magana ba.
Abin da ya faru shi ne, ranar dana suma, Abbie ya shigo yin wanka ya ga bana numfashi, shi ne ya ɗaukeni domin ya kaini asibiti, to dama Abba ya saka mashi ido saboda rashin yarda da shi da yayi, dan in baku manta ba Abba ya fara zargin akwai wani abin dake faruwa, shiyasa ya sakawa shige da ficen yayan nasa ido.
Abba yana ganinsa ta window ya ɗauko, ya nanneɗeni cikin bargo ya sani a bayan mota da nufin ya fita dani gidan. Yana fita kuma ya rufe gate na gidan. Aikuwa Abba ya fito ya rufe su Hassan a ɗaki ya hau ta katanga ya bi bayansa. Da yake Abbie na gudu sosai sai ya kusa ɓace mashi, Abba na fita bakin hanya ya samu abin hawa, ya bi bayan yayan nasa. Wani private hospital na kaini.
Da Abba ya ga in da ya shiga sai ya kyalesa ya nufi wajen motarsa, a lokacin Abbie yana cikin asibiti yana magana da likita, Abba ya yi sa'a motar abuɗe, Abbie bai rufeta ba saboda yanzu zai zo ya fita dama.
Abba ya fara bincike cikin motar, nan ya samu wayansa amma bai samu nawa wayar ba, ɗauke wayansa ya yi tare da barin cikin motar, ya koma gefe ya tsaya, sai kuma ya hau mashin ya koma gida. Yana komawa ba jimawa Abbie ya dawo, fitowa ya yi daga ɗakinsa, ya tambayi Abbie ina nike, sai Abbien ya ce mashi ai na tafi Kaduna, sai ya ce amma ya kira Safiyya ta ce bana Kaduna.
Nan Abbie ya fara kame-kame, daga karshe ya ce magana ta gaskiya na ɓata ne ana ta nemana, shi yanzu haka daga police station yake. Tsananin mamaki ne ya kama Abba, ai daga nan ya san akwai matsala, sai ya amsa da okey kawai. Abbie ya wuce cikin gida, shi kuma Abba ya koma ɗakinsa, ta ciro wayansa a caji.
Number Safiyya ya fara kira, amma taki ɗagawa saboda tana jin haushinsa. Ba shi da number kowa na gidanmu sai nata, rashin sani yasa taƙi ɗaukan kiran. Daga baya ya yanke shawarar tura mata saƙo, ya rubuta mata cewa sister ɗinta tana cikin matsala, please ta ɗauki waya magana yake son yi da daddynmu.
Aikuwa Safiyya ta ga saƙonsa amma taƙi buɗewa, saboda ta zaci hakuri zai bata, ya dinga tura mata saƙonni sun fi kala ashirin, amma yarinyar nan taki buɗewa. Daga karshe dole ya hakura ya kyaleta, tamkar zai yi hauka ya fara neman yadda zai samu number wani a gidanmu.
Can ya tuna yana da number Ahmad, da sauri ya kirasa, amma a kashe, hankalinsa a matuƙar tashe ya kira number shago, nan ma a kashe. Zarya ya fara yi a cikin ɗakin, sai uban haɗe gumi yake yi, har karfe ɗaya na dare, amma ya gaza samun number wani na gidanmu.
Can har ya fidda rai sai ga kiran Safiyya, zuciya bata da ƙashi, tana son Abba sosai, ta gagara share saƙonninsa shiyasa da ta kwanta zata yi barci, bayan ta gama chatting ɗinta sai ta ce bari ta duba saƙonninsa, ai tana dubawa ta ga abin da ya rubuta jikinta har yana rawa ta fara kiransa.
A lokacin da kiran ya shigo sai da ya durkushe a ƙasa saboda tsananin farinciki, jikinsa har yana rawa wajen picking, hankalinta a tashe ta ce. "Yah Abba ina Auntyn take?".
Muryansa har tana sarkewa wajen cewa. "Baiwa daddynku ko babban yayanku waya, zan faɗa maki in da take daga baya, dan ALLAH ki basu waya da sauri"..... Ai tun bai gama rufe baki ba ta diro kasan gadonta, da gudu ta nufi ɗakin babban yayanmu. Ta dinga buga mashi kofa a haukace, yana tsaka da barci ya ji wannan bugu, tashi yai ya zo ya buɗe. Ta matuƙar bashi tsoro yadda ta dinga bugu, ai kafin yai magana ta bashi wayar tana faɗin Yah Abba ne ƙanin mijin Aunty Aisha.
Babban yayanmu ya duba time wajen karfe ɗaya da rabi, ai daga nan ya san ba lafiya ba, karɓar wayan ya yi tare da karawa a kunne. Abba bai ɓoye mashi duk abin da ya gani da wanda ya sani ba, bai duba cewa Abbie yayansa bane ya rufe mashi asiri, ya faɗawa yayanmu komai.
Aikuwa yayanmu ya ce yanzu zai kamo hanya, ba zai iya jira sai da safe ba. Abba ya yi farinciki har da kwallansa, babban yayanmu ya ɗauki number Abban a wayansa, sannan ya ce Safiyya ta je ta kwanta. Ta sa mashi kuka sai ya faɗa mata me yakefaruwa, ya ce zai faɗa mata amma yana zuwa. Bai jira amsarta ya koma ciki ya rufe kofa, a cikin ransa yana ta kara jinjinawa uwa, domin kuwa tun satin ɗaya da ya wuce Hajiyarmu take ta ce mashi ita fa sai mafarki Aisha a cikin mawuyacin hali take yi, ta damu sosai, ya ce babu komai Aisha na lafiya, ko jiya sai da Hajiya ta ce mashi idan ta tuna Aisha tana jin faɗuwar gaba, ya ce ba komai ta mun fatan alkhairi, ashe ita tasan me take ji, kai jama'a ku ce uwa uwa ce, ita kaɗai ke fahimtar yaren ƴaƴanta ko suna tare da ita ko basu nan. ALLAH ka karawa iyayenmu daraja da kima game da lafiya da nisan kwana mai amfani.
Ya shirya a gurguje ya fito, ya shiga ɗakin Hajiya, sai ya same ta a kan dadduma tana sallah, ya jira ta idar, tana idarwa ta ce mashi. "Babana nifa tunanin ƴar uwarku ya hanani sukuni, yanzu haka mummunar mafarki na yi a kanta shi ne na tashi nike mata addu'a"...... Nan fa babban yaya ya kara jinjinawa uwa, dan yana da tabbacin addu'ar hajiyarmu a kaina ne ALLAH ya amsa har yasa suka san halin da nike ciki.
Yaya bai faɗa mata halin da nike ciki ba, sai ya ce babu komai In Sha ALLAH, yanzu haka tafiya ta kamashi zuwa Kaduna, In Sha ALLAH gobe da safe zai ƙarisa cikin Abuja ya duba ni. Hajiya ta mashi fatan alkhairi, da yake brothers ɗina sun saba tafiyar dare sai Hajiyarmu bata damu ba, suka yi sallama tana mashi fatan nasara. To a wannan rana yaya ya kama hanyar Abuja, ya isa washegari da safe.
Yana isa ya kira Abba. Aikuwa Abba ya rufe su Hassan a gida ya je ya ɗauki yaya suka nufi asibitin, da suka likitocin basu hanasu ganina ba, saboda Abba na tsananin kama da Abbie, da kaɗan Abbie ya fisa haske, to sai suka zaci ma Abba ne ya kawoni saboda da daddare Abbie ya kawoni ba zasu iya banbantawa ba.
And da suka ga yaya yana kama dani sosai. Har ɗakin da nike suka kaisu, ina sume ban san in da kaina yake ba. Da Abbie ya zo da safe dubani, ai yana zuwa bakin kofar ɗakin da nike zai shiga ya hango su Yaya a ciki, yana ganinsu ya laɓe yaƙi shiga, a lokacin kuma suna tattaunawa da Abba, Abba ya faɗawa yaya shi yana zargin Abbie gaskiya, watakila wani matsala muka samu Abbie ya dakeni ko wani abin. Yayana ransa in ya kai miliyan ya ɓaci, ya ce ba zai bar Abbie ba, sai ya koya mashi hankali.
Shi kuwa Abbie da yana jinsu sai ya sha alwashin ba zai bar Abba ba, Abba ya ɗebo ruwan dafa kansa.
Intakaice maku labari dai Abbie ya gudu ya bar asibirin dan asirinsa na gab da tonuwa, ya je yai tsubbace-tsubbacensa ya rufe mun baki dan kada in faɗi abin da ya ce mun naƙi yarda, shi ya mayar dani kurma, ya hana bakina yin magana. Yaya ne yai jinyata, Abba kuma tun daga wannan rana da ya bar asibitin yaya bai sake ganinsa ba, yana ta kiran wayansa a kashe, yaya ya je gidanmu babu kowa, so ya rufe gidan ya taho da key ɗin. Yana ta neman Abba da Hassan and Hussain amma shiru bai gansu ba, ya nemi Abbie ma bai gansa ba.
So sai ya shigar da report, ya nemi iyayen Abbie dake Kaduna, ya ce Yah Abbas ya je gidansu Abbie ya haɗasu a waya, ya je ya haɗasu, Yaya ya tambayi Mama ina Abbie ta ce bata sani ba, rabonta da waya da Abbie ya kai sati, haka ma matarsa Zainab, sun kai sati basa waya. Da jin haka yaya ya kara karfafa zarginsa kan Abbie, yai jinyata har ya kammala bai sake jin ɗuriyar kowa ba, shi ne ya ɗaukeni muka dawo gida, likitoci sun ce lafiyata lou, basu ga abin da ya hanani yin magana ba, nan kuwa Abbie ne ya haɗani da bakin aljani ya rike mun harshe.
Kwanaki na biyu da dawowa gida, wani irin tsananin so nike jin ina yi wa Abbie tamkar zan yi hauka, na damu sosai da sosai, ina yawan jin faɗuwar gaba idan na tuna yarana, a ranar kwanaki na uku da dawowa Hajiyarmu ta ce amun sauƙar Alqur'ani a'a fara neman mun maganin rashin maganar nan na gida.
Da yake daddynmu ɗan boko ne bai yarda da gargajiya ba sai yaki, ya ce ba wani maganin gargajiya, zai fitar dani waje a sake dubani, Hajiyarmu ta ce ita kam gaskiya a wannan karon ya barta ta dafawa ƴarta, a wancan karon ya yi son ransa da rayuwana yanzu kuma ya kyaleni. Ku fahimci abu ɗaya, daddynmu ɗan boko ne, Hajiyarmu ƴar gargajiya, shiyasa suke da mugun banbancin ra'ayi, dayawan lokuta suna faɗa a kan abu karami, domin daddy ya iya watsi da abubuwa masu muhimmanci da sunan gargajiya ne baya so, ita kuma Hajiyarmu akwai rike al'adunta da gargajiya.
Ba yadda hajiya bata yi ba daddy yaki yarda da batun maganin gargajiya, ya ce babban yayanmu ya shirya zai fita dani a je neman mun magani. Hajiyarmu ta ce bata yarda ba, daddy ya ce a kan ƴaƴansa dama baya neman yardan kowa, suka dai yi rikici wanda daga karshe Hajiyarmu ta hakura ta rabu da daddy.
Satina guda da dawowa ana ta shirye-shirye tafiyata, ina tsaka da barcin rana na yi wani mummunar mafarki wai ga ɗana Hussain can yana kwance tsakiyar wuta, jikinsa duk rubutu-rubutun tsubbu, an ɗaɗɗauresa da wasu igiyoyi na karfe, ta kafafunsa an mashi rubutun Alqur'ani, sai aka ɗaura shi kan shinfiɗar wuta, ƙasan shinfiɗar wuta ne yake ciki, yaron yana ihu yana mammy kizo ki taimakeni, Abbie zai kasheni.
A firgice na tashi ina haɗa uban gumi, wani irin mummunar faɗuwar gaba ne ya riskeni, duk bayan minti ɗaya sai gabana ya yanke ya faɗi, na gigice da wannan mafarki, ina son yin ihu ba bakin magana, jikina ya dinga rawa, Hajiyarmu na zaune a kan dadduma ta yi sallar azahar, da ta ga na tashi a firgice ta zo ta rikeni tana faman tambayata lafiya, ban iya amsa mata ba saboda baki yaki samuwa.
Sai ta fara tofa mun addu'oin tana mun sannu, dan ta gano mummunar mafarki na yi. Safiyya ta shigo rike da Muhammad, ina ganinsa na sake firgicewa, sai naga kamar Hussain ne a hannun Safiyya, na miƙa mata hannu ta bani shi, Hajiyarmu ta ce a'a kada ta bani, sai dai kafin Hajiyarmu ta furta gada ta bani Safiyya ta miƙo mun shi. Da karfi ya kwace yaron, yana dariya ya zo jikin mamarsa, sai kuma dariyarsa ta tsaya cak lokacin da na daddage na buga shi da ƙasa.
Wani irin ihu Safiyya ta yi tare da nufan yaron a kan tiles, har kansa ta fashe jini ya fara zuba, Hajiyarmu bata motsa ba, ta rikeni da kyau tana cigaba da tofa mun addu'a, ita kuwa Safiyya ta ɗauki Muhammad da gudu ta nufi waje da shi tana kwalawa babban yayanmu kira.
A daidai wannan lokaci kuma daddynmu yake faman yanke hukuncin wai a kira mashi mijina da shi zamu yi tafiyar nan tun da matar aure ce ni, nan babban yayanmu yake faɗa mashi ai ba'a ga Abbie ba. Daddynmu ya ce to ba tafiya har sai an ga Abbien, dan ba yadda za'ayi in tafi ba tare da mijina ba.
Babban yayanmu ya yi ƙoƙarin nunawa daddynmu cewa yana zargin Abbie, amma daddy ya murje idanunsa ya ce sam Abbie ba shi da laifi kuma mutumin kirki ne yayanmu ya daina zarginsa. Dole babban yayanmu yai shiru dan baya ja da iyayensa.
Da gudu Safiyya ta kawo mashi Muhammad tana faɗin Aunty ce ta buga shi da ƙasa ta fasa mashi kai, yaron kwata-kwata baya motsi, da alama ya suma ko ma ya mutu. Cikin zafin nama babban yayanmu ya karɓesa, da sauri ya nufi waje da shi. Daddynmu ya ce da hankali a kaina kuwa zan buga yaro da ƙasa? Safiyya ta ce wlh daddy Aunty bata da hankali, wlh ta haukace, kawai fa ta karɓesa ta buga mashi kai da ƙasa.
Daddy ya ce. "Mu je in dubata".
Suna shigowa ɗakin suka isko ina dambe da Hajiyarmu, faɗa na gaske, Hajiya na rike hannuna ina son kwacewa, tana ta tofa mun addu'oin amma sai kara birkicewa nike yi.
Aikuwa daddy ya shigo da gudu da nufin yakamani, Safiyya ta fita da gudu ta je ta kira Yah Abbas dan shi ma yana gida.
Duk yadda suka yi su kamani a gidan sun gagara, dan har daddynmu sai da na buga mashi kai da bango, Yah Abbas ya so kamani shi ma capkesa da kokawa, ya ɗauki glass na tukunyar flower zai buga mun Hajiya ta hanasa, ta ce kada ya cutar dani, kawai ya kamani ne su ɗaureni.
Haka na zama mahaukaciyar karfi da ya ji, na dinga duka kaina ina jiwa kaina ciwo, ga karfi kamar doki, sun gagara kamani har sai da Yah Abbas ya dakeni da wannan flower a kai na faɗi na suma, sannan suka iya kamani, Safiyya nata faman kuka tamkar zata mutu, yau an yi tashin hankali a gidanmu, wai nike faɗa da iyayena, faɗama ta hannu da hannu, innalillahi wa inna ilaihi rajiun, wannan wace iriyar musifa ce?..............
(To mata gareku, ku ji tsoron ALLAH kada ki biyewa mijinki ya kaiki ya baroki, irin Abbie su suka fi yawa a cikin al'umma a duniyar yau, wlh akwai labarin wata da ta bani, true life story ne shima, amma shi bana jin zan iya rubuta shi saboda muninsa yai yawa, mijinta ya ce ta dinga luwaɗi da abokinsa duk saboda neman duniya, abokin yana kwanciya da ita ta baya, ita kuma ta yarda, and ta yarda ne saboda tsoron iyayenta, ta jima zaune a gida bata yi aure ba, ta kai 32 years, da kyar aka samu wannan mutumi ya zo neman aurenta, iyaye suna burin su aurar da ita, so ba dogon bincike suka aura mata shi, ba zan tsaya faɗa maku yadda aka yi ba, dan abubuwa munana sosai sun faru, dan dogon labari ne, in takaice dai tana tsoron aurenta ya mutu saboda iyayenta sun mata gargaɗin kan dole ta zauna tun da taga da kyar aka yi aure, ashe mutumin nan ɗan tsubbu ne, ko wata ba'ayi da aurensu ba ya bijiro mata da wannan magana, dole ta aminta saboda tsoron kada ya saketa iyayenta su tsine mata, dan mahaifinta ya ce idan ta kashe auren bata babu shi. In yanke maku wannan labari bayan abubuwa sun ta faruwa ta zo ta yarda, abokin yana kwanciya da ita ta baya, to yanzu da ake wannan magana ta lalalace, ta ruɓe, wlh tsutsotsi ne yake fita ta bayanta, kuma mijin ya saketa, yama gudu ba'a san in da yake ba bayan ya barta da cuta mai tsanani, tana da yarinya guda ɗaya ya salwantar da rayuwar yarinyar, kunga abin da take gudunwa ɗin watau saki sai da ya faru, ga shi ta cuci kanta na har abada, ta saɓawa mahaliccinta, ta lallata rayuwarta na har abada, ta rasa ƴarta, kullum suna yawon asibiti sauki yaƙi samuwa, yakamata ace na rubuta wannan labari saboda zai faɗakar sosai, amma wlh munin dake cikin labarin ya fi karfin tunaninku, na yi wa wannan mata hawaye har ban san adadi ba, wlh wasu iyayen ku ji tsoron ALLAH, ku sani ƴaƴa amanace a wajenku, saboda tsoron ku tsine mata ga shi kun zama sanadiyar halaka rayuwarta, kun cutar da ita, yanzu kuna danasani maras amfani, and mata kuma ku ji tsoron ALLAH, kada ki yarda ki biyewa namiji ki lalata rayuwarki, dan kina lalacewa wlh rabuwa da ke zai yi ya auri wata, so yakamata ku dinga fin karfin zuƙatanku, ku sani gwara ku shiga duk wahalar da zaku shiga kan ku saɓawa mahaliccinku. Yakamata ace na rubuta labarin, amma yana mugun sakani kuka ne nike jin kamar ba zan iya ba rubutawa ba akwai abin tausayi sosai. Sannan akwai wani labarin ma true life mai kusan the same irin haka, shi ma duk ire-irensu ne, kuma shi ma yana da babban darasi. Yanzu abin nan yana nema ya zama ruwan dare, mata kune masu laifi da kuke yarda da mazan, ki sani wlh ko kin yarda sai ya rabu dake idan ya sami abin da yake so, da ace A'isha ta yarda da bukatar Abbie, wlh shima gaba luwaɗi zai bijiro mata da shi, gaba-gaba har ya ɓata mata rayuwa tun da dama ba sonta yake ba, ku sani kuma wlh zai rabu da ita da zarar ya samu abin da yake so, to yakama mata ku shiga hankalinku ku farka, ALLAH ya cigaba da tsaremu yasa mu fi karfin zuƙatanmu)
labarin A'isha zai dinga zuwa maku labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi.
FATEEMA ZAHRA MUSA
A-K-A
QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥
LABARIN AISHA.🥹💔
PART 24
Haka na shafe shekara guda cikin wannan ciwon haukan, kuma har lokacin ba'a Abbie ba yarana ba kuma Abba, duk yadda iyayena suka sha nemansu basu gansu ba, ba'a sake jin ɗuriyarsu ba har da Zainab.
Duk wata kunci ta rayuwa da uku ba na sha shi, ciwon hauka na tsawon shekara, kullum ina ɗaure cikin sarka, daga karshe da Hajiyarmu ta ga babu sarki sai ALLAH tuni ta watsar da umarnin daddy, ta sanya Yah Abbas ya ɗaukeni zuwa wajen malamai dan a mun ruƙia, daddy ya ce shi bai yafe ba idan aka kaini, Hajiyarmu ta fusata ta ce in ya fe ma bai san ALLAH ba, aka yi mummunar ɓacin rai a gidanmu tsakanin iyayena a wannan rana ba.
Yah Abbas ya ɗaukeni, daddy yana cewa ya dawo dani ko ya mashi baki, Hajiyarmu na cewa ta idan ya dawo dani ALLAH ya isa bata yafe ba, aikuwa Yah Abbas ya ɗauki maganar Hajiyarmu ya kyale daddy. Ya ɗaukeni zuwa wajen wani babban malamin addini a Zaria.
Malamin yana ganina ya ce ai iska ne a jikina sosai, yasa Yah Abbas ya ajiye ni a parlonsa, ya fara mun karatun Alkur'ani mai girma. Take na fara haɗa uban gumi, kan kace me na fara ihu ina kuka, Yah Abbas ya tashi zai rikeni Malamin ya ce a'a kada ya taɓani, ba wani aljanin da ya isa ya mashi hauka a nan, zan natsu ne idan na gama kukan.
Haka kuwa aka yi, da na gama kukan sai na natsu, take muryoyi suka fara fitowa daga bakina suna baiwa Malam hakuri suna faɗin turosu aka yi. Shi kam Yah Abbas ja da baya ya yi, yana zazzare ido, ya ji murya har da na gardawa ne. Malam ya tambayesu meyasa suka shiga jikina, suka ce mijina ya turosu, aikuwa Yah Abbas bai yi ƙasa a gwiwa ba wajen ciro wayansa ya fara record duk abin da aljannun suke faɗe, ya naɗi komai, tun farkon aurenmu, yadda Abbie ya turasu suka shiga jikin daddyna suka sanya ya amince da batun auren, yanzu haka suna da ɗaki a jikin daddyna, kuma dama su suka sanya shi ya ce ba za'a kawoni wajen addu'a ba.
Duk wani abin da suka mun sai da suka faɗa. Malam ya ce to yanzu zaku fita ne ko dai sai na ƙonaku. Suka dinga baiwa Malam hakuri suna faɗin sun yi alƙawarin zasu barni kuma zasu bar jikin daddyna na har abada. Malam yaƙi yarda dasu, domin wlh aljanu maƙaryata ne ga shegen iya saɓa alƙawari, Malam ya kawo ruwan addu'a, ya watsa mun a fuska, suka fasa kururuwa suna ihun kada ya konasu, wlh zasu fita kuma ba zasu sake tunkarar zuri'armu ba, aikuwa Malam ya sake watsa masu.
Suna ihu suna bashi hakuri, sai da ya watsa masu har sau uku, sannan ya ce gargaɗi na maku wannan watsawar da na maku, wlh duk ranar da kuka sake dawowa wannan zuri'ar, to sai na ƙonaku, suka ce sun yarda, Malam ya ce su yi maza su kwashe kayansu daga jikina da kuma jikin daddyna su fice su bashi waje. Suka ce to. Jim kaɗan na yi atishawa mai karfi guda uku jere, sannan na sulale ƙasa na kwanta shiru.
Yah Abbas kam sai ido yana kallon ikon rabbi, Malam ya ce ba komai ya ɗaukeni ya mai dani gida komai ya wuce, ba zasu sake dawowa ba. Da farko Yah Abbas ya ƙi yarda, ya ce sai na farka a gaban Malam, amma daga baya da Malam ya ce zan jima ban farka ba, kuma zan farka lafiya da iznin ALLAH, sai ya yarda ya ɗaukeni, ya yi wa Malam kyaututtuka muka kamo hanyar dawowa gida.
Muna dawowa kuma muka ci karo da sabuwar fitina, daddynmu yana tsaye a tsakiyar parlo yana ta faɗa wai shi ba shi ya aurawa Abbie ni ba, wlh ba shi bane, ya ce wai sai dai in babban yayanmu, a lokacin da aljanun suka bar jikina shi ma sun sake shi ne, shi ne yake tambayar Hajiyarmu ina nike, saboda duk cikin yaransa ya fi sona, ni takwarar mahaifiyarsa ce.
Hajiyarmu ta faɗa mashi duk abin dake faruwa, aikuwa ya ce shi bashi bane, sai dai in babban yayanmu da Hajiyarmu ne suka mun aure, kuma ba zai yarda ba sai ya yi shari'a da su. Yah Abbas na zuwa ya ce su kwantar da hankalinsu bari ya raba masu faɗa, kowa ya zauna ya natsu, Yah Abbas ya kunna recoding da ya ɗauka a wajen Malam.
Aikuwa daddy ya dinga salati, ya ce ba zai bar Abbie ba, sai ya ɗauresa, to matsalar shi ne ba'a san in da Abbien bama yake. Ga iyayensa can suna fama da wahala, su Aunty Farida jiki ya yi evening, babu cin yau bare na gobe, Mama idanu ya raina fata, a tsawon wannan shekara da na ɗauka cikin jinya sun yabawa aya zaƙinta, sun sayar da komai da suka mallaka dan su ci abinci, babu mai taimaka masu dukka dangi, sun nemi Abbie sun rasa, suna tsaka mai wuya, dukkansu sun shiga hankalinsu yanzu.
Mama sau biyu ta zo ta dubani lokacin da nike jinya, duk ta ƙone ta jeme.
----------------
Kwanana ɗaya da dawowa daga wajen Malam na farfaɗo, na kuma farfaɗo da lafiyata ras, ina farfaɗowa da sunan su Hussain a bakina, sune kawai a raina kafin in kwanta ciwo. Hajiyarmu da Safiyya suka dinga rarrashina suna faɗin In Sha ALLAH su Hussain suna nan lafiya, na tuna komai da ya faru da ni a rayuwata, babu abu ɗaya da ya bar ƙwaƙwalwata. Wani irin kuka ne mai karfi ya kwace mun, ina tuna yadda na dinga baiwa mutumin da na tsana jikina. Wani irin kafurin tsana na yi wa Abbie na fitar hankali.
Na dinga kuka ina cewa Hajiyarmu nasan zai cutar mun da yarana, ai ya ce sai ya salwantar da duk abin da nike kauna, dan ALLAH su barni in je Abuja nasan zan gansa in kwato yarana. Iyayena suka hanani zuwa, ba yadda ban yi ba suka hanani zuwa.
Aikuwa wataranar laraba da tsakar dare na tashi na shirya, gida dukka suna barci na lallaɓa na fito, mai gadi yana ɗakinsa na lallaɓa na buɗe gate na fita, ban tsaya ko'ina ba sai tasha, ba mota a daren, haka na kwana a tashan nan, da asuba na samu motar Abuja, already na ɗauki kuɗi
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 19 Chapter of 38