Share this page
na da yawa idan na fad'a miki sunan sa ma ba san shi ba". "A ina ya ke"? Kafad'a Sameer ya d'aga ya na cewa. "Yana ko'ina". "Ban gane ya na ko'ina ba"?. "To Hajiya idan na fad'a miki in da ya ke amfanin me hakan zai yi miki"?. "So na ke na bashi umarni ya turo iyayen sa in dai da gaske ya ke ba mayaudari ba ne". "Da gaske ya ke man auren ta zai yi in sha Allahu Hajiya ki kwantar da hankalin ki ya kusa dawowa gari Zainab ta kusa ta bar gidan nan ta koma gidan mijin ta" yana rufe baki Hajiya ta d'aga hannu sama ta na sake ri'ke carbin ta da kyau ta ce. "Allah Amin Allah ya sa naga wannan ranar" sauke hannu ta yi ta na kallon Sameer ta ce "idan ma 'karya ka ke Allah ya biya bakin ka" mi'kewa ya yi ya na cewa "balle ma ba 'karyar na ke ba gaskiya ce na fad'a miki akwai mai son ta da aure kuma shi ne ya aiko ni da sa'kon fridge d'in" kai Hajiya ta d'aga ta na cewa. "Shikenan ba damuwa Allah ya bayyana shi sai ya zo d'in mu na nan mu na jiran sa". "Yauwa ko ke fa Hajiya Amin har kin sa na ji dad'i amma kullum ace sai an samu sa6ani haba wallahi abun nan ya na mugun 'kona min rai gida d'aya jini d'aya 'yan uwan juna babu bare amma had'in kai ya yi 'karanci duk laifin ya na gurin............... Katse shi Hajiya ta yi "ka ga Samar ka yi tafiyar ka na gane komai ya wuce na fahimta". "Ok sai da safe" ya fad'a ya na fita 'kofar su ya nufa daidai Aunty Murjah ta fito daga d'akin Zainab ri'ke da jakar kayan ta Auwal da ya zo d'aukar ta shi kuma ya shiga d'akin Umma su na gaisawa kallon ta Sameer ya yi yana cewa............................ ZUCIYAR ALIYU CE J.W.A @YUSRAH YMA PAGE 46 "Tafiya za ki yi ne dama motar da na gani a waje ta Daddyn Ikram ce"? Kai Aunty Murjah ta d'aga ta na cewa "eh dama mun yi da shi yau zai zo ya d'auke ni shi ya sa jiyan ma na dawo" kai ya d'aga yana cewa "ok ki gaida gida" ya fad'a ya na wucewa fitowa Auwal ya yi suka gaisa sannan suka fita su uku Zainab za ta yi musu rakiya zuwa 'kofar gida d'akin Zainab Sameer ya shiga ya na bud'e fridge d'in ya ga duk an saka lemukan da pure water murmushi ya yi dan yasan wannan shirin ba Zainab bace sai dai Aunty Murjah d'aukar juice guda d'aya ya yi ya fita daga d'akin ya shiga na sa. Su Aunty Murjah kam fitar su Auwal ya ce su shiga gurin Hajiya su gaisa da ita iya su biyun suka shiga Aunty Murjah za ta yi masa rakiya amma Zainab kam ko da wasa ba tai marmarin shiga ba, a d'aki su ka samu Hajiya ta na kwance da radio a kusa da ita ta na saurara jin sallama yasa ta rage volume tana cewa. "Waye a waje? Ku 'karaso man" Aunty Murjah ce ta fara shigowa sannan shi ma ya shigo ya dur'kusa ya gaida Hajiya gaggawa Aunty Murjah ta ke ya tashi su tafi saboda kar Hajiya ta 6aro wata maganar amma Hajiya sai jan sa ta ke da hira da labarai ganin dare ya na sake yi yasa Aunty Murjah ce wa. "Sweet ya kamata mu tafi goma ta kusa tara da mintuna" kai ya jinjina yana mi'kewa tare da saka hannu a aljihu ya ciro dubu uku ya ajewa Hajiya ya na aje mata tun kafin ya ce wani abu ta d'ebe ta na cewa. "Allah ya yi maka albarka irin ku ake so wanda su ne na Allah bakwa gajiya da kyauta Allah ya 'kara bud'i ka ji? Ubangiji ya tsare ka daga sharrin ma'kiya". "Amin Hajiya na gode sai wata ran" ya fad'a ya na fitowa ya saka takalman sa ita ma Hajiyan mi'kewa ta yi har 'kofar fitowa daga lungun ta ta rako shi ta na masa addu'a kamar ba za ta daina ba sannan ta juya ta koma ciki waje suka fita Zainab dake ri'ke da jakar ta ta mi'ka mata tana murmushi ta ce. "To Allah ya tsare Momyn Ikki sai ranar da na sake zuwa miki Yaya Auwal ku gaida gida" kai ya d'aga yana cewa "mun gode Hajiya Zainab sai kin zo mana ziyara domin mu fa har yanzu ba mu ha'kura ba muna ciki" kamar Zainab ba ta san akan me yake magana ba ta ce. "Ku na cikin ina"? Murmushi ya yi ya na kallon yadda ta juyar da kai ya ce "ke ma kin sani ai da tare da Mukhtar d'in zamu taho dan kawai ya zo ya gan ki sai kuma uzuri ya tare shi" kai ta jinjina tana cewa "gara da bai samu damar ya zo ba dan da ya biyo ka ma ba gani na zai yi ba" da mamaki ya kalle ta ya na cewa. "Saboda me bayan ga ki a tsaye ina kallon ki amma ki ce shi ba zai gan ki da ace ya zo d'in"?. "Saboda ba zan fito ba ma balle mu had'u da shi har ya yi tunanin ko da gaske ina jin wani abu game da shi" d'an zaro ido Auwal ya yi ya duban ta ya ce "haba dan Allah Zainab aboki na ne fa yana matu'kar son ki wallahi dan kawai kin 'ki ba shi fuska ne amma da yanzu ya aure ma na ke kin tafi gidan sa kin ga wannan zuwan da na yi shima da sai dai kawai ya zo ya d'auke ki ku tafi gidan ku ko"? Kusan dariya ce ta so ya 'kwacewa Zainab da sauri ta danne tana cewa. "Hummm tabd'ijan" kawai shi ne abin da tace ta na kallon Aunty Murjah wacce ke tsaye jikin motar ta na dariya da har ta za yi magana sai ta fasa kawai ta ce "ku gaida gida a gaisar min da Ikram" kai Aunty Murjah ta d'aga ta na cewa. "Zata ji in sha Allahu sai da safe" ta fad'a ta na shiga mota Auwal da ke tsaye ya na d'an kad'a key d'in motar ta sa sake kallon Zainab ya yi yana cewa "to 'kanwa ta kuma wife to be d'in babban aboki na mun tafi". "Uhum mu kwana lafiya ku gaida gida" ta na fad'in haka ta juya ta koma shiga motar ya yi Aunty Murjah da ke kallon 'kofar gate d'in gidan na su tace "kai gaskiya Zainab sai a hankali ita fa gaskiyar abin da ya ke ran ta take fad'a" kai Auwal ya jinjina ya na cewa "ni ma na ga alama gaskiya Mukhtar ba zai ta'ba samun kar6uwa ba duba da lokacin da aka d'iba kawai sai dai ya yi ha'kuri" numfashi Aunty Murjah ta sauke tana cewa "uhm Allah ya kyauta mu je" tada mota yayi yana cewa "ta gidan Mama za mu bi mu tafi da Ikram saboda ta d'an jima a can ya kamata ta dawo gida haka". "Ka bari gobe da safe idan na yi abinci sai mu je tare na gaida Maman idan na wuni da yamma idan ka dawo daga wajen aiki sai ka je ka d'auko mu ko"?. "Ok tom shikenan hakan ma ya yi" ta fad'a ya na jan motar su ka bar gurin su kai gidan su..................... AYI HA'KURI IDAN AN SAMU TYPING ERROR MATSALAR KEYBOARD NE. ♥ZUCIYAR ALIYU CE♥ @YMA DUTSE PAGE 47 Sameer kam tun da ya shiga d'akin sa bai fito ba har Zainab ta dawo ta kwanta ya dad'e daga baya ya fito d'akin Asabe ya shiga ta na zaune ta gan shi d'an hararar sa ta yi musamman tuna d'azu da ta dawo daga anguwa Bilki ta fad'a mata ya shigowa da Zainab firiza kamar za ta yi masa magana akan hakan sai kuma ta share ta na d'auke kan ta daga saitin sa Sameer ya na tsaye bai zauna ba ganin ta na kallon juice d'in da yake hannun sa yasa ya ce "ga shi Umma idan na fita daga nan na shiga na d'auki wani" wani d'an iskan kallo ta yi masa ta na ta'be baki tare da nuna kan ta tace "wa ni? Allah ya rufa asiri na sha abin da ya fito daga hannun wad'ancan mutanen har abada" jin abin da ta ce yasa Sameer kallon ta ya na cewa. "Kai dan Allah Umma wai me yasa ki ke haka ne"? Harara ta sakar ma sa cike da takaicin ya za6i 'yar kishiya akan wacce su ke d'aki d'aya ta ce "au kai ka ke cemin? Iya kai ban da 'kafofi kaga Sameer ka fita safga ta ka kiyaye ni na fad'a maka hummm". "Ki yi ha'kuri dan Allah Umma ban fad'i hakan dan na 6ata miki rai ba" "Shikenan zan huce ne kawai idan ka fita ka siyo min nama ko kifi" jin abin da ta ce yasa ya saki murmushi ya na laluba jikin sa ya ce "ba damuwa Umma zan siyo miki amma yanzu ba kud'i a jiki na wallahi". "Kan uba lallai ma Sameer ka mugun raina min hankali amma da wancan yarinyar ce tace haka jikin ka yana 6ari za ka fita ka siyo ka kawo mata saboda gudun 6acin ran ta ko"?. "A'a Umma ba haka ba ne ita ma duk abin da za ki ga na kawo mata ba kud'i na bane sa'ko ne aka bani na bata ina na ga kud'in da zan ri'ka mata irin wad'annan abubuwan in dai zan samu kud'i kamar haka na fara gini man" wani karkataccen kallo ya sa, Asabe ta yi masa ta na cewa. "Ma'karyacin banza uban waye zai baka ka bata da gaskiya ne ka fad'i waye yake aiko ka mana amma saboda ka san 'karya ka ke ina gashi har yau ban ga idon wanda ya ke aiko ka d'in ba" murmushi ya yi yana kallon ta ya ce "wallahi da gaske na ke Umma amma tun da ba ki yarda ba bari na fita ko ATM d'ina sai na je da shi na siyo miki". "Kai ka sani wannan matsalar ka ce" juyawa ya yi yana fita daga d'akin ta na jin sanda ya ke kiran sunan Zainab tsaki ta ja tana cewa "na rasa wacce irin maita ce wannan dan bala'i ace in dai ka shigo sau goma saika kira sunan ta kamar tare aka haife ku? Aikin banza mtwwww ta sake jan tsaki ta na kwanciya jiran dawowar sa take ta tsawatar masa akan wannan shishshigin da yake ya fara isar ta................................ Yau ba yawa typing d'in ZUCIYAR ALIYU CE Yusrah Musa Abubakar ce. #Team Zainab #Team Aliyu ♥Y♥S♥R♥H♥ @YMA JIGAWA PAGE 48 POV SHAREEF Yana zaune a parlor tare da Mami su na magana ta kalle shi tana cewa "Shareef ni kuwa kamar kwanan baya ka ce min ka samu wacce kake son aura daga haka kuma ban ji ka sake cewa komai ba ko dama da wasa ka ke yi"? Kai ya girgiza ya na cewa. "A'a ban fasa ba kuma ba da wasa na ke ba". "To amma daga ihu d'aya sai murya ta dashe gaskiya ni fa na matsu na gan ni da suruka ta"?. "Zaki gan ta Mami har sai kin gaji da ganin ta idan na aure ta". "Anya zan gaji da ganin 'yata kuwa? Yadda ban ta'ba jin na gaji da ganin ka ba ita ma haka to amma a ina ta ke ko yarinyar nan da ta ta'ba zuwa gidan nan ta gaida ni"? Da sauri ya girgiza kai yana cewa "nooo Mami ba ita bace haba dai ni Shareef na auri wannan yarinyar Allah ya rufa asiri" da mamaki Mami ta ce. "Me ya sa"?. "Haba Mami akwai dalili man ni ba irin ta na ke son aura ba saboda ba zan iya da matsalolin ta ba". "A haka kuma lokacin da ta zo min yarinya me hankali da nutsuwa kamar ba ta da wata matsala"? Kai ya jinjina ya na cewa "fuska biyu gare ta Mami dan baki zauna da ita na d'an wani lokaci ba shi ya sa ki ke ganin kamar ba ta da wani matsala d'in amma a zahiri kuwa wannan yarinyar da ki ke gani humm ba ta da kyau". "To Allah ya kyauta wancan surukar ta wa a ina ta ke"?. "Tana anguwar su". "Ina ne anguwar su kuma"? Sake cewa ya yi "anguwar su can man na ke fad'a Mami anguwar su fa" cikin rashin fahimta Mami ta ce "ikon Allah Shareef kenan ai kowa ma ya na da anguwa sunan ta zaka fad'a min". "Neehal". "Nihal sunan ta"? Kai ya jinjina na tare da ya yi magana ba Mami ta ci gaba "a wacce anguwa ta ke"?. "Zan fad'a Mami amma ba yanzu ba". "Sai yaushe"?. "Idan na dawo daga hospital zan fad'a miki" ya fad'a yana mi'kewa tsaye da kallo ta bishi tana cewa "ka yi alkawari"?. "In sha Allahu Mami zan fad'a miki ina dawowa tun kafin na shiga part d'ina". "Shikenan ba matsala Allah ya dawo da kai lafiya ina sauraro". "Ok Mami ki wuni lafiya" ya fad'a ya na fita murmushi Mami ta yi bayan fitar sa ta yi shiru kawai kamar me tunani ta dad'e a haka daga baya ta sauke numfashi jin 'karar bud'e gate da rufewa ya sa ta fahimci an shigo gidan to amma waye zai zo a wannan lokacin Shareef dai yanzu ya fita balle ta ce shi ne to ko Alhaji ne ya dawo shi ma kuma me zai dawo yi? Ta na shirin tashi ta le'ka ta ga sun shigo da sallama Daddyn Shareef a gaba sai wasu maza mutum biyu a bayan sa d'aya tsoho d'ayan kuma ya kai misalin magidanci kallo d'aya Mami ta yi musu ta ji yawu bakin ta ya 'kafe numfashin ta yana neman tsayawa har ba ta san lokacin da ta zabura ba zama Daddy ya yi shi ma jikin sa sanyaye ya ce. "Kin ga wad'anda ba ki ta'ba tunanin zuwan su a irin wannan lokacin ba ko? Ni ma ina zaune a office akai min aiken ana sallama da ni ina fitowa na gan su ashe yau kwanan su biyar ma da shigowa Nigeria d'in" numfashi Mami ta sauke ta na cewa "sannun ku da zuwa Baba Sadoh" ta kalli d'ayan ta na cewa "Amru ku ne na ke gani ko mafarki na ke yi"? D'an murmushi Baba Sadoh ya yi ya na d'aga kai yace. "Eh mu ne dama mun d'an shigo ne gobe maza mu tafi mu koma Niger d'in shi ne nace wa Amru mu 'karaso mu gaisa da ku ba dan haka ba ma yau zamu tafi" hawaye ne ya fara cika idon Mami ta na jin yadda ran ta ke sosuwa da tuna ba ya tace. "Yauwa gara da ku ka zo dama tun da aka haifi Shareef bai ta'ba sanin a ina dangin mahaifiyar sa su ke ba bai ta'ba kawowa a ran sa ba ni ce na haife shi ba, lokaci ya yi da ya kama ta ace ya san komai" jin abinda ta ce yasa Baba Sadoh saurim girgiza kai yana cewa "a'a a'a ba wannan ya kawo mu ba ki ci gaba da ri'ke Shareef matsayin ke ce ki ka haife shi kar ki fad'a masa wannan maganar mu ba mu zo dan tarwatsa muku farin cikin ku ba gaisawa kad'ai mu ka zo yi domin koma mene ina tuna kalar ri'kon mutunci da amana da ku kai wa 'ya ta shi ya sa bana so na zama silar shigarku damuwa domin na zo na same ki cikin farin ciki ne". "Ba tarwatsa farin ciki ba ne lokaci ya yi daya kamata Shareef ya gana da ku dan Allah ku bari mu fad'a masa gaskiyar lamari idan bai sani ba shi ke nan fa a haka zamu ci gaba da tafiya ku kuma sai dai ku ha'kura da shi". "Dama mu mun dad'e da ha'kura da shi Shareef d'an ki ne na halak kar ki damu bayan me d'an da kanta ta furta kalmar ta yafe miki shi yaushe zamu karya wannan alkawarin tun da dai mun zo kuma mun gan shi hankalin mu ya kwanta ba sai ki fad'a masa ba dan Allah ki ci gaba da zama matsayin mahaifiyar sa kar ku bari ya gane ba kece kika haife shi ba har abada" kuka sosai Mami ke yi gabadaya hankalin ta nema ya ke ya bar jikin ta gaskiya ta na jin takaici ba'kin ciki da d'aci a duk lokacin da ta tuna cewa ba ita ce ta haifi Shareef ba amma a wannan karon ba za ta bari son zuciya ya hana ta fad'a masa gaskiya ba............... "Ki daina kuka haka mu za mu tafi sai Allah ya sake 'kaddara saduwar mu idan da rai a gaba" Baba Sadoh ya fad'a ya na mi'kewa ya kalli Daddy Amru kam ya na gefe yana sauraron su bai ce komai ba amma shi ma yana so ya ga d'an gidan 'kanwar ta sa ko sau d'aya ne a rayuwa........,... ZUCIYAR ALIYU CE NAJA'AT MUSA ABUBAKAR ✨ @YUSRAHMS PAGE 49 Bayan fitar su ma Mami ba ta iya yin shiru ta daina kukan ba musamman ta san indai Shareef shi ma ya fahimci ba ita ce ta haife shi ba sai shiga mummunan tashin hankali amma dai duk da haka ta na so a cire batun komai a fad'a masa ko da mene zai faru ita dai zata fad'a masa gaskiya kafin ya samu labari a gurin wa su hakan zai yafi 6ata masa rai akan idan su ne suka fad'a masa. Shareef kam bai samu damar dawowa gida ba sai jikin magriba a lokacin Mami ta na parlor jiran dawowar ta sa take yi sai kuma gashi ya yi sallama amsa masa ta yi tana 'karasowa bisa al'ada da d'abi'ar sa ya zo ya mata kiss ya na cewa "barka da yini Mami na fatan na same ki lafiya"? Ya fad'a yana zama a kusa da ita ya ri'ke hannun ta hawaye ne suke neman zubo mata ta yi saurin dannewa da'kyar ta ce. "Lafiya kalau Shareef ya wajen aikin na ku"?. "Lafiya Mami ai yau na sha wahala sosai a gajiye na dawo ga yunwa ma na ke ji bari naje na yi wanka da alwala idan na dawo daga masallaci sai naci abinci me aka dafa Mami"? Ya fad'a ya na mi'kewa 'kin d'agowa ta yi ta kalle shi saboda hawaye zasu iya fitowa daga idon ta tace. "Abin da ka ke so ne Rabi ta dafa maka". "Wow thank you Mami na gode da kulawa bari na je nayi wankan ina zuwa" wucewa ya yi yana hawa stairs d'agowa ta yi tana binsa da kallo kuka na neman 'kwace mata shi ya sa ta mi'ke ita ma ta tafi part d'in ta kafin ya fito ya same ta a haka ta ji yace a gajiye ya ke ga yunwa kar ya gan ta cikin matsala ya kasa cin abincin zata bari sai ya nutsu ta fad'a masa komai. Tun da ya fita bai dawo ba sai bayan sallar isha a lokacin Mami ita ma ta dawo parlon ta na jiran sa ya zo yaci abinci Daddy dama wani lokacin a nasa dinning d'in na part d'in sa can ake kai masa abinci ba kullum ya ke zama yaci a main parlor ba, su na zaune ta yi serving d'in sa yana ci ita kam ta kasa koda loma d'aya sai kallon Shareef kawai take ta na juya maganganun da za ta fad'a masa ba ta so ta gan shi a cikin damuwa amma ya zama dole a wannan karon ta fito masa da 6oyayyen sirrin da bai sani ba............ "Mami ya akai bakya cin abincin kina ta ri'ke da spoon"? Ta ji muryar ya katse mata tunani kai ta jinjina ta na cewa "ji nayi bana son ci". "Me ki ke so Mami fad'a min na siyo miki ko na tashi na dafa miki sabon abinci kar ki kwana haka"?. "A'a Shareef gabadaya yunwar ce ba na ji ba komai ba ne". "ba ki da lafiya"?. "Lafiya ta 'kalau". D'agowa ya yi yana kallon ta bisa tsautsayi idon su ya had'u da ta juna d'auke idon ta tayi da sauri tana kaiwa gefe daidai Daddy ya fito Shareef da ke kallon ta da mamaki ya ce "Mami lafiya na ga idon ki yayi ja kuma ya kumbura kamar wanda ki kai kuka"? Jin abinda yace yasa Daddy kallon ta ya ga ta sunkuyar da kai kuma ba ta yi magana ba zama ya yi a kujerar parlon ya na cewa. "Shareef zo nan" tashi daga dinning d'in ya yi yana zuwa gurin Daddy ya zauna a kusa da shi ita ma Mamin ta mi'ke jikin ta na rawa ta je in da suke hawaye Shareef ya ga suna zuba a fuskar ta wanda a rud'e ya mi'ke ya na ri'ko ta yace "Mami wai lafiya kuwa kukan me ki ke dan Allah ki yi shiru haka za ki d'aga min hankali na" ya fad'a yana goge mata hawayen kai Mami ke girgizawa ta na jin yadda ya saka ta a jikin sa cike da kulawa da so ta ya zata iya fad'a masa wannan maganar bata so ya shiga wani hali yanzu me ye madafa me ya kamata ta yi? samun kan ta tayi da fashewa da kuka tana cewa. "Dole na yi kuka Shareef dole na yi ba'kin ciki akan abin da ban san yadda zan kwatanta maka ka fahimta ba Shareef ina neman yafiyar ka Shareef ka yafe min dan Allah"? Ta fad'a tana had'e hannuwan ta cikin rashin fahimta ya ce. "Kamar me kenan Mami wani abu ne ya faru ni babu abin da ki kai min ki daina kukan nan dan Allah" kai ta girgiza sabin hawaye masu zafi da 'kuna su na sake kwararo mata tace "a'a Shareef zaman lafiyar mu da ga ni har kai shine kar ka so sanin abin da ya saka ni a cikin wannan damuwar domin kai ma za ka samun kan ka a irin haka". "Saboda me Mami damuwar ki damuwa ta ce fad'a min dan Allah kin ji"?. "Tabbas a wannan karon ma kuma damuwar ta wa damuwar ka ce kai abun ya fi shafa ma ban san ta yadda zan yi maka bayani ka fahimce ni ba a yau ina matu'kar jin kunyar ka Shareef". "Ni fa Mami ban gane ba dan Allah ki daina kukan haka ki fad'a min abin da ya faru"? Kai ta girgiza Daddy da ke zaune ya na kallon su ya ce "Shareef samu guri ka zauna ni zan yi maka bayani ka ji" jin a yadda Daddy ya yi maganar ya sa Shareef kallon sa ya ga shi ma damuwa ne tsantsa a fuskar sa to wai me ye haka ne amma dai koma menene ya faru ba abu ne me dad'i kuma me sauki ba.......... "Ka na ji d'azu bayan fitar ka mun shigo gidan nan tare da kakan ka da kuma yayan mahaifiyar ka" d'an shiru Daddy ya yi yana girgiza kai wanda a 6angaren Shareef ya kalli Daddy da mamaki yana cewa "wanne kakan nawa Daddy mahaifin ka ya rasu tun kafin a haife ni mahaifin Mami na taso na tarar shi ma kuma yanzu ya rasu to wanne kakan na wa ka ke fad'a"? 'kak'karfan ajiyar zuciya Daddy ya sauke yana cewa "kakan ka wanda ya haifi asalin mahaifiyar ka na ke nufi". "Mahaifiya ta kuma Daddy"? Ya fad'a cike da tsananin mamaki tare da juyawa 6angaren da Mami ta ke zaune ta na gurzar kuka ya ce "dama Mami ba ke ce ki ka haife ni ba ko me ban fahimta ba"? Kasa magana Mami ta yi saboda a wannan lokacin ba ta san me za ta ce masa ba ko ta ina za ta fara ba kukan da ta ke yi ba zai bar ta ta iya yi masa bayani ba Daddy da ya fahimci halin rud'un da ta shiga ya sa yace. "Shareef Mamin ka ba za ta iya yi maka magana ba a halin yanzu ni ne zan yi maka bayani ka saurare ni da kyau kuma ka fahimci abin da zan fad'a maka kamar yadda ka ke tambayar Mamin dama ba ita ce

Chapter 20 of 34