kallona daga kan Abba, saboda yau idanunsa sun mun wani irin kaifi, idan ina kallonsa ina jin wani irin spark a cikin zuciyata, a raina nace ko dai shima haka yake ji shiyasa baya son kallona ne?.
A fili kuma na ɗan yi murmushi kafin in ce. "Awwwww, yanzu ne nike da anfani ko? Ni zaka yi wa wayau nawan? Ni zaka yi wa daɗin baki? To ba zan shiga case da babu ruwana ba"............. ALLAH buwayi gagara misali, watau ALLAH yana fitar da rayayye daga cikin matacce, ya kuma fitar da matacce daga cikin rayayye, duk gidansu Abba gayyan ƴan bin malaman tsubbu ne, mushirika ne, sun yarda da zancen bokaye fiye da faɗar ALLAH, kuma abin da zai baku mamaki ilimin addini garesu kamar me, Abbie idan ya fara janyo maku aya da hadisai sai kunyi mamaki, amma basu da tauhidi da iklasi, duk cikin gidan Abba ne kawai ya fita daban, shi ne kawai ALLAH kaɗai ya rike, bai ma san me bin bokaye yake nufi ba, bai ma yarda da wasu bokaye ba.
Duk abin da kake yi a duniya confirm shi zaka ga kamar wani yana aikatawa, meyasa Mama take cewa lallai bokaye Aisha take bi? Saboda abin da take yi kenan, wlh duk abin da kake yi shi zaka ga kamar kowa ma yake yi, shiyasa makaryaci baya taɓa gasgata maganar mutane, dan gani yake karya mutane suke mashi, saboda ya saba yi shi, haka munafuki baya taɓa yarda ya sake da mutane sosai, domin yana ganin kamar suna munafurtansa, shi kaɗai zai dinga tsarguwa yana binciken abokansa ko suna munafurtansa, duk ya takura kansa, haka magulmaci, magulmaci baya taɓa yarda da mutane, dan zai ga kamar suna zaginsa a bayan idanunsa, to haka rayuwa take, idan kuna son sanin asalin waye mutum, to ku saurari kalamansa, idan kuka ji yana yawan karyata mutane, to shararren makaryaci ne, idan kuka ji yana yawan cewa a wane ba dan ALLAH yake zaune dani ba, yana munafurtata, to tabbas shi ne munafukin, haka idan kuka ji yana ni ai bana yarda da mutane, saboda maciya amana ne magulmata, to shi ne maci amana magulmacin!. ALLAH yasa mu dace mu fi karfin zuƙatanmu
-----------------------
Ya ɗan marairace mun fuska. "Please mana tawan, ai nasan ba zaki bar burina da wahalarki su tafi a banza ba, zan yi biyayya"........ Na ɗan hararesa. "Zaka yarda kai ƙanina ne?". ........ Ya ɗan cukule fuska, sai kuma ya wurga mun wani irin kallo mai wuyar fassaruwa, yana ɗan tattauna gefen lips ɗinsa, a natse ya ce. "Jariri ne ni ba ƙaninki ba".
Dariya ne ya kubce mun, dan yadda yai maganar kai innalillahi, Abba sai shirin ALLAH........... Ya zuba mun ido yana kallon yadda nike dariyar dake kara mun kyau, can na ɗan tsagaita kafin in ce. "E fa, gaskiya ka faɗa, kai jariri ne, dama kuma kani a wajen yayyunsa ai shi tamkar baby ne, ɗan yaro kawai"............. "Awwww yanzu kin yarda ni babynki ne?".
Na jinjina kai ina murmushi. "Kai kam ma kafi baby, babys kamar su Hassan ne, kai kuma treating ɗinka kamar Muhammad zan yi, kaga ka wuce baby".......... Ya ce uhm yana sauke ajiyar zuciya, sai kuma ya sake cewa. "Nine baby ko?"......... Na jinjina kai ina kallonsa, sai kuma na ce. "Na faɗa maka ka wuce baby fa, ka yarda da hakan sai in samu Abbie in lafaza maka shi, ka yi biyayya".
Ya ɗan jinjina mun kai, can ƙasa-ƙasa ya ce. "Na yarda, amma na yarda ni baby ne a wajenki kawai, na miƙa wuya, to yanzu please a rokanmun shi"............. "Dama ai nawa ne bana kowa ba, zan roka maka shi, amma fa da sharaɗi ɗaya"....... Yana ta kallon kyawawan yatsun kafafuna da nike ɗan motsasu a hankali ya amsa da. "Wani sharaɗi kenan?"......... "Idan ka je ba zaka dinga jimawa ba zakana dawowa da wuri, shi ne sharaɗin".
"Meyasa?". Ya tambaya yana dawo da kallonsa kan fuskata. "Saboda muna kewanka sosai idan baka nan, su Hassan su yi ta damuna da kukan rashinka, nima bana jin daɗi, dan dai babu wanda zan je in yi wa kukan ne da nima kuka zan yi irin nasu Hassan"......... Ya ɗan ɗage gera guda. "Wai da gaske dama kewata da kuke yi har ta kai haka? Dama kuna sona sosai har haka?".
Na hararesa kafin in ce. "Fin hakan ma, kasan yadda muke sonka kuwa?"..... Ya motsa lips ɗinsa tamkar zai yi magana, sai kuma yai shiru yana ɗan kakkauce mun, like bashi da gaskiya.
Na ce. "Lafiya?"........ Ya girgiza kai alamar a'a, amma bai yi magana ba. Zan sake magana sai ga Hussain ya fito yana faɗin. "Uncle daddy I'm feeling hungry". Yana magana yana mutsuke idanunsa dake duk barci, yana turo baki irin shagwaɓar uncle daddyn nasa, yana sanye da sportswear a jikinsa, duk Abba ya ɓata mun yara da sanya kayan wasanninsu.
Da sauri Abba ya buɗe mashi hannu, ya zo ya faɗa jikinsa, Abba ya ɗaga shi sama ya ɗauka kan kirjinsa, ya sumbaci kumatunsa kafin ya ce. "Me kake son ci babyn daddynsa?"......... Ni kam na saki baki ina kallonsu, watau tsananin son da Abba yake yi wa su Hassan har mamaki yake bani, ya fi ubansu Abbie kaunarsu, coz Abbie zai iya kwanaki uku bai gansu ba, kuma baya damuwa ya tambayeni ina suke, idan zai shigo gida sau goma, to ko sau ɗaya ba zaku ji ya tambayeni ina su Hassan ba, sai in ya samesu a parlo suna wasa ne ya shafa kansu ya wuce.
Suma kuma idan Abbiensu ɗin zai shigo gidan ko oyoyo basu damu su yi mashi ba, amma kuma Abba na shigowa, ya salam, har wani rige-rige suke yi, suje su rungumesa, idan fa suka ce ba zasu ci abin da na dafa ba Abba da kansa yake dafa masu abin da suke so, gaskiya shaƙuwarsu da kaunar da yake masu har mamaki yake bani wani lokaci.
Hussain ya ce. "Uncle daddy rice and beans with stew and egg I want"....... Abba ya kalleni, a natse ya ce. "Mammy zamu ci rice and beans, a girka mana"....... Na hararesu game da cewa. "Kun ajiyeni ne da zaku wani tashi daga barci kawai ku ce ga abin da kuke so?".
"Awwww sai mun ajiye ki ne za'a bamu abincin da muke so?"..... Na jinjina masu kai alamar e mana. Ya ɗan yi kwafa tare da cewa. "A lallai to dole in ajiyeki, babyna zo mu je hai, da ace daddynka bai iya girki bane sai ta mana rigima, amma na iya, muje in girka maka". Ya miƙe ya ɗaukesa cak suka nufi waje. Ina ƴar dariya na miƙe na bi bayansu.
Ta kofar kitchen muna nufi shiga cikin gida, ƴan uwansu wasu suna zazzaune ta baya, sai magana suke ƙasa-ƙasa da suka ganmu, Abba ya ji su sarai, amma bai tanka ba, muka wuce ciki.
Abba ya rigani shiga, ina sako kai cikin kitchen ɗin muka ci karo da Amina, tana rike da katon tray na abinci sai ya kife, gabaɗaya ya zube a ƙasa, ya zube mun a kafa, ga abincin da zafi, ita ma ya zuba a kafarta.
Kara ta fasa tare da cire hannu zata mareni tana huci. Daga bayanta Abba ya rike hannun nata. Ai ja da baya ta yi ta cire kafarta cikin zafin, cikin faɗa ta juyo dan ganin wani shafaffe da mai ne ya rike mata hannu ya hanata marina. Nima baya na ja ina karkaɗe kafata, wani irin azababben zafi da na ji yasa na sunkuya a wajen.
Tana juyowa suka yi four eyes da Abba, ya tamke fuskan nan tamau tamkar bai taɓa sanin me dariya ba. Duk da yake ƙaninta sai da ta ji ta tsorata da shi, ya sake mata hannu ba tare da ya yi magana ba, ya nufi juyawa zai bar wajen kenan ta ce. "Abba, ina ruwanka dani da zaka shiga faɗar da ba naka ba? Baka ga ta ƙonani kuma ya zubar mun da abincina bane?".
Ko sannu bai ce mata ba, ya goya Hussain a bayansa tare da tsayawa a gaban gas na kitchen ɗin, ya ɗauko tukunya ya zuba ruwa, ya ɗaura kafin ya shiga neman wake, bai sake waigowa in da muke ba. Ni kam dana karkaɗe kafata na shigo cikin kitchen ɗin, ban yi mata magana ba nima, na nufi wucewa. Da sauri ta ce. "Uban waye zai kwashe abincin da kika zubar ɗin to?".
Na baiwa banza ajiyarta, dan ni kam su ba sa'anin yina bane, yayansu ne sa'an yina watau Abbie, na bar kitchen ɗin na haura sama zuwa ɗakina. Ban san ya suka kare ba, na kwanta na sha barcina, sai can yamma na farka, ina farkawa na ɗauki wayata kenan sai na ga saƙon Abba da ya tura mun tun ɗazun, na buɗe saƙon.
"Fatan dai baki ƙone a kafar ba, sorry, ALLAH ya kiyaye gaba"..... Mamaki ne ya ɗan kamani, coz na ga ai bai ganni ba, yana ta cikin kitchen ɗin, yaushe ya san abincin ya zube mun a kafa har na ƙone?...... Na ja siririn tsaki saboda tunani na neman mun yawa, na ajiye wayar, zan miƙe sai kuma na fasa, na dawo na ɗauki wayar, na rubuta mashi. Na ƙone kam har kafar ta kumbura. Haka kawai na tsinci kaina da rubura abin da ba shi ba, bayan ba wani kumburar da kafata ta yi, coz na ce bari in tsokanesa ne kawai.
Ina turawa na tashi na shiga toilet, ina shiga sai ga kiransa, wayar tana silent ban ji ba, na watsa ruwa na ɗauro alwala na fito. Sallah na yi sannan na sanya kaya, atampa ɗinkin 8 pieces sket da blouse, ɗinki ya zauna a jikina sosai, har an fara walima, mutane sun zozzo sosai, na ɗauki after dress na sanya a saman kayan, ban ɗaura ɗankwalin atamfar ba, sai dai na yafa mayafin after dress ɗin a kaina.
Na ɗauki wayata na nufo waje. Ina fitowa parlon sama na kalli Abba zaune a kan kujera, murya ta a sanyaye sosai saboda barci na ce. "Uncle daddy ya dai?"..... Da sauri ya ɗago kansa, a maimakon ya kalleni ya amsani sai ya fara kallon kafata. Ni kuma ina kallonsa.
Slowly ya ɗago idanunsa a kan fuskata. "Aunty, dama saboda ki tada mun hankali ne yasa kika ce kafarki ta kone ko? Ina ta kiranki kuma kika ki ɗaukar kira, to ina ƙunar yake?". Ya faɗa yana ɗan haɗe rai..... "Ban ga call ɗinka bane, na shiga wanka, batun kafa kuma wasa nike yi, ya dai yi ja amma bai kumbura ba"....... Ya miƙe yana faɗin. "Zan rama ne"...... A natse ya tako zuwa dab ni, sai ya sake kallon kafata da kyau, ya yi ja sosai saboda hasken fatata.
Ina dariya na ce. "Sai dai ka rame"..... Na dawo da kallonsa kan fuskata, bai yi magana ba ya juya ya nufi waje kamar wanda zai je ya duba wani abin.
Ni ma na nufi sauƙa ƙasa kenan sai na ji Abbie ya kirani daga ɗakinsa, ashe yana jinmu duk abin da muke cewa, ban yi tunanin yana gidan ba. Ɗakinsa na nufa, baki a ɗauke da sallama na shiga, yana ta faman safa da marwa a cikin ɗaki, har gumi yake haɗawa.
Cike da mamaki na kallesa, shi ma ya kalleni, na ɗan girgiza kai. "Abbie lafiya?".......... Kai ya girgzia mun kai alamar a'a, sai ya ce. "Babu lafiya Habibiya, ina cikin matsala, ke kaɗai ce kuma kawai zaki iya fitar dani wannan matsalar".
Na kariso ciki, a kusa da shi na tsaya game da cewa. "Abbie in dai nice zan fidda kai matsala kaddara ka fita kawai, faɗa mun menene yakefaruwa?"...... Hannayena ya riko cikin nasa, muka zauna a gefen gado, sai na ga ya kama ƴan kame-kame.
Na ce. "Ka faɗa babu damuwa, ko menene zan yi maka"....... Ya kalleni da kyau, sannan ya ce. "Nagode sosai habibiya, kuma nasan ba zaki bani kunya ba dama, kina iya ƙoƙarinki a kaina"...... Na ji daɗin kalamansa dan su ne na farko da ya fara mun kalaman yabo. Na jinjina kai game da cewa ya faɗa ina jinsa.
Ya yi ƙasa da murya wajen cewa. "Kada ki mun mummunar fahimta, ki fahimceni ta fuskan basira". ...... Na ce mashi okey ba damuwa....... Ya kara rike hannuna cikin nasa kafin ya ce. "So nike kusancinki da ƙaninki ya fi haka"..... Cikin rashin fahimta na ce. "Ban gane ba, ka mun bayanin yadda zan gane".
Ya ɗan matsa hannuna cikin nasa kafin ya ce. "So nike ki kwanta da Abba, sau ɗaya kawai, ta hakance kawai dukiyata zata dawo kamar da, zan ma fi da dukiya saboda taurari zasu haɗe ne sosai"........ A wani irin zabure na miƙe tsaye, take jikina ya fara rawa, na wani kallesa, muryata har tana sarƙewa wajen cewa. "Abbie anya kasan me kace kuwa? Ka ji abin da ka ce da kyau kuwa?".
Ya miƙe shima yana ƙoƙarin rungumata dan ya ga na tsorata, da sauri na ja da baya ban bari ya taɓani ba ina kallonsa, ya yi ƙasa da murya wajen cewa. "Please habibiya, wannan hanya ce kawai zata sanya arzikina ya dawo, idan taurari suka haɗu sosai, suka samu kusanci sama da yadda suke a da nasarata zata ninku fiye da yadda nike a baya, zamu samu arziki sosai Habibiya".
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun na dinga maimaitawa ya fi kafa goma, sai kuma na dawo da kallona kan fuskansa, tabbas yanzu na fara zargin Abbie baya sona, ba dan sona yasa ya aureni ba, take na fara tunano irin abubuwa da na dinga mashi kan ya sakeni a farkon aurenmu amma yaki, na wahalar da shi, masifa ba kalar da ban mashi ba kan ya sakeni yaki, kenan dama shi yasan meyasa ya aureni? Saboda yana ganin ni ɗin nasara ce? Taurarina suna da haske? Kai innalillahi wa inna ilaihi rajiun, a raina na ce to me hakan yake nufi. Coz ni ban san malaman tsubbu ba, ko da Mama take cewa na je wajen boka wlh ban san ya suke ba, ban ma san me ake gani a wajen ko me ake zuwa ace a wajen ba, shiyasa kwata-kwata ban gane in da Abbie ya dosa ba, sai nike ganin kamar sabon abu ya zo da shi.
Ya matsoni yana neman shawo kaina in amince, na janye kaina daga gare shi, na ce wlh ba zan amince ba, kuma ni ba zan taɓa aikata zina ba a rayuwata, In Sha ALLAH har na koma ga mahaliccina ba zan aikata zina ba. Ya yi iya yinsa naki yarda, tun daga wannan lokacin ma sai na fara gudun Abba, ko in da yake bana son zuwa, bawan ALLAH shi ma fa bai san komai ba, amma nike gudunsa, dan ina ganin kamar shi ma Abbie ya faɗa mashi abin da ya faɗa mun kuma shi ya amince shiyasa Abbie ya tunkareni da maganar, ban san bai sani ba.
Abbie ya ɗauki tsawon kwanaki yana bina ta lalama, amma na rantse mashi da girman ALLAH ba zan yi ba sai dai ya tabbata a matsiyacin talaka. Wataranar laraba da ya matsa mun ma na ɗauki Alqur'ani mai girma nai mashi rantsuwa da girman ALLAH kan ba zan yi ba, na ce wlh ko mutuwa yake yi ba zan yi ba, kai bama shi ba, ko mutuwa uban da ya haifeni yake yi a gabana kan in ban yi zina ba, to wlh sai dai ya mutu, amma ni kam ba zan saɓawa mahaliccina ba, ko kashe ubana za'ayi a gabana to sai dai a kashesa, dan nasan in an kashesa wajen wanda ya fi kowa adalci watau UBANGIJINMU zai koma, kuma ALLAH zai saka mashi. Dan haka ba zan yi ba!!.
Nan fa ya fusata ya ce dole sai mun haɗe da Abba dan nasararsa in ba haka ba wlh mu fuskanci uku ba, na ce ba uku ba ko uwar me zamu fuskanta sai dai mu fuskanta amma ni kam ban ga dalilin da zai sanya in saɓawa mahaliccina ba, idan ya ga dama ya kasheni ba uku ba. Nan fa ya kwace wayata, ya kwace duk wani abin da zai sanya in yi magana da wani ko wata, ya fita ya barni a ɗakin.
Na rushe da kuka ina jin tamkar na shiga ukuna, wani irin rayuwa ce wannan?. Ina kallonsa ta window ya shiga motarsa zai bar gidan, ga mamakina sai naga ya rufe gidan da kwaɗo, dan a yanzu bamu da mai gadi, and kunga ƴan uwansa sun koma bayan walima, gidan ya rage daga ni, sai Zainab, sai kuma Abba dake Bq tare da su Hassan.
Nan fa na gane to akwai matsala, me Abbie yake shirin yi kenan? Meyasa ya rufe mu a gidan to? Ina zai je da ya fita?. Na rasa amsoshin tambayoyina, na cigaba da murzan kukana tamkar zan haɗiyi zuciyata saboda tashin hankali.
Wunin ranar ko parlo ban fita ba, ga shi ba shiri muke da Zainab ba, shiyasa ko nemana bata yi ba, Abba ma yana ɗakinsa bai fita ba, dan shi bai ma san wainar da ake toyawa ba.
Jama'a abu wasa-wasa sai da na yi kwanaki uku ba waya, ban ga Abbie ba ban ga mai kama da shi ba, a kwanaki ukun nan na shiga tashin hankali, ga shi ina tsoron zuwa wajen Abba in rokesa wayansa saboda ina tunanin Abbie ya faɗa mashi abin da zamu yi kuma shi ya amince ni kawai ake jira, dan a tunanina tun da Abbie yayansa ne zai amince da maganarsa, kun san zuciya da saƙe-saƙe. Ban san Abba kam bai san komai ba, hasalima shi ma ya ɗan ja baya dani ne saboda tun ranar walimar nan da ya sameni kwance a parlonsa bai ji da daɗi a ransa ba, har mafarkina ya dinga yi, shiyasa ya ja baya dani, baya son ma muke haɗuwa sosai, ya daina shigowa cikin side ɗinmu.
Abbie kuwa, a ganinsa nice kawai zan bashi matsala, Abba dole ya karɓi umarninsa, to shiyasa ya fara ƙoƙarin tursasani, dan yana ganin da na aminta shikenan, Abba mai sauƙi ne.
Na shiga damuwa, ina ta kuka ina son kiran gida in faɗa masu abin dake faruwa, a wannan karon na yi alƙawarin faɗa masu komai, dan Abbie ya wuce tunanina yanzu kam, sai dai ba hanyar kiran gida. Yau yunwa tamkar zai halakani, kwanaki ukun nan duk ban da ruwa babu abin da nike ta faman sha, cikina har wani irin azababben ciwo yake mun. Duk kukan da nike yi Zainab na jina, amma yarinyar nan ko ta leƙoni, sai ma dariya da take mun, dan a tunaninta faɗa muka yi da Abbie ya ɓata mun yasa nike kuka. Abin mamaki kuma a waɗan nan kwanaki ukun dukka Abbie na dawowa cikin gidan, amma tsakar dare, a ɗakin Zainab yake kwana, shiyasa Zainab ɗin take mun dariya wai ina kukan miji ya barni, tana ta murna wai aikinta ne yai nasara.
Ta na ji zan iya mutuwa da yunwa sai na miƙe, ina dafa bango na fito, a lokacin karfe 9 na dare ya yi, da kyar nike taka kafata a kan staircase ɗin nan. Kitchen na sauƙo na shiga dan girka abin da zan ci. Sai dai ga mamakina na ga store ɗin a rufe da kwaɗo, ga shi babu komai a cikin kitchen ɗin. Hankalina a tashe na fara tunanin mafita, na dudduba fridge, suma duka a rufe da keys ɗinsu. Wani irin kuka na ji ya sake kubce mun, na sake fara dafa bango na nufi sama.
Ɗakin Zainab na buga, sai da na shafi mintuna biyu ina bugawa sannan ta buɗe. Da kyar na ce. "Bani key na store" ...... Ta bini da kallon walaƙanci kafin ta ce. "Ki tambayi Abba shi ya rufe ɗazun, ina ga ya tafi da shi"...... Na jinjina kai game da juyawa. Ina juyawa ta ce. "Yanzu ke saboda na kwace mijina ne kike wannan haukar tamkar zaki kashe kanki?".
Na yi banza da ita, na cigaba da dafa bangona ina tafiya, bana iya miƙewa sosai saboda azabar yunwa. Kai tsaye Bq na nufa. Kofar a buɗe, sai ka shiga, a parlo na tsaya tare da kiran sunan Abba ɗin. Yana kwance a kan gado, jin muryata yasa ya miƙe, ya sanya jallabiya a jikinsa, gently ya fito parlon.
Idanuna a runtse na ce. "Bani key na store". Coz na ji motsin fitowansa. A sanyayye ya ce. "Babu key ɗin store a hannuna, amma baki da lafiya ne Aunty?"....... Naki amsa mashi, ga wani irin jirin dake ɗebata, na ɗan matsa na dafa sofar kusa dani, da kyar na ce. "Ka bani key kawai". Na faɗa tare da waro idanuna waje.
Subhanallah, ai bai san lokacin da ya zaro idanunsa ba ganin yadda waɗan nan kyawawan fararen idanuna ɗin suka yi jajir da su, da sauri ya nufoni yana faɗin. "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, Aunty, baki da lafiya ne? Meyake damunki?".
Sai kawai na fashe da kuka, jikina ya tsananta kerman yunwa, na ji ba zan iya rike kaina ba, a saman sofar na zauna ina cigaba da kukan nawa. A kusa dani ya tsaya, cikin tashin hankali ya ce. "Aunty, please menene? Ko dai in kaiki asibiti ne?".
Kai na jinjina mashi, dan yanzu burina ya fitar dani daga gidan nan, da kyar na ce. "Abba, zan mutu, cikina na ciwo sosai, ka kaini asibiti"........ Hannayena ya riko yana faɗin. "To tashi mu je"........ Da kyar na miƙe da taimakonsa, na dafa hannunsa da kyau, ina jan kafafuna muka nufu kofar fita.
Sai dai ga mamakinmu muka ji kofar a rufe da key, da sauri ya duba wajen key ɗin dan ya buɗe, babu key a jikin kofar, kallona ya yi tare da cewa. "Da kika shigo kin rufe kofar kin cire key ne?"........ Kai na girgiza mashi. "A'a, a buɗe kofar ma take, turawa kawai na yi na shigo, ban san ya aka yi ta rufe ba".
Shiru ya ɗan yi, sai kuma ya ce.......
labarin A'isha zai dinga zuwa maku labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi.
FATEEMA ZAHRA MUSA
A-K-A
QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥
wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi.
FATEEMA ZAHRA MUSA
A-K-A
QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥
LABARIN AISHA.🥹💔
PART 22
Shiru ya ɗan yi, sai kuma ya ce. "Sakeni bari in duba wani key a ɗaki"....... Da kyar na iya sake shi, ya shiga cikin bedroom ɗinsa, Hassan and Hussain suna zazzaune a tsakiyar gadon suna wasa da kayan wasanninsu. Ya fara bincike ɗakin ta ko'ina yana neman wani key. Hussain sarkin manyance ya ce. "Uncle daddy what are you looking for?".
Abba ya ce. "This your big-big eyes I'm looking for"....... Ya turo baki. "Uncle daddy my eyes ai kama yake da naka, and kuma yana da kyau"..... Hassan dai ko kallon in da suke bai yi ba. Abba ya ce. "Who told you that? Ni idanuna basa wani kama da kai, and waye ya faɗa maka haka abu mai kyau yake? See that your small mouth sai magana"....... Ya faɗa yana bubbuɗe drawers na wajen gado.
Hussain ya ce. "Uncle daddy kai da bakinka ranar fa ka ce you really like my small mouth because it looks exactly like na mammyna"...... Abba ya ɗago ya kallesa, sai kuma ya ce. "Did I ask you?"...... Hussain ya saki dariya har dimple ɗinsa both sides suka lotsa sosai, sannan ya ce. "No Uncle daddy, but ai kai ne zaka zagi bakina shi ne na tuna maka you said my mouth is so beautiful because yana kama dana mammy and last time I saw you with my mammy.......... ". Katse shi Abba ya yi da cewa.
"Ba zai mun shiru a wajen ba? And ni na
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 17 Chapter of 38