dashi sai tasa a cireta ta nuna mata karshen isar wace ita amma ba komai....................
Wayarta dake 'kasa Shareef ya d'auko ya saka 'karamin towel d'insa ya goge mata ya mi'ka mata d'agowa tai tana kallon sa tare da saka hannu ta kar'ba ranta na 'kuna da'kyar tace "na gode" ta fad'a tana juyawa ta wuce sosai ransa ya 6aci jin yadda tace masa ta gode d'in kowa yaji yasan ba kamarin ciwon abinda Baby tayi mata taji ba amma ta danne ta nuna godiyarta ga yar kulawar daya bata a fusace ya shiga office d'insa ganin ta tsaye yasa ya nuna ta da yatsa yana cewa "Baby daga yau kinyi na farko kinyi na karshe kar tsautsayi yasa na sake ganin idan nazo kinje tara ta ki barni komai nauyin kayan da nazo dasu na d'auko da kaina kin gane"? Had'e rai tayi tana cewa "yanzu Shareef saboda wancan yarinyar shine ka d'auki fushi dani ban kyauta ba kenan abinda nayi ban burgeka ba har kazo kana tuhuma ta"? Buga table d'in dake gaban kujerar da yake zama yayi muryarsa na nuni da tsantsan fushi yace.
"How to impress you meye abun burgewar anan wannan jahilci kenan kika nuna ba komai ba" nuna kanta Baby tai tana cewa "Shareef ni ka kira jahila saboda nayi fad'a a kanka"? Sabuwar tsawa ya sake buga mata "you are no one but stupid and let me tell you today i am ending all this burden" ganin yadda yake fad'a yana mata tsawa yasa itama zuciya tazo mata wuya cikin d'aga murya tace.
"Tell that to who is afraid Shareef na gaji da wannan tsawar da kake min saboda nayi wancan abun ne zaka sakani a gaba da fad'a kamar wani ubana na mareta kuma wallahi da nasan ita xaka baiwa gaskiya idan ka shigo saina sake marin ta" kaiya jinjina yana nuna mata hanyar fita yace "get out from my office" tsananin mamaki ne ya kamata har batasan lokacin da tace "Shareef na fitar maka a office kace akan wancan yarinyar ko sonta kakeyi ka fad'a min"? bai bata amsar tambayar ta ba sai sake nuna mata hanyar waje dayai yana cewa "as from today I don't want to see you in my office again har abada indai ba aiko ki akai ba kin gane"? Baki ta bud'e zatai magana ya daka mata tsaya.
"Get of my sight kafin na 6alla ki" tsawar da bata saba jin irin taba a rud'e ta fice da gudu tana zubar da hawaye wani irin 'kak'karfan tsaki yayi tsabar yadda ta 'kona masa rai akan abinda bai kai ace damuwa ta shigo ciki ba tasa ya 'kara 6ata lokacin sa anan aje wayar hannunsa yai yana d'iban abubuwan daya kamata ya d'iba ya fita daga office d'in hango budurwar da Baby ta mara d'azu yayi tana tsaye tare da wani doctor abokinsa kamar zaije yayi magana da ita ya sake bata ha'kuri akan abinda Babyn tai mata domin gani yake kamar shine sila laifinsa ne da baizo da basket d'in ba da Baby bata d'auko ba sannan itama da bata bugeta ba har suzo a samu sa6ani wucewa yai saboda yana sauri bai tsaya a gurin su ba.
Ita kam bayan sun gama maganar da suke saida ya rakata har inda motarta take driver yana ciki yana jiranta har zata shiga ta sake juyowa tace "Yaya Ammar yaushe ne ya kamata na dawo asibitin"?.
"No shiga kawai kije gida zanyi magana da doctor Ishaq d'in duk abinda yake faruwa idan na dawo zamuyi magana dasu Abba kinji" kaita d'aga tana bud'e motar ta shiga suka fita daga asibitin kafin shi kuma ya juya zuwa 6angaren da yake.
ZUCIYAR ALIYU CE
@yusrah Musa Abubakar
PAGE 07
Tafiyar Zainab tayi nisa domin har aka koma makaranta bata dawo daga d'an yana ba iya damuwa Aliyu ya shiga gashi baya so ya nuna damuwar tasa a fili yana iya bakin 'ko'karin sa ya danneta amma duk da haka idan ka kalleshi kallo d'aya zata fahimci halin da yake ciki na azabtuwa da jarabtar so yauma haka suna zaune tare da Sameer yana gwada kiran Zainab yace "Sameer kabar batun kiran nan kawai naga alamar gara muje can na gaji fa".
"Sorry Marshall insha Allah ta kusa dawowa dan Allah ka rage yawan damuwar nan haka".
"Taya kake tunanin damuwa zata barni kasan fa zuciya wata iriyar abace wacce idan taga abu tana so dole saika bata abun nan shine samun salamarka da kwanciyar hankali amma nifa gashi da bata samu abinda take so ba sai wahalar dani take kullum bata iya samun kyakkyawan barci".
"Babu abinda zance saidai kayi ha'kuri nasan baka cikin yanayin jin dad'i amma insha Allahu zan sake kiranta nace mata Ya Sayyidi yace ta dawo islamiyya idan taji haka da sauri zaka ganta ta dawo".
"Ok indai haka ne ka kira a waya man ka fad'a mata sannan ka tambaye ta ranar da zata dawo kar lokaci ya 'kure harna tashi tafiya bata dawo ba kaga bazan ji dad'i ba sosai iya nine nasan irin azabar da nake ciki idan kuma kana ganin muje can d'in ne a shirye nake"?.
"A'a kayi ha'kuri insha Allahu bazata wuce cikin satin nan ba munyi waya da ita jiya na tambaye ta tace ta gama shiri maybe nan da two days ka ganta" numfashi Aliyu ya sauke yana cewa "Allah yasa abinda ka fad'a ya zama gaskiya domin maganar Allah Sameer bazan 6oye maka ba rashin ganinta da banyi ba Ina mugun azabtuwa zuciya ta baza iya d'auka ba kawai ina jurewa ne na danne yanzun kuma naga bazan iya ha'kurin ba".
"Karka damu zaka ganta zuwa kwana biyun kamar yadda nace maka in Allah yaso".
"Ok shikenan yana iya da lamarin ka Sameer Allah ya yarda kawai shine abinda zan iya cewa bayan hakan bani da bakin magana sai na ganta" dariya Sameer yayi cikin tsokana yace "sai dakai na gidana nidai indai dan nine na baka Zainab ka aureta".
"Dama ko baka fad'a ba wannan yarinyar in Allah ya yarda matar aure nace ai".
"Allah ma ya yarda Marshall lokaci ne kawai bai kai ba shima muna fatan zuwansa cikin gaugawa" "to Amin idan addu'a ce kayi min dan naga dariyar ka tafi yawa".
"Da gaske fa addu'a ce nayi maka ta gari ma kuwa angon zee-zee" d'an murmushi Aliyu yai yana girgiza kai domin iya angon ta da yace masa ya d'an ji sassauci kuma zuciyarsa ta rage nauyin damuwar data d'auka ko sunanta yaji an ambata yakan ji tamkar ana shafa mata sansanyar ruwa a lokacin da yake jin zafi.
@YUSRAHMS
PAGE 08
D'AN YANA
Zaune wata 'yar tsohuwa take a 'kar'kashin bishiyar zaitun mai yalwar inuwa a tsakar gida tana gyaran shinkafar tuwo lokaci zuwa lokaci tana d'agowa ta gano ko wutar na ci kasa ha'kuri tai ta d'an kallo kofar d'akin ta ganin takalmin wacce take tunani yasa tace.
"Zainab Zainab kina ina ne"?.
"Gani a d'aki kaka A'i ina zuwa yanzu sun dawo ne"? Wata sassanyar murya zazza'ka ce ta bata amsa yayin da ta fito sanye da bakar doguwar riga tana murmushi lokacin data kallo yadda tsohuwar take faman aikin gyara shinkafar kai masha Allah kyakkyawa ce fara da gani bata da hayaniya karasowa tai tana zama a kusa da tsohuwar tare da dauke turen shinkafar cikin tsokana tace.
"Lallai kaka A'i akan kimin maganar cewa an kawo na fito na gyara shine kika d'ora da kanki kuma da wanne idon kike gyaran shinkafar"? Dariya kaka A'i tai tana cewa "da idanuwa na mana da naki na ara? Ki daina min kallo mai dindimi ras nake ganin ki".
"Au ni da yaushe nace kina dindimi kaka A'i"?.
"Ba fad'a kikai ba amma niyyar ki kenan duba min tukunyar inaga kamar ruwan yayi kadan" "ok tom kaka A'i Zainab ta fad'a tana mi'kewa zuwa inda murhun yake bata buda tukunyar ba ta tsaya tare da juyowa jin A'i tace "yaushe ma kika ce zaki tafi gida ne Zainab"? Kafin ta bata amsa wata budurwa ta shigo da sallama tana cewa "kai kakus miye zaki bata idan ta fad'a miki ranar da zata tafi d'in"?.
"Babu fa kawai dai na tambaye tane saboda naji jiya d'an uwanta ya kirata a waya yana tambayar lokacin komawar tata".
"To ba yanzu zata tafi ba saita dad'e mana rabin shekara zatai anan saiki sake sabon shiri".
"Haka tace miki uwar ma'karyata kinga Najat ina raba ki da kiwon aura kina cewa aura ta haihu ko Zainab d'in ce zatai shekara kuma makarantar fa ko saita ha'kura saboda jin dad'i dama irinki ce an fad'a miki ita bata wasa da karatu ki koyi da ita"? Dariya Najat tai tana cewa "to me za'a fasa mutuwa ko hisabi"?.
"Ba wanda za'a fasa saidai kimin shiru domin ba ke na tambaya ba sai naji daga bakin ta idan kuma kunyi maganar ne naji ko gaskiya ne"? Mikewa Najat tai tana shiga d'aki tace "eh man gaskiya na fad'a miki ai gata nan ki tambaye ta nikam shikenan bari nai baccin rabin lokaci kafin a gama yi mana tuwon shinkafa da miyar ganye muzo muci dad'i ko kakus"? Da kallo kaka A'i ta bita tana cewa "haka kika iya baki iya aiki ba sai ci kamar gara zan had'a ki da Balarabe ne bari yazo gidan gaishe ni ko zuwa jimawa ne" wuf taga Najat ta fito daga d'aki tana dawowa inda take zaune ta d'auki wu'ka ta soma yanka ganyen da za'ai miyar tana cewa.
"Shikenan kakus na fito sai komai ya wuce basai kin fad'a masa ba kiyi hakuri so kike ya had'a ni da Yaya Auwal kisa yamin duka"?.
"Ke kika sani yarnan ni bance yasa Auwalu ta dake ki ba amma dai idan baki tsaya kin koyi girki ba yanzu yaushe zaki koya"?.
"Cab jimin tsohuwa ce miki akai ban iya girkin ba ko me duk abincin da ake kawo miki daga gidan mu nice nake dafawa ba Ummar mu ba kuma bari na baki mamaki Zainab zo ki zauna nayi mata tuwon nan yau dai tasan ni ba kanwar lasa bace wajen fannin girke-girke" tai maganar tana mi'kewa daidai Zainab ta dawo 'kar'kashin biyar ta zauna tad'an girgiza kai tana kallon Najat kafin tace.
"Gashi can saiki kula" mayar da hankalinta kan kaka A'i tai tana d'aukar ganyen da Najat ta fara yankawa taci gaba tana cewa "am kaka ranar juma'a ta sama zan koma insha Allah".
"To Zainab Allah ya kai mu".
"Amin Kaka A'i"............
✨✍️YUSRAH MUSA
WRITER
1__Yarima Abdul-maleek
2___D'an millionaire
3____Safreeyyah
4_______Royalty
5____Minister Ashraf
6__Me kamar sarki
And now
Zuciyar Aliyu ce
Later
Yarima Aryan
💓ZUCIYAR ALIYU CE💓
PAGE 09
Kwana biyu tsakani Hajiya tana zaune Umma ta shiga zata gaishe ta bayan ta dawo daga bikin da taje a Katsina sallama tai ta shiga tana samun guri ta zauna cikin ladabi tace "Hajiya ina yini"? Kamar ba za ta amsa ba ta kalleta sau d'aya ta d'auke kai murya can 'kasa tace "lafiya" shiru Umma tai cike da damuwa ta rasa me taiwa Hajiya a gidan nan kowacce suruka zata zo ta gaisa ita ta amsa mata cikin sakin fuska amma banda ita............
"Yaushe wancan yarinyar zata dawo"? Taji muryar Hajiya ta katse mata tunanin da take yi numfashi ta sauke tana cewa "munyi waya da ita d'azu tace min sai juma'ar sama zata dawo amma nace ta taho jibi saboda an koma islamiyya".
"Au ashe da ba'a koma makarantar ba baza kice ta dawo ba a gidanku zata je ta tare ana karanta mata rashin da'a ta fita duk sanda taga dama ta dawo lokacin datai ra'ayi saboda an koya mata karuwanci dama taya zata so zaman nan tunda anan akwai sa ido shiyasa ta'ki aure kenan tana can tana taro muku kud'i ko? To wallahi bari kiji idan baki kirata yau kince sa'ko daga ni nace ta dawo gobe ba tofa sai kin bar gidan nan dan wallahi a goben sai sun ganki sai nasa Abdullahi ya sakeki kuma saki uku ba d'aya ba balle kisa ran zaki dawowa mutane gida dan na fahimta dasa hannun ki Zainab take komai a gidan nan kuma wai a hakan ke d'in 'yar malamai ce 'yar malamai ko kuma 'yar malaun-malun mtswwww" idon Umma fal yake da hawayen damuwa da takaicin maganganun da Hajiya take fad'a mata to amma ya zatai da rayuwarta haihuwa ce ta bata sannan tasan cewa dama can Hajiya ba 'kaunarta take ba kawai Allah ne ya 'kaddara zaman aurenta a gidan badan haka ba yadda ta kafa mata 'kahon zu'ka take sukarta da muyagun maganganu da watace baza iya wannan ha'kurin datai ba sama da shekara talatin da biyar tana fama da kayan ba'kin ciki....................
"Tashi ki bani guri sannan kada Allah yasa kiyi abinda nace miki na rantse da Allah gobe indai banga Zainab ta dawo ba kema zamanki ya 'kare cikin gidan nan fatan kinji ni dakyau"? Shiru Umma bata ce mata komai ba sai mi'kewa datai ta fita daga sashin Hajiyan bata yarda kowa ya fahimci me yake faruwa ba duk da can ma ta je ta tarar Asiya da Asabe su na fad'a amma bata iya tsayawa ba saboda abinda ke ranta yafi gaban nasu su hayaniyar duniya ce da abin duniya yake rud'a su ita kuwa 'kiyayya ake nuna mata ake nuna 'yarta d'aya da take jinta tamkar da dubu.
Tana shiga d'aki ta d'auki wayarta hawaye na zuba ta kira layin Zainab amma wayar a kashe aje wayar tai tare da ranka tagumi tai shiru kusan mintuna biyar daga baya ta sake d'auka da gwada jin a rufen ake sake ce mata yasa ta kira layin yayanta tace ya bada a kaiwa Zainab magana zasuyi Najat ya aika takai mata a lokacin ta gama linke kayanta kenan ta maida su cikin trolley Najat ta shiga da sallama tana cewa "Zainab ga Ummanki tana neman ki" fitowa daga d'aki tai tana cewa "Umma kuma lafiya dai fatan ba wani abu bane"? Ta tambaya hankalinta a tashe kai Najat ta girgiza tana mi'ka mata wayar tace "wallahi ban sani ba nidai kawai ina shigowa gidan mu naji babanmu yana waya yace nazo nakai miki ta kiraki bata sameki ba wayarki a rufe".
"Eh na kaita shagon caji ne tun jiya da dare ta rufe bari na kirata zuwa jimawa nasan ta cika sai naje na kar6o" ta karasa tana bin bayan kiran da Umman tai jin ta d'aga yasa tace "assalamu-alaikum Umma ina yini"? Muryar Umma da alama damuwa tace "lafiya kalau Zainab na kira wayarki ban same kiba dama cewa zanyi gobe ki taho da safe kinji"? Da mamaki Zainab tace "Umma da akwai matsala ne naji kamar muryarki da damuwa ko"? Kai Umma ta d'aga tana cewa "eh d'azu bayan na dawo daga Katsina na shiga gurin Hajiya zan gaisar da ita shine take cewa na barki kin taho nan kin zauna idan baki dawo gobe ba nima sai tasa babanku ya sakeni a goben na taho nan saimu had'u mu zauna shiyasa nace ki taho goben da safe kinji" wani irin d'aci da zafi ne ya tsaya a 'kirjin Zainab wato har yanzu Hajiya bata canza halinta ba kenan tana zagin Umma akan ta rufe ido tai hawayen da suka cika shi suka fara fitowa waje a hankali ta jinjina kai tana cewa "shikenan Umma ba damuwa insha Allahu zan taho karki damu babu abinda zai faru nasan saboda ni Hajiya tai miki haka amma ba komai zan dawo Allah ya rufa asiri'' "Amin Zainab Allah ya miki albarka saikin dawo".
"To Umma ki huta gajiya" katse wayar Zainab tai tare da saka hannunta duka biyun ta rufe fuskarta hawaye suna zuba ranta a mugun 'bace karshe kawai ta fashe da kuka da yake Kaka A'i da Najat suna waje babu wanda yasan abinda yake faruwa harta gama kukanta a lokacin ana kiraye-kirayen sallar magriba ta mi'ke daga d'akin ta fito ta baiwa Najat wayar tad'au buta tai alwala tana idarwa ta mi'ke ta d'auki kud'in da zata kar6o cajin tana kar'bo wayarta data dawo tai sallar isha sakamakon tasan kafin taje gida an riga anyi dare yaja ta shiga d'aki kawai suna zaune suna zance a waje sai ganinta sukai ri'ke da trolley tana ja da mamaki duk suke kallonta kaka A'i data aje carbin hannunta tace "a'a Zainab ina zuwa haka baki gama linke kayan bane"? Kaita girgiza tana cewa.
"Na gama gida zan tafi" da sabon mamaki Kaka A'i ta zaro ido tana cewa "Subanallahi gida kuma Zainab a wannan lokacin ki bari saida safe man ko wani abu ne ya faru naga kunyi waya da Ummar taki yanzu"?.
"A'a babu abinda ya faru kawai tafiya zanyi gobe da safe zan koma makaranta ne".
"To amma Zainab wacce irin tafiya ce yanxu da dare me zai hana ki bari da safe idan kin karya saiki tafi kodai akwai abinda yake faruwa acan lafiya kuwa".
"Eh lafiya babu komai Kaka A'i dan Allah kuyi hakuri ki barni na tafi yau insha Allahu babu abinda zai faru zanje gida lafiya nafi so naje yau bazan sake kwana anan ba" ganin da Kaka A'i tai kamar hankalin Zainab din a tashe gashi ta'ki ta tsaya akan saidai ta tafi yasa tace "to shikenan Zainab ba damuwa Allah ya kaiki gida lafiya ubangiji ya kare ki nagode ki gaishe da kowa" Kaka A'i na rufe baki Zainab taja trolley tai gaba tana cewa "na tafi" da kallo kaka A'i ta bita tana cewa "to Allah ya tsare amma wacce irin tafiya ce wannan da dare ba shiri ga shi ita Zainab ta kasance yarinya me zurfin ciki ba za ta ta'ba fad'a min abin da ya sa za ta tafi d'in ba Allah ya rufa asiri kawai" Kaka A'i ta fad'a cikin rashin kwancyar hankali da jimami...................
See you tomorrow morning.
@YUSRAH YMA DUTSE
PAGE 10
Zainab na fita ta tari me mashin ya kaita tasha daga nan bayan mota ta tashi suka nufo Kano amma duk da haka bata iso da wuri ba sai wajen karfe goma da rabi na dare Umma tana d'aki a zaune ta zubawa guri d'aya ido taji sallamar Zainab d'in ta shigo da mamaki sosai ta d'ago tana kallon ta daidai ta karasa shigowa cikin d'akin ta saki hannun trolley ta cire hijab tace.
"Sannu da gida Umma ina yini"? Har lokacin kallonta Umma keyi da mamakin da ya'ki 6oyuwa tace "Zainab lafiya na ganki yanxu meyasa baki bari sai gari ya waye ba"? Kaita girgiza tana zama tace "Umma hankalina ya riga ya tashi da abinda naji kin fad'a tunda naji haka nasan Hajiya ce tai wannan ba komai ba na tabbata na sake kwana a D'an Yana saina ganki sai tasan yadda tayi ta tura ki gida ni kuma hakan ne bana so shiyasa kawai na taho kuma koba haka bama ina son dawowar saboda kayan mutane wanda ban d'inka ba".
"Tom ba damuwa tunda kin dawo naji dad'in hakan Allah ya rufa asiri" Amin Zainab tace tana mi'kewa ta d'auki trolley ta zata kai d'akin ta daidai Sameer ya shigo tsaye yayi yana kallonta cike da mamaki shima yace "a'a wata sabon gani Zainab yaushe kika dawo ban sani ba ko yanzu na ganki kina kokawa da akwati"? D'an murmushi tai tana cewa "eh ban jima da shigowa Yaya Sameer ina yini"?.
"Lafiya kalau fatan kin dawo lafiya ya kika baro Kaka A'in taki"?.
"Tana lafiya itama tana can na barota a 'yar barandar gidanta tana kan sallaya".
"Ok masha Allah naji dad'in dawowar ki sosai dama d'azu na had'u da wannan yarinyar Hamimah tana tambaya ta wai kin gama musu d'inkin su nace a'a ban sani ba bakya nan saidai idan kin dawo ashema kina kan hanya".
"Eh ai nata d'inkin na gama saura iya na 'kanwar su itama na yanka had'awa ne banyi ba saidai gobe da safe tunda ba makaranta zanje ba" kaiya jinjina yana shirin magana Asabe data fito ganinsa tsaye da kuma wacce suke magana yasa a masife tace "Sameer ina maganin da nace ka kawo min ko saina mutu sannan zaka fahimci bani da lafiya ka tsaya zancen banza da wofi wanda bazai amfane ka ba" ta karasa maganar tana zafgawa Zainab harara baiyi magana ba sai karasawa dayai yana mi'ka mata yace "kiyi ha'kuri gashi na taho kawo miki naga 'kanwata ta dawo shine na tsaya mu gaisa" tsaki Asabe tai tana juyawa ta shige d'aki shima Sameer d'in waigawa yai ganin ba Zainab alamar ta shige d'aki yasa shi komawa bakin kofar d'akin nata yana cewa.
"Zainab".
"Na'am Yaya Sameer" ta fad'a tana fitowa da 'karamin ba'kin mayafi a hannunta ta yafa shi a kanta "kina bu'katar wani abu ne"? Murmushin daba shiri tai saboda a rayuwa Sameer yana mugun burgeta yana sonta gashi dai ubansu d'aya amma baya nuna mata 'yan ubanci ba kamar Balki ba wanda ko kallon arziki ba ta yi mata sai habaici da ba'ka'ken maganganu.................
"Zainab nace kina bu'katar wani abu ne"? Kaita girgiza tana kallon sa cikin girmamawa tace "a'a Yaya Sameer na gode da kulawa".
"Ok bakya bu'katar komai kinci wani abu ne"?.
"A'a".
"Amma kikace bakya bu'katar komai please ki fad'a min abinda kike so na kawo miki bana so ki kwana da yunwa kinji"?.
"To Yaya Sameer kawo min gurasa mai 'kuli kad'ai ta isa".
"Ita kike so"?.
"Eh itan ma tayi".
"Ok bani mintuna ina zuwa" ya fad'a yana fita d'akin Umma ta koma ta d'auko handbag d'inta ta koma nata d'akin ta bud'e wayarta ta fara dubawa kafin ya dawo.
Fitar Sameer kam kai tsaye wajen wani mutum me soya doya da naman kaji a anguwarsu ya nufa ya siyo mata abar da tace tana so ya kawo mata godiya sosai tai masa harya juya zai fita tace "Yaya Sameer dan Allah kar'bi wannan ka siyo min klin da 'yan abubuwa a shago da safe zan kaiwa Hajiya kasan indai taga na dawo ban bata abun sannu da zuwa ba saita fad'a ni kuma ba tafiyar shiri nayi ba" murmushi yayi yana cewa "a'a barshi karki damu idan na tashi shigowa gida zan taho miki dashi saiki bata".
"To na gode Allah ya 'kara arziki" Amin yace yana fita itama ta tashi ta fita d'akin Umma ta shiga ta d'iba mata sannan ta koma taci iya wacce zata iya ci ta sake fitowa ta wanke hannunta ta komai fitilar wayarta ta kunna ta d'orata akan keken d'inkinta ta d'auko tsintsiya tai bismilllah ta share d'akin ta gyara katifarta ta fesa turare ta shimfid'a bedsheet tare da d'aukar wayar ta kashe fitilar ta kwanta.
ZUCIYAR ALIYU CE
@YUSRAH MUSA
PAGE 11
Kusan sha biyu da rabi babansu ya dawo daga gurin sana'ar sa dama already kullum saiya shiga gurin Hajiya sannan zai karasa kofarsa shiyasa yauma dukda dare yayi da harzai wuce sai kuma ya tuna indai baije ba gobe saita masa tas da safe shiga yayi ya tarar batai barci ba suna zaune tare da Haulat da su Balki kusan 'yan mata shida sun aje babbar waya suna kallo da sallama ya shiga ya gaisar da Hajiya ya aje mata tsaraba kamar yadda ya saba kullum yad'an siyo mata abun motsa baki ya mi'ke zai tafi tace.
"Abdullahi tsaya zamuyi magana dakai akan wancan yarinyar taka" jin abinda tace yasa saida gabansa ya fad'i tunda yaji tace haka yasan Zainab take nufi ya rasa me tai mata da jinin su baizo d'aya ba yarinya me cikakken hankali da nutsuwa wacce magana bata dameta ba amma Hajiya gabadaya tabi ta addabi rayuwarta ba dalili...........................
"Abdullahi ka kira Zainaba ka fad'a mata sa'ko lallai in jini ta dawo gida gobe wallahi tallahi na rantse da Allah idan bata dawo a gobe ba saika saki uwarta tabi bayanta ka gane kuma ka jini"? Shiru yai ransa babu dad'i bai iya ce mata komai ba cikin fad'a Hajiya taci gaba "nayi magana kayi banza dani saboda ka zauna da marar tarbiyya ta koya maka tsiya da yadda ake wula'kanta uwa shine zaka nuna min"? Kaiya girgiza a damuwance yace "dan Allah kiyi hakuri Hajiya idan na shiga yanxu zansa ta kirata zata dawo goben" gyara zama Hajiya tai tana mayar da hankalinta kan kallon da suke yi tace "wannan kuma ya rage ruwanka tsabar shashanci na rasa wanne irin so kake musu da baka ganin aibun su kodai asiri sukai maka nasan wannan son da kake musu ba banza ba idan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 34