Share this page
da zan je in bar matata a nan, ciki zamu shiga tare mu fito tare"...... Na ɗan zare mashi ido game da cewa. "Wacece matar taka?"....... Ya ɗauke kallonsa daga kaina game da cewa. "Ke mana". Na haɗe rai tare da cewa. "Ni bana son irin wannan wasan, kaga ba haka muka yi da kai ba, kada ka ɓata mun rai a banza".... Ganin da gaske na ɓata rai ne yasa ya ce. "To sorry tawan, yanzu dai ni dai ba zan barki ki shiga cikin wajen nan ke kaɗai ba, inma mu shiga tare ko dai ki fasa shiga". A daidai lokacin Ibrahim ya kira wayata. Ina gani na ɗago da kallona a kan Abba, shi ma ni yake kallo, na kai hannu zai yi pick-up sai gani nai ya kwace wayar. Yai pick-up tare da sanyawa a H-free, on the other side Ibrahim ya ce. "Tauraruwata tun ɗazun nike ta jiranki, ga shi har ina fitowa waje baki ƙariso ba, lafiya?"........ Abba ya ɗaga ido ya kalli gate ɗin wajen, sai ya hango Ibrahim ɗin na fitowa. Aikuwa tamke fuska tare da cewa driver ya juya kan motar su koma, dan shi bashi da lokacin tsayawa yin magana da wannan jahilin. Ina jin ya ce a juya mota nai saurin fara ƙoƙarin buɗe kofar motar in fita, da sauri ya janye hannuna daga jikin motar tare da cewa driver ya kulle motar. Ɗaure fuska na yi tare da cewa ya sauƙeni bana buƙata, yaki kulani, na dinga masifa amma bai saurareni ba, ba yadda ban yi ba, ya kwantar da kansa jikin kujerar mota, ya lumshe idanunsa yana ƙoƙarin danne tsananin kishinsa. Na yi ƙoƙarin karɓar wayata, nan ma ya hanani wayar, ba yadda ban yi ba, amma ɗan tahalikin nan yaki kulani har muka isa gida. Ana parking ya ɗago ya kalli driver ɗin, a natse ya ce. "Kada wanda ya fita daga gidan nan ba da izinina ba". Driver ya ce angama sir, sannan ya buɗe motar ya fita. Slowly Abba ya dawo da lallonsa kaina, na tamke fuska tamau, cike da nuna tsantsar so ya ce. "Tsoron kallon angry face ɗinki nike yi tawan"........ Na yi banza da shi ban ce komai ba. Ya ɗan riko hannuna tare da cewa. "Smile nooooow, fushi baya maki kyau". Kwace hannuna na yi tare da cewa. "Ka buɗe mun motar nan in fita"....... "Shikenan abin da kike da buƙata?". Nai banza da shi. Ganin da gaske na yi fushi yasa ya shafawa kansa lafiya ya buɗe mun motar. Na fita da sauri har kamar zan kifa. Kai tsaye ɗakin Zahra na shiga, na ɗauki Muhammad dake wajenta na fito, ɗakina na koma, na rufe kofar har da sanya key sannan na zauna a bakin gado, ina jin tamkar na aikata wani gagarumin laifi. Abba kuwa bin bi bayana ba, dan ya ga na hau dokin zuciya, na fusata sosai, tabbas idan ya bi bayana za'a samu matsala, dan haka ɗakinsa ya nufa, ransa fes, yau wai shi ne yake da aure, aurenma ga macen da ya fara so a rayuwansa, ba abin da zai ce da ALLAH sai godiya. Ya kwanta a kan gadonsa tare da buɗe wayata, ko password babu a ciki, ya shiga ya hau mun bincike kaman wani ɗan jarida. Babu number wani namiji daban idan ba brother ɗina ba, sai number Ibrahim. Ban tsaya bibiyar chat ɗinmu ba ya fita kan number, ya dinga kallon hotunana yana ƙarawa, ya mirgina ya yi kwanciyar ruf da ciki, a fili ya ce. "ALLAH Nagode maka da ka mallaka mun wannan baiwa taka, ALLAH ka sauƙaƙa mun diramar da zai biyo baya nan da sati guda, ALLAH ka bani ikon koya mata sona kafin nan da sati gudan nan, in ba haka ba akwai matsala, my dad Hussain, yau ALLAH ya mallaka mun mammynka mai ɗan baki irin naka, yaron kirki, ba zan taɓa mantawa da kai ba, inai maka addu'a kullum, my wife, gani nan zuwa mu buga dirama, ai ba zan kyaleki na har sai na koya maki sona". Ya ɗan nisa tare da kifa kansa a kan pillow, wani irin barci mai daɗin gaske ne ya fara fusgansa, coz ko kayan jikinsa bai rage ba, take ya fara barci. Ba shi ya farka ba sai 12 daidai. Yana farkawa ya duba time, da sauri ya miƙe, kayan jikinsa ya cire, dan ya wastsake sai ya watsa ruwa, sannan ya fito, ya sanya jessy a jikinsa, kai tsaye kitchen ya shiga, yazamar mashi dole ya shirya cin hanci da toshiyar baki, ya san ya yi laifi, dole ya shirya mun abincin da zasu sanyani farinciki. Da kansa ya shirya mun delicious, kala uku yai mun, sai drink kala biyu, daga nan ya kwashesu zuwa parlo, a gurguje ya je yai shirin zuwa Masallaci. Bayan ya idar da sallah ne ya dawo ɗaki, cire jallabiyar jikinsa yai ya sanya pj's farare tas, sannan ya gyara gashin kansa, ooooh, kirjinsa sai harbawa take da karfi, dan yasan masifa zai sha, amma haka ya gama shirinsa, ya zuba turaruka masu daɗin kamshin dake kwantar da hankali. Yana kammala shirinsa ya ɗauki wayansa, ya bar nawa a kan gadon nasa, ya fito ya nufi ɗakina. Duk tunanina na rufe kofar da key ba mai shigowa, ga mamalina sai gani na yi an turo kofar, ban taɓa sanin akwai fingerprint a jikin kofar ba. Zubawa kofar ido na yi dan in ga waye zai shigo, ina zaune a kan gado Muhammad na gefena, ya kwanta yana wasa, ni kuma ina rike da wani ɗan ƙaramin littafi ina karantawa, amma ba karatun nike yi ba, tunanin yadda zan bar mashi gidansa kawai nike yi, dan na gaji da ikon da yake nuna mun, na yanke shawarar dakatar da shi tun da naga abin ya fara wuce tinanina, all my thoughts yadda muke a da ne yanzu ma, ina ɗaukansa tamkar Yah Abbas ɗina, amma yana ɓata mun rai, na ji haushin yadda ya hanani ganawa da Ibrahim, ya kure hakurina yau. Tsabar taƙaici da kyar na yi wanka na canza kaya zuwa hoodie pink color, yanayin garin akwai hadari alamar ruwan sama, so sanyi ya sauƙa sosai shiyasa na sanya hoodie. Muhammad da gulma jin an buɗe kofa yai saurin miƙewa zaune yana zazzare ido ya ga waye zai shigo.......... labarin A'isha zai dinga zuwa maku labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi. FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥 LABARIN AISHA.🥹💔 PART 31 Muhammad da gulma jin an buɗe kofa yai saurin miƙewa zaune yana zazzare ido ya ga waye zai shigo. Gently Abba ya shigo cikin ɗakin, kansa a ƙasa ya rufe kofar, a natse ya nufo wajen fa muke. Da gudu Muhammad ya diro ƙasa har kaman zai kifa Abba yai zafan rikosa, ya fashe da dariya yana faɗin. "Daddy I missed you more"......... Abba ya sumbacesa a cheek tare da cewa. "Miss you more mah boy". Ya faɗa tare da zama da shi a kan gadon ta gefen da nike, ya sauke Muhammad a gefe yana faɗin. "Boy, keep quiet bari mu yi magana da mammy ko?". Ya amsa da okey daddy. Abba ya dawo da attention ɗinsa kaina, sai da ya ɗan sauke ajiyar zuciya kafin ya ɗan ɗago ya saci kallona, na ɗaura pillow a kan cinyata bayan na tankwashe kafafuna, sannan na ɗaura hannayena kan pillow ɗin rike da littafin......... Wani irin uwar harara dana dallah mashi ne yasa ya ce. "Oh my God, kyau yana in da yake, tawan kome ta yi kyau yake ƙara mata, idan ta yi fushi kyau, ta yi dariya tamkar sauƙar ruwan sama a sahara, kai ba zan iya kwatanta irin kyan da kike yi ba". Ya ɗan dakata da magana, slowly ya juyo da jikinsa gabaɗaya muna fuskantar juna, muryansa a matuƙar sanyayye ya ce. "Ki mun duk hukuncin da kika ga dama zan ɗauka tawan, amma please ki daina wannan fushin, har cikin raina nike jinsa". Nai shiru ban amsa mashi ba, hakan yasa ya kai hannu ka karɓi littafin hannuna, ya ajiye a gefe, sannan ya miƙe, ya kwanto da kansa kan pillow ɗin, ya ɗago kallonsa gabaɗaya sosai a kaina, can ƙasa ya ce. "Tawan, ki mun duk hukuncin da kike ga ya dace dani, ba zan ja dake ba". "Tashi mun a ƙafa". A ƙule na faɗa. Ya make mun kafaɗa tare da ɗan shagwaɓe murya wajen cewa. "Laps ɗin tawa ce ai, ni dai please a mun afuwa, ko dai so kike sai na maki kuka?".......... Tamkar wacce aka yi wa alluran masifa, na fara zazzaga masifa ina faɗin ya sanya a buɗe mun gate, dan gidan nan zan bari, ba zan sake zama da shi ba, dama ba da sanin iyayena nike nan ba, su duk sun zaci ina in da suka ajiyeni, ga shi saboda shi last week Yah Abbas zai zo na ce ya bari sai oper week, yanzu idan ƴan uwana suka san ina gidansa me zan ce masu, na dinga masifa tamkar zan kai mashi duka. Ya dinga bani hakuri, dan shi yanzu soyayyata yake nema ba rigima ba, duk abin da zai ɓata mun rai baya son ganinsa, farincikina kawai yake so. Ba ƙaramin fama ya sha ba kafin iya shawo kaina, dan ma dai yana da basira da iya magana ne, dan a wannan karon yadda na fusata ba kaɗan bane. Da kyar ya samo kaina, a cikin ransa sai godiya ga ALLAH yake yi, a fili kuwa ya ce. "Muje to in baki lunch kici ki ƙoshi". Ya faɗa yana riko hannayena......... Na kwace hannuna tare da cewa. "Ni sakeni rigimamme kawai, duk ka canza Abba, tamkar ba kai ba, sai masifa ka iya yanzu wanda kuma ba haka kake ba a da". Ya mirgina yai kwanciyar ruff da ciki, muna fuskantar juna, can ƙasa ya ce. "Kece sular masifar ai ƴar nema kawai, ni dai tashi mu je kici abinci kada ki zauna mun da yunwa"........ Na kai mashi dukan wasa a baya. Ya riko hannuna ya manna da lallausan kumatunsa kafin ya ce. "Tawan yanzu kin daina kula dani sosai kamar a baya, kin daina shagwaɓani, please ki dawo yadda kike mun a da kin ji?". Na wani kallesa, muna haɗa ido wani irin spark na ji zuciyata ta yi, da sauri na ɗauke kallona tare da kai ɗayan hannuna na tallabo kumatunsa both sides, a hankali na fara ɗan shafa kwantaccen sajensa kafin in ce. "Kai ne ai, ka zama rigimamme shiyasa na fita harkanka"......... "To zan zama yadda kike so dan in samu kulawarki". "Nawan, ka kara kyau sosai da sosai, kalli yadda face ɗinka ya yi gwanin ban sha'awa". Na faɗa a lokacin da nike cigaba da shafa sajensa. Sosai Abba ya ji daɗi ganin ya fara koya mun mance kaina da matsayina idan ina tare da shi, yasa na fara komawa kamar da yadda nike wasa da shi, yanzu so yake ya koya mun mance komai idan muna tare, in saki jiki in biye mashi. Ɗan lumshe idanunsa ya yi tare da sake warosu a kan fuskata, yai ƙasa da murya wajen cewa. "Ko rabinki ban kai ba a kyau, kin ganki kuwa? Hmmmmm, ALLAH ya kai damo ga harawa, ko bai ci ba zai yi ɓarna". Na ɗan matsa kumatunsa tare da cewa. "Ka ganka ko? Kyau ai yana wajenka nawan, uncle daddyn Muhammad". ....... Ya kama hannuna ɗaya dake kan kumatunsa ya dawo da shi saitin bakinsa, ya ɗan sumbata tare da cewa. "Daddynsa ne dai ba uncle daddynsa ba"........... Har cikin raina na ji wannan sumbata, jikina dukka sai da ya amsa, da sauri na zare hannuna tare da cewa mu je mu ci abinci, dan kada ya jefani cikin wani yanayi, rabona da namiji 2 year har da ɗan ɗoriya, to tun da ba itace bace ni ai dole zan ji buƙata, bare kuma a nemi motsa mun shi, duk sai na fara jin wani iri, gudun matsala yasa na kwace hannayena tare da cewa ya tashi mu je mu ci abinci. Bai so mu bar mood da muke ciki ba, amma haka ya daure ya miƙe, ya ɗauki Muhammad muka fito. Ya tasani gaba, shi ya ja mun chair na zauna. Muna zama sai ga Zahra ta fito, ta gaishesa ya amsa, sannan ya zuba mun abinci, ya hau bani a baki yana gaya mun kalamai masu narka zuciya, tun bana biye mashi har na saki jiki ina ɗan biye mashi a hankali, sai da ya tabbatar ya cika mun ciki, sannan ya ce please shi ma in bashi a baki. Da farko naƙi, amma da ya marairace mun ya dage sai ga shi na yarda, na dinga bashi har sai da ya ƙoshi, muka je ya rakani har ɗaki na kwanta, sannan ya fito ya shiga nasa ɗakin cike da tunanin yadda zai yi mu fara kwana ɗaki ɗaya, dan hakan ma zai taimaka mashi wajen samo kaina, yasan haka kawai ba zan taɓa yarda ba, dole sai ya samo dabara. Tun da ya shiga ɗaki bai fita ba sai lokacin sallar la'asar, ya fita zuwa masallaci, bayan ya yi sallah ya dawo ɗakina ya nufa. Without excuse kawai ya faɗo mun cikin ɗaki, ina tsaye daga ni sai towel, sai yau na fito da kayan da muka je shopping na hau dubasu. Na yi wanka ne na rasa kayan sakawa, shi ne na ce ba ri irin duka bayan da muka sayo ko akwai wanda zai mun in sa, dukka kayayyakina na gaji da sanyasu. Da gudu Muhammad yai kansa yana ambatar sunansa, ya kai hannu ya ɗauki yaron kallonsa a kaina, na juyo na kallesa sai kuma na haɗe rai tare da wucewa na ɗauko hijabin sallah ta, na sanya a jikina wanda ya tsaya mun iya gwiwa, na hararesa kafin in ce. "Sai ka dinga shigowa mutum ɗaki ba sallama ko?". Ya ɗan yi one sided smile tare da ƙarisowa ciki, can ƙasa ya ce. "Da kai da kaya ai duk mallakan wuya ne"....... Ban ji me ya ce da kyau ba, sai na ce ban ji ba. Ya ce. "Ban ce komai ba, na ce amin afuwa, kuma ni ɗana na zo gani, ban san da mutum a ɗakin ba"........ Na ɗan zare mashi ido, sai kuma na ce. "Ɗauki ɗan naka ku bani waje na sallameku". Ya ɗan nisa tare da cewa. "Har da kora tawan? Sanyi fa muke ji, ba zaki barmu mu ɗan sha ɗumin jikin Mammy ba? Ko mah boy?". Ya faɗa yana kallona amma yana shafa kan Muhammad.......... "Da ku da ɗumin duk kun ci gidanku, ni ku fita mun a ɗakin"..... Ya riko hannuna da sauri tare da cewa. "Zo kiji wata magana tawan"........ Ina ɗan hararansa na ce mekenan?. Slowly ya sauke Muhammad daga kan laps ɗinsa, ya ce. "Zauna a nan in faɗa maki"... Na kalli in da yake nunawa watau kan cinyarsa, na wani kallesa kafin in ce. "Wai kam nawan ni babynka ce? Ka ɗaura su Muhammad a kan cinya nima ka ɗaurani kan cinya?".......... Ko kaɗan ban san romance ba, in baku manta zamana da Abbie ba ai shi baya wani soyayya face biyan buƙata, dan haka ni ma abin da na sani tsakanin mata da miji kenan biyan buƙata, so yanzu gani nike ai sai yara ne zasu zauna a cinyar mutum, I'm not romantic at all. Can ƙasa ya ce. "Kin fi baby ma ai, zauna in faɗa maki wani abin a kunne"....... Na buge hannunsa da ya rikeni wanda yasa ya sakeni ɗin, ina hararansa na ce. "Ku fita mun a ɗaki bari in sanya kaya"........ Ya gyara zama game da cewa. "Ɗauko kayan sai in sanya maki"........ Wata sabowa, dariya ya bani wai ya sanya mun kaya, sai kace su Muhammad ne ni, ai yara ake sanyawa kaya a nawa tunanin. Na ce. "Kaga nawan bana son dogon surutu da iyashege, ni kada ka wani dameni, ka sanya mun kaya ni su Muhammad ne? Ni dai ku fita mun a ɗaki".......... Abba ya kalleni da kyau, da iya gaskiyata nike magana, hakan ya tabbatar mashi da kwata-kwata ban san romance ba, a ransa yana jin ba zan yi wahalar faɗawa son shi ba, domin zai yi wa zuciyata abin da ban taɓa sani bane, ba'a taɓa mun ba, tabbas yana jin cewa ko iya romancing ɗina yake yi zan fara son shi, bare ya bani asalin soyayya da kulawa. Muryata ce ta dawo da shi daga duniyar tunanin da ya afka, na ce. "Wai ba zaku fice mun daga ɗaki ba?". Na yi maganar ina jawo ledojin shopping ɗinmu na ranar. Na fara fito da kayayyakin ina duba wanne yakamata in yi amfani da shi, dan ga wasu ƙananan kaya masu kyau, akwai ni da son ƙananan kaya sosai. Na fito da wani wandon jeans baki wanda bai karisa kaiwa ƙasa ba, sai t-shirt ɗinsa fari da kwalliyan baki a jiki. Na ɗaga kayan, sun yi matuƙar kyau, na jawo ɗayan ledar zan duba me a ciki, unexpected na kalli bra da pant da nike son ɗauka amma naƙi ɗauka saboda Abba. Bala'in can, da sauri na ɗago na kallesa, yana ta faman biyewa gwalanniyar Muhammad, ya fito da tongue ɗinsa Muhammad na wasa da shi yana dariya. A raina na ce watau duk abin da nike yi a wajen shopping ɗin nan hankalinsa na kaina saɓanin yadda na zaci cewa hankalinsa na kan Muhammad? Watau ni yake kallo, har yasan na yi niyyar ɗaukansu ka sake fasawa, innalillahi wa inna ilaihi rajiun, sai na ji wani irin kunyansa ya kamani. Na sake duba cikin ledar, dukka biyu ya ɗauko mun ashe, sannan ba iya su ba, underwears ne dayawa a cikin ledar. Rintse idanuna na yi da ɗan karfi tare da mayar da ledar da sauri na rufesa, a hankali na zari wannan pant da bra makaken, na ɓoye cikin rigana ina satar kallonsa. Ko kaɗan hankalinsa baya kaina, amma ban yarda ba, dan a shopping ɗin nan da muka je ba zaka taɓa tsammanin ya kalli ko abu ɗaya da nike yi ba, ashe tsab yana kallona, dan haka yanzu ma ban yarda baya kallona ba. Na mike da sauri na nufi toilet. Ta ƙasan ido ya bini da kallo zuciyansa na ingiza shi da ya tashi ya bini........ Ni kam ina shiga toilet na jingina da jikin bango, ya Salam, haƙiƙa Abba ya taɓa zuciyata yau, wai har yasan abin da nike so, ya saya ya bini da shi, abin da ba'a taɓa mun irinsa ba a rayuwata, gaskiya idan na ce Abba bai jijjiga zuciyata da tsananin farinciki ba na yi karya. Na ɗauki minti biyu a haka ina ƙoƙarin dawowa daga duniyar mamakin da ya jefani, a hankali na zame hijabin jikina, sannan na kwance towel ɗin, bra da pant ɗin na fara sanyawa, sun kuwa zauna a jikina ɗas, na yi murmushi, har cikin raina na ji wani irin yanayi a kan Abba na wannan abin da ya mun. Na sanya kayana, sai na fito, na samesa zaune yadda barsa. Yana ganina ya bar danne abin dake zuciyansa ba, a cewarsa yanzu matarsa ce ni, so ya daina wahalar danne abin dake ransa. Ya miƙe yana yabon tsantsar kyan da na yi, ya ce in zo mu yi hoto. Wani irin daɗi sosai naji, ashe haka abin yake da daɗi idan ka yi kwalliya mutum mai muhimmanci a tare da kai ya yaba, a gaskiya na ji matukar daɗin yadda Abba ya dinga yabon kwalliyata. Ya tasani gaba sai da muka yi hotuna da shi, lokacin da muke ɗaukar hotunan ji yake tamkar ya sumbaceni a kumatu, amma ya daure dan kada ya ja mu yi faɗa. Haka ya zauna a ɗakina yana ta jana da hira, ai tun ina noƙewa har ban san lokacin da na saki jiki ba, muka dinga hira, wani lokaci ya kama hannayena yana wasa da su, ya ce ya ƙosa ya ga an zuba mun lalle a hannun nan nawa, coz suna bala'in tafiya da shi, har yau ya gagara mance ranar da na yi gyaran jiki aka mun lalle, a wannan rana kwana mafarkina ya yi. Ni kam na dinga jin daɗi ina farincikin yaba mun da yake yi. Bai bar ɗakina ba sai da aka kira sallar magrib, sannan ya tafi shirin zuwa Masallaci. Nan fa na samu damar juyawa zan ɗauki wayata in kira Hajiyarmu dan tun safe bamu yi waya ba, nasan kuma ta yi ta kirana, dan ba'a awa biyu bata kirani ba, sai dai ina dubawa wayar ban ganta ba, sai na tuna ai tana hannun Abba, dama idan mun gama waya da Hajiyarmu ina son kiran Ibrahim ma, in son bashi hakuri kan abin da ya faru na rashin ganina da bai yi ba. Miƙewa na yi, na yi sallah Muhammad na gefena yana kwaikwayon abin da nike yi. Bayan na idar da sallah na yi zaman ashkar da karatun Alqur'ani, har lokacin sallar ishai ta yi, na miƙe nai Sallah. Ina idarwa na tashi na cire hijab ɗina, na zauna ina tunanin yadda zan yi da Ibrahim, ina son haɗuwa da shi, amma da alama Abba ba zai bari ba. Ina tsaka da wannan tunani sai ga Abba ya shigo bakinsa a ɗauke da sallama. Muhammad yai wajensa da gudu yana oyoyo daddy, Abba ya ɗaga shi sama ya wurga sannan ya capke kafin ya mannasa da kirjinsa yana faɗin. "Mah boy, ka yi kewar daddy ko?". Ya jinjina shi ma da gulma, wai e ya yi kewar daddy. Abba ya sumbaci ɗan bakinsa game da cewa. "Tawan, tashi mu je ki ci abinci"......... "Kai dai ba zaka kar mutum ya huta ba". Na faɗa ina haɗe rai. Ya ja hannuna tare da faɗin. "Tashi ko in sauke boy in maki ɗaukar amarya"....... Da sauri na miƙe ina faɗin kada ya tara mun wahala. Ya ce ya fi maki, nai gaba ya rufa mun baya, dining room muka shiga, ya zauna ya tasani gaba sai da ya sanyani cin abinci sosai da sosai, sannan ya ci kaɗan shi kuma, muna kammalawa sai ga Zahra, ta zo ta yi zaman cin nata. Abba ya miƙe rike da Muhammad a hannunsa yana faɗin. "Tawan, bari in sanya boy ɗina barci, zan sameki a ɗaki mu yi wata magana"....... A natse na ce. "Abba, my phone". "Yana ɗaki zoki karɓa". Ya faɗa yana barin dining room ɗin. Da sauri na miƙe na bi bayansa ina faɗawa Zahra ina zuwa. Kusan a tare muka shiga ɗakin nasa, ina shiga ya rufe kofa ruff kamar cewa kin shigo kenan sai da safe, ni ban ma lura da ya rufe kofar ba. Yana zuwa wajen bed suka faɗa kan gadon da Muhammad a jikinsa, yaron ya fashe da dariya yana faɗin. "Daddy zamu yi wasan jiya ne?"....... Na kallesa cike da mamaki wai daddy zamu yi wasan jiya ne, watau har ma yasan wasan da suke yi, kai Abba duk ya lalata mun zuciyar yara da tsananin kaunansa. Abba ya ɗago yana sumbatarsa ya ce. "Yau har da mammy ma a cikin wasan". Ya faɗa yana ɗan satar kallona. Na ƙariso in da suke, zan yi magana wayar Abba ta fara ƙara. Jawo wayar ya yi tare da dubawa. Number Nigeria ce. Kamar ba zai yi picking ba, sai kuma ya ɗauka. Daga ɗayan ɓangaren aka ce. "Muhammad". ..... Ya ɗan yi shiru, sai kuma ya ce. "Kawu Badamasi". Mutumin ya ce. "Ashe dai baka manta dani ba"..... Ya ce. "Ya za'ayi na mance daku, kune fa duniyata, ya gida ya kaka?"..... Kawu Badamasi ya amsa da kowa lafiya lou, sannan ya ce. "Shehu ne ya ce mana kana raye shiyasa na ce ya bani lambarka......". Ɗiff kiran ta katse, da alama katinsa ne ya kare. Abba ya ɗago ya kalleni, ina tsaye na zuba mashi ido, na ce. "Abba, kawu Badamasi da na sani? Na kauye?"....... Ya jinjina mun kai. Sai na ce. "Yana da kirki

Chapter 26 of 38