Share this page
ta ri'ke ganin yadda su ka d'aure mata kai ita Zainab ta juya musu baya shi kuma Sameer ya dage akwai wanda za ta aura, huuuuuhhh ta sauke ajiyar zuciya ta na cewa. "To fa babba magana ni da aka ban sa'ko ya zan yi wannan al'amarin da nauyi" Zainab ta kalla ta na cewa "yanzu dai abin da za'ai idan ya dawo sai ki fad'a masa da kan ki domin ni ba zan iya ba ina jin kunyar sa" ta na rufe baki Sameer ya mi'ke ya na cewa "wallahi bai isa ba tashi mu tafi tun bai dawo ya same ki ba balle zuciyar sa ta ji dad'i idan ya gan ki" dariya Aunty Murjah ta yi tana kallon sa tace "kaii Sameer wannan har ka fi mai son Zainab d'in kishi irin wannan fad'a daga na fad'i haka ka tashi a zabure kamar an watsa maka ruwan wuta dan Allah ku tsaya man mu na hirar mu". "Kin san Allah tafiya za mu yi da gaske fa nake miki ba zai dawo ya same mu ba Zainab akwai wanda za ta aura idan ma kin fad'a masa ya'ki yarda shikenan shi ya sani dabara ta rage ta shi ko ya ha'kura ko kuma ya ci gaba da wahala idan yaga ta yi aure ya yarda tashi mu tafi Zainab ko dai ke ma ki na son sa ne kar na bada kai na"? Kai Zainab ta girgiza ta na mi'kewa ita ma Aunty Murjan tashi ta yi ta rako su har harabar gida suka hau mashin suka fita daga gidan suka barta ta na ta dariya.......... ZUCIYAR ALIYU CE J♣W♠A🤙 Story.Written.Editing “‰YUSRAH MUSA ABUBAKAR @YMA DUTSE JIGAWA PAGE 63 Su na cikin tafiya Zainab da ta sauke daddad'an numfashi ta ce "na gode Yaya Sameer gara da ka fad'a mata haka nima na huta Allah da gaske ko kadan mutumin nan bai yi mun ba" jinjina kai Sameer ya yi yana cewa "balle kuma ni gara da bai yi miki din ba ai da ko yayi miki dole ki bar shi" murmushi Zainab ta yi tana cewa. "Saboda me"?. "Saboda Aboki na man yaushe ina kallo zan bari wani Tom ko Jerry d'in zai zo ya na hira da ke bayan shi ya na so". "Ni fa Yaya Sameer abokin nan na ka bana saka shi a layin mutane da ace da gaske mutum ne da yanzu shi ma ya bayyana kan sa shekara kusan nawa ka na fad'a sai dai kullum ka ce zai bayyana har yanzu ya'ki bayyana d'in watakil ido ya bud'e maka kake ganin kamar mutum ne shi, ni dai ba ruwa na ba gara Mukhtar d'in ba tun da shi na gan shi da ido na kuma nasan mutum ne iri na da nayi soyayya da aljani fa"? Dariyar da ba shiri ta saka Sameer ya yi yana jinjina kai yace "da kyau kaiii da kyau tambaya me armashi, albishirin ki? To ki kwantar da hankalin ki ya kusa zuwa kwanan nan za ki gan shi in sha Allahu kun kusa had'uwa sai ki shirya tarbar sa" ya na rufe baki Zainab ta ja dogon numfashi ta na cewa. "Uhmmmmm!!" "Uhmm! kamar ya me ya faru"? Kai ta girgiza tana cewa "a'a babu komai" ta fad'a daidai sun 'karasa wani guri ya yi parking sau'ka ta yi shi ma ya sau'ka da mamaki ta kalli gurin ta na cewa "Yaya Sameer me za ka yi anan" key d'in mashin d'in ya cire ya na mi'ka mata ya ce "ri'ke min wannan ki jira ni yanzu ina zuwa" juyawa ya yi ya shiga cikin gurin ta na tsaye ya d'an jima kafin ta gan shi ya fito da plasma a hannun sa da mamaki ta kalle shi ta na cewa. "Yaya Sameer me za ka yi da plasma kuma ko a d'akin ka za ka saka"? Kai ya girgiza yana kar6ar key d'in ya tada mashin d'in ya na cewa "a'a ba tawa ba ce sa'ko ne dama yau zan zo na kar6a shiyasa na ce idan za ki dawo da Ikram ki yi min magana sai mu taho tare hau mu je" kai Zainab ta d'aga ta na hawa ya saka plasma d'in a gaban sa su ka d'auki hanyar gida. A 'kofar gidan ya aje ta, ta shiga sannan ya yi parking da mashin d'in shi ma ya shiga ya fara aje TV din ya dawo waje ya shigar mashin d'in ciki a lokacin an kusa kiran sallar magriba ya yi alwala ya fita daga gidan bai dawo ba sai bayan sallar isha su ka shigo tare da wani mutum sannan Zainab ta na d'aki ta ga Sameer ta yi ya shigo ya aje plasma d'in ya na cewa "ki fito daga nan ki shiga d'akin Umma wanda zai had'a miki TV ya zo" zaro ido ta yi a firgice ta nuna kan ta ta na cewa. "Wai ka na nufin dama na wa ne"? Kai ya d'aga ya na cewa "eh man in ji aboki na ba" dafe kai ta yi tana cewa "Innalillahi wa inna ilaihi raji'un ni dai ina cikin matsala wai Yaya Sameer wanne irin mutun................. "A'a ba sai kin ce komai ba na gane ki kwantar da hankalin ki ai na fad'a miki ya kusa zuwa ba za'a dad'e ba za ku had'u" ya na fad'in haka ya fita shiru Zainab ta yi zuciyar ta na bugawa da 'karfin gaske har Sameer ya shigo da mutumin ba ta iya tashi ba sai da ya sake le'kawa ya mata magana sannan ta mi'ke da'kyar ta na jan 'kafa ta fita ta shiga d'akin Umma, ita ma Umman ta na kallon ta kuma ta ga a yadda ta shigo sai dai ba ta da bakin magana akan wannan al'amari tun abun ya na damun idan ta gani ko tsoron a je a fad'awa Hajiya yanzu har ta watsar ko fargaba ba ta ji. Har mutumin ya gama aikin sa Sameer ya biya shi ba wanda ya fito sai dai su na jin maganar su dad'in abun ma Asabe ba ta gidan ta yi tafiya ana biki a dangin su da ace ta nan da yanzu ta had'a musu kururuwa ta kirawo mutanen gidan nan, jin da Zainab ta yi shirun ya yi yawa yasa ta fahimci sun fita har Sameer d'in mi'kewa ta yi jikin ta a mace ta fice ta koma d'akin ta kawai kallon iya TV d'aga mata hankali ya ke rasa inda za ta saka kan ta, ta ji dad'i ta yi ta na jin lokacin da Sameer ya shigo ya na tambayar Umma abincin sa ta fito ta saka masa. Ta na kwance idanun ta a rufe sai haske ta gani d'auu da sauri ta bud'e ido ta ga nefa aka kawo ga shi harda sabuwar 'yar yawo ta gani a gurin Sameer ya cire wancan tsohuwar ya saka mata sabuwa numfashi ta sauke tare da mayar da idon ta ji tayi Sameer yace. "Yauwa an kawo nefa Zainab ki na d'aki ne"? Sake bud'e ido ta yi a hankali ta ce "eh ina nan". "Ok" ya ce tare da yin shiru can kuma ta ji sallamar sa ya shigo ya na cewa "amma ba ki gwada kunnawa kin gani ko da akwai matsala ba"? Ya fad'a ya na kunnawa ya d'auki remote ya jawo kujerar da take d'inki ya zauna akai ita dai ta na gefen katifar ta da waya a hannun ta ba ta ce komai ba Sameer kam fita yayi ya koma d'akin sa ya d'auko abincin sa ya dawo d'akin domin so ya ke ya gani idan da matsala gari na wayewa zai kira mutumin ya zo ya sake saitawa sai kuma ya ga komai normal". ZUCIYAR ALIYU CE WRITTEN BY YUSRAH MUSA ABUBAKAR ✨ @YUSRAH MUSA DUTSE PAGE 64 Duk abin da ya ke faruwa Bilki ta na daga d'aki ta na jin su kai ta jinjina cike da takaici ta fito daga d'akin tare da takowa cikin sand'a a hankali ta le'ka window ta ga yadda TV take walwalin sabuntaka ji ta yi sabon ba'kin ciki ya rufe ta kamar ta d'auko katon dutsi ta jefa TV ya fashe tsaki taja ta na fita daga 'kofar tasu ta shiga gurin Hajiya ta yi sa'a ita kad'ai ce kuwa babu kowa ganin ta tayi ta baje naman kazar da Aminu ya siyo mata sai dagwargwaza ta ke zama Bilki ta yi tana cewa. "Tabd'ijan Hajiya ban ba ki labari ba kin san................... Tun kafin ta fad'i abin da take son fad'a Hajiya ta tare mata numfashi da fad'in "wani abu ne ya faru a gidan nan"? . "K'warai kuwa Hajiya gagarumi ma". "A ina su waye"? Cizon yatsa Bilki ta yi tana cewa"a 'kofar mu man d'azun nan Yaya Sameer ya shigo da wata 'katuwar TV na d'auka shi ya siyo wai ashe ta Zainab ce mai sakawa har yazo ya saka mata a d'akin ta ya saita mata tashoshi yanzun nan da aka kawo nefa Yaya Sameer d'in ya shiga d'akin ya kunna ba ki ji yadda 'kara ta ke tashi ba a 'kofar mu kamar gidan DJ" zaro ido Hajiya ta yi ta na daina cin naman ta ce. "TV kuma uban wa ye ya siya mata"? Kafad'a Bilki ta d'aga ta na cewa "taya zan sani Hajiya mafita d'aya ce kawai ki kira shi Yaya Sameer d'in ki takura masa ya fad'a miki wanda ya bashi ya kawo mata duk tsiya ai shi ya sani dashi ake had'a baki ana duk wata barna ta 'kofar mu domin duk wani abu da za ki gani a gurin Zainab shi zai kawo ya ce in ji abokin sa gashi har gobe abokin na sa ya'ki ya bayyana a san waye ai ko ta nan Hajiya ya kamata ki san 'karya su ke kawai raina ma na hankali za su yi dan kin ga misali kwanan bayan nan lokacin da ba ta da lafiyar d'in nan da ace ciki ne da ita wallahi Yaya Sameer za ku ritsa ya fad'a muku gaskiyar komai tun da duk wani abu da za'a kawo shi ne manaja da hannun sa komai zai zo gurin ta a hakan dan ma ba'a 'kofar ki ke ba da takaici ne zai kashe ki idan ki ka ga irin bushashar da ya ke kawo mata kala-kala naman kaji da na shanu kayan 'karfi zaki gan shi ya kawo mata ko chocolates da biscuits sai kace yarinya balle kuma su Faro da yogurts wadannan ai idan ana sallah ba'a magana Hajiya ku da ba ku sani ba shi ya sa hankalin ku ya ke kwance amma mu da muke 'kofar za'a kawo komai a gaban mu ba'kin cikin da mu ke sha'ka ya yi yawa ga masifar rowa ko zaka mutu ba za ta baka ba" ko kad'an bakin Hajiya ya'ki rufuwa tun da Bilki ta fara magana har ta kai 'karshen kai kawai take jinjinawa ta ce. "Kan bala'i dama irin abubuwan da suke faruwa kenan a 'kofar ta ku ban sani ba ko shi yasa na ga kwanan nan Abdullahi ya yi 'kiba har da naman wuya ashe dad'i ya ke ci ni ina nan a 'kai'kashe wato ga tsohuwar banza wacce ba ta da daraja sai a idanunsa bare humm ya yi kyau koda na ji shiyasa idan na tambaye shi kud'i ba musu yanzu zai d'auka ya bani ashe sabuwar rayuwa ya canza? Ai kuwa zan ci mutuncin sa zai zo ya same ni tashi ki je ki kira min Samar d'in shi ma wani munafikin ya zo na ji uban waye ya ke aiko shi da kaya gurin Zainab d'in yau sai na ci uban sa tashi ki kira min shi na ce". Zaro ido Bilki tayi tana cewa "tab ni ce zan kira shi so ki ke ya karya a gidan nan gashi Umman mu ba ta nan Baban mu kuma ba laifin sa ya ke gani ba gaskiya indai nice na kira shi cewa zaiyi ni na fad'a miki ki bari d'an wata 'kofar ya shigo sai ki aika masa". "To shikenan Allah ya kawo wani d'in yau ba zan yi barci ba sai na yi magana da Samar a gidan nan ko da ace zan samu nutsuwa" tashi Bilki ta yi ta na cewa "bari na nemo miki wani yaron sai ya kira miki shi" to Hajiya ta ce Bilki kuma ta fita ganin babu kowa ya sa ta le'ka 'kofar su Zakiyyah 'kanin Rasheedat ta gani a zaune ta ce. "Yauwa kai Adam ka je Hajiya ta na kiran ka yanzu" ta na fad'in haka ta juya 'kofar su ta koma da sauri ta fad'a d'aki a lokacin Sameer kam ya dad'e da fita a gidan Zainab kuma barci ma ya d'auke ta, sallama Adam ya yi shigo ba wanda ya amsa tun da duk sun yi barci shi kuma Sameer ya na waje le'kowa Bilki ta yi ta na cewa "Adamu ka tafi chemist d'in sa ya na can baya gida" ta na fad'in haka ta saki labulen ta koma fita ya yi daga gidan ya tafi chemist d'in ya fad'awa Sameer Hajiya ta na neman sa bai yi mamaki ba kuma ya na ji yasan dalilin kiran ba zai wuce wani ne yaje ya fad'a mata ya kawowa Zainab TV ba, humm mutanen gidan nan su na da abun haushi bari ya je yaji me za ta ce masa tun da dama dare ya fara yi goma har 'yan mintuna rufe chemist d'in ya yi ya tafi gida gabadaya idan ya fito daga gurin Hajiya kawai sai yayi kofar su. Ya na shiga kuwa abun da ya ke tunani ko sallama da yai ba ta amsa masa ba ta fara magana "kai Samar 'karshen alewa 'kasa yau sai ka fad'a min uban waye abokin ka wanda ya ke aiko da abubuwa ka ke baiwa Zainab haukan ya yi yawa abun ya wuce inda hankali zai d'auka alhali ku na da nagaba da ku amma ba mai tambayar ku saboda ba sa son su 6ata muku rai tun da zilamammu ne ku na d'an ba su wani abu ko kwanan baya ka shigo da firiza yau kuma har da kayan kallo duk waye ya ke aiko ka"? Kallon ta ya yi yana jinjina kai ya ce "tsinannan munafikin da ya ke zuwa ya fad'a miki gulmar ya zo kenan ya yi kyau amma ya manta bai fad'a miki har da katifa ba da yadin gado da fanka duka na kawo mata"? Zaro ido Hajiya ta yi tana cewa "au har da katifa da fanka kuma wai har da yadin gado kamar wacce ta kama d'akin mijin ta? na shiga uku ina raye a gidan nan an mayar da ni gawa wacce babu ita a duniya" tsayawa ta yi tana kallon Sameer ta ce "Samar uban waye yake aiko ka, ka fad'a min tun mu na mu biyu kafin na tara maka jama'a kasan Allah daga shi ba wani idan ba ka fad'a min ba sai nasa dukkan samarin gidan nan sun ri'ke min kai na ba su igiya su d'aure ka nasa Habibu da Aminu su yi maka dukan tsiya idan ba ka fad'a min ba" ta na rufe baki Sameer ya she'ke da dariya ya na dafe goshin sa tare da ri'ke ciki kai Hajiya ta jinjina ganin yadda ya ke dariyar ko tsayawa ba ya yi yasha numfashi ta ce. "Hummm! dole ka yi dariya tun da ga mahauciya ta na maka magana ka mayar da ni ban san abin da na ke ba" tsagaitawa ya yi yana zama a kusa da ita ya ce "Hajiya kin sani dole na zauna" ya fad'a tare da gyara zaman sa ya ci gaba "ni fa dariyar ce tazo min lokaci guda sakamakon nishad'in da nake ciki amma ba abun da ki ka fad'a ne ya sa ni dariya ba sannan maganar kayan da ake kawowa Zainab wannan gaskiya ne haka yake wanda ya ke son ta ne yake siya mata kuma auren ta zaiyi ya kusa zuwa kwanan nan za ku gan shi in sha Allahu". "Wanene shi"?. "Ki yi ha'kuri Hajiya ba zan iya fad'a miki ba za ki san shi amma ba yanzu ba sai lokacin da ya zo" ido Hajiya ta zuba masa ganin haka yasa yayi murmushi ya na cewa "ki yarda da ni gaskiya na ke fad'a miki" kai ta girgiza ta na cewa. "Ka ga Samar ba na son munafirci ka fad'a min waye"?. "Kaiii Subhanallahi Hajiya ki na da son ayi ta maimaita magana nace ba zan yi iya fad'a miki ba idan na yi haka ban ri'ke amanar da na dauka ba". "Har wacce amanar ce wannan kuma idan ba mutum ba ne ya za ka biya bashin aljani da ka ke d'auka irin wad'annan dukiyoyi"?. "Mutum ne man". "A ina ya ke d'an waye a garin nan"?. "Dan Allah Hajiya ki bar yi min tambaya a kan sa domin ko kashe ni za ki yi ba zan fad'i waye ba duk ranar da ya bayyana kwa gan shi" ya fad'a ya na mi'kewa hararar sa Hajiya ta yi tana cewa "kar ka fad'a d'in d'an me ba'kin hali wata uwar zan ce idan ka fad'a min ko kana tunanin zan cinye shi mayya ce ni"?. "A'a ni fa Hajiya ba ki ji haka daga baki na ba, duk abin da zan ce miki ba za ki ta'ba fahimta ta ba kawai sai da safe" ya na fad'in haka ya juya ya fita ya bar Hajiya ta na fad'a kamar ba za ta daina ba daga baya kuma tayi shiru tun da wanda ta ke fad'an dan shi ya tafi ba jin ta ya ke ba. ** ** YUSRAH MUSA ** ** Chat with me. +234 8160983083 WhatsApp number YMA DUTSE JIGAWA STATE. 1_💓Mai alfaharin jiha ta ce 2_🚗Ko'ina na ke inda zan zarce 3_🇳🇬A cikin Nigeria mu ke da gada mun taka kan Dutse 4_🌃Birnin daraja daya batse 5_🏜️Ga haske 6_🏞️🏔️Ga adon Dutse👍💙💃💚 💛JIGAWA TARON ALLAH💛 @YUSRAH MUSA PAGE 65 Baby ba ta ta'ba tunanin da gaske Shareef zai iya auren wata mace bayan ita ba saboda ganin irin sha'kuwar su ta d'auka idan yaga ta nutsu ta kame kan ta zai tausaya mata amma ta ga ba canji jiya iyau, Kamar kullum yadda ta saba yau ma lokacin da ta zo hospital ta ga motar sa amma kuma ta yi iya neman ta bata gan shi ba har ta ha'kura ta samu guri ta zauna tana zaune tayi tagumi 'kawarta Badiyah ta karaso gurin tana zama tace "ke Baby ina ta neman ki ashe ki na nan ban sani ba"? Kallon ta Baby ta yi cikin yanayi na rashin jin dad'i za ta yi magana Badiyah ta ce "tsaya ma na tambaye ki wai dama Shareef aure zai yi ne"? Sake d'agowa Baby tai jikin ta yayi mugun sanyi da'kyar tace "taya kika sani waye ya fad'a miki"? Wani d'an littafi ta d'auko daga jakar ta wanda bangon sa yake d'auke da sunan su alamar an yi mu su engagement mi'ka mata ta yi tana cewa "waye ya fad'a min kuwa bayan ga sheda nan na gani da ido na kalli man" kar'ba Baby tai hannunta na kakkarwa ta fara dubawa wani irin zaro ido waje tayi tana zabura a rud'e tace. "Mene wacece Nihal Alhaji Mustapha kuma"? Kai Badiyah ta girgiza tana cewa "oho duniya da fad'i taya zamu santa tunda ba a hospital d'in nan take ba amma dai kamar naji ance 'kanwar Doctor Ammar ce fa" kamar idon Baby zai fito waje ta ce. "Kanwar Ammar kuma? Innalillahi wa inna ilaihi raji'un na shiga uku" ta fad'a tana dafe kanta da yake juyawa tare da komawa da sauri ta zauna tana ri'ke kan da hannu biyu ta runtse ido sakamakon wani irin ciwo daya sara mata lokaci guda dafa ta Badiyah tai tana cewa. "Baby kina lafiya kuwa meya faru"? D'agowa Baby tai tana kallon Badiyah maimakon ta bata amsar data tambaye ta sai kawai ta fashe da kuka mamaki ne 'karara ya bayyana a fuskar Badiyah harta kasa gane me hakan yake nufi karshe tunani ya bata kodai son Shareef take shine dalilin wannan kukan nata shiru tayi ta zuba mata ido harta gaji ta share hawaye tana sau'ke ajiyar zuciya. "Wai Baby me ya ke faruwa ne kukan me ki ke yi"?. "Dole na yi kuka Badiyah 'kanwar Ammar fa me saka glass d'in nan wacce kwanan baya muka ganta tare da kanwarta harta buge mata glass d'in ya fad'i Shareef ya fito ya d'auka ya ba ta" kai Badiyah ta jinjina ta na cewa "kenan dama son ta ya ke" zazzafan huci Baby ta fitar tana sake kallon littafin memo d'in ta cije lips cike da takaici ta ce. "Taya zan sani bayan ba fad'a min yayi ba amma sai dai daga baya yake sonta domin ranar haduwar su ta farko bai santa ba a kanta har fad'a mu kai da shi ban manta ba" d'an murmushi Badiyah ta yi ta na cewa "abun mamaki zuciya kenan mai son abinda take muradi daga had'uwar su shikenan nan ya kamu da son ta irin haka ake so wallahi ka so mutum dan Allah" jin abinda Badiyah tace yasa Baby sake cije lips d'in ta har ta fara huda shi da ha'kori amma ko zafin ba ta ji rad'ad'in da ya ke cin zuciyar ta yafi wanda ta ke ji akan lips d'in na ta kallon Badiyah kawai take cikin takaici tace "na rasa me yasa Shareef yayi min haka meye bana dashi meye zanyi ya burge shi ya rasa a inda gayun nasa zai 'kare sai a kan nakasasshiya me ciwon ido ki na kallo fa a ranar da 'kanwar ta ta, ta buge mata glass d'in bata gani fa saida shi in ta cire kamar dare haka take ba ta ganin komai" jinjina kai Badiyah ta yi tana cewa. "Eh a hakan yaji zai iya zama da ita baki san dalilin sa ba akwai abinda yasa ya za6i ya aure ta kuma ya kamu da son ta". "Ba wani dalili Badiyah dan ya wula'kanta ni yayi haka nasan shine dalilin sa ba komai ba yana so ya nuna min idan ni bansan ciwon kaina ba ga wacce ta cancanta zamowa abokiyar rayuwarsa ne". "To ke meye ruwan ki a ciki ko son sa ki ke"?. "Ke za'a yi wa wannan tambayar idan ina son sa ma kin sani idan ba na son sa nan ma kin sani shekarar mu nawa tare da ke a hospital d'in nan ina da wata 'kawar bayan ke"?. "A'a ba ki da ita amma Baby a tunani na sirrin zuciya sai me ita taya ba ki ta'ba fad'a min ba kawai zan san ki na son sa? Amma yanzun na fahimta sai dai zan baki shawara dan Allah ki cire damuwar dake damun ran ki wai tsaya ma na tambaye ki kina kallon fuskar ki a mirror kuwa kin ga yadda ki ka koma kamar skeleton". "Hummmm!!" Kawai shi ne abin da Baby ta ce domin a halin yanzu yadda take ji ba ta san da yadda zata kwatantawa Badiyah ta fahimta ba ita kuma da take jin zafin da ciwon ba ta san ya zatai ba sake sau'ke ajiyar zuciya ta yi ta na mi'kewa ta ce "ina zuwa yanzu zan dawo". "Ok" Badiyah ta ce Baby kuma ta bar gurin cikin hospital d'in ta shiga sosai ta ri'ka tambayar doctor's da nurses ta na neman sa har sai da ta samo shi ya na can yaje wajen wani abokin sa a 6angaren 'yan surgery tuni zuciyar ta ta fara tashi ta na yun'kurin amai sakamakon kallon mutanen da su ke gurin gabadaya abun ba kyan gani da'kyar ta wuce ta shiga ciki su na office tare su na magana ta shiga da sallama tare da tsayawa daga jikin kofar ta na kallon Shareef wanda shi ma yake kallon ta tace. "Shareef dan Allah ina so za mu yi magana". "Ok nan ma maganar mu ke ki jira ni a waje ina zuwa". "Wai a gurin wad'annan 'yan surgery masu 'konannan jiki zan jira ka"?. "Eh idan ba za ki iya ba ki tafi can wajen office d'ina ina zuwa". "Gaskiya sai dai na tafi can d'in na jira ka

Chapter 26 of 34