli Sameer d'in ni fa Hajiya ba na son irin haka dama na san 'karshen abun nan sai mun yi fad'a kin ce a duba ta kuma na fad'a miki abin da ya ke damun ta kin ce 'karya na ke me yasa"?.
"Dole na ce 'karya ka ke domin kai ma ka 6oye min da kai za'a had'u aci amana ta ba ka fad'a min gaskiya ba ciki ne da Zainab".
"Ciki kuma Hajiya"?.
"Eh ciki duba min watan sa nawa".
"Ke d'in waye ya fad'a miki ciki ne da ita".
"Ciki baya 6oyewa duk tsiya dole zai nuna kan sa idan lokaci ya yi ga shi nan ance amai ta ke ga zazza'bi kuma na ce ciki kai ma kana neman mayar dani 'karamar yarinya wacce ban san me na ke ba kubar gani na tsohuwa ban fara gigi ba har yanzu kalau na ke kuma ina ganin kowa tas kamar idon yara" d'an kamarin tsaki Abdul-Razza'k ya yi ya na cewa.
"Wai Hajiya me ki ke yi haka ne a iya aman ta fa wannan zazza6in malaria ne ba ciki ba meyasa kike son 6atawa yarinyar nan suna ne wallahi ba abin da ya ke damun ta zazza'bi ne kawai ni ban ga komai ba haba dan Allah" nuna shi da yatsa Hajiya ta yi tana cewa.
"Kai Abdul-Razza'k ka kiyaye ni ka fita ido na bana son fitsara irin ta 'ya'yan Asiya ko kai ma d'an uwan Zaidu ne"?.
"Hajiya dole na fad'a miki gaskiya ko bakya so ni ba rashin kunya zan yi miki ba abin da na gani shi na fad'a miki Zainab ba cikin komai a jikin ta malaria ce kawai ya saka ta yalon amai amma idan ba ki yarda ba zanyi mata gwajin cikin"? Gyara zama Hajiya ta yi ta na cewa "da dai yafi amma wallahi ba zan ta'ba yarda ba ciki ne da ita ba sai na ga zahirin ba ta haihu ba yarinyar da ta ke yawo da samari masu gajerun wanduna da dare...................
"Oh my God innalillahi wa inna ilaihi raji'un Hajiya ya isa haka dan Allah ki yi shiru wannan ba tsari ba ne tun da so ki ke kiga zahiri bari na zo" tashi ya yi ya fita Sameer ya na gefe a zaune ya tsume ran sa in yayi duba ya 6aci ji yake ba dan Hajiya mahaifiyar mahaifin sa bace da ace wata daban ta yi wannan maganar sai ya mata dukan mutuwa sai dai idan hukuma ta kama shi ayi masa d'aurin rai da rai amma saboda kar ya yi magana turirin da yake ran sa ya fito ya nuna 6acin ran sa a fili ga Asabe ta na gurin shi ya sa ya yi shiru kawai har Abdul-Razza'k ya dawo da wata 'yar siririyar roba me d'an jan murfi ya bai Zainab ya ce ta tashi ta je ta kawo masa fitsari ya gwada duk da Zainab tasan ba wanda ta ta'ba baiwa kanta ta yarda da kanta amma sai da taji zuciyarta ta hau dukan d'ari-d'ari da'kyar ta mi'ke jikin ta ya na rawa ta fita ta ga waje ma har lokacin 'yan matan gidan su na kofar sun yi tsit kowa jira ya ke yaji salatin Hajiya ko na Asabe cewa cikin ne da Zainab ganin ta fito ta yi hanyar band'aki yasa suka bi ta da kallo har ta fito ta zo ta sake wucewa ta kai masa komawa ta yi ta kwanta ta na addu'a a zuciyar ta Umma ma gabadaya ta rud'e PT Abdul-Razza'k ya d'auka ya d'an saka ya dagwalo ya d'ago shi ya zuba ido kafin ya ja tsaki me 'karfi ya na mi'kawa Sameer ya ce.
"Kalli da idon ka, ka gani na rasa me ya ke damun 'yan gidan nan kamar rashin tarbiyya a kan su ta 'kare" kar'ba Sameer ya yi shi ma yaga dai layi d'aya PT d'in ya nuna ba layi biyu ba kai ya jinjina ya na cewa "Allah na gode maka d'an ba'kin ciki sai ya mutu duk wanda ya ke son ganin ba'kin cikin Zainab sai dai ya ci kan sa Allah ya fitar da ita daga zargi kuma sai Allah ya saka mata sharrin da akai 'yan ba'kin ciki kuma sai su yi tono su binne kan su alkaba'in da suke nema bai samu ba" kallon sa Hajiya ta yi tana cewa.
"Uban wa yace maka ba'kin ciki ake mata uban me ku ka gani a jikin wannan d'an siririn abun munafikai har ku ke fad'awa mutane magana" mi'kewa Abdul-Razza'k ya yi yana cewa "ba kin ce a duba miki idan ta na da ciki ba? To bata da shi" ya na fad'in haka ya juya zai fita Hajiya ta ce "kai Abdul-Razza'ku ba na son 'karya ka fad'a min gaskiyar abin da ka gani".
"Ai Hajiya gaskiyar abin da na gani na fad'a miki daga 'kin gaskiya kuma kowa ya san sai 6ata wallahi tallahi na rantse da Allah wanda ya halicce ni Zainab ba ta da ciki zazza'bin malaria ne ya kama ta sosai shi ya sa ku ka ga tana amai" sauke ajiyar zuciya Hajiya ta yi tana cewa "shikenan na yarda na san kana da hankali ba za ka min rantsuwa akan 'karya ba shi ya sa nasa aka kira ka amma da Samar ne ya fad'a min ba zan ta'ba yarda ba".
"Humm Allah ya rufa asiri Allah ya shiryar da 6atacce" Abdul-Razza'k ya na fad'in haka ya fita daga d'akin cike da takaicin jin ba ciki ba ne malaria ce Asabe ta harari Umma wacce ke gefe ta na goge hawayen fuskarta kamar za ta ja tsaki amma saboda kar ace ta na daga cikin 'yan ba'kin cikin gidan yasa ta saki labulen dake ri'ke a hannun ta tun d'azu ta fice fuuuu daga d'akin su ma na wajen jin abun da Abdul-Razza'k d'in ya fad'a yasa d'aya bayan d'aya su ke mi'kewa su na fita kowa murna ta koma ciki.
"Kin gani ko Hajiya kin ga irin abin da nake fad'a muku wai ana zuwa idan aka fad'a muku magana ba bincike sai ku hau ku zauna yanzu gashi kun zarge ta akan abin da bata aikata ba sai ku nemi yafiyar ta" Sameer ya yi maganar ya na tattare kayayyakin sa hararar sa Hajiya ta yi tana cewa "uban na nemi yafiyar ta dama ni ce nayi mata sharrin ina d'aki a zaune aka je akai kira na nazo kuma dan na sa an bincike ta meye abun laifi a
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 34