Share this page
da waya kawu Badamasi ya kwace wayansa yana faɗin su kyaleni in huta, dan su in aka biye masu surutunsu basa ƙarewa, ai kawu Badamasi na karɓar wayan na miƙawa Abba wayansa ina murmushi. Ya karɓa suka yi sallama Abba ya katse kiran. Ina ƙoƙarin barin jikinsa ya ƙamkameni game da cewa. "Hakan ya fi daɗi tawan, kada ki bar jikin mijinki"....... Hararansa na yi tare da cewa. "Sakannin in tashi"....... Ya sakeni yana kallona, a natse na bar jikinsa ina faɗin. "Mutanen kauye akwai karamci da haɗin kai, ga son al'umma da son nasu". Ya amsa da. "Sosai, and suna matuƙar son Innata ne saboda ita kaɗai ce mace cikinsu Kawu Badamasi, suna ji da ita, shiyasa suke sona sosai"....... Na ɗan hararesa kafin in ce. "Eyye Autan maza da mata"...... Ya ɗan yi one sided smile kafin ya ce. "Zo ki ji wani abin". Na make kafaɗa alamar a'a ba zan zo ba. Ya rike hannuna tare da cewa. "Idan na je Nigeria na dawo da babana kyautar me zaki bani a wannan rana?".......... Da sauri na ce. "Abba, da gaske zaka iya ɗauko mun shi?". ALLAH sarki uwa da ƴaƴanta, kullum da Hassan a raina nike kwana kuma nike tashi, addu'a kullum yana bakina a kansa, na yi kukan rashinsa har na gaji, a kan ƴaƴana babu abin da ba zan iya ba. "In Sha ALLAH tamkar na ɗaukosa ma na gama"....... Ai daɗi yasa ban san lokacin da na matsa kusa da shi ba, na rike damtsen hannunsa ina faɗin. "Please kana kallonsa kafin ma ka yi komai ka kirani video call in gan shi ka ji? Shekaru biyu rabona da shi, ina son ganinsa". Idanuna ne suka cika da hawaye tab......... Abba ya kai hannayensa dukka biyu kan fuskata, ya ɗan tallabo kumatuna kafin ya ce. "In Sha ALLAH, kada ki yi kuka, ki sanya a ranki nan da rana ita yau kina tare da babana, shi kuma babana Hussain ALLAH yasa mai cetone, and very soon zaki sake haifa mana wani irinsa". Na buge hannunsa dake kan kumatuna tare da cewa. "Abba baka da kunya kwata-kwata"......... "Kece sular komai ai". Ya faɗa yana rike hannuna. Haka yau muka wuni ba faɗa ba gaba tun da na ji za'a ɗauko mun Hassa, sai dai fa ba yadda bai yi ba naki fita parlo, ya yi juyin duniyar nan ina zaune a ɗaki. Har ɗaukata yai zamu fita na dinga ihu na ce kada ya fitar dani har sai an kwashe magunan nan daga gidan nan. Shi kuma ya ce a'a ba za'a kwashesu ba. Dole dai ya kyaleni a ɗakin, ya je ya kawo mun abinci, a nan na ci breakfast, lunch and dinner dukka, a daren yau ma tare muka kwana, washegari ya fara shirin barin ƙasar, ina ta faman tambayarsa batu kan Yah Abbas, ya ce kada in damu yasan me zai yi. A ranar da yamma ya ɗaukeni muka je sayayyar abubuwan buƙata a wancan tsohon benenmu, na sayi duk abin da zamu buƙata, sannan yasa aka je aka share gidan, bayan mun dawo washegari ranar da zai bar ƙasar, a ranar kuma Yah Abbas zai zo, sai ya sanya aka ɗaukemu zuwa tsohon benenmu, ya sanya guards biyu su dinga tsarona a benen namu, su sanya mun ido, amma ko ni kaina ban san da masu tsaron nawa a wajen ba. Ai a ranar da muka koma tsohon benenmu sai da na ji wani iri, gabaɗaya babu daɗi, haka na wuni sakaka babu wani walwala, na dinga duba wayata ko Abba ya kirani, shi kuma yana cikin jirgi, wayarsa tana kashe, duk na damu, ko girki na gagara yi wa Yah Abbas, Zahra ce ta mana girki gabaɗayanmu. Da magrib Yah Abbas suka yi landing, muka je airport da motar benenmu, na ji matuƙar daɗin ganin yayana, na rungumesa ina ta murna, ya ɗauki Muhammad yana tambayata shin bani da lafiya ne ya ga na rame har haka? Na ce a'a lafiyata lou, ya damu ya dinga tambayata, na kafe sam babu komai, ya ce ya ga kamar hankalina ba'a kwance ba, na ce a'a hankalina a kwance, kawai makaranta ce ta sakamu gaba. Tun da muka kama hanyar komawa yake ta faman mun tambayoyin kan yanayin canzawata, ga rama da ƴar duhu da na yi, ni kam na kafe sam babu komai. Yah Abbas kamar bai yarda dani ba, ya tambayi Zahra shin bani da lafiya ne, ta ce mashi e, na yi rashin lafiya last week, na manta da last week na faɗa mata bani da lafiya, a lokacin da muke rikici da Abba na keɓe kaina ina kuka, a lokacin ta ga na rame na canza shi ne ta tasani gaba da tambayoyi, sai na ce mata ban da lafiya ne, ashe tana rike da zancen. Yah Abbas ya ja kunnena ya murɗe yana faɗin karya zan mashi kenan ko? Na ce yai hakuri bana son hankalinsu ya tashi ne shiyasa ban faɗa mashi gaskiya ba. Ya ce kada in sake bani da lafiya in ki faɗa masu, na ce In Sha ALLAH. Muna isa gida ya fito yana rungume da Muhammad, ni ma fito, Zahra ta fito da akwatinsa muka nufi ciki, already na faɗawa Zahra kada ta faɗawa Yah Abbas mun zauna a gidan wancan yayan nawa, ta ce meyasa ya ce mata rikici ne na ahali, da yake su hakan ba abin kunya bane a wajensu, wai irin ayi rikicin ahali dangi su rabu, shi ne na faɗa mata ina da brothers guda uku, to rikicin ahali yasa kanmu ya rabu, ni kuma nice karama, dukkansu suna son ɗaukata, and kowannensu sai ya ce ni tashi ce kawai, ba ruwana da ɗayan yayana. To da yake ba sabon abu bane a wajensu sai ta yarda dani, na nuna mata na fi son Yah Abbas shiyasa bana son yasan ina zuwa wajen sauran brothers ɗina, bana son abin da zai ɗaga mashi hankali sam-sam. Aikuwa ta tayani rufe cewa mun zauna a gidan Abba. Da karfi da ya ji ta yi wa Yah Abbas karya, shi kuwa Yah Abbas tuni ya yarda da ita, yana mata kallon mai hankali, da alama ma da kallon farko ya faɗa, sai kallonta yake, ina ta ganinsa ni kuma, ita kuma Zahra tana son Abba, shi kuma Abba yana sona, ni kuma zuciyata na faɗa mun Ibrahim nike so.............. Wannan shi ne cakwakiya. Bayan Yah Abbas ya yi wanka ya yi sallah, muka zauna zaman cin abincin da Zahra ta girka, ya dinga santin girkinta yana yaba mata, dan ya tambayi waye ya girka na ce mashi ita ce, sai yaba mata yake tana murmushi, do ba karya ta iya girki sosai. Muna tsaka da cin abincin ne Abba ya kira wayata, ai ina ganin sunan da na yi saving numbersa watau NAWAN sai da na sauke nannauyar ajiyar zuciya, na miƙe tare da cewa Yah Abbas. "Yaya bari in je toilet". Ya jinjina kai, dama so yake fa in tafi in bashi waje ya tsara Zahra, kamar na tsaya mashi a wuya dama. Nima duk sun takura mun dama, da sauri na wuce ɗakina. Ina shiga na rufe kofa kafin in yi pick-up. Ina ɗauka ya sauke wani musulmin ajiyar zuciya tare da cewa. "Assalamu alaiki my wife"...... Ni kaina na ji tsananin daɗi, amma na haɗe fuska da cewa. "Wai Abba ba zaka bari ba, nice ma wife ɗin taka?". Ya ce. "Gaskiya ba zan bari ba, kuma idan ba ke ba wacece?"........ Na ɗan yi murmushi tare da cewa. "Uhm, ka bari bana so"..... Ya sake cewa. "Gaskiya ba zan iya bari ba"........... Ni da kaina ban san meyasa nike murmushi ba, na ce. "Ka isa lafiya?"..... Ya amsa da. "Lafiya lou, tun ɗazun na isa, ga su kamar zasu cinye, kinga wasu har da suma wai gawa ya dawo". Dariya ne ya kubce mun, sai da na yi mai isata sannan na tsagaita, yai shiru yana saurarata ransa fes tamkar ya ganni gani ga shi. Da na tsagaita ne na ce. "Ai sun ga fatalwa ba dole su suma ba, nima ai dan ina da karfin imani ne, da suma zan yi, shekaru biyu da mutuwarka kuma sai ka dawo". Ya ce. "Me kike yi yanzu haka?"...... Na ɗan yi shiru kafin in ce. "Ina zaune a bakin gado"....... "Ya yaya Abbas? Ya zo lafiya?"......... Na amsa da lfylou Alhamdllh, sannan na ce. "Ya ka samu su Mama?"...... "Ban je wajensu ba". Ya amsa mun. Da sauri na ce. "Why?"........ "Saboda ba wajensu na zo ba dama, babana na zo ɗauka, shi kawai kuma zan ɗauka in dawo"...... Cike da mamaki na ce. "To ina kake yanzu?"....... "Ina kauye wajensu Kawu Badamasi, amma kafin na zo kauye sai da na fara zuwa gidan Abbie muka gaisa, nan na samu su Amina shi ne har da sumansu wai gawa ya dawo". Na ɗan zare ido. "Kauye kuma? Ka iya kwana a ciki? Ya zaka yi da abincinsu? Ya ka kare da masoyanka?"........ Yana zaune kasan bishiyar mangoro, da daddaren nan ko tsoro baya ji ya amsa mun da. "Ai shigar sirri naiwa Nigeria, ni da na zo ɗaukan babana me nawa na faɗawa duniya ga in da nike bare masoya su yi rububin hanani watayawa, batun kauye kuma kin san abin da suka shirya mun da na ce zan zo ne?". Na girgiza kai game da cewa a'a..... Ya ce. "Har rago suka yanka mun, kin san na fi shekaru goma rabona da kauyen nan, sun ji daɗin zuwa sosai, sun kashe mun kuɗi sosai, sai murna suke yi"...... Na sauke ajiyar zuciya mai nauyi, zan yi magana ya rigani da cewa. "Eyye, da kin ɗauka jagwalgwalon abinci aka baiwa mijin naki ko? Har kin fara kukan kada ciwo yakamani ko?". Da sauri na ce. "Ni ba nufina kenan ba kada ma ka mun sharri"......... "E gaskiya ba nufinki kenan ba, tun da ga shi har da sauke ajiyar zuciya saboda kin ji ban ci jagwalgwalon ba, kayan daɗi na ci, tawan ke ko? Kina sona amma kike wahalar dani ko?". "Abba ka bari, idan ba haka ba zan kashe wayata"....... Uhm ya ce bai sake magana ba. Na ce. "Ina Hassan ɗina?"........ Ya amsa da. "Yana cikin gidan wajensu kawu Badamasi". Ai ban san lokacin da na zabura na miƙe tsaye ba, har ina haɗe words wajen cewa. "Da gaske kake yi nawan? Dama ka ɗauko mun shi? Ya aka yi Abbie ya baka shi? Yaushe zaka kawo mun shi to?". Duk ina rikice na yi maganar. Sai da ya nisa, in a cool way ya ce. "Kwantar da hankalinki mrs Muhammad Abba, babana yana tare dani, kuma jibi zamu dawo tare, Abbie kuma ce mashi na yi na zo ɗauka Hassan mu koma kasar da nike da zama, bai hanani ba saboda dama nauyi ta mashi yawa, kawai ya ce mun ba damuwa, in kula da shi, sannan kin san me Abbie ya ce?". Na wani sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da cewa. "A'a ban sani ba". Na faɗa ina komawa slowly na zauna a bakin gado. "Ya ce mun wai lallai in dawo in zauna da Zainab gida guda, kin ji wai sa'a zata dawo mana, dan ita ma Zainab taurarinta akwai haske sun kusa kai naki haske, kin ga ban faɗa mashi waye ni a yanzu ba, kawai na ce mashi ina Germany ina neman aiki, wai shi ne in bar komai in dawo mu zauna da Zainab, idan sa'a ta dawo mashi sai ya buɗe mun shago". Take nai kicin-kicin da fuska kafin in ce. "Me ka ce mashi kai kuma?"........ "Na ce mashi to kawai, na ce bari in je in tattaro abubuwana zan dawo, dama ni burina in ɗauki babana, idan na bar Nigeria yanzu ai su da ganina sai na zo gaida su Hajiyarmu in nemi yafiyar laifin da na yi, daga nan in ɗauki matata da lasisi". Wasu double musulman ajiyar zuciya na sauke tare da cewa. "To shikenan sai da safe"........ Ya ce. "Na sallameki ne?". Na amsa da a'a...... Yai ƙasa da murya wajen cewa. "Kinga ni fa yanzu ban san ta yadda zan yi in yi barci ba, na fara sabawa da kwana a jikinki"........ Na yi shiru na rasa amsar da zan bashi, saboda ni kam ban iya wani soyayya ba bayan cewa I love you. Ya sake cewa. "Kinga, yanzu fa ki fara shirin karɓana matsayin miji, tun da kin bada sharuɗa na bi, ga Baba na ɗauko maki, kin ce idan na ɗaukosa zaki karɓeni matsayin abokin rayuwa, so get ready, dan gaskiya ba zan iya cigaba da hakuri ba"....... "Abba, please ka bari mana". Na faɗa ina danne murmushin dake shirin kwace mun wanda ban san dalilin yinsa ba. "Me zan bari?"........ "Ka daina cewa ni matarka ce"....... Ya zazzaro ido tare da cewa. "Kai, kai, kai, aikuwa yanzu na fara, kinma yi sa'a bana kusa da na yi maganin ɗan bakin nan dake ƙoƙarin hanani cewa ke matata ce, kin san menene tawan?"....... Na girgiza kai ina cewa a'a........ "Tun yanzu ma gara ki fara shirin nema mun suna, dan dole ki daina ce mun Abba". Na dallawa ɗakina harara tamkar shi ne a gabana kafin in ce. "To sannu ka ji? Na ce sannu" .......... Ya ce. "Yauwa matar mijinta, kin san me nike so yanzu?"......... Na amsa da a'a....... Yai ƙasa da murya sosai wajen cewa. "Tausa zaki zo ki mun, duk na bi ba gaji, jikina sai ciwo yake mun, zo mu raba gajiyan, in sauke maki rabi a jikinki". Rasa me zan ce mashi na yi, yana neman fin karfina. Ya manna wayar da bakinsa kafin ya ce. "Tawan, ina buƙatar ɗumin jikinki irin na shekaran jiya, wancan lamari ya tsaya a raina".......... Wani irin yanayin da ya jefani ne yasa na fara biye mashi ba tare da na sani ba, ban san cewa na san wasu kalmomi na romance ba sai yanzu da na biye mashi a waya, ban san lokacin da na saka mashi shagwaɓa ba, ya mun wayau ya buga cikina, ya tambayeni ya na ji shekaran jiya. Ban san lokacin da na ce mashi daɗi sosai wanda ban taɓa ji ba, har mafarkinsa da na yi sai da ya mun wayau na faɗa mashi, a ranar na yi mafarki muna zuba wani irin soyayya mai tsayawa a zuciya, ya dinga romancing ɗina, har sunna muka raya cikin mafarkin, kuma duk na faɗa mashi, wlh ban san na faɗa ba, wayau ya mun da romantic words ɗinsa. Aikuwa ya ce. "Duk abin da kika gani a mafarkin nan ki shirya ina dawowa zan maki shi"........ Na ce. "Da gaske kake yi?".... Ya amsa da kwarai kuwa, sai kuma ya ce. "Ko dai in dawo dawuro ba zaki iya dogon jira bane?"....... Aikuwa ban san lokacin da na ce e ba, giyar soyayya da daɗin kalamansa ya bugar dani, na dinga biye mashi. Mun kai karfe 11 muna waya, sai da Yah Abbas ya buga mun kofa, sun ga ban dawo ba, nan ne na dawo cikin hayyacina, da sauri na katse kiran, shi ma Yah Abbas ya je can yana gina kaunarsa a zuciyar Zahra shiyasa bai farga ban dawo da wuri ba. Ina katse kiran na fara tuna irin suɓutar bakin da na dinga yi wa Abba, hannu nasa na dafe kaina ina danasani, Abba ya mun wayau. Da sauri na tashi na buɗewa Yah Abbas kofa. Ya wurga mun kallon tuhuma kafin ya ce. "A'isha, lafiyarki kuwa?". Ina ƴan kame-kame na ce. "Yah Abbas me ka gani?"...... Ya zubawa yatsun kafata idanu, yadda nike ta faman matsasu a ƙasa, sai ya ce. "Zo ki karasa cin abincinki, kuma ki rage kiraye-kirayen wayar nan"..... Da alama yayana ya gane na shiga wani duniyar soyayya, dan alamun feeling ƙarara sun bayyana a tattare dani, Abba bai kyaleni ba sai da ya tada mun da duk wata sha'awata ɗan rainin wayau. Na ce. "Yah Abbas na ƙoshi, zan sha black tea kawai"....... Ya ce a'a in fito in ci, dole na fito dan kada ya cigaba da zargina. Shi kuma ya wuce ɗakinsa, yana shiga ya kira babban yayanmu a waya, wai ya ce da iyayen Ibrahim su turo gida ayi batun aurenmu, dan a yadda ya fahimceni yanzu ina buƙatar namiji, coz da ban taɓa auren bane da sauƙi, amma na taɓa aure, gani da ƙananan shekaru, ai jiki da jini dole ma in buƙaci namiji, Yah Abbas ya ce nama yi ƙoƙari shekara biyu, gaskiya kada su shiga hakkina su mun aure in ya so Ibrahim ya biyoni nan in karasa karatu mu koma tare....... BABBAR MAGANA. Kwanaki uku da yin wannan magana iyayen Ibrahim suka dira a gidanmu, mahaifina ya amsa da ya basu saboda yasan da cewa ina son Ibrahim tun ina karama, dan har kuka na yi ina durkushewa gabansa ina rokon da ya dubi girman ALLAH kada ya rabani da Ibrahim, wannan dalilin yasa yanzu ya ce ya basu, kawai azo a kawo sadaki, a sanya rana.... TASHIN HANKALI. Ibrahim zuciyansa tas, yana jin yanzu kam zai mallakeni, sai dai kuma, mahaifiyarsa ta ce bata aminta da wannan aure ba, wai iyayena basu so shi tun yana talaka ba sai da ya yi kuɗi, wannan arzikinsa suka biyo, ya dinga cewa mamansa ba arzikinsa bane, Aisha ta zo shi tun bai da ko sisi, amma mamarsa taki yarda, wai ba zai auri bazawarar da ta yi haihuwa biyu yana matashinsa ba. Shi kam ya je ya faɗawa babansa aka je aka nema mashi, a taƙaice dai mamarsa bata yarda ba........ Ni ina can kullum ina waya da Abba babu wanda ya sani a gida. Ranar da daddyna ya baiwa Ibrahim ni, Hajiyarmu ta kirani ta sanar mun, wato sai da na ji kaina ya wani irin bugawa, muna gama waya da ita na kwanta a gado ina tunanin yadda za'ayi da wannan al'amari, sai ga kiran Abba ya shigo wayata, jikina duk a mace na ɗauka. Ina ɗagawa ya ce. "Matata kin san me?".......... Da kyar na iya cewa. "A'a"....... Ya ce........ labarin A'isha zai dinga zuwa maku labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi. FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥 LABARIN AISHA.🥹💔 PART 35 & 36 "Matata kin san me?".......... Da kyar na iya cewa. "A'a"....... Ya ce. "Yanzu zan bar kauye, faɗa mun abubuwan gargajiyar da kike so in zo maki da su". Ji na yi gabaɗaya na rasa me yake mun daɗi, muryata a ɗan raunace na ce. "Bana buƙatar komai"........ "Subhanallah, me yake damunki?". Da alamar damuwa a muryansa yai maganar. Na amsa da. "Babu komai nawan, kawai sai ka dawo, barci nike ji". Bai gamsu da amsa ta ba, sai ya sake cewa. "Please mana, zaki ɗaga mun hankali, zaki sanya in kasa sukuni in kasa samun natsuwa, please menene yake damunki?"........ Sai kawai na fashe mashi da kuka, damuwa sun mun yawa na rasa ya zan yi....... Innalillahi wa inna ilaihi rajiun ya furta tare da fara tambayata, ji yake tamkar yai tsuntsuwa ya gansa gani ga shi. Cikin kuka na ce. "Ni ma ban san me yake damuna ba, kawai na ji ina son in yi ta kuka ne"........ Ya sauke ajiyar zuciya duk da bai gamsu da amsa ta ba, in a cool way sosai ya ce. "Ko dai kewata kike yi ne?"....... Kawai na ce mashi e dan in rabu da shi. Ya ce. "To ki kwantar da hankalinki gani nan zuwa gareki, goben nan zaki ganni". Na amsa da okey kawai, ya dinga rarrashina har sai da na yi shiru, sannan ya kyaleni muka yi sallama. Na kwanta ina tunanin rayuwata, makomata da yadda zan gudanar da ita. Ibrahim kuwa, ya sake dawowa cikin rayuwata da karfinsa, har da cewa next week zai zo ya canza mun gida, dan yanzu daddy ya bashi ni, ba zai bari ina zama kusa da wani can ba. Ni kam jinsa kawai nike, amma bana tare da shi sam, coz damuwar dake kaina ta zarce tunani. Haka Yah Abbas yai kwanakinsa biyar a tare dani, tun da ya zo shi yake kaini school, idan mun fita class na kirasa ya zo da motar benenmu ya ɗaukeni mu dawo, har ranar da zai koma shi ya kaini school, sai da na dawo muka rakashi airport, dan jirgin yamma zai bi. Bayan mun ra shi airport ni da Zahra jirginsu ya ɗaga ne muka dawo gida. Muna shigo na wuce ɗaki domin rage kayan jikina, coz tun da Yah Abbas ya zo ƙasar nan nike ta fama da manyan hijabs dan tarbiyar gidanmu kenan. Tun a parlo na cire hijab ɗina, wandon jeans fari tas ne a jikina, sai t-shirt maroon color, na nufi ɗaki ina cewa Zahra. "Idan Muhammad ya tashi barci ki ce kada ya kuskura ya zo ya tasheni zan kwanta ne". Zahra dake ƙoƙarin kunna kallo tana murmushi ta amsa da okey kawai, dan tasan confirm sai Muhammad ya je ya tasheni tun aikinsa ne ya zama addabar masu barci, shi kuma zai yi barcinsa lafiya lou. Ina shiga ɗakina nai ido huɗu da Abba zaune kan gadona. Mamaki yasa na zazzare idanuna a kansa, muryansa a sanyayye ya ce. "Idan takwara bai zo ya tasheki daga barci ba, daddynsa zai hanaki barcin ma gabaɗaya"........ Na yi blinking eyes ɗina two times dan tabbatar da shi ne ko ba shi bane. Tabbas shi ne, already yasan password na buɗe kofar side ɗina, dan ranar da muka yi shopping tare muka kawo kayan, watau shi ne muna fita shi kuma ya shigo ko?. Na ƙariso cikin, zuciyata cike take tab da kewansa, ya Salam, ya ƙara canza mun, ina begen ganinsa amma sai na basar wai dan ma kada ya ga kamar na damu da shi, a ɗan dake na ce. "Yaushe ka shigo mun gida?". Na faɗa ina shirin zama a saman drawer gefen bed. Da sauri ya jawoni jikinsa, ya zaunar dani kan cinyansa yana faɗin. "Ga kan cinyan mijinki ina kuma kike neman wucewa ki zauna?"...... Da sauri na buge hannunsa da ya ƙankame cikina da shi, na ce. "Abba ka bari mana"....... Ya kai hannunsa ya matse ɗan bakina game da cewa. "Lokacin ya yi da zaki daina ce mun Abba, as from today my name is your baby ko your honey, dan na tabbata ma na fi zuma daɗi". Ya kai karshe yana kashe mun ido ɗaya. Na dallah mashi harara game da cewa. "Abba, please mu bar irin wannan abin, dan ALLAH ina ɗana? Yaushe ka dawo?"...... Ya nisa game da cewa. "Ɗanki na gida, na zo ɗaukarki ne ki je ki gansa"..... "Meyasa baka zo da shi ba?". Na tambaya a ɗan dake. Ya amsa da. "Bashi da lafiya ne sosai, ana bashi kulawar likitoci ne, ba zai yiwu in ɗaukosa ba, tun kwanaki biyu da suka wuce nike ta son in zo in ɗaukeki in kaiki wajensa, amma Yah Abbas yana nan shiyasa ban zo na ɗaukeki ba"........ Mamaki ne ya ɗan kamani, watau tun kwanaki biyu da suka wuce ya dawo, shi ne bai zo ba kuma bai faɗa mun ba, kai Abba sai shirin ALLAH. Na ce. "To mu je ka kaini in gan shi please"........ Ya ɗan sumbaci kumatuna, cikin sanyin murya ya ce. "Faɗa mun me yake damunki kwanaki biyun nan ko na kiraki bana samun kanki sosai? Meyakefaruwa?"....…..... "Ba komai". Na faɗa ina turo baki. "Zama ki faɗa mun ne, bari mu je gida". Ya faɗa yana yunkurawa zai miƙe dani a jikinsa, da sauri na bar jikin nasa ina sauke ajiyar zuciya. Ya karɓi hijab ɗin hannuna ya sanya mun a jiki, ya riko hannuna kan mu tafi. Muna fitowa na ce da Zahra ina zuwa, bari in je in dawo. Abba ya bini da wani irin kallo mai kama da zakiga dawowa ne. Zahra ta ce okey, Abba ya ce ina takwaransa, na ce mu bar shi yana barci, ya ce mun a'a kada ya tashi bai ga mammynsa ba ya fara kuka,

Chapter 29 of 38