gama watsa ruwa yana tsane jikinsa da towel, ya wani wurga mata mugun kallo kafin ya ce. "Lafiya?"....... Ta ɗan shagwaɓe mashi fuska kafin ta ce. "Ka yi hakuri mana".
Ya harareta bai sake yin magana ba, ya gama tsane jikinsa tana ta kara bashi hakuri, ya ɗauko robe ya sanya ya fito, sai ya ce mata. "Komai ya wuce, yanzu barci nike ji".
Da sauri ta matso jikinsa, ta rungumesa game da cewa. "Ban ci abinci ba fa baby"......... Ya ɗan kalleta kafin ya amsa da. "To me yahanaki ci?"...... "Ban yi girki ba".
Ya ɗan zaro mata manyan idanunsun nan. "Meyahanaki yi?"..... Ta kara narkewa a jikinsa tare da cewa. "Baka turo mun kayan cefene ba, ɗazun ina jin yunwa na ce bari in dafa indomie tun da ina da shi, sai na ga bani da shana".
"Wani irin cefene kuma bayan kina da ragowar shinkafar da kika zo da shi?"..... Ai da sauri ta wani sakesa tare da binsa da kallo sosai. "Kana nufin ni ba zaka mun cefenen da kai wa Aisha ba?!". In a harsh way ta faɗa....... "Ni nace maki na yi wa Aisha cefene?".
Ta kara yin kicin-kicin da fuska. "To da waye yai mata idan ba kai ba? Nan aka kawo mata komai kwali-kwali buhu-buhu ta ce zaka zo mun da nawa"......... Ya tamke fuska tamau kafin ya ce.........
labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi.
FATEEMA ZAHRA MUSA
A-K-A
QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥
LABARIN AISHA.🥹💔
PART 16
Ta kara yin kicin-kicin da fuska. "To da waye yai mata idan ba kai ba, nan aka kawo mata komai kwali-kwali buhu-buhu ta ce zaka zo mun da nawa"......... Ya tamke fuska tamau kafin ya ce. "Ni bani na mata cefene ba, sai dai idan ita ta yi wa kanta dan ta saba".
Tsalle Zainab ta yi ta dire tare da cewa. "Wlh ba zai yiwu ba, an gaya maka duk wani munafurci na maza ban sani ba ne? Ka je ka yi wa matarka cefene wadatacce sannan ka ce wai ita ta yi saboda kana son raina mun wayau ku tauye mun hakkina? To wlh baku isa ba, daidai nike daku"...... Ya wani kalleta. "Awwww ALLAH? To gara da kika san cewa matata ce, sannan kamar yadda na faɗa maki ni bani nai mata cefene ba, ga hanya zaki iya zuwa ki tambayeta". Yana kai karshe ya wuce ya hau shirin kwanciya.
Ta ce. "Wlh ba zai yiwu ba, na san kai ka saya mata, idan ba haka ba yaushe ta ga kuɗin sayan waɗan nan uban kayayyaki dukka? To wlh sai na je na kwaso rabona". Tana kai karshe fuuuu ta fito waje, yana kiran sunanta kan ta dawo, ina ai bata tsaya ba, dan wlh bata jin magana sam.
A bakin kofar part ɗina ta tsaya, tana huci ta hau dukar kofa dan already na rufe, tana yi tana faɗin. "Munafuka kawai, zaki ce zai zo mun da nawa, ashe duk makaryaciyar banza ce ke".......... A lokacin ina waya da Safiyya tana faɗa mun Abba zai dawo next week, har ina tsokanarta na ce zai dawo ba zai faɗa mun ba sai dai in ji a bakinki, to ai shikenan, jin ana dukan kofa yasa na ce da Safiyya. "Ke ina zuwa". Ban jira amsarta ba na katse kiran.
Ina fitowa sai ga Khalifar Aunty Farida ya fito daga ɗakinsu zai je duba wanene mai buga kofa, yaron nan ko sannu baya ce mun, kuma dan rashin kunya in yi girki ya ci, yana zaune a side ɗina, yana cin arzikina amma iyayensa sun koya mashi gaba dani, sun shafa mun bakin fenti, suka ce mashi ai ni bana son ya zauna a tare da kawunsa ya ci arziki, burina in koresa ya bar gidan, shi ne yake gaba dani. Ya wani kalleni ya ɗauke kai, aikuwa yana juyowa zai sake kallona na wani tamke fuska tamau, cike da bada umarni na ce. "Kada ka sake ɗaga idanu ka kalleni a gidan nan, kai harkar gabanka!". Babu wasa a tattare dani na faɗa, coz bana son rainin wayau, dan ya iya kallon mutun, in dai zan fito sai ya dinga kallona, kuma wai yana gaba dani saboda jahilci.
Da yake ba hankali ne ya isheshi ba, ga jahilci sai cewa yai. "Idan ban daina kallon naki ba dukana zaki yi?"......... Na yi shiru ban tanka mashi ba, coz bani da lokacinsa, kawunsa ne daidai yina ba shi ba, but na sha alwashin in dai ya sake bina da irin kallon da yake mun billahil lazi sai na yi maganinsa, zan gwada mashi karfin arziki, sai na kaisa in da sai ya durkusa yana kuka yana bani hakuri, ai naga iskancinsu yawa ne da shi, kuma na fahimci ko namar jikinka zaka yanka ka baiwa dangin miji sai wani ya ce baka yanka mashi sosai ba, dan haka gara kawai ku zuba rashin mutuncin sai ka fi zaman lafiya da su.
Ya wuce ya buɗe kofar, yana buɗewa ya ce. "Aunty Zainab lafiya a wannan dare?". Khalifa yana shiri sosai da Zainab, dan a lokacin neman aurenta yana sahun gaba-gaba na masu gaya mata halin da nike ciki a gidana, da duk abin dake faruwa.
Ta amsa mashi da. "Khalifa bani hanya, wannan yarinyar da kawunka zasu raina mun wayau ne, hakkina na zo ɗauka"..... Da yake Khalifa ba abin da ya fi iyawa sai faɗa sai cewa ya yi. "Gaya mun abin da ta maki in koya mata hankali". Shi fa bashi da hankali, a jahilcinsa idan an barsa zai iya sa hannu ya dagi matar aure, dan haka yana ganin zai iya dukana.
Ina tsaye ta shigo cikin parlo tana faɗin. "Kayan abinci ya sayawa Aisha ya hanani ni kuma, zai raina mun wayau wai ba shi ya saya mata ba, basu san duk abin da suke yi a gidan kafin in shigo nasan komai ba".
Na taɓe baki ina kallonta, Khalifa ya ce. "Ai fin haka ma zata maki in dai wannan ce"........ "To aikuwa wlh zata san ni ba'a mun in kyale, ke Aisha fito mun da rabon kayan abincina tun raina bai gama ɓaci ba".
Na ɗan yi shiru ina kallonta, duk zatona yadda take da shekarun nan har wajen 27 years na zaci tana da hankali, ashe shekarun ne kawai ba hankali ba ilimi. Khalifa ya ce. "Wai ba dake ake yi bane?".
Ko kallon in da yake ban yi ba, dan basu isheni kallo ba....... Sai Khalifa ya ce. "Aunty Zainab kayan na kitchen ɗinta, shiga ki kwashi abin da kike so in ga uban da zai hanaki"......... Ta kuwa gyaɗa kai game da wucewa zata nufi kitchen ɗin, a dake na ce. "Duk wanda ya taka cikin kitchen ɗin nan billahil lazi sai ya gane Annabi Isa ba ɗan ALLAH bane Manzon ALLAH ne, sai ya yi danasanin sanina!". Babu wasa a tattare dani nai maganar.
Suka tsaya tare da juyowa, babu alamar wasa a kan fuskata, na sha kunu dan naga abin nasu ya wuci rainin wayau, akwai buƙatar su san iyakarsu a gidan nan. Na kalli Zainab kafin in ce. "Ke babban kwabo, wuce ki fita a side ɗin nan tun ban sa kin yi danasanin sanina a rayuwarki ba". Cike da class da bada umarni nai maganar.
"Idan ban fita ba dukana zaki yi?". Ta faɗa tana juyowa ta nufo ni. Khalifa ya ce. "Ta dakeki in bata da hankali, da kuwa na wa yarinya mugun dukan mutuwa"..... Fahad da suka isheshi da hayaniya ne ya fito tare da cewa. "Haba Khalifa, kai kam sai yaushe zaka yi hankali ne?"....... Ai take ya ce. "Sai na ci uwar ubanka idan ka sake shiga maganata, banza dakiki wanda bai san abin da yake yi ba, in banda jahilci irin naka har zaka bar bayan danginka ka bi wata banza?".
A daidai lokacin Abbie ya shigo parlon fuskansa a murtuɗe sosai, ai yana zuwa bai yi magana ba ya wankewa Khalifa fuska da marin da sai da ya sanya shi yin baya-baya kamar zai faɗi, coz duk abin da suke faɗe yana jinsu sarai, Khalifa na ɗagowa zai yi magana ya sake ɗauke mashi fuska da mari game da cewa. "Idan baka da hankali baka da tarbiya zan koya maka yau!!". Yana faɗa ya zaro wayar TV a jikin TVna da karfi.
Khalifa akwai taurin kai, sai ya tsaya wai ba zai gudu ba, aikuwa kawun nasa ya mashi duka tamkar wanda aka saukowa da wahayin duka, coz dama Abbie yana kan dokin zuciya, saboda abin da Zainab ta mashi, ga shi tun safe yake fama da feeling bai samu ya kwantar ba, kun san wani abu ɗaya da namiji, in dai yana jin sha'awa kuma bai kwantar ba, wani irin mafaɗaci yake zama, yai ta faɗa babu dalili, da kin mashi abu kaɗan sai faɗa, to abin ne yake azalzalarsa a jiki shiyasa yake wannan masifa.
Ai Khalifa da ya ga kawunsa fa ya makance zai mashi illar sai ya nemi hanyar gudu, aikuwa Abbie ya rufe kofa, ya hanasa fita ya dinga dukansa yana ce mashi. "Idan baka san darajar aure ba ka koma uwarka ta faɗa maka, har kake ikirarin zaka sanya hannu ka daki matata, ko uwarka an gaya maka tana da ikon dukanta ne bare kai? Ko ce maku aka yi ku na aurowa ita?".
Zainab bata taɓa ganin ɓacin ran Abbie har haka ba, tuni ta ɓuya a bayana tana kallon yadda yake huci yake tattaka Khalifa da kafa tamkar wanda baya cikin hayyacinsa. Ni kam da na saba ko a jikina, dan before ya taɓa yi wa Abba wani dukan da ya targaɗa mashi hannu a kan ball, lokacin ya hana shi batun ball Abba ya dage sai ya yi, ya je makaranta sai ya ce ba zai je ba sai ball.
Shiyasa kuka ga Abba yana sona yana girmamani, nice nan na tsaya mashi sai da Abbie ya kyalesa da burinsa, da kyar na samu yayan nasa ya aminta, to shiyasa yake mutuntani, dan duk wani burinsa ni na tsaya mashi ya cinma, sannan Abbie ya sha dukan yaran shagonsa a gaba in suka mashi ba daidai ba, bashi da saurin duka, amma fa idan ya kama to ka gudu ne kawai ko a samu masu kwatanka, dan in ba haka ba sai buzunka.
Tun Khalifa yana iya kuka da karfi yana bashi hakuri har ya kwanta a ƙasa kukar bata fita sosai. Zainab iyayen rashin kunya ta gagara tunkarar Abbie ta ce zata dakatar da shi. Ni kam da na ga khalifan ya yi laushi Abbie zai iya mashi mummunar illah yanzu kam, sai na matsa kusa da shi daga bayansa na rike wayar hannun nasa, duk ya tsistsinka mun wayar Tv.
Cikin zafin nama ya juyo da tunanin Zainab ce ta rike, ya yi niyyar ɗauketa da mari in itace, amma yana ganin nice ya ce. "Sake shi!"........ Na yi ƙasa da murya wajen cewa. "Please Habibi, ya daku iya dakuwa, dan ALLAH ka rabu da shi haka, zaka ji mashi ciwo"....... Abbie ya ce. "Ciwon nike son ji mashi ai, saboda a shekarun san nan ciwon shi ne karatun da zai shiga kansa ba karatun makaranta ba, banza dabba irinsa!". In a harsh way ya faɗa. Kada ku yi tunanin saboda ni fa Abbie yak faɗar nan, a'a ko kaɗa, haushin dake ransa ya sauke kan Khalifa, tun safe yake kan tsini, ni kuma abin da yasa bai mareni da na rike wayar ba shi ne, yana son karɓar kuɗi a hannuna, ga batun gold time da muka sa ya kusa cika, Yah Abbas zai dawo in karɓa mashi, shi ne yasa bai yarda mu yi faɗa ba dan kada in ki bashi dukiyata. Abbie da kuɗi na 5&6.
"Please Habibi, dan ALLAH ka yi hakuri haka nan". Na kai karshen maganar tare da ɗan rungumesa kaɗan ina ɗan bubbuga bayansa. Su Hajiya sodangi sai ido kawai. Fahad ma yana tsaye a gefe sai ido kawai.
Abbie ya ce. "Ya tashi ya haɗa kayansa ya bar mun gidana yanzun nan"...... Na yi kokarin dakatar da shi, amma Abbie ya rantse sai Khalifa ya bar gidansa, a wannan daren yaron nan ya haɗa kayansa ya fita, na shiga tashin hankali da tsoron me zai biyo baya daga wajensu Mama? Ga Aunty Farida, duk nasan laifina zasu gani.
Abbie ya shige cikin ɗakina ya kwanta bayan ya cewa Zainab ta bar part ɗin nan tun bai mata lahaniba ita ma, ai da gudu ta wuce nata side ɗin, Abbie ya rufe gidan ya dawo ɗakina wai a nan zai kwana, ban hana shi ba, ya kwanta dan naga yana kan dokin zuciya, amma fa ban bashi kaina kamar yadda ya so ba, dan kuwa yana nuna mun abin da yake so na ce mashi a'a wlh, ya manta a wajen sodangi kawai yake samun gamsuwa ne? Ko ya manta ranar da aka kawota haka ya dinga faɗa? Daga ɗakina ina jinsu yana faɗa mata bai taɓa samun gamsuwa ba sai wannan rana, ashe shi da duk ba aure yai ba, yanzu ne yai aure, ita ce cikakkiyar mace mai gamsar da mijinta, duk ina jinsa ya faɗa mata, sai yanzu ya ce wai yana buƙatata, ai haba malam, karya ne wlh.
Wlh maza ku ji tsoron ALLAH, ku da kanku kuke haddasa fitina a cikin gidanku, yanzu me amfanin kana da mata biyu ka dinga gayawa ɗaya a wajenta kawai kake samun farinciki da gamsuwa? Me amfanin hakan fisabilillahi? Ba dole ku dinga haddasa faɗa ba, to duk wacce ake yabawa gani take kamar da gaske kuke faɗa basu san karya ce kawai kuke mata ba, dan duk abin da zaku faɗawa ɗaya ninkinsa ma zaku sake zuwa ku faɗawa ɗayar, duk su zo suna yi wa juna kallon raini, ba girmama juna, ina amfanin ka rusa gidanka da kanka? Ku ji tsoron ALLAH wlh.
Ya yi cikin-cikin da fuska kafin ya ce. "Ni na ce maki a wajenta nike samun gamsuwa? Aisha kinfi kowa sanin ke kaɗai kike iya gamsar dani, meyasa kike son hukuntani da laifin da ban yi bane?". Yana wani marairace murya na munafurci, burinsa kawai in taimaka mashi ya samu natsuwa....... Na wani kallesa, kai namiji ƙanin ajali.
Ya kai hannu zai jawoni jikinsa na miƙe game da cewa. "A'a, your happiness tana ɗaki, kuma itace nan kawai macen da zata iya gamsar da kai Habibi, dan haka goodnight"........ Ban jira amsarsa ba na ja wayata na ɗauki Muhammad na fice daga ɗakin, ɗakinsa na shiga tare da rufo kofa da key, na yi kwanciyata ina tunanin wlh ba zan baka kaina dan kana neman kwantar da abin dake damunka ba, in kaga na baka kaina to sai nan da wata huɗu kuma sai ka zo mun cike da soyayya ba wai dan ka ɓata da matarka ba! In dai don ka ɓata da matar ne zaka nemeni ban cika mace ba kenan, wlh baka isa ba, nasan kima da mutuncin kaina Malam Abbie.
Ina kwanciya ba jimawa barci yai awon gaba dani, Abbie tamkar zai mutu, ya dinga juyi a gado, ga shi shi wasanni basa sanyawa ya samu gamsuwa a sauƙaƙe, kwanciyar hankalinsa ɗaya ya biya buƙata kai tsaye, shi ko kallon batsa bata mashi, shi fa kawai ya samu abin da yake so, kuma wani abu da shi, bai san wasa ba, tun da nike da shi bai taɓa mun wasannin ma'aurata ba, jima'i kawai ya sani, babu wani romance, ko kiss babu ruwansa da shi, shiyasa kwata-kwata kwanciyar aure bai mun ba, ban taɓa sanin me daɗinsa ba, ni ban ma san kalan Abbie ba, zai iya jima'i dake sau uku lokaci ɗaya, kuma dukka babu wasa, kawai aiki kaman wani doki, kina mashi korafi yana kara abin da yake yi.
Aikuwa da ya ji azaba, yana neman rasa hankalinsa sai ya miƙe ya komawa Zainab, tun ina iya jiyosu suna masifa kafin barci ya ɗaukeni har nai barci.
Abinku da namiji tuni ya shawo kanta ta biya mashi buƙatar dake neman hallakasa, tun daga wannan rana ya ɗauki fushi dani, a raina na ce oho maka dai, dama ai ba uwar da kake karina da shi a gidan bare in damu dan kana fushi dani, komai ni nike yi wa kaina, dan haka na cigaba da rayuwar farincikina.
Sai da ya yi kwanaki uku ban ga ko kafarsa ba, haka ita ma Zainab ban sake ganin kafarta ba, ba kuma su sake yin faɗa ba, sai dai a rana ta ukun Mama ta kirani, ina ɗauka ta hau masifar na hana a sayawa Zainab kayan abinci ga shi kayan abincinta ya kare, kuma ta ce Sulaiman ya saya mun komai.
Na rasa me zan cewa Mama sai kawai na ce ta yi hakuri, ta dinga faɗa tamkar zata kai mun duka a cikin wayar, sai yanzu na gane yau ma Zainab da Abbie sun yi faɗa kan kayan abinci kenan, shi ne Zainab ta kira Mama ta faɗa mata. Kuɗin cefene ta ce Abbie ya bata, sai ya ɗauki 500 Naira ya bata, ta ce me zata saya da 500 Naira a wannan zamani, ya ce koma me take yi so ta saya shi iya abin da zai iya badawa a kowani rana kenan, tama samu gata ai, ni ko 500 Naira ɗin ai bai taɓa bani ba, sai na rasa ina bawan ALLAHN nan yake kai kuɗi, ko da yake dama duk kuɗin da kake nema ka tara baka ci ba baka sauke nauyin iyali ba tabbas wannan kuɗi ba zasu yi albarka ba, zaka nemesu ka rasa ne, ka yi ta wahalar nema amma duk a banza.
Na dinga baiwa Mama hakuri, ta kashe wayarta tana masifa, na buga uban tagumi ina tunanin rayuwa. A ranar da yamma Abbie ya zo rai a haɗe wai in kira Yah Abbas ya turo mun gold ɗin nan, na mashi kallon tsab kafin in ce. "A'a, babu wanda zan kira ya turo mun gold Abbie, na fasa sayarwa".
Ya sake haɗe rai game da cewa. To in bashi 5M ɗinsa da ya ara mun tun ba zan sayar da gold ɗin ba. Na miƙe tsaye game da cewa. "Ka ɗauka a 5M da na baka before ka bani, yanzu kuɗaɗena saura almost 52M a wajenka, ina da buƙatarsu, lokaci ya yi da zaka bani su"......... Nan fa ya sake tamke fuska game da cewa. "Aisha ni kike bi bashin kuɗi har 52M? A yaushe kika bani su? Ke har kun isa ki mallaki tsabar kuɗi irin wannan?".
Na wani kallesa da mamaki, coz yaya ya ce kada in yi faɗa da shi, amma kun san zuciya bata da ƙashi, Abbie ya kawoni har wuya, bashi da tausayi bawan ALLAHN nan, ga bala'insa gana danginsa, na rasa in da zan tsunduma raina in ji daɗi, coz a yadda naga alama ma wlh Abbie ba zai biyani kuɗina, dan wlh Naira kafin ya fita daga hannunsa sai an kai ruwa rana, tun da ALLAH yasa ma samu wasu kuɗaɗen kafin auren Zainab, so I decided to leave him kawai, ya je shi ya sani, shiyasa kawai na faɗa mashi gaskiyar ba wata gold da zan ɗauko.
"Na ji bana binka 52M, amma ai kasan ina binka 5M ko? To ka ɗaukesa ka biya Sadiq kuɗinsa, sannan daga yau ka shirya ciyar da iyalinka dan yanzu ni bani da ko sisi, da wannan kayan abincin namu ya kare zaka fara ciyar damu"........ Ya zazzaro idanu yana kallona, na zo har wuya da abin da mamarsa ta mun ɗazun, haba, ban ji ba ban gani ba su dinga zagina, kome aka yi nice wani irin masifa ce wannan, to na gaji, ai ba dutse bane a kirjina.
Aikuwa da ya ga haka sai ya ce. "Habibiya anya yau wani aljanin bai taɓaki ba kuwa?"....... Zai mun muryar yaudara, dan yasan a wajena kawai yake samun kuɗi, idan na ga Abbie na lallaɓani wlh kuɗi zai karɓa, yanzu ma da alamar akwai abin da zai yi da kuɗi ne yasa ya zo kara tada mun hankali kan wanda danginsa suke mun, ya mai dani ATM.
Ban ce mashi komai ba, ina numfashin a hankali-hankali. Ya hau lallaɓani yana bani hakuri, abinku da mata da miji, na sauƙo kamar bai mun laifi ba, na sake fuska har muka zauna muka hau hira, ya dinga mun wannan ɗakin bakin nasa, da ace akwai kuɗi a account ɗina wlh da a wannan lokaci zai iya sake galaba a kaina in sake bashi, tsakanin mata da miji sai ALLAH.
Sai dai kashe yaya ya kwace kuɗina dukka, ga kuɗin shago ya daina shigowa account ɗina, yanzu kai tsaye account na yaya yake tafiya, ginina na ta ƙara nisa, yaya ya sakawa shagona ido sosai, ga online business nata tafiya sai dai mu ce Alhamdllh. To da ace yaya bai karɓi kuɗin nan ba, da na ƙara dankarawa Abbie, dan ya iya mun daɗin baki, tuni ya kwantar mun da hankali.
Muka ɗan taɓa hira, yana ta bugan ruwan cikina yana son sanin in da nike kai kuɗina, sai dai ALLAH da ikonsa ALLAH bai bani ikon na faɗa mashi ba duk yadda ya mun daɗi baki, sai dai na ce mashi yanzu babu kasuwa sosai ne, sai ya ce bari ya duba shagon nawa ko za'a samu 1M. Na amsa mashi da okey, ya mike ya fita, yana fita na kira Ahmad, na ce duk kuɗin da yake shago ya tattare ya bar bai wuci kuɗin Abaya guda ɗaya ba, ya ɓoye kuɗin.
Ya amsa mun da okey, muka yi sallama. Na buga uban tagumi ina mamakin irin mijin da ALLAH ya bani, wai ba zai iya ciyar da iyalinsa ba, ba zai sauke hakkin dake kansa ba, ya bar mun ragamar gidan na ɗauka ma ba zai kyaleni ba sai ya sake dawowa ya tatsi kuɗi daga jikina, na nisa tare da cewa ALLAH ya bani ikon cin jarabawata.
Na miƙe na shiga cikin room, yau wani irin sabon tunanin Ibrahim ya dawo mun, a lokacin da muke soyayya, wlh bashi da kuɗi kuma bashi da tsayayyen sana'a lokacin amma bawan ALLAHN nan ko kiransa na yi baya ɗauka sai dai ya katse ya kirani, a lokacin gidanmu sun fi nasu kuɗi sosai, ina iya saka katin 5k, amma Ibrahim ba zai taɓa ɗaukar kirana ba, idan na saka mashi kari yai ta faɗa, ya ce kuɗina nawa ne nashi kuma namu ne, in ce a'a kuɗina namune kamar yadda nashi ma yake namu.
Wlh Ibrahim ko kyauta na mashi irin na masoya sai ya nemi kuɗin abin da na saya mashi cikin dabara ya biyani, yana da zuciya baya son mace ya mashi sai dai yai mata, yau an wayi gari ya yi kuɗin da yake ta cewa zai yi kuɗi mu rayu cikin farinciki amma bana tare da shi, wani irin kuka ne ya zo mun, na kara jin na tsani auren da aka mun, na dinga buga kaina da jikin gado ina kuka.
A haka na kwana cikin ƙunci, washegari na gama tsara wankana, na shirya zan fita shopping, mayukan shafawana sun kare, and ina son zuwa wani shop na gyara a fara mun gyara dan watanni sun fara ja a cikin lokacin da na ɗebawa Abbie, zan yi sabon gyaran da zai tashi kai. Na shirya cikin tsadaddiyar abayata, na yi rolling veil, sai tashin kamshi nike yi, na fito parlo rike da Muhammad.
Na kwantar da shi a kan kujera ina ƙoƙarin gyara towel ɗin hannuna in ɗauke, lokaci guda na tsaya cak saboda wani irin bugawa da kirjina ya yi, na kalli Muhammad dake ta faman dariya dimple ɗinsa irin na takwaransa na lotsawa.
Slowly na ɗago da kallona zuwa bakin kofa, da sauri na wani dafe kirjina da ya buga da karfi tare da zama kusa da Muhammad, na lumshe idanuna kafin in ɗaga kai sama ina sauke numfashi a hankali. Na kai minti biyu a wannan hali kafin a hankali na motsa lips ɗina wajen cewa. "Nawan meyasa zaka mun hakan?
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 38