Share this page
ai da kin zauna kin jira ya dawo ɗin sai ki taho da shi"..... Na ɗan zare mashi ido kafin in ce. "Amma Abbie ta yaya zan zauna sama da wata ɗaya da rabi a gidan iyayena bayan da aurena kuma lafiya lou muke dukkanmu, ba jinyar ciwo na je ba, sannan ba wani waje mai nisa muke ba, ina Kano ina Kaduna da zan je in yi wannan uban jimawa da suman ziyara ga yara suna makaranta, kana son daddy ya zargemu ne?". Sai ya ɗan sassauta haɗe fuskan kafin ya ce. "Haka ne kuma, amma idan ya dawo ai za'a turo mana gold ɗin ko?"........ "Sosaima, ai su Hajiya sun yarda dani, sai yaba maka suke yi, wai ka yi ƙoƙari ka natsar dani na zama mai hankali". Ya ɗan yi murmushi kafin ya ce. "Na sha fama dake ai kafin in rabaki da yarintar nan, kai Aisha kin bani wahala, kin fa taɓa cewa zaki kona mun gida in ban sakeki ba, wannan ɗan bakin naki sai masifa ya iya lokacin, ni ban san ma ya aka yi daga baya kika daina masifar kika natsu ba". Na ɗan yi dariya tare da cewa. "Duk kai ne sila ai mijina, kai ka natsar dani da salon soyayyarka"....... Shi ma ya ɗan yi dariya mara sauti kafin kuma ya ɗan haɗe rai ya ce. "Yanzu ya zan yi da kuɗin Sadiq da na baki? Babu wasu kuɗi a account ɗinki ne dan in rage mashi?". Cike da nuna damuwa yai maganar, Abbie ya iya makirci kala-kala mutumin nan. Na amsa da. "Babu ko biyar a account ɗina"........ Ya ɗan zaro ido. "Kina nufin ki je gida har ki dawo su daddy basu baki komai ba? Da fa idan kika je suna baki wajen million ɗaya idan zaki dawo, baban yaya ya baki, Hajiya ta baki, daddy ya baki, Aunty Maryam ta baki, kai har Safiyya baki kuɗi take yi in zaki dawo, amma kice mun basu baki ba?". Na amsa da. "Daddy ya ce ni da zan ɗauki gold ai ba sai sun bani kuɗi ba, dubu hamsin kawai ya bani"..... Kuma karya nike, Hajiyarmu kawai dubu ɗari biyu ta bani, Yah Abbas da yake students ne ya ban 100k, Safiyya ce ta bani 50k, daddynmu ma ya bani 200k, da yake duk gidanmu ƴan kasuwa ne, yaro tun yana karani a gidanmu ake buɗe mashi business ɗinsa, a buɗe account daban ana zuba mashi riba, wannan shi ne tsarin daddynmu, ana haifar yaro ya kai 5 years za'a samu waje a buɗe mashi nashi business ɗin, ana tara mashi kuɗin a account daban, da wannan ribar tasa daddynmu yake biya mashi kuɗin makaranta da komai, idan ya girma ya mallaki hankalinsa ya gama karatu sai a miƙa mashi kasuwancinsa a lokacin ta kafu sosai, ga riba a account, yanzu haka Safiyya tana da katon shagon sarar da kayan masarufi, amma har yanzu daddynmu bai mallaka mata komai a hannunta ba, shi yake saka ido a kai, ana zuba mata riba a account, sannan da wannan ribar ake biya mata kuɗin makaranta, kunga sana'arta na karantar da ita, wannan shi ne tsarin gidanmu, shiyasa duk ƴan gidanmu ba cima zaune ba ne, da ƴan kuɗaɗensu, Abbie ma tun asali yaron shagon yayanmu Abbas ne tun Yah Abbas na ƙarami. Kafin yaro ya girma an tara mashi. Hakan dabara ce mai kyau ga iyaye, ku buɗe masu kasuwanci tun suna ƙanana, ku buɗe account kuna tara masu riba, ku yi amfani da wannan riba wajen karantar da su, saura ku bar masu, da sun girma sun mallaki hankalinsu ba sai kun sake ɗaukar dukiya daga naku kun bashi jari ba, ga nasa already tun yana karami, kuma already kun kafa mashi kasuwancin a lokacin ya yi karfi kowa ya san shi......... Wannan shawarace nike baiwa iyaye, ko ba da kuɗi mai yawa ba, 200k zai sama maki sana'a ɗan daidai da zaki buɗewa yaro kina tara mashi kuɗi, zaki ji daɗin hakan matuƙa, kuma zaki gina iyalinki, ba zasu taso a wahale ba, idan kika buɗewa na farko, zaki iya amfani da ribansa da kika tara ki buɗewa na biyu ma. Shiyasa ƴaƴan manyan nan suke tasowa da kuɗaɗensu, tun da aka haifi yaro ake samu katafaren waje a buɗe mashi kasuwanci da sunansa a buɗe mashi account ana zuba riba, haka suke yi, yaro ya taso da kuɗaɗensa a jiki. ------------------------ Abbie ya ce. "To tura mun dubu Hamsin ɗin, amma yanzu ya za'ayi mu biya Sadiq kuɗinsa ne ma?" Na amsa da. "To idan Sadiq ɗin yana sauri da kuɗin ka bashi a cikin 5M ɗin da ka karɓa a hannuna last time mana"...... Take yai kicin-kicin da fuska. "Gori zaki mun dan kin bani 5M?!". Cikin faɗa ya faɗa...... Na ce. "Haba Abbie, ai kasan gori ba gadon gidanmu bane, mu bama gori, domin tsakani da ALLAH muke duk abin da zamu yi".. Nan ma ya fara sababi wai na yaɓa mashi magana, kenan ina nufin su ne danginsu ke gori, ni kam da nasan kuɗi na zo sake tatsa a wajensa me zai ja mun faɗa da shi, sai cewa na yi. "Kwantar da hankalinka angon Zainabu abu mai tagwayen suna, ba haka nike nufi ba, ALLAH ya baka hakuri".. Har cikin ransa ya ji daɗin kalamaina, sai ya ɗan sake fuska, wai in tura mashi dubu hamsin ɗin, na ce mun yi cefenen gida, mun sha mai a mota, babu ko sisi da ya rage, kuma karya nike, duk kuɗin da na samu gabaɗaya babban yayanmu na baiwa domin ya fara tara kuɗin gini, ban dawo da ko sisi ba dan ma kada ya gani ya karɓa, amma na ce mun yi cefenen gida. Nan ma zai fara masifa na sake bashi hakuri, sai da na sanya shi dariya sannan na ce. "Habibi yaushe ne aurenkan nan, na matsu fa?". Ya ɗan yi shiru, sai kuma ya ce. "Gaskiya fa ni har yanzu Zainab ɗin nan bata kwanta mun a rai ba, na bari ne zuwa gaba in ji ko zata kwanta mun a rai". A zuciyata na ce. "Namiji ƙanin ajali, wai ya bari ne ko zata kwanta mashi a rai, kai maza, hmmmmm".. Aikuwa nai caraf na ce. "A'a ni ban yarda ba, da zafi-zafi ake dukan karfe, maza tura mun kuɗi in fara zuwa haɗa kayan lefe, naga idan na barka ba zaka yi abin da ya dace da wuri ba, da kaina zan haɗa mana kayan lefe, komai iri ɗaya zaka yi mana ka ce ai ko?". Ya kuwa gyaɗa kai munafikin, sannan ya ce. "Kin dai matsa sai anyi auren nan ko?". .... Na ce. "Kwarai kuwa, yanzu me tsarinka? Da nawa zaka fara haɗa kayan lefen nan?". Ya ɗan yi shiru, can ya ce. "Da kamar 2M ai ya yi ko?"....... Da sauri na ce. "Kai Abbie ƴar tsana zaka auro ne? Me kuma 2M"..... Ya ce. "Ai farawa kika ce"...... Na jinjina kai. "Haka ne, to yanzu gobe zan fara zuwa haɗa kayan, ka tura mun kuɗin". Ya jinjina kai game da cewa. "Ki zaɓa maku masu kyau-kyau fa, zan ce Zainab ɗin ta kiraki, zata faɗa maki size da kalar da take so"........ Nai maza na capke da cewa. "A'a Abbie, ka tambayeta ta faɗa maka sai ka faɗa mun, ba sai ta kirani ba". Ya jinjina kai sai murmushi yake yi, dan ya ji daɗin yadda nike goya mashi baya a wannan auren, bai san duk tarasa nike ba, akwai ranar girbi. Yake ƴar uwata mace, kada ki tada hankalinki idan namiji zai kara aure, ki bi dabara irinta Aisha, In Sha ALLAH zaki ji dadi, domin kuwa ko kin tada hankali ko baki tada ba sai ya kara idan yai niyya, gara ki kwantar da hankalinki, ki shiga jikinsa ko 500k ne ki samu ki kwato daga wajensa, a wannan lokaci kome kike so zai maki, ki samu wannan kuɗi ki samawa ƴaranki jarin kasuwanci, da kaɗan-kaɗan har kasuwancin ya girma, ba'a rigima yanzu, amma mu je mu ga ya Aisha zata yi sai mu ɗauki daras. Na dinga yi wa Abbie daɗin baki har ya tura mun 2M ɗin nan, munafuki ashe yana da kuɗin, ya tura yana kara mun kashedin kaya mai kyau fa zan saya. Yana tura mun ya miƙe wai bari ya je yai wanka, ya bar wayansa a wajen saboda yana tunanin ban san password ba. Yana shiga wanka na ɗauki wayar na gudu ɗakina, na haye gado tare da cire password ɗinsa, kai tsaye na shiga chat ɗinsu da Zainab. Abin da na fara cin karo da shi shi ne inda Abbie yake ce mata. "Ina mutuwar son mace mai manya-manyan boobs sosai, amma ALLAH bai bani ba sai yanzu da na sameki"........ Da sauri na kalli kirjina, tabbas Abbie ya yi gaskiya, bani da manyan breast, ƴan daidai da jikina suke, amma kuma nawa suna tsaye tamkar ban taɓa shayarwa ba saboda ƙanana dama basa faɗuwa, kuma wlh nawa sunfi nata fasali da kyan gani, sai dai ba manyan bane, amma kuma abu ɗaya, Zainab tana da uban yawan breast amma bata da ƙasa sam, baya a shafe kamar allo, bata da shape kamar giwa take. Ni kuwa ALLAH ya bani hips sosai, har wani round ƙasana yai, ga shape sosai nike da shi, cikina can ciki a shafe yana manne da baya, dan ƴar siririya nike, Zainab kuma ƴar lukuta sosai, tana da katon cikin da ya fi nawa da na haifi yara uku saboda kibarta, ni jikina ɗan cas, bai yi karya ba da ya ce ban da breast manya, amma abin ya mun zafi, meyasa zai faɗawa wata yanayin halitta ta? Wannan abu ya mun ciwo. Ban tashi firgita bama sai da na kara gaba a chat ɗin nasu, Ya Salam, innalillahi wa inna ilaihi rajiun, Zainab ta turo mashi hotunan kirjinta tsirararsu, ta tuɓe ta ɗaukesu wasu baƙaƙekirin, rusa-rusa kamar kan mutum, har sun kwanta saboda manya ne sosai, ga nawa ƴan daidai farare tas saboda jikina fari, har kan nipple ɗina jajir yake saɓanin nata bakinkirin, a ƙasan hoton ta rubuta mashi ka gansu, suma sun matsu a ɗaura auren nan su zo gareka ka yi yadda kake so da su. Shi kam ya rubuta mata wash my happiness kin gama kunnani, please ki tayani kwantar da abin da kika tayar. Aikuwa babu kunya babu tsoron ALLAH Zainab ta dinga zuba mashi sexy words, kalaman batsa, yana tayata, har da video call suka yi, a ƙasan video call ɗin ta turo mashi gaskiya kana jimawa baka samu gamsuwa ba, watau in na fahimta a sex video call suka yi, innalillahi wa inna ilaihi rajiun, shi kuwa ya rubuta mata sai ma kin shigo zaki san ina jimawa, dan tun kina hakura sai kin fara kuka, yanzu ma dai kawai na danne ne amma ban gamsu ba, da zan ganki a fili yanzu da kin sha mamaki, please ki kula mun da kanki, kin san ke kaɗai nike samun natsuwa a wajenta......... Sai yanzu na gane meyasa Abbie baya nemana mu yi kwanciyar aure, watau ta waya Zainab ke biya mashi buƙata, innalillahi wa inna ilaihi rajiun, ji na yi numfashina na sama-sama yana about to ɗaukewa, ya Salam, wani irin sara mun da kaina yai sai da na zaci fashewa zai yi, na gagara iya cigaba da kallon chat ɗinsu, na yi saurin fita na kashe wayar, jikina ya dinga kerma, hawaye sun gagara zuba daga idanuna, ya rabbi wani irin musifa ce wannan?. To ƙirana ga ƴan mata, ku ji tsoron ALLAH, ku sani duk abin da kuka yi wa uwayen gidanku a lokacin neman aurenku billahil lazi sai an maku irinsa, ku rinƙa biyewa maza kuna kwantar masu da sha'awarsu ta waya ku hanasu kusantar matansu na sunnah saboda tabbatar rashin hankali irin naku? Sai ku ji mace tana complain tun da ya fara neman aure baya nemanta su yi sunnah, ashe shi yana can ana biya mashi buƙata ta waya, wlh ƴan mata ku ji tsoron ALLAH, UBANGIJI ya ce duk abin da ka yi wa wani sai an maka, ku daina biyewa mazan nan, idan su basu yi hankali shauki ya rufe masu ido, ku baku da hankali ne? Mata fa kuke! Baku tunanin kafin ya auri uwar gidan nasa ya mata abin da ta fi wanda yai maku na kalamai da nuna kauna? Baku tunanin sun so juna a baya, amma duk da wannan so ya watsar da ita ya je neman aurenki, baki tunanin kema watarana zai watsar dake? Idan taƙamarki ke budurwace, kirjinki a cike a tsaye, gabanki a matse, to ki sani ita ma haka take a baya, sannan ki sani dole zaki haihu, kirjin da kike taƙama dashi kike mata yanga zai zama kila ma ya fi nata lalacewa da kwanciya, dan kowa da irin halittarsa, budurcin da kike taƙama da shi ki sani ita ma ta yi takama da nata a baya, amma sai da ya kwace mata shi, to ki sani kema zai karɓi naki, kamar yadda ya karɓi nata bai hana shi karoki ba, haka zai karɓi naki ba zai hanashi karo wata ba, namiji bashi da alƙibla a wannan ɓangare ki ji kuma ki sani, dan haka kada ki cutar da ƴar uwarki mace saboda shi, ki ji tsoron ALLAH ki ɗaurasa a kan hanya, kisa ya kyautatawa uwar gidansa ko dan kema mai zuwa ta gaba ta kyautata maki, shawarar da zan baiwa ƴan mata kenan, ku kuma uwayen gida Aisha ce da kanta zata maku karatu a aikace, ku dai ku cigaba da bibiyarta. Kwanciya nai a wajen na ci kukana har sai da na ji alamar yana zuwa, na miƙe da sauri na faɗa toilet, ya shigo ya ɗauki wayansa yana tsorace kada ace na buɗe, jikinsa har yana rawa ya buɗe wayar, ALLAH ya taimakeni na fita chat ɗin na goge bai nuna kamar an buɗe ba. Ya sauke ajiyar zuciya game da ficewa daga ɗakin dan lokacin sallar magrib ta yi. Ina jin ya fita na wanke fuskata na ɗauro alwala na fito, tsabar tashin hankali wlh ban san sallah raka'a nawa na yi ba a wannan magrib ɗin, ina kai sujjada ina kuka, ina ɗagowa ina kuka, hawaye har da majina, da kyar na iya rarrashin zuciyata. Bayan sallar ishai suka dawo, Abbie ya wuce ɗaki, na ce mashi abinci fa, ya ce mun ya ƙoshi, duk ya ƙosa ya je su cigaba da lalata da Zainab a waya saboda bala'in sha'awarsu. Na ɗauke kai na zubawa su Abba abincin tare da basu, sannan na wuce ɗaki, ban ko kula da su ba, Abba ya fahimci mun samu matsala da yayansa, amma bai yi gigin bina ya tambayeni ba, ya ɗauke kansa. Na kwana kuka, karfe 2 na tashi na fara sallah, ina kuka ina sallah, ban ma san raka'a nawa na yi ba, da na yi biyu zan yi sallama, tashin hankali yana neman zautar dani. Babu abin da ya fi bani takaici wai kirjin matarsa ƙanana, kuma wai a wajen Zainab kawai yake samun natsuwa, tun bai aureta bama, to idan ya aureta me zai ce kuma? Bola zai mayar dani?. A haka a kan dadduma around 6 barci ya ɗaukeni. Ban farka ba sai 12, Abba ya zo ya sameni ina barci sai bai tasheni ba, ya shirya su Hassan suka yafi school. Ina farkawa nai wanka, idanuna sun kumbura sosai, Abbie ya tafi kasuwa, yanzu Abbie fa ko abinci baya nema a gidan. Ina wanka na shirya na shiga ɗakin Abba, Fahad kawai na samu yana zaune rike da waya. Yana ganina ya ɗaga mun gaisuwa, na ce mashi ina Abba bayan na amsa, ya ce ya fita tun da safe. Khalifa na shagon kawun nasa. Na dawo ɗaki na kira Abba a waya, bugu ɗaya ya ɗauka, na ce. "Nawan zo ka kaini kasuwa". Karfin hali kawai nike, amma duk na fita hayyacina. Ya amsa da ga shi nan zuwan. Na zauna a parlo ina jiransa. Jim kaɗan sai ga shi ya dawo sanye da kayan kwallo a jikinsa, kallo ɗaya ya mun ya ɗauke kai, ya canza fuska, coz idanuna sun kumbura sosai. A takaice na miƙe muka tafi kasuwa, muna tafiya a hanya bai ce mun kala ba nima haka ban ce mashi ba har muka isa. Kayan lefen na fara saya mana, na kashe 1.5 instead of 2M da ya bani, na rage 500k, tun a kasuwar na turawa yayana 500K ɗin, ba'a cikin kuɗin kayan Zainab na rage ba, a cikin kuɗin kayana na rage, sannan na samu saukin wasu abubuwan a kasuwa, na turawa yayana kuɗin muka kamo hanyar dawowa gida. Wasa-wasa sai da aka shafe wata Abbie bai nemeni in biya mashi buƙatarsa na sunnah ba, nima kuma ban damu ba, dan ni dama bani da wani karfin sha'awa, kawai ina daurewa ne in biya mashi bukatansa, so sararin da ya bani ma ta ɗan mun daɗi saboda da ALLAH ya gani yana takura mun ba wani romantic ba komai shi kawai a biya mashi buƙata, so da ya janye zuciyata shar na huta da wahala kam gaskiya, dan haka ban damu ba. Abba yana sane damu na duk abin da yake faruwa, amma ban saka mana baki ba, a haka lokacin tafiyarsu Abba buga kwallo ta yi, suka tafi ƙasar South Africa a can za'ayi wasan, team zasu jagoranci Nigeria, a ranar da zai tafi na rakosa har bakin gate, yana rike da akwatinsa, Hassan da Hussain sai kuka suke yi zasu bishi. Shi kuma yana kallona ƙasa-ƙasa ya ce. "Aunty, na jima ban maki magana a kan batun Yaya da Zainab ba, ina binku da ido kawai, amma ki sani duk halin da kike ciki ina sane da komai, ban son cika tsoma baki a case ɗinku ne, sai dai yanzu zan yi nisa daku, dan ALLAH aunty ki kara hakuri, babban tashin hankalina shi ne yadda zan tafi ban san me zai biyo baya ba, gara ina nan ko ban saka baki na nasan zan ga abin dake faruwa wanda in ta kama in tare maki dole in tare, amma yanzu ban san a wani hali zan barki ba, wani hali zaki shiga, amma koma dai me, ki sani akwai ALLAH da baya barci yana ganin komai, dan ALLAH ki tsananta addu'a, ki kaiwa ALLAH kukanki, dan ALLAH ki taimakeni kada ki bari damuwa ta maki illa, na san akwai ciwo, amma ki tuna kina da ALLAH". Na ɗan nisa tare da kama hannun Hassan dake ta faman ihu, na amsa da. "In Sha ALLAH nawan, zan yi ƙoƙari, ka mai da hankali ALLAH ya bada sa'a". Ya amsa da amin, sannan ya ja akwatinsa ya buɗe gate zai fita, ya sake juyowa muka haɗa ido dan shi nike kallo nima, ina jin tamkar zai tafi da iskan farincikin da nike shaƙa ne, ya ɗan ɗauke kallonsa daga kaina, shi kaɗai yasan me yake ji a zuciyansa, ya ja akwatinsa ya fice. Da sauri na juya cikin gida ina jin kuka na kwace mun wanda ban san dalilin yin sa ba, su Hassan ma suna rera nasu kukan, na zauna a kan kujera na buga uban tagumi sai ruwan hawaye. Ina tsaka da kuka sai ga kiransa, jikina har yana rawa na ɗauka, ina ɗauka ya ce. "Aunty na ji a jikina kamar kuka kike yi ko?". Sai kuma dariya ya kubce mun na ce. "Yaushe ƙanina ya zama malamin duba?"......... "Ban zama malamin duba ba, kawai dai na ji hakan ne"........ "To ba wani kukan da nike yi"...... Ya ɗan yi murmushi tare da cewa................. labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi. QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥 LABARIN AISHA.🥹💔 PART 13 Sai kuma dariya ya kubce mun na ce. "Yaushe ƙanina ya zama malamin duba?"......... "Ban zama malamin duba ba, kawai dai na ji hakan ne a jikina"........ "To ba wani kukan da nike yi"...... Ya ɗan yi murmushi tare da cewa. "Na maki farin sani fa Aunty, to amma shikenan, tun ban yi nisa ba har kewanku na neman yi mun illah, shiyasa na kiraki". Ina murmushin ga sauran hawaye a fuska na amsa da. "Uhm nawan ni kaɗai nasan irin kewarka da zan yi, please ka kula mana da kanka, idan ka samu lokaci ka dinga kiranmu muna gaisawa"........ "Kiranku ai ya zama dole my Aunty, zamu yi waya anjuma, ki kula kin ji?". Na amsa da In Sha ALLAH. Muka yi sallama, na buga uban tagumi ina tunanin yadda zan rayu. Haka rayuwa ta cigaba da tafiya, na kara kwantar da kaina ga Abbie, ban taɓa nuna bana son auren nan nasa ba, na dage na mayar da hankali kan karɓar kuɗi a hannunsa domin kaɗa kayan lefe. Batun gold kuma in ya tambaya sai in ce mashi Yah Abbas bai dawo ba, ba su yi hutun school ba, ranar da ya matsa mun na ce to ya kira Yah Abbas ɗin mana ta tambayesa, nasan ba zai iya kira bane yasa na ce haka, dole ya hakura yana ta fushi, na yi shiru ban kula ba. Sai da ya sauƙo daga fushin nasa ne na sake kai mashi lissafin kuɗin lefe, ya sake bani kuɗi, na dinga nuna mashi ina tausaya mashi, dan haka kayan lefen na nuna mashi ai ɗan daidai zamu haɗa domin tausayinsa da nike ji. A tunaninsa Aisha mara wayau da ya sani a baya ce, sai ya yarda ina mugun tausaya mashi kamar a baya, so duk abin da na kama mashi kuɗin sai ya biya dan yana ganin na kure neman mashi sauƙi, kun san maza ba sanin kuɗin abubuwa suka yi ba, ba komai suka san farashinsa a kayan mata ba, bare kuma quality, aikuwa na ce in kasan wata baka san wata ba. Na dinga zare kuɗina a hankali a ciki, ya gama sake jiki ina ta haɗa mana kayan, do na haɗa kayan Zainab yadda na yi ra'ayi, amma ba yadda ya zata ba, sai na tsuga mashi kuɗi kan abu, dan in zare dukiyata, saboda duk da kuɗina ake wannan, abin 50k sai in ce mashi 70k ko 80k, to kun san za'a kara aure lallaɓa uwar gida ake yi, ba'a son amun ba daidai ba, ya samu ma ina tayasa neman auren ai wani farinciki yake ji da kara girmamani, duk shawarar da na kawo zai ce e hakan ma ya yi, duk abin da nike ganin ya dace in yi, na nuna mashi tamkar nice uwar biki. Sai da shirye-shirye yai nisa na bijiro mashi da batun canza kayan ɗaki. Sai ya ce to in yi wa daddyna magana mana tun da dama dangin mata ke masu kayan ɗaki. Aikuwa na nuna mashi raina zai ɓaci, na ce sun mun ma farko yanzu ina gidansa shi ne da alhakin yi, na ce in dai ba zai mun kayan ɗaki sabbi kamar yadda Zainab zata zo da sabbi ba ni wlh ba zan zauna a gidan ba. Ya ce in yi hakuri, in samo kujeru na 1M da gado ma na 1M sai ya saya mun, na dinga nuna mashi sun yi local, na mashi daɗin baki, na ce habibi kana son Zainab ta shigo ta rainani ne? Ya ce a'a, na to ai gara in yi abubuwa masu kyau. Ya ce haka ne, da kyar na kwato 3M na kayan ɗaki a hannunsa, 1.5 na kujeru, gado ma 1.5, na turawa yayana kuɗin dan a satin nan za'a fara mun gini, na share batun canza kayan ɗaki, ai ba compaction nike da Zainab ba, dan za'a mata abu sai nima in yi? A'a, ni gina kaina in tsaya da kafata nike ƙoƙarin yi, ki gina kanki ki tsaya da kafarki shi ne zaki wuce raini ba ki tsaya cewa duk abin da mutum ya yi kema zaki yi ba, idan kika gina kanki kika tsaya da kafarki zaki sayawa kanki abin da ya fi na amarya, amma mata dayawa in za'a maku kishiya ku tashi kuna haukar neman sabbin kayan ɗaki, duk kuɗin da kuke da shi ku kashe a shaye-shayen kayan ɗaki da maganin mata

Chapter 9 of 38