Share this page
mashi harara ba, a kule na ce. "Abba, dama haka ka zama ko? Sai ka dinga rungumar mata da sunan fans ko?". Cikin faɗa nai maganar. One sided smile ya ɗan yi tare da kai hannunsa ɗaya ya zare Zahra daga jikinsa, a natse sosai ya ce. "To ni yanzu dani da ita waye ya zo ya rungumi wani da kike mun masifar ina rungumar mata?"........ Na dallah mashi wani hararan, zan yi magana Zahra ta sake ƙoƙarin rikesa tana faɗin su yi hoto. Tsawa na daka mata da cewa. "Zahra, wai baki da hankali ne da zaki dinga rungumarsa? Kin san shi ne?". Dariya ne ya so kubcewa Abba, a ransa ya ce wannan idan ta fita tare dani tsab zata kifawa wata mari, dan kam masu rungumansa ai bai san adadi ba, sai dai in bai fita ba, mata da yara, samari da manya duk rungumesa suke yi idan sun gansa. Ganin Zahra bata kulani ba zata sake shiga jikinsa ne yasa nai saurin zuwa na janyeta ina mata faɗa, Abba yai folding hands ɗinsa a kirjinsa yana kallonmu, wani irin farinciki ya lulluɓe mashi zuciyansa. Na ja Zahra muka koma gefe, shi ma ya ɗan juna kamar zai fita, bai san me na faɗawa Zahra ta natsu ba, sai gani yai mun dawo a tare ta natsu sosai, ta gaishesa a mutunce, ya amsa sau ɗaya sannan ya ce in zo mu je ya kaini ɗaki. Na yi sallama da Zahra muka fito, Zahra ta rakomu bakin kofa, Abba ya ce za'a kawo mata abinci, ta ce okey ta gode. Muna barin ɗakin Zahra ya ce mun. "Me kika cewa kawar nan taki ta natsu ne?"....... "Ce mata na yi kai mai shan jini ne, zaka sha jininta idan bata natsu ba". Da sauri ya zaro ido tare da dakatawa da tafiya. "Da gaske abin da kika ce mata kenan?". On a serious note yai maganar. Na gyaɗa mashi kai alamar yeah...... "Baki da hankali ne? Kin san me kike shirin yi kuwa? Kina son jefani cikin musifa ne? Okey so kike duniya ta kalleni a matsayin wanda ya ɗaukaka ta hanyar shan jini?!"........Bai taɓa magana da wannan murya ba tun da nike da shi sai yau, cikin faɗa da zafa yai maganar tamkar zai kai mun duka, saboda abu ne da ya shafi rayuwa, idan Zahra ta faɗi cewa yana shan jini kowa zai ce dama shiyasa ya ɗaukaka sama da manyan ƴan kwallon da suka fi shekaru 20 a harkar, shi ya zo daga baya ya ɗaukaka fiye dasu, ga bala'in farinjinin da yake da shi, za'a ce dama ƙungiyar shan jini ya shiga suka bashi ɗaukaka. Na tsorata da yadda yai magana hakan yasa na gagara iya amsa mashi, sai na fara ja da baya da baya daga kusa da shi. Hannu yasa ya damki waist ɗina game da jawoni gabansa, babu wasa ko kaɗan a kan fuskansa ya ce. "Meyasa kika ce mata hakan?". ...... Murguɗa mashi baki na yi tare da buge hannunsa dake kan waist ɗina, sannan na amsa da. "Ya za'ayi in ce mata hakan tun da ni ba mahaukaciya bace kuma ba yarinya bace, tsokanarka kawai nike yi, ni ba haka nace mata ba, cewa na yi zaka rainata, hakan da take yi zubar da mutunci da class ɗinta ne a matsayinta na ɗiya mace, idan ta natsu ta kama kanta sai ka fi respecting ɗinta har ma ka girmamata, dan mu mata ababen girmamawa ne, amma idan mun girmama kanmu tukun nan". Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da ɗan miƙewa tsaye, sai kuma ya wurga mun kallon ƙasan ido, a hankali ya ce. "Kin mun one zero, but zan rama, mu je ki kwanta"...... Ya faɗa tare da riko hannuna muka ƙarisa ɗakin, wannan ɗaki ne dai da ya kaini ɗazun. Har tsakiyar ɗakin ya rakoni tare da cewa. "Idan akwai abin da kike so, ki kirani". Yana gama magana ya karɓi wayar hannuna ya shigar mun da numbersa, sannan ya juya. Har ya taka step ɗaya sai kuma ya sake juyowa, ya ɗan rage tsawonsa daidai da nawa, muna fuskantar juna, yai ƙasa da murya wajen cewa. "Ke yarinya ce sosai, shiyasa na yarda zaki iya faɗawa kawarki ina shan jini, dan haka batun kice mun ke bayarinya bace bai taso ba, baby kawai". Dundu na nufi kai mashi a baya, da sauri ya miƙe, da baya-baya ya fara takawa ya nufi door yana kallona, sai da ya kai dab zai fita ya ce. "Dubeta a wajen sai baki, maza kwanta ki yi barci, goodnight". Yana gama faɗar hakan ya fice tare da jan kofa ya rufe. Nannauyar ajiyar zuciya na sauke, sannan na nufi in da nike zaton toilet ne. Wanka na yi, na fito na fara dube-duben me zan sanya. Ganin babu kaya a ɗakin yasa na kira numbersa da ya saka mun. Ina kira ya ɗaga, tamkar yasan nice ya ce. "Kin kasa barci ne in zo in tayaki hira?"....... Uhm nace tare da cewa. "Kayan sakawa nike so, na yi wanka ba kaya a ɗakin"........ Ya amsa da okey, sannan ya katse kiran. Zama na yi a gefen gado ɗaure da towel a kirjina ina tunanin rayuwar da muka yi a baya, abubuwa dayawa sun faru, wasu ka yi kuka, wasu kuma dariya...... Ina tsaka da tunani sai ganin Abba na yi a ɗakin, da sauri na miƙe game da janyo duv na kan gadon na rufe jikina, ban yi tunanin zai shigo haka ba, na zaci sai ya yi knocking na buɗe mashi, na manta gidansa ne ba ruwansa da knocking tunda ya san yadda ake buɗe kowani kofa. Ɗan rintse idanunsa yai a lokacin da ya ga na yi sauri ina rufe jikina, shi kansa bai yi tsammanin haka zai ganni ba, ya ma zaci ina cikin toilet ban fito ba sai ya ajiye mun kayan a kan gado. Gently ya ƙariso wajen da nike tsaye, can ƙasa ya ce mun. "Sorry tawan, na zaci kina cikin toilet ne shiyasa na shigo kawai". Ya kai karshen tare da ajiye mun kayan a gefena, sai ya juya da sauri ya fice...... Na bi bayansa da kallo, yana fita na sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da komawa bakin gado na zauna, sannan na jawo kayan, sai naga ai sleeping dress ɗinsa ne, sai tashin kamshi mai kwantar da hankali suke yi. Miƙewa na yi na shirya cikinsu, sun mun yawa sosai, amma haka na haye gado na kwanta, na lulluɓa da duv, a maimakon in yi barci sai na jawo wayata, na kunna data, kai tsaye kan number Ibrahim na shiga, ya turo mun saƙonni dayawa bawan ALLAH, reply na fara mashi. Yana online, aikuwa yana ganin reply ɗina guda ɗaya sai ya danna mun kira. Ina ɗauka ya marairace mun game da cewa. "Tun ɗazun ke nike ta jira sarauniyata, ko abinci na kasa ci, fatana in ji ya kika wuni, ya gajiyar gajiyar mun dake da Zahra ta yi?"......... "Sorry Ibrahim, sai yanzu na kammala cin abinci, na yi wanka na dawo ɗaki na kwanta ne"........ Cikin wani irin murya dake nuna zallar soyayya ya ce. "To ko in zo in maki tausa ne har sai na sauke maki wannan gajiya gabaɗaya?". Na ɗan yi dariya game da cewa. "Nesa bata maganin kusa"....... Ya sake marairace mun da cewa. "Dan ALLAH tauraruwata ki barni in zo in ganki, please, zuciyata tana cikin wani hali, ba zan iya jira sosai ba"...... Na nisa tare da cewa. "To shikenan, next week ka zo kawai"...... Wani irin farinciki da ya ji har ɗan kara ya saki, sai ya ce. "Zan zo maki da babban bazata kuwa tauraruwata, na gode sosai, ALLAH ya mallaka mun ke". Na ɗan yi murmushi. "Wani irin bazata zaka zo mun da shi?". Cike da matsuwar son jin menene zai zo mun da shi nai tambayar. "A'a, sai na zo zaki gani". Ya bani amsa..... "ALLAH ya kawoka lafiya". Na faɗa a natse. Ya amsa da amin, nan fa ya fara jana da hira sosai, sai da ya sanyani farinciki sosai duk da ban yarda cewa soyayya muke yi ba, dan a cewata bani ba wata soyayya bare aure har abada, a haka zan kare rayuwata. Sai around 2 na dare Ibrahim ya barni dan in huta, a Nigeria kuma 3 na dare kenan, muka yi sallama, na ajiye wayata na yi addu'ar barci. Ba jimawa barci yai awon gaba dani. While shi ma Abba yana shiga bedroom ɗinsa ba jimawa barci ya ɗaukesa, dan yana cikin tsananin farinciki sosai da sosai. Washegari da safe, tun da Abba ya dawo daga masallaci ya shiga cikin katafaren kitchen ɗinsa da kansa, kukun gidan mutum biyar ne, suka zube suna gaishesa cike da girmamawa, ya amsa fuska a sake, cikin girmamawa suka fara tambayar me yake so? Ya ce. "Yau na hutar daku girki, da kaina zan yi, gimbiya ta ce girkina take son ci"..... Suka dinga kallonsa cike da mamaki, tun da suka fara aiki a gidan nan yau tsawon watanni shidda basu taɓa ganin ko tukunya ya ɗaura a wuta ba, in ya shigo kitchen ya shigo ce masu su haɗa mashi wani abin ne. Tambayar kansu ma suke yi wai ya iya girkin ne kam. Shi kam bai bi ya kansu ba ya wuce ya hau fara shirya abinci, sai da yai mun girki kala uku na abincin Nigeria, ciki harda ɗanwake best food ɗina, ya dafa shinkafa da miyar stew, sannan ya dafa tuwon shinkafa da miyar kuka, duk yana da kayan amfanin gida Nigeria, dan bai daina cin abincin gida ba, ya fi jin daɗinsu. Kukunsan nan sun yi mamakin ganin yadda yake aiki, ga natsuwa da tsabta, ya kammala komai, da kansa ya ɗauka ya je ya shirya a dining table, sannan ya koma dakinsa dan yai wanka. A lokacin kuma wayata ta cika da saƙonnin soyayya masu narka zuciya na barka da safiya daga Ibrahim, ni kam har lokacin barcina nike yi ban farka ba........... labarin A'isha zai dinga zuwa maku labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi. FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥 LABARIN AISHA.🥹💔 PART 28 Bayan yai wanka ya tsara shirinsa cikin wasu tsadaddun ƙananan kaya tamkar wanda zai fita zuwa wani wajen, ya duba time 8:30 ta yi. Ya ɗan tsaya a tsakiyar ɗakinsa tare da sanya yatsa ɗaya a baki tamkar mai tunanin wani abin, sai kuma ya ɗan zauna a bakin gado, tunani yake yi ya je ya dubani ko dai ya kyaleni sai na tashi da kaina? Ya damu kuma yarasa meyakamata ya fara yi. Ni kuma ban tashi farkawa ba sai 9, ina tashi na jawo wayata, ganin 9 na safe yasa na diro kasan gadon da gudu, ko sallar asuba ban yi ba, jiya na biyewa Ibrahim ban samu barci da wuri ba, da gudu faɗa cikin toilet. Jim kaɗan na fito, babu dadduma a ɗakin, dan haka na tsaya a kan tiles ɗin da yake ƙal-ƙal yake, na lulluɓa duv ɗin a jikina saboda nasan ko na kira Abba ba kawo mun hijab babba zai yi ba tun da ba mata bane a gidan nasa. Bayan na idar da sallah na yi zaman askar, sai 9:20 na tashi a wajen, shi ma kiran da ya shigo wayata ne yasa na tashi. Ɗaukar wayar na yi sai naga Ibrahim ne, pick-up na yi tare da karawa a kunne. "Assalamu alaikum". Na faɗa ina zama a bakin gado, ya amsa sallamar game da ɗaga mun gaisuwa, a mutunce na amsa sannan na ce. "Ya na ji muryanka wasau yau?". Yana dariya ya amsa da. "Kin san ko barci ban yi ba? Na gagara runtse ido, tsananin farincikin kin aminta in zo gareki yasa na kasa rintsawa, dole ki ji muryata haka ai, almost one year ban ganki kin ganni ba, two years ma zan ce, dan lokaci da kika dawo kina jinya an hanani ganinki". Ina murmushi na ce. "Shi ne kaman wanda aka bawa aljanna?". ...... "Uhm, Aesh ba zaki gane yadda nike jinki a raina bane, da zaki gane haƙiƙa da ba zaki tambayeni ba"..... Uhm na ce ina ɗan sunkuyar da kai, dan ni kam har ga ALLAH bana son wani zancen soyayya. "Kin yi breakfast? Me kika ci? And fatan kin ƙoshi sosai?". Muryansa ya katse mun tunanin da nike yi....... Na ɗan ɗago idanuna ina ganin kofar ɗakin, dan na ji kamar an taɓa, na amsa da. "Ban yi breakfast ba, yanzu nike son yi"....... Ya ce. "Kai, 9:35 fa yanzu, gaskiya ba zan lamunci zamanki da yunwa ba, maza tashi ki je ki yi breakfast yanzu, dole ma in shirya in zo dan in dinga sakaki cin abinci a kan lokaci". Ya bani dariya, na ɗan dara tare da cewa. "Shikenan sai mun yi waya, idan na kammala breakfast ɗin zan kiraka"...... Ya amsa da okey. A daidai lokacin aka turo kofar ɗakin, na sauke wayar daga kunnena ina kallon kofar. Lokaci guda na ɗan zaro idanuna a kansa ganin kyan da ya yi, ya kara kwarjini da cika ido, hannunsa rike da wani leda baki, bakinsa a ɗauke da sallama ya shigo. Na dinga kallonsa har ya iso kusa dani, a saman side sofa na ɗakin ya zauna tare da cewa. "Good morning tawan"...... "Uhm, yau kam ka tashi da biyayya kenan ko?".... "E to kusan hakan ne, yau da biyayya na tashi gaskiya". Ya bani amsa kansa a ƙasa kamar mai jin kunyata....... "Abba". Na ambata..... Ya amsa bai ɗago kai ba. "Lafiya?"...... "Kalou". Ya bani amsa still bai ɗago ba. "Ban yarda lafiya ba, ban yarda da kai ba, wani abin kake ɓoyewa ko?"....... Sai a lokacin ya ɗago ido ya kalleni, muna haɗa ido sai kawai na tsinci kaina da fashewa da dariya, shi ma siririn murmushi ya saki har sai da dimples ɗinsa dukka biyu suka lotsa, sannan ya ce. "Baki da dama tawan". Pillow na ɗauka na ɗan bugesa a damtsen hannu ina faɗin. "Kai ne baka da dama, ni ban ma san me yasakani dariya ba".... "Idona ne ya sakaki dariya mana, dama nasan sai kin yi dariya saboda irin kallon da zan maki". Na ƙara kai mashi duka da pillow ina murmushi, ya sauke kallonsa daga kaina game da miƙo mun ledar hannunsa, yana faɗin. "Ga kayan sakawa, ki zo mu yi breakfast idan kin saka"...... Na karɓa tare da cewa Nagode. Ya miƙe ya nufi kofar fita. Na bi bayansa da kallo, har ya kai dab kofa sai kuma ya juyo, muna haɗa ido na sake fashewa da dariya, saboda gabaɗaya yau irin kallon da yake mun ban ma san yadda zan fassara ba, shi ma ya ɗan yi murmushi kafin ya fice. Yana ficewa na mike ya shiga toilet dan watsa ruwa da shiryawa. ------------------------ A can gida Nigeria kuwa, Ibrahim yana can yana ta faman shirinsa na zuwa Germany, amma fa bai faɗawa mahaifiyarsa ga in da zai je ba, dan mahaifiyarsa da hajiyarmu basa shiri ko kaɗan, amma mahaifinsa bashi da matsala da alaƙarmu, a lokacin da muka yi soyayya da Ibrahim abaya Hajiyarmu har gida ta je ta dakawa mahaifiyar Ibrahim warning kan ta jawa ɗanta kunne ya fita harkata, saboda a lokacin suna ganin Ibrahim zai lalata mun rayuwa ne kawai, dan kansa na rawa, akwai gigin kuruciya, tabbas da gaske Ibrahim ya so ni, amma yanayinsa yasa suke cewa lalata mun rayuwa zai yi. Hajiyarmu ta yi wa mahaifiyar Ibrahim tas, ta ce bata son wannan alaƙa, daga wannan lokaci Mahaifiyarsa ta ce lallai ya fita harkata, ya dinga bata hakuri, ta ce bata so, sai da mahaifinsa yasa baki sannan ta hakura, to da na yi aure ta dinga yi wa Ibrahim faɗa wai ai dama ta faɗa mashi masu kuɗi ba zasu aurawa talaka ƴaƴansu ba, yanzu ai ga shi nan na yi aure na barsa, ya yi ƙoƙarin faɗawa mahaifiyarsa ba laifina bane, dole aka mun, kuma ba mai kuɗi na aura ba, zaɓin babana ne, amma mahaifiyarsa taki sauraronsa, ta zagesa tas, sannan ta ce idan zai je ya nemi kuɗi ma gara ya je ya nema ya fita batun soyayya, wannan magana tasa yai zuciya ya faɗa kasuwanci gadan-gadan, amma ya yi alƙawarin jirana ba zai yi wani aure ba. So Mahaifiyarsa bata shiri da Hajiyarmu, dan haka mahaifinsa kawai ya faɗawa zai je Germany wajena, ya mashi fatan alkhairi da fatan nasara, daga nan ya cigaba da shirinsa. A nan gidanmu kuwa, su Hajiyarmu suna nan suna shirinsu, Hajiyarmu ta haɗa Safiyya da wani ɗan yayanta, watau ɗan kawunmu, sunansa Aliyu Haidar, Safiyya bata wani damu ba, coz Haidar cikakken namiji ne kuma tsayayye, yana da ilimi addini da boko, Haidar shi ya ga Safiyya ya ce yana so, sai ya faɗawa Hajiyarmu, ta bashi izinin zuwa gida su dinga ganawa da Safiyya, idan ya shawo kanta ta fara son shi, shikenan sai ayi, to yanzu dai sun fara fahimtar juna, dan gaskiya Haidar wayayye ne, ya san yadda zai sarrafa zuciyar mace. A can gidansu Abbie kuwa, abubuwa sai kara dakule masu yake yi, yanzu haka Abbie yana shirin dawowa Kaduna, dama gidan da yake haya ya kama almost 4.5M, kun san yadda haya take a estates na Abuja, shegen tsada, amma saboda neman a sani ya je ya kama haya, and Zainab kawayenta sun kaita wajen wani Malami lokacin da ta koma gida bayan bayyanarsu, aikuwa malamin ya fi Abbie hatsabibancin, kun san ance gaba da gabanta aljani ya taka wuta, aikuwa wannan malami ya fi Abbie hatsabibancin, yai wa Zainab aiku ta samu kan Abbie, duk tsubbace-tsubbacensa ya gagara gane abin da ta mashi, dama malamin da ta je wajensa ya faɗa mata Abbie fa ɗan tsubbu ne, sai anyi bakin aiki a kansa, aikuwa ta ce ko green ɗin aiki ne ai mata. Haka ta biya 2M yarinyar nan, ta roki ƴar uwarta da ta bata aron kuɗi cikin gadonta, da farko ƴar uwarta taki, amma da Zainab ɗin ta rasa ballin to a sayar da gidansu a bata kason kuɗinta sai ƴar uwar ta bata aron kuɗin, ta kaiwa malam aka yi bakin sihiri. Tun daga wannan lokaci Abbie ya dawo tafin hannunta, sai abin da take so yake yi, aikuwa ta kwace duk kuɗin dake hannunsa, ashe ita ma kanta a buɗe yake, kuɗin da ya sayar da gidanmu na Kano 45M, ya kama haya da sauran abubuwa 5M ta tafi, saura 40M, Zainab ta dinga tatsan shi, kuma baya iya ce mata a'a, duk kuɗin da ta buƙata dole yake bayarwa, tashin farko ta kwace 25M ɗinta, tana cewa tana so ya cire ya bata, aikuwa daga nan ta dinga karɓar kuɗi, daga ta ce 1M, sai ta ce 2M, da haka ta tatse shi tas ya zama zero, sai dai ita ma kuma, da rashin lissafi yana kanta wai zata fara irin business da nike yi da kuɗin, aikuwa bata nemi shawaran kowa ba, wai so take ta yi komai a sirran ce sai dai a ganta ta yi kuɗi, aikuwa ta ga wani kamfani a online suna sarar da abaya. Nan ta masu dm, suka karɓeta hannu bibbiyu, aka ta buga ciniki, ta sayi kayan 35M nan take, dama kash Abbie ya bata, suka ce mata akwai yaransu a Abuja dake da shago amma shagon ba kayan da ta zaɓa, kayan da ta zaɓa daga Dubai za'a kawo, dan haka ta baiwa yaran shagon kuɗin idan an kawo kayanta ta je ta ɗauka. Ta yarda suka bata number wani mutum, ta dinga waya da shi yana mata kwatancen shago har ta je ko Abbie bai sani ba, ta yi satar fita. Aikuwa sun nuna mata shago kam ga shi nan, amma tun da suka karɓi kuɗi suka daina ɗaukar kiranta, suka yi blocking ɗinta bayan sun ce mata sati ɗaya kayanta zai zo, sati biyu suka wuce shiru, nan ta fara nemansu. Aikuwa tamkar zata zauce, ta dinga ihu, ta faɗawa Abbie, anje har shagon da suka nuna ashe ba nasu bane, tsayawa a kofar shagon kawai suka yi tamkar nasu, ta dinga kwatanta mutumin da ta baiwa kuɗi, aka ce ba a san shi ba, abu dai har ƴan'sanda ciki, daga karshe dole ta hakura an damfareta. Wannan abu yasa ta natsu ta sake komawa tatsan Abbie, ashe komai ya kare mashi shima, ga kuɗin hayansu na gab da ƙarewa, to shi ne yake shirin tattarawa ya mayar da ita Kaduna su sake faro kasuwanci daga farko tun da komai ya kare, ko yaron shago ne Abbie ya nema. Wannan kenan a ɓangaren Nigeria. To idan muka koma Germany kuma, na kammala wankana na shirya cikin Turkish dress da ya kawo mun, rigar tai bala'in yi mun kyau, sai dai rigar tsurarta ya kawo mun, ba underwears a ciki, kuma bana son mayar dana jikina, duk sai na ji babu daɗi, haka na mayar dana jikina na fito. Rigar irin Turkish marasa ɗankwalin nan ne, nan ma na ji babu daɗi, na ɗauki ƙaramin hijab ɗina na sanya a jikina, na yi kyau sosai, na zo zan ɗauki wayata sai naga alamar abu a cikin ledar rigar, ina dubawa naga kwalbar turarece, ga mamakina sai naga wannan turare da Abba ya ce mun baya son kamshinta a baya ne, wannan turaren irin wanda Hajiyarmu ta bani ɗin, itace dai ya kawo mun. Na yi mamaki, amma na fesa a jikina, na ɗauki wayata na nufi kofar fitowa. Da kyar na iya buɗe kofar, ina sako kai waje na yi kiciɓis da shi, yana tsaye a wajen, ya yi folding hands ɗinsa a saman kirjinsa. Muna haɗa ido ya motsa lips ɗinsa wajen cewa. "Wow". Ya faɗa ba tare da fitar sauti ba. Ya shaƙi wannan kamshin turaren dai ya ɗan lumshe idanu ya sake buɗewa a kan fuskata. Tafin hannunsa ya buɗe ya miƙomun da nufin in ɗaura nawa. Na buge hannun nasa ina faɗin. "Ka yi gaba zan bika a baya".... Ya ce. "An gama ranki shi daɗe". Can ƙasa yai maganar. Sai ya wuce gaba, na bi bayansa, sai kallonsa nike yi har muka isa dining. Like wow, na yi matuƙar mamaki da tsantsar farinciki ganin abincin Nigeria, ya Salam, rabona da abincin kasarmu shekara guda kenan, dan haka kowanne sai da na taɓa, amma na fi cin ɗanwake sosai. A gaskiya idan na ce Abba bai kashe mun zuciya da farinciki ba na yi karya, na dinga murna ina murmushi, ya yi folding hands ɗinsa a kirji yana ta kallon yadda nike murna, Musamman yadda nike cin ɗanwaken. Da naga sai kallona yake yi sai na ɗauki ɗanwake ɗaya a fork na miƙo mashi, ya ɗan turo mun baki kafin ya ce. "Bana cin yaji saboda kwallo"..... Na manta fa, saboda gudun da suke yi a wajen kwallo basa cin abu mai yaji, yaji zai iya affecting kirjinsu da ma lafiyar jikinsu, ai kunga ba gudun wasa suke yi ba, and suna motsa jiki sosai, suna gym, cin yaji zai masu illa gaskiya. Na ɗan tsuke baki tare da cewa. "To in haɗa maka mara ya ji kana so? Nasan ma kana son ɗanwake ai"......... Ya ɗan girgiza kai game da cewa. "Ba sai kin haɗa mun ba, bana jin cin komai, amma tabbas ina son cin ɗanwaken nan, abin da za'ayi ki tsotse mun yajin sai ki bani"....... Na ɗan yi dariya tare da cewa. "Na bakin nawa zaka ci?"...... Na ɗaga mun gera guda. Na zaci wasa yake yi, dan in gwadasa yasa na kai ɗanwaken bakina, na tsotse yajin ɗanwaken na jikin fork sannan na fitar na miƙa mashi. Ga mamakina sai na ga yasa baki ya karɓa. Zazzaro ido a kan fuskansa na yi, sai kuma nai blinking eyes ɗina two times dan tabbatar da cewa da gasken ne ya karɓa ya ci? Aikuwa dai da gaske ne, cike da mamaki na ce. "Abba, yanzu na bakin nawa ka ci? Da yawuna

Chapter 23 of 38