Share this page
ai daga yau sayan magani ba fashi, ko bai tambayi kuɗin ba dole in bashi, ban isa ba, ahalin mutunci muke, a raina na kudurci niyyar idan Abbie ya dawo yau lallai zan yi mashi maganar yai maza a yiwa Abba aure, dan kada a samu matsala. Tun daga wannan lokaci wani irin kunya ta shiga tsakanina da shi, ko na fito mun haɗu bana taɓa yarda mu haɗa ido, shi ma baya yarda mu haɗa ido, ko magana yake mun kansa a ƙasa, komai ya ɗan canza tsakaninmu. labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi. LABARIN AISHA.🥹💔 PART 8 Tun daga wannan lokaci wani irin kunya ta shiga tsakanina da shi, ko na fito mun haɗu bana taɓa yarda mu haɗa ido, shi ma baya yarda mu haɗa ido, ko magana yake mun kansa a ƙasa, komai ya ɗan canza tsakaninmu, mun rage wasan kanin miji da muke yi, na ɗan ja baya da shi saboda kunya, idan na gansa kalaman kawai nike tunawa. A haka muka shafi sati muna wannan ɓoyewa juna. Yau takama Saturday, kowa yana gida har Abbie, mun haɗu a parlo muna hira, sai Abbie ya miƙe ya fita, ya ce yana zuwa, na amsa da okey, Abba na zaune Hassan da Hussaini sun haye jikinsa suna wasa, yaran nan shaƙuwar da suka yi da Abba ko ni uwarsu basu yi shi dani ba bare Abbie da ba zama yake yi ba, komai uncle Abba komai uncle Abba. Ya zaunar da Hussaini a kan cinyarsa yana gyaggyara mashi gashi kansa, Hassan kuma ya haye bayan wuyansa yana lilo, sai dariya suke yi. Na zubawa Abba idanu ina kallonsa, yana kama da Abbie sosai, sai dai Abbie ya ɗan fisa haske, shi yai chocolate sosai. Cikin zolaya na ce. "Nawan gashin gerarka ya kusa haɗewa, zaka zama dodon su Hassan, Safiyya zata raina mun kai, yakamata in gyara maka"....... Kamar yasan ina kallonsa, sai yaki ɗago ido, ya kara yin ƙasa da kai ma kafin ya ce. "Auntyn tawa bama ki ji me Sofi ta ce mun ba fa". "Me ta ce?". Na faɗa ina murna na ganin sun fara magana da Safiyya, na ji matuƙar daɗi........ "Cemun ta yi wai na fi dukka yaran Mama kyau, amma na cika shagwaɓa kamar mace, ita bata son namiji mai halin mata, Aunty please ki faɗa mata wlh ba halin mata nike da shi ba, zama cikin matan ne ya lalatani, ki faɗa mata ke kike sakani yin aikin mata, ke kika ɗaura daga kan in da su Aunty Farida suka tsaya daga gida, sannan ki faɗa mata jarumin namiji ne ni". Har ya kai karshen maganar ɗan tahalikin nan yaki ɗago kai, yana ta fama da gashin kan Hussaini. Na fashe da dariya, cikin zolaya na ce. "Ai ta yi gaskiya, kai mata maza ne, ni ban taɓa ganin namiji da shagwaɓa ba, kuma ban taɓa ganin namijin da ya iya duk wani abin da mace ta iya da kuma shiririta ba sai kai"........ "Aunty nine mata maza?". Ya faɗa a sanyaye, still bai ɗago ido ba........... "Kwarai kuwa, mata maza kake, rago kawai". Na faɗa ina dariya. Ya ɗan jinjina kai game da ɗan ciza laɓɓa bai yi magana ba, zan sake yin magana wayata ta fara ƙara. Da sauri na jawota, Safiyya ce, ina ɗauka ta ce. "Aunty albishir?". "Safiyya babu sallama sai albishir dan gidanku?". Na faɗa ina kallon Abba da ya ɗan turo lips ɗinsa na ƙasa kaman mai tunanin wani abin da ya shafi shagwaɓa, amma da ya ji na ambaci Safiyya sai ya ɗago waɗan nan dara-daran idanun nasa da suke ja kullum ɗin, yana ɗagowa muka yi four eyes dan shi nike kallo, da sauri ya ɗauke kansa tare da cewa. "Please Aunty ki ce mata ina sonta sosai, ta yarda dani". Ya faɗa yadda Safiyya ba zata ji ba. Sai ya sake cewa. "Please Aunty ki sakata a hand-free, ni bata mun magana sosai, sai okey da uhm ta iya cewa, ina son jin muryanta, ko na kira bata ɗauka, please tawan". A wannan karon ma yai magana bai ɗago ba. Aikuwa na sanya Safiyya a hand-free, daidai lokacin take cewa. "Aunty murna yasa na mance da sallama"...... Abba ya ɗan yi murmushi yana sunkuye da kai, har da sauke ajiyar zuciya na ya ji muryanta. Yadda Abba yake mugun kama da yayansa sai ɗan haske da Abbie ya fisa, haka nima nike mugun kama da Safiyya sai haske nima dana fita, and na fita manyan idanu kaɗan. "To faɗi me yafaru ake murna haka?"..... Ta ɗan sheƙe da dariyar farinciki kafin ta ce. "Aunty Muhammad ɗin su Abbien Hassan ɗinki ya mun magana, ya ce yana sona, tun jiya na so faɗa maki, amma ban da lokaci saboda makaranta da hadda, Aunty ina son shi wlh, yana da kyau da hankali, kinga idanunsa irin na Abbie, kinga dimple ɗinsa mai kyau sosai, matsalar kawai ya fiye yin abu kamar na mata ne wani lokaci, ga shagwaɓa yana matsayin namiji, sannan wani lokaci akwai shi da shiririta". Yadda take magana cike da tsantsar farinciki kawai ya isa ya nuna da iya gaskiyarta take son na shi. Oooooo, Abba ya saki wani irin musulmin murmushi da ya kara fito da kyansa tare da ajiyar zuciya lokaci guda, a fili ya furta Alhamdllh. Haƙiƙa ya ji daɗin jin tana son shi, coz raina mashi wayau take ashe, kawai wasa da hankalinsa take yi da ta ce bata son shi. Ai da jin haka na ce. "Ki bari zan sake kiranki, yanzu ina aiki ne". Ban jira amsarta ba na katse kiran, na kalli Abba dake ta faman murmushi na ce. "Nawan ya zama lover boy, sai ka fara shirin yin aure, ka dai ji ta ce tana sonka". Bai yi magana ba sai ya ɗan ɗago ido a ƙoƙarinsa na son satar kallona, amma sai muka haɗa ido, da sauri ya sauke nasa yana faɗin. "Kai Auntyn tawa, kin cika sa ido, da mutum ya ɗago kai zai ga shi kike kallo". "Eyee angon Sofi, ni yau zaka cewa mai shegen sa ido? Ba komai, dole ka ce haka ai"...... Yana ɗan murmushi bai sake yin magana ba, coz yana cikin farinciki sosai, and yana jin tamkar ya tashi ya rungumeni saboda daɗi. Safiyya ta sake kirana, ina ɗauka ta ce. "Aunty hau Whatsapp bari in tura maki wani abin da Muhammad ɗin ya tura mun ɗazun ki gani, Aunty ya iya kalamai masu rikita ƙwaƙwalwa, kin ji me ya ce?". Na ɗago ido na lallesa, daidai lokacin shi ma ya ɗago, saboda a H-free na sanya wayar, jin me ta ce ne yasa ya ɗago. Na wani hararesa ya sunkuyar da kai yana murmushi, na amsawa Safiyya da okey rabin raina. Katse kiran ta yi, na kunna data da nufin in ga me ɗan kanin nawa ya tura mata. Ina ƙoƙarin buɗe sakonta sai ji na yi ya fisge wayar yana faɗin. "Ba zaki ga sirrin ma'aurata ba"....... Ai da sauri na zabura zan kwace wayata, ya ɗaga wayar sama wai idan na isa in kwace, coz na faɗa maku ya fini tsawo sosai, tsalle na fara yi wai zan kwace wayata ina faɗin. "Nawan ka bani wayata, sai na ga me kake shukawa". Ina magana ina haɗe rai. Ya ce. "Gajera kawai, sai son ganin gulma da son shiga harkar iyali, idan kina son ganin gulmar jeki aro tsawo ki dawo". Duk maganar da yake yi bai yarda mun haɗa ido ba..... Na ɗan koma baya na hau kujera, na daka tsalle wai zan kwace wayar sai ya ɗan ja baya yana dariya, saura kaɗan in faɗi ƙasa yai saurin tareni da hannunsa ɗaya yana faɗin. "Ke ba karfi ba, ba tsawo ba, Auntyn tawa ke kaɗai ma fa idan kina tafiya faɗuwa kike yi, to dan ALLAH ki rufa mun asiri kada ki ja Yaya ya ɗaureni na karya mashi mata". Ya faɗa yana sakeni. Na miƙe ina huci na wasa, na ce. "Ko ka bani wayata ko in kira yayanka"...... Yaki bani wayar sai da ya buɗe ya duba abin da Safiyya ta turo mun, chat da suka yi daren jiya ne, irin love stickers da ya turo mata, zafafan kalaman da ya dinga zuba mata, su ta yi screenshot ta turo mun. Yai murmushi a ransa ya ce. "Kuruciya da daɗi, daga ita har Auntyn nata yarintarsu ta yi yawa, bata taɓa soyayya ba kenan, shi ne duk ta rikicewa ƴan waɗan nan kalamai, a haka ma bata bashi damar ya saki jiki ya zuba mata kalamai ba amma duk ta rikice, bai san ita da Auntyn tata ma wacce ta fi kuruciya ba". Da ya gama gani sai ya miƙo mun wayar tare da komawa ya zauna, ya ɗaga Hussaini ya mayar kan cinyansa, coz Hussaini irin halin Abban ne da shi, bashi da yawan magana, and yana da hankali da natsuwa, Hassan kam, ba'a magana, mafaɗaci ne na gaske, ga bakin zuciya. Na karɓi wayata na koma na zauna a kan kujera, na shiga chat na Safiyya na fara dubawa, ina karantawa ina murmushi, Abba ya tsareni da ido dan bana kallonsa, ya dinga mamakin yarinta irin tamu daga ni har Safiyya, sai da na kammala karantawa tsab sannan na ɗago kai, da sauri ya ɗauke kallonsa daga kaina. Zan yi magana wayata ta ɗan yi kara, na sake dubawa, sako ne ya shigo Whatsapp ɗin amma da sabuwar number, hotuna ne dayawa aka turo mun. Da sauri na shiga dan ganin wanene?. Ya Salam, wani irin fargaba da tashin hankali na shiga, jikina na rawa na fara bibiyar hotunan ina karanta chat ɗin, hankalina a tashe. A kan wani hoton chat na tsayar da idona, zuciyata na rawa, duk wani murmushin dake kan fuskata ya kau, harshena na rawa na cigaba da karanta chat ɗin nan, wannan hoton da na tsayar da idanuna a kansa ya fi kowanne gigitani, ko ban san wacce ta turo mun ba yanzu na gane Zainab ce, chat ɗinta da Abbie tai screenshot ta turo mun. Ko a ina ta samu numberta?. A wannan hoto da na tsai da kallona na karanta shi ya fi sau hamsin, Abbie ne ya rubuta mata saƙo kamar haka. "Na sani, nasan zaki iya, dan mu wannan a jininmu yake, nasan ko da nafi haka karfin sha'awa zaki iya ɗaukata, my happiness please ki cika alƙawari, dan wlh ni kaɗai nasan irin azabar da nike ciki na rashin samun biyan buƙatata yadda yakamata, Aisha kin san komai a kanta, ta yi karama a farkon aurenmu, har a yanzu ma, bata iyawa, shiyasa kika ga na matsu ayi wannan aure, ina cikin wani hali, please kada ki bani kunya". A ƙasan wannan hoto Zainab ta rubuta mun saƙo kamar haka. "Ku dinga iya ɗaukar nauyin mijinku, ba ku barsu da ciwo a mara har sai ta kaisu wuya sun ji kamar zasu mutu su fita nemanwa kansu mafita wajen zafafa kamarmi kuma ku tashi kuna ihun baku son kishiya ba, ku dinga ƙoƙarin sauke hakkin aure, ba ku bar miji yana neman budurwar da zata iya da shi ba". Wani irin sama-sama na ji numfashina na yi, a hankali na fara ganin duhu-duhu, wlh ban taɓa gaza sauke hakkin bawan ALLAHN nan ba, tabbas bani da sha'awa ko kwatan wanda yake da shi, amma bai taɓa zuwa da buƙata naki ba, ko bana so, ko bana ra'ayi ina dannewa in biya mashi dan gudun ya faɗa wani hali tun da nasan matsalarsu, amma yake cewa ina barinsa da ciwo a mara, innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Wani irin sara mun mai tsanani da kaina ya yi ne yasa ban san lokacin da na saki wayata ta faɗi ƙasa ba. Abba ya ɗago ya kalleni, kafin yai magana sai gani yai na sulale ƙasa na kwanta flat bana numfashi........... NAMIJI BUHUN ƘAYA. Ai cikin zafa Abba yai kaina yana kiran sunana, ina, ai na suma, su Hassan duk suka yi kaina, ɗaukar wayata Abba yai dan ya ga me yafaru na suma shi da ya bari ina chat da Safiyya ina murmushi. Shi kansa da yake namiji sai da waɗan nan chat suka buga kansa bare ni, wani irin ɗaci ya ji a zuciyansa, jikinsa har yana tsuma saboda ɓacin rai, cikin zafa ya goge dukka chat ɗin, ya yi blocking number Zainab, sannan ya goge number gabaɗaya daga wayan, bai taɓa tsammanin Zainab bata da hankali ba sai yau. Ya ɗauki wayoyin da nawa da nasa ya shiga cikin ɗakinsa, jim kaɗan ya fito sanye da jallabiya, da yake yana da karfi ina sume amma ya ɗaukeni cak muka nufi mota, ya shigar dani gidan baya, ya sanya Hassan da Hussaini a gaba, ya shiga driving seat sai asibiti labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi. LABARIN AISHA.🥹💔 PART 9 Ban tashi farfaɗowa a asibitin ba sai can yamma, ina buɗe idanu sai kan fuska Abba dake zaune saman kujera rike da kwalayen magunguna yana dubawa. A wani irin slow ya ɗan kai kallonsa kaina, ganin na waro idanuna waje yasa ya juyo kai da kyau, sai dai bai yarda mun haɗa ido ba, a sanyayye ya ce. "Sannu Auntyn tawa". A daidai lokacin Abbie ya shigo hannunsa rike da wasu ledojin magani da fruits, shi ya kawo wanda Abba yake dubawa ɗin nan ma, coz ya ta fi sayo saura ne, magunguna ne da allurai. Hankali a tashe Abbie ya ƙariso kusa dani ganin na farka, ya zauna a gefen gadon tare da rike hannunna, ya ajiye ladar maganin hannunsa a kusa dani, cikin sanyin muryan nan nasu na gado ya ce. "Sannu habibiya, ya jikin? Akwai in da yake maki ciwo ne?". Cike da nuna damuwa yai maganar. Na ɗan saci kallon Abba ta wutsiyar ido, ya tamke fuska tamau tare da miƙewa, bai sake kallon in da muke ba ya nufi waje, coz haushin yayansa yake ji, saboda koma me shi ya ja, and yasan irin rayuwar da muka yi ta amana da yayansa a baya, and ya ga abin da Zainab ta turo mun, gabaɗaya ya ji ya haushin ganin yayan nasa, dan ya ga wannan son kai ne da cin amana ƙarara, shiyasa ya tamke fuska ya fice daga ɗakin, saboda takaici ta kawo shi har wuya, baya zalunci kuma baya goyan bayan ayi zalunci, kowaye yai rashin gaskiya ba zai goya mashi baya ba, koda uwar da ta haifesa ne, shiyasa gabaɗaya haushin yayan nasa ya kama shi. Ban ji daɗin yadda naga ya haɗe rai ya fice ba, amma na basar game da dawo da kallona a kan Abbie, muryata can ƙasa na ce. "Yaushe ka zo?"....... Yana kallona ya amsa da. "Tun ɗazun da Abba ya kirani, dama baki da lafiya ne baki faɗa mun ba? Meyake damunki? Ko dai batun auren nan ne? Na faɗa maki bana son yarinyar nan, ke kika matsa sai na aureta, and har yanzu ina kan bakata na bana sonta, in har zata sanya maki damuwa a ranki zan faɗawa Mama na janye maganata, farincikinki shi ne nawa". A yadda yake magana billahil lazi da ace da baki Zainab ta faɗa mun chat ɗin da suka yi, tabbas da ba zan yarda da Zainab ba, da zan yarda da Abbie ne, amma ƙarara naga komai, har fa cewa yake watanni biyu sun yi nisa a saka aurensu, dan ya ƙosa ta shigo, amma ji abin da yake faɗa mun yanzu wai baya sonta, ya rabbi wani irin musifa ce wannan? Namiji, namiji, namiji, namiji zai kasheka lokacinka bai yi ba. Amma kuma duk da haka, da soyayyar Abbie sosai a raina, sai dai na rasa yarda a tsakanina da shi, coz yanzu duk abin da zai faɗa karya kawai nike gani. Na wani kallesa, na ƙaƙalo murmushin yaƙe, ina tuna a lokacin da nike yarinya a makaranta lokacin da ake ce mun dila sarkin wayau, kuma sarkin rainawa mutane hankali da mannin hauka, tuna rayuwata na baya yasa na ce bari in gwadawa Abbie wancan halin nawa kaɗan. Murmushin da ya fi kuka ciwo ne a kan fuskata, na ɗan nisa tare da cewa. "Me Abba ya ce maka?"......... Abbie yana shafa fuskata ya amsa da. "Ya ce kuna zaune kika yanke jiki kika faɗi, bai san me yake damunki ba". Na ƙara faɗaɗa murmushin da nike jin tamkar wuta aka watsa mun a fuska, ina tuna kalaman yayana na kada in yarda mu yi faɗa, sai na ce. "Aure ai ni na aminta ka yi, wannan abu ne daban Abbienmu, ina son Zainab, ina son ta shigo, ko dan farincikinka dana Mama ya ɗaure da sakayyama, sannan ina son farincikinka fiye da komai mijina, duk abin da zai sanyaka farinciki ko menene zan tayaka nemansa, kasan ina sonka ko?". A yadda nike magana zaku rantse da ALLAH har cikin zuciyata ce, alhalin nan kawai ina yi ne dan makar da tunaninsa, tun da na gano Abba bai faɗa mashi komai na dalilin suma na ba. "Nasan kina sona, nima ai ina sonki ko?".... Na jinjina kai. "Sosaima kake sona, son da kake mun ma ai ya fi wanda nike maka, na shaida, shiyasa nike sonka nike son farincikinka"....... Yai wannan murmushin nasu mai kara fito da kyansu, sannan ya ce. "To faɗa mun abin dake damunki yanzu in yi maganinsa". Ina cigaba da murmushin dole zuciyata na kuka na amsa da. "Ina ganin fa gajiya ce kawai ta mun yawa"....... "Ko kuma damuwar abin da Mama ta maki ko?". Ya tari numfashina da faɗin hakan..... Na ɗan tsuke fuska. "Da wannan ma Abbie, coz a maka kazafin mai bin malamai ai babu daɗi". Ya ce. "Haka ne my Habibiya, to dan ALLAH ki cire wannan damuwa a ranki, ki yi hakuri kin ji? Komai mai wucewa ne, ki sani ALLAH yana tare da masu hakuri". Na kallesa cike da mamaki, ya san ALLAH a baki tamkar da sunan a manne da bakinsa, amma yana karya dokokin ALLAH, yana fakewa da sunan ALLAH ya ci amana. Na ce. "Ai komai ma ya wuce Abbiena, yanzu dai ina neman wata alfarma"..... Ya jinjina kai alamar yana saurarona, coz daga shi har Abba wlh basu da yawan magana, kuma basa son hayaniya, in kunga suna magana to da ni ne, ga dai su Khalifa a gidanmu suke kwana in sun dawo daga shago, amma ba zaka taɓa jin Abba yana magana da su ba, kuma ɗaki ɗaya suke. "Abbie ina son zuwa Kaduna gobe, yaya baya jin daɗi, sannan please ina son wani abu ɗaya"...... Ya kalleni kafin ya ce. "Okey to ALLAH ya kaimu gobe sai Abba ya kaiki, amma da kin bari kin kara samun sauki tun da naga akwai allurai ma a cikin magungunar naki". Na girgiza kai. "A'a, zuwana can shi ne samun sauƙin nawa, ka barni kawai in je". A cikin kwayar idanunsa na ga alamar farinciki da tafiyar tawa, watau a gidan ina takura mashi baya samun damar yin waya da Zainab tsakar dare. Ya jinjina kai tare da cewa. "ALLAH ya kai mun ke lafiya ya dawo mun dake lafiya Matata, menene abu ɗaya da kike so ɗin kuma?". Yana ɗan murmushi ya faɗa. "Ina son dan girman ALLAH Abbie kada ka taɓa kama sunana a wajen macen da zaka aura, bana son ka taɓa magana a kaina ko ya yake, ku yi hirarku iya abin da ya shafi tsakaninku, babu ruwanta da batuna, please ba dan ni ba, dan ALLAH, kome zata tambayeka a kaina bana son ka faɗa mata, in short da akwai dama ma ko sunana bani da buƙatar ta sani". Ya kara riƙo hannuna da kyau kafin ya ce. "Na yi maki alƙawarin hakan, dama ni ban taɓa maganarki ko da dasu Mama bane bare kuma wacce zan auro, sirrinmu sirrinmu ne, abu ne da yake a tsakaninmu". Yau na kara tabbatarwa wasu mazan basa tsoron ALLAH, ya zauna ya gama faɗawa Zainab bana gamsar da shi ɗin, yanzu kuma wai sirrinmu sirrinmu ne, kai innalillahi wa inna ilaihi rajiun, wai wasu mazan ina suke son kai haƙƙi a kansu ne? Wasu kuwa anya zasu ga Annabi? Waye yasan ma me dame yake faɗa mata, amma wai sirrinmu sirrinmu ne, kai jama'a. Muryansa ta katse mun tunani da cewa. "Akwai abin da kike so ne kuma?"...... Da sauri na girgiza mashi kai alamar a'a, na yi shiru ina tunanin rayuwa. Muhammad na a kwance a gefena yana ta sharara barcinsa. A ɓangaren Abba kuwa, tun da ya fita ya zauna a kan kujerun bakin kofa, ya haɗa kai da gwiwa, zuciyansa tamkar zata fashe, ya tsani cin amana da tauye yarda, zamba cikin aminci, shi da yake matsayin kanin Abbie ma ya shaida na tallabi rayuwansa, ni nake biya mashi kuɗin makaranta, komai yake so ni yake tambaya dan yasan yayansa ba zai bashi ba, Abbie mutum ne da bashi da kyauta sam, shiyasa ƴan uwansa suke kuka dani, wai yana da shi na hanasa taimaka masu, shiyasa suka shirya shigo da Zainab a tunaninsu ita tasu ce zata dinga kwasa tana kai masu, basu san ɗan nasu ne bashi da kyauta ba, ko wanda suke samu ake masu suna rainawa ma ni nike masu ba shi ba, shi kam ba'a cin kuɗinsa. Ko batun kwallon Abba ni na tsaya mashi, yanzu haka zai shiga gasar kwallon kafa ta jaha, na kashe kuɗi a kan hakan ya fi a kirga, ko sutura ni nike sayawa Abba, na hanasa kasuwanci, na ce ya zauna ya natsu yai karatu, yanzu brother na Ahmad ya shiga hundred level a jami'a, ina ta fama da shi shi ma ya ajiye kasuwancin nan ya mai da hankali ga karatu, amma ya kafe zai kula da dukiyata, idan bai da class yana shago, Abba kuwa ya kafe zai kula da kwallon kafa, idan bai da class yana wajen training na kwallo. To shi da yake ƙanin Abbie ya raɓu da Abbie ma ya ci arzikina ya shaida na mashi kuma yana jin zafin abin da ake mun bare Abbie, amma Abbien bai nuna wani damuwansa a kaina sosai ba. Ni kuma har yanzu fa bin shawarin yaya kawai nike yi, amma bawai bana son Abbie ko na yarda zai ci amanata ba, ina ganin kamar kawai yanzu Zainab na ɗauke mashi hankali da kafuran tsiraran kalaman nan nata marasa tsarki ne, a tunanina da sun yi auren shikenan hankalinsa zai natsu ya dawo jikinsa. Abba na kife da kai yana tunanin rayuwa sai ga kiran Safiyya ya shigo wayana, ya fitar da wayar daga aljihunsa, yana ganin na rubuta half of my life ya ɗan sauke ajiyar zuciya, coz yasan itace, pick-up yai tare da kara wayar a kunnensa, cikin shagwaɓa Safiyya ta ce. "Aunty wai ina kike ne ban ganki a Whatsapp ba? So nike ki faɗa mun amsar wani abin". Ya sake nisawa kafin ya ce. "Shagwaɓaɓɓiyata kuma rigimamma, to ba Auntyn bane, a haka kike cewa in canza hali ko my Sofi? Yanzu dai ga shi kina ji kin fini iya shagwaɓa sai rigima". A sanyayye sosai ya faɗa....... Dariya ta ɗan yi game da cewa. "Kaga Malam bawa Auntyna wayanta hai, kuma ni ba irinka mata maza bace". Uhm ya furta damuwa cunkushe a ransa, zai yi magana ya ga Abbie ya fito daga cikin ɗakin, sai ya miƙe tare da cewa Safiyya. "Zan kiraki idan na koma in da take, bama tare". Bai jira amasarta ba ya katse kiran. Da sauri ya ƙarisa shigewa cikin ɗakin bakinsa a ɗauke da sallama. Tun da ya shigo na zuba mashi idanu, ban yi magana ba har ya ƙariso in da kujerar yake, shi kuwa tun da ya shigo kansa a ƙasa, saboda har yanzu baya iya haɗa ido dani tun wancan magana da muka yi. A kujera ya zauna tare da cewa. "Aunty ya jiki?"........ Still ina kallonsa na amsa da. "Da sauki sosai nawan, Nagode ALLAH ya biyaka da jallatul firdaus, ina wayata?". .... Sai a lokacin ya ɗago kansa

Chapter 5 of 38