Share this page
dan haka Zahra ta ɗauko shi mu tafi da shi. Zahra ta miƙe ta ɗauko shi, ta saɓa a kafaɗa, dama da hijab ɗinta a jikinta, sai kawai muka wuce. Kai tsaye gidansa muka koma, muna shiga parlo na yi arba da kyakkyawan fuska ɗana a zaune kan sofa yana wasa da ɗayan wayan Abba. Ya yi muguwar rama sosai, ya yi duhu, kuma Hassan ya fi Hussain haske dama, amma sai ga shi yai duhun wahala. Na juyo na kalli Abba da ya jingina da wall na kusa da door, kashe mun ido ɗaya yai alamar yane?. Na ce. "Abba, ba ka ce bashi da lafiya ba?"...... Ya amsa da. "Kafin mu isko ne ya samu sauki"........ Duka na kai mashi a kirji, watau wayau Abba ya mun dan in dawo gidansa. Wannan magana da na yi yasa Hassan ɗago kansa, ai yana ganina ya kwala kiran sunana, da gudu ya sauka daga kan sofar ya nufoni. Na durkushe ƙasa na rungumesa ina sauke nannauyar ajiyar zuciya, sai hawaye ya biyo baya, na yi kewansu sosai. Hassan ya ce. "Mammy ina Hussain da little uncle daddy? Kullum sai na kira Hussain amma baya amsa mun, kuma shi ya ce ba zai taɓa tafiya ya barni ba"........ Wani irin sabon kuka ne ya kwace mun, mutuwar Hussain ta dawo mun sabuwa dal, shi kansa Abba sai da ya ji kamar zai yi kukan, ALLAH sarki. Ya ciro ɗayan wayansa yai mana short video muna wannan kukan, sai kuma ya matso kusa damu ya durkusa, a natse ya hau rarrashinmu, Zahra ma ta matso, duk da bata jin Hausa, yanzu ta fahimci dukkansu yarana ne da aka rabamu tsawon lokaci, so bata tambayeni ba, dan a tunaninta wannan rikicin ahali da na ce mata ake yi ne ya ja wannan matsala dukka, ta matuƙar tausaya mana sosai. Sai da Abba ya rarrashemu sosai, ya sanyamu dariya, sai ya ciro wayansa ya ɗaukemu hoto mu ukun dukka muna murmushi, ya goge mun hawayena tare da sake ɗaukanmu hoto. Ya karɓi Muhammad da ya tashi barci yanzu daga hannun Zahra. Ya matso ya haɗamu mu huɗun yai mana hoto mai kyau, duk muna murmushi. Ya miƙe yakama hannuna ya miƙar dani, ya wuce dani izuwa ciki. Hassan na ƙanƙame da hannuna, cikin ɗakinsa muka shiga, Zahra kuma tai zamanta a parlo. Muna shiga cikin ɗakinsa ya sake hannuna game da zama a bakin bed, ya sanya hotonmu da muke murmushi wanda ya ɗauka yanzu a status ɗinsa, a ƙasa ya rubu happy family. Na ja hannun Hassan muka ƙarisa bakin sofa zamu zauna ya ce. "Babana zo abinka"...... Da gudu Hassan ya sakeni, ya koma wajen Abba, Abban ya dire Muhammad a kan gado ya rungumi Hassan yana satar kallona. Can kuma ya ce. "I you ready?"........ Na ɗago na kallesa game da cewa. "Ready to what?"....... "Accept me as your husband, abokin rayuwa". Na hararesa game da girgiza kai alamar a'a, ya ɗan yi murmushi bai sake yin magana ba. Sai ya kwanta Hassan da Muhammad suna ta hayewa jikinsa suna murmushi. A daidai lokacin na buɗe status ɗinsa, ina kallon hotunan murmushi ne ya kubce mun, a raina na maimaita happy family, na ɗago na saci kallonsa, yana ta fama da yaransa, sai sakashi magana suke yi, musamman Muhammad da ya ɗauko irin halin Hussain a iya zaro zance. Shi dama Hassan ba magana ne da shi sosai ba, in kunga yana magama ma to da Abba ɗin ne. Wayarsa da ta yi ƙara alamar shigowa saƙone yasa ya ɗago idanunsa a kaina, sai ka ce an ce mashi ni na turo saƙon. Muryansa can ƙasa ya ce. "Saƙon me kika turon mun kuma? Gani gaki ba zaki iya faɗa mun ba?".......... Na wurga mashi wani irin kallo mai kama da harara kafin in ce. "Daga jin wayarka ta yi ƙara sai ka ce ni na turo maka saƙo? Ka duba ka ga nice? Kawai kai dole sai ka zargi mutum?". Cike da alamar rashin gaskiya na yi maganar. Ya ɗan yi one sided smile tare da cewa. "Ai wannan kara naki ne ke kaɗai, so ina jinsa nasan saƙon or kiran daga wajenki ne".... Da sauri na ɗauke kallona daga kansa, ya kamani, dama nina turo mashi saƙon. Laluɓo wayar ya yi game da kunne hasken screen ɗinta, Muhammad sai faman sumbatar bakin Abban yake yi, duk Abba ya koya mashi iyayi. Da sauri na miƙe na nufi kofa, ya ɗan bi bayana da kallo har na fice, sannan ya buɗe saƙon. Hoton da ya ɗaura a status na yi screenshot na sake turo mashi, sai na rufe fuskansa da emoji mai tambarin heart, a ƙasan hoton na rubuta, abu ne mai tsada mai daraja. Ɗan ɗaga idanunsa ya yi tamkar mai tunanin wani abin, sai kuma ya saƙi ƙayataccen murmushi wanda yasa dimple ɗinsa dukka biyu lotsawa. Take ya hau rubuta mun amsa kamar haka. "Me kike nufi tawan?". Dooo ya gane nufina sarai, neman magana ne. Na dawo mashi da amsar babu komai. Sai ya ce. "To me na guduwa? Baki da gaskiya ne?"...... "E kusan hakan". Shi ne amsar dana dawo mashi da shi. Yai murmushi tare da duba time, magrib ya kawo kai. Fita kan chat ɗinmu yai dan ya bar Whatsapp ɗin, ya Salam, nan ya ga abin mamaki, ta ko'ina messages ne tamkar ruwa suke shigowa wayansa, abokansa ƴan kwallo, kowa tambayansa yake yi su waye mu? Family ɗinsa ne? Kowa ce mashi yake ni kanwarsa ce?. Ya ɗan taɓe baki, bai amsawa ko mutum ɗaya ba ya nufi barin Whatsapp ɗin kenan sai ga saƙo da number Abbie, shi ma yai mashi reply a kan status ɗin nasa ne. Shiga kan saƙon yai...... "MUHAMMAD WANNAN BA AISHA BACE?". Shi ne abin da Abbie ya rubuta mashi. Da ya je Nigeria dama ya baiwa Abbie numbersa, shi dama already yana da number Abbien, kuma ya yi saving ɗinta, shiyasa Abbie ɗin ya iya kallon status ɗinsa...... Abba ya amsa mashi da. "YEAH, ITA CE". Ya amsa tare da fita Whatsapp ɗin gabaɗaya, ya miƙe ya shiga toilet yana faɗawa su Hassan bari yai alwala, suka amsa da okey. Bayan ya yi alwala ya fito ne ya ce da Hassan. "Babana je ka yi alwala mu je masjid"....... Hassan ya miƙe da sauri ya shiga toilet, Abba ya zura jallabiya a jikinsa yana fesa perfume, Muhammad ya ce. "Daddy zan bika"........ "Really?". Abba ya faɗa yana ɗage mashi gera, Muhammad ya amsa da. "Yes daddy". "Okey, next time da kai zamu dinga zuwa, now dare ne, kada ina sallah ka tafi wani waje". Muhammad ya amsa da okey. Hassan na fitowa Abba ya rike hannunsa suka fito suka bar Muhammad kwance a kan gado. Ni kam ina ɗakina ina ta faman murmushi, da kyar na tashi na ɗauro alwala. Ƙa'ida ce idan muka yi sallar magrib bama tashi a wajen sai mun yi sallar ishai, yanzu ma ina idar da magrib nai zaman karatun Alkur'ani mai girma kafin lokacin sallar ishai. Da lokaci yai muka tashi muka yi ishai. Sannan na yi wanka, na canza kaya zuwa hoodie maroon color saboda akwai sanyi sosai. Ya fito parlo dan dubasu. Ina zama a parlo ba jimawa ɗaya daga cikin magunan nan ta shigo parlon da gudu daga ɗakin Zahra, ashe magen suna nan bai fitar dasu ba........ Wani irin razanannen ihu na zunduma tare da mikewa da gudu na nufi staircase. Ina haurawa muka ci karo da Abba da ya fito daga ɗakinsa zai je dubani, ba jimawa ya dawo masallaci. Muna cin karo na ƙanƙamesa ina faɗin. "Dan ALLAH Abba ka cire magunan dake gidan nan, zasu iya kasheni". Ina magana numfashina na wani irin sama-sama, is about to ɗaukewa. Abba ya rungumeni sossi a jikinsa, muryansa a sanyayye ya ce. "Ni dai gaskiya ba zan iya cire magunan nan daga gidan nan ba". ....... Da sauri na ɗago na kallesa. "Meyasa?". Na tambaya cikin tsananin damuwa. Ya ɗaura hannunsa ɗaya a kan mazaunaina game da cewa. "Saboda suna tayani ɗaɓɓaka Sunnah, ba ga shi suna sanyawa ki zo ki rungumi mijinki ba, wanda kuma sam baki yin hakan, ni gaskiya ba zan ciresu ba"........... Na marairace wajen cewa. "Kome kake so zan maka, amma dan ALLAH ka fitar dasu ka ji nawan?". Ya ƙara matseni a jikinsa game da cewa. "Zaki karɓeni matsayin miji?"..... Na jinjina mashi kai alamar e, jikina na ta rawa. Ya sake cewa. "Wani suna zaki dinga kirana da shi?"....... Fashe mashi da kuka na yi tare da cewa. "Nawan ka bari mana"...... Ya sauke ajiyar zuciya game da cewa. "Na bari to, amma yanzu yi mun alƙawarin idan muka yi dinner zaki rakani sayawa babana kayayyaki da wasu abubuwan"....... Da sauri na ce. "Na yi alƙawari". Ya shafa kaina zuwa tsakiyar bayana kafin ya ce. "To shikenan, yanzu dai muje ki yi dinner sai mu shirya mu je ko? Yanzu zan sanya a fitar da magunan"......... Na amsa da okey tom. Ya kama hannuna har dining room bayan ya raba jikinmu, sannan ya barni a dining ya sauƙo parlon ƙasa, ya kira guard ɗinsa guda ɗaya ya ce ya zo ya kama mashi magunan nan ya sanyasu cikin kejinsu. Yana gama bashi umarni ya dawo ya ɗauko Hassan da Muhammad, muka haɗu a dining room. Aka yi serving namu abinci, muka fara ci, sai satar kallonsa nike yi, sai dai duk in na ɗago eyes ɗina sai mun haɗa ido, hakan yasa na gaji na ce. "Wai me kake wani kallona ne?". Saboda idanun su Hassan yasa ya shiga Whatsapp game da shiga kan numberta, dan yaga wayata a hannuna, sai ya rubuta mun. "Kyau daga fuskar matata nike kallo mana"...... Na ɗan yi murmushi ƙasa-ƙasa kafin in ce. "Nawan kai ko kunyata baka ji ko?"......... Yana karantawa ya ɗago ya saci kallona, a lokacin nima na ɗago, muka haɗa ido, kashe mun ido ɗaya ya yi yana sauke ajiyar zuciya. Na ɗauke kallona game da rubuta. "Kallonka yana yawa sosai"........ "Halal ɗina nike kallo". Ya rubuta mun amsa. Na yunkura zan tashi ya ce. "Koma ki zauna ki ci, ko in maki ɗure"........... Muhammad ya ce. "Daddy irin yadda kake mun zaka mata ko?"....... Ya gyaɗa mashi kai alamar yeah, sannan ya ce. "Ku ci abinci da wuri in kaiku wajen Auntynku, anjuma zan zo in ɗaukeku". Muhammad ya ɗan yatsina fuska game da cewa. "Daddy sai ka barni da wannan Auntyn kai kuma ka je wajen mammy kuna wasa ku barni ko?".......... Ya ɗago muka haɗa ido, na ɗauki plate ɗin abincina na nufi barin wajen, sai da na zo dab zan wucesa, can ƙasa da murya nai wajen cewa. "Daddy sai a basu amsa". Ya harareni ta gafen ido tare da yin kwafa kamar cewa zan kamaki ne. Ni kam na yi wucewata waje, kai tsaye ɗakinsa na wuce saboda ina tsoron mage. Na shige nai zamana a kan carpet, na hau cin abincina a natse....... Shi kuwa ya ce da Muhammad. "Ba wasa nike yi da Mammy bafa, karatu nike koya mata, kaga sun kusa fara Exams". Muhammad ya ɗan yi dariya tasu ta yara kafin ya ce. "Daddy karatu ne sai ka kwanta a kanta kuma ka ce in rufe ido, and a kunne kake faɗa mata karatun?".......... Hassan dai babu ruwansa da magana bawan ALLAH, yana jinsu bai tanka ba. Abba da ya rasa abin cewa ne ya ɗan nisa, watau yaran yanzu da wayansu ake haifarsu, ka ji yaro yasan karatu ba a kunne ake yi ba, ko kaɗan Abba bai kawowa ransa Muhammad ya yi wayon sanin yadda ake koyawa mutum karatu ba. Sai ya ɗan waske da cewa. "That time laifi Mammy ta mun, hukunci zan mata shiyasa hakan, kuma ai ana koyawa mutum karatu a cikin kunne ma, dan ya shiga kansa sosai"....... Muhammad ya ce. "Nima ka dinga koya mun a cikin kunne daddy". Abba ya amsa da okey kawai, sannan ya ce su yi shiru su ci abinci, idan ana cin abinci ba'a magana. Haka suka yi tsit, yana ta kallonsu suna ci. Ya fito da wayansa dan ya mun message, suka cigaba da cin abinci, ni kuma ina ɗakinsa, yana turo sako ina mashi reply har na kammala cin abincina, sannan na ɗauki plate na abinci na fitar zuwa kitchen, na dawo ɗakinsa na haye gado, na ƙundundune cikin bargo saboda sanyin kasar, yanzu kwana a ɗakinsa ya fara zame mun jiki. Na kwanta kenan kiran Ibrahim ya shigo wayata, sai da na ji faɗuwar gaba, katse kiran na yi ban ɗaga ba, dan wani iri nike ji a raina idan na ga call na Ibrahim. Ina katse call ɗin na shiga Whatsapp. Ina ƙoƙarin yi wa Abba reply na saƙonsa sai ganin na yi ya sanya status, da sauri na shiga kan status ɗin dan in gani. Na sha madarar mamakin ganin hotona, hoton ya ɗauku da kyau, yanzu ya ɗaukeni a dining room kafin in fito, ga abinci a gabana, daidai na ɗago ido ina satar kallonsa ta ɗaukeni hoto, sai ya yi kamar ina binsa da wani irin kallo mai narka zuciya, ni da kaina hoton ya burgeni, da yake abokan kwallonsa duk turawa ne sai bai wani damu ba, yana ɗaura hotunanmu a status. A ƙasan hoton ya rubuta rigimamma, tare da emojis of heart guda biyu, a gaban emojin ya rubuta ki yi duk rigimarki ki gama ni dake takalmin gaza ne! Watau mutuka raba. Da Hausa yai rubutu dan ma kada abokansa su san me ya ce, coz status ɗin ni yai wa ba kowa ba. Ai kuwa na danna mashi reply da baka isa ba, babu batun takalmin kaza a nan. Ina tura mashi yana turo kofa ya shigo cikin ɗakin. Yana pressing phone ɗin nasa. Yana ƙoƙarin yi mun reply sai ya ga saƙon Abbie, buɗewa yai dan ya duba. "Muhammad baka da hankali ne wai da zaka dinga yin posting na matar mutum a status ɗinka? Idan abokanka suka buɗe fa?". Shi ne abin da Abbie ya rubuta mashi. Ya ɗan yi sama da idanunsa kan saƙon da Abbien ya tura mashi na ɗazun da ya tambayi wannan ba Aisha bane Abba ya ce ita ce, da ya amsa mashi ashe ya sake turo mashi da saƙon cewa wai dole zai dawo da matarsa ɗakinta, dan yanzu wani irin tsananin so yake yi wa Aisha, har da cewa Muhammad nasan kuna da kusanci, and ta shaƙu da kai, dan ALLAH ka tayani shawo kanta ta dawo ɗakin, wlh yanzu tsananin son gaskiya nike yi mata. Abba na karanta saƙo take ya haɗe rai sosai, ya ƙariso bakin gadon. Ganin ya haɗe yasa na ce. "Lafiya dai ko nawan?"....... Ya wurga mun kallon ƙasan ido yana ɗan danna waya, sai kuma ya kashe wutar screen na wayar, ya turata cikin aljihunsa, sannan ya haye gadon, maimaikon ya kwanta a gefe, sai ya kwanto kaina tare da mun rumfa da kirjinsa. Muna fuskantar juna, ya tsareni da kallo sosai tamkar zai cinyeni da ido, na hura mashi iska a fuskansa, ya ɗan lumshe idanunsa tare da sake warosu a kaina. Cikin wani irin salon kauna ya ce. "Kin shirya in cika maki mafarkinki na ranar?". Da sauri na girgiza kai alamar a'a, sannan na ce. "Abba, ka tuna iyayena mana, me kake so in ce masu ne? Kasan ba zasu yarda da aurenmu ba?"......... Ya amsa da. "Ke kin yarda ne? Ni bani da damuwa in dai ke kin yarda, to komai zai zo mun da sauƙi, please ki karɓi soyayyata tawan, zan zame maki mijin da baki taɓa tsammani ba". "Dama yaudarata ka yi ko Abba? Dama ba auren sati zamu ba?"....... Ya jinjina mun kai, a natse ya ce. "Sonki nike yi yasa na aureki, bana son wani ya rigani samunki ne yasa, please, ki saurareni kuma ki mun kyakkyawan fahimtar, soyayyarki ba yauce yake a raina ba, saboda ke na dage sai na cinwa burina, dan in samu duniya, in nuna maki me jin daɗi a rayuwa, ba zan iya hakuri dake bane yasa na bijiro da wannan hanya dan in mallakeki". Yadda yake magana gabaɗaya ya kashe mun jiki, sai na ce. "To amma su Hajiyarmu ba zasu yarda ba"....... Yai ƙasa da murya, can ƙasa ya ce. "Ke kin amince ne? Kina sona?"........ Na hararesa ban yi magana ba. Ya matso ya haɗe fuskokinmu. "Kin yarda in maye gurbin abin da kika rasa? Ki aminta dani mana, please ki bani sati ɗaya, ki yarda dani matsayin miji na sati ɗaya, idan har a wannan sati ɗayan ban canza tunaninki na sa kin samu mijin da baki taɓa tsammani ba, to na yarda zan rabu dake". Na ɗan yi shiru, iyayena kawai nike tunawa, dan nasan wacece Hajiyarmu, mace mai kafiya da zafin rai, bata ɗaukar nonsense........... Can na ce. "Iya sati ɗaya ko?". Ya gyaɗa mun kai alamar e. Na ce. "Ka yi alƙawarin sati ɗaya".... Ya amsa da. "Na yi alƙawari sati ɗaya, amma kema ki ɗauki alƙawarin zaki mun duk abin da mata yake yi wa mijinta?". Shiru ma ɗan yi ina jin kamar ba zan iya wannan alƙawari ba, amma kuma sai na tsinci kaina da amsa na yi alƙawarin. Wani irin Musulmin ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa. "To tashi mu je ki rakani shopping da kika ɗauki alƙawari ɗazun"...... Na ce. "Akwai sanyi sosai garin"..... "Kada ki damu ɗumin jikin mijinki yana nan"........ Na ɗan haɗe rai, zan yi magana ya rigani da cewa. "Kin fa yi alƙawarin zama mace tagari a gareni na sati ɗaya, gada ki fara mun tsiwa, alƙawarin sati ɗaya, biyayya da soyayya zaki nuna mun". Na ɗan turo baki tare da cewa. "Ni kam tashi mun a kai ka mun nauyi"...... Ya sumbaci gefen cheek ɗina tare da cewa. "Nauyi kuma? Da saura fa, kuma tsab sai kin ɗauke"..... Oho ban gane nufinsa ba, na ɗan turesa. Miƙewa yai yana murmushi, nima na miƙe, hannuna yakama muka nufi waje, da yake hoodie ɗin jikina mai hula ce sai ya ce muke kawai ba sai na saka wani kaya ba, and dare ne ai. Na yarda na bisa, muka fito harabar gidan, already an shirya motocin da zamu fita. Cikin motar tsakiya na comboi ɗin ya nufa, guard guda ɗaya ya buɗe mana kofa muka shiga ciki. Muna shiga ya jawoni jikinsa, aka tashi motocin shi kuma ya fara nasa aikin a jikina, ya dinga shafe mun jiki yana bina da kalamai masu melting heart. Na kwanta shiru a jikinsa ina sauke numfashi mai ɗan nauyi, wani irin tsananin daɗin abin da yake mun nike ji, na ƙara shigewa jikinsa, ya rankwafo kaina yana faɗin. "Tawan, mekike tunani yanzu?"...... Na kama hannunsa dake yawo a jikina na rike, na ɗan murza yatsunsa kafin in ce. "Bana tunanin komai face Hussain ɗina". "Zamu samu Hussain Junior very soon matata, kawai ki aminta dani, kinga dai twins a jininmu suke, bappana da babana twins ne, and duk cikinmu ba wanda ya samu twins ɗin sai Abbie, su Aunty Farida duk basu samu ba, amma In Sha ALLAH nima zan samu yadda Abbie ya samu". Na amsa da. "Ni fa da farko ban yarda baba da bappa mutum biyu bane, na ɗauka duk mutum ɗaya ne, sai daga baya nike banbantasu". ........ Yana zame hular hoodie ɗin jikina ya amsa da. "Sai da kika yi wannan magana ma na tuna su kaka sun bani abubuwan kauye wai in kawo maki". Da sauri na dago kaina daga kirjinsa, sannan na ce. "Me suka bani?"...... Ya amsa da. "Abubuwa dayawa gaskiya, ban duba ba, idan mun koma sai mu duba tare"..... Na ce. "ALLAH sarki mutanen kirki".... Ya ƙarisarmu da cewa. "Ba irinsu mama ba ko?"..... Na ce uhm ban yi magana ba. Ya cigaba da shafa hair ɗina zuwa hadon bayana, yana hira masu daɗi har muka kai Super market ɗin. Kaya sosai ya sayawa Hassan, tun ina iya ƙayyade adadin har na hakura, haka ya biya maƙudan kudaɗe, muka kamo hanyar komawa gida. Muna isa gida Ibrahim ya fara danna mun kira, Abba yana ƙoƙarin fitar da kayan Hassan bai lura ba. Da sauri na wuce cikin gida dan in ɗauki kiran Ibrahim, ina shiga ɗakin Abba kiran ta katse, zama na yi a bakin bed ina ƙoƙarin bin kira, sai ga kiran ta sake shigowa. Ina pick-up sai ga Abba ya turo kofar ya shigo. A take ALLAH ya dasa mun tsoron yin magana da Ibrahim ga mijina, sai na ji zuciyata na rawa, da yake zan yi crossing line na musulunci. Abba ya ɗauka da gida nike waya, ya ƙariso ciki yana faɗin. "Ki gaida munsu". Coz bai ma san Hajiyarmu ta ja mun kunne a kan kada in kula shi ba...... Da sauri na cire wayar daga kunnena, ina ƙoƙarin katse kiran amma na gagara saboda rawa da hannu yake yi. Sosai na baiwa Abba mamaki, ya miƙa hannu ya karɓi wayar yana faɗin. "Lafiya kuwa........." Maganarsa ta tsaya ne daidai lokacin da ya ga number Ibrahim. Ai wani irin tamke fuska tamau ya yi tare da katse kiran, dan a cewansa ya wuce class na magana da Ibrahim, ya juyo da kallonsa kaina, a fusace ya ce. "Kina matata kike magana da wani?"....... Na haɗe rai nima, duk da ya mun kwarjini hakan bai hanani cewa. "Kaga na yi magana da shi ne? Ko da ma ace na yi magana da shi me naka a ciki? Kada ka manta auren yarjejeniyar sati ɗaya muka yi, ina da damar kula wanda nike.......". Maganata ta tsaya cak ne sakamakon tureni da ya yi na kwanta a kan gadon, yai kwanto kaina, fuskansa tamkar hadari, a fusace ya ce. "Baki da damar kula kowa, ke tawa ce ni kaɗai, yanzu kuma zan tabbatar maki da hakan". Yana kai karshen maganar ya haɗe bakinsa da nawa. Cikin zafa ya fara kissing ɗina tamkar sani mayinwacin zaki da ya ga nama. Ƙoƙarin turesa na fara yi, amma ina, ko motsa shi na gagara........ labarin A'isha zai dinga zuwa maku labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi. FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥 LABARIN AISHA.🥹💔 PART 37 Follow my TikTok account 👇 https://www.tiktok.com/@princess_teema1?_r=1&_t=ZS-92AoEpYYmwP Follow my Channel account 👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S Ƙoƙarin turesa na fara yi, amma ina, ko motsa shi na gagara, na fara bubbuga bayansa ina ƙoƙarin ya rabu dani, Abba bai kulani ba, sai da yai kissing ɗina mai isarsa, sannan ya sakeni game da fara ƙoƙarin zame rigar jikina. Na sanya iya karfina na turesa ina shirin miƙewa ya sake damkeni. Kuka na fashe mashi da shi ina faɗin. "Abba dan girman ALLAH ka yi hakuri, ba zan sake ba, na yi alƙawari, please ka kyaleni, na tuba dan ALLAH". Sosai nike kuka tamkar wacce aka cewa wani nata ya mutu....... Lokaci guda ya dakata da abin da yake ƙoƙarin yi, sai kuma ya kwanta tare da jawoni jikinsa, yana wani irin numfashi mai nauyin gaske. Na kwanta shiru a jikinsa ina jin bugawar zuciyarsa na wani irin bugu da karfi-karfi. Coz ya kyaleni ne saboda ban taɓa rokonsa abu ba a rayuwarmu, yau na roke shi harma da bashi hakuri, sai ya ji ba zai iya kin mun abin da nike so. After like 5 mins da kwanciyarmu haka, in a cool way muryansa ya doki dodon kunnena da cewa. "Bana son ki sake kula wani namiji, bana so bana so! Ke ɗin tawa ce ni kaɗai". Ina shessheƙa na amsa mashi da. "Ba zan sake ba"........ Ya fara shafa gashin kaina zuwa gadon bayana, sai ya ce. "Sorry, ya isa haka kukan"........ Na ƙara shigewa jikinsa, can ƙasa na ce. "Ba dole in yi kuka ba, ka zo ka danneni"......... Ya juyar dani, na koma kan katifa shi kuma ya kwanta a gefena, muna fuskantar juna ya ce. "Kece silar komai ai". Na ɗan turo baki ban yi magana ba, ya sumbaci bakin nawa game da cewa. "Kalleta a wajen, kome kika yi kyau kike ƙarawa, kin san me na ce

Chapter 30 of 38