ya kamata ki fara yi na ga kin zauna"? Zainab ta fad'a tana kallon yadda Aunty Murjan ta ke neman kwanciya ta ci gaba "daga gurin dinner ki ke ba wa'azi ba balle ki ce can ma lada ki ka samo dan Allah ki tashi" tashi zaune Aunty Murjah ta yi ta na mi'kewa ta cire rigar da ya ke jikin ta ta na ajewa ta ce.
"Ke ni fa hutu na ke ba don haka ba ai kema kin san ba zan zauna ban yi sallah ba ko"? Kai ta d'aga tana cewa "haka ne bari na tambayo Umma me ta dafa" dakatar da ita Aunty Murjah ta yi "kin san abin da ta dafa ke ma ai sai dai ki je kalan magana ni kam ba zan ci tuwo ba zo kiyi mana wainar fulawa kawai".
"Ai kuma ba fulawa fa a gidan nan" kallon ta Aunty Murjah ta yi ta na cewa "kin yi sallar isha d'in"?.
"Eh na yi tun kafin shigowar ki".
"Ok bari na tashi mu je mu had'o kayan yi muzo muyi kawai tun da nasan ba za'a rasa gawayi ba" kai Zainab ta d'aga ta na cewa "eh buhu guda Abban mu yake ajewa sai ya 'kare ya kawo wani".
"Ok bari na yo wanka idan na fito sai mu je dan yanzu wani irin zafi na ke ji ta ko'ina a jiki na gashi babu nefa balle mu kunna fanka" ta fad'a tana d'aukar zanin wankan Zainab ta fita.
Kusan awa guda ba ta dawo ba har sai da Zainab ta gaji da jira ta na shirin tashi ta fita taga inda ta tsaya sai kuma ga ta ta dawo".
"Kai Aunty Murjah wannan wankan na ki kamar ki na canza fata"? Goge jiki Aunty Murjah ke yi da d'an farin towel ta na cewa "ai ni ko a gida haka na ke wanka na ban iya kware-kware ba".
"Lallai Yaya Auwal ya na ganin duniya" dariya Aunty Murjah tai tana juyowa ta kalli Zainab tana cewa "kamar kin sani dan kwanan baya ma haka ya ce wai idan mutum gudawa ya ke na shiga band'aki saidai mutum yayi a jiki ban fita ba".
"Hum ai gaskiya ya fad'a irin wannan dad'ewa haka kamar me wankan mutum nawa"? Hijab Aunty Murjah ta saka ta na cewa "mu bar zancen nan mu je a had'o kayan wainar nan dan rabo na da abinci tun rana shi ma ina sauri ban tsaya na ci me yawa yadda zan 'koshi ba".
"Ba ki ci a gurin dinner d'in ba ne"? Zaro ido waje Aunty Murjah tai tana cewa "uwar me zan ci a gurin me suka kai wanda bana ci a gida na har zan yi sha'awar cin sa a gurin" murmushi Zainab ta yi suna fita daga gidan shagon 'kofar gidan a nan suka tsaya suka siyo fulawa da manja sannan su ka koma ba wacce ta shiga d'aki duk 'kofar kitchen su ka tafi suka zauna akan kujera Zainab ta d'auko mangal ta zuba gawayi ta had'a musu wuta Aunty Murjah kuma ta jajjaga musu taruhu ta yanka albasa ta saka maggi ta 'kwa6a musu su ka fara soyawa.
"Zainab yaji fa ko babu"? Aunty Murjah ta tambaya ta na kallon ta kai ta d'aga tana cewa "eh babu amma bari na tambayo miki Umma ko za'a samu" ta fad'a tana shirin mi'kewa "a'a zauna ki soya mana bari ni na je" komawa Zainab ta yi ta zauna ita kuma ta mi'ke saidai ba yaji a gurin Umma gashi gaskiya ita ba za ta iya ci babu yaji ba ganin Asabe ta shigo zata shiga d'aki ya sa tace.
"Umma Asabe dan Allah ko kina da sauran yaji ki bani zan ci waina"? Kai ta d'aga tana cewa "bari na duba" baki bud'e Zainab ta kallo kofar d'akin ta ga ta shiga wato bari ta duba ko dan ita ba'a gidan ta ke ba shi ya sa baza ta yi mata wula'kanci ba ta tabbata da ace ita ce ta ro'ka ko kallon ta baza ta yi ba Aunty Murjah ta na tsaye ta bud'o labule ta mi'ko mata gabadaya robar yajin tana cewa "je ki da shi idan kun gama kya dawo min da shi" kar6a Aunty Murjah ta yi tana cewa "yauwa Umma Asabe na gode" zaro ido Zainab ta yi tana jinjina kai amma ba tai magana ba gudun kar da tace wani abu Asaben ta fito ta hau bala'i ana zaune lafiya dawowa Aunty Murjah tai ta zauna tana cewa.
"Kai haba malam sai yanzu nasan ina cin waina" murmushi Zainab ta yi tana d'auko wacce ta soya ta sake aje mata tana cewa "lallai Aunty Murjah kin taki sa'a".
"Sa'ar me"?.
"A'a ba sai na fad'a ba kawai gara na yi shiru domin yin shirun nawa ya fi alkhairi".
"Ok yayi" kawai Aunty Murjah ta ce tana ci gaba da cin wainar ba kamar Zainab da ta ji ba tai mata ba har suka gama soyawa suka tashi Zainab ba ta ce komai ba Aunty Murjah ta mayarwa Asabe yajin ta ta had'a mata da wainar sannan ta shiga ta kai wa Umma ma sauran suka wuce da ita d'aki akan keke ta aje plate d'in ta na cewa "to masha Allah sai yanzu na ji na dawo daidai Allah yasa su kawo nefa wallahi da zafi ko dan na ci abu me d'umi yanzu ne" ta fad'a tana d'aukar wani mafici na roba ta fara fifita da shi ita kuma Zainab ta d'auki littafin ta ta fara assignment d'in da bata samu ta yi ba dama ta bari da la'asar za ta yi sai kuma Sameer ya zo suka tafi dinner har Aunty Arabiyyah ta shigo su ka sake sabon zama ita da Aunty Murjah su ka yi ta hira Zainab ta na gefe tana jin su sai dai idan an yi abun dariya ta d'an yi murmushi 'karshen wannan wainar Aunty Arabiyyah d'in ce ta cinye ta.
ZUCIYAR ALIYU CE
@YMA DUTSE
PAGE 43
Washe gari da safe ba wanda ya tashi sai wajen sha d'aya da rabi a lokacin Sameer ya shigo da firiza ya aje ta a 'kofar d'akin Zainab da katon d'in lemuka guda biyu da ledojin pure water ya wuce na sa d'akin sai da ya yi abin da zai yi ya fito sannan ya fito yana dawowa 'kofar d'akin Zainab ya dafe fridge d'in yana cewa.
"Zainab kin tashi ne"? Jin shiru yasa ya sake cewa "Zainab Zainab" kamar a mafarki haka Zainab ta ji muryar Sameer sama-sama ya na kiran sunan ta da sauri ta yaye bargon da suke barcin da shi wanda hakan ya yi silar tashin Aunty Murjah cikin magagin barci ta ce "Zainab lafiya irin wannan zabura haka kin tsora ta ni"? Kai ta d'aga tana mi'kewa ta ce "eh lafiya kamar muryar Yaya Sameer na ke ji a waje ya na kira n...................
"Zainab" ta sake jin ya kira ta ba ta 'karasa fad'awa Aunty Murjah maganar ba ta ce "na'am Yaya Sameer" ta fad'a tana fita a tsaye ta same shi har lokacin hannun sa yana dafe da firizar.
"Ina kwana Yaya Sameer"? Kai ya d'aga ya na cewa "lafiya klou ina Murjah"?.
"Ta na d'aki".
"Ok sorry ki na barci na tashe ko? Ga alama nan na ga idon ki ya yi ja ki taso Murjanatun ta taya ki ku shigar da wannan fridge d'in d'akin ni zan fita" jin abin da ya ce yasa da Aunty Murjah fitowa da gudu turus ta yi ta tsaya daga ita har Zainab d'in su na bin firizar da kallo cike da tsananin mamaki cak Zainab ta yi ta kasa motsin kirki tsoro da tashin hankali ya rufe ta kai Aunty Murjah ta jinjina ta na kallon Sameer ta ce.
"Wannan fridge d'in kuma daga ina Sameer"? Murmushi ya yi ya na kallon Zainab shi kuma ya ce "ita wacce na kawowa ta san daga in da ta ke wani ne ya bayar a ba ta saboda yanzu lokacin zafi ne ta ri'ka shan ruwan sanyi haka ya ce sa'ko ne daga gare shi" da sabon mamaki Aunty Murjah ta ce.
"Wani kuma"?.
"Eh aboki na ne ki taya ta ku shiga da ita d'akin" ya na fad'in haka bai sake kallon yanayin da Zainab d'in ta ke ciki ba ya fita juyawa Aunty Murjah ta yi da tsantsan mamaki ta na kallon Zainab wacce ta 'kame kamar wacce ta suma numfashi ta sauke ta na cewa "ke Zainab waye abokin sa har ya siya miki fridge saboda ki ri'ka shan ruwan sanyi son ki ya ke ko me"? Shiru Zainab ta yi tana kallon fridge d'in jikin ta sai rawa yake ko maganar da Aunty Murjah take mata bata ji tsabar rud'ewa ganin ba ta cikin hayyacin ta yasa ta dafa tana cewa.
"Zainab wai lafiya ba ki ji abin da na ce bane"? Kai Zainab ta girgiza hawaye yana neman fara zubo mata da sauri ta shige d'aki ta bar Aunty Murjah a tsaye a gurin shiru Aunty Murjah ta yi gabadaya kan ta ya kulle ta kasa fahimtar komai Umma dake d'aki tana jin su ita ma hankalin na ta a tashe yake musamman jin wai firiza aka kawo wa Zainab saboda kawai ta ri'ka shan ruwan sanyi wai waye wannan abokin Sameer d'in ita ma yanzu gaskiya tana son sani ko dan samun zaman lafiyar su kafin a fara zagin su a gidan nan ko a d'auka da gaske asiri ta ke tura Zainab D'an Yana mi'kewa ta yi ta na fitowa ta kalli Aunty Murjah wacce har lokacin ta ke tsaye a wajen ba ta bi bayan Zainab ba kallon firizar ta yi ta na cewa.
"Murjanatu ina Zainab d'in"? Sauke ajiyar zuciya Aunty Murjah ta yi ta na cewa "ta na d'aki Umma wai lafiya na ga ta shiga damuwa dan Sameer ya kawo mata wannan fridge d'in"? Jiki a sanyaye Umma tace "Murjah dole Zainab ta damu dole ta shiga tashin hankali idan na fara lissafo miki abubuwan da Sameer yake kawo mata yana cewa abokin sa ne ya ke mata wai son ta yake amma yafi so sai ta gama makarantar da take yi yanzu idan ya dawo sai ya fito ya nemi auren ta kuma makarantar ma shi ne ya biya mata wannan dalilin ya sa ki kaga ta shiga damuwa".
"Na fahimta to waye shi abokin Sameer d'in a ina ya ke wannana na ke son sani"? Kai Umma ta girgiza ta na cewa "wallahi ni ma har gobe ban san waye shi ba Sameer ne ya sani kuma ya'ki fad'a mana ya ce abokin na sa ba ya so a san shi da kan sa ya ke so ya zo ya bayyana ya gabatar ma ta da kan sa" sabuwar ajiyar zuciya Aunty Murjah ta sake saukewa ta na cewa "ko dai akan haka na ga yanzu ta shiga wani irin yanayi".
"Ba dole ta shiga yanayi ba Murjah ni kai na kullum hankali na a tashe ya ke idan na ji Sameer ya kira sunan ta saboda nasan abu zai bata ke fa hatta kud'in da take hawa Napep ta je makarantar kullum dubu d'aya wancan abokin na sa ne yake baiwa Sameer d'in yana bata kwalin indomie chocolates biscuits haka zaki gan su kala-kala ya kawo mata wai kawai ta ri'ka ci ban da kayan sakawa fa" Kai sosai Aunty Murjah ta ke jinjinawa ta na kallon Umma tace "gaskiya dole ta shiga damuwa musamman da ba a san waye ba shi ne abun matsalar yanzu bari Sameer d'in ya shigo na tambaye shi" murmushi Umma ta yi ta na cewa.
"Ko kin tambaye shi ba zai fad'a miki komai ba sai dai ya ce da lokaci ko me za ki yi ba zai fad'a mi ki ba".
"Ok shikenan Allah ya kai mu lokacin Ubangiji ya sa shi ne miji na gari mafi alkhairi a rayuwar ta".
"Amin shi ne kawai abun fatan yanzu ki shiga d'akin ki mata magana ta fito ku d'auke tun kafin a zo a gan ta magana ta fita" Umma ta fad'a tana juyawa ta koma d'aki Aunty Murjah kuma d'akin Zainab d'in ta shiga ta gan ta ta kwanta akan katifa ta na kuka zuwa ta yi ta d'ago ta tana goge mata hawayen tace.............
ZUCIYAR ALIYU CE
@YUSRAH DUTSE
PAGE 44
"Zainab tun da kin san ga wanda ya ba ki meye abun da zai sa ki damu kan ki dan Allah ki daina kukan nan" kai ta girgiza muryar ta da alamar kukan ya kama ta sosai ta ce "Aunty Murjah na kasa fahimta na kasa gane komai kyautar yau daban ta gobe daban abubuwan masu tsada yanzu kuma komai ya wuce yadda na ke tunani firiza fa ya siyo min dan kawai ana zafi na ri'ka shan ruwan sanyi abun nan yana bani tsoro wallahi".
"Na sani amma tun da ki ka ga Sameer ya mayar da hankali akan abun na tabbata yana da muhimmanci kuma in sha Allahu alkhairi ne dan haka abin da na ke so da ke ki yi hakuri yanzu ki tashi mu je mu shigo da ita ciki" Aunty Murjah ta na rufe baki da sauri Zainab ta girgiza kai ta na cewa.
"A'a ni ba na so kawai bari Yaya Sameer d'in ya shigo na ce ya d'auka ya mayar masa ko ya saka a chemist d'in sa amma ni dai ba na so" da mamaki Aunty Murjah ta ce "ya kai chemist kuma? A'a ba wani chemist da zai kai ta wallahi tana nan a d'akin ki mazaunin ta ya ke dan haka ki kwantar da hankalin ki tashi mu shigo da ita ciki ki ri'ka zuba pure water d'in ki da abubuwa ki na sha haka kawai zaki mayar da hannun kyauta baya ba zai yuwu ba gara da ban tafi gida jiya ba na dawo nan ashe alkhairi ne ya dawo da ni za'a yi wannan abun a gaba na" ita dai Zainab ko motsi ba tai ba daga haka kuma ba ta sake magana ba duk abin da Aunty Murjah ta ke ta na jin ta.
Shigar Umma da Aunty Murjah d'aki bayan sun gama magana da sauri Bilki ta fito daga d'akin su tana kallon firizar takaici da ba'kin ciki ya gama rufe ta yatsa ta ciza tana hararar kofar d'akin su Zainab da sauri ta fita daga 'kofar ta su ta tafi gurin Hajiya har da gudu kamar wani ne zai riga ta ta na shiga ta ce "Hajiya albishirin ki kin san Zainab ta na da saurayi me kud'i kuwa"? Kallon yadda ta ke haki Hajiya ta yi ta na cewa.
"A ina ta yi saurayi me kud'in? Taya zan sani tunda ba shigowa guri na take ba bayan haka Hauwa tana jin haushi na na takura mata can ta yi aure yaushe za su fad'a min 'yan gadon ba'kin hali ne fa" tsaki Bilki ta ja kamar za tai ihun takaici ta ce "to wallahi yanzu ma maganar da na ke miki ba ki ga wata 'katuwar fridge da Yaya Sameer ya kawo mata ba da katon-katon na lemuka da ledojin pure water wai abokin sa ne ya ke son ta kuma shi ya siyo mata ta ri'ka zuba kayan sanyi tana sha yanzu lokacin zafi ne" gwalo ido waje Hajiya ta yi ta na cewa.
"Aw kawai tsabar jin dad'i dan ta ri'ka shan kayan sanyi ya siyo mata 'katuwar firiza ki ka ce waye wani abokin Samar kuma a ina ya ke ko Aliyu ne"? Da alamar tambaya Bilki ta ce.
"Wanne Aliyun"?.
"D'an gidan Alhaji Ahmad d'in nan Minister nan nake fad'a mana ko shi ne tun da na ga shi ma abokin na sa ne"? Ta'be baki Bilki ta yi tana yatsina fuska ta ce "kaiiii a'a cafd'i me Aliyu zai yi da Zainab ya na d'an me kud'i baban sa Minister mu kuwa baban mu da ya ke sana'ar kayan miya da gawayi gaskiya ba shi bane saidai idan wani ne daban".
"To yanzu ina firizar ta ke"? Cike da munafirci ta ce "ta na can a d'akin ta har sun jona ta sun siyo ruwa sun zuba da lemuka sun zuba su na ta dariya da shewa Umman su kuwa har da rawa ta na cewa ina Hajiya ta zo taga arzikin Zainab ya fara sauka d'an ba'kin ciki sai dai ya mutu tun da gashi ita ma na ta masoyin ya bayyana" gwalo ido Hajiya tai tana cewa.
"Iye haka Hauwan ta ce a kai na"?.
"K'warai haka ta ce kuma ba 'karya na ke ba su na can su na ta gulmar ki wai dama a gidan nan ba wanda ki ka takurawa irin 'yan d'akin su" cikin fad'a Hajiya ta ce "ka ji matsiyata in ji uban su na ke takura musu ko dan sun saba yi min sharrin 'yan gadon ma'karyata, yanzu ki ka ce har sun siyo ruwa sun zuba a firizar wanne za'ka'kurin ne gwanin zuba ruwan? Murmushi Bilki ta yi tana gyara zama ta ce.
"Waye kuwa bayan Aunty Murjah ke ma Hajiya ai kin sani sai dai ita".
"Au Murjan dama ta dawo gidan nan jiyan ba ta tafi ba shi ya sa ta ce dad'a kwana dan ta yi wa mutane rashin arziki tashi ki kira min ita dan uban ta" Hajiya ta fad'a ta na kallon Bilki wacce ta girgiza kai ta na cewa "kai Hajiya gaskiya idan na je za su ce nice na zo na fad'a miki".
"To su fad'a man dan uban su tsoron su ki ke kome za su dake ki ne"?.
"Ni ba tsoron su na ke ba amma za su iya fad'awa baban mu kuma yace kar na sake yiwa Zainab rashin kunya kuma kar na sake shiga safgarta" cikin fad'a Hajiya ta ce "kuma ina ruwa na tashi ki kira min Murjanatun na ce ko"? Tashi Bilki ta yi tana fita tare da tsayawa a 'kofar Hajiyan ta 'ki zuwa kiran Aunty Murjan ganin khaleel ya fito daga 'kofar su zai yi hanyar waje ta ce.
"Kai khaleel zo na aike ka kaje 'kofar mu kace wai Hajiya ta na kiran Aunty Murjah" to yace yana juyawa ganin ya shiga yasa da gudu Bilki ta fice daga gidan dan kar ma su zarge ta.
Su Aunty Murjah su na d'aki su ka ga khaleel ya shiga yana cewa "Auntyn Ikram wai Hajiya tana kiran ki" kallon juna su kai da mamaki Zainab wacce ke gefe daya tayi tagumi jin ance kira daga Hajiya yasa tace "kin gani ko Aunty Murjah na san ba zai wuce ace wani ne ya je ya fad'a mata an kawo min firiza ba gashi har ta turo a kira ki meye laifin ki a nan"? Mi'kewa Aunty Murjah ta yi ta na d'aukar mayafin ta ta ce "sai me waya damu? bari na je naji me za ta ce min zan ga uban da ya kai saran na ki cewa an kawo miki fridge tun da ba uban mai fad'ar ne ya siya ba" kai Zainab ta girgiza ta na cewa.
"Dan Allah Aunty Murjah kar ki biye mata idan har ki ka tafi akan Umma za ta sauke fushin ta" huci Aunty Murjah ta fitar ta na cewa "wallahi Zainab sai na fad'i gaskiya sai dai ta tsabar 'kiyayya ta dafa Umma ta cinye bayan tafiya ta amma ba zan 'kyale ba wannan cin fuskar ya yi yawa ai dai iya 'yan d'akin mu ta ke wa bari na dawo" fita ta yi tana d'aukar takalman ta daidai Umma ta fito daga kitchen ta gan ta tsayar da ita ta yi da cewa.
"Murjah ina zaki je"?.
"Zan je gurin Hajiya ne Umma ina dawowa yanzu" tana fad'in haka dan kar Umman ta sake jefo mata wata tambayar ya sa da sauri ta fita daga 'kofar saboda ran ta a 6ace ya ke har matsuwa ta yi ta shiga gurin Hajiyan ta na zuwa kuwa ta same ta a 'kofar d'aki ta na hutawa zama ta yi ta na cewa....................
💓ZUCIYAR ALIYU CE💓
@DUTSE JIGAWA
PAGE 45
"Hajiya ga ni" kallon ta Hajiya ta yi ganin yadda ta had'e fuska ya sa ta fara magana "wato Murjah kamar yadda ki kai wa mutane itama wannan yarinyar haka take nufi ko uban waye ya kawo mata firiza d'azu wai abokin Samar ne ko? Shi ma Samar d'in munafiki yanzu da zan kira shi ba zai fad'a min waye ba saboda da ya iya 'kulle-'kulle ke ki fad'a min waye ya kawo mata"? Kai Aunty Murjah ta girgiza cike da takaici ta ce.
"Dama na san ba zai wuce akan haka ba matsala ta da ke Hajiya saurin d'aukar zuga yanzu wanne munafukin ne har ya zo ya fad'a miki an kawowa Zainab firiza saboda tsabar sharrin harda wani ta fara siyar da pure water da zobo da kunun aya daga kawo tan yanzu har ta fara wad'annan sana'o'in sai kace wata inji haba jama'a wacce irin masifa ce wannan"?.
"Aw Murjanatu nan d'in zuwa ki kai ki zage ni kenan saboda na ta'bo 'yar uwar ki Hauwan ce ta aiko ki ko kuma rashin kunyar ta ki ce ta juyo kai na"?.
"Ni fa Hajiya gaskiya na zo fad'a miki ba wai goyon bayan Zainab ko kuma na miki fitsara kamar yadda ki ke tunani bane gaskiya kuma dole na fad'e ta saboda ina gani ba za'a yiwa 'yar uwa ta 'kazafi ba".
"Iyeeh maza ki ci gaba da fad'ar gaskiyar d'ora daga inda ki ka tsaya nace ci gaba da zagi na Murjanatu uban wa ki ka ji yace 'kazafi akai mata ko akan hakan ki ke shirin zagin na wa"?.
"Hajiya kar ki sa mutanen gidan nan su d'auka da gaske zagin na ki nayi kawai raina ne ya 6aci akan wannan rainin wayon da ake mana ta ya baki san komai ba bayan yanzun nan Sameer ya shigo da firizar ko d'aki Zainab ba ta shigar da ita ba tana nan a waje inda Sameer d'in ya aje ta ko ta'ba ta ba ta yi ba amma har an samu wani d'an Allah bani mu huta gori d'in ya zo ya ta da fitina to duk wanda ya zo ya fad'i wannan maganar kar Allah ya bar shi ya kwana lafiya Allah ya tsine masa Ubangiji ya tarwatsar aniyar sa duk wanda ya ke son ganin ba'kin cikin Zainab in sha Allahu shi ne zai shiga cikin masifa da bala'i sai yaga 'karshen sa kowanne tsinannan ne ma" ta na fad'in haka ta mi'ke ran ta a 6ace sosai ta fice daga 'kofar Hajiyan ganin ta fita ya sa Hajiya mi'kewa ta na shirin bin bayan ta shigowar Bilki da sauri shi ya hana ta fitan kallon Bilki ta yi tana cewa.
"Je ki kira min Samar duk inda ya ke ya zo yanzu ina neman sa"? "Tom Hajiya bari na kira miki shi" Bilki ta fad'a tana juyawa ta fita Hajiya kuma ta koma ta zauna kafin Sameer d'in ya zo dan tasan tun da har Aunty Murjah ta na gidan yanzu idan ta je 'kofar ma akwai me tarewa Umma shi ya sa ta ha'kura sai bayan ta tafi.
Sameer kam da sa'kon Hajiya ya iske shi ma bai zo ba saboda shi kan sa yasan dalilin kiran ba zai wuce akan firizar d'azun ba ce dan haka ya bari sai da akai sallar magriba ya shigo 'kofar ta ya fara shiga domin ya ji me ya sa take neman sa samun ta ya yi tana sallar nafila ya jira ta yi raka'a shida ta yi sallama ko addu'a ba ta tsaya yi ba ta juyo tana kallon sa tace.
"Sannu isashshe sai yanzu sa'kon na wa ya riske ka ko kuma saboda tsabar ba ka mayar da ni mutum ba ya sa da aka fad'a maka ba ka zo akan lokaci ba"? Kai Sameer ya jinjina ya na cewa "ki yi ha'kuri Hajiya ban samu na zo bane tun lokacin da ki ka aika saboda ina ta duba marasa lafiya ba damar na rufe chemist d'in na zo".
"Yayi kyau dama tambayar ka zan yi Samar uban waye ya siyawa Zainab firiza"? Kallon Hajiya ya yi kamar zai fad'i wata maganar daban amma saboda baya son hayaniya ya sa kawai ya ce mata.
"Aboki na ne" sabuwar tambaya ta sake jefo masa.
"Waye abokin ka"?
"Aboki na man abokai
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 34