sosai.
In takaice maku labari jama'a tun daga wannan rana Abba bai sake kirana ba, ko na kirasa baya ɗagawa, tamkar an mana farra'u da shi har ya shafe wata guda, tun ina damuwa ina kuka har na haƙura na zubawa sarautar ALLAH ido.
A ɓangaren Mama kuwa, kamar yadda ta faɗa ta diro garin Kano, ta zo ta saka mu a gaba da maganin makarin asirin da ta mana shekara baya, yanzu ma haka ta zo ta ƙuntatawa rayuwata, duk yadda Abbie yake son kasancewa dani sai da ta rabamu dan dole, sai dai tsakiyar dare ya saci hanya ya zo wajena mu ɗan rage dare.
Haka Mama ta yi sati biyu tana gana mun azaba, wlh na yi kuka har na rasa yadda zan yi, ban iya faɗawa kowa daga gidanmu ba, ga shi Abba baya nan, da shi ne mai ɗebe mun kewa, ko da ranar girkina ne idan Abbie ya dawo sai Mama ta ce ya wuce ɗakin Zainab, wai ba zai kwana dani ba sai an gama makarin asiri, dole haka yake wucewa.
Kwanakin Mama goma sha uku da zuwa Kano ranar muka tashi da wata musifa, gobara ta ci kasuwa ta ƙone shaguwa, aikuwa shagon Abbie ya ƙone ƙurmus babu abu guda ɗaya da aka iya fitarwa, coz gobarar ma ta tsakiyar dare ce, wutar nepa ta jawota.
Wlh na jima ina yi wa Abbie magana kan fitar da zakka haƙƙin ALLAH, amma sai ya ce ina ruwana, wannan tsakaninsa ne da UBANGIJINSA, to yau ga shi ALLAH ya cire haƙƙinsa, dan kuwa babu abin da ta rage a shagonsan nan.
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Abbie tamkar zai zare, kuka ya dinga yi yana ƙarawa tamkar ƙaramin yaro, na ce ya yi hakuri tun da ba wani jari ne sosai a ciki ba, ko 50M bata kai ba, ya godewa ALLAH sai ALLAH ya ƙara bashi wani. Aikuwa ya ɗauke mun fuska da wani mahaukacin mari, ya tashi tamkar zai dokeni yana ta masifa, ai na ruga da gudu sai cikin ɗakina na rufe kofa ina kuka.
Abin da ban sani ba ashe Abbie shaguna har uku yake da su manya-manyan shaƙe da kaya a kasuwar, kuɗi kamar su kashe mutumin nan ashe, babban shagonsa kaya ne a danƙare a ciki ban sani ba, ni ashe ɗan ƙaramin cikinsu na sani, ashe shiyasa ya kusa ɗan karamin hauka.
Daga wannan gobara abubuwa suka sake kwaɓe mana, komai ya canza, dama Abbie ba mutum ne mai yi wa iyalansa ba, bare kuma yanzu da babu ai kuma wahala ta ƙaru................ Satinmu ɗaya a asibiti da Abbien fa yana jinya, dan suma yai bai san in da kansa yake ba, sai da aka kara mashi ruwa, sati muna asibitin kafin ya farfaɗo a sallamemu muka dawo.
Note. duk dukiyar da zaka tarata, matuƙar ba zaka sauke nauyin iyali dake kanka ba, ba zaka fidda haƙƙin ALLAH ba, ba zaka kyautatawa iyayenka da su ba, wlh ka sani babu in da wannan dukiya zata je, ALLAH zai zare mata albarka ne, ba zata taɓa amfananka da komai ba, daga karshe ma rasa dukiyar zaka yi, duk yadda Abbie ya kai ga son dukiyansa ga shi a lokaci guda yau ya rasasu, ya rasa komai, baya taimakawa iyayensa, baya cire haƙƙin ALLAH, baya sauke nauyin iyali, tayaya ALLAH zai barshi?
Sati biyu da faruwar wannan abin Mama ta koma Kaduna, ko kuɗin Mota Abbie bai iya bata ba, dan bashi da komai, yanzu ya zama zero, ni na bata kuɗin Mota. Gwamnati ta ce zata ragewa waɗan da suka yi asara a gobarar raɗaɗi, amma kuɗin bau iso kan su Abbie ba, bai samu komai ba, haka muke tura rayuwa.
Kwanakin 12 da faruwar wannan gobara Abbie ya fara dawowa daidai, ranar da ya dawo cikin hankalinsa ya ce a bashi wayansa, ina zaune a gefensa a ɗaki, na ɗauko mashi, tun da muka dawo baya magana sai yau ya fara. Na jawo wayansa na miƙa mashi, number Abba ya laluɓo ya kira.
Abba yai picking, yana ɗauka sai Abbie ya ce. "ALLAH ya isa tsakanina da kai Muhammad, ba zan taɓa yafe maka ba, kome ya faru dani kai ka ja mun, kuma daga yau babu ni babu kai, kada ka sake nuna ka sanni a rayuwarka, azzalumi kawai".
Daga ni har Zainab dake gefensa mun kiɗime da jin zancensa, na kallesa cike da mamaki kafin in ce. "Abbie lafiya? Me Abba yai maka......". Wani irin tsawar da ya daka mun ne ya sanyani zabura na miƙe..... "Ki mun shiru munafuka azzaluma, kema ai kina daga cikin waɗan da suka ja mun wannan musifa ba iya Muhammad kawai ba!!".
Ikon GOD, na saki baki ina kallonsa Zainab na kallona, ta yaya za'a ce gobar da ALLAH ya kawo kuma ni da Abba mu zama sularta? Anya kan Abbie ɗaya kuwa? Anya asarar bata sanya ya zauce ba kuwa?"........
Zainab dai sai ido, tana tura cikinta da ya fara girma sosai yanzu. Abba ya dinga kiran yayan nasa amma Abbie yaki ɗauka, daga karshe ma Abbie ya yi blocking number Abba ɗin. Sosai hankalina ya sake tashi, a daidai lokacin Abba ya kirani a waya.
Fita daga ɗakin na yi dan ma kada Abbie ya ji muna waya ya sake haukace mana, dan yanzu na yarda Abbie ya fara samun matsala......... Ina fita na ɗauka, cikin tsananin tashin hankali Abba ya ce. "Aunty lafiya? Meyakefaruwa a gida?".
Wani irin ajiyar zuciya na sauke, rabona da jin muryan Abba har na manta, har cikin raina na ji sanyi. Muryata a ɗan dishashe na faɗa mashi duk abin dake faruwa, sai shi ma ya faɗa mun abin da Abbie ya ce mashi yanzu. Na ce. "To ko dai akwai abin da ka mashi ne?"....... Ya ce. "A'a, rabona da magana da ku ya kai kwanaki 20 yau, wayata ma gabaɗaya tana kashe na turata cikin jaka, babu abin da na yi wa yaya nikam".
Muka yi shiru muna neman mafita, na faɗawa Abba nima ya ce da laifina a ciki, Abba ya ce mu kyalesa zafin rashi ne, idan ya dawo daidai komai zai wuce. Na ɗauki wannnan shawara na ɗan yi nisa da Abbie, muka bashi waje, shi kaɗai muke bari a ɗaki.
Wasa-wasa har sati ta shuɗe ba abin da ya canza, zai fita ya je ya dawo amma ko sannu baya ce mun, sai ma hararata da yake yi, kamar ya tsani ganina, amma kuma baya yi wa Zainab hakan.
Wataranar litinin muna zaune ni da su Hassan a parlo ba sai ga Abbie da dillalai ba, wai zai sayar da gidan nan mu koma gidan haya, ya salam, na shiga tsananin tashin hankali, na yi ƙoƙarin yin magana da shi amma bai bani fuska ba.
Ina ji ina gani ya sayar da gidan ya karɓi kuɗi, ya buƙaci da waɗan da suka sayi gidan su bamu wata ɗaya zamu tashi. Ni kam izuwa yanzu na daina shiga lamarin Abbie, dan wlh ya fara wuce tunanin, ya zama kaman wani zararre, abin mamakin ma shi ne iyayena suna ta kiransa zasu mashi jaje bawan ALLAHN nan yaki ɗaukar wayansu, suma yai blocking ɗinsu, wai ni da Abba muka ja mashi asarar.
Jama'a duniya ta mun zafi, na rasa me yake damuna, na yi kuka har na godewa ALLAH, a wannan ƴan tsakanin Yaya ya kirani an sayar mun da ɗayan gidana 350M, already an kammala ginin tun last two weeks ago. Saboda tashin hankalin da nike ciki ko murna ban yi ba, na cewa yaya kawai ya yi duk abin da yake ganin ya dace.
Sati uku da sayar da gidanmu saura sati ɗaya kenan kunga mu bar gidan da muke ɗin, dama wata ɗaya Abbie ya ce a bamu, ina zaune a parlo ina rike da waya sai ga Abbie ya shigo, a kaina ya tsaya tare da cewa. "Ki shirya kowaccenku zata wuce gidan ubanta har sai na samu gidan haya na kama sannan ku dawo". Yana kaiwa karshen nan ya wuce. Coz na yi mamakin jin hakan, a tunani wata ɗayan da ya nemi a bashi haya zai nema, to me ya yi kenan?.
Wani sabon kuka na ji ya zo mun, na kifa kaina a saman hannun kujera na hau kuka babu kama hannun yaro. Ina tsaka da kukan sai ji na yi an ce. "Komai yai zafi maganinsa ALLAH Auntyn tawa"........ Da sauri na ɗago kai, waye zan gani, Abba tsaye a tsakiyar parlon, ya yi folding hands ɗinsa a kirji, duk da fuskansa babu alamar fara'a ko annuri amma ya ƙara kyau sosai, sai dai ya yi muguwar rama kamar ba shi ba, manyan idanun nan nasa sun kara girma sosai.
A zabure na miƙe game da cewa. "Nawan, yaushe ka dawo?"........ Ya sauke hannunsa tare da ɗauke kallonsa daga kaina. "Lokacin da kike kuka na shigo, Aunty, wai ba kin mun alƙawarin ba zaki sake kuka ba?"
Ji na yi tamkar in je in rungumesa, har wani ingizani zuciyata take yi, na dinga kallonsa tamkar ba zan daina ba, shi ma kallona ya dinga yi, ya gagara dainawa. Can ƙasa ya ce. "Kalli yadda kika rame saboda sawa ranki damuwa, meyasa dukka wannan?".
Cikin kuka na ce. "Kai ma meyasa ka rame haka? Ka yi ciwo ne? Meyake damunka?"......... Ya ɗan sauke kallonsa daga kaina, can ƙasa yai wata magana da ban ji ba, sai na ce. "Me ka ce?".
Ya ɗan girgiza mun kai alamar babu komai. Ya taka step biyu ya matso dab gabana, hannunsa ya kai kan fuskata ya fara goge mun hawaye. Wani iri na ji a jikina, na dinga jin tamkar in rungumesa, amma ban yi haka ba. Sai ya sake taka step biyu baya ya matsa daga kusa dani, a natse ya ce. "Ina yaya?".
"Yanzun nan ya fita, ya ce in shirya zai mai dani gidanmu dan ya sayar da gidan nan"........ Abba ya ɗan waro idanunsa a kaina, ya maimaita kalmar sayar da gidan nan a ransa, sai kuma ya jinjina kai, bai yi magana ba ya juya ya ja akwatinsa ya nufi ɗakinsu. Ai yana shiga ɗakinsu sai ga Abbie ya sake shigowa, kai tsaye cikin ɗakinsa ya nufa.
Da sauri na bi bayansa, ina shiga ya daka mun tsawar in fita mashi daga ɗaki, na rufe kofar ɗakin tare da cewa. "Magana nike son yi da kai"........ Ya yi shiru bai yi magana ba. Ya haɗe natsuwata kafin in ce. "Zan baka gidana mu zauna a ciki kafin ALLAH ya hore ka gina naka na kanka".
Da sauri ya ɗago kansa ya kalleni, sai ya ce. "Kina da gida ne?"....... Na jinjina mashi. "Ina da sabon gida da na gina a Abuja, dama haya zan saka, to zan baka mu zauna kafin ALLAH ya hore". ....... Take ya saki fuska, sai ya ce mun. "Abba ya dawo ne?". ..... Na jinjina mashi kai, ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa. "Ina takardun gidan da key?".
Na amsa mashi da . "Zan kawo maka, yanzu dai mu fara shirin komawa Abuja"...... Haba take ya shiga saka mun albarka babu ko kunya. Sai na ce. "Amma please kada ka faɗawa kowa gida nane, ka nuna kamar gidanka ne". Da sauri ya amsa da okey. Na buɗe kofa na fita. Shi ma ya fito ya shiga ɗakin Abba, ban san me suka tattauna ba ya fito ya nufi part na Zainab.
Ni kuma na fita na shiga ɗakina, na kira yayana, yana ɗauka na faɗa mashi komai dake faruwa, Yaya ya ce. "Shawara ce mai kyau ki baku gidan ku zauna, amma kuma ba zan baki takardun gidan da komai da ya shafi gidan ba, key kawai zan bamu sai furnitures da zan zuba maki sabbi"......... Na yarda da hakan muka yi sallama, sai dai dana faɗawa Abbie sai ya ce lallai in karɓo takardun gidan ya rike mun a hannunsa tun da dama shi yake da gadona..
Na ce a'a ni ba zan iya jayayya da yaya ba, sai dai in shi zai kirasa ya faɗa mashi, aikuwa shi ma ya ce ba zai iya ba, dole dai ya nuna mun ya hakura da batun takardun, amma a cikin zuciyansa bai hakura ba, domin kuwa akwai abin da ya ƙulla, sai ma da muka je ya kalli gidan, innalillahi, ai rikicewa ya yi, tampatsetsen gida haka, cikin katon estate, irin gine-ginen estate ne dai, katon parlo a ƙasa da kitchen mai girma shi ma, sai wani ƙaramin ɗaki a wajen kofar shigowa parlo, a cikin parlon akwai dining area, a cikin katon kitchen ɗin akwai store, sai kofar baya ta cikin kitchen da zai sadaka da BQ da kuma wajen tankin ruwa na gidan, a wajen kusa da dining area akwai staircase da zai kaika sama wanda a nan ɗakunan masu gida yake. Ɗakuna huɗu ne a saman, sai ƙaramar parlo da katon balcony, kowani ɗaki da toilet ɗinsa a ciki, sai ɗan ƙaramin waje domin wasan yara, ɗakuna guda huɗun nan uku ne manyan ɗakuna, ɗayan ɗan madaidaici ne, shi ne ɗakin baƙi. Gidan ya haɗu matuƙa, sun iya tsara gini, ga wasu haɗaɗɗun flowers ɗin da aka shuka dan ƙawata ginin da su, sun kewaye ginin ta ko'ina.
Nan fa Abbie ya ƙara rikicewa, sai ya sake matsa mun sai na karɓo takardun gidan, ni kam na ce ba zan iya ja da maganar yaya ba, sai ya nuna mun ba komai in bar takardun wajen yayan kawai.
Kada mu ja wannan waje da nisa dan sauran labari na gaba. Dan haka a cikin satin muka shirya muka koma Abuja. Abbie ya nunawa kowa cewa gidansa ne, Sodangi sai wani kauɗi ake ana rawan kai, yarinya ta zo Abuja, ga tampatsetsen gida, ai kullum cikin ɗaukar hotuna take, ta dinga turawa ƴan uwanta, tana wani jiji da kai, wai yanzu kam ta wuce tsara mijinta ya yi gini na alfarma.
Ni kam binta da ido kawai nike yi, ina sha'anin gabana. Abbie kuwa har yanzu yana hannuna, domin da ya samu mafita muka dawo Abuja sai ya sake manne mun, dan dai wajena kawai yake samun gamsuwa, nan fa rigima ya tashi ya tsaya tsakaninsa da Zainab, ta ce ba zata yarda ba, ya daina tauye mata hakkinta, ya je ya tare a wajena ya zama mijin tace. Shi kuwa yai banza da ita, kullun yana ɗakina. Ta fusata ranar ta ce ya biyata kuɗinta, ai ko kallon in da take bai yi ba, tun ma da ya bar ɗakin nata bata sake ganin idanunsa ba, tuni ya fita neman shagon da zai kama a Abuja, sai ya zuba kaya da kuɗin gidansa na Kano da ya sayar, shi ne shawarar da ya yanke, yana fita ganin gari domin ya ga irin sana'ar da zata dace da wajen.
Ni kam komai nawa ai kunga yana hannun yayana, dan haka ko a jikina, yaya shi ya saya mana furnitures da kayan abinci kafin mu dawo, so akwai komai shiyasa Zainab ta karo walaƙanci, ta ga cikin kitchen ɗinmu komai a shirye, abinci enough, and ga sabbin furnitures, tsoffin namu mun tarasu waje guda ta wajen tankin ruwan gidan muka ajiye.
Zainab da ta ga miji fa baya hannunta sai ta haukace, ya kira kawayenta tana kuka ta faɗa masu. Aikuwa kawayen nata suka bata shawarar wai ta bi malamai ita ma dan ta samu kan Abbie dan suna tunanin cewa ni ma malamai na bi na samu kansa, basu san kawai zallar gyara bace, suka ce mata yanzu Abbie ya zama mai kuɗi fiye da a can baya, wlh ta kwace mijinta dan ta ji daɗi, suka ce mata kuma ta zage ta yi ta haihuwa ta fini yara dan ta zama itake da wannan tampatsetsen gidan.
Da yake kan nata ba lissafi sai ta aminta ta ɗauki shawarinsu, daga wannan lokaci ta fara bin bokaye yarinyar nan, ta dinga yi wa mamarta karya tana karɓar kuɗi tana turawa kawarta tana zuwa mata wajen bokaye a Kaduna, dan a nan Abuja kam bata san ko'ina ba bare ta je, kawayenta ke zuwan mata su haɗata da bokan a waya ta mashi bayani.
Ni dai ko a jikina, ina ta ƙara gyarawa mijina kaina, ina sallah ina salati, ga sadaka da zama da kowa lafiya.
Satinmu ɗaya da dawowa Abuja Abbie ya shirya gagarumin walima na komawa sabon gidan da muka yi. Danginsa sun zo, ai nan naga kauyanci. Sun cika gidan, Mama ma ta zo, abin da yai mugun bani mamaki shi ne yadda basu nemi jin in da ya samu kuɗin ba, harta Mamansa da ta san sun yi gobara bata nemi jin a ina ya samu kuɗi ya sayi wannan tampatsetsen gidan ba, ita dai sai murna take yi ɗanta ya yi katon gida.
Tun da danginsa suka zo suke faman jefa mun maganganu, wai dama ni mai farar kafa ce mai ƙashin tsiya, ga sodangin jinin arziki daga shigowarta ko shekara ba'ayi ba Abbie ya yi tampatsetsen gida a Abuja. Ni kam ko sannu ban iya ce masu ba. Da suka dameni da habaice-habaice ma sai na bar masu cikin gidan na koma BQ.
Bq ɗin kuma na Abba ne da babys ɗinsa su Hassan, Fahad yana Kaduna bai dawo ba tukun nan, tun da aka yi gobara ya je gida, Muhammad har yanzu yana wajen Hajiyarmu sai dai in yi video call da shi.
Ban yi tsammanin Abba na gidan nan ba, na shiga na kwanta a saman sofa na parlon, na ɗaura hannuna a kan fuskata na lumshe idanu, ba jimawa barci yai awon gaba dani.
Abba na kwance a cikin ɗakin tamkar ance ya fito parlo, sai ya miƙe ya fito, coz shi ma bai yi tsammanin ganin mutum a parlon ba, yana sanye da jallabiya fara tas ya fito. Ya sha madarar mamakin ganina kwance a parlon. Gently ya tako zuwa gaban sofar da nike.
Ya ɗan wawwaiga kamar mai duban wani abin, sai ya sake dawo da kallonsa kaina, can ƙasa ya ce. "Tawan". A tunaninsa ba barci nike ba na rufe ido ne kawai, amma da ya ji shiru sai ya fahimci na yi barci. Tsugunnawa yai a gaban sofar, ya haɗe hannayensa dukka biyu a saman faffaɗar kirjinsa, ya zubawa fuskata idanu, shi kaɗai yasan me yake tunani, ya ɗan bi kayan jikina da kallo, doguwar riga ce mara nauyi mai karamar hannu. Ya ɗan motsa lips ɗinsa, yai wani magana wanda sauti bai fita ba sai dai ka karanta laɓɓan nasa.
Sai kuma ya ɗan tsai da kallonsa kan dogon kyakkyawan wuyana, a hankali ya sauke ajiyar zuciya tare da ɗan matso da face ɗinsa kusa dani. A daidai lokacin wayansa dake cikin aljuhu ta fara ƙara. Hakan yasa na ɗan motsa. Shi kuma da sauri ya miƙe, hannunsa har yana ɗan rawa wajen sanyawa zai ciro wayar. Slowly na buɗe idanuna masu cike da barci, kai tsaye sai kan face ɗinsa.
Da sauri ya juya yana picking call ɗin. Nima da sauri na miƙe zaune ina faɗin. "Nawan dama kana nan?"...... Ya ƙara wayar a kunnesan bai mun magana ba, sai na ji ya ce. "Ina ɗaki"....... Sai kuma ya zare wayar daga kunnensa, ya samu waje saman sofa ya zauna, a natse ya ce. "Ina nan Aunty, ya kika zo nan kika kwanta? Su Aunty Amina suna takura maki ko?"......... Na ce. "A'a, suna hirarsu ne hayaniya ya yi yawa, ina yaran naka? Na zaci kun tafi yawo da su ai".
Ya ɗan girgiza kai yana wani sauke idanunsa ƙasa. "Sun yi barci, suna ciki"...... Muka ɗan yi shiru, can na katse mana shirun da cewa. "Nawan"....... Ya ɗago manyan idanun nasa a kaina.
"Menene ya canza mun kai sosai haka ne?"...... Ya ɗauke kallonsa daga kaina kafin ya amsa da. "Babu, kawai girma ne, and yanzu ina jin kunyarki saboda surukata ce ke, kin bani Safiyya"........ Na hararesa kafin in ce. "Har yanzu kana jin zaka sameta ne?"
Ya ɗan mun kallon ƙasan ido, sai yanzu ya fahimci na san sun rabu ashe shi ne ban nuna mashi na sani ba. Ya ɗan jinjina kai, a natse ya ce. "Sosai, dede da rana ɗaya ban taɓa jin zan rasa abin da nike so ba, kawai nasan lokaci ne bai yi ba, idan lokaci ya yi zan samu, matata ce In Sha ALLAH".
Na ce. "Eyeee, to ina maka fatan samun nata, rabbi ya karɓi addu'armu, nawan ina son ka sameta sosai, na damu da na ji an rabaku".......... Ya wani sauke ajiyar zuciya, zai yi magana kenan Abbie yai sallama ya shigo cikin parlon.
Ai wani irin ƙayataccen murmushi Abbien ya saki ganinmu tare, ya ƙariso ya zauna a kan sofa mai zaman mutum ɗaya yana faɗin. "Hira kika zo wajen ƙanin naki ne?".
Na gyaɗa mashi kai alamar e....... Sai ya sake cewa. "Ina matukar jin daɗi in ganku a tare, ina alfahari da hakan, da ace kun san farincikin da nike shiga idan kuna tare, tabbas da kun dinga kasancewa haka har abada".......... Na kallesa ina murmushi kafin in ce. "Meyasa to?".
Yana murmushi shi ma ya ce. "Saboda haɗuwarku waje guda ita ce nasarata, ita ce farincikina, ita ce komai ɗina, akwai wani sirri mai karfi dake tattare da haɗuwan taurari biyu dake bada nasara mai karfi".
Daga ni har Abba muka zare idanu muna kallonsa cike da mamaki, wani sirri tattare da taurari biyu kuma? Wani sirri kenan? Su waye kuma taurari biyun?.
A tare muka dawo da kallonmu kan juna ni da Abba, lokaci guda jikinmu ya yi wani irin spark, yadda kuka san an saka mana wasu abubuwa a ido, muna ganin juna duk sai da jikinmu yai kamar spark na nepa. Muka sake mai da kallonmu kan Abbie. Shi kuwa sai ya ce. "Muhammad magana zamu yi da kai kan kwallon nan naka".
Abba ya ƙara natsuwa game da cewa. "Ina sauraronka"....... Abbie ya ce. "Daga yau ba zaka sake zuwa wajen kwallon nan ba, zaka zauna tare damu a nan"...... Da sauri na ce. "Meyasa?".
Ya amsa da. "Saboda rashin ɗaya daga cikin taurari yana iya haifar da gagarumin matsala, tafiyar da ya yi ya je ya jima a wancan karon ne yasa shagona ya ƙone, dan haka babu in da zai sake zuwa, dole ku kasance tare waje guda in ba haka ba zamu sake shiga cikin bala'i fiye da wanda muka shiga a baya".
Zazzaro idanu a kan fuskansa muka yi, coz ya jefamu cikin duhu, idan ɗaya daga cikin ni da Abba basa nan zamu shiga mashi fa kuma? Kamar yaya kenan fa?
E to akwai matsala, kenan dama shiyasa Abbie ya haɗa Aisha da Abba waje guda? Kuma kenan shiyasa baya damuwa kome zasu yi? Me yake nufi ne to?....... Uhm.
labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi.
FATEEMA ZAHRA MUSA
A-K-A
QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥
LABARIN AISHA.🥹💔
PART 21
Zazzaro idanu a kan fuskansa muka yi, coz ya jefamu cikin duhu, idan ɗaya daga cikin ni da Abba basa nan zamu shiga masifa kuma? Kamar yaya kenan fa?
Cikin rashin fahimta na ce. "Abbie ban gane me kake nufi ba?"..... Ya yi murmushin tare da cewa. "Habibiya ba zaki gane ba, bar zancen, yanzu dai Muhammad na faɗa maka babu batun kwallon kafa, ka zauna a gida, kome kake so ga Auntynka, and ina son maku nasiha da ku haɗa kai, ban da faɗa, ku koma kamar da can a baya shi ne nasarata, dan haka ka zauna a nan, ka bani result ɗinka zan samo maka aiki a nan".
Abba dai shiru bai ce kala ba, yana ta satar kallona dai. Abbie ya gama surutunsa ya tashi ya fita, Abba ya ɗago idanunsa da kyau ya kalleni, cikin sanyin murya ya ce. "Aunty, please kada ki bari burina ya tafi a banza, dani dake duk mun sha wahala kafin in samu abin da nike so, ni bana son wani aiki, karatu na yisa ne kawai domin in yaki jahilci, amma ba dan in yi aiki ba, ni kwallon kafa ce burina, please Auntyn tawa, ki saka baki, ki rokanmun shi".
Yau dai ni na ɗauke
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 38