Share this page
Kasan zaka iya sanya zuciyata ta buga ko? Irin wannan dawowar bazatan?". Na kai karshe tare da waro fararen idanuna a kansa. Ya yi folding hands ɗinsa a kirji, yana tsaye a bakin kofar shigowa, ga katuwar akwatinsa a gefensa, yana sanye da kayan kwallo, ya ɗaura jacket a sama, wlh ya kara kyau sosai, ya kara cika da kwarjini. Ina waro idanu sai cikin nasa da yake ta faman kallona, da sauri ya sauke idanunsa tare da nisawa, a hankali ya sake hannayensa, ya kama akwatinsa tare da karisawa ciki, sai da ya zauna a kan kujerar kusa dani, ya sake sauke ajiyar zuciya kafin ya ce. "Bazata nike son yi maki, shiyasa ban faɗa maki ba". Na ɗauki pillown dake kusa dani na jefesa a fuska ina hararansa. Ya capke pillow ɗin a kan fuskansa tare da zamesa a hankali, ya ɗan kalleni ta gefen ido ƙasa-ƙasa...... "Ina zaki je da kika sha wannan haɗuwa?". Unexpected na ji muryansa a kunnena, na ɗago dan na ji ba da wasa yai tambayar ba. Na amsa da. "Shopping da wajen gyaran jiki"......... Ya ɗan zaro ido, sai kuma ya ce. "Wannan jikin har sai an wani gyarasa kuma? So kike ki wuce gona da iri ko?" "Ka dawo kenan zaka fara saka mun takunkumin da ko yayanka baya saka mun ko?". Abba akwai iya sakawa mutum takunkumi, wani lokaci zan fita ma ya hanani wai sai gobe kamar shi yake aurena. Ya amsa da. "To ai amanarki yaya ya bani, yanzu ma babu in da zaki je, kawo kalar man da kike shafawa zan je in sayo maki da kaina, dama ai nine ɗan aikanki, na dawo babu in da zaki sake fita"........ Ina hararansa na ce. "Eyyeee, to baka isa ba, idan ka sayo mun mayukan shafawana shi kuma gyaran jikin fa?"......... Ya ɗan rungume pillown da na harbesa da shi a kirji tare da cewa. "Sai in ɗauko mai gyaran jikin ta zo ta maki a nan, amma da gaske babu in da zaki je". Ya faɗa babu wasa a tattare da shi, dan ma in san da gaske yake yi. Na miƙe tare da ɗaukar wayata, na kira Abbie, yana ɗagawa na ce. "Zan je sayan man shafawa". Ya amsa da sai na dawo. Na kai hannu zan ɗauki Muhammad Abba yai saurin ɗaukesa yana faɗin. "Please my Aunty, dan ALLAH ki hakura ko dan dawowa da na yi". A ɗan shagwaɓe ya faɗa yana sauke idanunsa ƙasa. "Nawan ALLAH na rigada na yi niyyar zuwa, kawai ka bari in je"....... Ya ɗan jinjina kai. "Mu je in kaiki to, bari in ɗauko key ɗin motar"......... Na ce. "A'a nawan, yanzu ka dawo, ka je ka huta, ba zan jima ba zan dawo sai in zo in maka girki". Ya miƙe da Muhammad a hannunsa, ya ja akwatinsa bai yi magana ba, cikin ɗaki ya shige, jim kaɗan ya fito hannunsa rike da keyn mota, ya wuce gaba yana muje. Na bi bayansa, ya buɗe mun gidan gaba na shiga, kai tsaye muka bar gidan, ko ta kan Zainab dake ɗakinta bamu bi ba, ita ma tana can tana murzan kuka na yunwa, bata san me zata saya da 500 ta girka ba, Mama ta yi wa Abbie magana ya ce bashi da kuɗi Zainab ta yi hakuri idan kasuwa ya buɗe zai kara mata ko Naira 100 ce yazamana 600 zai dinga bata, ni kam ko a jikina ato. Kai tsaye wani katon shopping mall muka shiga da Abba, yana parking ya fito rungume da Muhammad ya tasani gaba, da na ce ba zan wuce gaba ba ya ce ban isa ba in wuce mu je, dole muka jera zuwa ciki. Duk in da ka yi yana biye dani, sai wasa da Muhammad yake yi, ina son sayan underwears amma ina jin kunyar ɗauka a gabansa, sai kawai na fasa sayansu, musamman breziya, har na zo wajensu na ɗan tsaya sai kuma na fasa saya, akwai wani fari da ya mun mugun kyau yana haɗe da pant ɗinsa, na so ɗauka amma kunyansa yasa na hakura na wuce gaba, shi dai sai wasa da Muhammad yake yi, bai mai da hankali kan abin da nike ɗauka ba. Na sha wata kwana zan je wajen mayukan shafawa kenan muka ci karo da wani. Kwandon kayan hannunsa suka watse, ina ɗago kai zan mashi sannu ba sai naga Ibrahim bane. Da mamaki na kallesa tare da cewa. "Sorry please"....... Na faɗa zan raɓa gefensa in wuce kenan ya ce. "A'isha, Aesh, meyasa kike guduna har haka ne? Ai sai ki tsaya mu gaisa tun da ba gaba muke yi ba ko?". Cikin sanyin murya ya faɗa, yana cikin shigar kaftan ta kamala wacce ta fito da kyansa na fulani. Ina ƙoƙarin amsa mashi Abba ya rigani da cewa. "Saboda me zata tsaya ku gaisa? Kana da alaƙa da ita ne?!". In a harsh way ya faɗa, ya tamke fuska tamkar ba nawan ba. Ibrahim ya ce. "Oh sorry". Ya faɗa da tunanin cewa Abba ne mijina. Ni kam da sauri na wuce, duk sai na ji sayayyar ta isheni, jikina ya mutu, sabon son Ibrahim ya dawo mun. A guguje na ɗauki mayukans dan mu bar wajen. Muka je wajen biya ga mamakina sai na ga Abba ya bada ATM ɗinsa wai a cira, ban yi magana ba, na bari sai mun je gida ya faɗa mun in da ya samu kuɗi..... Aka zuba mana komai a leda Abba bai barni na ɗauka ba ya ɗauka muka wuce mota, kai tsaye na ce wajen gyaran jiki da ƙunshi zai kaini. Bai amsa mun ba, ya haɗe rai kamar hadari, tun da ya yi wa Ibrahim wancan maganar har yanzu bai saki ransa ba. Na bashi address na wajen gyaran jiki, still bai amsani ba. Har muka isa, yana parking ya fito, na ce mashi maza basa shiga ciki, bai mun magana ba har sai da ya je ya leƙa cikin ya tabbatar ba maza, sannan ya dawo cikin mota yai zamansa rike da Muhammad. Ni kam na wuce ciki ina mamakin wannan uban haɗe ran fa?...... Shi kuwa ya zauna, almost 4 hours yana zaune, ya ciro wayansa sai hira da Safiyya suke yi, bai faɗa mata yana Kano ba, ya dai barta a sai jibi zai dawo, coz yana son yi mata bazata ita ma. Muhammad ya fara kuka yana neman nono, dole ya ɗaukosa ya nufi cikin wajen. Yana shigowa ya tsaya can idanunsa a kaina, ana shafa mun mayukan kai a gashina, an gama mun gyaran jiki da red and black henna mai musulmin kyau wanda ya kara fito da kyauna, gani fara tas, ya salam, ni da kaina nasan na haɗu ba karya. Abba ya dinga kallona ni ban ma san ya shigo ba, musamman gashin kaina dake bakinkirin har gadon baya, ga shi ya sha gyara sai sheƙi yake yi. Ɗaya daga cikin ma'aikatan wajen ne da ta ga ya tsaya cak yana kallona sai ta ce..... labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi. FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥 LABARIN AISHA.🥹💔 PART 17 Abba ya dinga kallona ni ban ma san ya shigo ba, musamman gashin kaina dake bakinkirin har gadon baya, ga shi ya sha gyara sai sheƙi yake yi. Ɗaya daga cikin ma'aikatan wajen ne da ta ga ya tsaya cak yana kallona sai ta ce. "Yallaboi lafiya?". Da sauri ya ɗauke kansa daga kallona, sannan ya matsa ya miƙo mun Muhammad, sannan ya juya ya fita bai yi magana ba. Ya koma cikin mota ya zauna, ya kifa kansa da jikin steering, sai faman sauke ajiyar zuciya yake yi. After 30 mins da dawowansa na fito daga cikin wajen, tamkar wanda yai barci, bai ga fitowana ba, yai nisa a cikin tunani, sai da na shigo cikin motar, ya ji rufe kofar ne ya ɗago kansa, idanunsa sun kara ciza ja sosai tamkar ya fara barci. Ya ɗan saci kallona ta wutsiyar ido kafin ya nufi tada motar. Sai kuma ya dakata, ya buɗe kofar motar ya fita. Cikin wajen gyaran gashin ya shiga, jim kaɗan ya fito hannunsa rike da ATM card ɗinsa. Yana shigowa cikin motar na ce. "Nawan, wai yanzu yaushe ka je ka yi payment na gyaran nan? Na je biya wai ka biya, dama ATM ɗinka ka basu ne?". Kai kawai ya jinjina mun bai yi magana ba. Na sake cewa. "Nawan wai a ina ka samu kuɗi, ka kashe kuɗi sosai wajen shopping, a nan ma haka, ina ka samu kuɗin"........... Ya cire password na wayansa tare da shiga kan sms sai ya miƙo mun wayar, ina karɓa ya tada motar bai yi magana ba, kuma bai sake ɗagowa ya kalleni ba. Ina shiga naga alert na kungiyarsu ta kwallon kafa ce ta biyasu kuɗi, coz yana cikin zakarun da suka ja ragamar wasan, ya samu kyaututtuka sosai da sosai. Na ɗaga ido na kallesa kafin in ce. "Bawan to sai ka karar da kuɗin dukka a kaina? Ba zaka sayi wasu abubuwan bane? Ga su Mama, and na ji ana cewa Hummaira zata yi aure, akwai abubuwan da zaka yi da kuɗi sosai, kai da Abbie ne kawai maza, kuna da ƴan uwa mata sosai, kada ka manta tamkar mahaifinsu kuke yanzu, and ga su Ummin Aunty Farida kannen Khalifa, duk sun tasa aure nan ba da jimawa ba, kaga bai kamata ka dinga kashe mun kuɗinka ba". Yadda kuka san da steering motar nike yi, bawan ALLAHN nan bai amsani ba, yana driving yana ɗan dafe kansa, ciwo take mashi sosai, na so sake tambayarsa me yake damunsa, amma na share saboda naga bai amsa tambayar farkon da na mashi bama. Kai tsaye gida muka wuce. Yana parking a gida ya buɗe motar ya fito. Ya buɗe gidan baya ya ɗauki kayan da muka saya, ya nufi ciki. Na fito na bi bayansa, a parlo na iskosa tsaye, ya ajiye kayan a tsakar parlon, ya ɗan riko waist ɗinsa da hannayensa. Ina zuwa na ce. "Ka je ka huta bari in yi mana girki". Ya miƙa mun hannunsa alamar in bashi wayansa bai dai yi magana ba, kuma taki ɗagowa muga juna. Na miƙo mashi wayansa, ya karɓa, kamar zai juya, sai kuma ya tsaya, yai ƙasa da murya, a natse sosai ya ce. "Duk waɗan da kika lissafa a ɗazun babu wanda ya tsaya mun a lokacin da nike fafutukan neman cinwa burina, duk cikinsu babu wanda ya taɓa taimaka mun da Naira ɗaya, kome zan zama a rayuwa kece sula, da kuɗinki, da lokacinki, da damarki, kina da damar komawa makaranta kika zaɓi in koma, duk wata wahalata ke kika sha shi, idan har zan samu kuɗi, to ki sa a ranki naki ne, kafin kowa ya ci sai kin rigasa, ke ta daban ce a rayuwata, ba zan taɓa mantawa dake ba, sunanki ba zai taɓa fita daga bakina ba a lokacin yin addu'ata, ina maki fatan alkhairi a kodayaushe tawan". Ya kai karshen maganar tare da juyawa. Na jima ban ga ɗan halak irin Abba ba a rayuwata, na bi bayansa da kallo, lallai ɗan halak baya manta alkhairi, duk abubuwan da na mashi wlh na mance ma da na mashi su a rayuwarmu, amma shi suna ransa, tabbas a lokacin na zaɓi ya koma makaranta ni in hakura dan a lokacin ba zai yiwu mu koma mu dukka ba, duk na manta da wannan ma, ashe shi yana nan a ransa. Na zauna a zauna a kan kujera ina ta mamaki, na yi wa yayansa abin da ya ninka wanda na mashi sau goma, amma daidai da rana ɗaya Yayansa bai taɓa ce mun even ALLAH yai maki albarka ba, sai dai idan muka samu ɗan saɓani ya ce bana tausaya mashi, hmmmmm rayuwa kenan. After 20 mins ina zaune na miƙe na shiga kitchen, haɗaɗɗen abinci na girka mana mai rai da lafiya, yau ina fashin sallah, so ina gamawa na tsara wanka sosai, na shirya cikin wani doguwar riga da babban yayanmu ya kawomun zuwansa Makkah last year, sai tashin kamshi nike yi. Na duba time 2:30, na fito daga bedroom ɗina rike da Muhammad, shi ma na mashi wanka tas da shi. Ina fitowa sai ga Abba ya fito daga nasa ɗakin hannunsa rike da key ɗin mota. Baki a ɗauke da sallama Fahad ya shigo parlon, yana ganin Abba ya ce. "Kai, kawu yaushe ka dawo". Abba ya saci kallona ta wutsiyar ido kafin ya ce. "Ɗazun". Ya faɗa tare da wucewa zai nufi waje. Fahad ya ce. "Sannu da dawowa ya hanya?"........ Abba bai amsa ba, ya yi wanka ya canza kaya zuwa ƙanana jeans and t-shirt, ya nufi ficewa, da sauri Fahad ya ce. "Kawu bani key ɗin motar na dawo zan je in ɗauko su Hassan ne daga school". Can ƙasa Abba ya ce. "Bari in ɗaukosu". Ya faɗa ya fice ko juyowa bai yi ba. Fahad ya kalleni, cikin girmamawa ya ce. "Ina wuni Aunty"........ Na amsa da. "Lafiya lou, kaga ubansu ya dawo ya huttasheka ɗaukosu"..... Yana ɗan murmushi ya ce. "E wlh, bari in koma shago"....... Na ce. "A'a, tun da ka zo ga abinci nan, idan ma kana sauri kasa a kula ka je da shi". Ya amsa da okey ya gode, a saka mashi a kula, na amsa da to, na matsa na zuba mashi abincin a kula, sannan na koma na zauna a kan kujera ina jiransu Abba su dawo mu ci abinci, azumi ya kawo kai, ana ta shirye-shirye, na yi zama rubuta kayan abincin da zan sayawa dangin Abbie da mabuƙata, na shirya komai na kammala kamar yadda aka saba, har na sanya yayana ya biya kuɗin, coz sadaka zan yi, baya hanani sadaka da kyauta, dan shi ne sirrin arzikina, sadaka na yelwata arziki sosai, jama'a ku lizimci yinta zaku ga daidai sosai. A wannan lokaci Abbie ya shigo parlon a fusace, ɗakinsa ya wuce tun kafin in yi magana, na bi bayansa da kallo ko a jikina, ban tashi na bi bayansa ba. Ina zaune ya fito, a saman kujera ya zauna tare da cewa. "Jeki kawo mun abinci". Ya faɗa tare da ɗago kai ya kalleni, ya wani ɗan zaro mun idanunsa, ya ga na haɗu, na sha gyara, skin ɗina yana wani irin sheki sosai, ga henna da na sha, ya Salam, na haɗu na karya, gagara ɗauke kallonsa daga kaina yai. Sai ya ce. "Ki kawo mun abincin ɗaki"...... Kamar zan ki bashi abincin in ce ban dafa ba kayan abinci ya kare, amma da na tuna iyayena basu koya mun hakan ba, kuma shima yana daga cikin sadaka, sai na miƙe na nufi dining area ɗinmu. Ya wani bini da mayen kallo, yana jin tamkar ya jawoni jikinsa. Ni kam tsabar iyashege har da kara jujjuya mashi mazaunai na dan ko ban juyo ba nasan yana kallona, saboda nasan halinsa sarai. Gabaɗaya lokaci guda ya birkice, ya fara haɗiyar yawu, maƙogwaronsa tana wani sama ta sake yin ƙasa, da sauri ya miƙe ya wuce cikin ɗaki. Na zuba mashi abinci na bi bayansa ɗaki, na ajiye mashi saman carpet na gaban bed ɗinsa, na ɗauko mashi ruwa da cup, na juya zan fita ya ce. "Habibiya waye zai ciyar dani kenan?". Yana zaune a gefen gado. Na wani kallesa bayan na juyo, na ɗan taɓe baki kafin in ce. "Sodangi mana, ba part ɗinta zaka koma ka ci ba, coz naga ba a nan kake ba".......... Ya ce. "Ban gane me kike nufi ba"........ Na bisa da wani kallo mai kama da na rainin wayau kafin in ce. "Wai Abbie yanzu kwanakinka nawa rabonka da side ɗin nan?". Cikin kwantacciyar murya saboda yana son abi a wajena ya ce. "Kefa kika ce in zauna a side na Zainab na wata huɗu, shi ne kuma kike jin haushi dan ban zo wajenki ba?"...... Na yi wani irin murmushin kafin in ce. "Awwww ALLAH? Abbie kenan, amma da na ce ka zauna a side nata sai na ce da ciyarwarmu dake kanka duk ka haɗa ka mayar da shi kanta kenan ko?". Ya girgiza mun kai tamkar kara min yaro alamar a'a. Na ce. "Right, yanzu ma dan ALLAH ka koma side ɗinta, dan sai mun cika alƙawarin watanni huɗun nan"...... Da sauri ya ce. "Matsalata dake kafiya habibiya, dan ALLAH bar dukka wannan magana, zoki ji wata magana"......... "Ina jinka". Na faɗa ina tsayem Ya sake yin ƙasa da murya wajen cewa. "Please Habibiya ki zo jikin mijinki sai in faɗa maki"......... Na girgiza kai. "A'a ni ba zan zo gaskiya, hakan cin amanar matar so ce watau sodangi"......... Da sauri ya ce. "Amma Habibiya kin san matsala shi ne kike hukuntani da raunina a kansa ko? Kin san da cewa ALLAH yana tsinewa duk macen da mijinta ya nemeta taki yarda ko?". Na saki murmushin takaice game da cewa. "Haka zalika ALLAH yana tsinema mai karya alƙawari, alƙawari muka yi da kai zaka kasance a ɗakin matar so a wajenka na wata huɗu, dan haka sai waɗan nan kwanaki sun cika, ka je ta kwantar maka da buƙatarka mana, duk abin da nike da shi tana da shi, awww na manta na ta fini, ka ce a wajenta kawai kake gamsuwa, sannan idan ka ga kirjinta kawai kana jin ka biya, ni da bani da su, ni da nawa suke ƙanana me zaka yi da su? Ka manta ka ce mata ta fi komai daɗi a duniya? Duk ka manta waɗan nan kalamai? Ka mance ka ce mata baka taɓa gamsuwa ba ka matsu ta shigo dan ita kaɗai zata gamsar da kai, ka manta ko? To ni ban manta ba, ka je ta gamsar da kai, ni da bani da komai, and idan ka cika matsa mun billahil lazi zan jingine auren nan tun da dama ba wajibi bane sunnah ce!". Ina kai karshe na juya na fita, hawayen da nike ƙoƙarin dannewa suka cika mun ido, amma ban bari ya gansu a idona ba, sai da na fita ɗakin suka fara zubowa. Jikinsa yai wani irin mangariba bama la'asar ba, ya ji tabbas bai kyauta ba, shi da kansa yasan wlh ba wata mace da yake gani feeling ɗinsa ta motsa sai ni, wlh ko zai kwana da Zainab tana tsirara sha'awar tasa baya tashi, amma ni da zarar ya ganni abar zata motsa mashi, ni'imata dana Zainab daban-daban, tabbas Zainab tana iya jure ko sau goma zai yi, amma matsalar bata taɓa bashi gamsuwa ne, yana yi ne kawai dan lafiyar jikinsa, ni kuma kalar ni'imar da ALLAH ya mun sau ɗaya idan ya yi zai samu gamsuwa, amma saboda ni'imata sai ya kara dan bala'i irin nasa, son zuciya ce da ruɗin soyayya yasa ya dinga faɗan abubuwan da ya faɗa wa Zainab, yanzu ya shiga nadama. Jiki a mace ya sauƙo ƙasa ya fara cin abincin da ta zame mashi dole ci, yunwa yake ji sosai, ga shi ya ganni abar ta tashi, sai ta haɗe mashi biyu. Ni kuwa ina fita na shiga ɗakina, na ɗan yi kukan huce haushi kafin in shiga toilet, na wanke fuskata na fito, a parlo na zauna tare jawo wayata. Daidai lokacin Abba da su Hassan suka shigo, ai yaran nan yau ko kallona basu yi ba small daddynsu ya dawo, ɗakinsa suka bisa da gudu, ina kiransu suna gudu wajensa. Ina zaune anjuma suka fito da uban niƙi-niƙinnkaya a hannunsu, suna sanye da sabbin sportswear a jikinsu, da alama shi ya saya masu. Zazzaro ido na yi ina tambayansu. "Wannan kayan fa"...... Hassan ya fi iya magana shi ne ya ce. "Uncle daddy ne ya ce mu kawo maki"....... Basu ƙariso in da nike ba suka daɗi saboda ledojin kayan ya fi karfinsu. Da sauri na tashi na taresu ina mamakin wannan uban kaya haka ne da me a cikin ledojin? Watau tsaraba aka kawo mana, shi kuma Abban yana ɗaki a kwance. Da sauri ya hau buɗe ledojin, su kuma suka juya da gudu suka koma ɗakin nasa......... A tunaninku me uncle daddynau Hassan ya kawo mana matsayin tsaraba? Me a waɗan nan ledoji? labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi. FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥 LABARIN AISHA.🥹💔 PART 18 Da sauri na tashi na taresu ina mamakin wannan uban kaya haka me da me a cikin ledojin? Watau tsaraba aka kawo mana, shi kuma Abban yana ɗaki a kwance. Da sauri na hau buɗe ledojin, su kuma suka juya da gudu suka koma ɗakin nasa. Ina buɗe leda na farko na ga wasu kyawawan dogayen riguma, outfit na mutanen South Africa ne, ɗayan ledar wannan atamfa nasu mai kaman zanen tabarman ne har guda uku a ciki, atampan fa yana da mugun tsada, amma har uku ya saya mun. A ɗaya ledar culture dress ɗinsu ne a ciki, sai abin wuyansu na culture mai shigen na tabarma, da abin hannu, sai kuma abayas guda biyu. Kayan sun yi matuƙar kyau sosai da sosai. Ya Salam, kyauta ta farko dana fara samu daga dangin Abbie kenan ta hannun Abba, da kuɗinsa ya saya mun ba da kuɗina ba, wlh ba zan iya misilta tsananin daɗin da na ji. Na kwashi kayan na kai ɗaki, na dawo zan zauna kenan Hassan ya fito tare da cewa. "Mammy uncle daddy ya ce ki bashi abincinsa in kai mashi zai ci a ɗaki"....... Na ɗan yi mamaki, amma ban takura ba, na zuba mashi a plate, na rakasa bakin kofa sannan na bashi dan kada ya zubar, sai na ce ka ce Hussain ya zo ku ɗaukawa uncle daddyn naku ruwa da lemu and cups. Ya shiga yana amsawa da okey. Na koma dining area na zauna, na hau cin abincina a natse ina tunanin mafita wa rayuwata. Jama'a bana son labarin Aisha yai tsawo, ni da a part 10 na so ya kare, amma kunga ya zarce damu har muna neman ashirin, na yi iya kokarina in taƙaita labarin amma ban samu yadda nike so sosai ba duk da ina katse wasu abubuwa, dan haka yanzu ma bari mu ɗan ja labarin dan mu gama shi in the next 10 days masu zuwa In Sha ALLAH. Washegari Abba ya shirya tun sassafe ya mun sallama ya tafi Kaduna, kwanansa biyu a can ya dawo, a ranar da ya je Safiyya ta kirani tamkar zata yi hauka wai Abba ya zo har sun zauna sun gana da Hajiyarmu, kuma ya kawo mata tsarabar kaya masu kyau, ta dinga murna tana jin daɗi. Sai dai muna yin sallama da ita sai ga kiran Hajiyarmu ya shigo, na ɗauka a natse, bayan mun gaisa ta ce. "Aisha ban san baki da hankali ba sai yau"....... Na ce. "Hajiya Mammy lafiya? Me na yi?"......... Hajiya ta dinga faɗa sosai kafin ta ce. "Saboda rashin hankali da ƙuruciya na ɗawainiya dake sai ki haɗa alaƙa tsakanin ƙanin mijinki da Safiyya? Ke kanki yaushe kika fita daga cikin ukubar danginsu? And ke kanki ba har ruwa muka kai rana da daddynku kan bana son ki auri mutumin nan ba ya matsa sai kin auresa? Me a cikin dangin nasu banda gayyar marasa tarbiya marasa hankali?". Wani irin ciwo na ji a raina da Hajiya tana zagin Abba, na dinga bata hakuri, na yi ƙoƙarin fahimtar da ita Abba ya sha banban da danginsa, amma ta ce bata son jin komai daga bakina, kuma ta gayawa Abba ya rabu mata da ɗiya bata so, ya kuma ce In Sha ALLAH zai fita harkarta, dan haka kada in sake gigin haɗasu bata so, in ba haka ba zata sassaɓa mun. Wlh na yi kuka a wannan rana ba

Chapter 13 of 38