Share this page
Auwal ya fito Aunty Murjah ta na ciki 'karasowa inda Zainab ta ke ya yi yana cewa. "Sannu 'yar 'kanwa ta ashe ba ki da lafiya ai ban sani ba sai da na dawo princess ta ke fad'a min kuma gashi ke da baki da lafiya amma ki ka fito rakiya"? D'an murmushi Zainab ta yi daidai Aunty Murjah ta fito ta ce "ai da ya ke zazza'bin dare na yi daga shekaran jiya zuwa yau ne". "Allah ya kawo sau'ki ko dan ya kawo ma tun da gashi kin ware" kallon Aunty Murjah ya yi yana cewa "mu je dare ya na dad'a yi" kai ta d'aga su na fita a lokacin Ikram ta na kafad'ar Zainab ta yi barci jikin motar su ka zo Aunty Murjah ta bud'e baya ta shiga da mamaki Zainab ta kalle ta za ta yi magana ta ga an bud'e murfin gaban motar an fito zaro ido ta yi tare da d'auke numfashi ganin da wanda su ka zo............... Ya na ri'ke da murfin motar ya kalle ta da murmushi ya ce "barka da dare malama Zainab ya jikin na ki"? Har lokacin numfashin ta bai dawo daidai ba da'kyar ta iya ce wa. "Da sau'ki". "Masha Allah Ubangiji ya 'kara afuwa". "Amin na gode". "Na so ace mun d'an samu zama ni da ke mu tattauna amma ba lokaci sai dai idan na ji ni free zan sake dawowa in sha Allahu sai mu yi magana ko"?. "To" ta sake cewa muryar ta bai fita sosai kai ya jinjina yana komawa cikin motar ya zauna murmushi Aunty Murjah ta yi tana kallon ta tare da mi'ko hannu ta ce "kawo ta mu tafi" kai Zainab ta girgiza ta na d'an 6ata fuska ta ce "Aunty Murjah dan Allah ki bar Ikram a nan tun da gobe asabar ce ba school jibi zan kawo mi ki ita har gida da kai na Yaya Sameer ne zai rako ni". "Ai kuma akwai islamiyya"? Zainab za ta yi magana Sameer ya karaso gurin sakamakon ba ya nan su ka zo fitowa Auwal ya yi yana bashi hannu suka gaisa cikin tsokana ya ce. "A'a me gida Alhaji Sameer kana sha'anin ka sai yaushe za mu zo biki ne ko ba rana"? Dariya Sameer ya yi yana cewa "wanne biki amma ba nawa ba"?. "Na ka mana yaushe ne"?. "Tab ba rana ni da ko gini ban fara ba ka ga ina batun aure a gu na"? Da mamaki Auwal ya ce "kai haba dai"?. "Wallahi da gaske ne ke maka iya fili na ke da shi sai daga baya zan fara aikin sa" kai Auwal ya jinjina ya na cewa "ok Allah ya taimaka Allah ya kai mu lokacin". "Amin na gode" ya fad'a ya na juyawa inda Zainab ta ke tsaye ya ce "ya jikin na ki gaskiya ke 'yar gata ce sai zuwa duba ki ake uhm mu je a bani nawa abun dubiyar na san ya nan a d'aki jibgi-jibgi" dariya Aunty Murjah ta yi ta na cewa "tabbas ya na nan lodi-lodi ku je ka kar'bi rabon ka". "Hum ki ji fa har albishir ake min please Zainab mu je dan Allah" ita kuma Aunty Murjah ta ke kallo tare da cewa "to Aunty Murjah dan Allah na tafi da ita kwana biyu kawai kin ga fa ta yi barci"? Tun kafin Aunty Murjah ta yi magana Auwal ya ce "ba damuwa je ki da ita". "Yauwa Yaya na gode in sha Allahu jibi da kai na zan kawo ta sai da safe Yaya Sameer mu je ku gaida gida" ta na fad'in haka ta juya su ka shiga gida tare da Sameer saboda ya kar'bi Ikram tun da ta yi barci kuma Zainab d'in ba lafiya ce da ita ba har d'aki ya shiga ya kwantar da ita ganin dare ya d'an fara yi yasa daya fito ya d'auki bokitin da zai yi wanka ya fita daga 'kofar ta su. Sosai Zainab ta sha mamakin ganin babbar leda a ajiye a kusa da katifar ta kenan Aunty Murjah ce ta shigo da ita d'aukowa ta yi ta na shirin bud'ewa ta duba sai kuma ta ga kiran Aunty Murjan ya shigo d'agawa ta yi ta na cewa "hello Aunty Murjah wannan ledar ke ce ki ka shigo da ita"?. "Eh ni ce dama na manta ban fad'a miki ba shi ya sa na kira ki duba ledar nan za ki gan ta a d'akin ki kayan 'karamar ledar na mu ne na babbar kuma na masoyin ki ne Mukhtar" ta na fad'in haka ta yi dariya tare da kashe wayar dan ta san in ba haka ta yi ba sai ta yi mata 'korafi shiru Zainab ta yi hankalin ta a tashe ta kasa saka hannu ma ta bud'e ledar balle ta ga abin da ya ke ciki matsawa ta yi daga gurin ta koma kan katifa ta cirewa Ikram kayan ta sannan ta gyara mata kwanciya kafin ta tashi ta fita daga d'akin..................... 💓 ZÜÇÏYÄR ÄLÏYÜ ÇË💓 ♣Y♠ü♥s♣r♠ä♥h♣ ♣M♠ü♥s♣ä♣ ♣Ä♠b♥ü♣b♠ä♥k♣ä♠r♥. @YUSRAH MUSA ₱AGE 58 Washe garin ranar asabar da yake ba school za ta je ba islamiyya ce shiyasa ta dafa ruwa da wuri ta yiwa Ikram wanka ga shi ba'a zo mata da kaya ba dad'in abun ma akwai irin wanda idan sun zo su ke barin sa shi ta birkito a cikin kayan ta, ta saka ma ta. Su na d'aki Momy ta shiga tare da Husnah ta yi sallama Umma dake waje ta na shara ganin wacce ta shigo ya sa ta mi'ke tsaye cike da mamaki ta ce "a'a Hajiya Barakah ke ce a gidan na mu yau da kan ki"? Murmushi Momy ta yi tana cewa "wallahi ni ce ai dole in zo na duba 'yata ta na ina"? Aje tsintsiyar Umma ta yi tana cewa "bismilllah 'karaso" shiga d'akin Umma ta yi suka gaisa ta na cewa. "Ya mai jikin kuma ai jiya ina ta jiran Afifah na ga ba ta koma gida da wuri ba ashe nan ta zo duba ta fatan ta warware"? Kai Umma ta d'aga tana cewa "alhamdulillah jikin ta ya yi sau'ki sosai ya kwanan yaran". "Masha Allah haka ake so yara su na lafiya ta na ina yanzu"?. "Ta na d'akin ta tare da Ikram" mi'kewa Momy ta yi tana cewa "ok bari na je na duba ta Husnah tashi mu je" fita su kai Umma ta bud'e labulen 'kofar d'akin Zainab ta na cewa "Zainab ki na ciki ne ga Maman Afifah ta zo duba ki" sakin labulen Umma ta yi tana cewa "bismilllah Hajiya Barakah ki shiga ta na nan" komawa Umma ta yi ta ci gaba da shara Momy kuma ta shiga d'akin Zainab da 'yar fara'a Zainab ta ce. "Lah Momy ke ce sannu da zuwa" ta fad'a tana tashi ta d'auko sallaya ta shimfid'a mata zama Momy ta yi bayan sun gaisa ta ce "ya jikin na ki da sau'ki ko"? Kai ta d'aga ta na cewa "eh na samu sau'ki ina kwana"?. "Lafiya 'kalau Zainab Allah ya 'karo miki lafiya kin ji". "Amin Momy na gode" ta fad'a ta na ri'ko hannun Husnah ta ce "Husnah har da ke aka zo ina su Elham da Fati"?. "Su na gida Aunty Zainab ya jikin"? "Jiki alhamdulillah Husnah da sauki" mi'kewa Momy ta yi tana cewa "Auta tashi mu je" tashi Husnah ta yi su ka fita daga d'akin a lokacin har Umma ta gama sharar da ta ke yi ganin su ya sa ta ce "kun fito"?. "Eh za mu tafi Allah ya sauwake". "Amin Hajiya mun gode Allah ya saka da alkhairi". "A'a ba komai Zainab ai 'ya ta ce dan na zo duba ta dad'i na ji yara su na yabon ta sosai kuma su na matu'kar jin dad'in karatun ta a islamiyya kullum sai sun fad'a shi ya sa ni ma har ta shiga rai na sosai" murmushi Umma ta yi cikin jin dad'i daidai Momy ta juya za su fita a 'kofar ta ce "sai anjima a sake yi mata sannu idan ta fito". "To in sha Allahu Hajiya mun gode Allah ya saka da alkhairi" ta fad'a ta na shirin shiga d'aki Asabe ta fito tana kallon ta tace "oh! Ni 'yasu na shiga d'aka ni jikar mutum hud'u anya Hauwa ki na neman zaman lafiya kuwa ashe asirin naki har ya bar kan mu 'yan gida ya koma kan masu kud'in anguwar nan meye had'in biri da gada ki fad'a min in dai ba sharrin asiri ba ko a mafarki wannan matar ba za ta tako gidan nan ba balle har ta yi magana da ke ta na matsayin matar minister ke kuma matar me siyar da kayan miya da gawayi" juyawa Umma ta yi tana kallon ta jin abin da ta ce ya sa ta girgiza kai cikin takaici ta ce. "Ai ke Asabe na dad'e da jingine ki a gefe duk wani abu da zaki fad'a a kai na ko 'ya ta sai dai na kalle ki da ido" a masife Asabe ta ce "yo ai dole kin kalle ni da ido man tun da kin gama dani kin cuce ni kin raba ni da miji na kin raba ni da d'ana bani da ma'kiyiya sama da ke a duniya duk wani ma'kiyi na sai dai ya biyo bayan ki" numfashi Umma ta sau'ke tana cewa. "Allah ya kyauta sannan Allah ya tsare ni da wadannan mugayen abubuwan da kike siffata ni da shi ban kasance mai aikata shirka ba ban ta'ba zuwa gurin malami ba balle boka sharrin da kike min idan ban yafe miki ba sai Allah ya saka mun" Umma na rufe baki Asabe ta yaryara gud'a mai zafi ta na cewa "ahayyye ayuririiiiiiiii ji ba'kin munafirci da baki aikata ba zan fad'a ne? Dad'in abun ma kin yi kuma dole na fad'a ko zaki mutu Allah ya sauwake na yi wa tsogalgalar mace sharri irin ki ni zuciya d'aya nake zaune da ke kece kike nufi na da sharri kuma sai dai ya koma kan ki" ta fad'a ta na tofar da yawu ganin da Umma ta yi kawai Asabe neman ta take da fad'a ita kuma ba za ta biye mata ba sai kawai ta ce "ki fad'i komai ki zauna lafiya domin ni ba zan kula ki ba amma zan ro'ki Allah ya fitar da me gaskiya tsakanin mu" ta6e baki Asabe ta yi tana cewa "ai kuma ni ce me gaskiyar ke wacce gaskiya ki ke da ita 'yar d'an Yana". "Kan ki ake ji". "Ke ma ana jin naki kan shi yasa na ga 'yar ki ta'ki auruwa saboda kowa yana gudun d'iban annoba ya kai gidan sa kar a mallake shi da asiri". "Ki fad'i komai Asabe ba zan tanka miki ba Allah ya fiki" ta na fad'in haka ta wuce d'aki ita ma Asaben ba ta sake magana ba ta ci gaba da aikin had'a kayan karyawar da ta ke yi da gudu Ikram ta d'auko kofi ta yo waje duk kiran da Zainab ke mata ba ta koma ba har 'kofar d'aki ta biyo ta tana cewa "Ikram ke Iki ina za ki je dawo min da kofin nan" Ikram ba juya ba gurin Asabe ta zo tana mi'ka mata tace "a zuba min shayi na" d'agowa Asabe tayi tana kallon ta tare da fisge kofin ta yi jifa dashi tana cewa "to 'yar gidan maciya bamu da shayi a gidan nan ban dafa ba matsa ki ban guri 'yar gadararru harda wani a zuba miki shayin ki uban shayin ki za'a zuba miki Auwal ya siyo Lipton din ya kawo ne"? Shiru Ikram ta yi ta zubawa Asabe ido wanda ya sa Asabe cewa. "Mayya ko cinye ni za ki yi naga ki na yi min irin wannan tsinannan kallon"? Jin abun da Asaben ta ke fad'a akan yarinyar da bata fi shekara hud'u ba ya sa Zainab fitowa ta tsaya daga wajen 'kofar d'akin ta tace "Ikram zo nan". Hararar ta Asabe ta yi tana cewa "eh tazo nan d'in domin ko wuni za ta yi anan bazan bata wannan shayin ba saina gama had'a komai na baku rabon ku idan kuma wuta ce a cikin tama saidai ta cinye ta 'yan masu da gadara haka kawai da gidan uban ta tsabar son a sani ku ka kar'be ta wallahi kun kar6i banza ba zan ta'ba raba abinci da ita ba har tabar gidan nan yadda nake zuba muku haka zan zuba ba ruwa na da wata yarinya idan kun ji haushi ku mayar da ita gidan uban ta" ita dai Zainab ko tari ba ta yi ba ta d'auke Ikram daga gurin suka koma d'aki ta zaunar da ita ta d'auki biscuit ta 6are ta bata kar6a ta yi tana ci ganin haka yasa ta d'auko mata buredi ma ta aje mata a gefe sannan ta d'auki indomie guda d'aya ta fita zata dafo mata ganin abin da za ta yi yasa Asabe ta6e baki ta na cewa. "Eh da hakan ku kai dai yafi domin shi kansa mai gidan ko biyar bai dad'a a kud'in abinci ba yadda ya ke bayarwa haka ya bada balle kuce ya had'a da nata kud'in harta bar gidan nan ni dai bazan ta'ba raba abinci da ita ba idan kun ga taci sai dai ranar girkin munafikar kakar ta" sosai takaici ya rufe Zainab amma har lokacin bata yi magana ba shigowa Sameer ya yi yana waya ganin Zainab d'in a waje ya sa yayi wajen inda take ya na cewa. "Eh a'a kar ka kashe na shigo ga ta nan bari na ba ta" mi'ka mata ya yi yana cewa "kar'bi za'a duba ki" har zata tsaya tambayar waye sai kuma ta fasa ta kara a kunne tare da yin sallama ya na dafe da saitin zuciyar sa ya na jin yadda ta ke bugu sakamakon jin muryar ta kawai gaida shi ta yi duk da ta so ta d'auki muryar shi a lokacin da ya amsa mata sallamar amma ta kasa gane weye......................... "Ya jikin na ki fatan kin samu lafiya"? Ta ji ya katse ta kai ta d'aga a hankali kamar ya na gurin ta ce "da sau'ki". "Alhamdulillah Allah ya 'karo sau'ki ko kina jin wani abu har yanzu"?. "A'a na warke na samu lafiya". "Ok ya yi kyau Allah ya 'kara lafiya". "Amin na gode". "Ba komai ba godiya tsakanin mu baiwa Sameer d'in" mi'ka masa ta yi ya kar6a yana murmushi ya kara a kunne yana cewa "ok" "ok eh shikenan sai zuwa jimawa" daga haka ya sauke wayar yana kallon ta yace "ina Ikram ko bata tashi a barci"?. "A'a ta tashi tana d'aki indomie na ke dafa mata". "Ok" kawai ya ce ganin ya na shirin fita kuma bai fad'a mata waye ya duba ta ba ya sa ta ce "Yaya Sameer" dakatawa ya yi tare da juyowa ya ce "na'am". "Waye wannan da ya duba ni"? Murmushi ya yi yana cewa "Aboki na ne man" da alamar tambaya tace "Abokin ka"?. "Uhm ya akai"? Jiki a sanyaye ta girgiza kai 'kare mata kallo ya yi daga baya ya yi yana sake yin sabon murmushi daidai Ikram ta fito tana jefar da ledar biscuit d'in da taci hannu Sameer ya bud'e mata yana cewa "oyoyo 'yar Abban ta yau kin kwana a gidan mu ko zo nan" 'karasowa ta yi ya d'auke ta ya na kallon Zainab yace "bari mu dawo" ya fad'a su na fita daga 'kofar yatsa Asabe ta ciza kamar za tai hauka ganin yadda suka bi su ka kanainaye mata d'a huci kawai ta ke fitarwa jira take ya dawo ta yi masa zagin 'kare dangi Zainab kam indomie ta juye mata ta tafi d'akin kafin su dawo............. ZUCIYAR ALIYU CE ❤️️YMA DUTSE JIGAWA STATE Ni YUSRAH MUSA ABUBAKAR ina alfahari da jiha ta domin ba ni da kamar ta duk in da naje a fad'in duniya ❤️JIGAWA❤️ zan dawo ga shi abun sha'awa a cikin Nigeria mu ne muke da gada sannan mu ke taka kan ❤️DUTSE❤️ idan ka ji ana cewa birnin daraja wanda ya cika ya batse da al-umma to fa ♥JIGAWA STATE CE♥ ga haske a cikin ❤️JIGAWA❤️ ga kuma adon ❤️DUTSE❤️ ta ko'ina garin dad'i ❤️JIGAWA❤️ kafin Allah. ❤️JIGAWA❤️ jiha ta ce abar alfahari na ce sannan mu na zaune lafiya da juna ba ma rigima ko tashin hankali ni fa idan an ce ❤️JIGAWA❤️ har wani tunkaho na ke ji Masha Allah ina godiya ga Allah swt da ya kaddara min kasancewa ta cikin ❤️JIGAWA❤️ ba karamin falala ba ne gare ni. @YUSRAH YMA DUTSE PAGE 59 Ta na zaune ya shigo ya na aje Ikram da abin da ya siyo mata kallon sa Zainab ta yi tana cewa "lah Yaya Sameer wai abun karyawa ka siyo mata kaga fa taci biscuit ga buredi kuma kaga indomie ma ita na dafowa" kai ya d'aga yana cewa. "Ba ta 6aci ba ki aje mata wannan d'in kafin a gama girkin rana sai ta ci tun da yarinya ce kowanne lokaci za ta iya neman abinci ki saka mata a cooler sauri na ke zan koma chemist". "To Yaya Sameer an gode Allah ya 'kara arziki". "Amin" ya na fad'in haka ya juya ya fita daidai Asabe ta fito daga d'aki ta gan shi ya na shirin ficewa da sauri ta ce "kai Sameer zo nan" komawa ya yi inda take ya zauna a kusa da ita ya na cewa "ga ni Umma" wani irin kallo Asabe ta yi masa ta na cewa. "Wai me ka ke son mayar da kan ka ne soko shashasha saki tumaki 6allo jakuna kake son mayar da kan ka akan wadannan mutanen ko me? Da mamaki Sameer ya ce "da na yi mefa Umma"? cikin takaici ta ce "da ka yi uban ka wato ma saboda ka na son mayar da ni shashasha shi ne ka ke tambaya ta wai me ka yi ko"? Had'e hannu Sameer ya yi yana cewa "Umma dan Allah kiyi ha'kuri idan na 6ata miki rai yanzu ana jira na a chemist zan shigo zuwa jimawa sai mu yi maganar kin ji" kai ta jinjina tana cewa "shikenan je ka" tashi ya yi ya fita Asabe da ta gama had'a komai ta kallo 'kofar d'akin Umma ta na cewa. "To isashshiya na gama idan kin ga dama ki fito ki d'auke mu ku" ta na fad'in haka ta bud'e labulen d'akin ta, ta shige kai Umma dake kwance a d'aki ta girgiza tana sake gyara kwanciyar ta kusan mintuna goma ba wanda ya fito domin Zainab duk zaton ta ko Umma ta fito ta d'auke sai da ta fito sannan ta ga komai a gurin zuwa ta yi ta d'ebe ta shigar da shi d'akin Umma ta tarar barci ma ta ke kawai ta ajiye ta fita ta koma d'akin ta, ta d'auki kayan d'inki ta soma duba wanda ba ta d'inka ba ko zuwa jimawa ne sai ta yi. NA'IBAWA Saukar wata mace a Napep kenan bayan ta biya me Napep d'in kud'in sa ta 'kwan'kwasa wani gida dake rufe tare da d'an komawa baya ta tsaya kafin a zo a bud'e mata jin shiru yasa ta sake 'kwan'kwasawa daidai an bud'e 'kofar ta kalli wacce ta bud'e tare da sakar mata harara ta na cewa "wato ke idan aka zo gurin ki sai mutum ya 'kai'kashe baki zo kin bud'e masa 'kofa ba ko wannan da abun cutarwa ne ya biyo ni sai dai ya kashe ni ai" dariya ta yi tana matsawa ta ce "haba ke kuwa 'kawa ta ai kema kin san ba halina ba ne ban ji da wuri ba ina kitchen Nassar ya na parlor yana kallon cartoon shi ne ya fad'o min fa". "Humm lallai ya yi". "Shigo man ki ka tsaya a nan"? "A'a ba zan shigo ba kuma idan Yaa Sayyidi ya na nan fa ni da na zo mu yi magana". "Hum'um da yana nan ma ba ruwan sa dake balle baya nan sai ka ce yau ki ka fara zuwa gidan ki shigo dan Allah mu je". "Ok mu je to tun da baya nan" shiga su kai sakamakon Nassar ya na parlor ya na kallo su ka wuce can cikin bedroom su na zama Samirah da ta aje mayafin ta ta ce "lallai 'kawar arziki gaskiya ba amana wallahi ba amana yanzu tsakani da Allah ba dan na ji labari ba da shikenan sai dai daga baya na zo miki jaje duk tsiya ai mu ne 'yan danna 'kirjin ko"? Cikin rashin fahimta Sabirah ta ce "ban gane danne 'kirji ba? 'kirjin wa za ku danne"? Dariya Samira ta yi tana cewa "ina wata bayan ke"?. "Har yanzu ban gane abin da ki ke nufi ba fa ni me ye had'i na da danne 'kirji"?. "Ki na da had'i dashi man tun da mijin ki ya fara 'ko'karin neman aure" zabura Sabirah ta yi tana zaro ido ta ce "ban gane ba aure ya ce miki zai 'kara aure fa? Amma ya kasa fad'a min waye ya fad'a miki"?. "Ina zaune na ji zancen ya same ni shi ne ma dalilin zuwa na, na ji inda gaske ne". "Gaskiya duk wanda ya fad'a miki ma bai ji daidai ba saidai idan wani Yaa Sayyidin ake nufi amma ba wannan ba". "Yauwa abun ya bani mamaki shi ya sa har na kasa ha'kuri na zo fa" dariya Sabirah ta yi tana cewa"ya 'kara aure a ina zai saka ta bayan ba fili ne dashi ba kuma shi ba wata 'kwak'kwarar sana'a ba". "Ki ka sani ko had'a ku zai yi"?. "Ya had'a wa? Ai kuwa da yaga tashin hankali dan wallahi sai na 'kone duk shegiyar da ya aura sai dai ni ma a kashe ni". "A'a hakan ma ba zai faru ba tun da jita-jita ba gaskiya ba ne mu bar maganar kawai" mi'kewa Sabirah ta yi ta na cewa "ki dawo parlor fankar d'akin ta lalace kuma akwai zafi bari na je kitchen na duba kar abincin ya fara 'konewa saura kad'an ruwan sanda na fito" tashi ta yi su ka fita tare ita tayi waje Samirah kuma ta zauna a parlor ta na d'auko wayar ta daga handbag ta saka caji.................................. ZUCIYAR ALIYU CE ≈≈≈≈≈≈≈≈≈≈≈≈≈≈≈≈ J.W.A @YUSRAH YMA ₱AGE 60 A ranar Sabirah ba ta samu sun yi magana da Yaa Sayyidi ba sakamakon bai dawo gida da wuri ba sai washe gari da safe bayan ya yi wanka ya shirya ya taje gemun sa ya debi littafai zai fita ta ce "Abban Nassar wai da gaske ne ka na neman aure"? Jin tambayar da ta yi masa ya sa ya tsaya ya na jinjina kai yace "eh gaskiya ne" zabura Sabirah ta yi ta na cewa "aure za ka 'kara me nayi maka meye na rage ka dashi ka ke son yi min kishiya"?. "Dama waye ya fad'a miki sai mace tayi laifi sannan ake mata abokiyar zama ra'ayi ne yasa zan 'kara saboda ina so ba wai dan kin gaza da yi min wani abu ba". "Ai kuwa wallahi ba zai yuwu ba gaskiya ba zan iya ba wannan ai masifa ce haka kawai ina zaune ni kad'ai ban damu da kowa ba za ka d'aga min hankali". "Ke ki ka d'agawa kan ki hankali tun da ke ce ki ka fara tada maganar ba ni ba". "Me ka ke nufi"? "Zan ba ki amsa idan na dawo" ya na fad'in haka ya juya ya fita rasa in da za ta saka kan ta taji dad'i ta yi kenan jita-jitan da Samirah taji gaskiya ne tun da akwai 'yar uwar su Yaa Sayyidi da ta ke aure a makoftar su wato a nan ta ji labari, da sauri ta d'auki waya ta na danna kiran Samirah ta shiga amma ta na ta ringtone ba'a d'aga ba har ta katse sake kira ta yi nan dai no answer wani irin takaici ne ya rufe ta aje wayar tare da cizon yatsa ta ce "humm ba dai aure za ka 'kara ba? Zan ga tsinanniyar da za ta aure ka idan kwanakin ta ne a kusa sai na kashe ta walla.................. Kiran wayar ta da akai shi ya katse mata tunanin da take yi

Chapter 24 of 34