ce zan zagi bakinka ne? See you, you like too much of talking-talking, chop-chop kawai".
Hussain ya fara dariya, Abba ya hararesa tare da cewa. "Kada ku fita ko parlo ne, ina zuwa"........ Hussain ya ce. "Uncle daddy wani waje zaka je?"........ "Yeah, but not far, ba zan jima ba zan dawo, don't go anywhere, koda cikin gida ne"....... Hussain ya amsa da okey safe journey, Hassan dai bai tanka ba, kuma yana jinsu shiryayyen.
Abba ya nufo parlo. Da sauri ya ƙariso in da nike, na gagara cigaba da tsayawa tuni na kwanta a ƙasa. Ƙoƙarin buɗe kofar ya yi, amma ina taki buɗewa, ba yadda bai yi ba. Daga karshe ya tsugunna a gabana, cikin sanyin murya ya ce. "Aunty, kofar taki buɗewa, and na buga har na gaji babu wanda ya amsani, babu kowa a gidan ne?".
Na ɗago kai, cikin tsananin ciwo na ce. "Abba kenan ka yarda da maganar Abbie shiyasa ka rufe kofar da gangan?"..... Ya kalleni cike da rashin fahimta kafin ya ce. "Ban gane ba, wani maganar Abbie kenan?".
Na rintse idanuna zafafan hawaye na bin gefe da gefen fuskarta, da kyar na iya cewa. "Dan girman ALLAH Abba kada ka ci amanata, ka yi hakuri ka buɗe mun kofa, ni in kuna so ma daga yau zan bar maku gidan in koma gidan iyayena, dan ALLAH Abba kada ka mun abin da yayanka ya ce".
Shi kam bai fahimceni ba ko kaɗai, sai ya zaci zafin ciwo ne ya sanyani sambatu, dan haka sai ya miƙe tare da ɗagani cak, a kan sofa ya kwantar dani. Duk da ina cikin tsananin ciwon ciki na yi ƙoƙarin tirgewa da ya zo ɗagani, amma bai kulani ba, dan ya zaci na fara fita hayyacina ne.
Ya sake komawa jikin kofar bayan ya kwantar dani, ya fara ƙoƙarin karya kofar, sai dai ina, ba kofar da zata karyu yadda yake zata bane, ya yi iya yinsa ko motsawa kofar bata yi ba, ya dinga bugawa, babu wanda ya zo ya buɗe mana. Windows na parlon duk ya bi ya buɗe ya leƙa, babu ta yadda za'ayi mu fita, salati ya dinga yi a ransa. Daga karshe ya dawo kusa dani a kan sofar ya zauna.
Yana zama na ce. "Dan ALLAH Abba kada ka taɓani, ka dubi girman ALLAH ka buɗe mun kofa"........... A natse ya ce. "Please Aunty ki yi shiru, ki daina magana, kina cikin zafin ciwo"........... "Ni ba wani zafin ciwon da nike ciki, ni dai dan girman ALLAH kada ka mun komai"........ Cikin rashin fahimta ya ce. "Wai Aunty wani irin komai kike ta faɗin kada na maki? Shin dama na taɓa yi maki wani abin ne?".
Da kyar na waro idanuna a kansa, bibbiyu nike kallonsa saboda zafin ciwo. Hawayena na cigaba da zuwa daga idanuna na ce. "Ni dai ka mun alƙawarin ba zaka mun komai ba"....... Har yanzu yana tunanin zafin ciwo ne kawai, sai ya ce. "To na yi alƙawarin ba zan maki komai ba, yanzu dai ki yi shiru bari in maki tofin addu'oi tun da ba hanyar fita, In Sha ALLAH nasan zaki samu lafiya".
Kai kawai na jinjina mashi tare da mayar da idanuna na rintsesu........ Ya ɗan zubawa fuskata idanu kafin a hankali ya fara karanto addu'oin yana tofa mun..... Wannan shi ne abin da yasa ALLAH ya karemu a wannan ranar, da confirm sai Abbie ya ci galaba a kanmu, amma zaman da Abba yai yana mun addu'oin nan ya kore duk wani shaiɗanin dake wannan ɗaki.
To bari mu ji asalin waye Abbie da dalilinsa na yi wannan abin dukka. Abbie dai shi da kansa ba zuwa wani waje yake ba, shi da kansa mai bugun ƙasa ne, watau malaman duba kenan, tun yana ɗan shekara 18 yake bugun ƙasa, a wannan buge-bugen kasan nasa ne ya ce ya ga taurarin Aisha suna da tsananin haske da nasara a rayuwa, dalilin kenan da yasa ya yi tsubbace-tsubbacensa na malaman tsubbu sai da ya aureta, ya tsubbace babanta ya ce lallai sai shi za'a baiwa ita, Aisha tana secondary school a lokacin, baiwar ALLAH a lokacin take tasowarta, tana tsakanin ƴan uwa da iyayenta, tana karatunta cikin kwanciyar hankali da farinciki, rana tsaka babanta ya ce sai ya aura mata ɗaya daga cikin yaran shagonsu.
Hajiyarsu Aisha taki yarda, amma babanta ya kafe, a takaice dai sai da aka yi wannan aure, Abbie tun asali ba son Aisha yake yi ba, nasarar da ya hango a tattare da ita yake so, amma da suka fara zaman aure ya fara sonta ko in ce sha'awarta dan jikinta yake so har yanzu. To aurensu da shekara ɗaya watarana yana buge-bugen kasansa ya sake bugo taurarin ƙaninsa Muhammad Abba, a lokacin Aljanun dake bashi amsa a bugun kasan suka ce mashi idan ya haɗa Abba da Aisha waje guda lallai yana tare da nasara har sai lokacin da suka yi nisa da juna, wannan dalilin yasa ya ɗauko Abba, a da kwata-kwata bai damu da rayuwan Abba ba, tamkar ba ɗan uwansa ba, amma tun da ya bugo taurarin yaron suna da haske da karfi, akwai nasara a tattare da shi, daga nan ya mai da hankali kan Abba sosai.
Aisha ta ce bata son shi ba zata zauna da shi ba, sai ya haɗata da wani aljanin da ya nitsar da ita, ya kuma cusa mata son Abbien ta karfin tsiya, to shiyasa ta hakura ta zauna, kuma ta so shi alhalin ba son ALLAH bane, yau da za'a raba Aisha da wannan aljani, babu wanda ta tsana a rayuwarta biyun Abbie, ya rabata da Ibrahim ɗinta, ta so Ibrahim tamkar zata yi hauka, shiyasa ta tsani Abbie kamar me, yai amfani da aljannun dake mashi aiki ya dasa mata son shi. But tsakaninta da Abba ba wani aljanin da ya haɗasu, shaƙuwa ce saboda tun asali Aisha tana da kyan zuciya, and Abba ma haka, yana da kyan zuciya, jininsu ne ya haɗu matuƙa.
Lokacin da Abbie ya haɗa Aisha da Abba gida guda, tabbas ya ga nasarar kamar yadda aljanun nasa suke faɗa mashi, yana samun kasuwa sosai har yai shaguna manya-manyan har uku, sai dai kuma duk lokacin da Abba da Aisha suka yi faɗa, to ranar baya samun ciniki a kasuwa saboda ya yi imani su ne nasararsa da arzikinsa, shiyasa baya son su yi faɗa, kullum ya zauna da su ya dinga masu nasiha kan su kaunaci juna su haɗa kai, abin takaici kuma mugun ilimi garesa Abbien, dama kun san malaman tsubbun nan sai sun yi karatu, suna da ilimi sosai suke take sanin, to haka Abbie yake, yana da ilimi sosai da sosai, idan ya fara janyo aya zaku zaci limamin babban masallacin jumma'a ne, nan kuwa kasurgumin ɗan tsubbu ne. Tsawon shekaru bai taɓa bari an san yana bugun ƙasa ba, kowa kallon mutumin kirki yake mashi, to ya kware wajen janyo aya da hadisi ne ɗan banzan. TO KUN JI A TAƘAICE KENAN ABIN DAKE WAKANA, ABBIE BA SON AISHA YAKE YI BA, NASARARTA YA HANGO SHIYASA YA AURETA.
---------------------
A yau wannan addu'a da Abba ya dinga yi shi ya hana aljanun da suke yi wa Abbie aiki shiga jikin Aisha da Abban su birkitasu su sanyasu aikata abin da Abbie yake so, ɗakin ma ya gagari aljanun shiga, dole suka tsaya a bakin kofa.
Abba ya dinga tofa mun addu'a, tun ina jinsa har barci yai awon gaba dani. Da ya fahimci na yi barci sai ya dakata da yin addu'ar, a hankali ya zame ya sauƙa daga kan sofar, ya zauna a ƙasa a gabana. Slowly ya kai hannunsa kan nawa hannun dana dafe ciki, ya zame hannuna daga kan cikin zuwa ƙasa, ya ɗan gyara mun kwanciya dan kar wuyana yai ciwo. Ya zauna ya dinga kallona tunanuka kala-kala a ransa.
Da yake ina jin tsananin yunwa sai barcin bata yi tsawo ba, ban fi mintuna 30 ina barcin ba na farka. Da wani azababben yunwa na sake farkawa, ina waro idanuna sai kan fuskan Abba dake ta faman kallona ya gaza ɗauke idanunsa.
Da sauri na zabura na mike, sai na hau tattaɓa jikina ina tunanin ko ya mun wani abin ne, ya bini da kallon mamaki, na dawo da kallona kansa nima, a firgice na ce. "Abba me ka mun?"........ Ya lura na firgice dayawa fa, sai ya ce. "Aunty, please menene yakefaruwa?".
"Amsa mun tukun nan, me ka mun?"..... "Kamar me kike tunanin zan maki ne wai? Ni kin sakani a dubu, ban gane ba?". Ransa a ɗan ɓace yai maganar, coz ya ji haushin yadda nike ta mashi wannan tambaya tun ɗazun, har ya fara zargin wancan abin nike cewa kada ya mun, gabaɗaya sai ya ji ransa ya yi baƙinƙirin.
Ganin haka yasa na ce. "Sorry nawan". Sai kuma na daidaita natsuwata. Ya sake tambayata me yakefaruwa ne, na ce mashi babu komai. Ya wurga mun kallon tuhuma kafin ya ce. "Ina wayanki bari mu kira yaya ya zo ya buɗe mana kofa".
Ina kallonsa na amsa da. "Wayanka dai, ni wayata yana wajen yayan naka, ina naka wayar?"........ Ya ɗan girgiza kai. "To fah, lafiya yaya ya karɓi wayarki kuma ya karɓi nawa? Yau kwanaki uku kenan wayata tana hannunsa"....... Nan fa na ji gabana ya faɗi rass, innalillahi wa inna ilaihi rajiun, kenan dukkanmu Abbie ya kwace mana wayoyi, ya salam
Ganin na yi shiru yasa ya ce. "Aunty meke going ne?"......... Na dawo da kallona kan gashin kansa. "Uhm, ni dai Abba yanzu yunwa nike ji, kaga wannan ciwon cikin dukka yunwa ce, please abinci nike so".......... Yana ta mamakin meyasa yau gabaɗaya tun da na shigo naki ce mashi nawan da na saba, sai sunan shi nike kira.
In a cool way ya ce. "Iya ledojin cin-cin ɗin su Hassan ne a ɗakin nan, sai chips da ayaba da na ɗauko a fridge na kitchen ɗazun".... Muryarta har tana rawa wajen cewa. "Ni ka kawo mun koma menene zanci, yunwa nike ji sosai". Idanuna suna kawo ruwa nai maganar......... A natse ya miƙe ya shige cikin room ɗinsa.
Yana shiga Hussain ya ce. "Uncle daddy welcome"........ Abba ya wuce wajen kayan ciman nasu, ya fara ɗebosu yana faɗin. "Baka yi barci ba babyna?"........ Ya sauko kasan gadon, da sauri ya zo ya rike Abba yana faɗin. "I'm waiting for you ka dawo mu yi barci tare ne". Shi dai Hassan ya yi barci abinsa.
"Oya mu je parlo mammy na can"....... Sosai Hussain ya fara murmushi. Abba yai gaba ya rufa mashi baya. Yana ganina da gudu yai kaina yana oyoyo mammyna. Abba yai saurin rikesa da hannunsa da ya riko ayabar yana faɗin. "Mammy ba lafiya kada ka je ka haye mata jiki ka karisa gawar da ba namu ba".
Hussain ya zazzaro ido. "Mammy me ya sameki? Uncle daddy ciwo ta ji ne?". Tamkar zai yi kuka ya faɗa....... Abba yana ajiye kayan a ƙasa kusa da sofar da nike kai ya amsa da. "No, ciwon ciki ne, keep quiet, mammy bata son hayaniya".
Hussain ya haye kan sofar yana toshe bakinsa da hannu wai dan ya yi keeping quiet ɗin, sai da ya haye sofar ne ya kama hannuna, da muryansa har yanza bata fita ras sosai ya ce. "Ayya mammy sannu, ALLAH zai baki lafiya, ki yi addu'a, malamin islamiya ya ce idan baka da lafiya ka gayawa ALLAH damuwarka zai baka sauƙi cikin gaggawa, ki yi da taƙawa da iklasi"........ Abba ya ce. "To Al-Shaikh Hussain, mammy ma ta je islamiyar kafin ka je, maza sauko kada ka dameta".
Bawan ALLAH ya kuwa sauko daga sofar, ya haye jikin Abban yana faɗin. "Uncle daddy amma mammy zata samu sauƙi ko?"..... Abba ya sumbaci lallausan cheek ɗinsa game da cewa. "Mah boy mammy zata samu sauƙi yanzu ma kuwa, je ɗaki ka kwanta"....... Ya ɗan tsuke fuska. "Uncle daddy ka bari in zauna da mammyna ina kallonta, bana son tafiya ɗaki, I want to pray for her har ta zamu sauki a nan".
Abba ya rungumesa sosai yana manna mashi zazzafar sumbata. Intently ya ɗago ya kalleni. "Sauƙa ki ci abincin kin ji!". Ya faɗa yana shafa kan Hussain.
Kawai sun mugun burgeni ne da na gansu haka, sai na ji dama ace Abba ne mahaifinsu mana, sun fi son shi sun fi sabawa da shi. A hankali na sauƙo, cin-cin ɗin na fara kai hannu zai ɗauka, Abba ya rigani ɗauka, dama yana jiran in zaɓi abin da zan fara ci ne sai ya buɗe mun. Ya yage ledar cin-cin ɗin ya miƙo mun. Na karɓa na fara ɗauka ina kaiwa baki.
Na ɗago kai sai na kalli Hussain nata kallona, na ce. "Baby zai ci ne?"...... Ya girgiza mun kai alamar a'a kafin ya ce. "No mammy, kece baki da lafiya, kici sosai dan ki samu lafiya"........ Na ɗauki guda ɗaya na kai bakina, na gutsira rabi, sai na turawa Hussain rabin a ɗan bakinsa dake irin nawa sak. Murmushi ya saki mai ƙayatarwa kafin ya fara taunan cin-cin ɗin, sannan ya ce. "Mammy is so sweet da yazamana kece kika bani, ya fi na ɗazun da muka ci Sweet, akwai albarka a hannunki mammy".
Na ce. "Baby ɗan bakinkan nan ya iya magana, yanzu kuma waye ya koya maka wannan magana?"....... Ya turo ɗan bakin nasa kafin ya ce. "Mammy kada fa ki zagi bakina, because uncle daddy said my mouth is so beautiful, kuma ya ce yana kama da naki and he said........."..... Abba ya katse shi da cewa. "Oya jeka kwanta tun da ba wanda yake tambayarka kake faɗan abubuwa". Yana magana yana satar kallona.
Na bisa da kallon tuhuma, na fara dawo cikin hankalina da kyau tun da na ji abu a shiga cikin cikina, cike da tuhuma na ce. "Abba me ka faɗawa boy?"........ Ya ce. "Babu komai, kai jeka kwanta dare ya yi".
Na kamo Hussain, na jawosa jikina zan tambayesa, da sauri Abba ya janyesa yana faɗin. "Kada ki hurewa yarona kunne ki ɓata mun tarbiyyar da na jima ina yi, and baby wuce ɗaki, jeka kwanta"....... Hussain ya mike yana kallon Abba, yaron nan yaƙi yarda mu haɗa ido, na so mu haɗa ido in mashi raɗa yaki juyowa saboda Abba ya hure mashi kunne, ya riga ya koya masu sun yi hadda.
Ina gani yaron nan ya shige ɗaki. Na dawo da kallona kan Abba, na watsa mashi kallon tuhuma kafin in ce. "Abba ka koya masu wani hali ko?"....... Ya girgiza mun kai alamar a'a...... "To yanzu faɗa mun me kacewa Hussain dangane da bakina? Zagina ka yi ko?"......... Ya ce. "Kawai fa ce mashi na yi bakinsa mai kyau irin na mamansa, amma shi sai shegen surutu da iya zaro zance, while mamansa kuma ba haka take ba, iya abin da na ce".
Na wani hararesa tare da cewa. "No, ban yarda da kai ba, kawai faɗa mun ainahin abin da ka ce, na san ba yabona ka yi ba, zage mun baki ka yi, in yabo ne ba zaka hana Hussain faɗa mun ba"........ Ya ɗago manyan idanunsa a kaina kafin ya ce. "Da gaske yabonki na yi, amma da gaske ne ba yadda na faɗa yanzu bane, amma ki bini bashi zan faɗa maki". Ya kai karshe tare da ɗauke kallonsa daga kaina.
Zan yi magana ya rigani da cewa. "Please kada ki sakani faɗar dole, zan faɗa ki bini bashi"......... Na jinjina kai kawai, na cigaba da ɗaukar cin-cin ɗina one by one ina kaiwa baki. Ta ƙasan ido ya dinga kallon yatsun hannuna yadda nike ɗaukar cin-cin ɗin.
Na fahimci yana kallona, sai na zaci ko cin-cin ɗin ne ta mashi kyau yake son ci, dan haka sai na ɗauki ɗaya na miƙa mashi, ɗan ɗago ido yai a kaina, na ɗan lumshe mashi idanu alamar ya karɓa. Aikuwa rankwafowa yai yasa bakinsa ya karɓa instead of hannunsa. Ya ɗago ido muka kalli juna, na ɗauke nawa kallo, ban yi magana ba na cigaba da cin cin-cin ɗin.
Unexpected na ji muryansa can ƙasa ya ce. "Ashe Hussain gaskiya ya faɗa, cin-cin ɗin da daɗi amma idan ke kika baiwa mutum da hannunki, to me sirrin dake hannun naki?". Yai maganar yana ɗan kwantar da kansa a jikin sofar, ya wani zuba mun ido.
Na dawo da kallona kansa kafin in ce. "Dama ai da kai da yaran naka duk halinku ɗaya"...... Ya ɗan yi one sided smile bai yi magana ba, ni kuma na cigaba da cin cin-cin ɗina. Can ya ce. "Please a ƙara mun".
Na miƙo mashi har da ledan, sai yaki karɓa, na kallesa sai ya ɗauke kai, kome ya tuna sai kuma ya miƙa hannu ya karɓa. Ni kam na jawo ayabar na ci guda biyu, sannan Abba ya kawo mun ruwa na sha.
A takaice dai yau a ɗakin na kwana, amma babu abin da ya shiga tsakanina da Abba, ya ce in kwanta a gadonsu, naki yarda dan hankalina bai kwanta ba, na ce parlo ya isa, da ya ce zai kwanta a parlo sai ni da yarana mu kwanta a gado, na ce a'a ya bani bargo in kwanta a nan. Haka ya kawo mun bargon, na kwanta kan sofa doguwa, ba jimawa nai barci, da dare ta tsala Abba ya dawo parlo, dan hankalinsa yaƙi kwanciya su suna ciki ni ina nan, sai ya zo ya kwanta kan two seater ya bar su Hussain a parlo.
Washegari shiru-shiru ba'a zo an buɗe kofa ba, abin tun yana bamu mamaki har ya fara bamu tsoro, kuma muka dinga bugawa aka ki kulamu. Wasa-wasa sai da muka yi dare biyu a cikin wannan ɗaki, daga karshe Abba ya yanke shawarar fasa pop na ɗakin ya haura sai ya sauƙa ta wajen ɗakin ya duba wai ko ba kowa a gidan ne sai mu kawai.
Na yarda da shawararsa, muka ciro karfen curtain na ɗakin, da shi ya dinga bugawa pop ɗin har ya fasata ta wajen kusa da gini ta jikin window. Ya hau kan window ɗin sannan ya sake fasa pop ɗin da kyau kafin ya samu ya haye sama. Na samu wajen saman sofa na zauna, su Hassan suka dinga damuna zasu fita waje, duk cin-cin na ɗakin mun cinye su saboda rashin abinci, Hussain ya dinga kukan yunwa.
After 30 mins da fitan Abba sai ga shi ya buɗe kofar ɗakin ya shigo. Da sauri su Hassan suka yi kansa, cike da mamaki nike tambayarsa ina ya samo key ɗin. Sai ya ce mun. Ya shiga cikin gida yana ta faman neman key ɗin, ya duba Abbie baya nan, duk wahalar da ya sha ashe key ɗin tana jikin kofar ta baya, da aka rufemu sai aka bar key a jiki, sai da ya zo zai duba ko akwai yadda zai ɓalla kofar ta waje ne sai ya ga key a jiki.
Da sauri na mike na fito daga ɗakin ba tare da na mashi magana ba. Kai tsaye cikin gida na wuce, ga mamakina sai ban ga Zainab a gidan ba, babu kowa kenan, na shiga ɗakina. Wanka na fara yi kafin sallolin dake kaina, sannan na yi zaman tunanin yadda zan yi in sanar da gida abin dake faruwa. Ina wannan tunani har aka kira magrib, na tashi na yi sallah.
Bayan na yi sallar ishai na fito dan girka mana abin da zamu ci. Na girka mana shinkafa da stew. Around 9:30 na kammala, na kira su Abba muka haɗu a babban parlon muka ci, sai raha muke yi, bayan mun kammala ne na ce ya sanya su Hassan su yi barci ya zo mu yi magana. Ya amsa da to ya ɗaukesu suka fita, na yi niyyar faɗa mashi duk abin dakefaruwa dan mu nemi mafita a tare.
Aikuwa yana fita sai ga Abbie ya shigo, da sauri na miƙe na taresa ina faɗin ya bani wayata in kira gida kuma ya bani key ɗin gate. Ya wani mun kallon rainin wayau kafin ya ce. "Idan har kina son in baki, sai kin mun abin da nike so, in kuma ba haka ba, tabbas zaki rasa farincikinki na har abada, kuma ki sani duk wani abin da kike so sai na salwantar da shi muddin baki mun abin da nike so ba".
Rass gabana ya faɗi, cike da tashin hankali na fara mashi magiya, aikuwa yaki saurarata, ya wuce ɗakinsa, da gudu na bi bayansa, wannan tsautsayi na bin bayan nasa da na yi ita ce babban kaddara a rayuwata, ina shiga ɗakinsa ya rufe kofa, ina ta mashi magiya ya yi hakuri ya barni, ba zan iya aikata zina ba, zinar ma da ƙaninsa wlh ba zan yi ba. Ina magiya ya sanya igiyar da ban san daga ina ya samo shi ba, ya ɗaure mun hannuna da kafafuna, da naga kamar cutar dani zai yi sai na fara ƙoƙarin ihu, ya rufe mun baki da tsumma, ya ɗaukeni sai cikin toilet ɗinsa. Ina ganinsa ya ajiyeni cikin jaccuzi ya fice abinsa.
Na yi kuka babu mai jina, na yi danasanin biyosa da na yi, na ɗauka abin da sauƙi zan iya jura, haka na kwana cikin banɗakin, Abba ya dawo bai ganni a parlo ba, da ya ga motar Abbie a gidan sai ya zaci muna tare, dan haka ya koma ɗakinsa.
Wasa-wasa kwanaki biyu suka shuɗe ina cikin toilet, ba ci ba sha, ba wanka babu komai, kuma duk dare Abbie zai shigo yai wanka ina ganinsa, amma ko kallona bayayi, abu ɗaya yake tambayata shi ne na amince da buƙatarsa, idan na girgiza kai alamar a'a baya sake kulani yake ficewa, ba sallah ba cin abinci, ko ruwa bai barni ina sha ba, hannu da kafata a ɗaure haka ma baki, kuma zai rufe kofar toilet ta baya da key, sannan ya rufe kofar ɗakin ma.
Kwana biyu Abba bai ganni ba yau da safe ya shigo cikin gida, ya dubani ko'ina bai ganni ba, kuma bai ga Zainab ba, hankalinsa ne ya fara tashi, yai shiru yana tunanin ranar da muka kwana a ɗakinsa, yadda nike rikice ina cewa kada ya mun komai, da yadda Abbie ya kwace wayoyinmu, daga nan ya fahimci akwai matsala, sai ya koma ɗakinsa domin neman mafita.
Ni kuma a daidai wannan lokaci azaba ta ci karfina, yunwa yai mun illah, ga ƙishin ruwa, hakan yasa numfashina ya ɗauke, a cikin jaccuzin na suma, tun daga wannan rana kuma ban sake sanin in da kaina yake ba, ban sake sanin komai ba.
Ban san ya akayi kome ya faru ba sai buɗe idanuna na yi na ganni a..............
labarin A'isha zai dinga zuwa maku labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi.
FATEEMA ZAHRA MUSA
A-K-A
QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥
LABARIN AISHA.🥹💔
PART 23
Ban san ya akayi kome ya faru ba sai buɗe idanuna na yi na ganni a wani ɗaki mai kama dana asibiti, na fara wuwwurga idanuna ina ganin sassan ɗakin, amma sai naga babu alamar mutane a ciki. Na runtse idanuna ina karanto addu'oin da suka zo bakina, ga ƙarin ruwa da aka mun.
Na kai kamar mintuna ashirin da farkawa sai na ji an buɗe kofar da nike ciki ɗin, da sauri ya buɗe idanuna. Ido huɗu muka yi da babban yayana, wani irin double ajiyar zuciya na sauke tare da yunkurawa zan miƙe. Da sauri ya kariso yana kada in tashi, ya rikeni ya mai dani na kwanta.
Ina son in yi magana amma na gagara, ina ta kallon yayana da likitoci suna jele a kaina, amma ban samu damar tambayar me yakefaruwa ba. Sai da na ƙara kwanaki biyu a haka, a rana ta ukun ne aka sallamemu, Yayana ya ɗaukeni zuwa gida har lokacin na gaza buɗe baki in yi magana, abin sai yai ta bani mamaki, ina kuma jin abin da mutane suke faɗe. Wasa-wasa har muka koma gida bana iya magana, ina son sanin ina yarana? Ina mijina? Ina Abba? Duk babu mai amsa mun saboda ban iya
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 18 Chapter of 38