Share this page
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels LABARIN AISHA.🥹💔 PART 1 Sunana A'isha, na yi aure ina da shekaru 15 a duniya, mijin dana aura duk kusan na gida ne, makocinmu ne amma baya zama a garinmu, mazauni Kano ne, a can ya yi karatu. Ya nuna mun soyayya fiye da yadda ake zato a farko, ƴan uwansa sun nuna mun soyayya a farko, a lokacin ina tashen kuruciya, ina da wanda nake so wanda kuma iyayena basu kaunarsa, na nuna bana son wannan mijin nawa, amma iyayena suka kafe lallai sai na auresa, aka aaura mun shi ta dole, amma shi yana matuƙar sona. A lokacin farkon aurenmu babu irin haukan da ban mashi ba kan ya sakeni, amma ya daure saboda yana ganin ni yarinya ce kuma yana girmama iyayena, a lokacin zai kai shekaru 30 a duniya, ni kuma ina da 15 kawai. Ƴan uwansa sun nuna mun soyayya a farkon aurenmu, mamansa ta so ni a farko, kome nake so shi suke so suma, yakasance yana da kanne mata huɗu da yayarsa mace dake gidan miji ɗaya, su biyu ne maza wanda ɗayan kaninsa ne, ƙanin nasa karami ne da bai wuci 20 years ba, mijina ɗan kasuwa ne, yana da rufin asirinsa daidai gwargwado, shi yake ɗaukar nauyin gidansu da kannen nasa gabaɗaya saboda basu da uba. Tun bana son shi ina haukar zan fita in auri saurayina da nake so, har na hakura na zauna da shi saboda kyautata mun da yake yi, baya son ya ganni cikin damuwa, yana lallaɓani da kula dani spsai. Watarana na je Kaduna gida iyayena suka ce yakamata in fara sana'a, zama gidan miji shiru ba sana'a ba nawa bane, iyayena suna da kuɗi Alhamdllh, mahaifina ya kawo kuɗi ya bani matsayin jari, a lokacin da na dawo Kano gidan mijina kenan, na sanar da mijina iyayena sun bani jari in fara sana'a, ya bani goyan baya, kasancewar ya yi karatu mai zurfi sosai sai ya bani business ideas kala uku, na zaɓi na ukun watau sayar da su zannuwan gado da su laces. Na fara business a hankali, iyayena kullum suna kara mun karfin gwiwa da saka mun albarka, mijina ma haka, komai na tafiya mun daidai har na fara manta wancan saurayin nawa, na yi ƙiba na yi kyau hankali ya kwanta. Ina da kyauta sosai, hakan yasa ribar kasuwancina a lokacin duk yake karewa a kan kyauta ma ƴan uwa, dangi da abokan arziki, mutane suna sona sosai saboda kyautata. Cikin ikon ALLAH kasuwata ta karɓu abubuwa suka bunƙasa, na fara samun manyan kuɗaɗe, mijina yana kasuwancinsa shi ma cikin kwanciyar hankali sai dai abubuwa sun ja mashi baya sosai, kuɗi sun rage shigo mashi. Amma hakan bai bayyana ga ƴan uwa ba, saboda nawa kuɗin, na cigaba da tallafa mashi da nawa kuɗin domin rufawa juna asiri, a hankali soyayya mai karfi ta ƙullu a tsakaninmu, dama shi already yana tsananin sona, nima na kamu da sonsa sosai, sai na sallama mashi komaina, ina kasuwanci muna kashe kuɗinmu tare cikin haɗin kai, har ta kai ta kawo shi ya rasa nasa kasuwancin, amma bamu wani damu ba, na ɗebi kuɗi daga nawa kasuwancin na bashi ya sake cigaba da juyawa, nima na mai da hankali kan nawa kasuwanci sosai fiye da baya, nauyin gida ya dawo kaina, iyayensa da ƴan uwansa nike masu komai ba tare da sun san ni nike yi masu ɗin ba, sun ɗauka shi ne, idan suka zo Kano suna ɗauka komai na gidan shi yake yi. A wannan lokacin ALLAH ya albarkace mu da samun ciki bayan shekara da aurenmu kenan, ƴan uwansa da nawa sun yi murna matuƙa, na cigaba da kasuwancina ina renon ciki, na fara saro kaya daga ƙasashen waje ina kawowa Nigeria, komai ya cigaba a gareni, a haka har cikina ya shiga wata tara. A ranar haihuwa na haifo ƴan biyu dukka maza, lamarin da ya yiwa zanginmu daɗi, anyi murna anyi shagali sosai. A haka rayuwa ta cigaba, shekaran ƴan biyuna biyu a duniya na sake samun wani cikin na uku, mijina bai taɓa canza mun ba, a lokacin ƴan uwansa ma basu canza mun ba, arziki ya fara zaman mun sosai da sosai, na fi mijina kuɗi nesa ba kusa ba a yanzu saboda ni dik kuɗin da nake nema bana komai dasu face karawa a kan kasuwanci saɓanin shi dake ɗaukar nauyin abubuwa da dama a kansa, dik da ina taimaka mashi sosai amma dole wasu shi yake yi. Cikina na biyu na sake haifan ɗa namiji, a daidai wannan lokaci yayan Mamar mijina wanda ya rike mijina ya girma a hannunsa ya faɗi ya rasu, dangi sun yi kuka saboda shi ne babba, shi ne jigon dangin. Mun je gaisuwar rasuwansa kenan ƴan uwan mijina suka rikesa wai sai ya auri babbar ɗiyar kawun nasa, ya duba maraicinta ya aureta. Mijina ya ce bashi da ra'ayin auren mata biyu, kuma yanzu abubuwa sun mashi yawa a kai, ba zai iya ba, dangi suka ce bai isa ba, saboda uban yarinyar shi ya rikesa tun yana yaro, dan haka ko dan alkhairin ubanta ya duba ya aureta, shi kam ya ce a'a ba zai iya ba, bashi da karfin rike mata biyu a yanzu, mahaifiyarsa ta yi fushi, ta ce lallai yazame mashi wajibi ya auri wannan yariya idan ba haka ba babu ita babu shi. Abubuwa sun ɗauki zafi, mijina ya shiga damuwa da tashin hankali, bai san tayaya zai ɓullowa lamarin ba, hasalima baya son yarinyar da ake son haɗasu, bata mashi ba, ga shi yana jin nauyi da kunyan iyayena, abin da baku sani ba shi ne, mahaifina ne ya biya mashi kuɗin karatun da ya yi dukka, mahaifina ya mashi komai, shi ya fara ɗora shi a kasuwanci, yaron shagon mahaifina ne a baya kafin ya tafi makaranta, saboda hankali da natsuwansa yasa mahaifin nawa ya aura mun shi ashe, ni duk lokacin giyar yarinta na ɗebata ban san mahaifina ya biya kuɗin karatunsa ba, ban san komai ba, so ya ji nauyin tinkarar iyaye na da batun. Ni ma ba zai iya zuwa ya gaya mun zai auri yarinyar ba, saboda duk abin da ake yi a dangi ban sani ba, meeting suka yi a gidan kakansu ban sani ba, so ban san ance ya auri yarinyar ba. Ina zaune a ɗakin mamata a gida ya shigo hankali a tashe, ina son tambayarsa me yake faruwa ya ce. "Ɗauki jakarki mu tafi". Zan yi magana ya hanani, dole na miƙe na haɗa kayana dana yarana,a wannan rana muka koma Kano bamu sallami kowa ba, duk abin da ake yi ni ban sani ba. Komarmu da kwana ɗaya na kira Mahaifiyarsa dan in kara yi mata ta'aziya, tana ɗauka sai cewa ta yi. "Kin rabani da ɗana, har ni Sulaiman zai bijirewa umarnina saboda ke? To ki koma ki faɗawa bokanki yayi kaɗan, in dai juranku bin malamai da raba uwa da ɗanta ne wajen kuka zo, ki jirayi sakamako". Hankalina a matukar tashi na ce. "Mama ban gane ba?"........ Cikin faɗa ta ce. "Ba zaki gane ba ai munafuka algunguma, har ni Sulaiman zai kallah ya ce ba zai iya maki abokiyar zama ba saboda in yai haka bai yi adalci ba, nasan ba laifinsa bane, dan ɗana mai biyayya ne, shiyasa na kyalesa, amma ki jira wlh sai na warware kullin da kika masa dake da iyayenki!!". Tana gama magana ta katse kiran. Cikin tashin hankali na kira kanwarsa dake binsa. Kira uku bata ɗauka ba, na kira ta biyun ita ma bata ɗauka ba. Ina ƙoƙarin kiran ta ukun sai ga ta farkon mai suna Amina ta kirani, jikina har yana rawa na ɗaga, ina ɗagawa kafin in yi sallama na ji ta ce. "Munafuka me kuma kike wani kirana bayan kin rabamu da ɗan uwanmu?". Tun daga nan na gane akwai matsala, sai kawai na kashe wayan ba tare da na yi mata magana ba, jikina na rawa na kira mijina, yana ɗagawa na ce. "Abban Hassan me yake faruwa?". Ya nuna mun bai san komai ba, ya ce. "A ina fa"........ Na ce. "A gida mana, meyake faruwa, Mama tana ta faɗa, ko na mata wani laifi ne?". Ya ce. "A'a ki kyalesu kada ki sake kiransu zuwa su huce su sauka daga kan dokin zuciya"....... Na yi na yi ya faɗa mun me yake faruwa, amma ya nuna babu komai in kwantar da hankalina. A haka muka yi sallama sai na yi maza na kira kaninsa mai suna Abba. A lokacin Abba ya tafi ɗauko su Hassan a makaranta, dama Abba tare muke da shi a gidan ɗaya. Abba na ɗauka ya ce. "Aunty ina tuƙi bari in isa makarantar zan kiraki"....... Cike da tashin hankali na ce. "Abba ba zan iya jira ka isa ba, kawai ka bani amsata, kuma tsakani da ALLAH zaka faɗa mun, meyakefaruwa a dangi?"...... Muna da kyakkyawan alaƙa tsakanina da Abba, yaro mai hankali da natsuwa, yana sona tsakani da ALLAH. Dan haka ya kwashe labarin dik abin dake faruwa ya faɗa mun, cikin tsananin tashin hankali na miƙe tsaye, ina da zafin kishi sosai da sosai, ban san lokacin da wayata ta faɗi a hannuna ba saboda tashin hankali, mijina zai auri wata bisa umarnin iyaye da dangi?....... Babban magana. Wannan shi ne farkon kaddarar A'isha a gidan aurenta, shi ne farkon labarin, labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi. LABARIN AISHA.🥹💔 PART 2 Gabaɗaya sai na ji jikina ya saki, na rasa me yake mun daɗi, kaina na juyawa, a wannan wuni na gagara koda girkin dare ne, na zauna da tunani fal cikin raina, shin da gaske ne zai aureta? Meyasa sai shi dangi zasu zaɓa? Meyasa zasu juya mun baya? Hakan na nufin a kodayaushe ɗan uwanka ɗan uwanka ne? Ɗan uwan wani ba zai taɓa zama ɗan uwanka ba har abada ba, dole watarana sai ya nuna maka cewa ɗan uwan wani ne shi. Abba ya dawo dasu Hassan, da yake sun saba da bappan nasu ko wajena basu wani zauna ba, suna dawowa ya cire masu uniform yai masu wanka, ya canza masu kaya ya basu abinci, shi ma bai shigo side da nike ba sai can yamma, ya shigo sanye da sportswear a jikinsa zai tafi buga kwallo da ya saba. Tun daga bakin kofa kafin ya karasa shigowa ya fara tsokanata kamar yadda ya saba, sai dai yana shigowa parlo ya tsaya shiru yana kallona, tun in da na zauna ban bar wajen ba har karfe huɗu saura yanzu, almost awa biyu ina zaune a wajen. Ya kalli parlon da kyau ya kuma kalleni, sai ya fahimci ina cikin damuwa, dama sau dayawa idan ina cikin damuwa Abba ke sakani farinciki, ya ƙariso ciki yana cewa. "Hajjajo lafiya kika zauna kaman an sassakaki? Ko dai kewata kike yi ne?". Na ɗaga ido na kallesa amma ban yi magana ba, ya faɗaɗa murmushin kan fuskansa tare da zama a kusa dani, ya fara tsokanana yadda ya zaba, dole ba dan na so ba na fara murmushi, saboda ya saba ya san hanyar sakani murmishi, zan iya cewa ya fi yayansa iya zama da mutane sosai. Sai da ya sakani dariya na fita daga kunci ne ya ce. "Faɗa mun wanda ya taɓaki in je in rama maki"....... Ina ƴar dariya a lokacin na ce. "A'a, wannan kam ba zaka iya rama mun ba nawan, sai shiru kawai"....... Ya ce. "Yaya ne ya taɓaki ko?"........ Na ɗan hararesa cikin wasa kafin na ce. "Kai da kasan komai, waye zai taɓani idan ba shi ba" "Gaskiya yaya baya duba mana, a kan me zai dinga ɓata maki rai?". Ya faɗa cikin zoyala. Na ɗan yi murmushi, da yake maganar dake zuciyata ta tsaya mun sosai a kahon zuciya, na kasa danneta sosai, sai na ce. "Yanzu Abba meyasa yayanka ba zai auri yarinyar ba to? Ya duba maraicinta mana?". Na faɗi hakan ne ba wai dan hakan ne a raina ba, sai dan bana son kowa ya fahimci bana son haɗin, bana kuma son kowa yasan kishina a fili. Abba ya ɗan yi kicin-kicin da rai kafin ya ce. "Aunty idan Yaya ya auri yarinyar nan bai maki adalci ba, na faɗawa Mama tun lokacin da ta tado da maganar nan, na faɗa mata yaya bashi da karfin rike mata biyu, yanzu ma fama yake yi, amma taki fahimta, saboda tana ganin duk abin da yake gidan nan yaya ne yake yi, bata san ke kike yi ba, na yi ƙoƙarin faɗa mata haɗarin dake tattare da wannan haɗi, amma ta ce in mata shiru ni yaro ne da ban san komai ba, to ni wlh bana goyon bayan wannan haɗi, kuma ba zan taɓa goyon baya ba, bugu da kari wannan yarinya da aka ce yaya ya aura bata da kunya, bata ganin kowa da daraja, mamarta ma haka, kina ji duk dangi zagin mamanta ake yi, mamanta fa har kwalar rigar babanta take kamawa tana ya saketa in shi ɗan halak ne, ai da karfi maman ta kashe aurenta ta shiga yawon duniya, har kotu ta kai kawun namu dan ya saketa, to ya za'ayi barewa ta yi gudu ɗanta ya yi rarrafe? Wai sai ace a duba maraicinta da rashin uwanta a gidan, hmmmmm kowa ma hakuri yake a duniyar nan". Da iya gaskiyansa Abba yai magana. Hankalina ya kara tashi jin irin halin mamar yarinyar da kuma yarinyar, na shiga damuwa sosai mara misaltawa, amma a gaban Abba ban nuna damuwar ba, na danne game da cewa. "Abba ba'a ja da maganar iyaye fa, amma kuma iyaye basu isa tilastawa yaro yin aure ba, zasu iya saka shi ya saki matarsa, amma a batun aure basu da hurumin tilasta mashi ya yi, saboda shi kaɗai yasan karfinsa da lafiyansa". Abba ya ce. "Aunty bar dukka wannan zance ma, wlh yaya ba zai auri yarinyar nan ba, saboda bata da kunya, a lokacin da muka je gaisuwar rasuwar nan da aka yi maganar auren yaya ya ce ba zai iya ba, da ya fita ya haɗu da yarinyar, ya kirata, ina jinsa a bayan window ɗina ya ce mata ta je ta faɗawa dangi bata son shi in ba haka ba ranta ne zai ɓaci, da buɗar bakinta sai cewa ta yi ko yaki ko ya so sai ya aureta, iyaye sun zartar da hukunci, kuma ita ba wanda take so sai shi, magana without respect take mashi, da isa da gadara". Nan fa na ji hankalina ya sake tashi, amma na danne dan in kara jin me dame aka ce a dangi bananan. Abba ya cigaba da cewa. "Ina ji mama ta dinga yi wa yaya faɗa saboda yarinyar ta je ta cewa Mama yaya ya zazzageta ya ce mata mara tarbiya kuma ba zai aureta ba, mama ta mashi faɗa sosai, ta bashi number Zainab ɗin wai kullum ya yi mata magana in ba haka ba bata yafe mashi ba". A lokacin da Abba yake wannan magana ji nake tamkar guduma ake buga mun a kai, tsabar tashin hankali ban san lokacin da na ce. "Abba gara ka je wajen kwallonka kada lokaci ya kure maka". Na faɗi hakan ne dan ya tafi, ba zan iya jurar jin abubuwan ba, ashe abubuwan da suka dinga faruwa kenan da muka je gaisuwar, duk ban sani ba ni kam, dan a lokacin a gidanmu na sauƙa, da yamma na je family house ɗinsu nai masu gaisuwar na koma gidan babana, washegari ma da safe na sake zuwa na koma da rana, ashe duk abubuwan da ake ta yi kenan ba gaisuwar rasuwar ake karɓa ba, ashe a lokacin duk kallon banza suke mun, kuma yarinyar da aka ce ya aura Zainab, yarinyar ina haɗuwa da ita a gidan rasuwar, ko magana bata mun nima bana kulata, ashe duk kallon banza take mun.... Tashin hankali. Abba ya miƙe yana cewa. "Aunty kuma haka ne, bari in je kada a buga a barni, me zaki dafa mana da daddare?". Yana murmushi ya faɗa. Na ɗan hararesa kafin in ce. "Ka dawo ka yi girki dan ba zan maka ba, na gaji da wahala da kai"....... Ya ɗan haɗe rai, yana da mugun shagwaɓa kamar ba namiji ba, saboda shi ne auta, kuma ya taso cikin mata har guda huɗu sisters ɗinsa, dan haka sai ya shagwaɓe fuska kafin ya ce. "In ajiyeki a gidan ki ce ba zaki mun girki ba? Kin ma isa? To wlh sakwara zaki daka mun da miyar egusi kafin in dawo". Na miƙe ina faɗin. "Na isa har ma na yi yawa, wuce ka bani waje, ba abin da zan girka"......... Da yake yana da tsawo sosai, duk ban fi kirjinsa ba dana miƙe, sai ya zunguri tsakiyar kaina yana faɗin. "Da kuwa na baki red card"......... "Yellow dai zaka bani ba red ba, wuce mun daga parlo tun wuri, kuma ka yi maza ka nemo matar aure tun ban gama gajiya da kai na watsarka a bola ba". Ina ɗaure fuska na faɗa, mun saba irin wannan wasa da shi sosai, har fin haka ma. Ya ɗan shagwaɓe fuska kafin ya ce. "Please my Aunty mu bar wasa me zaki dafa mana?"....... Da yake ina son ya tafi sai na ce. "Abin da ka fi so, kai dai jeka, ai kasan wajen girki baka da matsala dani"..... Ya ɗan yi murmushi har dimple ɗinsa irin na mamansu ya lotsa kafin ya ce. "Shiyasa nake sonki matar yaya, ki saka mana barkono kaɗan". Na hararesa ban yi magana ba, saboda ni damuwata kawai ya fita ya bani waje. Ya juya yana mun sai ya dawo, na amsa da a dawo lafiya, ya shiga ɓangarensa ya ɗauki Hassan da Hussaini suka wuce zai kaisu islamiya kafin ya wuce wajen buga kwallonsa. Yana fita na shiga ɗaki na rushe da kukan da ban san yaushe ya kwace mun ba, kukana ya tashi jaririna daga barci, Muhammad ya tashi ya fara kuka shi ma, na ɗaukesa muka cigaba da kuka tare. A wannan wuni ban yi girkin dare ba. Karfe 6 Abbinsu ya dawo daga kasuwa, side ɗinsa ya shige kamar yadda ya saba. Ina jinsa ban fito na tarbesa yadda muka saba ba, ko wanka ban yi ba, in da na zauna rike da Muhammad ina kuka har ya mai da barci ban matsa daga wajen ba. Abbinsu ya yi wanka, ya shirya zuwa masallaci ya fito, lokacin an tada hiƙama, tabbas ya so shigowa side na ya duba meyasa ban fito na tarbesa yadda muka saba ba, amma bai samu damar shigowa ba saboda an fara sallah, dan ya samu jam'i ya wuce. Sai bayan sallah ishai suka shigo dukkansu har Hassan da Hussaini dake wajen Abba. Dama mun saba bayan sallar ishai muke haɗuwa mu ci abinci. Kai tsaye ɗakina Abbinsu ya shigo, ina kwance kan dadduma, sallar ma da kyar na yita, ban saba da irin wannan tashin hankali ba, na taso cikin gata da kulawa, kome nake so shi nike samu, ban taɓa neman abu na rasa ba, kullum cikin farinciki nike, yau ce bakincikina na farko a rayuwata dole hankalina yai mummunar tashi. A gabana Abbi ya tsugguna tare da cewa. "Habibi lafiya yau ko motsinki ban ji ba?". Wani irin kuka na ji ya zo mun, amma na daure game da cewa. "Bana jin daɗi ne".......…... Ya kalleni da kyau kafin ya ce. "To meyasa baki faɗa mun ba?"...... Na yi shiru ban amsa ba, saboda maganar ma bana son yinta, haushin kowa nike ji. "To tashi mu je ki ci abinci sai ki sha magani"........ Na yi banza da shi. Yasa hannu ya ɗagani, na ce. "Dan ALLAH ka barni, bana son cin komai, ni ban ma girka komai ba". Ya ce. "Bar batun girki, me zaki ci sai in sayo maki, girkin zan mana yanzu"...... "Ba zan ci komai ba". Na bashi amsa a gajarce, na koma na kwanta. Ya sake kai hannunsa kumatuna. "Menene yake maki ciwo?". A taƙaice na ce. "Abbi kaina ke ciwo kuma na sha magani hutu nake buƙata dan girman ALLAH ka rabu dani". Daga haka ban sake mashi magana ba, dole ya rabu dani dan ya yi ta yi ban amsa mashi ba. Ya miƙe ya fito parlo. Ya shiga side ɗinsa, jim kaɗan ya fito sanye da jallabiya ya shiga kitchen yana faɗin. "Abba bari in maku girki Auntynku bata jin daɗi". Abba ya amsa da okey, sai ya miƙe ya shigo ɗakina, ya ganni kwance in da yayansa ya barni, cike da kulawa ya mun sannu ya jiki, ina jinsa ban amsa ba, sai ya zaci barci nike yi, ya juya zai fita Muhammad ya tashi ya fara kuka. Da sauri ya zo wajen gadon ya ɗaukesa wai dan kada ya tasheni, ya fita parlo da shi, ya shiga kitchen ya haɗa mashi madara, ya fito ya zauna a parlo, yana bashi yana jijjigasa har ya ƙoshi. Sai ya kwantar da shi ya bi yayansa cikin kitchen dan tayasa aiki. A tare suka yi girki suka gama, suka zuba mun, ba yadda yayansa bai yi ba naki ci, ya ce me nike so naki magana, dole ya hakura ya barni. Abba ya shigo da Muhammad, ya kwantar da shi a gado ya fita bai mun magana ba saboda yayansa na ɗakin. Ya

Chapter 1 of 38