Share this page
uwansa sai sun dunga goranta mun cewa kuɗinsa na biyo, da farko sun ƙisa sai da yai kuɗi suka so shi. Wannan dalilin yasa Abba jin kwarin gwiwar daƙile alaƙarmu, ya sa a ransa in dai yana raye, to wlh da ya bari na auri Ibrahim gara na mutu ba aure, coz ko ba zai sameni ba, ba zai bari in auri Ibrahim ko na auri wani da zai walaƙantani ba, dan ya lura jahilci na ɗawainiya da Ibrahim sosai, ya ɗauka kuɗi ita ce komai. A natse Abba ya ce da guards ɗinsa su zo su fitar mashi da Ibrahim waje, kuma ko da sunan wasa kada su sake barinsa ya shigo wannan gida. Da gudu wasu madaka karti su biyu suka yi kan Ibrahim, bai ankara ba suka mashi ɗaukar amarya, sannan suka ɗauki akwatinsa a bayan mota, yana ta zazzaga masifa yana zagin Abba, amma ina, Abba bai kulasa ba, ya juya cikin zafin nama ya komo cikin gidan domin ya kwantar da wutar da ya kunna. Yana shigowa tsakiyar babban parlonsa ya ci karo dani rike da akwatina, ina kuka sosai. Da sauri ya dire Muhammad a kan sofa tare da ƙarisawa in da nike. Akwatin ya riƙe, in a cool way ya ce. "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, bani da bakin yi maki magana, amma koma dai me please ki yi hakuri". Na janye akwatina game da cewa. "Ka sake mun kayana Abba, ai saboda gidanka na zo shiyasa zaka ciwa bakona mutunci, da a gidana ne ai baka isa ba, so bari in bar maka gidanka"........ Ya ce. "Ko da a gidanki ne ba zan bari wani ya raɓeki ba, ki sani ba wai dan gidana ne yasa na maki hakan ba, please tawan ki fahimceni". Na ƙara janye akwatina ina cigaba da kuka zan wuce. Da sauri ya sake rike akwatin, intently ya durkushe ƙasa a gabana, ya zube gwiwowinsa a ƙasa, ya rike akwatin gam, in a cool way sosai ya fara bani hakuri, ya ce in zaɓi duk punishment da nike so in mashi zai karɓi laifinsa, kuma ya yi alkawarin ba zai sake ba, amma yanzu dai ya kori Ibrahim, in yi hakuri. Duk yadda na so in sharesa in wuce, amma na gagara, coz ni kaina ina tsananin jinsa a zuciyata, haka na durkushe a ƙasa kusa da shi, na kifa kaina a jikin akwatin na fashe da kuka mai sauti. Muhammad dake kan sofa ya sauko ƙasa ya nufo mu, Abba ya janye akwatin gefe ya riko hannayena cikin nasa, yana jin tamkar ya rungumeni ya rarrasheni, amma ya daure bai yi hakan ba, Muhammad ya zo ya faɗa jikina yana kira Mammy-Mammy. Abba ya jawosa ya rungume yana cigaba da rarrashina, ya ɗago haɓata muna fuskantar juna, idanuna a rufe haka ya dinga goge mun hawaye yana bani hakuri. Da kyar na hakura, sannan ya ce to in tashi ya kaini shopping da kansa ba saƙo ba, dole ya fita da kansa yau. Na ce ba zan je ba, ya dinga rarrashina har sai da na aminta. Muka sake shiri muka fito ina ta kunkunin meyasa ya kori Ibrahim, yana rike da Muhammad ina biye da shi yana ta ƙara lallaɓani kan in daina maganar Ibrahim baya so. Yau ya sanyani saka abaya har da nose mask, while shi ma ya sanya nose mask ɗin. Haka muka fito a jerin comboi na motocinsa, motarmu na tsakiya, Zahra na gida tana barci bata san wainar da ake toyawa ba. Wani katafaren super market muka shiga. Kamar koyaushe ina shopping yana biye dani a baya yana wasa da Muhammad, yau ma kamar wancan karon a Kano, na so ɗaukar underwears da su bra, amma saboda yana biye dani yasa na fasa, kuma nawa duk sun tsufa, ina buƙatar sabbi, kunyansa yasa na fasa ɗauka, a wannan shopping ɗin ma na ga wani farin bra da pant a haɗe masu mugun kyau, haka kuma naga wani baki shi ma bra da pant a haɗe, sun shiga raina, amma na ɗauke kai tare da wucewa. Ban kwashi kaya sosai ba na ce ya isa mu je, ya ce sai na ƙara, haka ya dinga sanyani kara kaya har na jidi kayan da ni da kaina ban san adadinsu ba. Ya tura keken zuwa wajen biyan kuɗi yana ta sumbatar Muhammad. Bayan an kammala yi mana lissafi Abba ya ciro ATM ɗinsa zai miƙa masu kenan muka ga an miƙo masu cash na kuɗin. A tare muka juyar da kallonmu. Ibrahim ne tsaye ya miƙa masu cash ɗin dolars wai ya biya mun kuɗin sayayyar da na yi. Da sauri na dawo da kallona kan Abba, ya tamke fuska tamau, tunani na shiga yi ya aka yi Ibrahim ya biyo mu?................ labarin A'isha zai dinga zuwa maku labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi. FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥 LABARIN AISHA.🥹💔 PART 30 Ibrahim ne tsaye ya miƙa masu cash ɗin dolars wai ya biya mun kuɗin sayayyar da na yi. Da sauri na dawo da kallona kan Abba, ya tamke fuska tamau, tunani na shiga yi ya aka yi Ibrahim ya biyo mu?..... Abba ya baiwa matar ATM ɗinsa bai kula Ibrahim ba, dan tun da ya fahimci Ibrahim jahili ne ya ce bashi da lokacinsa. Ibrahim ya koma gefena ya tsata tare da cewa. "Aesh, ban taɓa tunanin akwai watarana da zata zo babu auren kowa a kanki ki bi wani namijin ki barni ba". ....... Ban san ya akayi ba, ban san meyasa tsoron Abba ya shiga raina ba, coz yana da kwarjini da cika ido sosai, na ji tsoron kula Ibrahim a wajen, sai kallon Abba nike yi shi kuwa ya ɗauke kansa daga kallona. Na gagara amsa Ibrahim wanda ban san dalili ba, ya dinga rokona kada in rabu da shi a karo na biyu, ban iya bashi amsa ba, da ya cika matsa mun sai na juya da sauri na fice daga wajen, na koma wajen motocinmu, ban san ya suka kare ba, na shiga motarmu na zauna, na kifa kaina da jikin kujera ina kuka sosai. Ban san yaushe Abba ya fito daga cikin wajen ba, ban ma san yaushe ya shigo cikin motar ba, sai ji na yi ya riko hannayena dukka biyu da hannunsa ɗaya, ya kai ɗayan hannunsa ya ɗago fuskata muka fuskanci juna. Driver ya tada motar muka kama hanyar gida, Abba ya ce. "Please ya isa kukan haka, saboda ke fa yasa ban sanya an karya yaron can ba, na maki alkawari a gida kafin mu zo kan cewa ba zan sake ba, kinga ai ban sake ba ko? One thing na sani shi ne zan ɗauki mataki da gaggawa, dan ba zan iya bari wani yana saka mun ke kuka ba". Uhm, kuka nike ta yi ban wani sauraresa ba, hakan yasa ya ce. "Takwara zo ka tayani bawa Mammy hakuri, ta daina kuka ko muma mu fara tayata". Ya faɗa yana jawo Muhammad dake gefensa. Muhammad ya haye jikina yana faɗin. "Mammy uncle daddy baya son kukan nan ki bari". Harshensa bata fita sosai, amma zaka iya gane me ya ce. Abba ya ce mashi. "Ba na ce ka daina ce mun uncle daddy ba? Ka ce mun daddy kai tsaye, ni ne daddynka"........ Ya ce. "To daddy"........ Suka cigaba da bani baki, naki kulasu har muka isa gida, muna parking na fito da sauri na wuce cikin gida. Kai tsaye ɗakin Zahra na shiga, na fara jin tamkar ba zan iya cigaba da zama a kasar nan ba, tun da na zo na keɓance kaina, ko waje bana fita duk gudun kada in sake shiga wata damuwa, ko yawo bana zuwa, kai daga gida sai makaranta, a makaranta ma ina class ko da mun fita, idan na bar class to gida zan dawo, babu in da na sani a cikin school ɗinmu face ajinmu da hanyar komawa, bana kula kowa bana shiga komai, amma duk da haka na gudu ban tsira ba, matsala sai da ta sake nemoni ta dawo cikin rayuwata, wani irin musifa ce wannan. Abba ya shigo da kayan da Muhammad a hannunsa, ɗakina ya kai mun kayan sannan ya wuce nasa ɗakin, ya kwanta a kan gado yana ɗaura Muhammad a kan kafafunsa yana ɗaga shi sama ya sake sauƙewa. Nan fa ya fara tunanin yadda zai yi wa wannan matsala madakata, dole yai wa tufkar hanci, meyakamata ya yi?. A fili ya ce. "Ina tsananin sonta, na shafe shekaru ina dakon hakan, ba zan iya hakura da ita ba, danginta basa son danginmu, ba zasu bani ita ba, dangina sun wahalar da ita, anmana kuɗin goro, ina son ganin tana rayuwar tsananin farinciki tamkar yadda ya sanyani farinciki, ina son ganinta a kusani dani, meyakamata in yi?". Muhammad yana dariya yana kallonsa, Abba ya dawo da shi kan cikinsa, ya hau sumbatar yaron, can ƙasa ya ce. "Ina tunanin hanyar da zan mallake mammynka cikin sauri kuma cikin sauƙi ne my baby". Ya sake sumbatarsa tare da ɗauko wayansa, ya kunna data ya shiga media yana kara tunanin yadda zai samu damar mallakeni cikin sauƙi kuma nan take, dan wlh yanzu baya son ko kwana ɗaya a kara bai mallakeni ba. Yana shiga Media ya ci karo da wani hotonmu a shopping, a ƙasan hoton an rubuta shahararren ɗan wasan ƙwallon kafar nan da ludayinsa ke kan damu, wanda yake tashi tauraronsa yake haskawa a yanzu watau ABBA MUHAMMAD HUSSAIN, an gansa tare da wata zuƙeƙiyar budurwa a shopping, haka zalika mun ji daga majiya mai karfi cewa yana da manyan baki a gidansa na Germany wanda cikinsu har da wannan budurwa da yake yawo da ita, jama'a me zaku ce a kan hakan?. Ɗan dafe kansa ya yi, abin da yake gudu sai da ta faru, watau duniya na ƙoƙarin dole sai ta tona ko shi waye, kai ɗaukaka ko wahala, kai rayuwarka a takure take, yanzu yaushe aka san ya kawo wasu gidansa ban da sa ido da sharrin ɗaukaka, kome kake kallon jama'a a kanka saboda wannan ɗaukaka. Ya ja siririn tsaki tare da jefar da wayar can gefe a kan gadon. Ya yunkura zai miƙe da Muhammad a jikinsa kenan wata idea ta faɗa mashi a cikin kwakwalwarsa, da sauri ya koma ya zauna ya hau tunani. Jim kaɗan ya saki wani ƙayataccen murmushi, da sauri ya miƙe ya fito yana ta mannawa Muhammad sumbata a kumatu tamkar zai cinye mashi kumatu. Kai tsaye ɗakin Zahra ya nufa, nan ya iskoni kwance a kan gado na tada kai da cinyar Zahra, cikin harshen Hausa ya ce. "Tawan"....…. Na yi banza da shi, ina jinsa kuma....... Kallon Zahra ya ɗan yi tare da cewa. "Sauka a gadon bari in yi magana da ita"........ Da sauri ta sauka ta fice ya bamu waje wai ita irin mai biyayyar nan dan ta sace zuciyansa. Ya dawo gefen gadon ya zauna, sai da ya sha fama da rarrashina kafin ya samu kaina, sai da ya dinga bani hakuri, ya ce ko dai yai tsallen kwaɗo ne, na dai sharesa, da ya matsa ne na kindaya mashi sharuɗa, na ce. "Daga yau ba zaka sake mun abin da ka mun na walaƙanta baƙona ba, kuma ka yi alƙawarin rage abin da kake mun na kafa mun dokoki"........ Aikuwa duk abin da na nema ya ce zai yi yadda nike so, hakan yasa na sake har na miƙe. Ya matsa mun sai da muka je ya bani abinci na ci, sai da ya bari mun yi sallar magrib da ishai, hankalina ya kwanta, na koma walwalata tamkar da, around 9 na dare ya iskoni a ɗaki, a lokacin Muhammad ya yi barci ya kwantar da shi a ɗakinsa, sannan ya zo ɗakina. A lokacin na kammala waya da Ibrahim, na dinga bashi hakuri kan abin da ya faru, ya ce mun ba komai, ai mai nema baya fushi, na ji daɗin yadda bai yi fushi ba, muka yi sallama kan zamu haɗu a chat, dan bana son yawan surutu, amma idan chat ne sosai zan yi dan typing ne ba magana da voice ba. A saman side sofa Abba ya zauna tare da cewa. "Tawan barka da dare"...... Fuskata a ɗauke da murmushi na amsa da. "Yauwa brk dai nawan, ka zo sakani cin abincin dole ko? To a ƙoshe nike, ɗuren da ka mun da rana ma bai sakeni ba"........ Ya ɗan nisa tare da cewa. "Uhm ba wannan bane, tawan ina cikin tsananin damuwa da tashin hankali ne". Na ɗan zazzaro ido tare da cewa. "Kai, subhanallah, damuwa kuma? Meyafaru?"........ Ya ɗan nisa tare da ciro wayansa ya nuna mun hotonmu da aka yi posting a media muna wajen shopping, ya ce in kalli wannan. Na kallah, sai ya ce in karanta abin da aka rubuta, na karanta, bayan na kammala na ɗago na kallesa, fuskansa ɗauke da alamar damuwa. A sanyayye ya ce. "Kariyata tana fuskantar barazana, yanzu sharri aka mun wai na kawo karuwa gidana, makiya suna neman cin galaba a kaina, idan hakan ya tabbata dole in hakura da burina na kwallo"........ Na ƙara zazzare ido a kansa, ban san komai dangane da kwallo ba, sai abin da ya sanar dani, hankalina ya yi bala'in tashi, cikin rawar murya na ce. "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, yanzu ni ce karuwar, na shiga ukuna na lalace, shiyasa na ce maka ba zan zauna a gidan nan ba, ga shi yanzu wahalarka na shekaru biyu na ƙoƙarin tashi a banza, nima kuma duniya na neman ɓata mun suna, ga yarana na girma, yanzu me abin yi?". Ya nisa tare da cewa. "Yanzu team da nike bugawa kwallo sun kirani dan jin ta bakina, bani da zaɓin da ya wuce na ce masu ke matata ce ba budurwata ko karuwa yadda suke tsammani ba, na faɗi haka ne dan in kare kariyata kuma in wanke maki sunanki a idanun duniya kuma, to amma da na faɗa masu ke matata ce sun ce dole in kawo masu shaidar aurenmu domin su nunawa duniya su wanke kariyata dake ƙoƙarin girgiza kema su wankeki"........ Da yake nasan duk wanda aka yi wa ƙazafi da mace ana lalata mashi suna sai na yarda, naga ko shugaba, ko wani soja or ɗan'sanda idan aka masu irin wannan sharrin har rasa aikinsu suke yi, sai na yarda zai iya rasa kariyansa, wani irin tsananin tausayinsa ne yakamani. Na ce yanzu me abin yi? Shi kam ganin da alamar ya yi nasara, alamar tausayinsa ya bayyana a fuskata ne yasa ya gyara zama, dama yasan zai yi nasara a kaina saboda ya san halina da tsananin tausayi, in dai dan in cire wani musulmi daga cikin wata matsala ne to zan iya sadaukar da komai nawa, dan haka ya san raunina kenan shi ne tausayi, shiyasa ya zo mun ta wannan siga. Ba karamin daɗi ya ji da nace me abin yi. Sai ya ce. "Please tawan ki yarda mu je a ɗaura mana aure, a ƙasar nan idan sun ɗaura mana aure akwai takardun da zasu bamu na shaida, idan na kaiwa team ɗinmu suka sanya hannu, suka yarda ke matata ce, daga nan kin ceci kariyata kema sunanki zai wanke, kinga daga baya sai in sawwaƙe maki". A zabure na ja da baya ina kallonsa, muryana har tana rawa wajen cewa. "Aure kuma Abba?"...... Ya jinjina mun kai game da cewa. "Dan ALLAH ki taimakeni, ni shaidar auren kawai nike so, da zarar na kai masu shikenan, sai mu dawo ko da sati ɗaya ne sai in sawwaƙe maki kinga kin ceci kariyata kin kuma ceci mutuncinki". Na ce. "Amma ai su Hajiyarmu ba zasu yarda da wannan ba, Abba ba'a wasa da aure, ka aureni sati sai ka sakeni, wannan ba isgili muke shirin yi wa sunnar ma'aiki ba? Gaskiya ni bana son duk abin da zai sanya ran iyayena ya ɓaci ma, ba zasu yarda ba na sani". Ya yi ƙasa da murya, cikin nuna tsananin damuwa ya ce. "Wannan aure ba sai su Hajiyarmu sun ji ba, kinga ba auren farko bane, sannan kin haura 18 years, and kuma kinga auren sirri zamu yi, kariyata da mutuncinki kawai zaki ceta, ba zamu bari su hajiya su ji ba, a sirrance zamu yi har mu rabu kinga babu wanda ya sani". Na girgiza kai alamar a'a, na ce ni dai ba zan yarda na. To hankalin da tunanin mace da namiji ba ɗaya ba, kuma aka ce wanda ya rigaka kwana dole ya rigaka tashi, aikuwa ya dinga nuna mun fuskan tausayi, har kamar zai mun kuka, ya dinga lallaɓani yana nuna mun ba sai su Hajiyarmu sun ji ba, saboda abu ne da za'ayi dan in ceci kariyansa da mutuncina kawai, ko dan ƴaƴana na ceci mutuncina da duniya ke ƙoƙarin kirana da karuwa, ba batu ake ta iya Nigeria ba, shi ɗan kwallo ne da ya zaga duniya, dan haka duniya ne gabaɗaya zata yarda cewa ni karuwa ce, za'ayi ta posting hotona, idan yarana suka tashi da wani fuska zasu kalli wannan abin? Duk yadda na so naƙi yarda tausayinsa da tunanin makonar yarana yaki barina, tabbas ina da zuciya mai rauni da tsananin tausayi shiyasa ma nike da saurin kuka. A wannan dare dai bai kyaleni ba sai da na aminta da zamu yi auren sirri na sati ɗaya dan in ceci kariyansa da mutuncina da ƴaƴana, muka yi yarjejeniyar sati ɗaya zai sakeni babu wanda zai sani, ya aminta da hakan, har da rubutawa muka yi kowa yasa hannu. Sai ya ce ba ina da kawunai a kauye ba? Na ce mashi e, ya ce in bashi number mutum ɗaya, zai san yadda zai mashi dabara ya zame mun waliyi. Da farko na tsorata kada ya ja su Hajiyarmu su ji in shiga ukuna, amma da ya kwantar mun da hankali sai na samu natsuwa. Na ɗauki number yayan daddynmu dake kauye yaƙi dawowa birni da zama na bashi, farinciki tamkar zai cinyeni ɗanya, ya dinga mun godiya yana saka mun albarka, ni duk na ɗauka yana mun godiyar na ceci kariyarsa ne, ko kaɗan ban kawo komai a raina ba. Ya miƙe da sauri zai fita na ce mashi. "To kai waye zai maka waliyi kenan?"...... Ya juyo yana ɗan sauke ajiyar zuciya, ya ce. "Ƙanin Innata kawu Shehu"......... Na ce. "Ban san shi cikin ƙannen Mama ba". Ya amsa da. "Ba ƙanin Mama bane, ƙanin Innata ne, ke dai ina zuwa, zan dawo anjuma". Na ce okey, ya fita da sauri. Tsantsar farinciki yasa yana fita ya tafi ɗakinsa yai wa UBANGIJI sujudur shukur, sannan ya kira number kawuna dana bashi, bayan sun gaisa ya faɗa mashi duk abin dake faruwa bai ɓoye mashi komai ba, sannan ya faɗa mashi nufinsa. Wan babanmu da yake babban mutum ne kuma mai tsastsauran ra'ayi, dan daddynmu ma ba ta daɗi yake kwasa a hannunsa ba, dan haka ya ce gaskiya ne, babu wanda ya dace ya aureni dama sai Abban, saboda shi ya sanni sosai, a haka kuma yake sona, sannan yana tsananin son yarana fiye da ubansu ma, bugu da ƙari yana tausayina sosai, ga kulawa, and ɗan halak ne da baya manta alkhairi, ai duk duniya in akwai wanda zan aura to shi ne. Kun san maza su abin kunya ba damunsu yai ba, dan haka babu ruwan wan babana da wani abu wai shi Abbie tun da musulunci bai haramta ba, ya cewa Abba da zarar ya je masallacin ɗaurin auren ya kirasa a waya zai tsaya mashi, idan an ɗaura in muka dawo kasar sai a sanar da su daddynmu duk ma wacce za'ayi ayi ne shi zai tsaya mana, wan daddy da iya kara bala'i har da wani gaskiya ya yabawa Abba, ya dinga jinjina mashi da sanya mashi albarka, duk ban san me yakefaruwa. Yau dai kwanan tsananin farinciki Abba ya yi, ya kira kawunsa Shehu ya faɗa mashi shi ne Abba, kuma yana raye, ya bashi hakuri kan buyan da ya yi, sannan ya ce kada ya faɗawa kowa yana raye, ya bari karshen shekarar nan zai zo ya ga kowa. Kawun nasa yai mashi faɗa sosai kafin ya kyalesa. Sannan Abba ya bijiro mashi da abin da yake so, kawun bai ja wata magana ba ya ce ba damuwa. Ai Abba kwana sallar ya yi saboda godiya ga ALLAH da ya cika mashi burinsa. Ni kuma na kwana waya da Ibrahim, mun shirya a kan gobe da safe around 9 zamu haɗu, ina da class around 2, so zamu haɗu mu yi hira har zuwa 2 in wuce school, mun yi da shi zamu haɗu a wajen wani garden dake kusa da tsohon gidanmu. Ina nawa shirin Abba na nashi. Washegari da safe Abba ya shirya cikin wasu dakakkin gezner golden color, yai fitina cikin kayan, ga ɗinkin tai balain zama a jikinsa sosai, ya sha wata king hat da kuma half cover shoe mai fitinannen kyau da tsada, dukka sabbi ne bai taɓa sakasu ba sai yau, wani tsadadden diamond watch ya ɗaura a hannunsa. Ko maƙiyinsa ya kallesa sai ya sake kallonsa, dan ya haɗu larshen haɗuwa. Tun around 7 ya kamma shirinsa, sai 8 ya tasheni daga barci, yau ko breakfast bamu yi ba, haka ya sanyani shiryawa wai zamu je a ɗaura aure. Ban wani damu ba tun da auren sati ɗaya ne, na shirya cikin abaya nai simple make up, sannan muka tafi. Tun da muka fito nike satar kallonsa, yai wani bala'in tafiya da imanina ne, yai kyau, hair ɗinsa sai wani sheƙi yake yi, ga kwantaccen sajen nan nasa, ya salam, ya haɗu karshen haɗuwa. Wani katon masallaci muka je, har ciki muka shiga tare, ni a tunanina taimako zan yi, ban san ni Abba ya rainawa wayau ba. Aikuwa ya kira waliyina da wayinsa ya haɗasu, ga liman aka yi magana, wan babanmu wai a bani sadaki dubu talatinma ya isa, abin ku da mutanen kauye, nan gani suke kuɗi ne dubu talatin. Ina jinsu amma ko a jikina, na ɗauko wayata na cigaba da chatting da Ibrahim, ya ce mun ya isa wajen da zamu haɗu, na ce mashi nan da 20 mins zan zo wajen. Ya ce okey ya matsu ya ganni. Ban san nawa Abba ya yanke sadaki ba, ina can ina biyewa Ibrahim, sai ji na yi Abba ya ce. "To tashi mu tafi my wife"......... Na ɗago na kallesa kafin in ce. "A'a fa, kada ka fara, ni auren sirri ce". Murmushin da bai taɓa yin irinsa ba ya yi har dimples ɗinsa sukka biyu suka wani lotsa sosai tare da kama hannuna yana faɗin. "To na ji dai tashi mu je"....... Na kwace hannuna tare da miƙewa, muka fito, kai tsaye muka koma cikin motocinmu. Mun fara tafiya na ce. "Nawan ku saukeni a nan akwai in da zan je". Ya wani kalleni kafin ya ce. "Ina ne in kaiki da kaina?"........ Na ɗan turo baki. "Zan je da kaina, ni ka saukeni kawai"...... "Ban yarda ba". Ya faɗa yana haɗe rai...... "Ai ni ba yardanka nike nema ba, ina da daman zuwa ko'ina, kawai ku sauƙeni"....... Yai shiru bai amsani ba. Na sake cewa su saukeni, sannan ne ya ce. "Ba in da zan barki ki je ke kaɗai, kawai ki faɗa mun in da zaki je in kaiki". Na haɗe rai game da cewa. "Ba fa zan faɗa maka ba kawai ku sauƙeni"...... Yai shiru bai sake biye mun ba, na dinga su sauƙeni bai kulani ba. Sai da na ga da gaske ba kulani zai yi bane yasa na ce. "Garden na bayan tsohon benenmu zaka kaini"...... Ya umarci driver da ya juya mota mu nufi wajen. Na dinga hararansa, yana ganina bai kulani ba, kamar cewa kyayi masifar ki gama yanzu dai ke mallakina ce, zaki yi bayani ne. Muna isa bakin garden ɗin na ce su sauƙeni a nan ya isa su tafi. Abba ya ce. "Malama, babu in

Chapter 25 of 38