Share this page
a ɗakin Hajiyarmu kuma na ɗauki wayar Safiyya, dan haka na biya kuɗin Mota sai kama hanyar Abuja, uwa da ƴaƴanta, ba zan iya hakura in barsu a hannunsa ba, ko da zan sara saina sai na karɓosu. Gida basu tashi sanin bana nan ba sai around 12 na rana, a lokacin Safiyya ta je kirana in zo in yi breakfast, sai taga bana nan, while ni a lokacinma na kusa kaiwa Abuja, nan suka fara nemana, amma ina, ba'a ganni ba, hankulansu ya tashi, suka dinga kiran wayan Safiyya dake hannuna amma naki ɗagawa. Intakaice maku sai da na shiga Abuja na fara neman number Abbie, amma a kashe, sai na tuna wata tsohuwar numbersa da yake amfani da ita, number ce ta gidansa kawai, aikuwa ina kiran wannan number ta shiga ya fara ringing. Sai da ta kusa katsewa aka ɗaga, yana cewa hello na gane shi ne. Cikin tsananin tashin hankali na ce. "Sulaiman ina yarana?"....... Daga ɓangarensa na ji ya fashe da dariya mai ɗan sauti kafin ya ce. "Yaranki ko yarana A'isha?". Ashe shi ma ya gane muryana. Cikin faɗa na ce. "Wlh ka bani yarana ko kuma ka yi danasanin sanina a rayuwarka"......... Yana dariya kaɗan-kaɗan ya amsa da. "To shikenan zoki karɓi yaran naki mana, ina nan a gidan dake kusa da naki gidan, dan nasan ko ba ji ma ko ba daɗe zaki zo neman yaranki shiyasa na kama hayan gida a kusa da naki dan jiran zuwanki". Aikuwa jikina ka rawa na ce gani nan zuwa, ban kawowa raina komai ba face yarana, ban yi tunanin za'a cutar dani ba, kawai yarana nike so, aikuwa na samu abin hawa na hau, kai tsaye na je wajen gidana na tsaya, na sake kiransa a waya, ya ce in zo cikin wannan gida dake wajen gidana yana ciki yana jirana. Ba tsoro na nufi gidan, na tura gate na shiga, babu mai gadi, ina ta tunanin yadda zan ga yarana, su nike kallo a idona, musamman Hussain, a rana ta karshe rabuwana da shi ranar da yake damuna da surutun zan samu lafiya na ce mashi eh, tun daga ranar nan sake ganinsu ba...... Na nufi kofar shiga parlon gida, tsabar sauri ko addu'a ban yi ba na faɗa cikin parlon. Babu kowa a ciki sai na haura sama. Ina haurawa na tsaya ina kalle-kalle, sai na ciro wayan Safiyya zan kirasa kenan na ga an buɗe kofar kusa dani, Abbie ne ya buɗe ya fito. Yana sanye cikin dakakkiyar shaddarsa fara tas mai shegen kyau, Zainab na biye da shi a bayansa suka fito. Wani irin kallon taƙaici da tsananin tsana na dallah mashi kafin in ce. "Ina ƴaƴana?"....... "Ƴaƴanki ko ƴaƴana Aisha?". Ya faɗa yana kare mun kallo. Zainab ta ce. "Uwar gida haka kika dawo duk a fige kamar ƴar yunwa? Ina kyan jiki da shape mai kyau ɗin? Ko dai kin shiga wani hali ne mu taimaka maki?"...... Ko kallon in da take ban yi ba, tana rike da wani yaro mai kama da ita wanda ko ba'a faɗa ba kasan ɗanta ne. Zan sake yin magana daga bayana na ji ance. "Zo ki wuce ki kyalemu da shi"...... Da sauri na juya dan ganin wanene? Sai naga babban yayanmu a tsaye tare da ƴan sanda. Da gudu na juya na sauƙo ƙasa, na zo na rike babban yayanmu ina kuka ina faɗin ya rokanmun shi ya bani ƴaƴana, Yayanmu ya ce in je Yah Abbas yana waje zai mai dani gida, ƴaƴa kuma sai sun kawo mun su har gida. Dama ashe suk fitan da na yi babban yaya da Yah Abbas suna kallona, kuma sun bi bayana, dama sun shirya tarkon kama Abbie ne, ga shi kuma sun yi nasara. Suka kama shi ni kuma suka mai dani gida, sai kuka nike yi ina ni dai a bani yarana. Daddynmu ya shigar da Abbie karar ya aura mashi yarinya ba da saninsa ba, suka ta buga shari'a, daga karshe dai kotu tasa Abbie ya sakeni tun da daddynmu ya ce baya son auren, sannan kotu ta umarci Abbie da ya fito da yaran mamarsu ta gansu, nan fa Abbien ya ce ALLAH ya yi wa Hussain rasuwa saura Hassan shima bashi da lafiya yana asibiti. Kotu ta nemi jin me ya kashe Hussain, ya ce haɗari suka yi shi da kawunsa Abba, dukkansu ALLAH ya masu cikawa, a motar Hassan ne kawai ya fita a raye. Bincike kotu ta yi dan tabbatar da gaskiyar lamarin, sati ana bincike, nan kotu ta gano da gaske ne lallai Abba da Hussain and Hassan sun yi haɗari shekara ɗaya baya, lallai duk abin da Abbie ya faɗa gaskiya ne, Abba da Hussain sun mutu saura Hassan. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, a lokacin da na ji wannan labari zarewa ne kawai ban yi ba, duk cikin yarana na fi son Hussain saboda wayonsa da iya zaro zancensa, yaron nan akwai ilimi da hankali, uwa uba mutuwar Abba, ta yi bala'in gigitani, a lokacin da na samu labari sai da na suma tsawon kwanaki uku ban san in da kaina yake ba, har aka gama zaman kotu Abbie ya biya abin da zai biya ni bana cikin hayyacina, lokacin da na farfaɗo an kammala komai, damuwa sun cunkusu a raina, abubuwa sun mun yawa. Gudun kada na kamu da wata cuta yasa daddynmu yanke shawarar fitar dani waje in koma makaranta, a cewarsa idan na yi nisa da gida zan manta abubuwan da suka faru, Hajiyarmu ta yi na'am da wannan shawara, su suka shirya nema mun makaranta. Sai dai kuma a lokacin da suka fahimci ban yi University ba sun yi mamaki, domin kuwa a farkon aurenmu daddyna ya buƙaci da na koma makaranta, ya tura mun kuɗi in yi rijistar Jamb in rubuta, a wannan lokaci ne na sadaukar da karatuna na barwa Abba, a maimakon in yi sai na biya mashi ya yi, a lokacin ban fara sana'a ba, iyayena ne dama zasu ɗauki nauyin karatun, so lokacin da ya ci jamb iyayena suka biya kuɗin registration da sunan ni suka biyawa ba tare da sun san wani nike biyawa ba. Duk tunaninsu ni nike karatu, da na zo na fara sana'a sanaar ta yi karfi sai na ce su bari zan dinga biya, a lokacin Abba yana three hundred level, da ace na ga dama da a lokacin ni ma zan shiga school, amma sai na mai da hankali kan business, to duk tunanin iyayena na gama University, sai suka ga iya secondary ɗin ne. Daddynmu ya ajiye ni ya tambayeni, nan na faɗa mashi gaskiya, ya ji takaici, ya dinga faɗa, ya ce meyasa ban ce ya biya mun ni da Abban a tare ba, ai da zai biya, yanzu na ɓata tsawon shekaru a banza a zaune a gida, babana ɗan boko ne sosai, so yana son karatu matuka. Na dinga bashi hakuri, da kyar ya hakura ya ce bari a nema mun hanyar samun University a can kawai. In takaice maku labari kada ya yi tsawo dan akwai labari a gaba. Bana son fita ƙasar waje, amma haka na hakura iyayena suka turani Germany karatu. Farkon zuwana ƙasar bana gane komai a makarantar, and naki zama a hostel, dole daddy yakama mun gidan haya a wajen makaranta, kullum ina cikin kuka da tunanin yarana, daddy ya yi alƙawarin karɓo mun Hassan daga hannun Abbie, amma Abbie yaƙi ya bashi, daga karshe Abbie ya shigar da daddy kara wai zai kwace mashi yaro, to kun san dai uba shi ke da yaro, dole daddy ya hakura ya bar mashi ɗansa. Abbie ya ce wai idan ina son yarona to in dawo gidansa mu cigaba da zaman aure, daddyna ya ce a'a ya rike ɗan nasa kawai. Muhammad dai yana hannun Hajiyarmu, Abbie ya so kwace yaron, amma Hajiyarmu taki bashi. Kullum muka yi waya da daddy sai na tamnayesa ya karɓomun Hassan sai ya ce a'a zai karɓo shi in kara hakuri, daddyna ya gaza iya faɗa mun cewa ba zai iya kwato mun ɗana ba dan Abbie uban yaron ne, sai kullum yai ta kwantar mun da hankali da sunan zai kwato mun shi, babban abin haushin kunga iyayena basu yi rabuwar daɗi da Abbie ba, har kotu aka shiga, shiyasa Abbie ya hana ɗan dan ya kuntata rayuwata sosai. Yanzu haka Hajiyarmu ta ce in Muhammad ya kara shekara biyu ya kai shiga school za'a kawo mun shi Germany, dan haka in kwantar da hankalina in yi karatu. Kullum sai na yi kuka ina yi wa Hussain and Abba addu'ar ALLAH yai masu rahama. Lokaci ya ja, abubuwa sun canza, na fara mai da hankali a kan karatuna a fannin likitanci, na canza, na kuma fara mai da kyau da jikina, na yi wata ƙawa mai suna Zahra, kyakkyawar balarabiya mai kyan zuciya, bata da son hayaniya, halinmu ya zo ɗaya shiyasa muke abota, ita ba fanni lafiya take karatu ba, benenmu ne ɗaya da ita yasa muka kulla abota, ɗakinmu na kallon na juna, ita a ɓangaren wassanni take, mayyar buga snooker ce sosai, kullum tana zuwa gidana dan ɗebemun kewa, asalinta ƴar ƙasar Qatar ce ta zo Germany karatu, so ita ma ita kaɗai ce a gidanta shiyasa bata zon zama take zuwa wajena mu zauna, na fara rage damuwar dake raina. Yau takama weekend, ba makaranta, ina zaune a parlona sanye da hoodie baki a jikina, Zahra ta zo tana kitchen tana haɗa coffee, mayyar girke-girke ce yarinyar nan, ba zata wuceni a shekaru ba, watau bata wuce 22 years ba, akwaita da son girki sosai. Wayata ne na ji ta yi ƙara a ɗaki. Na mike na shiga ɗaki, na yi mamakin ganin baƙuwar number kuma daga Nigeria, kamar ba zan yi picking ba, sai kuma na yi pick-up. A ɗan tsorace na kara wayar a kunnena game da cewa. "Hello"..... Jama'a yanzu mugun tsoron mutane nike ji sosai da sosai. Daga can wani sanyayyan murya ya ce. "My sarauniya fatan ban tasheki daga barci ba?"..... Na yi jim ina ɗan tunani, sai kuma na ce. "Ibrahim"....... Ya ɗan yi dariya kaɗan kafin ya amsa da. "Ashe ba zaki taɓa mantani ba Aesh?"........ Na sauke ajiyar zuciya game da cewa. "Har abada Ibrahim, ba zan taɓa mantaka ba, ina wuni?"........ Ya sauke ajiyar zuciya mai nauyi kafin ya amsa da. "Lafiya lou sarauniyata, ya karatu?". "Uhm, waye ya baka numberta?"....... "Da sauri haka? Ai kya bari mu gaisa ko?".... Na ɗan nisa tare da cewa. "Ai gara in sani ne"........ Ya ce. "To babban yaya ne ya bani, na takura mashi da zuwa gida neman numberki shi ne ya gaji ya bani, tun dare nike ta faman kiranki baya shiga, sai yanzu asuba ya shiga, ko barci na gagara yi dan fatan samunki a waya"....... Na kalli agogonmu a 6:30 na safe, su kuma Nigeria yanzu 5:30, dan awa ɗaya ne ratan lokaci a tsakaninmu. A natse na amsa mashi da. "Uhm, to shikenan nagode sosai, ina ɗan aiki ne yanzu, zamu yi magana wani lokaci". Ban jira amsar shi ba na katse kiran. Na tsaya shiru ina tunanin rayuwa, sai na ji ƴar kara kil a wayar, saƙo ne ya shigo a Whatsapp. A natse na shiga dan dubawa. Number Ibrahim ne, da ɗan sauri na shiga, lokaci guda na ɗan zaro idanu. Ya turo mun hotonsa shi da Muhammad ɗina a cikin gidanmu, ya ɗaura Muhammad a kan bayan motansa ya masu selfi, sai dariya Muhammad yake yi yana wasa da suman kan Ibrahim. Wani irin fari na ji zuciyata ta yi, lallai ne maso uwa ya so ƴaƴanta, sai na ji wani irin sabon son Ibrahim a raina. A ƙasan hoton ya rubuta mun ya kika ga yarona yadda ya girma ya kara kama da mamansa Queen of Beauty. Murmushi ne ya kubce mun wanda na jima ban yi irinsa ba, na dinga kallon hoton ina karawa tamkar zan lashesu, sun yi kyau sosai tamkar in kirasu su amsa. Lokaci guda kuma na tuna da Hassan dake hannun Abbie, sai na ji wani irin ɗaci da ɓacin rai ya ziyarci zuciyata, take na ajiye wayar na fice daga ɗakin ina jin ruwan hawaye na ƙoƙarin zubowa daga idanuna. Na zauna a kan sofa, na buga uban tagumi, sai na hau tuna lokacin da nike tare da Abba, na fara tuna yadda yake kula dani, yadda yake son yarana, idan ina mashi magana yadda yake mun wani irin kallon ƙasan ido mai tafiya da zuciya, sai yanzu ma nike tuna wasu kallon da Abba yake mun wlh na zallar kauna ce, sai ma idan na ce nawan, in ya ɗan ɗago. Na tuna ranar da Abbie ya rufe mu a ɗaki, yadda na bashi cin-cin a baki, a yadda ya kwantar da kansa a kan sofa yana mun wani irin kallo ya Salam, a lokacin duk ina firgice bana gane komai, sai yanzu yanayin kallon yake dawowa raina, tabbas wancan rana kallon da yake mun idanunsa cike suke da sirrin dake zuciyansa, ya lankwaɓar da kansa jikin sofa, shagwaɓar da ya mun a ranar har cikin raina na jita, har yanzu da na tunata sai da zuciyata ta amsa. Wani ɓangare na zuciyata ta ce me Abba ya faɗawa Hussain dangane da bakina ranar, ya ce in bisa bashi, ga shi bai faɗa mun ba har ya koma ga ALLAH. Wasu zafafan hawaye ne suka fara wanke mun fuska, tamkar an buɗe tap haka hawayena suka fara zubowa............ SORRY TEAM ABBA, ALLAH YAI MASHI RAHAMA SHI DA HUSSAIN!. To maza masu raba mata da ƴaƴansu wai dan sun saki matan sai su kwace yaran, wlh ku ji tsoron ALLAH, ku sani raba uwa da ɗah sai ALLAH, wai dan ku kuntatawa mace sai ku ce ta baku ƴaƴanku, ku baku tunanin ALLAH yana da hanyoyi da dama da zai kuntata maku ne ku? Wlh ku bari babu kyau, ku tausayawa uwa, kada ku rabata da ƴaƴanta kome zata maku, ku sani duk abin da kuka yi wa wata za'a maku watarana, babu abin da ya fi yi wa mace ciwo a duniya irin a rabata da yaranta, dan girman ALLAH ku daina wannan zaluncin, ku ji tsoron ALLAH ku bari, ku sani ko kun rabata da yaran nan muddin suka girma zasu nemeta, kuma idan suka ji abin da kuka yi mata ba zasu taɓa ganinku da daraja ba, ba zasu girmamaku ba, kuma ku sani ko a cikin kabari uwa take muddin ƴaƴanta suka girma sai sun je wannan kabari dan ganawa da ita, to meyasa zaku zubarwa da kanku girma da kima wajen rabata da ƴaƴanta wanda kun san in sun girma ko mutuwa zaku yi sai sun je in da take. labarin A'isha zai dinga zuwa maku labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi. FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥 LABARIN AISHA.🥹💔 PART 25 A haka Zahra ta fito daga kitchen ta zo ta sameni, a kusa dani ta zauna tana faɗin. "Kin sake tuna gida ko?"......... Ban taɓa bata story ɗin rayuwata ba, kawai dai idan na tuna ina kuka sai in ce mata gida na tuna, ta yi ta rarrashina. Yanzu ma haka ta dinga rarrashina har na yi shiru, ta bani coffee naki sha, saboda abin da Abba ya fi son sha kenan ko black tea, in dai zan sha sai na dinga tunasa, shiyasa na daina sha. Da ta ga na yi shiru ta zauna a kan sofa tana shan coffee ɗinta tana ƙara rarrashina. Miƙewa na yi na koma ɗaki, wayata na ɗauko na dawo parlo. Zama na yi tare da laluɓo number Safiyya. Bugu ɗaya ta ɗauka, na saita natsuwata kafin in ce. "Sofia".... Ta amsa da. "Aunty ina kwana ya makaranta?". Na amsa da. "Lafiya lou Alhamdllh ina su Hajiyarmu?"........ Ta amsa da. "Suna ɗaki nima yanzu na idar da sallar asuba ina son komawa barci"......... Na ɗan nisa tare da cewa. "Kina da hotunan Abba da na su Hassan ne?"......... Ta ɗan yi shiru, sai kuma ta ce. "Bani da hoton Abba shi kaɗai, duk hotunan da yake turo mun a lokacin da muke tare to a tare yake da su Hussain, bai taɓa hoto shi kaɗai ba ya ce mun". Muryata har tana sarƙewa wajen cewa. "Turo mun su yanzu please, dukka zaki turo mun"......... Ta amsa mun da okey, muka yi sallama, kai tsaye na shiga Whatsapp cike da matsuwar son ganin hotunansu. Tana turo mun jikina har yana rawa wajen buɗewa, wani irin dogon numfashi na ja a lokacin da na fara cin karo da kyakkyawan fuskansa, Hussain yana sumbatarsa a kumatu, Hassan uban ƴan miskilanci yana gefe ya saƙalo wuyan Abban fuska a haɗe. Ji na yi tamkar in kirasu su amsa, haka na dinga bin hotunan one by one, almost hotuna 30, kuma dukkansu Abba yana tare da yarana, lallai ba shakka duk wanda zai so yarana, tabbas ya biyo bayan Abba, yana sonsu tamkar yaransa ne, sun saba sosai. Na jima ina kallon hotunan kafin in ajiye wayar, na sake buga uban tagumi ina kallon fuskan Zahra dake aikin dannar waya, ƙwaƙwalwata ta fara tunano mun kalaman Abba. Na tuna watarana dana taɓa tambayarsa nawan me plan ɗinka game da aure, and me ka tsarawa matarka?. Amsar da ya bani ta tsaya mun a rai, tabbas a ranar na ji cewa da ma ace nice matarsa, daga lokacin na yanke hukuncin haɗa shi da safiya, dan ina mata kwaɗayin ta rayu tamkar sarauniya. A lokacin yana tayani aiki a kitchen ne, ya ce mun plan ɗinsa a kan aure shi ne, matansa zata rayu tamkar sarauniya, kuma shi ba zai zauna da ita a in da wani ya sansu ba, waje mai nisa zai kaita wanda kafin azo wajensu sai an jijjiga, kuɗin mota kawai ya ishi mutum, can zai kaita, saboda baya son a takurawa matarsa, yana son ya samu wani wajen da babu wanda ya sansu, a nan zai ajiyeta, ba zata dinga fita yawo ba, in kuma zata fita, kafarshi kafarta, zai kaita ya kuma dawo da ita, a shekara zata je ganin gida sau ɗaya, yara uku kamar nawa zasu haifa, and zasu raba aikin gida tare, zai yi rabi ta yi rabi, kuma shi mace ɗaya yake so, baya son hayaniya and baya son a cika gida da yara, ya fi son yara ƴan daidai wanda gabaɗayansu zasu samu lokacin mahaifinsu da kulawansa, zai na masu lesson a gida da kansa wanda idan yaran suna da yawa ya tabbata ba zai basu ishasshen lokacinsa dukkansu ba, amma idan su kaɗan ne zasu samu ingantaccen tarbiya a wajensa tamkar dai yadda ya baiwa Hassan da Hussain tarbiyya, so shi ma yara uku sun ishe shi. Uhm, na ɗan yi jim, sai kuma ka tuna ranar da ya dinga cewa ba zai shigo parlo ba sai na wuce ɗaki, tabbas a wannan rana ban fahimci nufinsa ba, a yau na fahimta, na tuna yadda fuskansa ta koma wancan ranar. Nannauyar ajiyar zuciya na sauke game da miƙewa tsaye, na koma ɗaki na kwanta, na rungume pillow a kirjina cike da kewar Abba and Hussain, da haka barci yai awon gaba dani. ---------------------- A can gida Nigeria kuwa, izuwa yanzu su Mama sun gama gane cewa Abbie dai ba shi ya rikesu ba a baya, saboda yanzu duk da ya dawo baya taimaka masu da kyau, ko Mama ta faɗa mashi basu da abinci sai ya ce bashi da kuɗi, idan ta matsa sai ya tura mata dubu ɗaya, ya ce iya abin da yake da shi kenan, kuma karya yake yi, kawai baya son kyautata masu ne, yanzu haka suna cike da danasanin abubuwan da suka mun, domin Fahad ya faɗa masu duk abin da suka ci a baya nice nan mai saya masu ba Abbie ba. Mama ta wanke kafarta ta zo gidanmu domin ta nemi in yafe mata, sai dai bata sameni ba, Hajiyarmu ta ce bana ƙasar, kuma Hajiyarmu taki kirana ta haɗamu, dan bata son wani abin ya sake haɗani da dangin Abbie, Mama ta ce yaushe zan dawo Hajiyarmu ta ce ba zan dawo ba, na koma can da zama sai dai su kai mun ziyara. Sai Mama ta ce to a bata numberta, Hajiyarmu ta ce babu waya a hannuna, Hajiyarmu akwai zafi, bata son rainin wayau sam, duk yadda Mama ta so haɗuwa dani ko a waya ne Hajiyarmu ta hanata, ta toshe duk wata hanya. Haka Mama ta ce to idan an sameni dan ALLAH a faɗa mun tana neman afuwata. Hajiyarmu ta ce to zata faɗa, amma bawai zata faɗan bane, kawai dan ta rabu da Mama ne yasa ta ce, dan ta yi alƙawarin ba zata bari wani abin da ya shafi danginsu ya sake haɗa hanya dani ba, su Muhammad babu yadda zata yi da su ne, da akwai da ta raba kawai. Haka Mama ta koma zuciyarta cike da danasani. Tana komawa ta ɗauki waya ta kira Zainab tana tambayarta ina Abbie wayansa a kashe tun jiya. Aikuwa Zainab ta ce. "Ban san in da yake ba"......... Mama ta ce. "Ina kiransa baya shiga, idan ya dawo ki faɗa mashi wlh ko abin da zamu ci yau bamu da shi". Ba kunya ba tsoron ALLAH Zainab ta ce. "Haba Gwaggo haba Gwaggo, wai ku meyasa baku son barin gidajen ƴaƴanku su zauna lafiya ne? Yanzu kina son ɗan kuɗin da muke da shi ɗin mu ɗauka mu dinga ciyar dake da su Amina ko? To mu kuma mu ci me? Ƴaƴanmu su ci me? Kada ki manta zai biyawa ƴaƴanmu kuɗin makaranta, ga ciyar damu, gaskiya yakamata a dinga ɗan dubawa Mama, ai yakamata ku dinga jin kunyar wasu abubuwa, su Amina duk su je su yi aure su koma ƙarƙashin kulawar miji ba kulawar yayansu ba, shi ma yayan nasu yana da iyalinsa!". Mama kam ta saki baki kawai tana sauraron Zainab na zuba mata masifa, sai ta tuna lokacin da zata kirani tai ta mun masifa wai na hana Sulaiman taimaka mata, in ta bata hakuri in ce yana dawowa zai mata, ina kashe wayar in turawa Abba kuɗi yai mata, a lokacin da nike gidan bata taɓa neman abu ta rasa ba, amma son zuciya yasa bata ganin hakan a matsayin kyautatawa, gani take ma ai na hana a bata a wadace ne, yau kuma ga shi kiri-kiri Zainab na cewa ba za'a bata ba, ko kunyarta bata ji ba, ya Salam. Katse kiran kawai ta yi tare da zama kan tabarma ta hau rusa kuka, su Amina sun tafi yawon neman abin da zasu ci. Wannan shi ne abin dake faruwa a Nigeria. A can Germany kuma, na dukufa na mai da hankali kan karatu sosai, kullum sai Ibrahim ya kirani wajen sau goma a rana, wani lokaci in ce wai shi baya gajiya ne, sai ya ce in dai a kaina ne ba zai taɓa gajiya ba. Tun bana biye mashi har na zo na fara sakan jiki da shi. Lokaci yanata tafiya. Watannin Ibrahim shidda da dawowa cikin rayuwata wataranar litinin ya kirani da yamma, ina ɗagawa bayan mun gaisa ya ce. "Tauraruwata gaskiya yakamata ki mun izini in zo in ganki"......... "Kai, ni dai a'a gaskiya". Na faɗa ina zaro ido, coz wlh mugun tsoron mutane nike ji yanzu, dan tun da muke waya da Ibrahim ma har yanzu ban ce ina son shi ba, shi kaɗai yake kiɗinsa kuma yai rawansa, duk da na sake da shi sosai yanzu, amma kullum amsata daga uhm, hmmmmm, e, a'a, okey, toh, shikenan amsoshin, dan a yanzu bana sha'awar aure ko soyayya, duk ya fita a raina, Abbie ya ganawa zuciyata azaba, dan ma dai Ibrahim shi na fara so a rayuwata ne yasa nike iya sauraransa, ban da haka kullum na fita school sai na haɗu da maza kala-kala, amma gudunsu nike, ban taɓa tsayawa ba, dan gani nike kowa irin Abbie ne. Ibrahim

Chapter 20 of 38