dama ba ke ya siyawa ba amma yace na kawo miki"?.
"gashi nan kuma ya fad'a ni kam ai na kai masa kuma na ha'kura ko siyowa ya yi ya taho min da shi ba zan kar6a ba" dariya Amirah tai ta na cewa "ki ce na fara shiri idan ya baki bakya so zan zo masa sannu da zuwa sai na kar6a".
"Sai dai ke d'in amma ni kam ina da zuciya" sabuwar dariya Amirah ta sake yi tana cewa "ahh mu kam bamu da zuciya musamman a gurin mutane irin Aliyu" kai Afifah ta jinjina tana cewa "ai kuwa kin had'a kan ki da aiki duk wanda zaki nuna masa kome ya yi miki daidai ne zaki kwashi takaici da ba'kin ciki a gurin sa musamman lokacin da ku ka samu sa6ani yana sane zai ri'ka yin abinda ran ki baya so saboda kawai ya ba'kanta miki".
"Ke Afifah wa ya fad'a miki mutane irin su Aliyu su na haka ai duk wanda ki ka ga yana wula'kanta d'an Adam bai san darajar kan sa bane amma in dai mutum ya na da hankali bazai tozarta d'an uwansa musulmi ba".
"Haka ne kin yi gaskiya ke ma kin zo da magana a nan sai anjima".
"Ok zuwa dare maybe zan sake kiran ki".
"Ba matsala" Afifah ta fad'a tana sau'ke wayar ta kalli Momy tana cewa "ki ji Amirah da wata magana dan Allah haka kawai zan li'ke a abinda ba'a saka da ni ba bazan iya irin wannan rayuwar ba ko kowa bai ganin kima ta ni zan yi 'ko'kari na kare kimar tawa domin duk daren dad'ewa za'a samu wanda zai ga kimar tawa kuma ya martaba ni" murmushi Momy tai tana jin ta bata ce komai ba.
Sameer kam duk wunin yau yana chemist tunda ya bud'e bai samu ya koma gida ba sai dare daya rufe chemist d'in ya tafi gida Zainab ta riga ta yi barci shiyasa ya bar agogon sai da gari ya waye kafin ta tafi school tana zaune a 'kofar d'akin ta akan sallaya tana karyawa da indomie ya zo gurin yana tsugunawa a gaban ta d'agowa tai tana kallon sa tace.
"Ina kwana Yaya Sameer"? Kai ya d'aga mata yana d'aukar fork d'in da ya gani a aje akan indomie domin ita da hannu ta ke ci loma biyu yayi ya aje fork d'in yana cewa "da me kika dafa"?.
"Ba komai indomie ce kad'ai sai Maggi da albasa da attaruhu".
"Ok ta yi dad'i kuwa" ya fad'a yana bud'e ledar ya fito da agogon yana bata yace "ri'ke kar6i wannan" da mamaki Zainab ta ce "wannan agogon kuma fa daga ina"? Kai tsaye ya bata amsa.
'Ke ma kin san waye zai ba ki aboki na ne man" jin abinda yace yasa taji numfashin data sha'ka ya tsaya mata a 'kirji 'kure agogon tayi da kallo kafin ta d'ago ta kalli Sameer wanda yace "yayi kyau ko sai kisha kwalliya da abun ki" yana fad'in haka ya mi'ke zai fita da sauri tace.
"Yaya Sameer" dakatawa ya yi yana cewa.
"Umhum ya a kai"? A rud'e tace "wai dan Allah waye wannan abokin na ka"? Jin abinda tace yasa ya juyo yana kallon ta gabadaya tashin hankali yaci karo dashi akan fuskarta wanda bazai iya gane yanayin da take ciki ko ya kwantanta ba...
"Ina jin ka Yaya Sameer ka fad'a min" kai ya jinjina yana cewa "ok karki damu zan fad'a miki amma ba yau ba dan Allah Zainab ki nutsu da aboki na ki tsaya da zuciyar ki guri d'aya shine masoyin ki na hakika mai kaunar ki ta gaskiya wanda yake burin ki zama uwar 'ya'yan sa ya kamata ki gane hakan ki daina tambaya a kan sa da sannu zai zo miki ki na zaune" hawaye ne shar shar taji yana zuba mata ta soma girgiza kai tana kallon sa ta kasa magana da sauri ta mi'ke ta wuce d'aki gudun kar wani ya shigo ya ganta tsaye Sameer ya yi a wajen kamar zai le'ka d'akin ya yi mata magana sai kuma ya fasa ya fita.
Zainab kam ka sa jurewa ta yi sai da ta yi kuka me isarta sosai sannan ta fito ta wanke idon ta indomie d'in da bata karasa ci ba ta ha'kura ta shirya ta d'auki jakarta tai wa Umma sallama ta fita gudun kar ta shiga gurin Hajiya ta sake saka mata wata sabuwar damuwar wacce gara ta yanzun da ta ke ciki hakan yasa ta fice ta je ta kar6i dubu d'aya kamar yadda ta saba a gurin Sameer ta tafi shi kan shi yasan tana ciki damuwa domin ko iya godiya ba ta masa ba kawai yana bata ta juya ta fita a wajen chemist d'in Napep d'in daya aje wasu mata biyu shi ta tsayar ta shiga su ka tafi.
K'arfe biyar da rabi aka tashi ganin lokaci bai 'kure mata ba kuma har zata iya zuwa gidan Aunty Murjah ta kar6o d'inkin su gashi ya fi kusa daga school d'in nasu akan ta ce sai ta dawo gida kawai da ta fito daga ciki ta tare me Napep ta ce ya kaita gadon 'kaya ta yi sa'a kuwa lokacin dawowar Aunty Murjah kenan daga anguwa ta sauka a Napep ita ma ta sauka da mamaki Aunty Murjah tace.
"Tofa Hajiyar kulle yau kece a gidan nawa ashe yau za'ai ruwan sama" d'an murmushi Zainab ta yi tana kallon Aunty Murjah wacce ta juya tana bud'e musu kofar gidan suka shiga a parlor Zainab ta zauna ita kuma ta wuce ciki ta rage kayan jikin ta sannan ta fito.
"Ina Yaya Auwal d'in ko baya nan"? Kai Aunty Murjah ta d'aga tana cewa "yana Abuja yau kwanan sa hud'u sun tafi shi da wani abokin sa Mukhtar wanda ki ka ta'ba zuwa gidan nan ya gan ki yace yana son ki kika 'ki" d'an jinjina kai Zainab ta yi tana cewa.
"To tsakani da Allah Aunty Murjah ina zan kai wannan buhun mutumin nan haba dan Allah kina ganin sa wani shirgege da shi" dariya Aunty Murjah tai tana juyowa ta kalli Zainab tace.
"Oh kice saboda 'kibar sa ki ka 'ki amince masa ai kuwa da ya sani sai ya sha maganin slimming ya zafge kodan ke saboda yana matu'kar son ki dan dai kin 'ki ne da yanzu idan yara ne ma kina da d'aya ko biyu" tana rufe baki ta sauke ajiyar zuciya mai 'karfi har saida Aunty Murjah ta kalle ta tana dariya tace.
"Ya dai"?.
"Please dan Allah Aunty Murjah ki daina fada kar ki sa na daina zuwa gidan ki Allah dama yanzun ma dan nasan lokacin da bazan samu Yaya Auwal a gida bane balle ace shi wancan Mukhtar d'in ya zo ya gan ni".
"Humm shikenan zan bari sai sun dawo na ce kizo ki wuni min sai ku had'u Allah ina so ki auri Mukhtar ko dan ki taho kusa da ni kin ga gidan sa daya kammala ginawa anan zai zauna iyayen shi suna Sharad'a".
"Hum'um ni fa ko tare da su zai zauna ba ruwa na wallahi haka kawai wannan gayen baya burge ni" dariya sosai Aunty Murjah ke yi tana kallon ta cikin tsokana tace "kai Zainab duk wankan da ya ke d'auka"?.
"Yo ni tun da ba yimin yayi ba ai ko kyan sa bana gani balle kuma na tsaya kallon wanne kalar wanka yake d'auka".
"To kin ga indai haka ne ki bari sai ranar weekend ba ki zo min ki wuni shima zan fad'awa Daddyn Ikram ya fad'a masa sai ya zo ku gaisa".
"Da wa zai gaisa amma ba da ni ba"?.
"Da ke man ji wani iskanci zan ce ya zo ya gaisa da ni ne".
"Ai kuwa in dai da nine zai dad'e bai gaisa ba balle ma ni bana samun lokaci a weekend kullum ina d'inki ne ko had'a baseline da shampoo shiyasa ma ba zan iya zuwa ko'ina ba" da hannu Aunty Murjah tai mata jinjina tana cewa "uhm kina lokaci Hajiya Zeey yayi kyau masu sana'a goma maganin me gasa yanzu ya ake ciki ko dama zuwa ki kai mu gaisa ko kuma tun da Sweet baya nan ki tsaya ki kwana ko"? Kai Zainab ta girgiza tana cewa.
"So ki ke yau a saka ni a lasifika kenan ana cewa na tafi gurin saurayi na kwana ko"?.
"Kamar ya wanne irin saurayi kuma"?.
"Aunty Murjah ke ma kin sani ai tun da ki kai aure ki ka bar gidan nan Hajiya ta sako ni a gaba maganar yau daban ta gobe daban wai na'ki aure kamar yadda ke ma saida aka sha fama a kanki ta rasa wanne irin hali ne damu mun gado uwar mu ke fa maganganu marasa dad'in ji ni wani abun ma bazan iya maimaitawa ba saboda takaicin sa".
"Subanallahi Hajiyan ce take fad'ar hakan"?.
"Hajiyan to tsaya ki ji me kankat abun da zai baki ba'kin ciki yau kwana uku anyi tuwon shinkafa da dare ni kuma bana so sai na fita na je Yaya Sameer ya raka ni bayan layin mu gurin Maman Sabeer me awarar nan kin san ta ai"? Kai Aunty Murjah ta d'aga tana cewa "tabbas na san wannan matar tun mu na yara take awarar saidawa har yanzu bata daina ba ke nan"?.
"Eh bata daina ba tana yi tofa gurin ta ya raka ni wajen 'karfe tara zan siyo awara ashe wai Haulat ta gan ni ita kuma saukar ta kenan daga Napep babu wanda yasan inda ta je tun safe har dare amma da yake ita 'yar gaban goshin Hajiya ce ba wanda ya kula ta sai ni tana sauka ta tafi ta cewa Hajiya wai ta ganni tare da wani saurayi na yi bayan layi kuma gajeren wando ne a jikin sa hankalin Hajiya a tashe harda gayyato su Yaya Zaid wai ya taho ya daki 'kwarto kawai sai ji nayi Yaya Sameer yana cewa meya fito da Hajiya yanzu Ina kallo gurin su na gan su gayyar su guda muka had'u ta ri'ka fad'a min magana shi ma Yaya Zaid haka har da fad'a su kai da zage-zage a gurin shi da Yaya Sameer ya ri'ka kira na da 'yar iska wa zai aure ni shi dai Allah ya rufa asiri ya zauna da ni hum abun dai babu dad'i 6atacciya aka yi ranar".
Aunty Murjah dake dafe da kunci kai kawai take girgizawa har Zainab ta yi shiru sannan tace "kai Subanallahi innalillahi wa inna ilaihi raji'un wacce irin masifa ce wannan shi Zaid d'in uban wa yace ya aure ki har zai ri'ka fad'a ba'kar magana"?.
"Waye kuwa bayan Hajiya wai haka kawai ta kama lissafin samarin gidan da 'yan mata akan kowanne ya auri d'an wani 'kofar kuma duk ciki ba wanda ya amince domin kin san Allah Aunty Murjah da na auri Yaya Zaid tunda bai san daraja ta ba gara na auri wannan abokin Yaya Auwal d'in nasan zai ri'ke ni da mutunci tun da yana so na".
"Gaskiya ne Zainab amma ban ji dad'in wannan abun ba Allah ya rufa asiri da yake na dad'e ban je gida ba shiyasa ban san abinda ya ke faruwa ba sai yanzu amma in sha Allahu Sweet yana dawowa zan tambaye shi na je na kwana d'aya na taho Allah ya sa ya barni na kwana".
"Amin idan bai bari ba sai ki wuni".
"A'a ki yi min addu'a ma ya barni dan na fi son kwanan" mi'kewa Zainab tai tana cewa "to Allah yasa ya barki d'in bari na tashi na tafi domin ba zama nazo ba gashi har an kira sallah".
"To me ye a ciki sai ki tsaya kiyi sallar kya tafi ni sai na kai ki a motar Sweet ma da kaina dan kar su tuhume ki".
"A'a wallahi kar ki wahalar da kan ki d'inki Ikram kawai zaki d'auko min na tafi da ki ka ce kuna da bikin 'kanin mijin ki shi na zo kar6a".
"Ok kin san me ya faru ma? Ashe da ya siya mana atamfar sai ya kai shagon d'inki wani telan 'kanwar sa ne zai d'inka mana amma dama ina da wata atamfa da nake so ki d'inka min ni da Ikram d'in bari na d'auko miki ita kawai ki tafi da ita" ta fad'a tana mi'kewa ta shiga bedroom ta d'auko mata ta saka a cikin leda ta kawo kar'ba Zainab tai tana cewa.
"Ni ina Ikram d'in ne ban gan ta ba"?.
"Tana gidan kakarta tun jiya da Salimat ta zo suka tafi harda uniform d'in ta maybe sai ranar Monday idan an kaita school daga can ta taho".
"To shikenan Aunty Murjah ni kam na tafi sai na gan ki".
"Wai dan Allah Zainab ba za ki tsaya na dafa abinci ki ci ba ko taliya ce gashi harda kifi na siyo zan yi miya dan Allah ki dawo ciki saurin me ki ke ne"?.
"Hum Aunty Murjah 'kyale ni na tafi na tabbata yanzu haka ma jiran komawa ta ake tun da bana kaiwa sama da shida a makaranta yanzu kuwa gashi bakwai ta kusa" ta fad'a tana bud'e kofar parlon ta fita suka nufi 'kofar waje nan ma ta bud'e ta mata sallama ta fita................................
ZUCIYAR ALIYU CE
STORY WRITTEN ND EDITING
YUSRAH MUSA ABUBAKAR.
@YMA DUTSE JIGAWA
PAGE 35
Lokacin da ta fito daga gidan Aunty Murjah ganin lokaci ya ja yasa ta tare Napep tun daga layin suka fito ya kai ta gida d'akin ta ta fara shiga ta aje jakarta da atamfar da ta kar6o ta fita ta yo alwala ta dawo d'aki ta yi sallar magriba tana idarwa ta ji an kira isha tashi ta yi taci gaba saida tai sallama ta yi addu'a ta shafa sannan ta tashi ta fita a waje ta ga Umma ta fito da kwanuka daga d'aki ta kai gurin wanke-wanke da mamaki Umma ta ke kallon ta tace.
"Yaushe ki ka shigo"?.
"Ban dad'e ba na je gidan Aunty Murjah ne bayan an tashi daga school na je hana ni tahowa ta yi wai sai na kwana a can nace mata a'a saboda ina da ayyuka a gida kuma ko ba haka ba ma kin ga ban fad'a a gida ba".
"Eh gara da baki kwana ba gaskiya da a kaina abun zai 'kare Hajiya tana ji zata ce ba gidan Aunty Murjah ki ka je ba wani gurin ne daban".
"Humm shi ya sa ai ban zauna d'in ba ita ma tace min zata samu lokaci ta zo ta gaishe ku ta dad'e ba ta zo ba".
"Gaskiya ta dad'e kam Allah ya kawo ta lafiya ya su Ikram da Aiman d'in".
"Duk basa gidan ita Ikram tana gidan kakar ta shi kuma ban ganshi a gidan ba kuma ban tambayi in da yake ba".
"Shikenan to ki zo ki ci abinci" Umma ta fad'a tana shiga d'aki bin bayan ta Zainab tai tana cewa "me aka dafa"? Zama a bakin gado Umma tai tana cewa "gashi nan a cikin cooler jallof d'in shinkafa ce" bud'ewa Zainab tai tana d'agowa ta kalle ta tana cewa "amma dai ba ke ce kika dafa ba"?.
"Uhm ba ni bace Asabe ce ni sai jibi zan kar6i girkin ai tunda kwana uku-uku ne" maida murfin Zainab ta yi ta rufe tana cewa "ni ba ci zan yi ba".
"Kin ci kenan a gidan Murjanatun"?.
"A'a ko ruwa ban sha ba ni sai da ki ka fad'i haka ma na tuna ban bud'e fridge d'in ta ba maybe ta yi kalolin zobo da juice iri-iri na taho da shi kuma har kayan had'e-had'en na gani ta shigo da su".
"Ba rabon ki sai kin sake komawa".
"Ni kam ba zan koma a kwana kusa ba".
"Me ya sa"? 'yar dariya Zainab ta yi tana girgiza kai ta'ki cewa komai saboda kar tace saboda abokin mijin Aunty Murjah ne Umma ta yi mata fad'a ita ma Umman daga haka ba ta sake magana ba har wani lokaci tunani ma take a ran ta taje ta samu Sameer ya siyo mata wani abu a waje amma tsoron abin da ya faru ran nan ya sake faruwa kawai ta fasa 'karshe ma tashi ta yi ta fita ganin takalmin baban su yasa ta fasa shiga na ta dakin ta tafi d'akin sa ta shiga ta gaida shi tana fitowa Sameer ya shigo da leda a hannun shi shima ya shiga d'akin Abban ya aje masa ya fito kallon sa Zainab ta yi tana cewa.
"Yaya Sameer ina yini"?.
"Lafiya ya akai yau baki dawo da wuri ba"?.
"Na je gidan Aunty Murjah ne shi ya sa ban dawo ba me ka siyowa baban mu"? Murmushi yayi yana kallon ta yace "shiga ki tambaye shi ko ki ce ya sam miki kad'an" kai ta girgiza tana langwa6ar da kai ta ce "a'a saboda samun lada ka siyo masa ni kuma saboda da rashin kunya da zilama ban siya na 'kara masa ba sai na je ya bani".
"Ai ba rashin kunya bane kuma ba zilama bace soyayya ce ke ma ba za ki ci shinkafar ba kenan"?.
"Wallahi Yaya Sameer ba ta yi min bane haka kawai na ji bana son cin abinci me nauyi irin su shinkafa da taliya ko dai su doya".
"Uhm ka ga babbar yarinya sai 'kwai da 'kwai ke nan"? Ya fad'a cikin tsokana yana kallon ta dariya ta yi tana girgiza kai tace "a'a ni na isa nace sai haka bani da gashin wance ban isa na yi kitson wance ba ni da ba 'yar kowa ba mahaifi na talaka ne bana kai kaina inda Allah bai kai ni ba".
"To yanzu fad'a min me ki ke so sai na kawo miki".
"Idan zan samu awara na ke so irin ta ranar ka ji".
"Tom ina dawowa Allah ya sa ki gan ni da wuri" ya fad'a yana fita kamar za ta ce masa ya jira ta su fita tare ta kar6o amma tsoron abin da zai faru irin na wancan karon yasa kawai ta shige d'aki tana d'aukar wayar ta ta kwanta ganin kiran Afifah kusan uku yasa ta bi bayan kiran amma ta ji bata da kati kuma Sim d'in ta baya flashing dole sai dai gobe sa had'u dan gaskiya ba zai yuwu komai ta ri'ka d'orawa Sameer ba kuma shi Yayan ta ne ba yaron aiken ta ba gashi yanzu ta ce ya siyo mata awara ta ya sai ya siyo ya kawo mata zata sake cewa kati ina dahuwar hankali ayi ta da ruwa.
Pillow ta jingina a jikin bango ta jingina a jikin sa ta d'an kwanta ta kunna kallo kafin ya dawo bai dad'e ba ta ji ya shigo yana aje mata ledar ya ce gashi nan kar ki tambaye ni komai akan wannan daga baya kin san ba arziki na bane" yana fad'in haka ya fita saboda ya tabbata idan ya tsaya sai ta yi masa tambaya akan hakan.
Aje wayar ta yi ta jawo ledar kusa da ita ta bud'e zaro ido tai da mamaki ta na kallon abin da ya ke ciki rufe baki ta yi tana mi'kewa da sauri ta le'ko waje ko za ta ga takalman Sameer d'in idan ba fita yayi ba amma sai ta ga 'kofar d'akin sa a rufe alamar ba zama ya yi ba fita ya sake yi, komawa ta yi tana zama a fili tace.
"Wannan wanne irin abu ne na tabbata Yaya Sameer ba zai siyo min kaza guda ba kuma kazar ma mai tsada kai innalillahi wai waye abokin nan na sa ne yaushe gaskiya za ta bayyana a gare ni ina jin tsoron wannan al'amarin hankali na ba'a kwance ba ta ya zan ci na ji dad'in ta"? Shiru ta yi ta rasa me za ta yi can ta mi'ke tana d'aukar ta ta shiga d'akin Umma ta na ajiyewa tace.
"Umma kin ga na ce Yaya Sameer ya siyo min awara idan ya fita saboda ba zan ci shinkafa ba amma kin ga daya fita sai na ga ya kawo min wannan kuma ya ce wai kar na yi masa tambaya a kan haka tun da na san wanda zai ba ni" kallon ta Umma ta yi tana cewa "me ye a cikin nan d'in"? Jiki a sanyaye ta ce.
"Kaza ce".
"Kaza kuma"? Umma ta fad'a tana bud'awa ta ga tabbas kaza ce babban gashi sai 'kamshi ta ke d'agowa tai ta kalli Zainab wacce ke tsaye damuwa 'karara ya bayyana akan fuskar ta tace "wannan d'in ma daga abokin na sa ne"?.
"Eh".
"Waye shi"?.
"Nima ban san shi ba yace min baya gari wai sai ya dawo zai sanar min" numfashi Umma ta sauke tana cewa "to Allah ya bamu ji da gani na gari Ubangiji ya dawo da shi cikin alkhairi" shiru Zainab ta yi ta na kallon guri d'aya kallon ta Umma ta sake yi tana cewa "d'auki abar ki ki tafi man ki ka tsaya" kai ta girgiza tana cewa.
"Ni ba zan ci ba".
"To waye zai ci miki idan ma ba ki ci ba zaki kwana da yunwa ne".
"Gara kwana da yunwa akan cin abin da hankali na bai kwanta a kan sa ba".
"Me ye abun rashin kwancyar hankalin zai sako miki maganin wani abu ne Sameer d'in ne fa ya siyo ba shi wancan abokin na sa bane ki d'auka ki ci zuciyar ki d'aya".
"To ai tayi min yawa ko rabi ba zan iya cinyewa ba ki raba ta biyu kin d'auka" kai Umma ta girgiza tana cewa "a'a je ki da kayar ki ni na ci abinci".
"Ta yi min yawa ne".
"Na sani ki je da ita idan baki cinye ba da safe sai ki d'umama ta" shiru Zainab ta yi ta kafe Umma da ido kamar me nazarin wani abu zuwa can ta dur'kusa tana raba ta gida biya ta saka rabi a kwano ta mi'ke da d'ayar tana cewa "gashi nan sai da safe" tana fad'in haka ta fita ta koma d'akin ta kawai ta aje ledar ta kwanta ta bud'e wayar ta taci gaba da kallon ta har dare ya ja wajen sha d'aya sannan ta kashe ta fita ta yo alwala ta zo ta saka rigar barci ta kwanta ta rufe ido barci ya fara d'aukar ta taga tarrr a idon ta da sauri ta bud'e ta ga ashe nefa ce aka kawo ta manta ba ta kashe 'kwan ba tashi ta yi ta saka caji bata kashe nefar ba saboda dama akwai d'inkin da za ta sakawa stones d'aukowa ta yi ta zo ta fara jerawa tana saka iron tana dannewa har ta gama na rigar ta saka a skirt ta sake d'auko doguwar riga guda d'aya ita ma ta saka mata wajen 'karfe d'aya a lokacin bata gama sakawa a doguwar rigar ba ma ta ha'kura sakamakon dare yayi ta mi'ke ta sake sabuwar alwala ta zo ta yi nafila da yake daren juma'a ne ('yan uwa ku ri'ka yin wannan nafilar daren juma'a raka'a biyu ce "FATIHA DA IZAZUL SAU GOMA SHA BIYAR" raka'a ta biyu ma "FATIHA DA IZAZUL SAU GOMA SHA BIYAR" idan kayi sallama sai ka karanta "YA HAYYU YA K'AYYUM YA ZULJALALU WAL IKRAM 'KAFA D'ARI (100)" Idan kayi haka Allah zai tsare ka da azabar kabari da 'kuncin sa da nau'o'in azabarsa Kuma Allah zai haskaka 'kabarin ka ba za ka mutu ba sai ka ga mazaunin ka a aljannah, dan Allah 'yan uwa ku ri'ka yin wannan nafilar DAREN JUMA'A).
Sai da ta idar sannan ta tashi ta cire kayan ta mayar da rigar barcin ta ta kwanta bata dad'e ba barci ya d'auke ta...........
J*W*A
Ina jinjina ga 'yan ANNURI WRITER'S ASSOCIATION home of hospitality and harmony gidan kar6ar mutane hannu biyu da zaman lafiya ANNURI haske le'ka gidan kowa ko da ma'kiya na kallon ka ramin kura sai 'ya'yan ta.
SAFIYA ALIYU WAKILI ZARIA ina mi'ko gaisuwa mara adadi tare da fatan samun nasara da kwanciyar hankali a gare ki Maman khaleel Allah ya ja kwana marubuciyar littafin "MASAUKIN SO".
Tare da FATAHIYYAH MUHAMMAD YAKASAI oum Yasmeen marubuciyar littafin "UWAR GAFALALLU" ina mi'ko gaisuwa da jinjina.
@YUSRAH YMA DUTSE
PAGE 36
Washe gari juma'a bata da lecture a school shi ya sa ya wuni ba ta je ko'ina ba ta 'karawa sakawa mai doguwar riga stone sannan ta yanka wasu ma ta fara d'inkawa a wunin dai babu inda ta je har dare sai d'ari biyar da ta baiwa Sameer ya siyo mata kati ta
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 34