Share this page
wai dan ku yi daidai da ita. Calm down Madam, ki bari lokacinta ya wuce, kafin nan ki gina kanki, sai ki zo da salon da bata taɓa gani ba, amma mu bi Aisha mu ga ya zata yi, fatana ku ɗauki darasi ku daina wannan shirme da kuke idan za'a auro wata, ku kashe duk kuɗin da kuke da shi a shirme wai dan ku fita, ina batun finta bayan biki kin zo baki da ko sisi miji yaƙi baƙi kuɗin cefene ki zauna kina zazzare ido mutunci ya zube? Ku dai mu bi Aisha mu ga nata salon. In taƙaice maku labarin nan kada yai tsawo sosai, ranar juma'a sati uku da tafiyar Abba kenan aka ɗaura auren Zainab da Abbie. Wlh na ji tsananin azaba a zuciyata, amma na daure, na cije, ko kaɗan ban nuna na ji wani abu ba. Tun ranar Monday su Safiyya da Aunty Maryam kanwar daddynmu suka zo Kano wai tayani zama, iyayena basu san da batun zai kara aure ba sai satin da za'a ɗaura, Hajiyarmu ta dinga faɗa daddy yana tausarta. Suka kirani suka mun nasiha mai ratsa jiki, na dinga godiya da hamdala ga ALLAH da ya bani iyaye nagari. Washegari ranar Saturday dangin su Abba suka dira a Kano da amarya Zainab rasa kunya. A lokacin da suka zo ina kwance a ɗaki, na manta ban faɗa maku ba Abbie yai gyara gida, an yi fenti an yi komai, ya tambayeni sabbin furnitures ɗina na ce ba'ayi ba tukun nan, mai yi ya ce sai next week, alhalin dukka kuɗin yayana na turawa har an fara mun gini. A wasu ciki da parlo dake ta bayan side ɗinmu mai kama da BQ Zainab zata zauna, dan babu wadatattun ɗaki a side ɗinmu, ta ji takaici, wai ita a babban part ɗin nan take so, Abbie ya dinga dannarta yana bata hakuri, bata hakura ba, a lokacin dai ta yi shiru ne, amma ta ci alwashin bayan jama'a sun watse sai tasa ya dawo dani ƙaramin part ita ta koma babba. Tun da family ɗinsu suka diro Kano bamu haɗu ba, suna ta hidima ta baya, basu nemeni ba nima ban nemesu ba, duk sun bi dangi sun shafa mun bakar fenti, kowa baya sona yanzu. Ina jinsu ta bayan window suna ta gulmace-gulmacensu wai bakinciki ne ya hanani fitowa, wata har da cewa kila ma na haɗiyi zuciya na mutu. Ni kuwa ina kwance rike da wayata, tabbas na ji zafi, zuciyata na suya, amma ban bari ya bayyana a kan fuskata ba, Safiyya na kwance kusa dani tana dannar waya ita ma, Aunty Maryam da yake ita babbace tana waje tare da su, su Hassan suna wajen Fahad ɗan Aunty Farida, da yake Fahad ɗin yana da hankali sai yai ƙoƙarin maye masu gurbin uncle Abba da suka rasa. Muhammad sarkin rashin rigima yana ta barcinsa. A haka muka wuni a gidan har dare, da daddare around 9 muna tare da su Aunty Maryam a ɗakina muka ji sallama a parlo, Aunty Maryam ta fita dan dubawa. Jim kaɗan ta dawo tare da cewa. "A'isha ki zo zangin mijinki ne, wai zaku gana da amaryarki". Safiyya ta yi caraf ta capke da cewa. "Ba zata je ba gaskiya Aunty Maryam, bamu buƙatarsu, su tafi"........ Na saki wani irin murmushi, na kalli kayan barcin jikina, dogon wando ne da riga mai dogon hannu da suka fito da kyauna sosai, headband ne a kaina wanda iya gaban goshi ya rufe, yelwataccen bakin sumar kaina a kwance har gadon bayana yana wani sheƙi, na yi shirin kwanciya ne ma, dan ban tuna wani abin zai haɗani da su ba. Ƙasan bed ɗin na sauƙi tare da ɗaukar wayata, na nufi parlo ban yi wa su Safiyya magana ba, zuciyata cike da tunanin irin gulmace-gulmacensu da suka dinga yi ɗazun wai takaici ne ya hanani fitowa, sai na ce bari ni basu takaicin da suke ikirarin ina ji, bari in barsu da abin tunani a zuciya. A yadda nai shirin kwanciyata na fito, ga wani musulmin kamshin da nike bugawa. Na daka masu cikakken sallama irin ta addini a natse, duk suna zazzaune a kan kujeruna suna ta kalle mun parlo, sai ALLAH kaɗai yasan me yake a ransu. Na wuce na zauna a saman one seater da babu kowa, na kalli Aunty Farida fuska da ɗan murmushi kaɗan na ce. "Aunty sannunku da zuwa". A wani irin natse nai magana, muryata babu wata alamar ina cikin damuwa. Ai take suka sha jinin jikinsu dukka, su Khadija iyayen rashin kunya sai aka natsu, da sun zaci zan so da faɗa ko fuska a haɗe ne su zuba mun habaici da rashin kunya, amma sai suka ga garau nike. Na ɗauko wayata tamkar mai duba wani abin, sai na ce. "Khady ba zaku gaishe da ni bane? Ko dai yanzu kun mai da Abbie ƙaninku ne kun zama surukaina?". Na faɗa ina ɗan murmushi ina ɗan danna wayar da ban san me nike dannawa bama, kawai dan in nuna masu ni fa ina da abin yi ne. Ai bakin su Khady mutuwa yai, sai ido. Daidai lokacin Safiyya ta fito ta zauna a hannun kujerar da nike, ta ce. "Sannunku da zuwa". Aunty Maryam ma ta fito ta zauna a kujerar gefena. Aunty Farida ta ce. "Aisha amaryar Sulaiman muka kawo maki dan ku fahimci juna". ..... Na ɗan ɗago kaina irin cike da mamakin nan, sai kuma na ɗan yi murmushi game da cewa. "Kai Aunty Farida kina nufin ki ce satin nan aka ɗaura auren ne? Ai na ɗauka tun satin da ya wuce aka yi? To wai me ya shiga kaina ne na mance?". Ai sake baki suka yi suna ganin ikon GOD, na kuwa sake faɗaɗa murmushina kaɗan tare da cewa. "Sorry yama sunan amaryar? Na zaci tun last week aka kawo mana ke, har ina cewa Auntynsu Hassan ɗin nan bata son mutane bata taɓa leƙowa mun gaisa ba, ashe ni ce ban sani ba, yi hakuri, abubuwa ne duk suka sha kaina, ban zauna na natsu ba bare in fahimci me ake ciki". Kam bala'i, yau sun ga abu, watau tsabar ina busy ban ma san ranar auren mijin nawa ba, a tunanina ma an jima da yi, gaskiya na goge masu hadda, wlh duk sai da jikinsu ya yi sanyi, masu cewa takakci yasa zuciyata ta buga duk sai da suka sha jinin jikinsu su ka yi tsit. Na kalli Safiyya game da cewa. "Kawo masu ruwa ke". Sauran dangi sai kallona suke yi, musamman dangin Mamar Zainab, sun ga na fi ƴarsu kyau da fasali, ga jiki mai kyay ɗan cas. Safiyya ta miƙe ta shiga kitchen. Aunty Farida sai ta ji harshenta yai mata nauyi, Zainab jiki yai evening, ta ga ashe ni bama kishi bane a gabana, a yadda ta fahimta ma mijin ma baya gabana kenan, kam bala'i, wannan ai faɗa dani ma ita ce da ciwon zuciya. Safiyya ta kawo masu ruwa, rasa kunyar cikinsu watau Amina mai bin Abbie a wajen haihuwa ce ta iya cewa. "Mu ba zamu sha ruwa ba, ga dai so dangi nan mu kawo maki ku fahimci juna, ruwa kuma mun sha a side na so dangi". Ka ji wata suna wai so dangi, duk dan in ji haushi, watau wacce dangi ke so, to ai shikenan, ni kam sunan ma dariya ya bani, na ɗan saki murmushi game da cewa. "To so dangi barka da zama ɗaya daga cikin member na gidan Sulaiman, muna maki lele, ALLAH ya taimakemu ya shige mana gaba, ƙaramar nasihata a gareki shi ne ki sani aure ƴar hakuri ce, sai ki daure kin cije, sannan sai kin haɗa da kula, ALLAH ya wanzar da farinciki da zaman lafiya a rayuwarmu". Zuciyata yadda kuka san ana soyata a cikin mai, amma haka na daure nike wannan jawabi, duk jikinsu Aunty Farida ya yi evening, ta gagara magana ma, daga karshe haka suka kwashi Zainab suka fice, na bisu da murmushi da fatan alkhairi ina to sodangi a rike batun hakurin nan dai sosai. Suna fita Safiyya ta watse da dariya tana maimaita sunan sodangi, sai da na ɗan bugeta tare da cewa. "Ke ban son shirme, sodangin Sulaiman ɗin kike yi wa shakiyanci?". Haba ai Safiyya sake fashewa da dariya ta yi, ni kuwa na wuce cikin ɗaki, na shiga toilet na sha kuka tamkar raina zai fita, na wanke fuskata, na jawo towel ina ƙoƙarin goge fuskata sai ga call ɗin Abba ya shigo wayata da na ɗaura a kan wash hand base. Na goge fuskata kafin in ɗauki kiran. Ina ɗauka ya ce. "Auntyn tawa zuciyata ya bani kina kuka".......... Sai kawai nai murmushin yaƙe zuciyata na ƙara ƙuna na amsa da. "Ni kam Abba anya kai ba aljani bane? Kawai sai ka dinga cewa mutum yana kuka". A natse ya ce. "Wlh ina zaune kawai na ji zuciyata na faɗa mun kina kuka, daga wajen training muka dawo ba jimawa, my Aunty please me ya sakaki kuka bayan kin ce ba zaki sake kuka ba?"........ Abba da yasan yau ake auren yayansa, yasan dole zan shiga damuwa, shiyasa ya kirani dan ɗebe mun kewa, ya dinga jana da hira, na dinga kauce mashi kan bana kuka, daga karshe dai dole na yarda kukan nike yi, ya tambayeni dalili, ban ɓoye mashi komai ba na faɗa mashi har chat ɗin da yayansa yake da Zainab kafin auren, ban ɓoye mashi komai ba. Sai ya ce. "To bari ki ji wani abu, kinga ita wannan Zainab ɗin ko?"........ Na amsa da e. Ya cigaba da cewa............... labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi. QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥 LABARIN AISHA.🥹💔 PART 14 Sai ya ce. "To bari ki ji wani abu, kinga ita wannan Zainab ɗin ko?"........ Na amsa da e. Ya cigaba da cewa. "Kafin Mamar Zainab ta zo gidan uncle ɗinmu mace daya yake da shi, bata taɓa haihuwa ba, ba irin abin da ba'a ce mata a dangi ba, amma ta jure, kakarmu lokacin tana raye, sai ta tursasawa baban Zainab kara aure daga cikin dangi, dole ya auro wata ƴar kawunsu, yadda kika ga suka maki, haka suka yi wa uwar gidan kawuna, wacce aka aurawa kawuna ɗin ita ma sodangi suke ce mata, suka takurawa uwar gidan kawuna, daga karshe dai zaman yaki daɗi, dole uwar gidan kawuna ta nemi ya saketa ba zata iya zama ba, ya rage iya wannan sodangin nasu a gidan. One day one time kawuna ya zo da batun karin auren, zai auri mahaifiyar Zainab, kowa a dangi da farko yaki, amma da kawunmu ya matsa, dole suka amince, kin san me ya biyo baya?". Na girgiza mashi kai alamar a'a. Ya ɗan nisa tare da cewa. "Kawuna ya auro mahaifiyar Zainab, dangi duk sun tsaneta suna mata abin da suke so, amma da ta shigo, duk sai da kowa ya natsu ya shafa mata lafiya, dan Mamar Zainab bata da kunya ko kaɗan, duk wacce tai mata dakuwa zata yi, bata dariya kuma bata ɗaukar nonsense, da gangan kawuna ya auro masifaffa dan ya ga ita ce daidai da danginmu, coz iyayen Mamar Zainab suna da kuɗi sosai, dan haka dangina sun san idan suka taɓata daga nan har birnin sin zasu buga shari'a da iyayenta, cikin ƙanƙanin lokaci Mamar Zainab ta zama sodangi dole ita ma, dole suka sota, biyayya dole su yi mata, Aunty Amina da kike ganin nan a hannun Mamar Zainab ɗin ta girma ai, wani irin dakuwa ne bata yi ba? Da zata baki labari da kin daina damuwa, a kwana a tashi suka juyawa ƴar uwarmu da suka aurawa kawun namu baya, suka koma son Mamar Zainab, saboda batu na gaskiya Mamar Zainab tana da kirki, sai dai bata da kunya ga masifa, ko uwar miji ta mata a lokacin zata gyara mata, bata ɗaukar iskanci manya ma bare na yara, idanunta a buɗe yake". Na yi mamakin, watau tun asalin danginsu masifaffu ne kenan, amma sai na ce. "To me ya fitar da Mamar Zainab daga gidan uncle ɗinka?".......... Ya ɗan nisa game da cewa. "Kawai rana tsaka ta ce uncle sai ya saketa, ba yadda ba'ayi ba ta ce auren ya isheta, da aka ce saboda me ta ce wai auren dole ne? Ai ba farillah bane, sunnah ne, dan haka ita ya isheta, ba duka ba zagi, sai ma biyayya da dangi suke yi mata, amma ta ce bata buƙatar auren yanzu, dole kawu ya saketa, yanzu da nike maki magana babbar ƴar kasuwa ce, tana yawonta a gari ba aure, ta ce auren nan ba dole bane, ba zata yi ba, idan akwai wanda take zaune a kansa to ya sauketa ya ajiye, mafaɗaciyar mata ce sosai da sosai, to dan haka ki fita harkar su Aunty Farida, su basu da aiki sai tada husuma da kike ganinsun nan, duk uncles ɗina ba wanda basu addabawa ya kara aure ba, duk da su kuntatawa wacce ba sodanginsu ba". Ni kam na saki baki, sai kuma na ce. "Amma naga Aunty Farida ai ita kaɗai ce a gidan aurenta, and duk sauran su kaɗai suka zauna a gidan aurensu babu kishiyasa, sai su addabawa wasu a masu kishiya?"........ Ya amsa da. "E, a gidajensu su ɗaiɗai ne amma su addabawa gidajen wasu"....... Na ɗan taɓe baki ina mamaki hali irin ka dangin mijin nan nawa. Haka muka yi ta hira da Abba, idan na ce mashi sai da safe sai ya ce mun a'a akwai abin da yake son faɗa mun, idan na tsaya sauraronsa sai ya jani da wata hira, ko kaɗan bayan son mu yi sallama, tun Safiyya na jiran mu kammala waya ta fara waya da shi, har ta hakura, tun ina toilet har na fito ɗaki kan gado na kwanta, na dinga tsokanarsa waye ya saka mashi kati, yaƙi faɗa mun, yana dai ta faman jana da hira. Sai around 1 na dare, ya natsu, yai ƙasa sosai da murya, sannan ya ce. "Ban so barinki ki yi barci yanzu ba my Aunty, banƙi yau mu yi ta hira har 3 saboda in ɗauke maki hankali daga kan gidan nan ba, amma naga alamar da gaske barci kike ji, to zan barki ki kwanta, amma kafin nan kin san me? Magana ta fahimta nike son mu yi". Na ce a'a ina jinjinawa hankali irin nasa, watau dama domin ya mantar dani yau aka kawo mun amarya ya kirani ya jani da hira, ALLAH sarki. Ya ƙara yin ƙasa sosai da murya, cikin natsuwa ya cigaba da cewa. "Abbie zai gama duk abin da zai yi a duniya Aunty ba zai taɓa samun mace irinki ba, yanzu kawai na tabbata wasu abubuwa biyu zuwa uku ke ɗaukar hankalinsa a tattare da Zainab, amma batu na gaskiya babu ma mahaɗi tsakanin qualities ɗinki dana Zainab, ajiye wannan a gefe, ki sanya a ranki Abbie zai dawo, zai dawo gareki, nasan waye shi sosai, abinda yake ɗaukar hankalinsa a tattare da Zainab ba zai taɓa bashi abin da yake so ba, yana gani daga nesa ne kawai, duk karfin sha'awarmu akwai abin da ganinsa da ido kawai idan muka yi kaso 50 cikin ɗari na feeling ɗinmu sai ta motsa kuma muke jin daidai a zuciyarmu, kallonki kawai a lokacin idan ya yi yana biya bare a kai ga taɓawa, idan kika yi la'akari da tun farkon zamanku, kin fita daban da sauran mata, duk karfin feeling ɗinsa kina iya ɗaukewa a zuwa ɗaya, saboda kin haɗa duk wani qualities da irin jininmu yake so, amma Zainab fa? Sai ta tura mashi wani ɓangare na tsiraicinta ne yake iya motsa shi wanda ke fuskarki kawai a lokacin idan ya gani birkicewa yake ya fasa fita, kin manta ne in tuna maki? Kin manta yaya sai yai wanka sau uku a safiya wai zai fita kasuwa, kin manta sai kin rakasa waje ya sake kamaki ku dawo, kin manta tare da ku na karasa girmana, kin manta duk abin da yakefaruwa ina sane, kin manta sai ya fita ya sake dawowa, kin manta a safiya kawai yana iya wanka har sau uku duk saboda sai ya fita ya sake dawowa in kina ɗan mashi shagwaɓa kaɗan, duk kin manta wannan? To na tuna maki, kin fita daban da saura, zai gama duk tsalle-tsallensa ba zai taɓa samun gamsuwa wajen kowacce mace ba sai ke, ki yi zamanki zai dawo, macen da ta kai mace ita ce wacce fuskanta kawai idan an kallah komai na halittar jikin namiji sai ya motsa, kuma ALLAH ya baki wannan baiwa, shaukin sonta ne yake ɗebansa yasa in ya ganki sha'awa zata motsa, amma sai ya kirata a waya wai ta kwantar mashi, ki basu watanni uku zuwa huɗu, kina zaune zai dawo". Abba ke magana kunya kamar ta kasheni, ban taɓa tunanin duk zamana da yayansa yaron nan yasan me yake faruwa a tsakaninmu, ashe duk abin da muke yi yana ganinmu, kai innalillahi wa inna ilaihi, yau ya gama bani kunya, da yana gari ina ga ba zan sake ɗaga ido in kallesa ba. Shi ma a nasa ɓangaren dan bamu ganin juna ne yasa yai waɗan nan maganganu dukka dan ya sanyaya mun zuciya, da ace muna ganin juna a irin kunyar nan tasa wlh ba zai yiwu ba. Amma kuma duk abin da ya faɗa gaskiya ce, haka zamana da yayansa ya kasance, sai ya yi wanka zai fita kasuwa da na rakasa haraba sai ya sake dawowa, mu ɗaura daga in da muka tsaya, sai yai ta sake wanka har sau uku huɗu, daga karshe ma idan ina son ya fita zama nike a ɗaki in ki rakasa ko parlo ne, dan gajiyar dani yake, and nasan yana dawowa da yamma zai dasa daga in da ya tsaya, ban iya wahala, ashe duk Abba yana ganinmu yaron nan, kai amma dai kam anyi shiryayyen yaro. Zuciya da saƙe-saƙe ga sharrin shaiɗan sai na hau tunanin kenan shi ma Abba haka ne? Kenan shi ma idan ya ganni ina tada mashi da feeling? In ba haka ba ta ya aka yi yasan ganin fuskana kawai yana motsa duk wani lafiyayyen namiji? A ina ya sani? Sai na shiga tunanin irin zamanmu, tun farko yadda muka rayu cikin farinciki da shaƙuwa ga yarinta, tunanina ya tsaya ne cak a watarana da na shiga ɗakinsa ina kwala mashi kiran ya zo ya ciro mun wasu dinner set a saman drawer kitchen ɗina zan sanya abinci dan tsawona ba zai kai ba, ina shiga ɗakin na zame na faɗi a bakin kofa, da bakin kofar ɗakinsa dana toilet ɗinsa suna kusa ne, ya fito daga wanka kafarsa da ɗan ruwa-ruwa ya taka tiles ɗin ya wuce, shiyasa ina shigowa na taka ruwan nai wani irin mummunar zamewa na faɗi sai da na ji bayana ya tsaya cak tamkar ya fita daga jikina. A lokacin yana tsaya wajen mirror yana taje sumar kansa irin na buzayen nan, ya gyarata sai sheƙi yake yi, yana sanye da kayan kwallo a jikinsa, ya ɗaura jacket a sama saboda ruwan saman da ake yi sanyi ya sauƙa. Da sauri ya ajiye comb da yake taje kai ɗin ya nufeni yana faɗin subhanallah. Na runtse idanuna ina kuka hawaye bibbiyu dan na ji azaba, a lokacin ban fi 16 years ba, shi kuma 21 years. Ya tsuggunna a gabana yana mun sannu, ban kulasa ba, ya kama hannuna zai jani na miƙe na sake fasa ƙaran da yasa dole ya sakeni yana kallona, sai ya rage tsawonsa ya ɗaukeni cak, a parlo ya zaunar dani kan kujera, a wannan lokaci ya dinga kallona kuma yaki yarda mu haɗa ido, ya dinga ce mun sannu. Haka na dinga tuna rayuwarmu na baya, sai na dinga jin kunyar wasu abubuwa da suka faru, musamman yadda a da can baya yake goyona, gaskiya yarinta akwai shirirtia, shiyasa aka ce kuruci dangin hauka, da gaske ne wlh, duk da ban ji kunya ba sai yanzu abubuwan suke bani kunya. Katse mun tunani yai da cewa. "Baki jina ne my Aunty?"......... "Nawan kafi karfina, ka wuce tunanina, sai da safe, ga Safiyya na ta jiran mu gama waya ku yi waya har ta yi barci"........ Ya ɗan tsuke fuska tare da cewa. "Nima wlh tun ɗazun tana raina, amma na daure ne dan in sakaki farinciki, please Aunty ki mun wata alfarma mana". Na ce ina jinka..... Ya ɗan nisa tare da cewa. "Aunty tun da yamma nike ta bin Safiyya ta tura mun hotunanta ko kuma mu yi video call amma taki, dan ALLAH zankiraki video call ki nuna mun face ɗinta, ina tsananin son ganinta".......... Na yi murmushi na amsa da okey, hankalina ya yi mugun kwanciya da kalaman Abba, kuma nasan gaskiya ya faɗa mun, da wuya a samu wacce zata iya gamsar da Abbie, ba ƙarin auren bane ai, wacce zata iya gamsar da kai ne, kuma ba jima'in bane, gamsuwar ne aiki, so kalaman Abba sun faranta mun rai over. Ina ta sauke ajiyar zuciya da farinciki sai ka kiransa ya shigo, na tashi na kunna wutar ɗakin dukka ta yadda haske ya gauraye ko'ina kafin in ɗaga kiran, Aunty Maryam tana ɗakin baƙi ta shiga ta kwanta. Abba yana zaune a sama kusa da wasu kujeru dake cikin hut tamkar wajen shaƙatawa ne, Abba ya ƙara kyau sosai, ƙasar ta ƙarɓesa, har wani ɗan haske ya yi. Fuskansa ɗauke da ƙayataccen murmushi ya ɗan lumshe idanu kafin ya sauke ajiyar zuciya, slowly ya warosu a kan face ɗina sannan ya ce. "Ina kibar Auntyn tawa ya tafi? Kin saka damuwa a ranki ko? Dubi yadda kika dawo, fuskanki duk ya rame"......... Na hararesa game da cewa. "Ni ka kira ka gani ko Safiyya?"....... Ya ɗan shafa ga shi kansa game da cewa. "Sorry my Aunty, nuna mun matar tawa, kema ɗin dai dole in ganki ai dan in tabbatar kina cikin aminci". Na ɗan yi murmushi game da matsawa kusa da Safiyya mai barci, na hau haska mashi fuskanta, a maimakon ya kalleta Abba ni yake kallo, amma ban lura da hakan ba dan ya sunkuyar da kansa ƙasa, sai zan kashe video call ɗin kuma ya sake ce mun minti ɗaya, na dinga ɗan biye mashi dai har 2:30, sannan muka yi sallama da kyar, na ajiye waya. Da alama Abba yana jin wani abin a ransa game dani, amma saboda yayansa yana ƙoƙarin dannewa baya son ya fito fili, sai dai ni kwata-kwata ban san da hakan ba. Muna yin sallama nai addu'ar barci na kwanta, dama barci ya cika mun ido. A wannan dare Abba ne ya ɗauke mun hankali har na manta da Abbie ya yi aure. A washegari danginsu suka koma, gida ya rage ni da Zainab sai su Safiyya. In takaice maku labari a kwanaki uku na kawo Zainab da aka yi daidai da dare ɗaya Abba bai barni na mai da hankali har na iya tuna cewa Abbie na can kwance da wata ba, da yake yasan danginsa sun koma Abbie zai shiga ɗakin Zainab, da anyi sallar ishai zai kirani, yaron da baya da yawan magana, amma sai ya zage ya dinga surutu dan ya kwantar mun da hankali. Nima mugun jin daɗin hiran da shi nike yi, har bana son mu yi sallama, sai 2:30 kullum yake barina in kwanta, a lokacin barci ya cika idona sai ya barni in kwanta, ina matuƙar jin daɗin hira da Abba sosai. A kwanaki ukun nan kullum haka muke yi, wlh Abba ya taimakeni sosai, dan a irin kishin da nike da shi zan iya mutuwa idan na ji Abbie a ɗakin wata, Abba yasan da hakan, shiyasa ya bi dani ta wannan hanya, nakuwa ji daɗi na gode wlh. After kwanaki bakwai da zuwan Zainab ina ɗaki kwance, su Safiyya sun koma, su Hassan suna school, Muhammad yana zaune tsakiyar gado ga kayan wasansa a gaba yana yi, ina rike da wayata ina rubutawa brother na Ahmad kayan cefenen da zai sayo mun, dama Abba nike aika kullum, to Abba baya nan sai nike

Chapter 10 of 38