kaɗan ba, na rasa waye ya faɗawa Hajiya halin da nike ciki da dangin mijina, coz ban faɗa mata abin da dangin nasa suke mun ba, babban yayana kawai na faɗawa, amma ya aka yi ta sani? Na so ace Safiyya ta samu Abba, yaron kirki, amma ina mata fatan samunsa har yanzu....... Haka yai kwanaki biyu a Kaduna a gidansu kafin ya dawo, a ranar da ya dawo bamu haɗu ba dan cikin dare ya dawo.
Washegarin ranar Safiyya ta kirani cikin tsananin damuwa, ta ce mun tana ta kiran Abba baya ɗauka, shi ne yasa taki furta mashi tana son shi da wuri, ga shi ranar da ya zo ta faɗa mashi tana son shi har ya fara juya mata baya. Nan na fahimci Hajiya bata faɗa mata komai ba, an barta tana murnar Hajiya da Abba sun gana shikenan zata mallaki Abba, bata san nan Hajiya ta rabasu ba, shi kuwa yana ganin kiran Safiyyar, amma ya yi wa Hajiya alƙawarin zai rabu da ita shiyasa baya ɗaukar kiranta, and yana jin nauyin yai blocking ɗinta, ace kamar kanwata yai blocking, wannan nauyin yasa ya barta kawai bai yi blocking ɗin ba.
Ta mashi saƙo a WhatsApp har ta gaji, tun jiya take ta fama, amma yaki dubawa, wlh Safiyya ta kamu da son shi sosai, ta dinga kuka da bai ɗauka ba. Rarrashinta na yi game da faɗa mata zan yi magana da shi, idan ma laifi ta mashi zai faɗa mun sai in faɗa mata ta gyara, ta ce mun Aunty ki faɗa mashi wlh ina son shi sosai, dan ALLAH kada ya walaƙantani.
Na jinjina kai kawai ina tunanin ko dai in faɗawa daddynmu sai ayi maza a masu auren tun da tana son shi shima yana sonta? To amma idan na faɗawa daddy Hajiya ta gano ni na faɗa mashi ta yi fushi dani fa? Nan ma na sake shiga damuwa sosai.
Haka na fito na shirya mana breakfast, ba mu haɗu da Abba har can yamma, na ga shiru-shiru bai fito ba, sai na shiga room ɗinsa dan dubasa, na samesa kwance lulluɓe da bargo, zazzaɓi mai zafi ya rufesa. Cikin tashin hankali na fara kiran sunansa, na yaye bargon, ganin daga shi sai short a jikinsa yasa nai saurin mayar mashi da bargo, na fito na nufi part na Zainab dan duba yayansa ko yana nan, dan a lokacin yamma ta yi sosai.
Na kuwa yi sa'a Abbie yana nan, haka ya zo ya dubasa, ya ɗaukesa sai asibiti, sai da Abba yai kwanaki biyu a asibitin, ya sha karin ruwa sannan aka sallamemu........ Rayuwarmu haka ta yi ta tafiya da daɗi babu daɗi. Babu abin da ya canza a rayuwar Abbie sai ma abin da yai gaba, Zainab kuma a lokacin da shinkafar gararta na aure ya kare sai Abbie ya dawo bata 1k na cefene har da sayan abin da zata dafa ma'ana shinkafa ko taliya, ya dawo bata 1k instead of 500 da yake bata lokacin da akwai shinkafa. Kullum cikin faɗa suke da ita kan abincin da zata ci, wlh Abbie yana da kuɗi, badawa ne kawai ba zai yi ba.
Da Zainab ta haɗa shi da su Mama ta mashi faɗa ya ce shi bashi da shi ne. Haka ta cigaba da hakuri tana danasanin aurensa. Watarana kawai ya bijiro mata da batun ta bashi motar ɗeban yashin da babanta ya mutu ya bar mata gado ya sayar da motar ya zuba kuɗin a kasuwa, idan ALLAH ya buɗa ya samu riba sai ya ninka mata kuɗinta sau biyu ya bata. Sai a lokacin na fahimci meyasa Abbie ya auri Zainab, babbar magana, dama domin ya cinye mata dukiyar gadonta ne, e kam akwai case kuwa!...... Jama'a ku ce ya Salam! Su sodangi manya.
Ita kuwa bata san halinsa ba, ta kira ƴar uwarta dama su biyu ne mata, sannan suka kira Mahaifiyarsu, mamarsu ta aminta, ta ce mijinki ne ki rufa mashi asiri, do Zainab ta ce mata bashi da shi, ga shi ba mai taimaka mashi, sai Maman ta ce ko dan ki zama na gaban goshinsa a gaban kishiya ki bashi, a tunaninsu su bashi zai fi son Zainab sai a mun walaƙanci. Aikuwa aka kimkimi mota ringiɗi-ringiɗi aka kai kasuwa. Irin manyan rokoki na ɗeban yashin nan ne, guda uku babansu yake da shi, yana ɗeban yashi da su itacen bamboo da shi, aikuwa Zainab ta ci gadon ɗaya, ƴar uwarta ma ta ci gadon ɗaya, ɗayan kuma ya shiga cikin gadon iyaye.
Aikuwa aka sai da motar nan 25M, Zainab ta ɗauki kuɗin dukka ya baiwa bawan ALLAHN nan, ya karɓe su yana ta zuba mata albarka, har da cewa dama ta ƙasan kafarsa zata shiga aljanna to yanzu ya ɗaga ta shige dama ita ƴar aljanna ce. Ni kam naga bariki ai, ina daga gefe ina shan kallo nida uncle daddynsu Hassan.
(Kai jama'a ku ce Queen Of Surprise taku ta amana, su sodangi manya, wai zata zama na gaban goshin Abbie, mu faɗa mata gaskiya ko mu bari duniya ta faɗa mata?)
A wannan rana da ta bashi kuɗin yai mata cefene enough, komai ya saya mata, shinkafa buhu biyu da duk abin da zata buƙata. Wlh ko tsinke bai saya mun ba, duk abin da suke yi ina jinsu, ban damu ba, dan ba yau ya saba rashin saya mana abu ba.
Haka muka cigaba da rayuwa a wannan gida, Zainab ta kara zama ƴar gaban goshinsa dai kamar yadda suka hara, sai wani yanga take mun dan tana ganin yanzu yana mata abin da take so, tana ji da ta bashi kuɗi.
Haka muka tura ina jurewa har ya kai watanni uku a ɗakin Zainab, saura wata ɗaya ya dawo ɓangarena a alƙawarinmu, aikuwa na ɗauki hutu na tafi Kaduna na bar Abba dasu Hassan saboda school, na koma gida na yi gyara mai rai da lafiya, a lokacin na cire Muhammad a nono, yana da watanni 15 kenan a duniya, ina zuwa Kaduna na yayesa, na sha maganin gyara, aka mun gyaran jiki sosai, na gyara ciki da waje sosai. Na murje na yi kyau, na ƙara zama mace, ga shi a gida nike na ƙara ƙiba daidai Masha ALLAH, na sha maganin gyaran breast da suka hana breast na raguwa bayan yaye Muhammad, suka tsaya a cike fam sosai, maganin kamar ya daskarar da ruwan nonon ne a ciki koma yaya ni dai Hajiyarmu ta bani, dama ta ce idan zan yi yaye in kawo mata Muhammad zata bani wani kyauta na larabawa, shi ne ta gyara mun breast ɗina sosai, suka ƙara girma amma ba sosai ba, har yanzu dai ƴan daidai da jikina suke, sun cicciko ne suka kara kyau suna wani ɗaukar hankali.
Tsawon sati uku na kwashe Aunty Maryam tana mun gyaran jiki na larabawa, skin ɗina ko na jariri albarka, Aunty Maryam ta zugani wai mu je asibiti a mun ɗinki dan in ƙara haɗewa, Hajiyarmu bata sani ba na bi shawarin Aunty Maryam, muka je aka mun kuwa, daga ciki har waje, mun kashe kuɗi sosai, Yaya ne ya biya ba tare da ya san kuɗin me ya biya b, amma na sha azaba ba karya, sai dai kuma an dawo da martaba, gyara da wahala sosai amma na gyaru matuƙa. Kullum muna waya da Abba, amma abin mamaki har yau Abba bai faɗa mun abin da Hajiyarmu ta ce mashi ba, ya kyaleni a kan suna tare da Safiyya har yanzu, ita kuwa Safiyya Hajiya ta zaunar da ita ta ja mata kunne sosai a kansa, dan dole Safiyya ta hakura ta daina kiransa ba dan ta so ba, amma kullum sai ta ɓuya ta yi kuka a kansa.
Wankan turare ma sai da na ɗauki kwanaki bakwai na satin da zan dawo ina yi, kamshin turaren hajiya da Abba baya so ya kama jikina sosai, ko ban saka shi ba fatana ne yake fitar da wani musulmin kamshin, har bakina ban bari ba, na je asibiti aka mun wankin hakwara, babu abin da ban gyara ba a jikina, na dinga zaman ruwan zafi na ɗinkin da aka mun har na warke, sai da na yi wata curr a Kaduna. Amma na je Abuja mun duba gini ni da Yaya, komai yana tafiya daidai, abubuwan ma sun yi nisa, har gini ya kai linta dukka biyu, an yi su rufin an kuma fara pilasta.
Bayan na cika wata guda a Kd sannan na haɗa kayana na fara shirin dawowa Kano, Hajiya ta ce zan bar mata Muhammad a nan sai ya yi wayau in zai shiga makaranta sai a maido mun da shi. Na faɗawa Abbie ya ce ba damuwa. Na shirya ranar wata jummaa driver ɗin hajiyarmu ya ɗaukoni zai dawo dani gida......... Karfe 4 na yamma muka dira garin Kano, kai tsaye gida ya kaini. Ina sanye da katon hijab har ƙasa a jikina, dan bana son kowa ya ga gyaran da na yi face wanda na yi dominsa watau mijina, ban so Zainab ma ta gani.
Lokacin da muka shigo gida tana harabar gidan kuwa, ta wani matse cikin ƙananan kaya, ita da wata maƙociyarmu na ganta, na yi mamakin ganin maƙotanmu sun fara shigowa gidammu, dan nasan tsakanina da su gaisuwa idan mun haɗu a hanya, sai ga shi har sun fara shigowa. Aikuwa ina fitowa daga cikin mota na gyara nose mask na fuska dan ma kada Zainab ta ga skin ɗina. Wani harara Zainab ta fara bina da shi, na ɗauke kai ina taɓe baki, a raina na ce yarinya zaki gane baki da wayau, dan wlh lokacin karɓan mijina ya yi, na bari ne sai ya mai dake tsohuwa sannan in zo mashi a sabuwan al'amari in kwace martaban, in dawo da matsayina.
(Jama'a kun ji yadda ake kishi ta masu hankali, ba wai ki tsaya lokacin da yai aure kina haukar gyara da su shan magunguna ba, ai ki barsa ya gama ragargaza amaryar ya mai da ita sai sorry, ki tarawa ƴar ƙaniya wahala, karki karɓa mata shi, ki barta da shi na ɗan lokaci, ki koma gefe ki basu waje, sai ya tsufar da komai nata sannan ki haɗo naki gyaran na ban mamaki dan ki dawo da matsayinki, ya mance cewa ita ce amarya ya ɗauka kece, ya haɗe maki matsayinta da naki duk, ki gigita shi ki gwada mata da da gasken uwar gidan ran gida kike, kece da gidan! Amma yana zumuɗin amanarya kina sai kun je daidai da ita, ai zub da kai ne, ɗan basu waje daga baya ki dawo ki kwace kayanki, a lokacin tana fama da laulayin ciki ma, WANNAN KARATU NASAN BA ZAI YI WA AMARE DAƊI BA🌝 TO KU RUNGUMI SORRY, KARKU DAMU ZAMU HAƊE DAKU A WANI LABARIN.)
Driver ɗin Hajiyarmu ya sauko mun da akwatina, ya ce mun zai kai mun ciki na ce mashi a'a ya barshi. Ga mamakina sai naga maƙociyarmu na hararata tana mun kallon ƙasƙanci, ashe Zainab ta gama gaya masu Abbie baya sona, yanzu watansa huɗu a ɓangarenta bai leƙa nawa ɓangaren ba, zagi dai na cin mutunci da zubar da kima ta mun a wajensu yasa suke mun wani gani-gani yanzu.
Ko a jikina na ja akwatina zan wuce ciki Zainab ta ce. "Aisha, nasan baki da kayan abinci a ciki tun da an jima a gidan dattijo, idan kina buƙata sai in ɗeba maki ko kwano ɗaya ne ki fara amfani da shi kafin baby ya waiwayeki duk da cewa da kamar wuya ya waiwayeki ɗin ma".
Na juyo na kalleta, na mata kallon tsab nan na fahimci tana ma da ciki, a raina na ce good, haka nike ta fata dama, in dawo in sameki da ciki, zaki gane ALLAH da girma yake yarinya, ai mu kyanmu natural ne, baki haihu bama uban tunbi tamkar mai ciki wata tara bare an haihu, ai ina ga da zarar kin haihu kin daina saka ƙananan kaya kenan dan rufawa kanki asiri. Yarinya yanzu mai waje ta dawo kwace wajenta, dole mai tabarma ya naɗe, Abbie ai ni nike da shi, wait and see jooooooh.
A fili kuwa na ɗan yi murmushi kaɗan, na ja akwatina ban tanka mata ba, dan yanzu yadda nike jin kaina wlh na wuce kula irinta.
Side ɗina na wuce, a buɗe side ɗin yake, da alama wani daga cikin Fahad ko Abba suna nan. Na yi sallama na shigo, Fahad ya amsa mun sallamar tawa daga ɗakinsu. Ya fito yana mun sannu da dawowa, na amsa cikin mutunta juna sannan na wuce cikin ɗakina. Ai wanka na tsala bayan na gyare ɗakin, bai da na wani kura sosai, na gyare ko'ina na zuba turarukan da kan da na dawo dasu masu musulmin daɗi.
Bayan na yi wanka na sanya wandon jean da ya kamani sosai, sai crop-top da na sanya, wanda ya tsaya mun a cibiyata, shafaffen cikinsa a waje. Na nisa ina kallon kaina a mirror, ni kaina na san na haɗu, ga wani ƙunshi da na sha, watau ina mugun alfahari da wannan ɗan jikin nawa mai kyau da fasali, ɗan caras cas.
Na sanyo hijabi na fito zuwa kitchen saboda rigar da na sanya zuwa cibiya shiyasa na sanya hijabi dan kada su Abba su ganni, na nufi kitchen dan girkawa Habibi abinci. Ina dab zan shiga kitchen Abba ya shigo parlo bakinsa ɗauke da sallama, da sauri ya ja baya yana ɓoye hannayensa a bayansa. A bakin kofar parlon ya tsaya, duk yadda baya son mu haɗa ido sai da ya zuba mun ido yana kallona.
Na ɗan yi murmushi mai ƙayatarwa kafin in ce. "Nawan, lafiya ka tsaya a bakin kofa?"........ Da sauri ya ɗauke kallon daga kaina, can ƙasa ya ce. "Sannunki da dawowa, sauƙar yaushe?"........ Ina kallon kayan jikinsa da yake duk rubutu na amsa da. "Yanzu ba jimawa, ya naga jikinka duk rubutu ne?".
"Zan faɗa maki anjuma, yanzu dai jeki in da zaki je". Ya faɗa a matse da in tafi....... "Korata kake yi?"...... Ya girgiza mun kai alamar a'a bai yi magana ba, na wuce cikin kitchen dan na gano dalilinsa na cewa in wuce, kamshin turarena ne da ya taɓa ce mun baya so kwanaki, na rasa meyasa baya son turaren, sai na wucen.
Ya bi bayana da kallo har sai da na wuce ciki, sannan ya zo da sauri ya afka ɗakinsu har kamar zai faɗi, hannunsa rike da wata ƴar ƙaramar mage, ashe ita ya ɓoye a bayansa da kada in gani, coz yasan a duniya babu abin da nike tsananin tsoro sama da mage, kyankyaso, da ɓera, and ƙadangare, waɗan nan abubuwa idan suka taɓani wlh zan iya suma, shiyasa ashe ya ɓoye mun baya son in gani, yanzu ya je ya je ya sayo magen, ƴar ƙarama fara tas da ita, kyakkyawa mai yawan gashi a jiki.
Yana shiga ɗakin ya hau shirya kayansa, ashe gobe yana da tafiya a kungiyarsu ta kwallo, yau suka rubuta final exam shiyasa jikinsa yake duk rubutu, da ace yasan zai dawo ya sameni a gida ba zai shigo da magen ba, bai yi tsammanin zan dawo yau ba, a tunaninsa gobe zai wuce da magen shiyasa ya zo da ita tun da bana nan.
Ni kam na tsara girkina, na kammala na koma ɗaki nai sallar magrib da ishai, sannan na kara gyara kaina. Na ɗauki wayata na kira Abbie, a lokacin yana ɗakin Zainab tana zuba mashi barikanci, ta tuɓe a gabansa tana son jansa, dan bata son ya fita ya ce zai zo yi mun sannu da dawowa.
Yana ganin kirana ya ɗaga. Na ɗan shagwaɓe murya game da cewa. "Abbie ka zo cikina na ciwo, please ka yi sauri ina da magana, na dawo ina part ɗina". Ban jira amsarsa ba na kashe wayar, na tashi na cire hijabin jikina, na naɗe na kayar cikin wadrobe, sannan na ɗan kwanta a gadona, yau na shirya kwace mijina ko ta kan su Abba ban bi ba. Shi ma Abban kaman yana tsoron haɗuwa dani, dan ko da ya zo ɗeban abinci sai da ya leƙo ya ga bana parlo sannan ya fito da sauri ya ɗebi abincinsa ya koma ɗaki.
Abbie ya miƙe game da cewa Zainab bani da lafiya yana zuwa bari ya dubani. Ya ɗauki jallabiyansa ya zura a jikinsa ya fito. Ai yana saƙo kansa cikin ɗakina wani musulmin kamshi da ya bugi hancinsa sai da ya lumshe idanu, da sauri ya ƙariso ciki, ina kwance ina kallonsa, ai yana kallona take ya birkice, gadon gabaɗaya ya haye yana tambayata meyakefaruwa? Yaushe na dawo and me ya ja mun ciwon ciki?.
Ni kam na ce. "Matso in faɗa maka a kunne". Jikinsa har rawa yake ya matso, kamar ba lafiya ba ya dinga shaƙar kamshin wuyana lokacin da ya sunkuyo kaina, aikuwa na rungumesa, na shige jikinsa, can ƙasa na ce. "Abbie yanzu fa lokaci na ne, sodanginka ta cika 4 months ɗinta, yau rana ce, zaka bani rana ne ko kuwa zaka kai mata?".
Ai ban samu wannan amsa ba, tuni ya bani amsa a aikace. Aikuwa na gigita shi a wannan dare, ya dinga mun sambatu har da shirme, coz ko lokacin da aka kawo mashi sabuwar amarya bai yi haukar da ya mun yau ba, sai dai fa ni ma na ji a jikina ba kaɗan ba, na gane ALLAH da girma yake, saboda abubuwan da Aunty Maryam ta sakani ci da sha, ga na sake matsewa sosai saboda ɗinkin da aka mun, kuma wlh dama can ni irin matan nan ne waɗan da suke a matse kamar roba haka, a cikin mata ɗari da wuya ka samu 2 masu waɗan nan baiwar halitta, to ALLAH ya mun, ba je kuma na jajuɓowa kaiwa aiki wai ɗinki, nakuwa ga ɗinki, dan kuwa Abbie ya saba mun yadda ya so, bai san komai ya canza ba, ga shi ya yi kewata over, aikuwa ya bani a jikina wanda wlh ko daren farkona ban ji wannan azaba ba, coz wancan a hankali ya mun, wannan da, hmmmm, tun ina kuka har na hau turesa da iya karfina danaga zai iya kasheni bai san yana yi ba sai sambatu, na yi danasanin yin wasu gyararrakin, dan kuwa sai na sha jinya.
Abbie kuwa bai kyaleni ba sai da ya yi sau biyu a zuwa ɗaya kamar yadda ya saba dan bala'i, wlh ko tashi na gagara saboda wahala, na dinga kuka, yana neman sake komawa ruwa na ce babu wannan magana, ba wanda ya ce in gudu na nemi hanyar gudu, ban ma san lokacin da na fara ƙoƙarin miƙewa ba, dan na ga zai iya kasheni a banza bai san ya yi ba. Aikuwa ya damkeni, tamkar wani mayinwacin zaki, yadda kuka san an shekara goma ba'a haɗu da abin ba.
Na gatsa mashi cizo a hannu wanda razana da tsoron kada ya sake komawa yasa na mashi ba dan nasan na yi ba, aikuwa tuni ya dawo cikin hayyacinsa, ya rikeni yana mayar da numfashinta, ya fara shafa kirjina yana mun sambatun na fi kowa, wlh bai taɓa jin azababben daɗi irin na yau ba, duk ya birki ce.
Na saka mashi kuka ina faɗin ya sakeni in ba so yake yi ya kasheni ba. Cikin wani marayar murya yake rokona da in barshi ya kara ɗaya. Haba na tsananta kukana, jikina har rawa yake yi sosai da sosai, idanuna jajir kamar wuta har sun kumbura.
Ganin haka yasa ya rungumeni yana faɗin in yi hakuri ba zan sake ba sai anjuma. Watau bama sai gobe ba sai anjuma, na ce ba wanan magana. Na sake saka mashi kuka, yai zaman rarrashin da wlh tun da muka yi aure bai taɓa rarrashina haka ba, har da mun kiss yau. Na ce to ya haɗa mun ruwan zafin wanka, ya ce angama my Habibiya, ya sauƙo ƙasan bed ɗin ya mai da shorts ɗinsa ya shiga toilet.
Ya haɗa ruwa ya zo ya kamani muka shiga toilet ɗin, tsabar na sha azaba dakyar nike taka kafata, haka na yi wanka sosai na gasa gabana saboda zafin da yake mun, kai Abbie sai shirin ALLAH wlh.
Bayan na fito na sanya wasu kayan barci masu shara-shara, sai na ce ya gyara mana gadon, ya kuwa gyara kamar ba shi ba, wlh zaka zaci asiri na mashi, komai na ce ya ce to, har mamaki ya fara bani. Ya gama gyara gadon na ce mu je ya bani abinci a baki ya ce mun to. Muna fitowa parlo sai ga Hajiya sodangi ta shigo da wani shegen rigar barcinta zuwa gwiwa, wai ta zo ta shaƙa mun takaici.
Na wani kalleta na watsar game da ɗingisa kafata na zauna a kan kujera, ta wani watsa mun harara kafin ta ce. "Munafuka, ciwon karya dan ki samu attention na shi ko? Duk wannan makirci mun san shi"........ Ai ko kallon in da take ban yi ba bare in tankata, a raina na ce ai mu wlh mun wuce mu yi ciwon karya dan mu samu miji ya zo wajenmu ya bamu attention, ai da kansa zai zo ne, muna ya tafi ma yana ba zai je ko'ina ba, ya manne mana kamar chewing gum.
Ganin ban tankata bane yasa ta sake cewa. "Dama ai ba zaki yi magana ba, banziya mara zuciya kawai, ba'ayi dake kina manne da mutum"........ Still dai ban ɗago na kalleta ba bare, na baiwa banza ajiyarta.
Ta dawo da kallonta kan Abbie da yake ƙoƙarin karisowa in da nike, ta ce. "Baby mu je, tun ɗazun nike ta jiranka kaki dawowa".
Dan na gwada mata da banbanci yasa na ce. "Habibi ka ɗauko mana abincin mu ci a ƙasa saman carpet ɗin nan, ba zan iya zuwa dining ba, ya mun tsawo sosai"....... Ya amsa da. "Okey, ko dai a saya maki fruits ko wani abin mai ɗanɗano ne?"....... Na girgiza kai alamar a'a ban yi magana ba, wai dan ma Zainab ta san ina da class ɗina, ko shi Abbie ban wani cika yi mashi magana ba, kun gane irin basarwan nan ai, sai dai ta ga shi yake ta rawan kafa a kaina ni ban wani damun nan ba.
Haba ai na kunnota, ta ce. "Baby magana fa nike yi"........ Ya wani ɗaure fuska game da kallonta da kyau kafin ya ce. "Baki san cewa yau a ɗakinta nike bane? In ma baki sani ba to na faɗa maki, ki kama hanyarki ki wuce side ɗinki". Babu alamar wasa a tattare da shi ya faɗa.
Ni kam na ce. "Habibi yunwa zasu yi wa ƴan hanjina lahani fa, ni ka ɗauko mana abinci da wuri tun ban fara maka kuka ba". Na shagwaɓe fuska sosai. Wlh gaban sodangi sai faɗuwa yake yi tun da ta ɗaura idanunta a kaina, coz ita da take mace ma na yi mugun tafiya da imaninta, dan fa gyaran nan ya gyaru ne jama'a.
(In Sha ALLAH a karshen labarin zan rubuta maku duk kayan gyaran ingantattu da zaku haɗa a gida da kanku idan ban manta ba, yanzu akwai dalilin da yasa ha zan rubuta.)
Musamman yadda taga kirjina sun ciko suna tsaye kyam, ga rigar barcin ya ɗan fito da surata, duk Zainab hankalinta yai mugun tashi, especially skin ɗina dake ta wani musulmin kyalli, ya Salam.
Ta wani uban dallah mun harara kafin ta ce. "Ai dama tun da na ji kin je Kaduna nasan wlh ba zuwan banza ba, ashe kuwa haka ne, wajen malamin naki kika koma ya shawo maki kansa kenan? To wlh kin ɗebo ruwan dafa kanki"........... A wani irin slow na ɗago fararen idanuna ƙalƙal a...............
labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi.
FATEEMA ZAHRA MUSA
A-K-A
QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥
LABARIN AISHA.🥹💔
PART 19
Ta wani uban dallah mun harara kafin ta ce. "Ai dama tun da na ji kin je Kaduna nasan wlh ba zuwan banza ba, ashe kuwa haka ne, wajen malamin naki kika koma ya shawo maki kansa kenan?
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 14 Chapter of 38