Share this page
a kan bakinki ranar?".......... Na girgiza kai alamar a'a. Ya ce. "Cewa na yi bakinki akwai kyau, da tsayawa a rai, kuma zai yi mugun daɗi sha sosai, coz ya tsaya mun a rai, rana ɗaiɗai ne bana mafarkin ina shansa". Duka na kai mashi a damtsen hannu ina faɗin. "Nawan, ka lalace, kai ko?"...... Ya rike hannuna ya sumbata kafin ya ce. "Da na yi me na lalacen?".......... Na yi ƙasa da muryata wajen cewa. "Waye ya faɗa maka size nasu underwears ɗina?".......... Ya ɗan zuba mun waɗan nan manyan idanun nasa na ɗan lokaci, can ƙasa ya ce. "Komai naki ai na sani tun ba yau ba"......... "Abba, idanu kake saka mun ko?". Ya ɗaga mun gera guda alamar kwarai kuwa. Ni kam na bushe da kallonsa na gagara sake yin magana. (Maza masu kawo kannensu gida su ajiye a karo na biyu zan sake yin magana a kanku, wai kuna tunanin su kannen naku waliyai ne? Kuna tunanun babu zuciya a jikinsu ne da ba zasu ji sha'awar abin da kuke jin sha'awarsa ba? Kun ji Abba ya ce ya san komai na ta tun ba yau ba, kuma da gaskiyansa, yo yana ganinta koyaushe, ya za'ayi ba zai sani ba? Ido ba mudu ba ai yasan kima ko? Ko a musulunci haramun ne amma dayawanmu mun ɗauki al'adu muna fifitasu a kan wasu dokokin ALLAH, UBANGIJI yasan da cewa ƙaninka zai iya sha'awar matarka shiyasa ya haramta irin wannan zama, shiyasa kuma matarka bata zama muharammansa ba, dan akwai aure a tsakaninsu, da ka saketa dai shikenan baku da wata alaƙa ta jini, tana gama idda ta halatta wannan ƙani naka ya aureta, kaga kenan kuskure ne babba ajiye ƙaninka a gida suna jera kafaɗa da matarka, idan ya zama dole ya zauna a tare da ku yazamana ko parlo yana da lokacin shiga watau idan kana nan, iyakarsa tsakar gida! Mata kuma gareku, sai ki ce ƙanin mijinki ne ba wata matsala, ki dinga fitowa a irin dressing da kika ga dama, ba mayafi bare hijab, to ki sani wannan babban kuskure ne kike yi, yana nan yana kallon duk wani motsinki yana karance surar jikinki. ALLAH yasa mufi karfin zuƙatanmu) Sumbatar ɗan bakina ya yi wanda hakan yasa na ɗan sauke ajiyar zuciya game da cewa. "Ni ka kyaleni barci nike ji"..... "Da gaske?". Ya faɗa yana ɗaga mun gera. Na shafa gefen kumatunsa ban yi magana ba. Lumshe idanunsa ya yi tare da sake warosu a kaina, sannan ya ce. "Ba'a taɓa mun abu mai daɗin wannan ba, please my wife, ki nuna mun so ko rabin wanda nike maki ne mana"........ Barci na ɗan ɗebana na amsa da. "Idan na baka so me zaka dawo mun da shi as a tukuici?". Wani iri fari ya ji ransa ya yi, a natse ya ce. "Zan dawo maki da kaunar da ba'a taɓa ganin irinta ba"....... Ya matsar da bakinsa dab kunnena sannan ya cigaba da cewa. "Zan kuma baki baby's kyawawa masu kama dake, zan baki kulawar da baki taɓa ganin irinsa ba, zan tallabeki, ina rarrasheki, in zame maki ruwa a lokacin da kike jin kishi, inuwa a lokacin da rana ya fito, haske a lokacin da duhu ya lulluɓe duniya, sanyi a lokacin da zafi yai maki yawa, ɗumi a lokacin da sanyi ya maki yawa, na yi alƙawarin kula dake tamkar yacce zan kula da kaina, kuma na yi alƙawarin ba zan taɓa bari ki shiga kunci ba muddin ina numfashi, koda kowa zai gujeki, ni zan tsaya tare dake, I love more than your expectations, and I love everything about you, coz you're so special my wife". Tun da ya fara magana gabaɗaya barcin dake kaina ya watse, coz nasan Abba baya karya, duk abin da zai faɗa gaskiyar kenan, gabaɗaya ya tashi kaina bawan ALLAHN nan, sai na tsinci kaina da cewa mashi. "Ni kuma in dai haka ne, na yi alƙawarin zama mata ta gari a gareka"......... Wani irin ƙanƙame ni ya yi, muryansa har yana sarkewa wajen cewa. "Da gaske kike yi tawan?". Na jinjina mashi kai kawai ban yi magana ba. Farinciki yasa ya fara sumbatata ta ko'ina, yana zuba mun ruwan albarka. Kiran wayansa da aka yi ne ya dakatar da shi, ya ɗan kwanto jikina tare da fito da wayar. Ya sha mamakin ganin number Abbie a wannan lokaci, katse kiran yai sannan ya kirasa, dan kada ƴar katin Abbien ya kare, kun san kiran number waje sai ka shirya. Yana ɗauka Abbie ya fara zazzaga mashi masifa, wai ya ce mashi ya cire hotona a status amma har yanzu bai cire ba, ya dinga faɗa, wai Abba bai san darajar matar mutum ba ko? Wlh sai ya ɓata mashi rai muddin bai cireni daga status ba, kuma daga yau yana mashi warning da kada ya sake sanya hotona a status. Abba yai shiru yana sauraransa, sai da ya kammala zazzafa masifar nasa tas, sannan Abban ya ce. "Ina da dama ɗaurata a lokacin da na so, sannan in cireta ba dan ra'ayin wani ba, already ba wani ya sanyani ɗaurawa bare wani ya sanyani cirewa, ko ita kanta bata isa sakani cirewa a lokacin da ban yi niyya ba, kuma ina mai gargaɗanka da babban murya kan kiranta matarka da kake yi, ita ba sa'arka bace yanzu, she's my wife, my happiness, my world, ka kiyaye wannan!". Yana kaiwa karshen maganar ya katse kiran ɗiff abinsa. BABBAN MAGANA. "Nawan menene yakefaruwa na ji kana faɗa?". Na faɗa cikin muryan barci..... Ya dawo da eyes ɗinsa kaina, nisawa ya yi tare da ajiye wayar da yake pressing a gefe, ya jawo jikina sosai, ya ɗan sumbaci gefen kumatuna tare da cewa. "Babu komai my wife"...... Da yake ina jin barci sai na amsa da okey kawai. Cikin wata murya ta zallar kauna ya ce. "Baby, please ki kirani da sunan soyayya ko sau ɗaya ne kin ji?"........ Na ɗan nisa game da cewa. "Honey shi ne karshen daɗi da zaƙi, amma ka ce mun kai kafi honey daɗi, to meyakamata in ce maka?". Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya kafin ya ce. "Ki ce mun honey ɗin ya yi tawan"..... Na jinjina kai. "To shikena, my honey I want to sleep"......... Daɗi tamkar ya maidani cikinsa, haka ya dinga lallaɓani har barci ya ɗaukeni, sannan ya miƙe ya rufeni da bargo da kyau kafin ya ɗauki wayata da nasa ya koma saman sofa ya zauna. Yana zama sai ga call ɗin Ibrahim ya sake shigowa wayata, tun ɗazun yake son kirana amma network na Nigeria yaƙi bada haɗin kai, sai yanzu ya samu call ɗin ya shiga. Abba kamar ba zai ɗauka ba, sai kuma ya ce bari ya jawa Ibrahim layi kan matarsa, sai yai picking. Yana ɗauka Ibrahim ya ce. "My love, menene yakefaruwa ne? Tun ɗazun nike ta faman kiranki baya shiga, ɗakun da ya shiga kuma kin ɗauka baki yi magana ba, kin san yadda na damu a kanki kuwa? Ko barci bana iyawa sosai, dole zan zo a satin nan in rabaki da gidan wannan banzan". Ɗan gyaran murya Abba ya yi, coz yana jin ko da wuta kake yawo a bakinka baka isa ka rabani da shi ba yanzu, kowa sai ya yi hakuri, bare ma yanzu da ya fara samo kaina, ai duk bala'in mutum nan gani nan bari. A natse ya ce. "Daga rana irin ta yau, idan ka kuskura ka sake kiran wannan number, ko ka kira matata ta sunnah da sunan soyayya, wlh sai ka yi danasanin zuwanka duniya, sai na maka hukuncin da baka taɓa tsammani ba". Yana kaiwa karshen maganar ya katse kiran ɗiff. Zuciyansa cike da tunani kala-kala ya mike ya fito. Kai tsaye ɗakin Zahra ya nufa. Nan ya isko ta yi barci ita da su Hassan ɗin dukka. Hassan ya fara ɗauka ya kai ɗaki, ya kwantar da shi kusa dani kafin ya dawo ya ɗauki Muhammad, shi ma ya kwantar da shi kusa da ni, sannan ta wuce toilet, sai da yai wanka haɗe da alwala, sannan ya zo ya fara nafilfili, ba shi ya kwanta ba sai 3 na dare, ya kwanta a kusa da su Hassan, sune a tsakiyanmu. Yana tunanin yakamata ace ya kawowa su Hassan mai aiki mace da zata dinga kula da shi dan a sauƙaƙa mun aiki, akwai ɗakin yara, so yakamata ya kawo masu masu aikin da zasu dinga kulawa da komai nasu, ga shi yana zon Hassan ya koma makaranta this coming Monday. Da wannan tunani a ransa barci ya kwashesa. Asuban farko kiran waya ne ya fara tashinsa, idanunsa sun mashi nauyi sosai saboda barci da bai samu damar yi da wuri ba. Ya laluɓo wayan nasa, idanunsa duk barci bai duba number ba ya zo zai yi picking, wayar ta katse. Siririn tsaki ya ja tare miƙewa zaune bayan ya yi addu'ar tashi daga barcin. Ga mamakinsa sai bai ganni a gadon ba, ɗan lumshe idanunsa ya yi ya sake warosu a kan gadon, da gaske bana wajen, wurga eyesball ɗinsa yai a kan toilet door, nan ya hango wutar ciki a kunne. Nisawa yai game sauƙowa ƙasa kafin ya miƙe, jikinsa duk a mace ya ajiye wayansa gefen gado, sannan ya nufi toilet. Yana shigowa ya hangoni cikin jacuzzi ina wanka. Wani Musulmin ajiyar zuciya ya sauke tare da nufoni, ina ta faman kallonsa har ya iso wajen jaccuzin. Na tsunduma cikin ruwa, ba'a ganin komai nawa a waje face kaina. Yana zuwa wajen na ce. "Good morning my honey, yau dai na rigaka tashi". .... Like seriously! Kai, ji yai tamkar a mafarki, like wow, anya kuwa nice? Ai zuba mun ido ya yi ya gagara amsawa. "Irin wanna kallo haka? Ai sai ka sanya in suma nawan". Na faɗa ina ƙara lumewa ƙasan ruwa wai dan kada ya kalle mun jiki. Still bai yi magana ba kuma bai ɗauke kallonsa daga kaina ba. Ruwa na ɗebo a hannuna na ɗan watsa mashi a fuska. Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya tare da ɗan ɗauke kallonsa daga kaina. A natse ya ce. "My beb, da gaske kece?". Na jinjina mashi kai alamar kwarai, sai na ce. "Ka manta jiya na ce zan zame maka mace ta gari ne? Yanzu dai je ka yi wanka sai mu yi sallah, daga nan mu fara neman hanyar sanar da su Hajiyarmu wannan gagarumin laifi da muka aikata"...... A natse ya zauna a bakin jaccuzin game da cewa. "Gaskiya mun aikata babban laifi, amma In Sha ALLAH zamu shawo kansu su aminta damu". ALLAH yasa na ce. A hankali ya ɓalle maɓallan rigan jikinsa, ya zare rigar ya ajiya a gefe, na ɗan ɗauke kallona daga kansa ina faɗin. "Kaga jikinka kamar na ƴan dambe"....... Ya saki one sided smile kafin ya amsa da. "Dole jikina ya zama haka ai saboda kwallo, sai da motsa jiki". Na lumshe idanuna ina tunanin yadda iyayena zasu aminta da Abba, ni dai na sanya a raina zan zauna da Abba, ko dan kaunar da yake gwadawa yarana, ba karamin so yake masu ba......... Ina can ina tunane-tunane na sai ji na yi ya shigo cikin ruwa. Ai a miliyan na waro idanuna waje, sai dai kuma, ina warowa sai kan fuskansa, ya kureni da kallo, ya shigo har ya matso in da nike. Da sauri na rintse idanuna game da cewa. "Nawan ka bari mana"...... Ya lumar da hannayensa cikin ruwan, ya jawoni jikinsa yana amsa mun da. "Me zan bari ƴan'mata? Taɓa halal ɗina? Ko kusantar halal ɗina?"......... Na ɗan shagwaɓe fuska kafin in ce. "Ka bari dukka"......... "Gaskiya ba zan bari ba, hakuri zaki yi dani, dan ma kin yi sa'a ban son yin ɓarna sai mun samu su Hajiyarmu ai da ina ga yanzu mun samu Hussain"........ Na sanya hannayena na rungumesa sosai a jikina, a shagwaɓe sosai na ce. "My honey lokacin sallah na wucewa fa, muje ka yi shiri.........". Maganata ta yanke ne a lokacin da ya kai hannunsa kan kirjina ta cikin ruwan, ya wani irin sauke ajiyar zuciya, bai bari na yi magana ba ya lallaɓa ya haɗe bakina da nasa, ya fara bani zazzafar kiss yana wasa da kirjina, gabaɗaya ya nemi ya susuce mun, sai da na yi da gaske ya iya sakeni muka samu damar yin wanka a tare, ba yadda bai yi ba naki yarda na fito daga cikin ruwan, sai da ya miƙo mun bathrobe ɗinsa, sannan na karɓa na miƙe ina kare jikina, shi dama already da shorts a jikinsa, so bai wani damu ba ya fito. A gurguje ya je yai shirin zuwa Masallaci, a lokacin har na tada sallah, sai da ya tsaya a kusa dani, ya sumbaceni kafin ya wuce masallaci. Ni kuma bayan na idar da sallah na yi zaman askar har zuwa san da ya dawo. Yana dawowa ya zo ya zauna a gaban daddumana, yau saura kwanaki uku yai tafiya, yana son mu tafi tare amma ga school ɗinmu. Yana kallona ina askar, sai ya miƙe ya ɗauko mun saƙona da mutanen kauye suka bashi ya kawo mun. Bayan na kammala ya miƙo mun saƙon, na karɓa ina ta godiya sosai. Ina buɗewa muka fara cin karo da su adduwa, su goruba, su karkashin ne, ƴaƴan magarya, kurna da sauran abubuwan kauye, har da su kukan sha wannan farin, na dinga dariya ina ɗaukan wasu abubuwan ina kaiwa baki. Abba ya ce. "Kai su kawu Badamasi, sun ɗauka nan ma kauye ne, ji har da daddawa suka baki fa"....... Ina murmushi na ce. "Ka sani ko gaba zasu mana amfani". Ya ɗago idanunsa a kaina, sai ya ce. "Gaskiya sosai ma zasu mana amfani gaba". Yai ƙasa da murya wajen cewa. "Idan na buga kwallona a raga ai dole ma su mana amfani, ga shi ni da short ɗaya nike zura kwallo a raga, kinga duk shekara sai kin haifa mana baby". Na kai mashi duka a kirji ina faɗin. "Ni ba nufina ba kenan, kada ka canza mun magana, ALLAH nawan ka zama mara kunya"........ Ya Salam, ya bini da wani irin kallo mai melting heart kafin ya amsa da. "Kome na zama kece sula, duk ke kike rikitani da soyayyarki, and nasan halinki ne ai da laulayi ga ragonta, da cikin takwara me ban gani ba, cikin su Babana lokacin kina yarinya sosai, da ciki kike tsalle ko a jikink, shi ma cikin takwara me baki yi ba? Wahalar dani da kika dinga yi, ALLAH ne kaɗai zai bani lada". Gaskiya a cikin yarana duk Abba ya sha wahala, tare da shi muke laulayin ma, coz duk abin da nike kwaɗayi shi yake zuwa ya sayo mun, mu ci tare, idan na girki ne shi yake girka mun muci tare, ko Abbie uban cikin bai sha rabin wahalar da Abba ya sha ba, zan yi amai shi zai wanke baya damuwa, haihuwar Hassan da Hussain Cs aka mun dan lokacin na yi ƙarama, ga ni ba kiba kamar a hure, a lokacin ban da faɗin baya, ba zan iya haifarsu ba, to lokacin da aka mun Cs ɗin nan Abba ya sha aiki, ina asibiti amma kusan komai na gida shi yake yi, Aunty Maryam na tare dani a asibiti, sau uku Abba yake zuwa a kowace rana, shi yake mana girki kafin a sallamemu mu koma Kaduna, so gaskiya Abba ya sha tayani laulayin ciki ba karya, Muhammad kuwa shi ne kawai na haifa da kaina, a lokacin ban koma gida wanka ba, Aunty Maryam ce ta zo ta zauna dani, Abba na kitchen yana taya Aunty Maryam girki, shiyasa ai nike ce mashi namata, dan kuwa ya aikatu a kaina ba karya, idan Aunty Maryam zata yi girki shi kuma zai yi shara da mopping, kai gaskiya Abba mutum ne, ɗan halak ne. ----------------- "Kai my honey, ni kada ka kawo mun kauli da badi, ni ba wani laulayin da nike yi"...... "Uhm, ALLAH ya kaimu lokacin, ɗan bakin nan zai zo yana rokona zai ci abu mai gishiri, nasan me zan maki ne". Zan yi magana wayansa ya fara ruri yana neman agaji. Miƙewa ya yi ya ɗauko wayar, ya yi mamakin ganin new number kuma daga Nigeria. Duk da bai san waye bane sai ya katse kiran ya kira yana dawowa kusa dani ya zauna, coz ya san koma dai waye daga cikin dangi ne tun da number Nigeria ne. Yana zama kusa dani aka ɗaga kira, shiru yai yana sauraran abin da ake cewa, sai kuma ya ce. "Ina kwana Mama". Daga ɗayan ɓangaren ta amsa da lafiya a hanzarce kafin ta ce. "Ba gaisuwa ce a gabana ba, kawai ka amsa mun, da gaske ne abin da Sulaiman ya faɗa? Kana tare da Aisha?"...... Ya amsa da. "Gaskiya ne, ina tare da ita". Cikin faɗa mama ta ce. "Abba baka da hankali ne wai? Matar yayanka ce fa"..... A ɗan dake ya ce. "Mama, matata dai, ki daina haɗa mun ita da wani bana so"..... Salati Mama ta kawo ta zabga, sai kuma ta fara masifa, wai kada ya sake danganta kansa da matar yayansa, da wuri ya nisanceta ya rabu da ita...... Yai shiru yana jinta har sai da ta kammala, sannan a natse ya ce. "Ko shaiɗan bai isa ya rabani da matata ba bare wani Abbie, Aisha matata ce, sonta nike yi yasa na aureta, dan haka ki jawa Abbie kunne, idan ya kuskura ya sake alaƙanta kansa da matata sai na ɗauresa! Kuma kema ki daina haɗa mun ita da wani bana so". Mama ta dinga salati kafin ta ce. "Muhammad yau ni kake mayarwa da magana ya a kan mace? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun"........ Ya ɗan nisa tare da cewa. "Ki yi hakuri"........ "Ba zan cen yi hakuri bane, umarni nike baka daga yau ka fita harkar Aisha, Sulaiman na shirin dawo da matarsa ne". A ɗan dake ya ce. "Ki yi hakuri, amma ba zan iya rabuwa da Aisha ba, ta rigada ta zama matata, dan haka ban karɓi wannan umarni ba"....... Mama ta ce. "Lallai Muhammad ka girma, to umarni na ce na baka ba shawara ba, ka rabunwa Sulaiman da matarsa". Ganin na tsaresa da ido ne yasa ya miƙa hannu ya jawoni jikinsa, ya rungumeni yana sauke ajiyar zuciya yana cigaba da sauraran masifar Mama, ni kuma burina in ji me yakefaruwa, na ji ana ta ambatar A'isha. Sai da ya kammala sauraran Mama tsab, sannan ya ce. "Ki yi hakuri, amma ba haifata kika yi ba bare yazama wajibi sai na bi umarninki, ina maki biyayya tamkar mahaifiyar da ta haifeni saboda kin rikeni tamkar ɗan cikinki tun ban san waye ni ba, tsawon shekaru 17 da kika reneni ban taɓa bijire umarninki ba, amma yau dai kam sai dai ki yi hakuri, ba zan iya rabuwa da matata ba, saboda ita ɗin bugun numfashina ne". Yana kaiwa karshen maganar ya katse kiran ɗiff, yana shafa jikina cike da tsantsar so. Ya sauƙo da kallonsa a kaina. Ganin yadda na tsare shi da ido ne yasa ya huro mun iska mai ɗumi daga bakinsa, na lumshe idanu ina murmushi, a sanyaye na ce. "My honey ya aka yi?"........ "Kyale su Mama da neman rigima, yanzu dai faɗa mun me kike so?". Ya faɗa yana kamo hannuna cikin nasa. Sai ya ɗaga wayansa dan yai mana video, ya kara jawoni jikinsa, na kwantar da kaina a kirjinsa, cikin shagwaɓa na ce. "Babu abin da nike so face kai, ka gama mun komai nawan, yanzu abu ɗaya ya rage"...... Cikin salon zallar kauna, muryansa can ƙasa ya ce. "Menene ya rage?"...... Na ɗan turo baki ina kara shigewa jikinsa, muryata can ƙasa a shagwaɓe na ce. "Ni kunyarka nike ji my honey". Ya ƙara yin ƙasa da murya tare da rankwafowa kaina kaɗan, ya ɗan sumbaci gaban goshina, yana kai hannunsa saman soft lips ɗina, yana ɗan shafasu ya ce. "Ni ai naki ne, me na jin kunyata kuma?"...... Na ɗago zan saci kallonsa sai na lura ashe video yake yi mana, na yi murmushi game da mai da kaina kirjinsa na kwantar, ina shaƙar kamshin jikinsa, na ce. "Zan faɗa maka abu ɗayan da ya rage, amma sai anjuma". ....... Daidai lokacin ya tsai da video ɗin ya ce. "To mu je in ciyar dake abinci a baki". Na shagwaɓe fuska game da cewa. "Sai dai ka ɗaukeni, ba beb kake ce mun ba? Ni beb ce, kawai ka ɗaukeni"..... Ya ce. "An gama matar mijinta". Yana gama faɗa ya miƙe ya mikar dani, ya zare hijab ɗin jikina ya ɗaura kan daddumar, sannan ya ɗaukeni cak sai waje, har lokacin su Hassan basu farka ba. Zama ya yi dani a kan cinyarsa a saman chair, an kammala shirya komai, ya sanya aka zuba mashi abinci wai zai ciyar dani. Ya fara bani a baki ina mashi yanga, sai na ja ransa nike karɓa. Sai da ya tabbatar naƙoshi, sannan ya ce nima ina bashi a baki. Na jawo abincin na fara bashi, yana karɓa yana dannar wayansa. Status na video ɗinmu na ɗazun ya yi, a ƙasan video ya rubuta MARRIAGE LIFE, ya sanya emojis dake nuna tsananin daɗi da enjoying da yake yi. Ai a lokacin da Abbie ya kalli wannan video numfashinsa ne ya ɗauke ya sumewa sodangi a kan kujera. Su fa maza dayawansu sun fi son su ga idan sun rabu da mace to macen rayuwarta ya tagayyara, ta walaƙanta, ta shiga wahalar da zata ce gwara gidansa, sun tsani su ga sun rabu da mace ta samu cigaba, samun cigabanta na iya fasa masu zuciya, dayawansu haka suke. Yanzu shi Abbie bama kishin bane farko, yadda yaga na canza, na ƙara tsananin kyau, har kumatu na yi, ga Abba yadda yake riritani tamkar kwai a saman faranti, shi ne abin da ya fara dukan zuciyansa, sai kuma kishi, coz yanzu tsananin sona da gaske yake yi, ALLAH ya jarrabe zuciyansa da yi mun wani bala'in soyayya ta gaskiya. To shi ne abubuwan da suka cusguna zuciyansa har da ɗaukewar numfashi ya sume. Shi kam Abba ko a jikinsa, ya ci abinci ya ƙoshi, sannan ya ce mu je sama gabaɗaya mu sha iska. Na ce okey, ya ɗaukeni cak muka koma sama gabaɗaya, wata ƴar karamar wajen shan iska mai ɗauke da kujeru da runfa ne a wajen, ga grass carpet, gaskiya wajen ya haɗu. Saman kujerun muka zauna. Muna zama wayata dake hannunsa ta fara ringing. Ya muƙomun, ina karɓa naga Hajiyarmu sai da gabana ya faɗi, sai na tsinci kaina da ban son ɗauka, har sai da wayar ta kutsa katsewa sannan na ɗauka. Ina karawa a kunne muryarta ya wani doki kunnena tamkar saukar aradu, ta ce. "Aisha Nagode, Nagode da abin da kika mun, ashe Aisha har karya kika koya?". Hankalina a tashe na ce. "Hajiyarmu me ya faru?"........ Cikin faɗa ta ce. "Baki ce mun baki tare da wannan yaro kanin Sulaiman ba? Baki ce tun ranar baki sake ganinsa ba?".... Muryata na rawa na ce. "Haka ne Hajiyarmu".......... Ta ce. "Ashe kina tare da shi A'isha? Har yana ɗaukar wayanki ya faɗawa mijin da mahaifinki ya baiwa ke cewa kada ya sake kiranki ke matarsa ce? Ashe aure ma kenan kika je kika yi? Ashe kin sake wasu iyayen bamu sani ba?". Kirjina dake barazanar tarwatsewa na dake da hannuna, kaina ya wani irin buga da karfi, ban san ta ya zan fuskanci iyayena da wannan magana ba, Ibrahim ya kasheni ya tona komai, yanzu ya zan yi? Hajiyarmu zafi tamkar barkono, daddynmu kafiyar bala'in, yanzu kuma ina jin Abba har cikin raina, kuma na gano shi ne kawai zai iya kula da yarana duniyata, ya rabbi ya zan yi ni A'isha?............ JAMA'A KU BAIWA A'ISHA SHAWARAR YA ZATA YI? labarin A'isha zai dinga zuwa maku labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi. FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥 LABARIN AISHA.🥹💔 PART 38 Follow my TikTok account 👇 https://www.tiktok.com/@princess_teema1?_r=1&_t=ZS-92AoEpYYmwP Follow my Channel account 👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S Muryata

Chapter 31 of 38