Share this page
To wlh kin ɗebo ruwan dafa kanki"........... A wani irin slow na ɗago fararen idanuna ƙalƙal a kansa, a hankali na ce. "Habibi please bana son hayaniya, idan dai zata zo nan ta ɗaga mun hankali ne ni kawai ka bita ku tafi na yafe mata kai, ku je kawai ka cike shekara by then sai ka dawo". Na kai karshen maganar a shagwaɓe sosai. Shagwaɓar da ta kara rikita Abbie, coz shagwaɓa ma kun san iyawa ce, kuma ba kowa take yi wa kyau ba, wani in yai rawa ya samu kuɗi, wani idan ya yi duka zai ci, aikuwa ni dai kuɗi zan karɓa a wannan bangare ba duba ba, dan dama ko a fuska ka ganni kalar shagwaɓa ce ni, mugun kyau take mun. Aikuwa baki Zainab ta saki, a ganinta kayan amai na yi na shagwaɓa ba, dan na yi wa mijina shagwaɓa. Sai ta hau ce mun. "Yarinya kawai, duk yarinta ya cika maki kai"...... Na dai yi banza da ita, dan ni ba daidai yinta bane, wanda ya ajiyeta shi ne daidai yi na, na wuce ajinta, haba ai ƙasƙanci ne ma in tsaya wai ina faɗa kishiya tana faɗa, wannan zubar da kima ne, wlh na wuce wannan layin. Daidai lokacin Abbie ya sauke mana abincin saman carpet ta gabana, ya ce. "Sauƙa kici ki ƙoshi sosai"....... Na turo mashi ɗan bakina game da cewa. "In ci in koshi saboda ka ji daɗin wahalar dani ko? To ba zan ma ci ba, dan wlh Habibi zaka iya kasheni ban shirya mutuwa ba".......... Ya saki murmushi, zai yi magana Zainab ta ce. "Wlh karya ne, ba'a haifi mutum ba, idan kun isa ALLAH ya tsine mun!!". Tana wani hura hancinta da ya kara kato saboda ciki. Ni kam na sakawa mijina kukan shagwaɓa game da cewa. "Habibi na ce maka bana son hayaniya, in dai za'a mun hayaniya ni zo ka ɗaukeni ka kaini ɗaki idan hayaniyar ya tafi sai in dawo in ci abincin ka ji?"......... Ya Salam, yadda na yi magana yasa bai san lokacin da ya dawo kusa dani ya zauna ba, ya ɗan rungumoni a jikinsa game da cewa. "Ai dole ki zauna ki ci ko in maki ɗure, ban isa barinki da yunwa ba kada in rasa kanki anjuma". Na ɗan buge mashi baki cikin wasa, zan yi magana ya rigani da cewa. "Zainab ki wuce ki fita a ɗakin nan tun ban maki abin da baki taɓa zata ba, ki wuce part ɗinki, yau girkinta ne kuma na dawo ɗakinta"....... "Babu in da zan je munafuki maci amana, wlh yau babu in da zan je sai dai dukkanmu mu kwana a nan, kuma wlh ALLAH ya isana". Tamkar zata yi kuka ta faɗa. Ai tana faɗin haka a raina na ce yarinyar sai dai ki kwana a nan ko? Zan kuwa sa ki gudu da kafafunki, in dai bariki ne to wajenta kika zo, dama dan bana samun romance daga wajensa ne yasa ban fito da asalin kalata ba, yanzu kuwa da yake hannu ai shikenan kuma, sai kin jira. Na ɗan yi ƙasa da murya game da cewa. "Habibi bana son kanan ɗaga murya sosai, yanzu dai zuba abincin ka bani a baki, zan ci a nan ɗin kawai sai mu shiga ciki"...... Ya amsa da okey, sai ya ɗan sumbaceni a cheek kafin ya sauƙo ya zuba mana abinci a plate. Yana buɗe abincin kamshi ta daki hancinsa, bai san lokacin da ya ce. "Mace mai iya girki duniya ce, yadda kuma ta iya sarrafa girki yai daɗi haka kike da ɗanɗano na musamman Habibiyata". Kubce mashi maganar ta yi bai shirya ta fito ba. Ni kam na sakar mashi murmushi, ya miƙe da abincin a plate ya zauna a saman kujera, a hankali ya ɗauki spoon da niyyar fara bani a baki. A fusace Zainab zafin kishi ya ɗebeta ta fatale abincin ya zube mashi gabaɗaya a jiki. Ai cikin zafa ya miƙe tsaye, kafin ta yi wani motsi ya ɗauketa da wani gigitaccen marin da yasa ta yi baya tana taga-taga tamkar zata faɗi. Ni kam ko ɗagowa in gansu ban yi ba, dan ko a jikina, ai tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa kan duka. Ya sake ɗaga hannu zai kara mata wani marin ta juya da gudu ta fita tana ihu. Ai da sauri ya nufi rufa mata baya nai saurin riko hannunsa, a fusace ya juyo, ban bari ya yi magana ba na rigasa da cewa. "Please Habibi, ka kyaleta tun da ta gudu".......... Ya wani sauke ajiyar zuciya dan muryar ta daki kawon zuciyansa, ya dawo kujerar da nike ya zauna yana sauke numfashi a hankali-hankali. After like 5 mins ya miƙe ya kwashe abincin tare da ɗaukar plate ɗin ya koma wajen dining table. Ya zubo wani abincin a wani plate, ya dawo, yana zama kenan sai ga Abba ya shigo bakinsa a ɗauke da sallama Fahad na bayansa, ashe bama su gidan tun ɗazun, ya je sayan kayayyan da zai buƙata a tafiyan nasa. Da sauri Abba ya nufi shigewa cikin ɗakinsu, tamkar baya son ganinmu. Ni kuma duk sai na ji kunya takamani, wlh na yi tunanin ma suna ciki sun yi barci ne. Fahad ma ya ɗagawa kawun nasa gaisuwa game da wucewa ciki. Abbie ya ce. "Kai Muhammad zo nan". Abba dake ƙoƙarin ƙarisa shigewa cikin ɗakinsu ne ya amsa da. "Ina zuwa yaya". Yana faɗar haka ya shige ciki. Na kalli Abbie, a natse na ce. "Ɗauko mun hijab ɗina Habibi". Ya wani kalleni kafin ya amsa da. "Hijab kuma? Ki yi me?"........ Na kalli kayan jikina kafin in ce. "Baka ga kayan barci bane a jikina? Kuma na ji ka kira Abba ya zo, and wannan ba normal kayan barci bane ka gani"........ Ya miƙe ya ɗauko hijab ɗin ya dawo, yana zama na karɓa na sanya a jikina, sannan na kallesa kafin in ce. "Amma Abbie na sha faɗa maka ka kamawa su Fahad haya mana, idan ka duba Fahad fa ba yaro bane, ya ɗan fini kaɗan a shekaru, kuma wlh hakan a addini ba daidai bane". A ɗan taƙaice ya ce. "Habibiya ƙannena ne fa? Baki son zama da su kenan?". ..... Na girgiza mashi kai alamar a'a, coz na jima ina binsa ya kama masu haya, saboda suna takura mun, ni ina son sanya ƙananan kaya sosai, ga su su ba yara ba, musamman kafin ya kori Khalifa a gidan, yaron nan sai ya dinga kallon surar jikina, amma Abbie saboda baya son cire kuɗi ya kama haya gara ya bar wasu karti a gidan nan muna musayar numfashi da su wanda kuma wlh ya sani sarai haramun ne a addini, yana da ilimin addini sosai, kawai dai yana son abin duniya ne shi, shiyasa baya amfani da iliminsa, ni kuma haddar Alqur'ani gareni, bani da sauran littafan musulunci sosai. Kai ni wlh ban taɓa ganin mutum irin Abbie ba, ga ilimi ga shagala. A daidai lokacin Abba ya fito, a ɗan baya ya tsaya game da cewa. "Gani nan yaya". Ya wani tamke fuska tamkar ba nawan ba..... Cikin zolaya na ce. "Da ka ɗaure mana fuska kam dan mu ji tsoronka ne? Kai soja ne?"..... Ya ɗan saci kallona ƙasa-ƙasa kafin ya ce. "Aunty, Aunty, Aunty, ki kyaleni na huta mana ni kam"....... Ina murmushi na ce. "Kallesa a wajen, idan kana gaban yayanka har wani musulmin natsuwa kake kara yi, nawan anya kana da gaskiya kuwa? Ni ka raina ko? Sai ni da kai ka ta mun rawan kai da yarinta". Ya ƙara kicin-kicin da rai, ya dallah mun harara ƙasa-ƙasa da waɗan nan dara-daran idanun nasa, ya ɗan ɗauke kansa yana satar kallona ta wutsiyar ido, coz sai yanzu ya lura da skin ɗina ya canza sosai, na ƙara kyau mai ɗaukar hankali. Abba idan yana gaban yayansa wlh natsuwa sosai yake kara yi. Abbie ya ce. "Ni ba shirme na ce ku zo ku mun a nan ba, kai Muhammad na ji zaka yi tafiya gobe ko?".......... Ya ɗan jinjina kai yana cigaba da satar kallona.... Na ɗan zare mashi fararen idanuna, coz ban san da batun tafiyar na. "To zoka zauna a nan mu yi magana". Abbie ya faɗa yana nuna mashi ƙasa kusa da mu. Abba ya ɗan girgiza kai kafin ya ce. "Please yaya ka faɗi maganar ina daga nan"..... Kwata-kwata baya son matsowa kusa da ni, saboda wannan kamshin perfume ɗin da ya kama jikina, wannan turare tana matuƙar gigita shi sosai, shi kaɗai yasan me yake ji idan ya shaƙesa a jikina, yanzu ma kawai dauriya ce yai ya tsaya a parlon. Abbie ya ce. "Kai ban son iskanci fa, ka zo nan na ce"...... Abba ya kafe shi wlh ba zai matso kusa dani ba. Ba yadda Abbie bai yi ba, amma yaƙi, daga karshe sai cewa ya yi sai dai Aunty ta shiga ciki sannan ya zo. Mamaki ne yakamamu daga ni har Abbie, muka tambayesa dalili, ya ce babu komai, ba yadda bamu yi ba yaki faɗa mana, daga karshe na yunkura zan miƙe Abbie ya ce in koma in zauna kuma Abba ya wuce ya zo nan ko ya tashi yai ball da shi, dan a ganin Abbie wannan ai rainin wayau ne, ta yaya za'ayi yana mashi magana yaki bin umarninsa, daga karshe ya kafa mashi sharuɗan wai sai na bar wajen zai zo tamkar shi sa'ansa ne?. Shi kuwa Abba ya kafe wlh ba zai zo kusa dani ba, in dai ban bar wajen ba to ba zai motsa daga in da yake da sunan ya ƙarisomu ba. Yau ga Ikon GOD. Amma duk da haka wai Abbie ya gagara gane nufin Abba yana matsayin babba mai hankali da ilimi, ni da bani da sani kan ɗabi'un maza ma na fara fahimtar wani abu, na yi shiru ina tunanin duk lokacin da na sanya turare mai ɗan karfi wlh Abba baya zuwa kusa dani, yana ja baya dani sosai. A raina na ce ko aljanu garesa ko kuma yana ƙoƙarin kare kansa daga shiga tarkon shaiɗan, saboda turare a jikin mace yana tada sha'awa matuƙa. Na ɗan zazzaro idanuna a lokacin da na tuna hakan, na ɗago na kallesa, yaki yarda mu haɗa ido, a raina na ce lallai Abba yana da hankali sosai da sosai, ALLAH sarki ƙoƙarin kare kansa yake yi daga shiga tarkon shaiɗan........ Maza masu ajiye ƙannensu a gida da tunanin cewa ƙannensu ne ai lafiya lou ne dan sun zauna da matansu, ku sani fa kamar yadda zaku ji feeling a kan matanku haka suma ƙannen naku zasu ji feeling tun da ba duwatsu bane su, kuma matankun nan ai basu haɗa komai na jini da ƙannenkun ba bare ku ce ƙannen naku ba zasu ji sha'awarsu ba, wlh tsab zasu ji sha'awarsu, maza nawa ne matan yayyunsu suke burgesu suke basu sha'awa, ALLAH ya fi mu sanin daidai shiyasa ya haramta ƙaninka baligi yana shiga in da matarka take a kodayaushe, dan yasan shi ma ƙanin zai iya jin sha'awarta tun da ba dutse bane shi, amma mazanmu basu wani damuwa sosai, sai su ce kannensu ne ai babu komai, wlh akwai komai, idan ma ta kama dole sai ƙaninka ya zauna da kai gida ɗaya to akwai dokoki da layin da zaka shata mashi tun farko, ba ayi zama tamkar an zama ɗaya ba, zata zama ɗaya da kai ne kawai ba da ƙannenka ba, ba zai taɓa yiwuwa su yi zama tamkar an zama ɗaya da kannenka ba, babbas kuskure dayawan mazanmu suke yi wlh, is better a gyara. ---------------------- Shi kuwa Abbie faɗa ya fara yi wai Abba ya raina shi. Yana cikin faɗan ne na katse shi da cewa. "Nawan jeka abinka, tafi kawai"....... Ai da sauri ya juya ya bar parlon, kai tsaye ya fice ma daga gidan bai koma room ɗinsu ba. Na dawo da kallona a kan Abbie, a natse na ce. "Abbie, yanzu kam ya isa, gaskiya ka kamawa su Abba haya, Abba ya girma, shiyasa baya son zuwa kusa dani, tun tuni nike faɗa maka ka kamawa yaran Aunty Faridan nan haya ka ce da gidanka ba zaka kama wani haya ba". Nan fa ya ce. "Wai da kike ta wannan magana Abba fa ƙanina ne, kina tunanin wani abin mara kyau ne a kansa?"......... "Bana tunanin komai, amma ka fahimci yanayinsa, ni dai ka kama masu haya kawai"....... Nan fa ya ce shi bashi da kuɗi, kuma ba wani hayan da zai kama, ai ƙaninsa ne ba wani abin bane, sai dai in ban ɗauki ƴan uwansa a matsayin nawa ba. Abu fa har ya kusa zama mana faɗa, da naga haka sai na ce zan biya kuɗin hayan tun da bashi da kuɗi, nan ma ya kafe sam ba yarda ba, shi ba wani hayan da zamu kama gaskiya bai yarda ba ..... A wannan dare na fahimci wani abu kaɗan, Abbie baya son rabamun waje da Abba, to meyasa? Duk lokacin da na kawo mashi batun rabuwarmu sai yaki, har faɗa sai mun yi, and sau da dama abubuwa suna faruwa da suke ƙoƙarin raba mana wajen zama Abbie na daƙile hakan, a lokacin da Abba ya shiga school, ya nemi da ya koma hostel da zama, amma Abbie yaki yarda. To meyasa Abbie yake son zamana inuwa ɗaya da Abba? Gaskiya akwai dalili, saboda duk wanda na ce zamu raba wajen zama da shi Abbie baya tada hankalinsa sai a kan Abba kawai, a farkon aurenmu ƙanwarsa Humaira ta zauna da mu, a lokacin kaina na hayakin yarinta sosai, mun sha faɗa da ita, da Abbie ya tashi ya rabamu, ya mai da ita Kd, su Khalifa, duk lafiya lou Abbie ya rabamu, meyasa Abba kawai yaki rabani da shi?. Na yi shiru ina tunanin farkon zuwan Abba gidan, kai gaskiya akwai dalilin da yasa Abbie ya haɗani da Abba tun farko, wlh ba haka kawai bane! And Abbie yana da tsananin kishi a kan matarsa tun asali, sai dai baya kishi da Abba, bai damu ba in yi kowani irin shiga idan Abba yana nan, then bai damu ba ko shekara zai barni daga ni sai Abba a gida, then duk irin wasannin da muke yi da Abba a gabansa yana gani bai taɓa damuwa ba, zan kama hannun Abba in jasa, ko in kama kunnensa, wani lokaci in yi ta shafa gashin kansa dukka a gaban Abbie lokacin da ban kai haka shekaru ba, wlh mutumin nan ko a jikinsa, ko sau ɗaya bai taɓa hanamu ba, amma idan a waje ne ko kallona wani ya yi sai ya ji dalili, na rasa gane meyakefaruwa!. Muryansa ne ya katse mun tunanin da nike yi ta hanyar miko mun abinci yana cewa in ci. Raina cike fal da tunani na fara karɓa ina ci, ina ta son gane dalilin da ya sa ya haɗani da Abba kuma babban tashin hankalinsa shi ne in ce ya raba mana wajen zama. Haka na dinga cin abinci har na ƙoshi, shi ma ya ci ya ƙoshi. Muka tattara muka koma cikin ɗaki, a wannan dare Abbie bai barni ba sai da ya sake morewarsa, ya dinga tambayata wai ya aka yi na canza, har da ce mun wlh na fi lokacin da aka kawo mashi ni ina sabuwa daɗi. Ni kam ina fama da azabar da nike ciki ban bi ta kansa ba, ga tunani a cunkushe a cikin zuciyata har barci yai awon gaba da ni. Washegari tun kafin in farka daga barci Abba ya bar gidan, coz baya son mu sake haɗuwa nan kusa, bai mun sallama ba, sai da ya san ya tafi sannan yai mun dropping sms a wayata kan ya tafi in yi hakuri bai tsaya mun yi sallama ba in taya shi da addu'a. Lokacin da na tashi naga saƙon na yi matukar mamaki, na sauko na shiga toilet, wanka na fara yi na zo na fara shirin biyan sallah asuba, karfe 7 na safe sai a lokacin na samu sallar asuba. Bayan na idar na fito na gyara gidan sannan na shiga kitchen, su Hassan Fahad ya kaisu school, basu tafi da abinci ba, ya dai basu snaks, ya ce anjuma zai kai masu abinci idan na girka. Tun daga wannan rana ban sake jin ɗuriyar Zainab ba, nama mance da ita, ashe tana can tana ƙitsa yadda zata yi maganina, ni ina nan ina rayuwata hankali kwance, har Abbie yai kwanaki biyunsa a ɗakina zai koma nata, bawan ALLAHN nan wlh cewa yai ba zai koma ɗakinta ba sai ya yi sati a ɗakina tun da ai ya mata watanni huɗu, ni kam na ce a'a gaskiya ya koma ɗakin nata, ya kafe shi wlh ba zai iya kwana ɗaya bai ji shi a jikina ba, ba zai iya ba. Da kyar na shawo kansa ya tafi ɓangarenta, yana zuwa suka hau bala'i, Zainab ba hankali, wai maimaikon ta tsaya tsayin daka wajen kwato mijin nata, sai ta tsaya faɗa da shi, wai ba zai shiga ɓangarenta ba ya koma in da ya fito, aikuwa ya ce ta fi nono fari, ya juya yai dawowarsa. Nan fa Zainab ta ɗauki wayarta ta dakawa Mama kira, ta zayyano karya da gaskiya dukka ta faɗa, har da cewa ya daketa mugun duka a gabana, ina shewa ina ya kara mata. Hankalin Mama yai bala'in tashi, sai ta ce na kara yi wa Abbie wani asirin ne, dole ta zo Kano sati mai zuwa, ta dinga kwantarwa da Zainab hankali tana kwarara mata gwiwa. A haka suka yi sallama, ran Zainab fes Mama zata zo ta kwata mata ƴanci. Ni kam da ban san me ake yi ba ina can ina rayuwata, kuma a satin na baiwa Abba 50k nasa ya baiwa Maman, ashe ban san na bata kuɗin zuwa wajen malamanta masu karya asiri bane, dama duk in zan bata abu ina cewa Abba ya ce in ji Abbie ne ba in jini ba, bana son su san ni nike masu komai wlh. Aikuwa da wannan kuɗi ta yi amfani zuwa wajen malamai ko in ce bokaye dai, dan malamai kam basu da haɗi da asiri bare har su karya, ta je ta zayyanawa bokanta abin dake faruwa. Aikuwa bokan ya kangara mata karyar wai asiri na yi wa Abbie, bakin asiri ma kuwa, shiyasa komai nike so shi yake mun, dan haka dole sai an karya asirin, Mama zata kawo 300k da bakin shanu ɗaya dan bakin asiri na yi wa Abbie. Hankalin Mama ya tashi, ta shiga tunanin in da za'a samu kuɗi, ta cewa Malam wai zata kawo kuɗin. Da ta dawo gida ta kira Zainab ta faɗa mata ai bokan ya ce asiri aka tyi wa Abbie, asiri ma bakin asiri. Zainab ta dinga shewa wai an gano sirrina, za'a karyasa kowa ya huta, ni kuma fa a lokacin ina ta fama da Abbie ya koma ɓangarenta bawan ALLAHN nan yaki, ya ce shi wlh in ya kwana bai jisa a jikina ba zai iya ciwo. Ni kuwa na yi fushi na ce wlh ba zan bashi kaina ba, ya dinga magiya na sharesa, ita kuwa Zainab tana can tana haukar zasu karya asirin da na yi mashi. Mama ta faɗa mata kuɗin da ake so aikuwa ta ce zata bayar, zata karɓo kuɗi wajen mamarta, zata ce washin machine zata saya dan nima na saya ita bata da shi kada kishiya ta mata dariya, suka tsara da mama a kan haka, ta kira mamarta tai mata karya, ai na faɗa maku mamarta ƴar kasuwa ce, akwai kuɗi a hannunta, aikuwa ta bawa Zainab cike da sa ran ƴarta na zaune a gidan aure cikin salama. Haka Zainab ta kwashi wannan kuɗi dukka saboda rashin wayau da rashin hankali ta turawa Mama, Mama ta ɗauka ta kaiwa wani katon banza cima zaune wai shi Malami, duk da sunan a karya asiri, suka sayi bakin shanu kato na 150k, suka kai nashi 300k, dama 500k Zainab ta roki mamarta. Suna nan suna haukarsu ni ina nan ina tsara ginina, yanzu haka ginin saura kaɗan a gama, amma fa an ja kuɗi, dan kuɗin yayana almost 20M ya shiga cikin ginin nan, shagona ya rame tas saboda ginin ya cinye kuɗin, Yaya ya ce kada in damu, idan ALLAH yasa muka kammala ginin lafiya, ɗayan bene da zan sayar zai iya kai 300M, in na sayar sai in buɗe katon shago a Abujan, shi ma sai ya cire kuɗinsa da ya ta zuba mun. Wannan magana nasa ta sanya ban wani damu ba, na cigaba da kwashe kuɗin shago ina turawa kawai dan a karisa ginin, in da na gaza na kakare Yaya ya tadani. Gini ba karamar abu bane, duk mun ji jiki, ga shi ginin har biyu, ai akwai wahala. Ita Zainab tana nan ta karar da kuɗin gadonta a kan Abbie, ita ba uba a raye ba bare in ace ko Abbie ya ci amanarta bai mai da mata da kuɗinta ba ubanta na'a raye zai taimaka mata, iya abin da ta mallaka ɗin ta bashi, ni kuwa da ALLAH ya bani zinaren yaya, ai ga shi ya gina mun rayuwata mai kyau cike da farinciki............. Jama'a akwai dirama a gidan A'isha, Mama na zuwa, wai ba dama ka mallaki zuciyar mijinka da gyaran jiki, hali mai kyau da kirsa sai ace wajen Malam ka je? Ga dai Aisha da ko fita bata yi kullum tana gida sai sanin kimar kanta da ta yi amma ake ƙala mata sharrin bin bokaye. labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi. FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥 LABARIN AISHA.🥹💔 PART 20 Haka rayuwarmu ta cigaba da tafiya, na daina yi wa kaina komai kamar a baya, saboda yanzu na samu kan Abbie, Alhamdllh yana rage mun wasu abubuwa amma ba dukka ba, dan shi ma yana samun abin yake so sosai. Na sha mamakin ganin Abba ya wuni ya kwana bai kirani ba, washegari da safe na kirasa bai ɗauka ba, na matuƙar damuwa sosai, wasa-wasa sai da ya shafe kwanaki uku sannan ya kirani ranar wata laraba, har kuka na dinga yi saboda rashin samunsa a waya, na dinga damun Abbie da ya kirasa sai ya ce mun in kyalesa suna wajen wasa ne, idan ya samu lokaci zai kirani. Ranar da ya kirani ina kwance sai da na miƙe, ina ɗauka na ce. "Nawan menene haka?"....... A natse ya ce. "Assalamu alaikum"........ A ƙage da son jin dalilinsa na kin ɗaukan wayata na amsa sallamar, ya ce. "Aunty ina wuni"......... "Lafiya lou ya aiki?"........ Ya amsa da lafiya, sai kuma ya ɗan yi shiru, muryansa cike da tsananin damuwa sosai, na ce. "Nawan menene yake damunka?". Can ƙasa ya ce. "Babu komai Aunty, kawai gajiya ce ya mun yawa, ina babys ɗina?"............ "Suna school, sai yaushe zaka dawo?"........... "Ba da jimawa"...... Na ɗan nisa tare da cewa. "Na yi kewarka sosai nawan"... Ya ce uhm bai yi magana ba, kamar dai bashi da lafiya, na damu ya faɗa mun abin dake damunsa a ransa, amma yaƙi, da na cika matsa mashi sai ya ce. "Babu wanda ya isa ya mun maganin abin dake raina face ALLAHN da ya ɗora mun shi, dan haka babu wanda zan faɗawa sai ALLAH, dama na kiraki ne kawai mu gaisa, in ji kuna lafiya, ki gaida mun da Sofi, sai anjuma". Ɗiff ya kashe wayar ba tare da ya jira amsa ta ba, na damu sosai, na sake kiransa yaƙi ɗauka, a raina sai nike jin kamar dan saboda an hana shi Safiyya ne yake fushi dani, na dafe kaina ina salati, ita ma Safiyya har fushi ta yi dani, wai tun farko ni na ja mata wahala, ni na haɗata da shi har ta fara son shi, yanzu laifina take gani, ga shi shima ya fara ganin laifina, innalillahi wa inna ilaihi rajiun, na damu

Chapter 15 of 38