mun mugun nauyi na yi a kan kyakkyawan fuskansa. Yana bina da wani irin kallo na tsantsar kauna ya ce. "Tashi mu je in maki wanka lokacin sallah na kurewa, karfe 6 ta kusa".......... Ɗan lumshe idanuna na yi, take na fara tuna abin da ya faru daren jiya, slowly na waro kallona a kansa.
"ALLAH ya maki albarka, ba zan taɓa mantawa da jiya ba a rayuwata". Ya faɗa yana kai hannunsa kan fuskata, ya shafa tare da manna mun sumbata a ɗan bakina da na ji ya mun bala'in nauyin buɗewa............ In a cool way ya sake cewa. "Kunyata da ake ji ya tafi ne ko dai sai na ƙara yin abin da na yi jiya zai tafi?".
Ni gabaɗaya ma mugun shakkarsa da tsoronsa nike ki, coz duk jaraba irin na Abbie bai taɓa mun rabin abin da Abba ya mun kiya ba, ya shigeni gabaɗaya har na ji tamkar zan mutu......... Ganin ban mashi magana bane yasa ya ce. "Okay bari in ƙara ko guda biyar ne dan ma in samu damar yi maki wanka da kyau".
Da sauri na ƙanƙame bargona, da kyar na ce. "Please my honey ka bari, yanzu ma zafi wajen yake mun sosai"........ Ya ɗan kashe mun ido ɗaya, yai ƙasa da murya wajen cewa. "Bari in duba mu gani"......... Da sauri na ce. "Please". Sai kuma na yi yunkurin fashe mashi da kuka. A natse ya ce. "Ni kada ki fara kukan nan ki mun asarar hawayena, na hakura zuwa anjuma, yanzu mu je in tayaki ki yi wanka".
Ina turo baki ban yi magana ba, ya kai hannu ya yaye bargon. Ɗan lumshe idanunsa ya yi in a romantic way, tamkar mai raɗa ya ce. "Light of my life and zan iya haƙura sai anjuma kuwa? Kinga jikinki kuwa?". Ya faɗa yana ɗaura hannunsa kan cinyata, sai kuma ya ce. "Ya Salam, ALLAH ban san wani irin godiya zan maka ba, UBANGIJI ka mun kyautar da ban isa kwatantashi da komai ba, ALLAH Nagode maka, Nagode, Nagode".
Ya dawo da kallonsa kaina. "Yanzu wanna kayan dukkan nawa ne my wife? Ni kaɗai?"........ Yunkurawa na yi na miƙe, jiki duk zafi yake mun, ban mashi magana ba na sauko da kafafuna kasan gadon ta side ɗin da yake. Ya kai hannunsa ya ɗan shafi kirjina yana cigaba da lumshe idanu. Ni tsoronsa ma nike ji yanzu, na yunkura zan miƙe ban ankara ba ya ɗaukeni cak sai cikin toilet cikin jacuzzin dake cike tap da ruwa mai zafi.
Still dai ban mashi magana ba, ya zare jallabiyar jikinsa ya ajiye a gefe, ko kunyar idona Abba bai ji ba ya zame shorts ɗin jikinsa, da sauri na ɗauke kallona daga kansa, ban san lokacin da ya shigo cikin ruwan ba. Ya dinga wasanninsa dani son ransa, ni dai ban ce mashi komai ba, sai da yai mai isarsa sannan ya sakeni muka yi wanka, har lokacin zafi jikina yake mun, ya bani bathrobe ɗinsa na sanya, ya ɗaukeni zuwa ɗaki.
Ya bani jallabiyansa na sanya, ya miƙo mun hijab ɗina dan in yi sallah shi kuma ya haye gado ya kwanta.......... Ina idar da sallah na zauna a kan daddumar ina askar, bayan na kammala sai nai kwanciyata kan daddumar ban koma kan gado ba. Har barci ya fara ɗaukata sai ji na yi ya ɗaukeni yana faɗin. "Har yanzu kunyar tana nan kenan? Sai na yi da gaske zan rabaki da ita ko?".
Gabaɗaya Abba ya canza, tamkar bashi ba, sai mamakin shi nike ta faman yi, duk wani kunyar dake a tsakaninmu Abba ya daina jinta, hankalinsa kwance yake taɓa duk in da yake so a jikina, ya kwanta dani a jikinsa, ya cigaba da wasanninsa da albarkatun jikina, tun ina jin shi har barci yai awon gaba dani, dan duk ya wahalar dani kiya ban da barci babu abin da nike ji...........
labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danna like and share fisabilillahi.
FATEEMA ZAHRA MUSA
A-K-A
QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥
LABARIN AISHA.🥹💔
PART 42
Follow my TikTok account 👇
https://www.tiktok.com/@princess_teema1?_r=1&_t=ZS-92AoEpYYmwP
Follow my Channel account 👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S
Ya cigaba da wasanninsa shi ma har barci tai awon gaba da shi, bamu tashi farkawa ba sai around 11, ni na fara farkawa, yunwa tamkar in ci babu, cikina har wani murɗamun yake yi, coz duk abincin da na ci daren jiya Abba ya karar mun da shi a chaskalen da yai a kaina, sai nike jin wani irin yunwa na daban.
Ina waro idanuna sai kan kyakkyawan fuskansa, ajiyar zuciya na sauke game da cewa. "ALLAH nagode maka da ka bani wannan zinarin mijin". Na kai karshen maganata game da yunkurawa zan miƙe, sai dai ina, ya rukunkumeni ta ko'ina tamkar zai mai dani cikinsa.
Muryata can ƙasa na ce. "Abba, Abba, Abba, ka ɗan sassauta mun rikon mana, bafa zan gudu in barka ba".....… Karaf a kan kunnensa maganar, ya ɗan motsa tare da kara jawoni jikinsa sosai, ba tare da ya waro idanunsa waje ba ya ce. "Daɗi, ɗumi da laushin jikinki da ya fi mun mattress ne yasa nai maki irin wannan riko ai". Ya kai karshe tare da waro idanunsa a kaina.
Na ɗan yi ƙasa da nawa idanun ina ɗan murmushi........ "Yau safiyata zata fara da nasara da kyau In Sha ALLAH, irin wannan kyakkyawan musulmin murmushi mai melting heart haka? Zaki sanya in ji yau na wadatu fa"........ Na sanya hannuna na ɗan rungumesa, na ɗaura hannun nawa a kan bayansa, cikin shagwaɓa na ce. "Kai ko? Zaka fara kenan".
Ya sumbaci gaban goshina. "Ba wani farawa, dama can haka ne, yanzu dai faɗa mun meyasa aka tasheni daga barci ina tsaka da mafarkin ina kara morewa kamar daren jiya".......... Na ɗago muka haɗa ido, na ɗan yi ƙasa da nawa kafin in ce. "Kai da waye kuke morewa a cikin mafarkin?". Ina haɗe rai na faɗa...... Ya ce. "Like wow, light of my life tana kishina, ya Salam". Da alama ya ji daɗin hakan sosai, coz maza suna son su ga mace na kishinsu, dan kishi shi ke nuna mace ta damu da kai kuma tana sonka, ana kishin abin da ake so ne kawai, shiyasa maza suna bala'in son su ga mata na kishi suna faɗa a kansu, daɗi suke ji, sai su dinga jin tamkar sun kai wani matsayi na musamman ne.
Turo baki na yi, a shagwaɓe na ce. "Ba dole in yi kishinka ba, ni dai ba wannan ba, faɗa mun da waye kake morewar?"...... Ya fara shafa gashin kaina zuwa gadan bayana.... "Ni da light of my life muke morewarmu tamkar yadda muka yi daren jiya, my wife faɗa mun mana, meyasa kika yi daɗin dake neman zautar dani? Wannan uban ruwan ni'ima daga ina? Kin ji me na ji kuwa?". Yana kara rungumeni ya faɗa.
Na ƙara kwantar da kaina a kirjinsa kafin in ce. "Abba, a ina ka san dukka wannan? Ka taɓa sanin mace ne?"........ Kai ya girgiza mun alamar a'a, sai kuma ya ce. "Ban taɓa sanin mace ba sai a kanki, but ina da sani dayawa a kan abubuwan da ya shafi mata, and abokai a school tun ina hundred level lokacin yarinta kai na rawa suna irin wannan magana, a nan nasan mata sun kasu kashi uku, and a nan nasan mace mai yawan ni'ima tana da wahalar samu, sannan a nan nasa ita kanta ni'imar, na san siffofin mace mai ni'imar".
Na yi shiru ina sauraransa har ya kai karshe, sannan na ce. "To amma ai baka san cewa in dai ka jijjiga mace a dare da safe tana tashi da watsananciyar yunwa ba ko?"............ Cikin zolaya ya ce. "Me kuma jinjinga mace? Kuma ni a yaushe na jinjina mace?"...... Sarai ya gane nufina, kawai so yake sai ya cire mun linzamin dake bakina na zama mara kunya kamar shi.
Na sharesa na ki amsawa, sai kuma na turesa ina son tashi. Da sauri ya damkeni, muryansa can ƙasa ya ce. "ALLAH ya huci zuciyar light of my life, idan kika yi fushi ai sai hasken rayuwata ta ɗauke, nasani nasan zata ji yunwa, amun afuwa, yanzu a faɗa mun me ake son ci?"....... Na ɗan turo baki. "Ni abincin Hajiyarmu nike son ci".
Cikin wani irin salo ya ce. "Da gaske? Ko dai na zura kwallo a ragana har an fara mun rigima ne?". ....... Na yi shiru ban amsa shi ba. Ya sake cewa. "Okay bari aje a kawo abincin Hajiyarmu". Ya faɗa tare da miƙewa, na zaci da wasa yake yi, sai naga ya jawo trolley ɗinsa, ya fitar da wasu tsadaddun shadda ruwan zuma, ina ta kallonsa ya kammala shirinsa, ya yi fitinannen kyau.
Dan in kurewa idanuna kallo ban yi magana ba, ya zo dab ni, sumbata ya manna mun a kumatu tare da cewa sai ya dawo. Ni kam wai dan in ga gudun ruwansa ban ce uppan ban. Ya fice daga ɗakin, na yi shiru ina tunanin ina zai je ne wai?.
Na jima ina tunane-tunane na, da naga babu mai bani amsa sai na miƙe zaune, na yaye bargon gabaɗaya, na sauke kafafuna ƙasa game da sauƙowa, na miƙe na nufi toilet, ruwa na ɗan watsa, na fito babu kayan sanyawa, na jawo trolley ɗinsa na hau dubawa, throbe ne kawai a ciki wanda zan iya sanyawa sai sleeping dress ɗinsa.
Na ɗan yi shiru, sai kuma na ce bari in sanya sleeping eyes ɗinsa mu gani, na gyara gashin kaina na ɗaure, sannan na sanya sleeping dress ɗinsa, na zauna a bakin gado cikina na murɗamun, ji nike tamkar in saka kuka....... Na yi zaman mintuna 30 a wajen sai naga an turo kofar ɗakin. Tun kafin ya shigo kamshin perfume ɗinsa ya faɗa mun wanenen yake tafe.
Na sauke nannauyar ajiyar, da sauri na waro idanuna a kansa ganinsa rike da basket mai ɗauke da kulan gidanmu da kuma wata bakar leda mai ɗan girma, da gaske kenan abincin Hajiyarmu ya je ya karɓo mun? A saman carpet ya ajiye abincin, sannan ya hau rage kayan jikinsa, a natse ya ce. "Light of my life, ga abincin Hajiyarmu nan ya iso, maza taso ki zo ki ci".
Cike da mamaki na ce. "Nawan ya aka yi ka samo abincin Hajiyarmu?"........ Yana ƙoƙarin naɗe rigansa ya amsa da. "Ba dai light of my life ta ce abincin Hajiyarmu take son ci ba? To ga shi ya zo, maza zo ki ci"...... Na miƙe a hankali game da ɗan shagwaɓe fuska kafin in ce. "Please mana nawan, ya aka yi ka ajiye kunyarka ka je ka karɓo mun abinci?".
"Zan faɗa maki, yanzu dai zauna kici". Ya faɗa yana dawowa kusa dani, ya rike hannuna muka karisa wajen abincin, ya zaunar dani, da kansa ya zuba mana a plate, soyayyar dankalin turawa da kwai da ya ji kayan kamshi, sai tea mai zafi, bayan ya zuba mana ya ɗauki fork ya fara bani a baki, in a cool way ya ce. "Zuwa na yi, bayan mun gaisa da Hajiyarmu na fito sai na kira Safiyya, na ce mata auntynta na buƙatar abinci please, shi ne ta kawo mun, na ce ta ɗauko mun kayanki ko kala biyu ne, sai ta ɗauko mun gasu". Ya kai karshe yana nuna mun kayan a leda.
Na ɗan zare mashi idanu kafin in ce. "Nawan, ya Hajiyarmu ta karɓeka?"..... Ya amsa da. Normal, sannan ya ce in yi shiru in ci in koshi. Haka muka ciyar da juna abinci cike da tsantsar so da kulawa, sai da ya tabbatar da na ƙoshi, sannan ya tattare kayan abinci, ya ce in shirya muje ziyara, dan gobe yake son mu wuce Abuja, daga nan mu koma Germany saboda karatuna.
Na amsa da okey, na tashi na ɗauki ledar kayan, na shiga toilet, yana kallona bai yi magana ba, dan baya son mu ɓata lokaci. Jim kaɗan na fito shirye cikin wata shadda mai ruwan zuma kalar nasa, tamkar lokaci ɗaya aka yi mana, Safiyya saboda ta ga irin kayan jikinsa ne sai ta ɗauko mun shadda kalarsa, ALLAH sarki.
Sai yaba kyauna yake yi, ya tayani muka karisa shiri da wuri, sannan muka fito domin zuwa ziyara, mun yi bala'in kyau sosai da sosai, mun fito a amarya da angon kuwa. Cikin motansa muka shiga, yana ta cigaba da yaba kyauna ya tada motar muka nufi hanyar gidansu, na yi mamakin ganin gidan mama zamu je, ban yi wani magana ba, har muka faka mota a kofar gidansu Mama.
Ya ɗan kama hannuna, a natse ya ce. "Muje ki gaisa da su sai mu wuce kauye ko?"..... Kamar zan ce ba zan je ba, amma a matsayinmu na sabbin ma'aurata bai kamata in fara bijire mashi ba, haka na fito shi ma ya fito. Ya kama hannuna muka tsallaka kwatar kofar gidan muka shiga ciki.
Baki a ɗauke da sallama muka shiga, nan muka iskosu a tsakar gida sun baje kayan wanki zasu fara, Amina da Humaira kamar wasu kuncen mahaukata, kai ba ɗankwali, sun tsefe kitso rabi sun bar rabi, dukkansu da ɗaurin kirji, Mama na zaune kasan bishiyar gwandar gidan, dukkansu dagaje-dagaje.
Suna ganinmu Amina ta miƙe tana faɗin. "Abba dama zaka zo gidan nan?"...... Ya ɗan tamke fuska kafin ya ce. "Baku iya amsa sallama ba kenan?"........ Humaira ta amsa game da cewa. "Sannunku da zuwa".... Uhm, duk da Abba yake matsayin ƙaninsu baya ɗaukar nonsense, sun sani sarai baya sake masu fuska baya wasa dasu, ba irin Abbie da yake gani ana ciwa iyalinsa mutunci yana zaune yai shiru ba.
Jin magana a tsakar gidan yasa Sodangi fitowa daga ɗan madaidaicin ɗakinta dake gefe ta bayan kitchen, ashe gida ɗaya suke haɗe. Mama ta ce. "Muhammad sannunku da zuwa". Jikin Mama duk yai evening, ashe da Abbie ya kwanta ciwo Abba ne ya ɗauki nauyinsa, shi ya biya kuɗin komai, da ya zo ma sau biyu ya je asibiti ya duba shi, Mama ta so su haɗu da Abban amma baya yarda su haɗu sai dai ta ji labarin ya zo ya bar wajen, dan dama ya shirya tare dani zai zo wajensu.
Su Amina sun ji labarin Abba yai kuɗi duk sun tanadi abin da suke son rokansa amma sun gagara haɗuwa da shi..... Na kai kallona kan Sodangi dake fama da uban cikin da zai iya kai watanni 7. Ita ma sai kallona take yi, coz a farko ma bata ganeni ba, sai da ta yi ta kallona sannan ta ganeni da kyar.
Mama tai mana iso, na ce ni kam ba zan shiga cikin ba, na ɗan ƙanƙame hannun Abba a cikin nawa, cikin sanyin murya can ƙasa na ce. "Ina wuni Mama?"....... Fuska ɗauke da fara'a ta amsa, tana tambayata ya gida?. Haushinsu nike ji har yanzu, jikina har yana ɗan tsuma dana gansu, tamkar in rufesu da duka na ce. "Nawan mu tafi please".
Ya kalleni game da cewa. "Yanzu kuwa". Sai ya mai da kallonsa kan su Mama. "Mama mu zamu wuce, dama mun zo gaidaku ne zamu je kauye"........ Amina ba kunya ba tsoron ALLAH ta ce. "Haba Aunty Aisha, sai ki zuga ƙanin namu kada ya zauna cikin ƴan uwansa? Ki bari mu gan shi mana". ... Izuwa yanzu duk sun san cewa ni matar Abba ce, dan tun satin da ya wuce maganar ta fita da iyayena suka ki bashi ni.
Ni kam da yake yanzu idanuna ya buɗe kuma yanzu nasan ba tare muke da Abbie ba sai na ce. "Duk wanda yake son ganin shi ya zo gidan aurenmu ya gan shi, yanzu kam muna sauri ne"....... Humaira ta ce. "Ko dai kina tsoron a mashi mata a dangi ne?". Cike da zolaya ta faɗa tana ɗan murmushi, saboda tasan halinsu da shegen auren dangi.
Na ɗan yi one sided smile kafin in ce. "A'a, ni ai bani tsoron kishiya ko zata zo ma bare kuma nawan nawa ne ni kaɗai ko nawan?". Na tambaya ina mai da kallona a kansa. Ya ce. "Faɗi ki kara da babban murya kowa ya ji ni naki ne ke kaɗai".
Tamkar Tv haka Sodangi ta mayar damu tana kallonmu....... Amina ta ce. "To me kike tsoro da kike cewa ku tafi?"..... Ba tare da na kalleta ba na ce. "Bana tsoron kowa kuma bana tsoron komai face ALLAH, kawai dai bana son ku ce zaku mashi hayakin makarin asiri ne ku sanya ya fara ƙauri bamu je in da zamu je a mutunce ba".
Nan fa suka fara kallon-kallo a tsakaninsu, harta Mama sai da ta ji kunya, sun tuna lokacin da suka kuntatawa rayuwata da makarin asiri. Shi ma nawan ya tuna lokacin, sai ya ji yakamata ya nuna masu cewa yanzu fa matarsa na samu peace of mind da kulawa sosai da sosai fiye da yadda ake zato.
Ya ɗan kama shoulder ɗina game da cewa. "Mu je da wuri"....... Na dawo da kwallona kansa sosai, ya kashe mun ido ɗaya, na ɗan yi murmushi ina ɗauke kwallona sannan ya ce. "Mama bari muje, zan baiwa Abbie saƙo ya baki". ...... Da sauri Mama ta ce. "A'a ni dai ka bani a hannuna, kasan halin yayan nan nasa"......... Na ɗan sake hannun Abba ina faɗin. "Ka sameni a mota bawan, bari in je".
Ya kama hannun nawa, sai kuma ya ce. "To ɗauko mun kuɗi a mota"..... Na ce. "Nawa zan ɗauko maka?"....... "Adadin yadda zuciyarki ta kwanta da shi"...... Na wuce gaba ina jin sanyi a raina, ko ba komai Abba ya nuna masu ina da muhimmanci a rayuwansa, abinda Abbie bai taɓa kwantatawa ba, na ji daɗi sosai, kuma yanzu nasan ba zasu kawo mun rainin sense ba.
Ina fita Amina ta ce. "Abba kana son Aishar nan sosai"...... Yai shiru bai amsa mata, dan shi yasan baki ba zai iya faɗar adadin tsantsar son da yake mun ba. Ita kuma Amina ta yi dan ta bugi ruwan cikinsa..... Humaira ta ce. "Ke kuwa ba dole ya sota ba, baki ganta bane? Kamar ƴaƴan larabawa".
Shi dai bai tankasu ba, Mama ta ce. "Amma Abba bai kamata ku tafi da wuri haka ba".......... "Akwai in da zamu je dayawa ne shiyasa". Cikin girmamawa ya faɗa, duk da Mama ba ita ta haifeshi ba yana girmamata sosai da sosai, dan tun yana jariri yake hannunta, tun bai kai shekara guda ba, kuma ta rike shi ba mugunta ba cutarwa, ba zaka taɓa cewa ba ɗanta bane, yadda ta rike ƴaƴanta haka ta rike shi, auta ma take ce mashi, coz shi ne karami duk cikin ƴaƴanta, ta shagwaɓa shi sosai, komai yake so shi take mashi da yana karami, so ba zai taɓa mantawa da ita ba, kuma ba zai daina girmamata ba.
A daidai lokacin na dawo rike da jaka a hannuna, na zo na miƙa mashi jakar ina faɗin. "Ga shi nan". ...... Ya karɓa ya buɗe, kuɗi ya fitar rafar dubu ɗaiɗai na dubu ɗari-ɗari rafa goma ya miƙawa Mama. Da sauri ta taso ta karɓa tana zuba mashi godiya, a ransa ya kuduri niyyar sanyawa a gyara mata gidan nan nata, amma ba zai faɗa masu abin da ya shirya masu ba.
Ya miƙawa Amina rafa biyu dubu ɗari biyu, haka ita ma Humaira ya miƙa mata, zai ya juya ya miƙa mun rafa biyu wai in baiwa Sodangi, ashe ya ganta tun ɗazun. Na karɓa na ƙarisa in da take tsaye, na miƙa mata zuciyata cike da tunanin ranar da ta ce mun wai saboda ta kwace Abbie ne duk na fige na fita hayyacina, sai dai kuma yau ga shi Abbien na hannunta amma tana fige tamkar gazar mayu.
Na miƙa mata kuɗin, hannunta na rawa ta karɓa. Abba ya juya zai nufi waje, na rufa mashi baya. Muryan Amina ya katsemu da cewa. "Abba dama ina son magana da kai"...... Ya juyo, sai ya ce. "Ina jinki". Ta ɗan kalleni alamar bata son yin magana a gabana kuma bata son su Mama ma su ji shiyasa bata iya faɗa mashi ɗazun dana fita ba.
Ya gane bata son yin magana a gaba nane, dan ya nuna mata girman muhimmancin da nike da shi, ya nuna mata cewa ni da shi duk abu ɗaya ne, kada su fara kawo mashi wani banzan shirirta sai ya ce. "Duk abin da kike so ki sameta ki faɗa mata, ba sai na saka baki ba zata maki komai!". Ya faɗa yana nunani, ya kai karshen maganar tare da ficewa da sauri. Sun sha mamakin yadda Abba ya nuna masu ni fa na fi mashi komai, coz sun ɗauka zai bada wata kafa ne su samu damar rainani yadda suke so, sai kuma bai yi wannan gangancin ba.
Nima da sauri na bi bayansa, ina fita Amina ta kalli Humaira game da cewa. "Shigiya da ke wata ce ai da kin san yadda zaki yi kin aure mana yaron nan ko zamu huta". Kun san Humaira ita ce ƙaramar cikinsu, da kaɗan ta fi Abba, bai wuci ta bashi 2 years ba.
Mama ta ce. "Wlh kuwa, da mun ji daɗi, amma wannan yaushe zata taɓuka abin arziki"...... A kule Amina ta ce. "Ji yadda yake nuna mana wannan banzar wai ta fimu muhimmanci a wajensa, har abu in muna so mu tambayata da hannunta, da yanzu kin aure shi duk da ba wannan magana ake yi ba".
Humaira ta ce. "Kanin nawa zan aura? Tab ALLAH ya kiyayye, kwaɗayin duniya bai kai haka ba"........ Amina da hasada ne yake ciyo mata rai ta ce. "Waye ya ce maki yaro idan yana da kuɗi yaro ne? Banza jaka ƙazama kawai"........ Humaira ta ce. "Jakuna ƙazamai dai"...... Amina zata kai mata duka a hasale ne Humaira ta yo waje da gudu.
Dogon tsaki Sodangi ta ja game da wucewa cikin ɗakinta tana masu tofin alwadarai da irin halinsu, sai sun tuba su sake komawa ruwa. Mama ta bita da kallo tana mata tofin ala tsine..
Mu kam duk bamu san ana yi ba, muna shiga cikim mota na kwanto saman shoulder ɗin mijina, ya tada mota bayan ya manna mun sumbata a forehead ɗina, yana zuba mun ruwan albarka, ina son tambayansa ina Abbie ban gansa a gidan ba, amma ina tsoron kishinsa ya motsa, sai kawai na yi shiru.
Ya ja motar bai dire a ko'ina ba sai kauye. Jama'a, naga kara da tsantsar kauna wajen ƴan uwan mahaifiyar Abba, sun nuna mun so, tamkar su cinyeni dan so, na ji kunyar ban saya masu tsaraba, ina tunanin me zan basu sai naga Abba ya buɗe bayan motar ya fara fito masu da atamfofi da kayyaki masu kyau, duk wanda ya baiwa sai ya ce ni na basu su mun godiya, already bawan ALLAH ya shiryawa zuwanmu kauyen ashe, shi ne ya sai masu tsara ban sani ba.
Hakan yasa suka ƙara sona, suka dinga jin daɗi. Suna ta jana gidan dangi da ƴan uwa na cikin kauyen, da kyar Abba ya kwatoni daga hannunsu muka kamo hanyar komawa.
Ana ALLAHU AKBAR magrib muka shigo cikin gari, na so mu je wajensu Hajiyarmu amma ya ce sai gobe, muka tsaya Central mosque muka yi sallar magrib da ishai, sannan muka yi sayayyar abin da zamu ci, muka koma hotel ɗinmu. Muna shiga ɗakinmu na faɗa kan gado ina faɗin wash bayana, duk na gaji. Abba ya ajiye kayan hannunsa ya wuce toilet.
Jim kaɗan ya fito, ina kwance ina mai da numfashi ban kara ba na ji ya ɗaukeni can sai cikin toilet, da kayan jikina da komai ya jefani cikin jacuzzin da ya haɗa ruwa a cike a ciki. Na tsuke fuska ina hararansa, ya saki one sided smile tare da fara zare kayan jikinsa zai shigo mu yi wanka tare, mu gasawa juna jiki tare
labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danna like and share fisabilillahi.
FATEEMA ZAHRA MUSA
A-K-A
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 35 Chapter of 38