maki"......... Ba dan na so ba na ƙarisa wajen na zauna, ina ta kallonsa har lokacin. Ya wuce ya shiga wani kofa da ya buɗe, na bi bayansa da kallo ina tunanin ya aka yi ya rayu?.
Jim kaɗan ya katse mun tunanin ta hanyar fitowa sanye cikin kayan barci, tun kafin ya fito kamshin perfume ɗinsa mai tsananin daɗin shaƙa ya ziyarci hancina. Na shaƙa na lumshe idanuna. Ta kasa ido ya fara kallonsa, ya haɗu iya haɗuwa, ya ƙara kwarjini zarra sosai.
A gefen tangamemen gadonsa ya zauna tare da cewa. "To yi tambayoyinki tawan". Ya Salam, a natse sosai yake magana....... Ban san lokacin dana hararesa ba, sai da na ga ya ɗan ɗaga mun gera guda na fahimci ashe hararansa na yi, na ɗauke kaina da sauri ina cewa. "Ya aka yi kake raye bayan an ce ka mutu? Ina Hussain ɗina? Ya aka yi kasan ina nan ƙasar har ƙasa aka kamoni?". Har na gama tambayar ban ɗago kai ba.
Ya ɗan nisa tare da cewa. "Ranar da na kira yaya ya zo asibiti, na koma ɗauko su Hassan gudun kada na barsu wani abin ya samesu, da na je ɗaukosu na samu Abbie a gida, ya kama wuyar rigana yana tuhumata a kan meyasa zan kira ƴan uwanki. Ya ɓata mun rai sosai, har ya ja na mayar mashi da martani na cewa na kira ɗin, kuma idan bai rabu dani ba wlh sai na mashi duka a gidan nan tun da ya ce shi zalunci kawai ya iya. Mun samu saɓani dai sosai, muka yi musayar yawu, yasan tsab zan iya dukan nasa shiyasa da na ce ya bani key na gate ya bani, na ɗauki Babana da Hussain muka fita gidan da motarki, to a hanyarmu ta komawa asibitin ne motarmu ta daki wata mota muka samu haɗari, daga nan a lokacin ban san me ya faru ba sai farkawa nai na ganni a wani ɗaki wasu maza biyu na jinyata. Da na tambayesu su wayesu shi ne suke faɗa mun a cikin makwararan ruwa suka tsinceni kwance cikin jini suka kawoni asibiti, daga nan suka dawo dani gida. Intakaice maki na yi jinya a hannunsu na wata, bayan na samu lafiya na fito ne na fahimci a Abuja still nike, amma ta wajen gari, sai dai ina shiga gari na tarar Abbie ya gama faɗin mun mutu ni da Hussain, hakan yasa na ɓoye kaina, dama Abbie na shirin rusa mun burina, dan cikar burina na ɓoye kaina na tabbata matsayin matacce, na koma ƙungiyarmu mun cigaba da buga kwallon kafa, da ALLAH ya tashi ɗaukakani ban yi watanni uku ina bugawa kungiyarmu kwallo bama manyan kungiyoyin kwallon kafa na duniya suka yi caaa a kaina saboda iya ball ɗina, kowani team yana so ya sayeni in bugawa team ɗinsa, ban so fasa bugawa Nigeria kwallo ba, amma a lokacin ina son fin yadda nike saboda dalilai biyu, na farko in koyawa Abbie da dangina hankali, na biyun kuma zan faɗa maki ki bini bashi"...... Ya ɗan nisa tare da sauke ajiyar zuciya kafin ya cigaba da cewa.
"Shiyasa na ɓoye kaina, na zaɓi ƙungiyar da zan bugawa kwallo, sun ɗaukeni, amma na ɓoye fuskana saboda bana son kowa ya san ina raye har sai na cinma abin da nike so".
Ya ɗan ɗaga mun gera guda saboda ya ga ina ta kallonsa kafin ya cigaba da cewa. "Batun sanin kina ƙasar nan kuma ban sani ba, tun da na bar Nigeria na watsar da komai na ƙasar, ban san me yake faruwa ba, abin da ya sa na san kina ƙasar nan shi ne, awa ɗaya da suka wuce na ganki a wajen restaurant da na je tayasu murnar opening, babban abokina ne mai wajen, shiyasa na je tayasa murna, na ganki a wajen, amma ke baki ganni ba, bana son kowa yasan komai a kaina shiyasa ban maki magana a wajen ba, na bari sai da kuka tafi nasa aka ɗauko mun ke, batun Hussain kuma da gaske ne ya rasu, shikenan tambayar ko akwai saura?". Ya faɗa yana ɗaga mun gera guda.
Na sauke ajiyar zuciya mai nauyi, na gagara sake yin magana, sai kallonsa kawai nike yi, gabaɗaya ya canza mun tamkar ba shi ba.
"Tawan"....... Ya ambaci sunana a hankali. Da sauri na ɗauke kallona daga kansa, sai kuma na fashe da kukan da na rasa gane na menene, shin na farinciki ne ko na ƙunci?.
Ɗan zare mun ido yai tare da cewa. "Menene kuma?". Ya faɗa yana miƙewa tsaye. Kan sofar ya dawo ya zauna tare da riƙo hannayena, cikin sanyin murya ya fara rarrashina. Duka na fara kai mashi a jikinsa ta ko'ina ina faɗin. "Shi ne kana raye baka nemeni ba saboda baka damu da ni ba, watau idan mutuwa ne ni in mutu a hannun yayanka ko?".
Ya rike hannun da nike kai mashi dukan game da cewa. "Ai nasan na miƙaki ga ƴan uwanki wanda nasan duk son da zan maki ko kula da zan baki ba zai kai rabin wanda zasu maki ba, ban barki a hannun Yaya ba".
Kuka mai sauti sosai na fashe da shi ina faɗin. "Ba wani nan, idan ka damu dani zaka waiwayeni, amma tsawon shekara biyu ka waiwayeni ko sau ɗaya ne?"....... Hanmunsa na ɗan rawa kamar ma yana tsoron taɓani haka ya ɗan jawoni jikinsa yana faɗin. "A nan kam na yi kuskure kuma na karɓi laifina, ki yi hakuri, and a zuciyata ina jin cewa kina cikin farinciki, da ace kina cikin bakinciki zuciyata zata matsa mun, idan ta matsa mun kuma dole in nemeki ai tawan".
Na kwace kaina daga jikinsa ina faɗin. "Kada ka sake mun magana". Na faɗa tare da miƙewa. Hannayena ya riko cikin nasa, can ƙasa ya ce. "Har yanzu dai rigimamma kike, baki canza ba, please forgive me tawan".
Na sharesa na ƙi kulasa, ya dinga bani hakuri yana lallaɓani har sai da na hakura, na tambayesa ina Zahra ƙawata, ya ce mun Zahra na ɗakin da aka bata. Na ɗan turo baki tare da cewa. "To ka mai dani gida"...... "Ba zaki kwana a nan sai da safe ba?".
Na gyaɗa mashi kai alamar e ba zan kwana ba. Ya wurga mun kallon ƙasan idonsa da ya saba yi mun ɗin nan kafin ya ce. "Ya aka yi yaya ya barki kika zo ƙasar nan ne?"..... Na ɗan hararesa tare da cewa. "Kawai ka ce in baka labarin abin da ya faru"...... Ya ɗan yi one sided smile kafin ya ce. "To a bani labari, na matsu in ji meyakawoki nan".
A natse na fara bashi labrin komai da ya faru, ban rage komai ba, sai dai kafin in kammala labarin hawaye sun gama wanke mun fuska. Ya yi matuƙar tausaya mun, amma sai ya tsinci kansa da farinciki, ya riko hannayena gam cikin nasa, can ƙasa ya ce. "Say Alhamdllh tawan"..….... Na sauke ajiyar zuciya, da kyar na furta Alhamdllh ɗin.
Hannunsa ɗaya ya kai kan fuskata ya fara goge mun hawaye, a natse ya ce. "Tun ɗazun da kike kuka ina son goge waɗan nan hawaye amma ina tsoron taɓa matar mutum in shiga uku, but now uhmmm ina da dama"........ Hannunsa na buge game da cewa. "Yanzun ma baka da dama, ni dai ka zo ka mayar dani gida please".
Ya make mun kafaɗa game da cewa. "Ai ɗazun da na ce zan mayar dake na zaci matar aure ce, yanzu kam ba gidan da zan mayar dake, tashi mu je ki ci abinci"..... Da sauri na ce. "A'a ni dai ka mayar dani gida"......... Yana ɗauke hannunsa daga kan fuskata ya ce. "Please tawan ki bani damar fara rama maki alkhairin da kika mun, kome nazama yau a duniya kece sula, yau a duniya duk in da na shiga ina da tarin miliyoyin masoya dake ihun sunana da cincirindon zuwa ganina tamkar wani tauraro, burina ya cika, na ɗaukaka a duniya, na yi kuɗin da ban taɓa zatan xan rikesu ba, team da dama nemana suke zasu biyani ko nawa in buga masu kwallo, sai na zaɓi team da nike so, haka sai na zaɓi ƙasar da nike son zama, duk kuma sanadinki ne, kece sular komai, dan ALLAH ki yi hakuri ki zauna a wannan gida har ki kammala karatunki, gida nane, kada ki zauna a gidan haya kin ji? Nan gidanki ne, kome kike so akwai, in babu za'a kawo maki, and duk karshen wata ina zuwa ƙasar nan ina sauƙa a nan, please ki zauna kin ji?".
Hawaye na cigaba da zuba a idanuna na ce. "A'a Nawan.........." . Yatsansa ɗaya ya ɗaura kan lips ɗina tare da cewa. "Dan ALLAH ba dan ni ba, kullum ina addu'ar ALLAH kada ya karɓi raina kada ya karɓi ranki har sai na samu dama na kyautata maki, na sanyaki farinciki, na sanya dariya a kan wannan kyakkyawan fuska naki, ba zan taɓa barin wani bakinciki ya samu gurbi a fuska ko a zuciyarki ba, yanzu na samu dama, kada ki hanani kyautata maki, kin ji tawan?".
Ban yi magana ba, na rasa abin faɗe, na sunkuyar da kaina ƙasa. Hannunsa ya sanya ya ɗago haɓata muna fuskantar juna, can ƙasa ya ce. "Hawayen nan ya isa mana tawan, suna damuna zubansu, please ki dakatar dasu ko in ɗauki mataki"...... Na ɗan turo baki tare da buge hannunsa hakan yasa ya saƙi haɓar tawa.
Da sauri na yunkura zan miƙe, hannuna ya rike. "Please, ki bari in kyautata maki kin ji? Nasan baki mun dan in biyaki ba, amma ɗan ALLAH ki bari in kyautata ma, and nasan ba zan iya biyanki ba kome zan maki, dan ke kin bani ne a lokacin da bani da shi, a lokacin da in kika barni rayuwata zata kare a garare ne kawai"...... Ya yi ƙasa sosai da murya wajen cewa. "Komai dana mallaka naki ne, har ni kaina naki ne, please".
Komawa na yi na zauna, sai na kifa kaina a kan gwiwowina, lokaci guda kukana ya ɗan tsaya, na ɗago kai na hararesa tare da cewa. "Ka yaudareni da daɗin baki ko?"...... Ya sauke wani musulmin ajiyar zuciya tare da cewa. "A'a, ba wani daɗin naki gaskiya ce".
Na yi shiru ina ɗan kallonsa ƙasa-ƙasa, shi kuwa kallona kai tsaye yake yi, ya zubawa facena ido yana mun wannan kallon nasa mai wuyar fassaruwa. Can na ce. "Abba ka ƙara kyau sosai"..…...... Ya ɗan ja dogon hancina. "Ko rabinki ban kai ba ai tawan".
Uhm na ce tare da cewa. "Yunwa nike ji to, kuma na gaji sosai, Zahra ta kaini yawo sosai har na gaji, ka kaini in ci abinci, ina son yin wanka, sannan kuma wayata, ina son yin kiran".......... Ya ce. "An gama ranki shi daɗe, idan akwai wani abin da kike so ma faɗi".
Na ce babu komai. Miƙewa yai zai fita na ce. "Zan bika"......... Ya ɗan kalleni, sai kuma ya ce. "Ina zuwa, gidan nan dukka maza ne, waje zan je"........ Ina kallonsa bai yi magana ba, ya wuce ya nufi waje, na bi bayansa da kallo har ya fita. Dawo da kallona kan ɗakin na yi. Like wow, ɗakin yai bala'in haɗuwa, a raina nace kile bedroom ɗinsa ne.
Ina zaune ya dawo hannunsa rike da wayata, yana zuwa ya miƙa mun tare da cewa. "To tashi mu je da kaina ma zan baki abincin nan a baki yau kam"......... Na karɓi wayata game da miƙewa, na yi gaba ina amsa mashi da cewa. "Yau kuma bai dani su Hassan zaka yi kenan?".
Daga ni har shi mood ɗin mu ne ya canza tuna su Hassan da muka yi, ya gagara bani amsa, ni ma na yi shiru har muka fito waje, daga nan muka nufi wani haɗaɗɗen corredor, na dinga kallon gidan, ya haɗu karshen haɗuwa, komai na gidan white and gold ne, harta kalar fenti white and golden ne.
Ƙasa muka sauƙo, naga wani katafaren parlo na alfarma, muna sauƙowa ya matsa ya kama hannuna muka canza hanya tamkar zamu bar parlon, sai naga mun shiga dining room. A natse ya ce. "Tamkar nasan zaki dawo cikin rayuwata, yunwa nike ji tun yamma, amma naƙi cin abinci, na ce sai na je wajen restaurant na abokina na dawo, ashe da rabon in yi cin abin da ban taɓa yin irinsa bane". Ya kai karshen maganar tare da jawo mun chair.
Na zauna ina danna wayata. A daidai lokacin kiran Ibrahim ya shigo. Pick-up na yi tare da karawa a kunnena. Daga ɗayan ɓangaren ya ce. "My sarauniya, ina kika jefar da wayan tun ɗazun nike ta faman kira amma baki ɗagawa, lafiya?"......... Na amsa da. "Lafiya lou, Zahra ta kaini yawo duk ta gajiyar dani".
Abba ya zauna a chair dake fuskantata, sai ya danna waya ƙararrawa, take wani katon bodyguard ya shigo dining room ɗin, sai kallona Abba yake yi babu kyaftawa, kaman yana son sanin da waye nike waya, nima sai satar kallonsa nike yi ina sauraran Ibrahim da ya ce. "Kai amma sai na hukunta Zahra ɗin nan, a kan wani dalili zata kai mun ke yawo, tana da izinin fitar da matar mutum ne? To take sai ya ja mun kin fara ciwo ko?".
Na ɗan yi murmushi game da cewa. "Bari in yi dinner zamu yi waya anjuma ka ji?"...... Ya amsa da. "Ko in zo in ciyar dake a baki ne my Aesh?"........ Ina satar kallon Abba da ya ɗauki spoon yana ɗan jujjuya abincin cikin plate ɗinsa na amsa da........ "Nesa bata maganin kusa ai".
Ibrahim ya ce. "Ke kika ja mana nisa da juna ai, ki barin in kawo maki kaina kina jan lokaci, da tuni muna tare da juna, da yanzu ni zan ciyar dake a baki".
Na buɗe baki zan yi magana Abbie ya tura mun apoon mai ɗauke da abincin da ya ɗebo a bakina, sannan ya mika hannu ya karɓi wayar dake manne a kunnena, ya katse kiran yana faɗin. "Lokacin cin abincinki ne, waye ne ma Ibrahim kuma?".
Na hararesa game da cewa. "Zaka fara kenan?"........ Ya ɗan ɗaga mun gera game da cewa. "Farawa kam mai zafi ma kuwa, mai hujja da dalili, waye shi ɗin?". Ya faɗa yana ɗaure fuska.......... "Eyeee, to sannu, kaga kada ka wani ɗaure mun fuska dan ba razanani zaka yi ba".
Ya ƙara haɗe rai game da cewa. "Yanzu ma duk ba wannan ba, kafin ku zo kan waye kuke waya kalli kayan jikinki, sleeping dress ne fa, da a haka zaku je cikin restaurant ɗin cin abinci? Yaushe kika canza har haka?". On a serious note yai maganar........ Na ɗan kalli kayan jikina, sai na ce. "No, ni dama a mota zan zauna Zahra tai mun takeaway, ta dage ne sai na rakota shiyasa kawai na fito haka dan already na yi shirin kwanciya".
Ya ɗan jinjina kai yana kara haɗe gerar sama da ƙasa kafin ya ce........
labarin A'isha zai dinga zuwa maku labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi.
FATEEMA ZAHRA MUSA
A-K-A
QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥
LABARIN AISHA.🥹💔
PART 27
Ya ɗan jinjina kai yana kara haɗe gerar sama da ƙasa kafin ya ce. "Amma ai a haka kika fita cikin mutane har na ganki ko?"....... Na ɗan turo baki gaba. "Duk Zahra ce sila, ita ta tafi ta barni ciwon kai na ƙoƙarin halakani".
Ya miƙa hannu ya ɗan taɓa kan nawa game da cewa. "Har yanzu yana ciwo ne in kaiki asibiti?"........ Na girgiza kai alamar a'a.
Uhm ya ce kafin ya cigaba da bani abincin a baki. Can kuma ya ce. "Shi kuma na wayan fa? Wanene shi?"........ "Uncle ɗin Muhammad ne". Na bashi amsa ina miƙa hannu zan ɗauki ruwa, ya ajiye spoon na hannunsa ya rigani ɗaukar ruwan, ya zuba mun a cup ya miƙo mun kafin ya ce. "Uncle ɗin Muhammad, uhm to shikenan ci abinci ki je ki huta"........ Na ce okey, ya cigaba da bani ina karɓa, sai tsokanansa nike, amma bai wani kulani sosai ba.
Cikin zolaya na ce. "Nawan kai ka yi girkin nan ko?"........ Ya ɗan girgiza kai alamar a'a kafin ya amsa da. "Kuku ne ya yi". ........ "Ka daina aikin mata ne?"....... Na jinjina mun kai alamar yeah ya daina..... Sai na ce. "Nawan yanzu so kake in daina ce maka na mata kuma rago ko? Shi ne yasa ka daina aikin mata?".
Ya ɗan zubawa bakina ido yana ɗan ciza gegen laɓɓansa a hankali, sai da na gama magana sannan ya ce. "A'a, ni ban ce ki daina ce mun na mata ba, cigaba da cewa, lokaci zai zo da babu wanda zai ce maki ki daina zaki daina ne, a wannan lokaci ko da kuɗi aka baki dan ki ce ba zaki ce ba"........... Na ɗan ɗage gera tare da cewa. "E to, idan ka yi aure ma zan ɗan rufa maka asiri in daina cewa dan kada matar da zaka aura ta raina mun kai".......... Ya wurga mun wani irin kallo bai yi magana ba.
Can na ce. "Nawan kasan me?"......... Ya girgiza kai alamar a'a...... Cikin zolaya na ce. "Girkinka nike son ci da safe, na yi kewar abincin da kake girkawa da hannunka".... "Really?". Yafaɗa haɗe da ɗaga gera guda. Na amsa da. "Yeah, na yi kewan abubuwa sosai".
"Faɗa mun duk abin da kike kewa sai in maki ki daina kewa". ..... Na ɗan zaro mashi ido alamar da gaske kake yi?. Ya jinjina mun kai alamar yeah da gaske yake yi. Na ɗan ture hannunsa da ya kawo abinci zai samun a baki. "I'm okey sir". Na faɗa......... Ya ajiye spoon ɗin tare da cewa. "Muje ki kwanta to".
"To kai baka ci abincin ba ai".... Ya ɗan girgiza kai game da cewa. "Na ƙoshi gaskiya"......... Na ɗan zare mashi fararen idanuna kafin in ce. "Yanzu fa ka ce mun kana jin yunwa"....... Ya ɗan jinjina kai, can ƙasa ya ce. "Before ki ci ina jin yunwa, yanzu kuma ina ga saboda kin ƙoshi ne na ji nima haka".
Ƴar dariya na yi game da cewa. "Kai dai kam ALLAH ya shirya mun kai, cikina da naka ɗaya ne?".…....… Yana ta kallona bai yi magana ba....... Na hararesa game da cewa. "Ka daina mun irin wannan kallo kana rikitamun tunani, bana gane wani irin kallo ne". ....... Shiru bai amsani ba, kuma bai daina irin kallon ba.
Hannu na miƙa na rufe idanunsa ina faɗin. "Kai ni bama zan zauna da kai a gidan nan ba, irin wannan kallo zaka sanya mutum suma, wai ni yaushe ma ka daina jin kunyata ne nawan?".......... Slowly ya kai hannunsa ya zare nawa, ya ɗan ƙanƙame hannun nawa a cikin nasa, wani irin tsananin farinciki yake ciki ne wanda yasa gabaɗaya ya gagara dannewa, ya ji in ya ce zai yi wani magana mai tsawo zai iya ruwan hawaye saboda tsantsar farinciki, shiyasa ya yi shiru kawai yana kallona.
"Abba, lafiyarka?". Na faɗa ina kallon fuskansa da har yanzu yaƙi ɗauke kallonsa daga kaina. Still bai yi magana ba. Ganin hakan yasa na yunkura zan miƙe, da sauri ya ce. "Please". Can ƙasa yai maganar.
"Abba, meyafaru kake mun irin wannan kallo haka? Lafiyarka kuwa?". Babu wasa a tattare dani na faɗa........ Ya furzar da iska mai ɗumi daga bakinsa kafin ya sake hannuna game da nisawa, a natse sosai ya ce. "Muje in kaiki ɗakin da zaki kwanta kin ji?"...... "Baka amsa mun tambayata ba". Na faɗa ina miƙewa.
"Ki bini bashi zan amsa maki wani lokaci"....... Zan yi magana ya ce. "Bashi uku kike bina yanzu, na ɗaya alƙawari kan maganar ɗan bakinki, na biyu dalilin da yasa na ɓoye kaina dan in koyawa dangina hankali na biyun kuma zan faɗa maki na ce shima, yanzu kuma dalilin kallonki, maganganu uku kike bina bashi, zan biyasu a ranar da baki taɓa tsammani ba".
Yadda Abba yake magana a tsananin natse ne yake mugun jan hankalina, nawan akwai natsuwa sosai........ Na amsa da. "To shikenan ALLAH ya kaimu wannan rana, mu je ka kaini wajen Zahrata tukun nan, sai na ganta"........ Shiru yai yana tunanin haukar da Zahra ɗin ta mashi farkon kawomu da aka yi, da ta gansa zaucewa ta yi, ta daka tsalle ta rungumesa tana faɗin dama akwai ranar da zata gansa ba securitys ba kowa kuma ba nose mask, da kyar ya janyeta daga jikinsa.
Ganin ya yi shiru yasa na ce. "Tunanin me kake yi?"....... Ya wurga mun manyan idanun san nan tare da ɗan girgiza kai alamar babu komai. Na miƙe shi ma ya miƙe, hannuna ya kama, ina ƙoƙarin kwacewa ya ce. "Sai kin ɓata hanya a cikin gidan nan"..... Ya san gidan akwai rikitarwa ne, hanyoyi, ɗakuna da tsarin ginin in ba ka saba ba ɓata zaka yi a cikin wajen shiyasa yake kama hannuna. Da sauri na ɗauki wayata.
Ina jin hakan na ƙara ƙanƙamesa, ya ce. "Kanwata sarkin tsoro". Ya faɗa a lokacin da muka fara tafiya........ Na ce. "Kai kai kai, wlh baka isa ba, nice ma kanwar taka? Ko kuma kai ƙanina ni Auntynka ba, ka manta ni Auntynka ce ko?"........ Ya ce. "Da gaske wai nine ƙaninki?"....... Na jinjina kai. Sai ya ɗan matse hannuna cikin nasa da ɗan karfi wanda yasa na saki ƴar ƙara har kamar zan tsuggunna ƙasa saboda zafi.
Ya ɗan yi one sided smile tare da cewa. "To kinga dai yanzu ni ne babba, dan in ni kika matsewa hannu haka ba abin da zan ji, ragwaye sune ƙanana a kan jarumai"..... A ƙule na kai mashi duka a bayansa ina faɗin. "Wasa-wasa ka zama mugu"........ Can ƙasa ya ce. "Tukun nan ma dai, ban zama ba, sai ranar da na kama wannan ɗan bakin na ce mun na mata zaki yi bayani".
"Karya na yi ne kai ba na matan bane? Ko karfi fa baka da shi, kullum kana kwance a gida". A ƙule na faɗa. Ya ɗaga mun gera guda tare da cewa. "Da gaske tawan?". .... Na ɗaga mashi gera nima. Dakatawa da tafiya ya yi, na bisa da kallo ina jiran jin me zai sake cewa mun kuma. Ban ankara ba sai ji nai ya yi sama dani, sai kan kafaɗansa.
"Very soon na kusa goge rainani da kika yi mun yarinyar nan". Ya faɗa yana nufar sauƙa kan wata staircase mai step 5......... "Ni ka saukeni". Na faɗa ina haɗe rai....... Ya ce. "Ni da bani da karfi, ai kin fini karfi, na mata nike, ai maza ki kwaci kanki". "Idan baka saukeni ba ALLAH cizonka zan yi".
Ya tsaya a wani waje game da cewa. "Eyeee, karfin cizo kawai kike da shi kenan?". Yai maganar tare da kai hannunsa jikin kofar dake wajen....... Da na ga da gaske ba zan iya kwace kaina ba sai na marairace murya, cikin shagwaɓa da sigar ban hakuri na ce. "Please nawan ka saukeni to"....... Ya ɗan yi one sided smile, a daidai lokacin kofar ta buɗe, ya sauƙeni ƙasa yana faɗin. "Muje Zahrar taki tana ciki".
Da sauri na wuce ina hararansa. Cikin zolaya ya ce. "Kefa ni na raineni, a hannuna kika girma, dan haka duk wani rigimarki ba kalar wanda ba sani ba, tun kina 14 years kike hannuna in ma kin manta ki tuna"....... Na watsa mashi harara ina shigewa ciki. A natse ya taka ya bi bayana muka karisa ciki.
Zahra na zaune a bakin wani katon gado ta buga uban tagumi, tana ganinmu ta miƙe da gudu ta nufoni, sai kuma ta tsaya ganin Abba a bayana, jikinta na rawa ta ce. "Dear, super hero ɗina ne fa, shi ne, ya buɗe fuskansa yau". Duk tana birkice. Kafin in yi magana ta ƙarisa wajen da Abba yake tsaye ya zura hannayensa a aljihun wandon jikinsa.
Tana zuwa ta rungumesa tana faɗin. "Dan ALLAH ya bari su yi hoto a haka"...... Na juya ina kallonta cike da mamaki, na ɗago ido na kalli Abba dake kallona, ban san lokacin da na dallah
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 22 Chapter of 38