fa a jiki, bama abin da zaka ji, ba wani ɗanɗano face yawuna, to me ka ji a ciki?".
Ya ɗan lumshe idanunsa tare da buɗewa a kan fuskata dake cike da mamaki kafin ya ce. "Daɗi sosai, ya fi duk abincin da na taɓa ci daɗi, please ƙara mun"....... Hararansa nai ban sake yin magana ba, na cigaba da cin ɗanwakena.
Can ya ce. "Please ƙara mun ko ɗaya ne"......... Na ce. "Sai dai in baka mai yaji". Ya ɗan girgiza mun kai tare da cewa. "A'a ni dai ki tsotse yajin sai ki bani"...... Aikuwa naki yarda, ba yadda bai yi ba naki sake tsotse mashi, dole ya hakura ya kyaleni, dana gama ci na kira Hajiyarmu a waya, bayan mun gaisa sai na ce mata. "Hajiyarmu kin san me?". Hajiya ta ce a'a sai na faɗa.
Cike da farinciki na ce. "Hajiyarmu na haɗu da Abba a wannan kasar, ashe yana raye". Nan na fara bata labarin da ya bani na yadda aka yi ya rayu. A tunanina Hajiyarmu zata yi murna, sai naga ina, domin kuwa wani irin faɗa da ta fara yi sai da na ji duniya ya tsaya mun cak, ta ce ta tsani in sake magana kan dangin Abbie, bata son sake ji, kuma ba ruwana da Abba, a cikin faɗar tata har da cewa ta yi dole a canza mun ƙasa dan ma kada in sake tuna rayuwata ta baya.
Duk jikina yai sanyi, na dinga bata hakuri ina son faɗa mata Abba fa bashi da laifi, amma taƙi saurarara, shi dai Abba sai kallona yake yi baya jin me Hajiyarmu take faɗe, a haka muka yi sallama, ban faɗa mashi komai ba, na ƙaƙalo murmushin dole dan kada ya fahimci komai, daga nan na ce ya rakani ɗakin Zahra, ya miƙe ba tare da ya ci komai ba face tea, ya ɗauki wayansa muka wuce ɗakin Zahra.
Bayan mu gaisa da ita, sai na ce mata zamu je benenmu in ɗauki kayana zan dawo nan da zama, ta ce mun sai dai mu dawo tare, na ce to ai ba damuwa, mu je mu ɗauki kayanmu.
Ta tambayeni me alaƙata da Abba, na ce mata yayana ne, aikuwa ta dinga murna, ta ce mun wlh tana son shi, ai dama ta ce mun in bata yayana ta aura, dan haka ita taga miji, na ce mata to idan mun dawo ta same shi ta faɗa mashi, idan ya amince ni kam na bata goyan baya, ta dinga murna, muka fito na ce ya kaimu nu kwaso kayanmu.
Ya ce za'a je a kwaso mana mu zauna a gida, na ce a'a akwai abubuwan da bana son kowa ya gan mun su, dan haka da kaina zan je. Yai ƙasa da murya wajen cewa. "Abubuwan sirri ne?"......... Na gyaɗa mashi kai alamar e. Sai ya ce. "To bari in je da kaina in ɗauko maki su tun da ni sirrinki ne, ke ki zauna a gida".
Na ce. "A'a ni da kaina nike son zuwa". .... Ba yadda ya iya dole ya haƙura yasa aka kaimu benen, muka kwaso kayanmu muka dawo, shi bai bimu ba.
Intakaice maku haka na fara rayuwa a gidansa, a hankali shaƙuwa tana ta kara shiga tsakaninmu mai karfi, ina waya da Ibrahim kullum shi ma.
Yau yakama ranar Monday, tun safe muna breakfast mu uku a dining da Zahra, yanzu da ita muke cin abinci tun da ta dawo gidan, sai ƙoƙarin burge Abba take yi shi kam baya bi ta kanta. Yana bani kulawa sosai, amma Zahra bata damuwa sosai saboda na ce mata yayana ne, so ta ɗauka shakuwan wa da kanwa ne kawai.
Na kalli Abba cike da kulawa na ce. "Ina da baki daga Nigeria yau, please kasa a ɗauko mun su a airport, and ni zan shiga kitchen yanzu dan yi masu girki da kaina"..... Ya ɗan zare mun ido kafin ya amsa da. "Like wow, to angama ranki shi daɗe, muke kitchen ɗin in tayaki, amma su waye zasu zo? Ko su Hajiyarmu ne?".
Cikin zolaya na ce. "Matarka Safiyya"..... Ya ɗan yi one sided smile tare da cewa. "A'a sisterta Safiyya dai, ni kam matata tana nan daban"....... Na ce. "Kai, kai, kai, yaudararmu zaka yi? Safiyyar zaka bari ka kama wata?".
Ya miƙe game da cewa. "Tawan ki bari mana, zo mu je kitchen in tayaki aiki, amma ni dai Safiyya sister ɗita ce". Ganin on a serious note yai maganar ne yasa na miƙe, na cewa Zahra muna kitchen idan ta gama, ta ce okey.
Muna shiga na fara shiryawa Ibrahim daddaɗar girki, dan ya ce girkina yake son ci, na yi alƙawarin girka mashi da hannuna. Ina yi Abba na tayani, bai san waye zai zo ba, ya zaci da gaske Safiyya ɗin ce........ Ya kore kukan dake kitchen ɗin dukka ya ce gimbiya zata yi aiki dun su fita, ina dariya na ce bakinka ne gimbiyar ai.
Muna tsaka da aiki unexpected ina yanka albasa kan chopping board kawai wuƙar ta taɓa mun hannu. Na jefar da wuƙar ina faɗin wash, sarkin saurin kuka har na fara ruwan hawaye. Da sauri ya matso ya rike hannuna yana mun sannu, sai ya ce mu je ɗaki ya gyara mun yana A-Box. Na bi bayansa muka nufi bedroom ɗinsa. A gefen katafaren bed ɗinsa ya zaunar dani tare da ɗauko box ɗin, a natse ya fara fito da komai, ya kama hannuna ya fara gyarawa.
Na tsuke fuska ina cigaba da kuka, dama ga albasa ya shiga idona, sai hawayen suka kara yawa. Ya dinga rareashina, yasa hannu yana goge mun hawaye, can ƙasa ya ce. "Ki kwanta a nan kawai ki huta bari in ƙarisa maki girkin"...... Da sauri na ce. "A'a, bakin nan suna da muhimmi a wajena, bari in ƙarisa masu"........ Ya amsa da. "Okay mu je to bari in yanka maki duk wani abin da ya shafi wuƙa". Na amsa da okey.
Ya miƙe ya mayar da box ɗin, sai satar kallon bedroom ɗinsa nike yi, komai tsab, ga wani kamshi dake tashi. Muka koma kitchen a tare, ya karisa yanka mun albasar, sannan muka hau karisa aikin, Zahra ta zo ta samemu a wajen, ta sanya mana hannu.
Bayan mun kammala suka tayani na shirya a kitchen, sannan na shiga ɗaki dan yin wanka, na tsara wankana, yau atampa na sanya, 8 pieces sket and blouse, sket ɗin daga sama daidai da shape ɗina, amma ƙasa yai wani bala'in buɗewa wanda yasa na fito sosai, ga blouse ɗin daidai da ni, ya Salam, na yi kyau sosai. Na ɗanɗasa ɗaurin ɗankwalina mai kyau wanda ya kara fito da ɗan madaidaicin fuskata, na zuba turaruka tamkar ba gobe, a raina nima na matsu in ha Ibrahim.
Wayata na ɗauka na duba time 12:40, karfe 1 kuma jirgunsu zai sauƙa, da sauri na fito na nufo room na Abba, coz yanzu na fara gane gidan. Knocking na mashi, daga ciki ya ce shigo. Na tura kofar na shiga, yana kwance kan gado sai ga shi ya miƙe zaune yana kallona ya ce...............
labarin A'isha zai dinga zuwa maku labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi.
FATEEMA ZAHRA MUSA
A-K-A
QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥
LABARIN AISHA.🥹💔
PART 29
Wayata na ɗauka na duba time 12:40, karfe 1 kuma jirgunsu zai sauƙa, da sauri na fito na nufo room na Abba, coz yanzu na fara gane gidan. Knocking na mashi, daga ciki ya ce shigo. Na tura kofar na shiga, yana kwance kan gado sai ga shi ya miƙe zaune yana kallona, ya ce. "Like wow, tawan, na jima ban ga atampa ba, dama kuma ke kaɗai yake yi wa kyau a duniyar nan".
Na ɗan jujjuya fararen idanuna sama wanda ya sanya shi sauke ajiyar zuciya, ya haɗiyi yawun da ya sanya maƙogwaronsa harbawa sama kafin ta dawo. Bai sake yin magana ba, sai ma ya ɗauke kallonsa daga kaina, dan wani irin yanayi dake tsananin fusgansa.
A natse na ce. "Nawan zo mu je airport ɗin, saura 20 mins jirginsu ya sauƙa fa"...... Sai da ya ɗan yi gyaran murya saboda sarkewa da muryar tasa ta yi, intently ya zuro kyawawan kafafunsa kasan gadon, bai miƙe ba ya ce. "No, ba in da zaki je, bari in sanya a ɗaukosu"......... Na ɗan zare mashi ido game da cewa. "Why?"....... Ya ɗan mun kallon ƙasan ido tare da cewa. "Baki ga kin yi kyau sosai bane? Ko da ma baki yi kyau ba ni ba in da zaki je".
"Kai dai anyi rigimamme, sai rigima kamar mace, ko da yake dama namata kake, in ban da haka me na wani wai na yi kyau ba zan fita ba? Neman rigima kawai, in ruwan wani dani dan na fita"....... Ya ɗago idanunsa a kaina, ya watsa mun wani irin kallon da ya zanya na ji wani irin spark tun daga tsakiyar kaina har tafin kafata, a hankali ya motsa lips ɗinsa wajen cewa. "Awwww, dama kin san in kika fita wasu ne zasu kalleki kenan?".
Na jinjina kai ina faɗin. "E, amma a ganinka ne hakan, ni a nawa ganin ba wanda zai ɗaga ido ya kalleni, ko da yake ma ƴan kasar nan ma sun iya saka ido, sun sha tareni"........ Ya ɗan ciza laɓɓansa da ɗan karfi coz he wish yana da cikakke dama a kaina, da yanzu ya koya mun hankali, especially wannan ɗan bakin nawa da bana saka mashi linzami wajen magana, nike faɗin abin da nike so.
Ganin ya yi shiru bai amsani bane yasa na ce. "Please ka masu magana su je su ɗaukosu ko kuma mu je tare"......... Ya ɗan furzar da iska mai ɗumi daga bakinsa, da kallon ƙasan ido ya saci kallon hips ɗina da suke tamkar zasu fasa sket ɗin jikina, barema yanzu da hankalina ya ƙara kwanciya, albarkatun jikina duk sun fara dawowa, abin ba'a magana.
Wani irin musulmin ajiyar zuciya ya sauke tare da jawo wayansa, ya fara pressing yana cigaba da kallon hips ɗina. Slowly ya ɗan lumshe idanunsa, In his mind, he started imagining a romantic moment, wai ya miƙa mun hannunsa, ba musu na zo jikinsa, he started romancing me like crazy. Oh God, ya ɗan datse idanunsa.
Sanyayyar muryata ta katse mashi tunaninsa, na ce. "Ka yi magana mana". Na faɗa a shagwaɓe sosai tamkar zan yi kuka..... Ya wurga mun wani irin Musulmin sahihin kallo mai narka zuciya wanda sai da yasa ƙararrawar zuciyata ta buga, sannan ya ce. "Na faɗa masu". Da kyar yai maganar, muryansa tamkar wanda yake cikin maye.
Na saki murmushi game da cewa. "Thank you so much my lovely bro"........ "Zo ki zauna mu yi hira". Ya faɗa yana nuna mun gefen gadonsa. Na maƙe mashi kafaɗa tare da cewa. "No, zan je in shirya tarban ɓakina"........ Kai ya ɗan jinjina game da cewa. "To zo in nuna maki wani abin". Ya faɗa yana jawo wayansa.
Na matsa kusa da shi, ya nuna mun gefensa, na zauna ina ɗan kame jikina. In a cool way sosai ya ce. "Kalli wannan hoton"........ Ya fitar game da miƙa mun, na karɓi wayar ina kallo. Hotona ne tun ban wuci 17 years ba, ko daga ina ya samo hoton? Lokacin ina da tsananin kyau fiye da a yanzu.......... Da sauri na ɗago da nufin in mashi magana, saura kaɗan fuskokinmu su haɗe da juna. Dan ya ɗan matsoni sosai, tamkar zai sumbaceni a kumatu.
Muka zubawa juna ido, a zahiri ba shi nike kallo ba, tuni na shiga duniyar tinani, ina jin wani abu a zuciyata dama gangan jikina gabaɗaya......... Shi kuwa ba wanda ya iya fahimtar me yake ji, sai shi da ya tsareni da idanu, musamman ɗan bakina. Mun ɗauki mintuna biyu a haka, ƙarar call da ya shigo wayansa ne yasa muka farga, da sauri muka janye kallonmu daga kan juna, ya kai hannunsa ya karɓi wayar yana wani jan dogon numfashi.
Pick-up na call ɗin yai tare da cewa. "Hello"....... Ban ji me aka ce a other hand ɗin ba sai na ga ya dawo da kallonsa a kaina. "Tawan, dama maza ne zasu zo?"...... Na gyaɗa mashi kai. Ya mai da wayar kunnensa game da cewa. "Yeah, ku ɗaukosu".... Daga nan ya katse kiran.
Na yunkura zan miƙe ya riko hannuna, a natse ya ce. "Su waye ne suke zuwa?".....
"Kai wai kai ɗan jarida ne? Name zaka titsiyeni da tambaya?".......... "Tawan, ki bar wasa, su waye ne suke zuwa?"........ Na buge hannunsa da ya rikeni, cikin masifa na ce. "Kai ko gadina aka baka sai haka, ka bari mana idan suka zo zaka gani, kada ka takura mun". Na faɗa ina ƙoƙarin barin wajen.
Ai cikin zafa ya damko waist ɗina ba tare da yasan ya damko ɗin ba, ya jawoni baya da karfi, gabaɗaya na tafi jikinsa na zauna kan laps ɗinsa, cikin faɗa ya ce. "Su waye suke zuwa? Samari ne ba? Me haɗinki da su? Su waye su?". Tsabar masifa bai ma san ya janyoni jikinsa ba, duk ya birkice tamkar zai kai mun duka. ........ Nan da nan na haɗe rai, na yunkura zan tashi ina faɗin. "Ba zan faɗa ba tun da babu ruwanka da baƙina".
Ƙanƙameni ya yi, ya mayar dani na zauna sosai a kan cinyarsa, ya kara tamke fuska tare da cewa. "Zaki faɗa mun ne ko sai ranki ya ɓaci yanzun nan?!". Babu wasa a tattare da shi yai maganar. Na ce. "Ba zan faɗa ba, kaga ni sakeni in tashi, idan suka zo koma suwaye ne zaka gani.........". Ban iya ƙarisar da maganar ba saboda wani irin capka da ya kaiwa wuyata, da marina ya so yi, but he controlled his anger, sai ya sauke hannun nasa a kan wuyata.
Cikin faɗa ya ce. "Har kin isa ki kira wasu maza su kawo maki ziyara? Saboda me? Me alaƙar dake tsakaninku?!". Yana huci yai maganar, gabaɗaya ya canza lokaci guda, ya birkice tamkar ba shi ba.
Ganin yadda ya birkice ya fusata ba ƙaramin razanani yai ba, wani irin tsoronsa ne ya shigeni, cikin sanyin murya na ce. "Sorry nawan....... Am...... In..... Dama ....... Uncle ɗin Muhammad ne ya ce zai zo mu gaisa, shi ne fa"........ Ya ƙara haɗe rai game da cewa. "Waye shi? Kuma waye ya bashi izinin zuwa ganinki?".
Na ɗan rike hannunsa dake kan wuyata, idanuna sun cika tab da hawaye, da kyar na iya cewa. "Abba, zaka kasheni ne? Zafi fa nike ji, bana numfashi sosai". Ina kai karshen maganar hawaye suka fara bin kuncina...... Slowly ya zame hannunsa daga wuyar tawa, in a cool way sosai ya ce. "Sorry, ɓacin rai ne, amma a kan me wani zai zo wajenki? Waye ya bashi izini to? Dama kina tare da shi ko?"
Maganganunsa sun mugun bani mamaki, ban gane me yake nufi ba, kenan kada wani ya zo wajena? To saboda me? Idan zan yi aure ma sai kada in kula wani ne? Zuciyata ta bani cewa yana taya yayansa kishi ne, watau har yanzu yana tunanin zan iya komawa yayansa, hakan yasa na haɗe rai sosai, nasa karfi na kwace kaina tare da miƙewa, na tsaya baya da shi kafin in ce. "Ban taɓa zatan hakan daga gareka ba Abba, watau duk irin wahalar dana sha a rayuwa kana mun fatan sake komawa cikinta kenan? Ai na ɗauka ko wani ka gani yana mun fatar komawa gidan yayanka sai in da karfinka ya kare a kansa ba wai kai da kanka ka mun wannan fata har kake taya yayanka kishi ba! Ka bani kunya!". Ina kai karshen maganar na juya da gudu na nufi waje cikin fushi.
Da sauri ya miƙe ya biyoni yana ambatar sunana, ina, ban tsaya ba, kai tsaye harabar gidan na nufa, yana kwala mun kira nai mashi banza. A harabar gidan ya cin mun bayan na tsaya, yana ƙoƙarin yi mun magana na ce. "Dan ALLAH ka kyaleni, ka rabu dani Abba, na ɗauka kai masoyina ne ashe ba haka bane, shame on you!".
"Tawan, yanzu ko wani kika ji ya ce maki ni zan goyi bayan ki koma gidan wancan mushirikin zaki yarda? Ni fa, amma gaskiya ban yi tunanin baki mun farin sanin da zaki iya sanin me zan iya da wanda ba zan iya ba"........ Na yi shiru ban amsa shi ba, in a cool way sosai ya sake cewa. "Please muje ki koma ciki, bana son guards ɗin nan su dinga kallonki, mu koma sai ki mun duk faɗar da zaki mun koda ma duka ne".
Na juyo na hararesa. Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da matsawa kusa dani sosai. "Please ɗan yi smile mana tawan"....... Murmushi ne ya kubce mun, na fara kai mashi dukan wasa ina faɗin. "Ni kada ka sake kulani"........ "Kulaki ai ya zame mun wajibi kuma farillah"
Guards na gidan sai suka tsaya suna kallonmu cike da mamaki, coz basu taɓa kallonsa haka ba, sai suka hau tambayar kansu wai shin wacece ni da super hero yake wasa dani har haka? Wasu su ce shi ma ya fara bin matan banza kamar wasu sanannun ƴan kwallon kenan, har ya ajiye karuwan a gidansa.
Ni kam sai murmushi nike ina dukansa a damtsen hannu. A daidai lokacin motocin da suka ɗauko su Ibrahim suka kutso kai ciki katafaren harabar gidan. Dakatawa na yi da kaiwa Abba duka, na natsu game da kai kallona kan motocin, shi kam Abba ya tamke fuska tamau yana jiran ya ga wanene?.
Shi ma Ibrahim suka parking da sauri ya fito daga motar ganina tare da Abba, coz ya zaci ai na rabu da familyn Abbie kenan. Zazzaro idanu nai a kan Ibrahim ganinsa rike da Muhammad, ban san lokacin da na yunkura da gudu zan je in karɓi ɗana ba, ashe babban bazatan da zai kawo mun kenan, ya Salam, ban taɓa tunani ba, ya aka yi Hajiyarmu ta yarda da Ibrahim sosai har haka ne? Ta ɗauki ɗana ta bashi wanda ko Abbie uban ɗan ta hana shi ko ganin yaron, kai ya Salam.
Ina yunkurawa Abba ya rike hannuna tare da cewa. "Wannan ba shi ne muka haɗu a shopping ba?"....... Na amsa da. "Shi ne, nawan sakeni bari in karɓo Baban a hannunsa"......... Abba ya ce. "Tsaya a nan bari in karɓo maki shi".
A daidai lokacin Ibrahim ya iso in da muke tsaye, Abba ya ƙara tamke fuska tamau, ya haɗe gerar ƙasa da sama, sannan ya miƙa hannu zai karɓi Muhammad, Ibrahim ya ɗan ja baya alamar ba zai bashi shi ba yana ƙoƙarin miƙo mun shi. Abba ya shiga tsakaninmu wai ba zan sa hannu in karɓi Muhammad ba dan ma kada hannuna ya ɗan taɓa jikin Ibrahim, dan haka ya bashi yaron shi zai miƙa mun. Yau naga ikon GOD.
Ibrahim da ya san ba auren Abbie a kaina sai ya tamke fuska shi ma, a dake ya cewa Abba. "Kai kuma waye da zaka hanata karɓan ɗanta?"....... Abba na wani dallah mashi mugun kallo kafin ya ce. "Uban ɗan!!". Babbar magana.
Da farko na ɗauki abin wasa, sai da na ji suna musayar zafafan kalamai a tsakaninsu ne yasa na ce. "Me haka wai? Ku bari mana"...... Ibrahim ya ce. "A kan me zamu bari? Ina ruwansa dake yanzu tun da ba a gidansu kike ba? Me nasa da yake tambayata abin da ya kawoni wajenki?".
Abba ya ce. "Na tambaya, me ya kawoka wajenta? And me haɗinka da ɗana da zaka ɗaukesa?!". Ya faɗa tare da sanya hannu ya kwace Muhammad daga hannun Ibrahim ɗin.......... Muhammad kam da yake ya saba dasu dukka biyu, ko a jikinsa, dan jini ya furgesa wajen Abba.
A fusace Ibrahim ya ce. "Meyakawoni wajenta kake son sani? To matata ce, kuma na zo jaddada soyayyata ne a gareta!!". Yana huci ya faɗa........ Abba ya ce. "Wannan ne kuma ba'a haifi mutum ba, dama tun da muka haɗu da kai a shopping na san take-takenka, dan haka ina mai yi maka gargadi da babban murya da ka fita harkarta, ka gogeta a babin rayuwarka, idan ba haka ba zaka jawa kanka danasani a lokacin da ba zai maka amfani ba!".
Cikin faɗa na ce. "Abba, Abba me haka? Baƙona ne fa, a kan me zaka dinga mashi faɗa haka? Koma menene ai ni zaka yi wa faɗa ba shi ba tun da ni na gayyacesa, amma sai ka nemi zubar mun da mutunci?"....... Yana huci tamkar zai haɗiyi zuciyar, ya wani juyo ya kalleni har sai da na firgita. Babu wasa a tattare da shi ya ce. "Wuce cikin gida yanzun nan!". Cike da bada umarni ya faɗa.
Zan sake yin magana ya daka mun tsawa da karfi kan in wuce tun raina bai ɓaci ba..... Wani irin kuka mai karfi na ji ya zo mun, da gudu na juya na basu waje. Bayana suka bi da kallo, Ibrahim ya yunkura zai bi bayana Abba ya rike mashi wuyar riga da hannu ɗaya, cike da nuna isa da izza ya ce. "Aisha matata ce ni kaɗai, dan haka ina mai gargaɗanka da babban murya da ka fita harkarta kada ka jawa kanka wani wahala, tafi karfinka, ba sana'ar aurenka bace!".
Babbar magana, zazzare ido a kan fuskan Abba Ibrahim yai, sai kuma ya fashe da dariya na ɗan lokaci, sannan ya ce. "Kai baka ji kunya ba, yayanka ya saki mace kuma ka ce ita kake so? And baka jin kunyar irin wahalar da danginku suka bata ba, har kana da fuska tunkararta da sunan soyayya? Zaka iya? Zaka iya kallon fuskanta ka ce kana sonta? Zaka iya na ce?!". In a harsh way ya faɗa.
Abba ya saki one sided smile tare da gyara rikon da yai wa Muhammad, amma bai yi magana ba...... Ibrahim ya cigaba da cewa. "Kuna matsiyata, ƴaƴan talakawa, waɗan da abincin ci ya gagareku a danginku, har kake ikirarin Aisha tafi karfina? Kai Malam, idan zafin talauci ne yai maka yawa ka zo in baka aikin yi, amma ka farka daga mafarkin da kake yi na cewa Aisha matarka ce, domin Aisha tafi karfinka tafi karfin dukka danginku, na tabbata wannan ƙasar da ka zo ma Aisha ce ta biya maka kuɗin jirgi, dan na ji an ce a baya ita ta rike danginku!".
Ya ɗan nisa tare da cewa. "Aisha ba matar yara bane! Yaro ka kama kanka ka je ka nemi sana'a ko ta dago ce, ka tara kuɗi domin su ne mutunci, ni kaina da nike maka wannan magana ba dan kuɗin da nike da shi ba dangin Aisha ba zasu saurareni ba! Power of money ake gaya maka! A baya sun tsaneni, sun rabani da ita, amma yanzu sun ga ruwan kuɗi sun miƙa wuya! Saboda haka malam ka je ka nemi kuɗi kafin ka yi faɗa kan mace, Aisha tawace ni kaɗai, kuma zan iya ƙarar da duk abin da na mallaka saboda in mallaketa, ka rubuta ka ajiye wannan!". Ibrahim yana huci sosai ya kai karshen maganar.
Zame hannunsa daga riƙon da yai wa Ibrahim ɗin Abba ya yi, coz yanzu ya fahimci Ibrahim jahili ne sosai, in ba haka ba ba zai yi furucin cewa saboda yana da kuɗi ne dangin Aisha suka karɓesa ba, watau yanzu shi a tunaninsa kuɗinsa yasa su Hajiyarmu suke sonsa, lallai ba shakka idan ya bari Ibrahim ya aureni sai na shiga kunci fiye da wanda na shiga a baya, dan kuwa da alama yana da halin gorantawa mutane, coz ko ba jima ko ba daɗe zai mun gorin cewa iyayena sun ƙisa a farko, amma da ya yi kuɗi sun karɓesa wanda kuma ba haka bane, a farko rashin hankalinsa da ƙuruciya suka guda, iyayena basu da matsala in ma mai kuɗi ko talata, Hajiyarmu dai mai hankali kuma mai ilimin addini take so, daddynmu kuma ɗan boko yake so, amma kuma Ibrahim bai yi boko mai zurfi ba, iyakansa secondary school ya tsaya ashe.
Abba ya gano cewa tabbas idan ya bari Ibrahim ya aureni harta iyayensa da ƴan
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 24 Chapter of 38