ya ce. "Meyasa baki son in zo? Baki son ganina ne?"...... Na girgiza kai tamkar yana a gabana. "Ni ban ce bana son ganinka ba, kawai dai ka bari ne please"...... Ya dinga mun magiya wanda daga karshe ya ce muyi video call yana ganina dan ya ji daɗin rokona.
Na ki amincewa da video call ɗin, ya dinga haɗani da ALLAH, daga karshe dole na yarda ba dan na so ba. Ya kirani na ɗauka ina zaune a bakin gado. Na sunkuyar da kaina ƙasa ina tunanin yadda zan ga fuskansa. Cikin natsuwa ya ce. "Aesh". Na amsa da na'am ban ɗago ba.
Unexpected na ji an ce. "Mammy". Da yaren gwarawa. Da sauri na ɗago kai, Muhammad na gani zaune a kan bayan motan Ibrahim, a gefe ga Safiyya, gidanmu ya je ganin Muhammad, ALLAH ya sanyawa Ibrahim son yaron nan, ba'a kwana biyu bai je ganinsa ba, ya yi ta saya mashi kayan wasa da abubuwa, har ɗaukansa yake yi suna fita yawo, da yake Hajiyarmu ta yarda da shi tana barinsa da Muhammad ɗin su je yawo, yanzu haka kayan wasa ya je ya sayo mashi dayawa sai ya kawo mashi gida, yasa Safiyya ta fito mashi da yaron, shi ne wai mu yi video call.
Ai ban san lokacin da na sake ba, na dinga kallon yarona, yanzu nawan nike ce mashi tun da na rasa Abba, dama Muhammad takwaransa ne, sai na maye gurbin sunan da Muhammad. Safiyya ta ce. "Aunty, Yah Ibrahim ya kawowa Muhammad dayawan abubuwan wasa, kin gansu kuwa? Masu kyau sosai"........ Na sauke ajiyar zuciya tare da cewa. "Safiyya bana ce ku dinga cewa Muhammad Abba ba? Please ku mai da mashi da wannan suna, ku kirasa Abba ko dan kada sunan nawan ya ɓace a bakunanku, ku dinga mashi addu'a a duk lokacin da kuka tunasa".
Ibrahim ya ce. "Aesh, waye Abba kuma?".......... Na dawo da kallona kansa, ashe tun ɗazun ya tsareni da kallo ina ta biyewa gwalanniyar Muhammad, duk sai na ji kunya ta kamani, nai ƙasa da murya wajen cewa. "Uncle ɗin Muhammad ne, shi ne ranar a Kano muka haɗu da kai da shi a shopping"........ Ya ɗan zare mun ido kafin ya ce. "Dama ba shi ne mijinki na wancan lokacin ba?".
Na jinjina mashi kai alamar yeah bashi bane. Sai ya ce. "To how comes yake tsananin kishinki har da mun faɗa?"....... "No, yana taya yayansa kare mutuncinsa ne". Na faɗa a taƙaice........ Ibrahim ya girgiza kai alamar a'a ba haka bane, kamar zai yi magana sai kuma ya fasa, ya ajiye topic na Abba ya ɗauko wani, cike da girmamawa da kula ya ce. "Please my tauraruwa, ki bani dama in kawo maki kaina gareki, ko da sau ɗaya a shekara ne in dinga zuwa".
Na ɗan kallesa kaɗan, ya salam, ya kara kyau matuƙa, ya ɗan ƙara ƙiba, kuɗi sun zauna, ga wani sheki da skin ɗinsa yake yi. "Uhm, to shikenan, yanzu mu sa lokaci"..... Da sauri ya ce. "Next week?"...... Na yi saurin girgiza kai. "A'a, ina gab da fara exams, bana son raba hankalina biyu, ka bari idan na gama exams ina hutu sai ka zo ko?".
Ya jinjina kai game da cewa okey tom. Haka muka dinga hira, Safiyya ta ɗauki Muhammad sun koma ciki, Ibrahim yai wa su Hajiyarmu sallama, ya shiga mota, har ya kai gidansu waya muke yi, yana ta zuba mun kalamai masu narka zuciya, ni kam na sunkuyar da kaina ƙasa ina ta tunanin rayuwa, yau almost 2 year without Abba and Hussain, one year na ciwon haukar da na yi ga shi na kusa one year a Germany without them, ga Hassan dake raye ma ban samu damar ganinsa ba, sai kawai na katse video call ɗin ba tare da na sallami Ibrahim ba, na ajiye wayar na nufi balcony.
Nan na isko Zahra zaune tana buga game, na zauna a gefenta na cigaba da karatuna, dan Exams na dinfaromu gadan-gadan.
Tun daga wannan rana kusan kullum sai mun yi video call ko sau ɗaya ne da Ibrahim, tun ina damuwa har na rage damuwata, na saki jiki muna hira, but har yau ban amsa da ina son shi ko bana son shi ba, hira kawai muke yi.
A haka har na kammala rubuta Exams ɗina, muka samu hutu, amma naki faɗawa Ibrahim mun samu hutu, na barsa sai ana sauran sati ɗaya a buɗe school zan faɗa mashi dan bana son ya jima idan ya zo, so sai na ki faɗa mashi. Tun da aka yi hutu Zahra take neman koya mun yawo, ni da bana fita, daga gida sai makaranta, amma wannan hutu tare da ita zamu yi a nan, a wannan karo ba zata koma Qatar ba, dama duk hutu tana zuwa can.
Wannan karon ta ce ta gaji da asarar kuɗin jirgi, dan haka da kuɗin jirgin zamu yi ta zuwa yawo da wajajen wasanni da kallon Film. Rana ta farko da muka je babban wajen buga snooker na ji daɗi, na dinga kallon mutane daban-daban, Zahra ta shige cikin tsakiyar maza tana buga snooker, ina ta kallonta da mamaki, na zauna a kan kujera ina kallonsu har suka gama, ta ce in zo in buga, na ce a'a, sai ta ce bari ta ƙara bugawa sau ɗaya. Na ce okey, ta shiga bugawa.
Ina zaune daga bayana na ji ance excuse me, na juya a hankali, wani kyakkyawan matashi ɗan bature ne a tsaye, kallo ɗaya nai mashi na ɗauke kai, ya ce zai iya zama a kusa dani? Na ce mashi a'a bana buƙata, ya ce why, na ce babu komai. Da na ga yana neman jana da surutu sai na miƙe na bashi waje, ya bi bayana yana damuna da magana, nai banza da shi, na gudu na koma cikin motar benenmu da muka ɗauko, nai zamana a ciki.
Yai ta mun knocking glass naki buɗewa, dole ya gaji ya koma gefe ya tsaya. Da Zahra ta gama buga game ɗinta ta kirani a waya, na faɗa mata ga in da nike. A lokacin da ta zo tana ƙoƙarin buɗe motar, da sauri wannan matashi ya ƙariso wajenta yana mata magana. Ta tsaya ta sauraresa, amma da ta ji ni yake nema ta ce yai hakuri kawai, dan tasan ba zan taɓa sauraronsa ba, saboda ta sha fama dani kan in saurari wasu a baya naki yarda, shiyasa yanzu da zarar ka mata magana a kaina zata ce ka yi hakuri kawai dan ba zata iya shawo kaina ba.
Haka ta shiga mota, ita ta ja muka nufi yawo, ni ban iya tuƙin mota ba har yanzu, duk inda zamu je ita take janmu. Na so mu je ƙasar Netherlands yau, ina son zuwa ƙasar sosai, Netherlands ƙasa ce dake arewa maso yamma na Germany, ƙasace dake kusa sosai da Germany, da mota ma zaka iya shiga cikin ƙasar, na ci burin in muka yi hutu in je, so fiyarmu ya yau na so mu je can mu yi kwana ɗaya ko biyu mu dawo, amma Zahra ta ce mu bari sai next week, yau ta dinga kai ni wuraren da take zuwa yawonta.
Muka sha yawonmu har dare sannan muka koma gida, jiki duk gajiya, nai wanka ina tunanin me zamu girka, ina tsaye a tsakiyar parlona sai ga Zahra ta shigo da waya a hannunta.
Ta ganni sanye da pjs farare a jikina, sai ta ce. "Eshart ki je ki shirya mu je cin abinci a sabon Chinese restaurant da aka buɗe ɗin nan"......... "Wai ke Zahra baki gajiya da yawo ne? Ni babu wani Chinese restaurant da zan je, ki zo mu yi girki a nan"........ Ta rikeni tana faɗin. "Please mana Eshart, daren yau zasu buɗe restaurant ɗin, zasu bada komai zaka saya rabi free rabi kawai zaka biya, kinga akwai sauki, and ina son Chinese food sosai, da akwai daɗi, ki zo mu je please".
"To ke kije, idan kika je kya mun takeaway, ni kam na gaji da fita, yanzu haka kafafuna zafi suke mun ƴar nema kawai, ke idan na biye maki har tsakar dare yawo zakina kaini"........ Ta ɗan shagwaɓe fuska, sai ta ce. "Eshart please idan kina da brother ki bani in auresa dan kina da kyau sosai nasan shi ma zai yi kyau, kuma ko dan in dinga baki umarni kina bi".
Na harareta ban yi magana ba, ina ƙoƙarin zama ta dinga jana wai sai mun tafi, dole ba dan na so ba na ɗauki ƙaramin hijab na sanya a jikina muka fita. Ita ta tuƙamu a komar benenmu, muka nufi restaurant ɗin. Kai, gaskiya wajen yai bala'in haɗuwa, tab, dukiya tayi mubaya'a a wannan waje, wannan sai manyan kai zasu na cin abinci a wajen saboda haɗuwansa, ba restaurant ne na yara ba gaskiya, wani irin bene ne mai hawa goma, kuma irin glass high rise building ɗin nan ne, aka yi butterfly design wanda ya ƙara gigitani da haɗuwa, sai nike ganin kamar abinci plate ɗaya zai iya kai kuɗin dake account ɗinmu gabaɗaya saboda haɗuwar wajen.
Haka Zahra da rashin tsoro ta kaimu, ita nan ta ga sauƙi, zaka biya kuɗin rabi ka samu rabi kyauta. Sai dai kuma, ko da muka je gate ɗin filin a rufe ruff, ga uban cincirindon al'ummar a waje kowa na son shiga, restaurant ɗin a cike yake fal ba wajen shiyasa aka rufe gate ɗin ma.
Na kalli Zahra dake ƙoƙarin fakin mota na ce. "Ke mu koma, ki dubi uban al'umma a nan? Ba waje ai"....... Ta ce. "Ke matsalata dake tsoro, zo mu je ki gani, bari in yi wa mai gadi dabara zai bamu hanya"...... Na ɗan taɓe baki na fito, ita ma ta fito, ta kama hannuna muka nufi cikin uban jama'ar nan, da kyar muke samun hanya, har dai muka kai bakin gate. Ko tsoro Zahra bata ji ta hau bubbuga gate ɗin tana son mai gadin ya fito ta kafaza shi ne.
Ni kam na ce. "Zahra please zan jiraki a mota kin ji?"....... Ta ce. "Gara mu shiga tare kema ki ga cikin"...... Na amsa da. "No dear, idan kin shiga ki mun video ɗin wajen".
Zata sake yin magana muka ji an hau buɗe gate ɗin, mai gadin ne ya hau cire locks ɗin, da alama ya gaji da bala'in bugun da Zahra take yi mashi..............
ALLAH yasa kada ya kwaɗeta da mari ma idan ya buɗe, dan yarinyar nan sai shirin ALLAH.
labarin A'isha zai dinga zuwa maku labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi.
FATEEMA ZAHRA MUSA
A-K-A
QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥
LABARIN AISHA.🥹💔
PART 26
Zata sake yin magana muka ji an hau buɗe gate ɗin, mai gadin ne ya hau cire locks ɗin, da alama ya gaji da bala'in bugun da Zahra take yi mashi. Yana buɗewa ya ce. "Ku bada hanya"........ Zahra ta wani hararesa kafin ta ce. "Dama kana jinmu muna ta bugu kenan ko?". Da turancinta da bata kware sosai ba ta faɗa, dayawan larabawa basu iya turanci ba.
Ya wani kalleta, yana sanye cikin security uniform ɗinsa, bai sake yi mata magana ba, sai gani muka yi an wangame tangamemen gate na restaurant ɗin. Wasu danƙara-danƙaran motoci ne a jere sun kai guda biyar suka kunno kai zasu fice.
Hannun Zahra na ja muka matsa masu a hanya, cikin faɗa ta kwace hannunta wai an raina mata hankali, ba zata bar mai gadin nan ba, ina ƙoƙarin dakatar da ita ta kwace hannunta ta wuce, wai saboda ita ba mai kuɗi sosai bane za'a walaƙantata, watau dama da suka ce zasu yi ragin 50P karya suke yi? Dama masu kuɗi kawai zasu yi wa ragin?. Tana masifa tana nufan wajen.
Ni kam na juya na koma wajen motanmu, coz ba zan iya rigimar Zahra ba, dan ta iya masifa idan aka kawo mata rainin wayau, bata ɗaukar nonsense. Na shiga cikin mota nai zamana ina sauke ajiyar zuciya. Lokaci guda naga jama'ar dake wajen sun fara gudu suna nufar waɗan nan motocin da suka danno wajen restaurant ɗin.
Na zuba masu ido ina mamakin ko uban waye a motar da wannan uban dubban jama'a suka yi cincirindon zuwa gani. Jama'a dayawa sosai, so ban iya ganin waye a cikin motar ba, hakan yasa na mai da kai kan wayata ina dannawa, kowa sai ɗaukar hoto yake yi dana cikin motar, masu yin videos dayawa suna ta faman yi, da alama wani celebrity ne suka gani.
Ina ƴan tunane-tunane na sai naga Zahra ta shigo cikin motar da gudu tana faɗin. "Sister kin san me?"...... Na ɗan harareta kafin in ce. "Ina zan sani tun da ban biki ba sarkin faɗa".
Ta rarumi wayarta zata fita na yi saurin cewa. "Zahra please mu je, ki haƙura da sayen abinci a nan ki zo mu tafi gida kin ji? Zan girka maki duk irin abin da kike so"............ Da sauri ta ce. "No my dear, yanzu ba batun abinci ake yi ba, ni nama ƙoshi da abincin, jarumina zan je ɗauka hoto, dan ALLAH ki zo ki gansa".
Na taɓa baki game da saketa ina faɗin. "Ba zan je ko'ina ba"......... "Ke kam ban san meyasa baki son zuwa wajen mutane ba, ni kam kinga tafiyata, dole in samu damar yin ko da hoto ɗaya ne da shi, wai kin san waye shi kuwa?"......... Na ja tsaki ina kallon yadda take uban rawan jiki, kai ni fa a duniya ban ga wani ɗan adam da za'a ce ga shi ya zo waje in je kallonsa ba, babu shi wlh, tun tasowata a rayuwata ni bani ma da ra'ayin kowa, masu zuwa kallon wasu wai celebrity ma kallon mahaukata marasa hankali nike masu, dan haka sai na ce Zahra ta zare, tana ta sambatu ina kallonta.
Ta ce. "Dear, shahararren super hero ne fa dake bugawa team ɗin real Madrid kwallon ƙafa, kowa yana son shi, yana da farinjini sosai, amma kuma shi kullum fuskansa a rufe da nose mask, please ki zo mu je ki gansa, jarumi ne, idan ya rike kwallo ba mai kwacewa sai ya zura a raga"........... Na taɓe baki ina kallonta, ni kam ban taɓa kallo mace da shegen son abubuwan maza irin Zahra ba, ita duk wani wasanni tana wajen, har kwallon kafa bata bari ba, basketball duk tana sahun gaba, ji yanzu kuma uban da ta jajuɓo wai jaruminta a kwallon kafa, kai wannan yarinya sai shirin ALLAH.
Ta gama surutanta ban kulata ba, ta gama zuzuta jarumin nata ko sannu ban ce mata ba, da ta ga fa ni ba zuwa zan yi ba sai ta wuce da gudu tana faɗin ita dai yau ko za'a mutu sai ta yi hoto da Super hero ɗinta. Yarinyar nan tana zuwa wajen cincirindon al'ummar nan ta yi tsalle ta afka cikinsu ta fara kutsawa ciki. Ni kam na sake baki ina kallonta da mamaki, duk fa kartin maza ne a wajen, amma ta afka tsakiyarsu ko a jikinta, ashe dukka cincirindon al'ummar nan ba domin restaurant ɗin suka zo ba, dan kallon jaruminsu ɗan kwallon kafa suka zo, shiyasa motocinsa na fitowa duk suka yi kansa.
Da na gaji da kallon jama'a na ɗan jingina da jikin kujerar motar ina sauke numfashi a hankali, wani irin bugawa da zuciyata ta yi ne yasa na fara maimaita lailaha illallah anta subhanaka inni kuntu minazzalumin, sai na lumshe idanuna a hankali. Wasa-wasa na kai mintuna 10 a haka Zahra bata dawo ba, ga shi bugun da kirjina yake yi ya tsananta, sai nike jin tamkar wani mummunar abu na faruwa.
Wayana na ɗauka na fara kiran number Zahra, amma yarinyar nan bata ɗauka ba, ban iya mota ba, da ba zata zo ta sameni a wannan waje ba, tafiyata zan yi. Bugun da kirjina yake yi ne yasa kaina ya fara ciwo sosai, hakan ya tilasta mun dole in fita in nemo Zahra dan mu koma, ga yunwa, ga gajiya, yanzu kuma ga wani uban buga mun da kaina yake yi. Haka na fito na fara rakuɓewa ina bin gefen mutane dan ma kada wani ya taɓani, na dinga neman Zahra, al'umma cike tab a wajen har kan titi, kai kace garin ne gabaɗaya a wajen.
Duk yadda na so ganin Zahra ban ganta ba, ga shi sai ture-ture al'umma suke yi. Na ji ba zan iya ba, na fara ƙoƙarin fita daga cikinsu, kaina na tsananta ciwo sosai. Da kyar na samu na koma cikin mota, na zauna a gidan gaba, na kifa kaina da jikin motar na fara ruwan hawaye, akwaini da saurin kuka, ciwon kai nike yi wa kuka yanzu.
Tun ina kukan kaɗan-kaɗan har na fara yi da ɗan sauti. Wasa-wasa Zahra sai da ta kara 20 mina, sannan ta dawo, ganina ina kuka yasa ta dinga bani hakuri, amma ban kulata ba, ta zaci saboda ta je ta jima ne yasa nike kuka, bata san nan azaban ciwon kai da bugawar zuciya bane kawai ya sakoni gaba.
Ta dinga ce mun in tashi in ga jaruminta ta mashi hoto, nai banza da ita. Da taga da gaske nike yi sai ta kashe wayarta tare da fara jan motar ta nufi barin wajen. Da kyar muka samu hanyar barin wajen, muka kama hanyar gida, har lokacin kuka nike yi sosai, kaina tamkar zai fashe.
Mun yi nisa da barin restaurant ɗin unexpected muka ga wata bakar mota ta faka a gabanmu. Dole muka taka mahaukaciyar birki wanda yasa sai da kanmu ya bugu da jikin steering motar. Cikin masifa Zahra ta ɗago zata fara masifar tata kenan ta ga wasu jiga-jigan maza madakata karti sun fito, suna sanye da guard dress a jikinsu, komai nasu bakake ne har da nose mask and hands gloves.
Zazzaro Zahra ta yi, sai ta hau taɓani tana faɗin. "Dear tashi ki gani". Tana magana tana zazzaro idanu. Ina fama da azaban ciwon kai ban iya ɗagowa ba, na kara danne kaina da jikin motar ina cigaba da kukana.
Waɗan nan karti suka nufo motarmu kai tsaye, suka buɗe, suka ce mu sauƙo, Zahra ta sauƙa jikinta na rawa tana basu haƙuri, ni kam ban iya motsawa ba, sai suka ce in sauƙo, ban motsa ba, ganin hakan ne yasa ɗayansu ya ja baya, ya koma gefe yai waya na minti ɗaya, sannan ya dawo wajen, sai suka ce Zahra ta kamani ta sauƙo dani.
Haka kuwa aka yi, ta zo ta kamani ta sauƙo dani ƙasan motar, na dafa shoulder ɗinta tare da kwantar da kaina a jikinta ina cigaba da kukana. Basu ce mana ko sannu ba suka kaimu cikin motarsu, suka dawo suka rufe motarmu, mutum ɗaya ya ja motar tamu, su kuma saura biyun suka zauna a gidan gaba na motansu, ni da Zahra muna gidan baya.
Da gudu suka ja motar suka bar wajen, tun da muka shiga cikin motar nan kaina na kife jikin Zahra bai iya motsawa ba sai kuka, ciwon kan ya tsananta mun, tamkar kan nawa zai tarwatse haka nike ji. Ban san wace waina ake toyawa ba, ban san ina suka ɗaukemu zasu kaimu ba, ban san komai ba sai ji na yi motar ta tsaya bayan tafiya mai tsawo sosai.
Ina ji aka buɗe kofofin motocin, ban iya ɗago kaina daga jikin Zahra ba, sai dai na ji an kama hannuna ana faɗin mu sauƙo.
Bin jana da ake yi kawai na yi na sauƙo, nasa hannuna na dafe kaina dake juyawa, idanuna a rintse gam........... "Tawan, menene yake damunki har haka?". Tamkar saukar aradu haka na ji muryar a cikin kunnena. Da wani irin karfi na waro idanuna waje, dishi-dishi na fara gani saboda tun ɗazun idanun nawa a datse ga kukan da nike yi. A hankali idanuna suka fara kallonmun mutum a tsaye a gabana yana riƙe da hannuna.
Da sauri na kai hannuna kan jikinsa ina ƙoƙarin taɓawa, a wani irin slow na ce. "Abba!!".......... Hannuna dake jikinsa ya rike, yai ƙasa da murya wajen cewa. "Kukan me kike yi haka sarkin ragonta?".......... A daidai lokacin idanuna suka washe garau a kan kyakkyawan fuskansa. Wani irin razana na yi ina ƙoƙarin kwace hannuna, sai dai ya rikeni da karfi, jikina ya fara rawa, dama wanda ya mutu yana dawowa ne?
Zan yi ihu yai saurin rufe mun baki da tafin hannunsa ɗaya bayan ya sake nawa da ya riƙe. Ai razana yasa numfashina ɗaukewa ɗiff. Na tafi gabaɗaya zan yi ƙasa ya rikeni da kyau yana mamakin irin razanar da na yi dan kawai an ce ya mutu yanzu kuma na gan shi....... (Abba gidanku na ce, bazata razana ba hauka ake yi, shekaru biyu kenan yanzu da cewa ka mutu kwatsam ya ganka ai dole ta sume,......... Awww, team Abba yau ana cikin alkhairi dumu-dumu.)
Ya rage tsawonsa ya ɗaukeni sai saman kafaɗansa, daga nan ya wuce cikin katafaren gidan da suka kaimu, tun daga wannan suma ban sake sanin komai ba sai farkawa na yi na ganni kwance a kan wani makeken king bed cikin wani haɗaɗɗen ɗaki. Na fara waige-waige, babu komai a cikin ɗakin face wannan gadon.
Wani irin zabura na yi na miƙe zaune a lokacin da na tuna dalilin sumana, sai na ce mafarki na yi, ba Abba na gani ba, dan in banda mafarki ya za'ayi wanda ya mutu ya dawo?. Sai kuma na ce to idan mafarki ne yanzu me ya kawoni wannan waje? Ina ne nan?.
Na yi gaggawar dirowa kasan gadon, da gudu na nufi in da naga kofa, kofofi uku ne a cikin ɗakin, sai wani glass door na balcony, dan haka sai na nufi ɗaya daga ciki. Da karfi na tura kofar nasa kai ciki, birki na ja na tsaya ina ganin sani katafaren bedroom kuma a maimakon waje, na fara zazzare idanuna ina jin kamar dukka fa a mafarki ne ba'a zahiri ba.
Juyawa na yi da sauri zan fita dan in duba sauran kofofin ko akwai na fita waje. Ina juyawa na bugi kirjin mutun, da sauri na ja da baya ina ɗago kai. Zazzaro ido a kan fuskansa na yi, muryata na rawa na ce. "Abba!".
Yana sanye da bathrobe a jikinsa, ya amsa mun da. "Har yanzu baki daina tsoro bako tawan?".......... Kara gigitani ya yi, na wage baki zan zunfuma ihu, dan wlh ban yarda shi bane, saboda bai nuna mun kamar irin yayi mamakin ganina ko wani abin makamancin hakan ba, yana magana hankalinsa kwance, cikin tsantsar natsuwa kamar dama yasan in da nike ko babu abin da ya taɓa faruwa damu.
Da sauri ya kai hannunsa ya toshe mun baki, can ƙasa ya ce. "Please, I will explain everything, ya isa ƙoƙarin ihun nan, ke ni ban san yaushe zaki girma ki daina tsoro ba tawan".......... Na buge hannunsa daga bakina tare da ja da baya, sannan na ce. "Dan ALLAH da gaske kai ne ko dai gizo ne, ko mafarki ne?"......... Ya juya ya tura kifar ya rufeta ruff har da sanya key, a natse ya juyo da kallonsa kaina.
"Da gaske nine sarkin tsoro". Ya faɗa yana kai hannunsa zai riko nawa, da sauri na janye baya ina kallonsa ba ki kyaftawa. "Awww yau baki jin kunyata kenan kike mun kallon kurewa kyanka gani ko?"...... Ya salam, na gagara yin magana, gabaɗaya Abba ya canza, a shekaru biyun nan gabaɗaya komai nasa ya canza, ya ƙarami girma da cikar zarra sosai, ga wani kwarjini na musamman, and ya ƙara haske kaɗan, ya ciko kaɗan, wani irin musulmin kyau na musamman ya kara, gashin kansa na buzayen nan ya ƙara kyau da sheƙi sosai, har manyan idanunsan nan sai da suka kara kyau, gashin gerarsa kamar zasu haɗu da juna, ya ɗan bar saje kaɗan this time.
"Ni dai ba zan yarda da kai ba har sai ka faɗa mun yadda aka yi kake raye". Muryata na rawa na faɗa. Ya nuna mun side sofa dake cikin ɗakin tare da cewa. "To zauna sai in faɗa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 21 Chapter of 38