Share this page
kad'ai za'a bari tunda d'inkin ta yafi komai muhimmanci sai taci d'inkin ta zauna a tsakiyar uwa da uban kafad'arta tana gogan ta uwarta". "Hhhhhhhh" duk guri ya kaure da dariya suna nuna ta da yatsa d'aya a cikin matan gidan tace "zamu ga karshen 'karya ai za muga uban da zaizo yace yana sonta muna nan muna zuba ido muga d'an waye d'an sarki ne ko d'an gwamna ko kuma d'an waye"?. "Waye kuwa zai kawo kansa gurin ta a yadda take d'in nan ai saidai takai kanta gurinsa yanxu Kuna da tabbacin idan ta fita makaranta take zuwa"?. "Kuma fa haka ne wallahi watakil hotel take tafiya tana holewa da mazan banza shiyasa ma ta'ki aure ta tsaya yawon karuwanci a gari kai anyi asara girma ya fad'i". "Shawara ce zan baki ki daina wannan karuwancin kije ki samu miji ko d'an shaye-shaye ne ki aure shi domin dashi kika fi dacewa wanda zai je mashaya ya shawu ya dawo miki gida a buge ya kama ki yayi miki dukan mutuwa babu mai ceton ki". Subanallahi innalillahi wa inna ilaihi raji'un kowa dai da abinda yake cewa a gurin sun rufu akan Zainab suna ta fad'a mata ba'ka'ken maganganu marasa dad'i tsabar ba'kin ciki kuka kawai Zainab take wanda Umma ta tashi tabar gurin saboda ita ma kuka take kuma bazata so Zainab ta gani ba zata sake shiga wata damuwar ne babu yadda zasu yi komai da yake faruwa a gidan nan sun d'auke shi matsayin kaddara baza su gaji da yin ha'kuri ba domin shi ha'kuri baya 6aci Kuma abinda ha'kuri bai baka ba rashin ha'kuri bazai baka ba komai dad'ewa wata rana Zainab zatai aure zata bar gidan nan ta huta da masifar tsangwamar da ake mata........ AYI HA'KURI YAU ANAN ZAN TSAYA. 🗡️J.W.A🗡️ ZUCIYAR ALIYU CE @YUSRAH YMA PAGE 23 Gajiya Sameer yayi ganin bata fito ba yasa ya dawo gidan da kan sa 6angaren Hajiya ya shiga har lokacin bata daina mata masifa ba ga sauran mutanen gidan suma kowa yana fad'ar ba'kin fata da mugun alkaba'i daga ba'kin su tsaki yaja mai mugun 'karfi yana zuwa ya hankad'e Rasheedat dake tsaye tana dariya ya karasa gaban Hajiya wacce ta d'ago tana kallonsa fuskarsa a mugun had'e ko gaisar da ita baiyi ba ya ri'ko hannun Zainab yana mi'kar da ita tsaye yace. "Muje". Cikin fad'a Hajiya tace "Samar ka kiyaye ni wato rainin naka har yakai haka ko tsabar mugunta akan wannan yarinyar ka kama Bilki da duka kamar zaka kashe ta bari uban naka ya dawo zan had'aka dashi yayi maka gargad'i karka sake ta'ba ta da sunan duka idan kuma ka'ki wallahi nan gaba ka sake dukanta da kaina zanje na d'ebo maka 'yan sanda saina had'aka da hukuma damu daidaita a gidan nan gara na sa akai ka gidan gyaran hali" zuba mata ido yayi har ta gama fad'ar abinda zata fad'a tsabar takaici da ba'kin ciki baisan lokacin daya sakar mata wani uban tsaki ba ya juya fuuu yabar gurin domin Zainab kam yana d'agata da sauri tabar sashen Hajiyan tayi waje. Bin bayanta yayi amma bai sameta a wajen ba tambayar d'aya daga cikin samarin gidan da yake zaune a waje yayi yace ga inda tabi da sauri shima yafi inda ya nuna masa a zaune ya same akan wani itace ta kifa kanta akan cinyarta tana rusa kuka mai ciwo karasawa yayi yana cewa "Zainab" a firgice ta d'ago duk ta ji'ke nikaf d'in nata da hawaye ganin Sameer yasa ta sake sakin sabon kuka tsananin damuwar da indai batai wannan kukan ba baza ta samu sassauci ba bakinsa ya cika da iska ya furzar tare da dun'kule hannunsa ya kaiwa iska naushi cikin rashin sanin abun yi agogo ya kalla ganin lokaci ya dad'a ja yace "Zainab kiyi hakuri da halin da kika tsinci kanki ya kamata ki cinye wannan jarrabawar taki akwai haske a gaban ki kina tare da nasara na rantse da Allah nan gaba Zainab duk mahassadan ki na gidan sai sunyi kuka da idanun su fiye da wanda kikai kiyi ha'kuri ki goge hawayen ki kinji"? Kaita d'aga badan kukan ya isheta ba sai domin abinda ya fad'a mata kuma bata so ya ri'ka shiga damuwa dalilin ta shiyasa ta d'auko d'an towel daga cikin school bag d'inta ta goge hawayen sannan ta mi'ke tana kallon sa da idonta dayai jawur tace . "Na gode Yaya Sameer" murmushi yayi yana nuna mata hanya alamar su tafi gyara nikaf d'inta tayi ta mayar dashi yadda yake ta rufe fuskarta sannan suka wuce duk yadda yasan zaiyi yasa ta d'an samu farin ciki saida yayi kafin ya siya mata abinda zatai breakfast sannan ya kaita har makarantar ya bata dubu d'ayan da yake bata kullum d'aya dawo gida yana shigowa sa'kon Hajiya ya same shi tana neman sa kai tsaye yace bazai je ba daya gama abinda zaiyi ma yabar gidan yaje ya bud'e chemist d'insa ya zauna yasa a ransa ko me zatai saidai idan har nan d'in zata biyo shi ta fad'a masa abinda take son fad'a masa ko kuma ta bari idan ya gama hucewa da ita duk ranar daya shiga gaida ita saita fad'a masa. Koda dare da Abba ya dawo yasha mugun fad'a a gurin Hajiya kusan awa biyu ta saka shi a gaba sai bala'i take masa akan indai yana son zama lafiya a gidan nan ya aurar da Zainab ta daina ganinta idan ya'ki zata saka ayi shelarta a masallaci ta sakar da ita tunda bata da wata daraja wannan maganganun sunyi wa Abba mugun ciwo a ransa domin kafin ya taso daga gurin Hajiya har zazza'bi ya rufe shi daya shigo kasa yin wanka yayi sai d'akinsa daya bud'e ya shiga da yake ba girkin Umma bane a d'akin Asabe yake shiyasa ma Umman tana d'aki bata san ya dawo ba har saida Zainab ta shiga gurin sa zatai masa sannu da dawowa taga yana rawa d'ari ta d'auki bargo ta rufa masa da sauri ta fita taje ta fad'awa Sameer yazo ya duba shi tsabar yadda ransa ke 'kuna daya zubawa fuskar Zainab dake zaune kusa dashi ido sai hawaye ne kawai yaji yana zuba masa Allah yana gani yana mugun son yarinyar nan baya so yaji ana sukar ta Hajiya mahaifiyar sace babu yadda zaiyi da ita amma da ace wani ne yake fad'a masa wannan maganar banzar akan Zainab saidai kotu ta raba su koda zai rasa komai nasa daya mallaka sai ya d'auki mataki akan duk mai muzanta masa kamilalliyar 'yarsa tun yana kallonta yana hawaye har barci ya d'auke shi juyawa Zainab tai tana kallon sa jin saukar numfashinsa sai kuma taga yayi barci amma ga hawaye nan a idonsa zaro ido tai tana sake kare masa kallo duk da batasan akan me yake kukan ba da tasan saboda ita ne batasan wanne irin hali zata tsinci kanta ba da mayafin jikinta ta goge masa hawayen ta sake gyara masa pillow da yake kai sannan ta d'aura masa net zata fita taji ya saki wani irin numfashi da sauri ta juyo tana dawowa inda yake ta dur'kusa a saitin fuskarsa wasu hawayen taga suna zuba kuma gashi barci yake sake cire mayafin nata tayi tana shirin goge masa Asabe ta shigo cike da son sharri ta saki salati tana cewa. "Laha'ilah ha'illallahu kashe shi za ki yi? Lahhh innalillahi na kama mashe'kiya tazo za ta danne masa kai da filo ya mutu ashe dama son kashe shi ki ke yi"? Ta fad'a tana tafa hannu mi'kewa Zainab tai batare da tayi mata magana ba tana shirin fita sha'keta Asabe tayi tana cewa "wallahi bazan barki ki fita ba sai kin fad'a min kashe shi zakiyi ko kuma uwar taki ce ta turo ki yi masa wani abu na asiri"? Nan ma shiru Zainab tayi batai magana ba Asabe dake ri'ke da kwalar rigarta taci gaba "idan ma kashe shin kike shirin yi dan ki samu gado shi dai fa'kiri ne kuma talaka babu abinda zaki samu idan ya mutu ma saidai sauran kayan miyar da yake siyarwa da gawayi da kwandunan da yake saro kayan miyar su kike bu'kata"? Ganin har lokacin kamar Zainab d'in bata mayar da ita mutum ba yasa cike da takaici Asabe ta turo ta waje tana cewa. "Asirin ki ya tonu Hauwa da kika aiko ta kashe shi ma na kamata ta saka tsumma ta danne masa hanci sai wutsul-wutsul yake da 'kafa Allah ya shigar dani d'akin wato kashe shi kuke son yi dad'in abun ma ba wata uwar ya tara balle ku samu gadon zilamammu kawai" ta karasa maganar tana hararar kofar d'akin Umma daidai ta fito bata kalli Asabe ba sai Zainab dake tsaye ta kalla tana cewa. "Zainab ki shiga d'aki ki kwanta dare yayi" to Zainab tace tana juyawa ta shiga d'aki kamar yadda Umma ta umarce ta itama Umman juyawa tai ta koma nata d'akin suka bar Asabe a tsakar gida sai faman surfa masifa take tana d'aga murya wai Zainab ta shiga d'aki ta dannewa Abban su kai zata kashe shi saboda su samu gado. ZUCIYAR ALIYU ZAINAB CE😍. •••••••••••••••••••••••••••••••••••••••••• J•W•A ______________Y ____________________M ___________________________A ♥♥YUSRAH♥♥ Chat with me. +234 816 098 3083 @Y♠M♠A DUTSE PAGE 24 Washe gari da Abba ya tashi zazza'bin ba sosai ya sake shi ba shiyasa ma bai tafi gurin sana'ar sa ba daya d'an daddafa bango yaje ya gaida Hajiya ya bata d'an wani abu saiya dawo yasa Asabe ta fito masa da tabarma waje ya kwanta a barandar kofar d'akinsa yana kwance Sameer ya shigo gai dashi ya siyo masa kayan karyawa daga waje ya d'aga shi da kansa ya zauna ya bashi sannan ya sake duba shi Zainab ma ta fito tayi masa sannu zata tashi yace ta kira masa Umman ta sannan Asabe ma yai kiranta ya kira Bilki duk suka taru a gabansa kallon su ya fara yi d'aya bayan d'aya har yakai kan Zainab sannan ya tsaya yayi shiru ita kam kanta yana kasa batasan yana kallonta ba saida taji yace. "Zainab". D'agowa tayi tana kallon sa cikin nutsuwa tace "na'am Abba". "Meya had'a ki da Bilkisu jiya bayan fita ta daga gida"? Duk gurin babu wanda ya kawo akan abinda ya tara su kenan domin Asabe ita tayi tunanin ko wasiyya ma zaiyi musu🙊 sai kuma taji batu sa6anin wanda take zato d'an shiru Zainab tayi domin bata so a sake tada maganar har abada badan yanzun da yake son sanin dalili ba muryarta a hankali ta soma magana. "Baba jiya da safe bayan na tashi ina sauri zan tafi makaranta shine na kunna wuta a mangal zan dafa indomie naci kafin na tafi na shiga d'aki kafin na fito Bilki ta d'ora tukunya da ruwa a ciki shine na tambaye ita ta d'ora tace min eh ni kuma a lokacin sauri nake yi domin zan iya makara shiyasa na sauke tata tukunyar na d'ora na dafa indomie kafin na d'auko plate na juye tazo tayi bol da tukunyar indomie ta zube Kuma ni bance mata komai ba ta fara zagi na har Yaya Sameer yaji yana d'akin sa shine ya fito ya dake ta wannan shine abinda ya faru" tana rufe baki Asabe tace. "Sannu munafika wato karyar da kika shirya kenan bayan kin mammari Bilki kalli fa yadda bakin ta ya kumbura saboda dake idanuwanta duk sun kumbura suma amma saboda babu Allah a ranki sai kinyi mata sharri"? Shiru Zainab tayi batai magana ba sai Abba daya kalli Sameer yana cewa. "Kai meyasa ka dake ta bayan baka san komai ba"? Gyara zama Sameer yayi yana cewa "Abba ina daga d'aki ina jin irin zagi da cin mutuncin da takewa Zainab bayan itace mara gaskiya raina ne ya 6aci shiyasa ina fitowa na mare ta hakan ma da naji ban huce ba na sake dukanta" kai Abba ya jinjina yana mayar da hankalinsa kan Bilki wacce kamarta ta canza tsabar dukan da Sameer yayi mata jiya yace. "Ina jinki ke meyasa ita ce ta fara hura wutar amma kika zo kika d'ora tukunya kuma kika zubar mata da abinci meyasa"? Shiru Bilki tai tunda tasan ita ce marasa gaskiya ko ina aka je ganin batai magana ba yasa Asabe cewa "ke dan ubaki ba magana ake miki ba banza kina ji kowa yana fad'ar 'karya dan ya kare kansa amma dan sakarci kinyi shiru wato kin kar6i laifin da ba naki ba kenan"? Ta karasa maganar a masife yayin da har lokacin Bilki batai ko tari ba takaici ne ya rufe Asabe tana shirin magana Abba yace "duk yadda akai kece baki da gaskiya a wannan lamari dan haka ki baiwa 'yar uwarki ha'kuri yanzun nan kafin ranki ya 6aci" tun kafin Bilki tayi magana Asabe tace. "Wannan wanne irin abu ne taya za'a dake ta sannan yanzu ace ita ce mai bada ha'kuri wato itace mai laifin kenan a cikin su gaskiya bazai yuwu ba" batare da Abba ya kallo inda take ba yana kallon fuskar Bilki da tayi kasa dakai yace "ban sako dake ba da 'ya'ya na nake magana ta". "Kuma tsakani da Allah shikenan bazan fad'i gaskiya ba saina bari ina kallo bayan cutar ta da akai azo a tilasta mata bada ha'kuri" fuskarsa Abba a had'e yace "Bilkisu baki ji abinda nace ba zaki bata ha'kurin ne ko nima saina dad'a marinki akan wanda Sameer d'in yayi miki" yana rufe baki da sauri Bilki tace "kiyi ha'kuri". "A'a ba irin wannan ha'kurin nake so ki bata ba ban gamsu ba a tsaye kikai maganar babu ladabi balle kwantar da harshe tana matsayin yayarki so nake ki fad'a yadda xan ji raina ya yarda" shiru Bilki tayi tana kallon kasa ta'ki magana alamar bazata bada ha'kurin yadda yace ba. "Bilkisu". Taji Abba ya kira sunanta kasa d'agowa tayi ta fuskance shi balle kwarjininsa yasa ta bata ha'kuri domin a yadda take ji yanzu a ranta ko kisa ne zata iya kashe Zainab ba tare data damu ba......... "Bilkisu". Ya kira sunanta a karo na biyu da'kyar tace "na'am" babu ma wanda ya jita domin a ciki ta amsa marin da Sameer ya sakar mata yasa ta fasa 'kara da gudu ta tashi daga kusa dashi tana kuka nuna yake da yatsa yana huci zaiyi magana Asabe tace "kai jama'a ni kam na shiga uku a gidan nan gaskiya wallahi kai dai Sameer kayi asara anyi mugun mutum anan kana 6ata min rai da wannan dabi'un na ka wacce irin masifa ce wannan jiya kayi mata duka bata gama warkewa ba yau ma kazo ka mareta to ka daki Allah ya isa" ta karasa maganar tana zafga masa wata uwar harara ji take kamar ta tashi ta rufe shi da duka ko ta huce wannan takaicin da yake d'ura mata Sameer kam bai kula zancen da Asabe take ba tsabar yadda ransa yake tafasa sai kallon Bilki dake gefe tana kuka yayi yana cewa. "Zaki dawo nan ki zauna ne ko saina tashi naci ubanki" da sauri ta dawo ta zauna a kusa da Asabe cike da tsoro tana matsar hawaye. "Wallahi sai kin gane kuren ki zan kama kine" ya sake fad'a yana cije lips tsaki Asabe tayi tana cewa "kayi asara dai Sameer wallahi a rayuwarka kaji kunya tunda ka d'auki 'yar uba ka bar 'yar uwarka kayi babbar asara ma wacce babu ribaa cikin ta ita wacce kake yi dominta ai ba gani take ba kuma ni na fad'a maka wata rana saita guje ka da zarar ta samu wata ni'ima zata manta dakai ya zama daga ita sai uwarta kaine sakarai shashasha ta mayar dakai mahaukaci shiyasa ka kasa ganewa amma ban sani ba ko kaima asirin tayi maka shiyasa idonka ya rufe ka koma 6angaren ta dan nasan duk rintsi babu inda ake samun 'yan uban suna irin wannan kyakkyawar mu'amalar da kuke yi dole akwai wani 6oyayyan abu kuma saina bincika ko menene idan na gano ba haka kawai suka barka ba wallahi hukuma ce zata raba ni dasu............ "Asabe ya isa haka" Abba ya fad'a fad'a ransa a 6ace ganin yadda ta mayar dasu biyo ta nan ta bud'e baki sai magana take kowa yana sauraron ta gashi sun tura mata aniyarta ta inda yake son Umma ke nan koda Asabe zata rufe ta da duka indai yace karta kulata tofa baza ta biye mata ba amma ya tabbata idan Asaben ce a matsayin Umma baza yarda ta ri'ka mata irin wannan wula'kancin tayi shiru ba. "Kayi ha'kuri Abba a manta da komai laifi duka na Bilkisu ne ba kowa ba domin duk inda za'a je itace mara gaskiya" Sameer yana rufe baki Asabe tace "inji uwar ka munafiki waya sako dakai a gidan uban wa kasan laifin Bilki ne"? Shiru Sameer yayi domin koma mene ne ita mahaifiyar sa ce dole yayi taka tsantsan karya kauce hanya duk abinda ake yi Abba yana lura da Bilki hankalinsa yana kanta yana kallon yadda take murgud'awa Sameer baki tana maganganu 'kasa-'kasa saita d'ago ta harari Zainab ta ta'be baki kai ya jinjina yana kallon ta da mamakin raini irin nata baisan yaushe ta koyi fitsara ba yasan dai da ba haka take ba ya akai ta canza rayuwarta kodai rashin zaman da yake a gida shine ya kawo hakan ajiyar zuciya ya sauke yana cewa. "Bilkisu ki bata ha'kurin abinda kikai mata jiya kafin ranki ya 6aci a gidan nan" ya fad'a yana kallon ta ita kuma Sameer ta kalla ganin yadda ya had'e rai yana watso mata mugun kallo yasa tace "kiyi ha'kuri" Kai Zainab ta girgiza tana cewa "babu komai ya wuce". "Shikenan Allah ya rufa asiri Bilkisu Zainab yar uwarki ce kuma yayarki ce jinin ku d'aya bana son wannan zaman takun sa'kar da kuke yi daga yau karna sake jin wani tashin hankali ya faru a tsakanin ku zaku iya tafiya" godiya sukai masa suka mi'ke kowa ya bar gurin har Zainab ta shiga d'akinta sai kuma ta sake fitowa ta dawo inda yake tace. "Baba kana bu'katar wani abu ne ka karya"? Murmushi yayi tun kafin yayi magana suka ji muryar Asabe tace "to munafika ai ba a d'akin uwar taki yake ba da zaki zo kina tambayar sa ya karya ko bai karya ba idan bai karya d'in ba wata uwar zaki kawo masa" shiru Zainab tai bata kalli inda Asabe take ba sai tashi da tayi ta koma d'aki ta d'auko hijab d'inta da nikaf ta saka ta fita. Asabe kuma kitchen ta shiga ta dama masa kunu ta fito tana cewa "kai da baka da lafiya haka zaka sha kunun ba sugar idan mu lafiyar mu kalau kai fa"? Ta karasa maganar tana karasowa ta aje kofin a gefensa tace "gashi nan" tun bata mi'ke ba yace. "D'auke bazan sha ba na 'koshi" kai Asabe ta d'aga tana kallonsa daga baya ta mi'ke tana cewa "saboda nayi fad'a akan gaskiya ta shine zakai fushi dani"? Shiru yayi mata kamar bai ji ba taci gaba "tabd'ijan lallai akwai 'kura a gidan nan akwai ba'kar guguwa an shanye min d'a sannan mijin ma baza a barni naji dad'in sa ba wallahi duk wanda yaje yayi min 'kulunboto yazo ya baiwa Abdullahi yasha ya tsane ni Allah ya isa tsakani na dashi" tana rufe baki yace. "Ba wanda ya shiga tsakanin mu halin ki ne ya haifar miki da wannan matsalar domin halin mutum shine sabulun wankan sa kar kiyi zargin kowa ki zargi kanki". "Ba wani hali nane ya jawo min kawai dai kace rashin adalcin naka daka saba min shi zakai na gaji gaskiya na gaji amma ba komai muje zuwa zan d'auki matsakin daya dace da kowanne tunda har anyi min shedar rashin arziki idan na fito muku da kalata zamu fi daidaitawa" tana fad'in haka ta d'auke kofin kunun data aje masa ta juya d'akin ta dashi tana tafe tana balbalin fad'a da kallo Abba ya bita tare da dafe kai ya girgiza kad'an ya sauke numfashi ya rasa da me zaiji idan yaje gurin Hajiya ta balbale shi saboda shi talaka ne ba'a cin dad'i a kofar sa sauran suna kai mata nama da kaji sannan abincin su yafi na kofarsa had'uwa tunda su suna d'aukar albashi idan ya shigo kofarsa domin ya huta nan ma Asabe ta tada tata masifar ta hana shi jin dad'i indai kaga yana zumud'in dawowa gida da wuri tofa saidai idan ranar a d'akin Umma yake shine kawai zai ci abinci cikin salama ana hira da dariya yayi barci cikin farin ciki ya tashi da annashuwa amma ba dai Asabe ba yana nan a kwance Zainab ta dawo ta shiga d'aki ta cire hijab d'inta ta fito da klin a hannunta tana zuwa ta wuce d'akinsa ta d'ebo kayansa masu datti ta kai gurin da ake wanki ta saka kujera ta zauna yana kallonta ta wanke masa kayansa tas ta shanya sannan ta wanke kafarta ta tashi ta d'an d'ora ruwa yayi d'umi tayi wanka ta shirya ta hau kan keke ta fara d'inki kafin wani lokaci tunda ba girki Umma bane balle tace zata kama mata yan wasu ayyukan. ZUCIYAR ALIYU CE. ♪♦Fatima Zarah Shamsuddeen ♪♦Ramlat Ikram Ibrahim Lele @YMA DUTSE PAGE 25 Nihal tana tsaye a jikin motar su driver yana ciki a zaune hangen ta inda zata ga Zarah ta 6ullo take yi amma babu alamarta gashi ta barsu suna jiranta kamar wanda tayi shanya d'an tsaki taja tana sake kallon kofar shiga school amma dai labarin d'aya ne ajiyar zuciya ta sauke tana juyawa ta bud'e mota ta aje takardun hannunta da handbag d'inta sannan tacewa driver. "Dan jira na shiga na duba inda tayi kamar fa ciki naga ta koma" kai ya d'aga yana cewa "ok madam ba damuwa" wucewa tayi tana shiga cikin school d'in ita kad'ai sai magana take "wanne irin iskanci ne a gurin Zarah yarinya rashin ji yayi mata yawa kullum sai ana jiranta kamar wata uwar mutane"? Ganin datai har 6anfmgaren da take karatun taje bata nan yasa ta dawo tana cewa. "Wai bata dawo ba"? Kai driver ya d'aga yana cewa "ban ganta ba bari na fito mu gani" d'an tsaki Nihal tayi tana kallon lokacin da driver shima ya tafi yana d'an hahhangawa ko zai ganta ita ma wani gurin ta sake shiga ta duba ta nan ma babu ita fitowa tayi a lokacin Shareef yayi parking da motarsa zai shiga gurin ya ganta farko yayi tunanin tare da yayanta Ammar take sai kuma yaga ita kad'ai ce yana so zaiyi magana mai muhimmanci da yarinyar nan amma sai ya fara samun Ammar d'in tukuna yana daga cikin mota yana kallonta kuma yaga yadda take waige-waige alamar akwai abinda take nema kamar zai fita yaje inda take sai kuma ya fasa yaci gaba da zama a cikin motar. Baby da Badiyah su na tsaye a gurin da Nihal ta shiga su kuma za su fito da alamar abu suka siyo hannun su ri'ke da ledoji ta'be baki Badiyah tayi tana kallon inda Nihal take tace "kinga irin 'yan 'karyan nan haushi suke bani kiga dai wancan budurwar yadda ta saka glass saboda iyayi sai wani sham 'kamshi take sai kace 'yar gwamna kuma maybe idan kika bibiya 'yar talakawa ce aron kayan take yi dan tazo ta burge samari" juyawa Baby tai tana cewa "a Ina kika ganta"? Da hannu ta nuna inda Nihal ke tsaye zaro ido waje Baby tai tana cewa "wancan ai yarinyar da Shareef yayi fushi dani a kanta ne". "Waye Shareef kuma"?. "Wani guy ne a hospital d'in mu yake masifar jin kansa tayi yawa a kanta nake ta faman binsa Ina bashi a ha'kuri amma ya'ki ya saurare ni bari naje naci uwarta kona huce takaici na" ta fad'a tana shirin fara tafiya da sauri Badiyah ta ri'ke ta tana girgiza mata kai tace "a'a kada kiyi haka bana son abun jawo rigima wannan ba girman ki bane" fisgewa tayi tana cewa "ke wallahi sai naje naci ubanta maybe idan nayi haka ta kiyaye ni a gaba". Nihal kam bata lura da su Baby ba hankalinta yana kan Zarah data fito tare da wata 'kawarta taga ice-cream suke je siya ba komai ba suna karasowa ta soma mata fad'a "haba Zarah me kike yi haka kinsa hankali na ya tashi dama nan kika taho siyan ice-cream kuma maimakon ki fad'a min kika barni

Chapter 10 of 34