Share this page
kyale mammy zan dawo da ita hanya, ka yi addu'a before kwanciya". Ya amsa da okey daddy, ya miƙe ya ɗauki tab ɗinsa ya wuce sama. Yana hayewa Abba ya jawo hannun nawa na faɗo jikinsa gabaɗaya, wani irin ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce. "Menene ake ta wannan faɗan? Wani laifi na yi ne?". Ban tanka shi ba, sai harara, kawai haushin kowa nike ji...... Ya ɗan sumbaci kumatuna kafin ya ce. "To idan ma ni na yi laifi sai a sauke a kan yarana ne? Me suka sani su? Laifin me ma na yi in bada hakuri?"...... Na turo baki, cikin tsiwa na ce. "Ɗanwake zaka mun na ce"......... Ya ɗan zuba mun ido na ƴan sekonni, sai kuma ya ce. "Tawan, anya kuwa ban zura kwallo a raga ba?". Like wow lai tamkayar. Dukan wasa na kai mashi a kirji ina faɗin. "Sai yanzu zaka san ka yi aika-aika ko?".... Da sauri ya rike hannun nawa da nike dukan nasa, ya kara matseni a jikinsa yana faɗin. "Da gaske? Are you sure?"......... Na gyaɗa mashi kai alamar I'm very sure. Ya Salam, cikin tsananin farinciki ya ɗaura hannunsa kan cikina, yana wani irin murmushi ya ce. "Yanzu a nan akwai jinina? Ɗana? Meyasa baki faɗa mun da wuri ba? Me kike so in baki? Me zan maki?". Duk a ruɗe yake magana, bakinsa yaki rufuwa saboda murmushi. Ina turo baki, na ɗan yatsina fuska kafin in ce. "Ni fa ɗanwake na ce ka mun"....... Ya ɗan ja hancina. "Masifaffiya kawai, dole in yi taka tsantsan da yarana kada ki dinga jibgan mun su, dama nasan laulayin cikinki da iya sakaki masifa, ko kallonki aka yi sai faɗa". "Ni wai zaka mun ɗanwaken ne ko ba zaka yi ba?". Cikin faɗa na faɗi, coz ni fa so nike kawai in ga ɗanwake ba in ji surutun shi ba. Ya sumbaci cheek ɗina. "Ɗanwake kai, yanzu ma kuwa". Ya faɗa tare da yunkurawa zai miƙe, sai kuma ya koma ya zauna tare da cewa. "Amma babyn nan nawa ba zai hanani morewa na ba ko?". A marairace ya faɗa. Ina hararansa ban amsa ba. Ya ce. "Ohh, sorry, wannan yaron masifarsa ta fi ta kowa, kai ko magana ba zaka bari ayi ba sai harara da tsiwa, to tashi mu je mu yi ɗanwaken kafin yaron nan ya fara kai duka". Dariya ya bani, na ɗan dara, ajiyar zuciya ya sauke ganin ya sanyani dariya. Ya miƙe dani a jikinsa, muka nufi sama, muna shiga kitchen ya goyani a bayansa, ya ɗebo flower, ya hau haɗa ɗanwake, na kwantar da kaina a bayansa ina kallon abin da yake yi. In less than 40 mins ya dafa mun ɗanwaken nan, ya kwashe, ya haɗa mun komai, sannan ya ɗauka muka je parlo. Na zauna na baje na hau ci tamkar wacce ta shekara bata ci ba, ya cire wayansa yana mun video yana tsonana ina masifa, wai zai ajiye tarihi. Sai da na cinye ɗanwaken nan tas ya rage guda ɗaya a plate ɗin ne na ɗago kai na kalle shi, sai na ce. "Zaka ci ne?". Na faɗa ina yatsina fuska. Dariya na so bashi sai ya ce. "To idan ma zan ci ina yake? Da alama wannan babyn nawa marowaci ne, irin wannan rowa haka?". Na harare shi kafin in ɗauki guda ɗayan da ya rage, na gutsira rabi na miƙo mashi rabin ina faɗin. "To ga shi, ni kada ka yi wa babyna sharri, bashi da wani rowa, kawai ya manta da kai ne"....... Dariya ne ya kama Abba, wai guda ɗayan ma sai da na gutsira zan bashi rabi. Sai ya ce. "Ni ya mun ya ji, ki tsotse mun ya ji sai ki bani". Ina hararansa na kai ɗanwaken bakina, na tsotse yajin na fitar mashi, ya karɓa, ya fara tauna a hankali kafin ya ce. "Na ci ɗanwaken nan ne kawai dan nasan in ban ci ba nan ma faɗa za'a mun"........ Na buɗe baki zan fara masifa sai ga amai, Abba yana zaune yana kallona, na hau tikar amaina babu kakkautawa, tamkar zan amayar da hanjin cikina, da Abba ya ga haka sai ya matso ya rikeni dan ya taimaka mun, sai da na amayar da ɗanwaken nan tas, gabaɗaya na galabaita na jigata. Ya jawoni jikinsa, yana ta faman ce mun sorry, ya kira masu aikin gidan su gyara parlon, sannan miƙe dani a jikinsa, muka wuce ɗaki, wanka ya mun ya taimaka mun na sanya kaya, sai sannu yake ce mun. Instead of in yi appreciating da abin da ya mun, sai na hau masifa, na ce dama ba da zuciya ɗaya ya bani ɗanwaken ba, ba dan son ransa ya girka mun ba, ai dama baya son in ci, da gangan ya ja na yi amai. Shi kam da yasan matsalar ciki ko a jikinsa bai damu ba, bawan ALLAH yasan laulayina, shi ya tayani yin laulayin cikinsu Hassan, ya zo ya tayani na Muhammad, ai yasan komai, sai ya dinga bani haƙuri, na ce ni sai ya sake mun wani ɗanwaken. Ya duba time 12:30 na dare, sai ya ce okey mu je kitchen ɗin ya mun, ba musu na bi shi ina haɗe rai. A wannan daren ya sake mun wani ɗanwaken, na ci kuma ban banshi ba kamar ɗazun, yanzu ko rabin ma bai samu ba, haka kuma ina gama ci na sake yin aman shi, Abba dai sai ido yake bina da shi, tamkar yadda muka sha wahalar cikin Muhammad tare haka ma yanzu muke shan wannan wahala na wannan cikin tare, a tare muke laulayin. Kome nike so biye mun yake yi, haka zai goyani a tsakar gida, duk wani wahalar laulayi tare muka sha shi, nai amai ya wanke, na ce abu gaza ya dafa, in tashe shi karfe ukun dare in ce danbu ko ɗanwake duk ya dafa, bai taɓa nuna gajiyawa ba, kullum fatan shi ALLAH ya fito mashi da babynsa jininsa lafiya. ------------------------ YA RABBI ka baiwa duk wata mace saliha mumina mijin aure irin Abba, duk macen da ta tsare mutuncinta ta kame kanta ya ALLAH ka bata mijin aure irin Abba ko ma fin shi, natsastsen mutum, kamili, mai hankali da sanin yakamata, ga kuɗi ga kuruciya uwa uba ga addini, ga tsantsar madarar kyau, mai yi mata soyayyar gaskiya, mai bata kulawa, bai sanyata farinciki, ALLAH gatanta shi ma ya zama gatanta, cikakken namiji gwarzo, ɗan halak wanda baya manta halacci. Ya rabbi duk macen dake gidan aure kuma ya ALLAH ka juya zuciyan mijinta ya zama irin Abba koma fin shi, waɗan da basu da aure ALLAH ka basu irin Abba, kanne, ƴaƴa, jikoki, ALLAH ka dubesu da idanun rahama, aure ya zama abin da ya zama yanzu, ALLAH ka dubemu, ka dubi kannenmu, yayyunmu, ƴan uwanmu, iyayenmu, ƴaƴanmu da jikoki ya rabbi, duk wata salihar mace mai fatan samun irin Abba ko fin shi ta ce Amin. ---------------------- Cikina yana da watanni shidda a duniya amma haka Abba yake ɗaukata ni da cikin nawa dukka, ga cikin ya yi ƙato sosai, Abba baya son barina in zauna shiru, ya dinga sanyani motsa jiki, yai ta sakani magana shi da yaran shi, su watsa ɗaki Abba ya ce lallai sai na gyara, in gyara kuma su sake watsawa, wai duk cikin motsa jikine, dan baya son in sha wahalar haihuwa, duk wani kayan zaƙi Abba ya hanani sha tun cikina na watanni huɗu a duniya, ya hanani shan kayan sanyi ma, dan kada in haifo mashi yaro da mura ko in sha wahalar dogon naƙuda, dan sanyi ma illah ne, haka zaƙi ma babban ilmah ne, yana jawo jingirin naƙuda ayi ta dogon naƙuda. Ina amare kuke? To sai a kula, sanyi da zaki babban illah ne, dan wlh zaƙi mugun jawo jinkirin haihu dogon naƙuda yake yi, ba zaki haihu ba sai wannan zaki ya gama zuba labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danna like and share fisabilillahi. FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥 LABARIN AISHA.🥹💔 PART 45 Follow my TikTok account 👇 I4rdkfldhfkdhxjdh ni . https://www.tiktok.com/@princess_teema1?_r=1&_t=ZS-92AoEpYYmwP Follow my Channel account 👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S Sam Abba baya son barina in zauna bana motsa jiki, ya dinga takura mun kenan, ga sakani yawo, bana son fita amma sai ya fitar dani, kuma sai muna dawowa idan mun kusa da gida ya kashe motar ya ce mu ƙarisa da kafa, na rasa waye ya koya mashi wannan duk, duk abin mata ya iya shi. Muna rayuwar farinciki sosai, cikina yana da watanni bakwai a duniya na ce mashi zan koma gida in haihu a can, ya ce bai san wannan zance ba, shi dai a nan zamu haihu tare da shi ya tayani naƙuda, in faɗi duk wanda nike son gani a gida zai sanya a kawo mun shi nan. Na ce ni dai ban yarda ba, tun da muka yi aure cikin faranta ran juna muke, bamu taɓa faɗa ba sai yanzu, a kan komawa gida mun yi faɗa sosai. Abba ya tirje a kan matsayansa, nima na kafe, yai fushi dani, baya kulani sosai, amma yana sa ido a duk abin da nike yi, baya shiga harkata sosai, yana ta harkokin gaban shi, nima ina nawa. Wasa-wasa muka yi kwanaki uku muna fushi da juna. Abba dan ya kara hukuntani sosai ma sai ya bar mun ɗakinmu ya koma ɗakin yaransa, tare da su Muhammad yake kwana. Na damu sosai, dan yanzu ina jin daɗin kasancewa kusa da shi, na zauna na yi kuka sosai, duk yana ganina bai kulani ba, dan ya rantse ba zan koma gida haihuwa ba, saboda shi yanzu ba zai iya zaman sati biyu babu mace ba.......... A rana ta huɗu da faɗarmu na gagara barci, duk na damu, shi kansa ya gagara rintsawa, coz bai saba da irin wannan yanayin ba. Shiru na yi ina tunani, tabbas ni ce da laifi, ni ce ban kyauta ba, Abba yana mun duk abin da nike so, ban taɓa cewa abu ya ce a'a ba, ko bata mashi ba yana hakuri ya ɗauka, yana nuna mun kula fiye da tunani, yana damuwa da damuwata, meyasa yau kawai zai ce ga abin da yake so ni kuma in ki yarda? Bai taɓa ce mun ga abin da yake so yake umartata da yi mashi ba face wannan karo, meyasa zan bijire mashi? Gaskiya ina da laifi. Jiki ba kwari na sauko ƙasan gadon, na kunna wutar ɗakin kafin in tura kofa in fito waje. Kai tsaye ɗakinsu Muhammad na nufa, ina sanye da guntun wando zuwa tsakiyar cinyoyina, da kuma ƴar rigar da iya breast ɗina ta rufe mun, katon cikina a waje. A hankali na tura kofar ɗakinsu Muhammad, ina shiga na kunna wutar ɗakin. Ina kunnawa muka yi four eyes da shi, coz yana kwance bai yi barci ba, Muhammad ya kwantar da kansa a kan kirjin Abban, Hassan kuma yana gadonsa a kwance. Kallona sosai Abba ya yi kafin ya ce. "Lafiya?"....... Wai dan ma kada ya ga na damu da shi, kun gane irin abin nan namu na mata ai? Sai na haɗe rai ina wani babbasar da shi na ce. "Cikina ne yake mun ciwo sosai".......... Ya ɗan zare mun idanunsa manyan nan, sai ya sauke Muhammad daga jikinsa, ya miƙe zaune yana faɗin. "Me kika ci?". Ina hararansa wai dan ma ya kara sanin ni fa ban damu ba ko zamu shekara muna fushi da juna, na kara tamke fuska sosai, ina turo baki na ce. "Ni babu abin da na ci, ka zo ka dubani". ........ Ya sauƙo kasan gadon ya nufoni, na tsuke fuska irin zafi cikin yake mun, raina fes, dan nasan muna shiga ɗakina zamu shirya, kuma na yi alƙawarin ba zan sake ja in ja da maganansa ba. Hannuna ya kama game da cewa. "Faɗa mun abin da kika ci?"....... Na ƙara tsuke fuska, cikin tsiwa na ce. "Ai na ce maka ban ci komai ba ko? Shi ciwo ba zai zo ba sai bawa ya ci wani abin ne?". ...... Ya ce. "Sorry my light, mu je in kwantar dake in maki addu'a zai daina, juyin wata bakwai ne kawai". Ya faɗa yana jan hanuna kan mu tafi. Na make kafaɗa ina faɗin. "Ni ba zan iya tafiya ba kuma yanzu"....... "Ni ban san yaushe zaki daina rigima ba tawan". Ya faɗa game da rage tsawonsa ya ɗaukeni cak muka nufi waje, ya rufowa su Hassan kofa muka fice. Muna shiga ɗakinmu ya shifiɗeni a gado, ya hau yin addu'a yana tofa mun. Ina ta faman zuba mashi shagwaɓa yana biye mun. Ya ɗauki lokaci yana mun addu'a kafin yai zaman motsa mun cikina, ya kwantar mun dani a cinyansa yana shafa cikina a hankali, hakan yana taimakawa mai ciki sosai, yana ɗan shafawa yana ɗan jujjuya cikin a hankali sosai. Ba ƙaramin daɗin hakan nike ji ba, tuni na mance da wani faɗa, na kara lafewa a jikinsa ina jin daɗi tamkar ba zan mutu ba, ya jima yana mun hakan har barci ya fara ɗaukata, sannan ya ce. "In bari haka ko in cigaba?". Na yi shiru ban tanka mashi ba, ya dawo da kallonsa fuskata, sai ya ga idanuna a lumshe, ya zaci barci nike yi. Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke tare da sunkuyowa ya mannna mun kiss a gaban goshi, a fili ya ce. "Ina sonki tamkar raina matar kirki, rigimammiya ta, kome kika yi kyau kike ƙarawa". A hankali yake lallaɓawa ya gyara mun kwanciya, ya duba time 1 ta yi, ya sauƙo ƙasan gadon ya shiga toilet, alwala ya ɗauro ya fito, tun ina jin shi yana sallah har na daina jin shi barci yai awon gaba dani, ban tashi farkawa ba sai asuba da na ji yana taɓani yana ambatar sunana. Gabaɗaya jikina ya mun mugun daɗi yau ɗin nan, saboda abubuwan da ya mun daren jiya, dan haka garau ɗina na miƙe yau, na miƙe na nufi toilet, shi ma ya miƙe ya cire jallabiyar jikinsa dan daga masallaci ga dawo, ya shinfiɗa mun dadduma ya kuma ajiye mun hijab kafin in fito, ya koma kan gado ya kwanta. Ina fitowa na tada sallah. Bayan na idar nai zaman askar, ina kammalawa na haye gado na koma jikin mijina na kwanta, ya rungume sosai muka hau barci. Tun daga wannan rana bamu sake faɗa ba, soyayyarmu ta sake dawowa sabo fil, muna tattalin juna, muna kula da juna, muna kuma kaunar juna sosai....... Cikina watanni tara tun da ya shiga Abba bai barni na huta ba, kullum sai ya sanyani motsa jiki, tun da wannan ciki ya girma bai yarda ya yi nisa dani ko nan da can ba, iya kar nisan tsakaninmu shi ne masallaci, ya je yai sallah ya dawo. Cikina na da wata tara da kwanaki goma, yau da sassafe na tashi da naƙuda, wani irin azababben ciwon baya instead of ciwon ciki, da yake na saba ni naƙudar baya nike yi sai na gane haihuwar ce ta zo mun. Abba yana ɗakin su Muhammad yana shiryasu su tafi makaranta, na laluɓo wayata na kira wayansa, sai na ji wayan tana ringing a ɗakin, ashe bai fita da ita ba, duk da na haihu sau biyu amma ita naƙuda ita ce ciwon da ba'a taɓa sabawa da ita, ko ɗari kika taɓa haifa in ta zo dole ki ji sabon ciwon da baki taɓa jin irinsa ba, sam bashi da sabo, dan haka ji nike tamkar mutuwa zan yi. Ga shi kullum wata muna zuwa awo, sun ce sai nan da sati uku zan haihu, sai ga abu ya zo a lokacin da ban tsammata ba, ba yadda Abba bai yi ba kan mu je mu yi scanning, amma naki yarda, na ce na barwa UBANGIJI na kayansa har sai ya fito mun da shi duniya, dan haka kayan da muka saya duk na wanda maza da mata zasu iya sanyawa ne. Tun ina daurewa abu yana neman fin karfina, na fara salati ina kamo addu'oin da na manta ma da na iya su a duniya. Tun daga kan gado na zamo na sauƙa ƙasa saboda azaba, ban ma san na zamo ba, dan gani nike fa a ƙasan zan fi samu sauki. Na kwanta a ƙasa ina juyi. Can ya ɗan lafa mun, na yunkura zan miƙe ya sake dawowa gadan-gadan. A daidai lokacin Abba ya shigo ɗaukan wayansa da makullin motar da ya fitar zai tafi ya kai su Hassan school. Yana shigowa ya ganni a ƙasa ina juyi da gudu ya ƙariso yana tambayata lafiya, tamkar zan yi kuka nike ce mashi ya kaini asibiti. Ɗagoni ya yi ya zaunar dani yana ƙoƙarin sakeni ya ɗauko wayan shi na ƙanƙame shi ina faɗin ya kaini asibiti. Rikeni ya yi, cike da tausayawa ya ce. "Zan kira likita ne ta zo gida ta karɓi haihuwarki". Already yana da likitocin shi guda biyu, mace da namiji dake dubamu. Na ƙankame shi ban yi magana ba, sai kawai na hau zare wandon jikina, wani irin zufa na keto mun, gabaɗaya fuskata ta yi sharkaf da gumi. Na ƙara ƙankame shi, da karfi na yi nishi sai ga babynmu ya faɗo, ooooooo, Abba bai taɓa tunanin zai iya karɓar haihuwa ba fa, sai ga shi da jaririn da jikinsa duk jini a hannunsa ya ɗauka, gudun kada yaron ya kamu da sanyi ne yasa ya ɗauke shi a ƙasan da sauri, ya jawo bedsheet na gadonmu dake fari tas ya nannaɗe yaron a ciki, sai ya kwantar da shi a saman carpet na kusa da bakin gado, kusa dani ya kwantar da shi saboda mahaifar yaron bata biyo shi ba tana cikin cikina. Ya rike shoulder ɗina yana kallon fuskata cike da kulawa yake mun sannu, sannan ya yunkura zai miƙe ya dawo ta bayana kenan na sake ƙanƙame shi ina numfashi sama-sama, hakan yasa ya koma ya tsuggunna yana tambayata lafiya?. Haba ban iya amsa mashi ba, na sake fara sabon naƙuda. Haka Abba ya dinga taimaka mun, tare muka yi wannan naƙuda na biyun, duk na yagushe mashi jiki saboda azaban da nike ji, idan cikina ya murɗa, sai in damki fatan jikinsa da karfi nima. A haka muka yi fama har tsawon mintuna uku, sannan baby na biyun ma ya faɗo, mahaifan yaran a haɗe suke, hakan na nufin suna tsananin kama, su ake cewa ƴan mahaifa guda, da turanci ace identical twins. Sai dai still ko da na haifesu mahaifa bata faɗo ba tana cikina, abin da yai mugun ɗagawa Abba hankali kenan, ya ji tsoron abin da zai biyo baya, dan babban matsala ne rashin faɗowar mahaifa da wuri, idan ya jima a ciki mahaifar na dagargajewa a ciki ne, dan already yaran sun fita. Ta bayana Abba ya koma ya zauna, ya zuro hannayensa a kan cikina, a hankali ya fara motsa cikin nawa zuwa wajen mara. Na sha madarar mamakin ganin hakan da yake yi mun, coz ban yi tunanin ya iya yadda ake yi wa macen da mahaifarta ya makale a ciki yaki fitowa ba, a haihuwar Muhammad hakan ta faru dani, kuma haka Aunty Maryam ta mun, sai dai ita ta sanya ni na saka wani roba a baki tana murzamun cikina a hankali, to shi Abba ya aka yi ya iya?. Yana motsa mun cikina yana karanto addu'oin dan ALLAH ya sauƙaƙa mana, ya ji tsoron rasani sosai, ga wani irin ciwo da cikin nawa yake yi mun saboda rashin fitowar mahaifar, sannan ga babys ɗin nan da ya sanyasu cikin bedsheet dukkansu a hankali ɗaya ya fara kuka, yana fara kuka ɗayan ma ya fara, shi ne matsalar waɗan da mahaifarsu ke manne, suk abin da ɗaya ya yi to fa sai ɗayan ma ya yi, idan ɗaya ya fara kuka sai ɗaya ma ya fara ko da kuwa basa waje guda. Gabaɗaya suka rikita mun mijina bawan ALLAH, ya rasa da wanne zai ji, kukansu ne ko dai ni dake fama tamkar zan mutu mahaifa yaki fitowa?. Yadda kuka san Abban ne ya haihu, duk ya yi wanka da jini da dattin mahaifa dana haihuwa, ga shi Jessyn jikinsa fari ne tas, ta ko'ina ya yi wanka tamkar shi ya haihu, ko kaɗan bai nuna kyamar dattin haihuwar ba, ya rikeni yana cigaba da mun addu'a yana motsa cikina a hankali. Can har ya fara fidda ran mahaifan zai fito sai ga shi ya faɗo. Wani irin nannauyar ajiyar zuciya ya sauka, sai ya kwantar da kansa a gefen shoulder ɗina wajen wuyana, haba ai sai hawaye, sai yanzu ya samu damar kuka, kukan farinciki haɗe dana wahalar da ya sha, ya ƙankameni ta ciki-ciki yana sauke nannauyar numfashi, hawayensa na zuba a kan bayana, an wahala sosai. Wani irin tausayin mata ne ya kara shigansa sosai da sosai, irin wannana azaba duk a kan wannan halitta mai rauni, ALLAH sarki mata, Abba ya mun kuka sosai yana jin ba zai taɓa bari in shiga kuncin rayuwa ba muddin yana numfasawa a duniya. Nima jikina gabaɗaya ya saki, wani irin barci na fisgata. After 3 mins ya farga da kuka babys ɗin, da sauri ya sakeni ya miƙe yana faman goge hawayensa, cikin toilet ya shiga, jim kaɗan ya fito game da ɗaukar wayansa, cike da kula da tausayawa ya ce. "Muje in kaiki ki gasa jikinki da ruwan zafi bari in kira likita ta zo ta duba yaran nan sai a masu wanka". Na ɗago idanuna da suka yi kumburin wahala da barcin da na fara ina kallonsa, ban yi magana ba, ya kira number likitan nasa, tana ɗauka ya faɗa mata halin da ake ciki, ta ce gata nan zuwa. Ya ajiye wayar ya dawo gareni, cak ya ɗaukeni sai cikin toilet, ruwa mai zafi ya haɗa mun, haka ya tsundumani cikin jacuzzin nan, ruwan na cike tab. Ai wani irin daɗi na ji, na saki jikina cikin ruwan har da jingina da jikin jacuzzin. Juyawa ya yi ya fito zuwa ɗaki yana ce mun yana zuwa. Yana fitowa ya hau gyaran wajen da jinina ya malala har ƙasan side sofa. Bawan ALLAHN nan sai da ya gyare ko'ina tsab, ya zuba kayan kamshi, ya wanke wajen jinin tas, ya yanke mahaifar daga jikin cibin yaran, sannan ya ɗauka ya sanya a cikin leda, sai ya tuna lokacin da na haifi Muhammad aka bashi mahaifar wai ya je ya binne dan Abbie baya nan, wancan karon an bashi ya binne a matsayin shi na ƙanin Abbie, wannan karon kuma zai je ya binne a matsayin shi na uban yaran, ALLAHU AKBAR. Ya sanya a leda ya fita da shi zuwa wajen flowers na gidan, ya samu wuƙa ya haƙa rami mai zurfi ya binne, guards na gidan duk sai kallonsa suke yi, sun ga jikinsa duk jini ta ko'ina. Shi dai bai damu ba, yana gama binnewa sai ga Dr ta zo a motarta, ya tarbeta suka shigo cikin gida. Har ɗaki ya kaita, matar nan bata yarda a ɗakin na haihu ba, dan ya gyare ko'ina sai kamshin dake fashi, ta ga ko'ina tsab-tsab. Shi kam ya barta da mamakinta ya wuce wajena a toilet, ya sameni barci ya ɗaukeni cikin ruwa, bude ruwan ta fita ya yi, ya ƙara ɗauraye mun jiki, ya bani bathrobe ɗinsa dan in sanya, na gagara ko motsa hannuna, sai da ya sanya mun, ban iya ko motsawa ba saboda barci, wahala da gajiya, hakan yasa ya ɗaukeni. Na ce mashi zan gyara jikina ya bani always and pant, ba musu ya ɗauko mun daga cikin drawers na toilet ɗin. Ya bani na sanya, kafin ya taimaka mun na fito, a kan gado ya zaunar dani, haba ai sai kwanciya, na kwanta na cigaba da barcin wahalata, ya ja bargo ya rufeni sannan ya koma wajen Dr. Ta yankewa yaran cibiya daidai ta ɗan kame bakin ragowar, tana ƙoƙarin shiryasu, sai a lokacin ma ya san cewa mace da namiji muka haifa, shi da ya ɗauka duk maza ne. A take a wajen nai wa namijin huɗuba da sunan Hussain, watau

Chapter 37 of 38