Share this page
na rawa na ce. "A'a Hajiya, ba haka bane, dan ALLAH ki tsaya in faɗa maki abin dake faruwa"...... Cikin faɗa ta ce. "Babu abin da zaki faɗa mun, tun da har wasu iyaye kika sake ai shikenan!". Tana kai nan ta kashe kiran. Hankalina idan ya yi dubu ya tashi. Saurin kukana yasa idanuna suka ciko da hawaye, ina ta faman buga lambar Hajiya, amma bata ɗauka, cikin tashin hankali na ce. "My honey, zuciyata zafi take mun sosai". ......... Ya rikeni a shoulder, in a cool way ya ce. "Tsaya shiru, ki kira sunan ALLAH sau uku a ranki, zaki ji sanyi". Na aikata abin da ya umarceni, cikin ikon ALLAH na ji zuciyata ta yi sanyi, na sauke nannauyar ajiyar zuciya, sannan ne ya ce. "Me yakefaruwa?"......... Ban ɓoye mashi komai ba, harta baikon da iyayena suka mun da Ibrahim na faɗa mashi. Tambaya ta farko da ya fara mun shi ne. "Tsakanin ni da Ibrahim wanene ya riga? Ina nufin an riga aurenmu kafin baikonsa ko dai da baikonsa a kanki muka yi aure?". "Mun yi aure da kwanaki kafin baikonsa, kwanaki biyu da suka wuce aka yi baikon". .. ajiyar zuciya ya sauƙe, coz bai son taka dokan ALLAH, da ace da baikon wani a kaina ne ya nemi aurena da matsala, dan ba'a nema cikin nema, amma tun da ya riga mallakata lafiya lou ne. Ya karɓi wayata, a sanyayye ya ce. "Daga yau kada ki kira kowa kuma kada ki ɗauki call ɗin kowa, bani passport ɗinki, gobe zaki wuce gida, ki ajiye duk abin da kike yi mu tafi, wannan ba magana ce ta waya ba, magana ce ta fuska da fuska, zamu je mu samu su Hajiya, kome zai faru mu shirya ɗauka, amma ina son ki mun alƙawari ɗaya". Na ɗago na kallesa. "Ina jinka, wani alƙawari?"......... "Ki mun alƙawarin duk wuya duk daɗi ba zaki iya rabuwa dani ba".... Na jinjina mashi kai game da cewa. "In Sha ALLAH muna tare da kai mijina". Ya saki one sided smile, a hankali ya shafa kaina zuwa gadon bayana. Abba akwai tsananin natsuwa da hankali, cikin natsuwa yake komai, har ya sama mun natsuwa da kwanciyar hankali, na dinga sauke ajiyar zuciya masu nauyi nauyi. Ya ƙara manneni da jikinsa yana cigaba da shafa bayana. Mun jima a wannan yanayi kafin ya ce. "Bari in duba yarana, time na tashi Muhammad ya yi"....... Mamaki ne ya kamani, coz ko ni da nike mahaifiyarsa ban rike time da yake tashi daga barci ba, amma Abba ya rike. Sakeni yai ya miƙe ya sauƙo ƙasa, na buga uban tagumi ina tunanin yadda zan kwashe da Hajiyarmu. Abba bai dawo wajen ba sai after 1 hour, ya dawo rike da Muhammad, Hassan na biye da shi a baya, ya masu wanka ya canza masu kaya yadda ya saba tun muna Naija, sun yi tsab-tsab da su, ya basu abinci sun ci sun ƙoshi. Yana zuwa ya zauna dasu kan sofa suka fara saka shi surutu, yana yi yana kallona, nima na tsaresa da idanu. Ya ɗaga mun gera guda alamar yane?. Na ce. "Ina ganin haɗuwarka da yaran nan ne, kuna kashe mun zuciya da kaunarku"......... Ya kashe mun ido ɗaya. "Mun ƙosa ki ƙara mana yawa, please yaushe takwarata zai samu ƙani?". Da sauri Muhammad ya ce. "Daddy ni bana son ƙani"....... Abba ya zazzaro mashi manyan idanun san nan game da cewa. "Meyasa baka son ƙani mah boy?". .... Yana tura baki irin shagwaɓar mamarsa ya ce. "Ƙani zai sanya mammy ta daina kula dani sosai"....... Cike da mamaki Abba ya ce. "Waye ya faɗa maka wannan karatun kuma?". "Uncle Ibrahim ne ya faɗa mun, ya ce wai idan mammyna ta sake haifa mun ƙani shikenan zata daina bani kulawa, hankalinta zai koma kan sabon babynta, ya ce mun ba zai bari mammy ta haifa mun wani ƙani ba, saboda kada a rage mun gata, wai ni kaɗai zan rayu a wajen mammyna"....... Kallon gefen ido Abba ya wurga mun, lallai kam, da matsala, ni ma kallon Abban nike yi sosai. Ya ɗan sumbaci cheek na Muhammad, a natse kuma yadda zai fahimtar da shi ya ce. "Mah boy, ƙani alkhairi ne, kuma ƙani ba zai hanaka jin daɗin rayuwarka ba, and daddynka yana sonka sosai, yana tsananin kula da kai, kuma ƙani abokin wasa ne, tare zaku dinga wasa, baka son abokin wasa ne?"........ Ya amsa da. "Ina son abokin wasa"....... Abba ya sake sumbatarsa. "To ka gani, ƙani abokin wasa ne, zaku ƙaunaci juna sosai, zai kula da kai sosai". Ya ce. "To daddy ina son ƙani, yaushe zaka kawo mana?"....... Ya ɗago da kallonsa a kaina, cikin harshen turanci ya ce. "Watau na zauna na yi wa yara tarbiya shi ne kika bari wancan yana neman gurɓata masu tunani ko? Kin ga manufansa ai ko? Baya son yara, har yana faɗawa takwara kada ya so ƙani, saboda kunna wutar gaba a zuciyar yara tun suna ƙanana". Na ɗan yi shiru, akwai point da Abba yake son kaiwa, amma sai ya fasa yin maganar, na gano hakan, sai na kai shi wajen da cewa. "Kenan dama Ibrahim ba son ɗana yake yi ba, kawai dan ganin ido ne domin kuwa a bashi ni, dan idan da ace yana son ɗana ba zai yi gigin nuna cewa baya son yara bama kwata-kwata, kenan a nufinsa idan muka yi aure ba zan haihu ba?". Maganar da Abba yake son yi kenan, amma ya fasa. Ya ɗan yi shiru, tamkar ba zai amsa ba, sai kuma ya ce. "ALLAH ya kyauta, amma daga yau kada ki sake bari wani ya ɗauka mun ƴaƴa ko na seconds biyar ne, idan kun je gida please ko'ina zaki je suna tare dake, ba zai yiwu ina masu tarbiya ana warware mun ba, ba zan ɗauki wannan ba!"....... Na jinjina kai, sai na ce. "Yaro yana da saurin rike abu sosai, dole a lokacin da yake tasowa a kula da maganganun da za'a shigar mashi ƙwaƙwalwa, lallai ƴaƴana sun daina nisa dani daga yau, da ace yanzu Muhammad ya tashi da wannan ɗabia ba zai taɓa son ƴan uwansa ba, zai ga tamkar suna hana mashi wani abin, suna tare mashi jin daɗi rayuwa, idan aka yi rashin sa'a suka fi shi wani abin, zai dinga ganin tamkar su suka tare shi baya samun nasara, kamar yadda Ibrahim ya gwada mashi cewa ɗan uwansa zai sanya iyayensa su rage son shi". Abba ya mai da kallonsa kan oga Hassan da ya kwanta a saman kujerar yana danna wayar da Abban ya bashi. Ajiyar zuciya ya sauke tare da cewa. "Exactly Bappana haka halin babana yake, ba ruwansa da kowa, haka bappana yake, na yi kewansa sosai". Na ce. "ALLAH yai masu rahama". Ya amsa da amin, Muhammad ya fara damun Abba da hirarsu yana sanya shi surutu, haka ya dinga biye mashi har lokacin sallar azahar suka tafi masallaci. Yau dai gidan haka muka wuni cikin tsantsar farinciki, Abba ya yi mana booking fly gobe by 2 In Sha ALLAH. Muka hau shirye-shiryen tafiya. Abba ya kashe wayata gabaɗaya dan ma kada a kirani. Da daddare Abba ya so mu raya Sunnah kafin gobe mu wuce Naija, amma naƙi yarda, ya yi ta mun magiya amma naki yarda, har ciwon ciki sai da ya yi saboda tsanannin karfin sha'awa da buƙata, dama in baku manta ba ya taɓa faɗa mun matsalarsa, amma duk da haka na ki yarda, ya dinga bani haƙuri ni kuma na dinga mashi kuka kan ban yarda ba, dole ya hakura ya kyaleni, ya kwanta yana dafe cikinsa yana nishi sama-sama. Ni kuwa na hana shi kaina ne saboda so nike sai na je gida, in gyara kaina sosai, yadda yake nuna mun kauna nima haka nike son nuna mashi tsantsar kauna, shiyasa na hanasa....... Da kyar ya samu saukin ciwon, ban da sannu babu abin da nike ce mashi, ya jawoni jikinsa ya ƙamkameni gam har ya samu natsuwa, sannan ya kwantar da kansa a kirjina yana sauke numfashi a hankali. Su Hassan already sun yi barci abinsu. Tsabar ya sha wahala yau ya gagara iya shiga toilet yai wanka, haka yai barci kansa na kwance a kirjina, ina shafa gashin kansa zuwa bayansa, shi kuma hannunsa ɗaya na kan bayansa ya yi kwanciyar ruff da ciki, ɗayan hannnunsa kuma yana kan kirjina ma'ana kan breast ɗina, dan su suka taimaka mashi ya samu natsuwa. A haka nima na yi barci, muna manne da juna kenan...... Washegari da safe tun da sassafe muka hau karisa shirinmu, Zahra ta ce zata bimu na ce a'a zamu dawo ba jimawa, ta cigaba da zama a nan. Ba dan ta so ba ta hakura muka tafi muka barta. Karfe 2 jirginmu ya ɗaga sai Naija, Abba bai bani damar shiga zulmi da fargaba ba, ya ɗauke mun hankali da salon soyayyarsa mai tsananin ɗaukar hankali. A Abuja jirginmu ya sauƙa, na sha mamakin ganin wasu danƙara-danƙaran motoci guda biyar sun zo ɗaukanmu, Abba ya kama hannuna muka shiga motocin, kai tsaye wani tampatsetsen estate kusa da asokoro muka nufa. Ashe ya yi gini a Nigeria, amma da alama ba'a jima da kammala ginin ba, dan sabon gini ne da bai wuci wata ɗaya da aka yi shi ba. Kai ƴan kwallo suna samun mazajen kuɗaɗe na gaske, musamman idan kana bugawa babban ƙungiya kwallon, ya Salam, waus mazajen kuɗi ne ke shigowa Abba na ban mamaki. Wannan gida shi ake cewa aljannar duniya, sai naga kamar ya fi gidansa na Germany kyau, komai na more rayuwa akwai a ciki. Haka muka shiga ciki, a nan muka kwana, washegari muka kama hanyar Kaduna. Muna isa kai tsaye gidanmu ya umarci driver da ya wuce damu. Haka kuwa aka yi, sai dai tun da na doso gida gabana yake faɗuwa, Abba ya yi ƙoƙarin kwantar mun da hankali, amma abin ya ci tura. A haka muka ƙarisa gida, muka yi horn mai gadi ya buɗe, muka danna hancin motar cikin gida. Sai da na ji kaina na wani irin ciwo mai matukar tashin hankali. Abba dai yana cigaba da kwarara mun gwiwa. Muna parking sai ga Safiyya tare da Haidar sun fito, ta sallami Haidar ya fice ita kuma ta jiya zata koma ciki tana kallon motar da muke ciki dan bata gane su waye bane, amma da yake ɗabi'ar ƴan gidanmu basu shiga harkar kowa sai bata wani damu ba zata wuce, ga shi motarmu tinted ne bata ga su waye a ciki ba. Abba ya sauke glass ɗin motar game da cewa. "Amarya bakya laifi"...... Safiyya ta zazzare ido a kansa, ta dinga kallonsa babu ko kyafta ido, Ya Salam, wani irin abu ta ji a ranta, innalillahi wa inna ilaihi rajiun, haƙiƙa ta yi rashin namijin da ake cewa namijin gaske, ya Salam, ko makawo ya shafa ya san Abba cikakken namiji ne tsayayye. Ganin yadda take kallonsa yasa har na fito da sauri na zo na rufe mata fuska bata lura ba, Abba yai murmushi kaɗan, dan ba cika son murmushi yai ba, a ransa ya ce. "Watau tawan yadda take kishina har ƴar uwanta bata bari ba". Wani irin sanyi ya ji a ransa, ya ji daɗi matuka. Ita kuwa Safiyya tana jin muryata ta fasa wani irin ihu tare da ƙankameni, na zame hannuna daga kan fuskarta, muka ƙanƙame juna cikin tsananin farinciki, tana murmushi a kunne ta raɗa mun. "Aunty kin ga yadda Abba ya ƙara wani musulmin kyau kuwa? Ina jin kamar ba zan iya rabuwa da shi ba, innalillahi wa inna ilaihi rajiun, kai Aunty ga namiji a nan kam". Tun da ta fara magana nike jin kirjina yake bugawa, ya zata ji idan ta ji cewa yanzu ni Abba yake aure? Duk da an bata miji amma son Abba na ranta, kuma da zata samu ƴar dama zata koma mashi, coz Haidar ta karɓesa ne kawai dan ba yadda ta iya. Hannunta na ja da sauri dan mu bar wajen, coz har cikin raina na ji wani iri da tana kalle mun miji. Sai da na kai dab zan shige cikin gida na waigo Abba, ya zuba mana ido yana kallon mu, ina waigosa ya kashe mun ido ɗaya cike da tsantsar so da kauna, na ɗan yi murmushi muka wuce ciki. Ya dawo da kallonsa kan su Hassan dake zaune a bayan mota, cike da kulawa ya ce. "Babana zaku bi Mammy ne ko dai mu tafi yawonmu tare?". Hassan ya ce. "Ni bana son gidan kaka uncle daddy, kawai mu tafi". Shi fa Hassan baya son gidanmu ne saboda brothers ɗina suna yawan ɗaukansa, wannan ya jasa ta nan wannan ma ya jasa ta nan, Safiyya ta yi ta faman yi mashi surutu, shi kuma baya son hakan, idan shi da Abba ne kawai a ɗaki zai kwanta shiru shiyasa ya fi son zama da Abban. Shi kuwa Muhammad da ya fi wayau a gidanmu sai ya ce. "Daddy zan bi Mammy"...... Abba ya buɗe mashi kofar motar yana sumbatarsa a cheek. Ya fito da sauri ya nufi cikin gida........ Ina shigowa parlo na isko iyayena a zazzaune, ga su babban yayanmu duk suna zaune. Jikina ne ya tsananta rawa, kirjina na bugawa da karfi na ƙariso ciki. Safiyya ta je da gudu ta rungumi Hajiyarmu tana faɗin. "Hajiya Aunty ta zo, dama zata zo ne shi ne baku faɗa mun ba"....... Hajiyarmu bata amsa ba, hakan ya ƙara kashe mun jiki. Muhammad ya shigo da gudu ya tafi jikin Safiyya, ta rungume shi suka kwanta a jikin Hajiyarmu......... Iyayena sun ɗauki zafi sosai, musamman Hajiyarmu da ta ce na raina su ne, ai yanzu gani nike daidai nike da ita, ta haifa na haifa shiyasa nike ganin zan iya yin komai ba tare da su ba, kalmar da ta fi komai kona mun rai kenan a maganar Hajiyarmu, dan kuwa a duniya babu abin da na fi girmamawa sama da iyayena, amma Hajiyarmu ta ce saboda na haifa gani nike daidai nike da ita, innalillahi wa inna ilaihi rajiun, wannan kalma ta bala'in kona zuciyata sosai, har kuka ta sanyani, na ji gabaɗaya na tsani rayuwata, na yi danasanin sanin zuri'ar Abbie gabaɗaya. Na tabka babban kuskure na sani, na san na aikata abin da dole iyayena su fusata, su sha wahala su karɓa ƴancina, har kotu suka yi shari'a da Abbie, suna nuna mun kauna, suka tsaya mun, amma na watsa masu ƙasa a ido na koma cikin family ɗin da suka yi faɗa a kai. Na san ban kyauta ba, haka na dinga kuka ina basu hakuri, babu wanda ya goyi bayana, da farko babban yayanmu ya tayani baiwa Hajiyarmu hakuri, amma daga baya da na faɗa da bakina cewa gaskiya ne mun yi aure da Abba, aikuwa babban yayanmu bai ma san lokacin da ya tashi ya rufeni da duka ba, dama duk family shi kaɗai ne mai bin bayana, duk wani rikici idan na ɗebo shi yake tayani tarewa, amma yau ta kai shi yake dukana, tun daga nan na kara girmama girman laifin da na masu. Muhammad ya yunkura da gudu zai sauƙa ƙasa yana faɗin a daina dukan mammynsa, Safiyya ta rike shi ta hana shi sauƙa, sai kuka yake yi. Hajiyarmu ta ce ba zata sake yin magana dani ba, na dinga bata hakuri ina kuka tamkar raina zai fita, daddynmu ma ya ce tun da ina da wasu iyaye a waje da zasu iya aurar dani ai shikenan sai in tafi wajensu. Ya Salam, tamkar zan yi hauka, na dinga basu hakuri. Da babban yayanmu ya ga xan iya zaucewa, ALLAH sarki ɗan uwa mai daɗi, jini ba wasa ba, sai ya tsoma baki, duk da yana cikin fushi shi ma, ga shi ya dakeni sosai, amma hakan bai hana shi sake dawowa muka haɗu muna baiwa Hajiyarmu hakuri ba, Yah Abbas kam ya rasa bakin magana, ya ce shi na fi rainawa hankali sama da kowa a gidan, dan shi ya je har kasar da nike, ashe lokacin ma da aure a kaina, na raina mashi wayau. Safiyya ta gagara motsawa daga jikin Hajiyarmu, ta gagara yarda cewa wai na auri Abba, innalillahi wa inna ilaihi rajiun, me zata kira hakan, cin amana ko kuma me? Ta gagara gane a wani point zata sanya wanna matsala. Mun sha bakar wahala kafin mu samu Hajiya ta kula mu, ta ce idan ina son ta sake mun magana sai na kira Abba yanzun nan ya zo. Jikina na rawa na doka mashi kira, bugu ɗaya ya katse ya kirani. Ina kuka kawai na ce ka zo Hajiya na nemanka, ina faɗin hakan na katse kiran. Do bai ma bar gidanmu ba, domin yasan ba zuwan daɗi muka yi ba, yana zaune cikin motansa. Fitowa yai ya shigo cikin parlo bayan ya ce da Hassan ya jirasa. Ai brothers ɗina tamkar zasu rufe Abba da duka, dan dai kawai a tsaye ya fisu cika da cika ido ne, ga kwarjinin bala'i, mu dukka gidanmu sirara ne, shi ma Abba bai da kiɓa amma yana da cika ido sosai kuma ya fi brothers ɗina cika, ga shi ɗan kwallo sai da motsa jiki...... Kwarjininsa yasa basu mashi duka bama, amma haushinsa da suke ji baki ba zai faɗu ba. Ya tsuggunna yana ɗagawa iyayena gaisuwa, daga daddy har Hajiyarmu babu wanda ya amsa mashi. Sai dai muka ji muryan daddynmu na cewa. "Ka sakar mun ƴata yanzu, kuma ka shirya haɗuwarmu a kotu". Ko kaɗan Abba bai ga alamar sassauci a tattare da su ba bare har ya nemi afuwa, bashi da mafita, ya yi ƙoƙarin basu hakuri, amma suka dakatar da shi, suka ce in dai ba kalmar saki zai furta mun ba, kada ya kuskura yai magana a nan....... Ya yi iya yinsa dan su famincemu, amma sunƙi, cikin kuka nima na ce. "Abba ka sakeni, mahaifiyata ta ce ba zata sake mun magana, da na roketa shi ne ta bada rabuwar aurenmu a matsayin sharaɗin da zai sanya ta dawo yi mun magana, na tabbata ba zaka so fushi na iyaye ya hau kaina ba, please ka sauwaƙe mun ka ji?". Kansa a ƙasa ya ɗan jinjina mun kai, ya ɗago muka haɗa ido, idanunsa sun yi jajir tamkar wuta, ganin idanunsa ba ƙaramin tashin hankali ya jefani ba, sai na ji ya yi bala'in bani tausayi..... A hankali ya motsa lips ɗinsa da suka mashi bala'in nauyi, ya ji tamkar an ɗaure mashi su ya ce. "Ni Muhammad Abba Hussain, na sak........." labarin A'isha zai dinga zuwa maku labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi. FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥 LABARIN AISHA.🥹💔 PART 39 Follow my TikTok account 👇 https://www.tiktok.com/@princess_teema1?_r=1&_t=ZS-92AoEpYYmwP Follow my Channel account 👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S Kansa a ƙasa ya ɗan jinjina mun kai, ya ɗago muka haɗa ido, idanunsa sun yi jajir tamkar wuta, ganin idanunsa ba ƙaramin tashin hankali ya jefani ba, sai na ji ya yi bala'in bani tausayi..... A hankali ya motsa lips ɗinsa da suka mashi bala'in nauyi ya ce. "Ni Muhammad Hussain, na sak, na s........." Cike da tashin hankalin na katse shi da cewa. "Dakata, dakata". Ina faɗa ina fashewa da kuka. Duk parlon suka kai kallonsu kaina, wani irin kuka mai karfi ya kubce mun, cikin tsananin tashin hankali, jikina na tsananta kerma, ina jin tamkar idan Abba ya furta wannan kalma ya ɗauke mun numfashina ne gabaɗaya, ba zan iya rabuwa da shi ba yanzu. Ganin duk family ana kallona ne yasa ban san lokacin da na ce. "Ina...... Ina........ina cikin period ɗina...... shiyasa na dakatar da shi". Abba ya ɗago ya kalleni sosai, coz yasan karya nike yi, saboda yau da asuba ma na yi sallah, har cikin ransa ya ji cewa ba zai taɓa furta mun wannan kalma ba, domin yadda na tsaya dan shi, na yi karya domin cetar soyayyarmu, lallai shi ma zai tsaya mun. To kun san ba'a saki idan mace tana jinin al'ada, bai halatta ba, ko an yi saki a wannan lokacin sakin bai yiwu ba, tana nan a matsayin matarka, wannan shi ne yasa iyayena suka ce to ya je, idan na yi wankar tsarki sai ya zo ya sakeni. Ai suna faɗin hakan ya miƙe da sauri, tamkar zai tashi sama ya fice daga parlon. Yana fita nima na miƙe da gudu na isa gaban daddynmu, ina kuka ina bashi hakuri, ina faɗa mashi nasan na yi kuskure amma dan girman ALLAH su yafe mun. Abin yai wa iyayena matukar ciwo, amma sun furta sun yafe mun da sharaɗin idan Abba ya sakeni, duk da haka na ji daɗin da suka furta sun yafe mun. Ina ta kuka na karisa wajen babban yayana, shi ma na dinga bashi hakuri, da kyar ya hakura, ya rungumeni yana rarrashina, tun ina kuka ƙasa-ƙasa har na yi shiru sai shessheƙa da nike yi kawai. Sai da barci ta fara ɗaukata ne ya ce in je ɗakina in kwanta. Da sauri na miƙe na haura sama. Ina shiga na rufe kofa har da sanya key, sannan na haye gado, ina kunna wutar screen na wayata uban message da number Abba na fara cin karo da shi. Na farko ya ce. "Please my wife, ki daina wannan kukan, komai yai zafi maganinsa ALLAH, kukan ya fi komai ɗaga mun hankali, please ki bari kin ji"......... Ina ƙoƙarin karanta saƙo na biyu sai ga kiransa ya shigo wayar kamar yasan na bar parlo. Jikina na rawa na yi pick-up. Ina kara wayar a kunne ya sauke wani irin nannauyar ajiyar zuciya, a sanyayye ya ce. "Alhamdllh, Alhamdllh, Alhamdllh, ALLAH na gode maka, bani da abin da zan biyaki da shi face addu'a, you saved my life today my wife, da kin barni na furta wannan kalma da ban san taya zan iya fita daga cikin wannan parlo da kafafuna ba". Na ja dogon numfashi tare da saukewa a hankali, muryata har ta dashe, da kyar na iya cewa. "Abba ina sonka sosai, ban tashi sanin hakan ba sai da na tabbatar sakina zaka yi mu rabu har abada, ba zan iya rayuwa babu kai ba Abba, please ka sama mana mafita ka ji my honey?". Nisawa ya yi, yana zaune a cikin motarsa, ya gagara yin nisa da gidanmu, ya fita gidanmu amma bai bar unguwar ba, yai parking a gaban gidanmu kaɗan, ya kifa kansa a jikin steering motar yana jin tsananin zafi a ransa, ya rasa in da zai tsunduma rayuwansa ya ji sanyi. "In Sha ALLAH zan samo mana mafita, yanzu dai zan yi tafiya gobe idan ALLAH ya kaimu, jibi muna da wasa a Brazil, zan dawo next week, kafin nan zamu nemi mafita kin ji? Ki daina damuwa, ke ɗin tawa ce ni kaɗai"........ Na amsa da. "ALLAH ya tsare mun kai, zan yi barci yanzu, idan na tashi sai mu yi waya". ............ Ya amsa da. "Ki kwanta da sanin cewa ina tsanani sonki matata, ki kula mun da kanki da mutuncinki, zamu yi waya idan kin tashi". Na amsa da In Sha ALLAH, ya sumbaci wayansa da nufin ya bani sumbatar barci, na ce na gode, ya ce bai yarda ba lallai in sumbace shi nima, dole sai da na sumbacesa muka yi sallama. Na ajiye wayar na gyara kwanciyata, na rungume pillow a kirjina, ina tunanin yadda muka kwana daren jiya da shi, na shige jikinsa, yana ta shafani yana gaya mun kalamai masu daɗi, ya ce in bashi dama mu raya sunnah, na ce na yi alƙawarin idan muka dawo daga Nigeria zan bashi dama, ya amsa da tom shikenan, mun sha hira sosai daren jiya kafin in yi barci. Ina ta wannan tunani har barci yai awon gaba dani. Ban tashi farkawa ba sai around 8 na dare. Ai da gudu na diro ƙasan gadon, toilet na shiga, sai da na fara wanka, na wastsake, sannan na shirya na tada sallah, sai da na biya basussukan sallolin dake a kaina sannan na yi

Chapter 32 of 38