faɗawa Ahmad ya sawo mun, karshen wata ta zo duk cefenenmu ya kare shiyasa zan yi sabo.
Tamkar a mafarki haka ka ga Abbie ya shigo ɗakina dakinsa ɗauke da sallama, yana sanye da wata dakakkiyar shaddarsa sky blue, sai wani murmushi yake yi, uhm rabona da shi yau kwanaki takwas kenan.
Tabbas na ji ciwo a raina na rashinsa, amma ban bari ya gane ba, ina ganinsa na ce. "Sannu da zuwa"...... Sai ya ɗan yi jim, dan a irin kishina da ya sani ya yi tunanin bala'i zamu yi dan wlh ni mafaɗaciya ce sosai a baya, har kona gidansa na taɓa cewa zan yi in bai sakeni ba, amma lokaci guda komai ya canza na zama shiru-shiru.
Kun san masu sunan Aisha kishinsu a jini yake, akwai mu da kishi, shiyasa Abbie yake shakkar shigowa part ɗina tun da aka kawo Zainab, amma ga mamakinsa sai ya ga ko a jikina, ina ma kwance nai mashi sannu, shi ne ya ɗan yi jim.
"Habibiya ban ji ɗuriyarki ba kwana biyu". Ya faɗa dan yana son buga cikina ya ji a wani hali nike. Sai na saki murmushin da ya fi mun kuka ciwo, na kara danne zuciyata game da cewa. "Kai da Habibi bari, ina can busy ya ɗauke mun hankali, shago da jama'ar online suna neman haukatani, ka san yanzu mun buɗe page na shagonmu a TikTok da saurin sassa na media, shi ne jama'a ke neman haukatani da oders". Kuma da gaske nike yi, Ahmad ya bani shawara mun fara tallar kayanmu har online, ALLAH ya sanyawa abin albarka, ta ko'ina oders muke samu sosai, abubuwa sun kara gaba, amma number shago ne a kan page ɗinmu ba numberta ba, sai na nunawa Abbie kamar numberta ce a wajen dan ma yasan na shiga busy da gaske.
Wlh take a wajen jikinsa yai sanyi, bai tsammaci haka ba, sai ya ce. "Watau habibiya baki damu dani ba kenan? Yanzu baki kishina?"......... A raina na ce watau maza fa ƴan rainin wayau ne wasu, so yake da kenan in ta hauka a kansa, aikuwa zan yi maganinka, sai na mai da kai kamar bola, zaka gane Annabi Isa ba ɗan ALLAH bane Manzon ALLAH ne.
Na mike zaune tare da cewa. "Sorry Habibi, abubuwan ne dai suka mun yawa, amma kana raina, ban samu isasshen lokacin dogon tunani a kanka bane"......... Duk jikinsa ta kara sanyi, yana ta kallon kayan jikina, wandon jeans irin palazon nan na sanya, daga sama daidai da ƙayataccen shape ɗina, daga ƙasa kuma kafafun ya buɗe sosai, na sanya ɗan karamin t-shirt daidai da jikina, na tara gashin kaina na ɗaure a tsakiya, kwanciyar da na yi yasa gashin ya watse abinku da gashi mai tsantsi.
A cikin kwayar idanunsa na fahimci yana kallona abar tasa ta motsa, amma sai yai ƙoƙarin kaucewa, ya so daina kallona amma ya gagara. Sai ya ce. "Zu mu je parlo ina da magana dake"....... Mamaki ya ɗan kamani, maganar ne ba zamu yi a nan ba?.
Ya wuce gaba, sai da ya fita na sauƙo ƙasa na bisa da tunanin shi kaɗai parlon, ina shigowa na ga ashe shi da sodangi ne. Tun da na fito take kare mun kallo, taga ƴar caras kamar ita ta yi kanta.
Ni kam ina kallonta na ɗan yi murmushi tare da cewa. "Ai sai kace mun kai da sodangi ne"...... Na faɗa ina ɗauke kaina daga kallonta, ta wani saka wani matsatten t-shirt dan ta gwada mun tana da manyan breast tun da ya nuna mata ni bani da shi, ta fito da halittar kirjinta sosai, sai dai kuma ta ji kunyar saka wando dan babu kwankwason, sai ta sanya irin buje sket ɗin nan, and tana da katon tumbi wandon zai tona mata asiri shiyasa ta sanya sket, iya breast da ta san tana da su ne ta bayyanosu a waje.
"Sodangi sannunki da shigowa". Na faɗa ina jawo wayata. Daga ita har Abbie sun fahimci nifa su basu ne a gabana ba, abin nan yai masu ciwo, Abbie ya so ya ga ana faɗa a kansa, watau maza daɗi suke ji su ga ana faɗa akansu, ita kuwa Hajiya sodangi ta so ne na tanka mata da faɗa ta yayyaɓa mun magana na abin da Abbie ya faɗa mata a kaina, har ta shirya irin gorin da zata mun, sai taga bata gabana ma.
Jiki duk ya yi evening ta amsa da. "Yauwa ina kwana"........ Na amsa da. "Lafiya lou Alhamdllh ya bakon wuri? Nasan sai a hankali zai maki daɗi ki saba".
Sai ta yi maza ta capke da cewa. "Baby yana nan ai dole waje yai mun daɗin zama, ban wani ji baƙunta ba, tuni ya mantar dani cewa na bar gida"......... Na saki murmushin karfim hali tare da cewa. "Ai nawan jarumi ne, kasan dama ba zaki fuskanci wani kaɗaici ko damuwar baki gida ba, Habibi ALLAH dai yai maka albarka".
Zainab ta sake jin jikinta ya yi sanyi, coz ta yi magana ne dama dan ta baƙanta mun sai kuma dai ban ji haushin ba.
Abbie ya ce. "To yanzu dai zan fita, na zo ne in maku nasiha da ku haɗa kai".... Na jinjina kai alamar to, ya dinga mana nasiha, ya dinga janyo ayoyi da hadisai tamkar wani malamin masallacin juma'a, ni kam yanzu Abbie ya daina bani mamaki.
Sai da ya gama nasihar ne ya ce. "Ya batun rabon kwana? Yau my happiness ta yi kwanaki bakwai kamar yadda shari'a ta ce, yakamata ku raba kwanan nan ko?".
A natse na ce. "A'a Abbie, kaga ita Zainab bata saba da baƙon wuri ba, zata ji kaɗaici idan ka fara barin ɗakinta tun yanzu, dan haka ni na ci girma, ku je na baka watanni huɗu, ka kula da ita tun da kaga amana aka bamu"........... Da sauri Zainab ta ɗago ta kalleni, na ɗauke kaina tare da mai da kallona kan Abbie da murmushi ta kubce mashi, ko kunya bai ji ba ya dinga zuba mun godiya.
A lokacin kiran Abba ya shigo wayata zai faɗa mun sun yi nasara kuma sun sha south Africa, sai daɗi yake ji. Na miƙe tare da cewa. "Sodangi ga Habibi ki kula da shi, ka baku watanni huɗu, kafin wata huɗun ki mayar mana da shi kato yai kiba". Na nufi cikin ɗaki ina pick-up na call ɗin Abba.
Zainab ta bi baya da kallo, sai take jin tamkar ta kwace shape ɗin jikina ta sanyawa kanta, ita da take mace ma sai da ta ji na tafi da ita bare kuma Abbie da tun da na miƙe yake ta faman bin bayana da ido, yana jin kamar ya bini ɗaki, amma zuciyansa na ingiza shi cewa Zainab ma tana da abin da nike da shi.
Sai da na shiga cikin ɗaki suka dawo da kallonsu kan juna, Zainab ta wani watsa mashi harara kafin ta ce. "Da kake wani kallonta binta zaka yi ne?"...... Ya ɗan haɗe rai game da cewa. "Matata ce fa, kallonta ya zama laifi ne a wajenki?".
Ta haɗe rai sosai tare da miƙewa, ba wani respect ta ce. "Amma ai a ɗakina kake ba a wajenta ba bare ka ce hakan, sai ka bari idan ka dawo wajenta ka yi abin da ya fi kallo".
Shi ma ya miƙe, ga abar tasu ta motsa ga tana neman ɓata mashi rai, a kufule ya ce. "Babu wacce ta isa gaya mun ga abin da zan yi a kan matana, babu wani shari'a da ya shata mun layi kan ganin matata, dan haka ki kiyaye wannan". Yana kaiwa karshe ya wuce fuuuu ya fita. Ita ma ta bi bayansa tana zazzaga masifar wlh bai isa a ranar da yake ɗakinta ya dinga kallona ba, ai na faɗa maku Zainab bata da kunya, ba respect ta dinga gaya mashi magana.
Dama yana sama, ya zageta tas, har da ce mata yai. "Uban me na tsinta a wajen naki da zaki ce ke kawai zan dinga kalla kada na ganta? Kin san dai Aisha ta fiki komai, duk in da ake kiran mace ta kai nan, dan haka ki kiyaye"........ Cikin faɗa ita ma ta ce. "Wlh bata fini komai ba, idan ta fini komai ba zaka je ka auroni ba, da waɗan nan ƴan ƙananan breast ɗinta kamar mangoron ne ta fini komai? Ka buɗe idanunka da kyau ka kalleni".
Ya nufi shiga bedroom ɗinsu yana faɗin. "Da yake dakikiya ce ke sai kike tunanin cewa manyan breast su ne mace? Kina tunanin sune daɗin aure?!". Aikuwa ta sake cika tamkar zata fashe, ta bisa cikin bedroom ta hau zazzaga masifa.
Duk abin da suke faɗe ina jinsu saboda sun ɗaga murya, ina waya da Abba amma ina iya sauraransu, kuma shi ma Abban yana jinsu sosai, har yake ce mun. "Daga aure sai faɗa kuma?"....... Na ce. "Nawan babu ruwanka, kai dai faɗa mun yaushe zaka dawo".
Ya amsa da. "A'a Auntyna da ruwana fa, saboda kece silar faɗar ai, kin ɗauki wankar nan naki mai gigitarwa ko? Shi ne kika kunna yayana ko?". A wata iriyar murya mai wuyar fassaruwa ya faɗa, ba zaka iya gane a wani hali yake ciki ba, but na ji kamar ya yi maganar cikin mood mara daɗi.
Na ce. "A'a ni babu ruwana nawan, kawai dai faɗarsu suke yi"........ Ya amsa da. "To shikenan my Aunty, zan ɗan kwanta kaina yana ciwo, zamu yi waya anjuma". Bai jira amsata ba ya katse kiransa. Ni kam na kwanta ina jin su Abbie har barci yai awon gaba dani, ban san lokacin da suka gama faɗar ba. Around 12 ina cikin barci na ji kamar hayaniya a harabar gidan.
A hankali na waro idanuna, jiki ba kwari na miƙe na fito, sai na ga Ahmad tsaye a tsakar gida Zainab ta taresa wai side ɗinta zai kawo cefenen. Shi kam ya ce a'a side ɗina zai kawo dan ni na aikesa, shi ne ta hanasa wucewa, dan a tunaninta Abbie ne yai cefenen, shi ne ta zaƙe wai ba za'a kaimun ba, dan tana tunanin za'a kawo mun ne ni in raba mana, shi ne wai ita zata raba, ta tare bawan ALLAH ta hana shi shigowa ya kaso mun kayana, da motarsa ya zo, ya gama fito da kayan daga bayan motansa kenan ta fito, shinkafa ne bugu biyu, mai jarka ɗaya, manja ma ɗaya, sai kaji guda 20 da aka fige aka gyara aka zuba a ledoji bayan an daddatsasu, da su maggi, su curry, har su tumatir da zamu zuba a fridge, kifi da dai duk wasu cefene, shi ne take tunanin ai Abbie ne ya aiko.
Ina fitowa na ce. "Ahmad lafiya?". Idanuna duk barci. Zainab ta wani watsa mun harara, dama a sama take na abin da Abbie yai mata da safe, shi ne take neman kan wanda zata huce.
Ahmad ya ce. "Aunty na kawo maki saƙonki ne wai ba zai shiga da shi ba sai dai in bata ta raba maku, dama ku biyu ne saƙon?".......... Na juya na kalleta kafin in ce........
Kai jama'a yanzu wasan zai fara fa, an zo daidai wajen.
labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi.
QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥
LABARIN AISHA.🥹💔
PART 15
Ahmad ya ce. "Aunty na kawo maki saƙonki ne wai ba zan shiga da shi ba sai dai in bata ta raba maku, dama ku biyu ne saƙon?".......... Na juya na kalleta kafin in ce. "Kash sodangi, ai baby zaki ƙira a waya sai ya faɗa maki yadda tsarin gidan yake ba ki tsaya faɗa da ɗan aika ba, wannan ai zub da girma ne, ki kira babyn naki a waya zai faɗa maki cewa naki na hanya dan daban-daban muke ba ɗaya ba".
Ta kalleni cike da rashin fahimta kafin ta ce. "Ban gane daban-daban muke ba"..... Na ɗan yi murmushi kafin in ce. "Kin san ke amarya ce kuma sodangi, cefenenki zai banbanta da nawa, ina da tabbacin special babyn naki ya maki cefenen shiyasa bai haɗo a nawa ba, wannan nawa ne ni kaɗai kamar yadda ya faɗa mun a waya, ina ga zai taho da naki idan yana dawowa".
Sakaryar sai ta wani yi fari da ido, ta ji na ce ita amarya ce nata daban, ta watsawa Ahmad harara kafin ta ce. "Dole ma ya mun nawa cefenen daban ai tun da ko ba mata ba ni kanwarsa ce, jini guda, jini kuwa ya wuce wasa". ....... Na ce. "Haka ne sodangi, ai tun daga kan sunan sodangi za'a san jini ya wuce wasa". Na mai da kallona kan Ahmad. "Bro shigo mun da kayana lokaci na kurewa ban ɗaura girki ba, su Hassan sun kusa dawowa".
Ahmad ya ce okey, ya naɗe hannun riga ya fara jido kayan yana shigo da su ciki. Zainab ta juya ta koma parlonta tana watsa mana harara, sarai na ganta, amma nai kamar ban ganta ba, na yi wucewana ciki, ni ina naga lokacin faɗa da wata aba wai kishiya, haba Zainab, ai na wuce wannan level ɗin yarinya, cikin ruwan sanyi zan yi maganinki ne.
Ahmad ya shigo mun da kaya ya mun sallama ya tafi, na tsaya jim a cikin kitchen cike da tunanin yadda zan shirya kayan kowanne a muhallinsa, da ace Abba yana nan da shi zai shirya mun dan shi yake yi dama. Na dawo ɗaki na ɗauko wayata, ina fitowa kitchen sai ga kiran Abbie.
Na ɗan yi jim kafin in ɗaga. A natse na ce. "Babyn sodangi barka da rana"...... Ya yi kicin-kicin da rai, a dake ya ce. "Habibiya ban son wasa, bana mood mai kyau"...... Na ɗan zare ido kafin in ce. "Haba dai Habibi, ango fa kake, kai da farinciki kuma ai har abada kuna tare, ka manta ur happiness ɗinka tana tare da kai ne?".
A ƙule ya ce. "Aisha zan saɓa maki fa, na faɗa maki ba wasa nike yi ba ko?"....... Na kai tafun hannuna saman bakina na toshe dariyar dake shirin kwace mun kafin in ce. "Sorry babyn sodangi, awww sorry Habibi na manta ne, ALLAH ya huci ran uban Hassan da Hussain da Auta Muhammad Abbanmu ɗan albarka". Ina faɗa ina danne dariya.
Cike da bada umarni ya ce. "Ki yi girki dani dan ɓangarenki zan dawo yau"..... Da sauri na ce. "Kai subhanallah, a'a fa Abbie, wlh ban yarda ba, ina zaka baro mun ƴar kanwata sodangi? Gaskiya a'a wlh, ai kana tare da ita sai wa'adin watanni huɗun nan sun cika, ka manta na yarje maka watanni huɗu ne? Kuma ka manta a wajen ka ce in yi alƙawarin watanni huɗu in basu cika ba ba zan ce ka dawo ɗakina ba? Ka manta na yi alƙawarin? To gaskiya ni ba zan saɓa alƙawarin nan ba, dan haka ka koma wajen sodangi ur happiness". Ina magana dariya na neman fin karfina saboda iya shege da ya cika mun ciki, akwai wani shiri a ƙasa da nike da shi ne yasa na ce sai nan da wata huɗu zai dawo ɗakina.
Coz so nike sai ya koyawa Zainab hankali, saboda ni nasan halin kayana, ba ita mai bakin cewa zata iya ɗaukesa ko sau hamsin a rana bane kafin su yi aure, to anyi auren, dan haka su je su ƙarata, a watanni huɗun nan bana son ta samu hutu, sai ta gane ALLAH da girma yake in dai Abbie ne, yaushe zan yarda ya dawo ɗakina ya tara mun gajiya ita in bata hutu? Ai wlh su karata, a rana yai mata service ko sau 7 ne, duk wani ruwan jikinta sai ya karar mata, sannan ne zan bata mamaki, duk abin da take taƙama da shi zan gwada mata na fita bayan wannan wata huɗun, shiyasa na ce su je su ƙarata, ina nan ina wani shiri na bayan wata huɗun.
Abbie ya ce. "A'isha wai yaushe kika raina ni ne?"........ "A'a babyn sodangi, ni fa ban rainaka ba, nama isa in rainaka, wane ni, kawai dai na tuna maka da alƙawari ne"...... Ya ƙara haɗe rai. "To ki dai yi girki dani a kawo mun side na Zainab ɗin".
Na yi maza na ce. "A'a Habibi, kana part na ur happiness kuma ka ce zaka ci abincina? Wai Abbie ka manta Zainab ce mace da ta fi kowa iya girki?"...... Coz a chat ɗinsu na gani yana ce mata yasan ta fi kowacce mace iya girki, ya ƙosa ya ɗanɗani girkinta.
Muryansa da alamun ɓacin rai ya ce. "Babu wani abin da ta iya sai surutu, please matar kirki ƴar aljanna dan ALLAH ki shirya mun delicious a kawo mun side nata". Da alamar rarrashi a muryansa....... Na kuwa murzawa idanuna toka, na ce. "Abbie, abin da baka so ayi maka kada ka yi wa wani, ba zan so kana ɗakina Zainab ta kawo maka girki ba, dan haka nima ba zan mata hakan ba, kuma wannan abin da kake shirin yi kana buɗe kofar faɗa da rashin zaman lafiya ne a tsakaninmu, dan haka please ka bari nasan kasan abin da yake daidai da ba daidai ba". Ina kaiwa nan na katse kirana ban jira amsarsa ba.
Haba zama nai kan kujerar parlo na fashe da dariya, cikin dariya na ce. "Su sodangi manya, sarauniyar iya girki, ai daga ganinki rusheshiyar nan ma yaushe zaki iya girki, ba zaki iya juriyar jeka ka dawo na duba girki ba, dan zama dakyar tashi da kyar dole ki yi girkin minti 40 a minti biyar kacal dan a huta da zaryar kitchen, to haka ina girki zai yi daɗi?". Ina magana ina dariya ni kaɗai kamar wata zararriya.
Sai da kira ya shigo wayata ne sannan na taagaita game da saita natsuwata, na yi pick-up tare da karawa a kunne, har yanzu da sauran murmushi a kan fuskata na ce. "Nawan ka tashi daga barcin ne?".
Ya sauke ajiyar zuciya game da cewa. "Alhamdllh, yau ɗaya dai na ji alamar farinciki a tattare dake, to ba zan tambayi dalili ba dan nasan bai wuce yayana ne ya sakaki farincikin ba, yanzu dai duk ba wannan ba, please my Aunty me sizes na abayar Safiyya?".
Na nisa tare da cewa. "Eyye kyautar masoya za'ayi mata?"........ Ya amsa da. "Wuce nan ma, ya fi karfin na masoya sai dai na mata da miji"........ Ƙayataccen murmushi ya kubce mun, coz ina son ganinsu tare wlh, bana duba fitinan danginsu nike son kanwata ta shigo cikinsu bayan nima ban iya zame kaina daga wahalar ba, saboda kaunar Abba da nike yi yasa kawai ban damu da fitinar danginsu ba.
Na ce. "Eyee, manya-manyan maganin ƙanana, to yanzu dai ka saya mata sizes ɗin nawa, dan kaga tsawonmu ɗaya, kiba ne ta ɗan fini kaɗan"........ Ya nisa tare da cewa. "Na san tsawonku ɗaya, ai ke ma ban san sizes ɗin naki bane shiyasa na tambaya".
"Kai nawan, yanzu sizes ɗina ne baka sani ba?"......... "Please my Aunty dena ja mun rai ki faɗa mun da wuri kin ji? Kin ga dai ina kasuwa ne". A shagwaɓe tamkar zai yi kuka ya faɗa, coz yana kasuwa ya gaji da tsayuwa........ Na faɗa mashi sizes ɗin kafin in ce. "To waye ya baka kuɗi da har zaka yi wa wata kyau?".
Shiru ya ɗan yi, yana zaɓan kaya, sai kuma ya ce. "Watarana sai na maki bazatar kujerar Makkah my Aunty"........ "ALLAH yasa my ɗan ƙanina"......... Uhm ya ce instead of ya ce Amin, wai na ce mashi ɗan ƙanina, duk in na ce mashi haka baya amsani, na fahimci hakan amma ban wani ɗauka yana jin ciwon kalmar ba, na zaci kawai ayi sha'ani ne.
Na ce. "To sai an juma zan je in yi girki".... Ba dan ya so ba muka yi sallama, da farko cewa yai mu yi video call ina girki yana tayani hira shi ma yana sayayya, na ce a'a zai ɓata mun lokaci ya hanani girki kan lokaci, hakan yasa ya hakura muka yi sallama.
Na tashi na shiga kitchen, a natse na hau shirya kayan nan, sai da na kammala tas, sannan na gyare kitchen ɗin kafin in hau aiki babu kama hannun yaro. Around 2 na kammala girki, na tsara wankata mai kyau, na fito ɗas dani, ina masifar son ƙananan kaya, shiyasa duk kayayyakina ƙanana sun fi yawa, in dai ba fita zan yi na ba'a cika ganina da manyan kaya a gida ba.
Yanzu ma wandon jeans wanda yai daidai da halittar jikina na sanya, ya kamani sosai, hips ɗina tamkar zasu fasa wando, sai riga mai dogon hannu mai naushi zuwa ƙugu, na gyara gashin kaina, sannan na sanya hijab har ƙasa na tada sallah, bayan na idar na ɗauki Muhammad na tsala mashi wanka, na gasa mashi jiki da ruwan zafi kafin in shiryasa. A haka yarana suka dawo daga school Fahad ya ɗaukosu. Na rungumesu cike da nuna so, nai masu wanka na basu abinci, suka ci suka yi salla nai masu shirin islamiya.
Suna fita zuwa islamiya sai ga Hajiya sodangi ta shigo ɓangarena babu ko sallama. Ina zaune a parlo na ɗaura kafa ɗaya bisa ɗaya na ɗago na kalleta ban yi magana ba. Tana wani yatsina fuska ta ce. "Aisha ashana zaki bani zan kunna gas".
Na ɗan yi shiru na ƴan sakanni kafin in ce. "Ni bana using matches, gas ɗina automatic ce"........ Ji ta yi gabanta ya faɗi, da ta raina ni, tana tunanin ta fini kayan aiki masu kyau, bata san kujerun parlona sai sun sayi nata sau huɗu zuwa biyar ba, coz nawa Turkish ne, foreign ne ba na Nigeria bane, nata bugun kafintar unguwa ne, shiyasa naki canza kujeruna ai, dan wannan na aurena ne, a lokacin ma kujerun kawai 4M iyayena suka saya, ita kuwa nata ƴan 700k.
Ta haɗe rai game da cewa. "To yanzu ya zan yi, dame zan kunna gas ɗin?"...... Na wani kalleta kallon rainin wayau kafin in ce. "Ki kira baby ya kawo maki ashanar mana, ke amarya ce kome kike so ai dole ayi".
Ta kara haɗe rai kafin ta ce. "Uhm ai fushi yake da ni"....... Na ce. "Toooooh, fushi kuma?". Ta gyaɗa kai. Sai na ce. "Kai amma babu daɗin ji, gaskiya shawarar da zan baki shi ne ki yi maza ki kirasa ku sasanta, ban da abinki waye ya ce maki ana faɗa da miji? Kin manta ko ba aure shi yayanki ne? Sodangi fa kike, shalelen dangi, gaskiya ki kira baby ku sasanta, kada ki bari ya rainaki mana, ai zai ja maki raini kina faɗa da shi haka daga sabon zuwa".
Zainab jiki ya kara evening, ta rasa gane in da na dosa, tana jin kamar ta zubar da makaman yakinta tun da taga daga ita har Abbie basa gabana, ta fara yarda ni mai sonta ce da gaske, bata yi zaton zance ta shirya da mijinta ba...... Ni kuwa na faɗa mata haka ne saboda bana son basu komai ƙanƙantar kofar da zai sanya su zargi ina kishin Abbie, shi ne nike nuna masu ban fa damu ba, shiryasu ma zanyi idan suka yi faɗa tsabar baya gabana.
Aikuwa ta ce ta gode da shawara, tana fita ta koma ɗakinta ta ɗauki waya ta kirasa, yaƙi ɗaga kiranta, dan wlh shegen zuciya ne dasu Abbie, in suka yi fushi sai ka sha fama zaka shawo kansu. Ta kirasa ya fi sau 20 yaki ɗagawa, daga baya ya kashe wayansa.
Hajiya sodangi sai aka gagara hakura, ta kira Mama ta faɗa mata Abbie yana fushi da ita, Mama ta ce ta yi hakuri zata kirasa ta mashi faɗa. Abbie dai bai sake kunna wayansa ba kuma bai shigo gidan ba sai 9 na dare shi da yake dawowa 5 na yamma. Yana dawowa ya wuce part ɗinta, ina jinsu ta tashi tana mashi sannu da dawowa, yai banza da ita ya wuce ciki, dan already ya ci abinci a waje abinsa, tun da na ce ba zan girka da shi ba ya biya Restaurant.
Zainab ta fito waje ta je ta dinga leƙa cikin motarsa wai ko zata ga kayan cefenenta, sai ta ga wayam, da sauri ta dawo ta bisa cikin bedroom. A lokacin yana wanka, gagara zama ta yi sai ta bisa cikin toilet ɗin.
Ya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 38