Share this page
ishai, sai na zauna kan dadduma ina addu'a ina kaiwa ALLAH kukana. A daidai lokacin shi ma Abba yana kan dadduma yana kaiwa ALLAH kukansa a hotel da ya sauƙa, bai je kauye ba kuma bai je wajen Mama ba, dan yana cikin damuwar da abu kaɗai zai kama faɗa da mutum ne, shiyasa ya keɓe kansa. Ina zaune Aunty Maryam ta shigo ta sameni, a gefen gado ta zauna game da cewa. "Idan kin idar ki zo ina da magana dake"...... Na juyo na kalleta dan a lokacin na kammala addu'ar tawa. Na miƙe na naɗe daddumar kafin in dawo kusa da ita in zauna, muryata har yanzu a dashe na ce. "Aunty gani nan". A natse cikin fahimta ta fara yi mun faɗa, ta ce bai kamata ba abin da na yi, ta ji zafin wannan abin, amma kuma hakan ma shi ne yafi a kan zina, da ace wani abin na je na aikata ai gara wannan aure, kuma tasan su Hajiyarmu sun san cewa gara hakan a kan zina, and sun san dole a ƴan shekaruna ɗin nan zan buƙaci namiji, su abin da ya masu zafi yadda na sake koma wannan family na mutanen banza. Jikina duk ya yi sanyi, ko Aunty Maryam bata faɗa ba nasan na tabka babban kuskure, amma kuma ai nima bada son raina bane, Abba ne yai wasa da tunanina. A natse na fara zayyanewa Aunty Maryam yadda komai yafaru, dallah-dallah ban ɓoye mata komai ba. ....... Cikin faɗa ta ce. "Aikuwa to in dai haka ne yazama dole ya zo ya sakeki". Da sauri na ce. "Aunty baki fahimta bane? Ina son shi sosai, ba zan iya rabuwa da shi ba, kin san adadin son da yake mun kuwa?"....... Ta girgiza kai alamar a'a, nan fa na shiga bata labarin irin zamanmu, kulawar da yake bani, tsantsar son da yake mun, son da yake yiwa yarana. Ai ina kaiwa karshe Aunty Maryam ta ce. "Lallai wannan shi ne mijin aure, gaskiya ba zan so ki rabu da shi ba Humaira, amma yanzu ya zamu yi da su Hajiya? Kinga dai yadda suka ɗauki tsananin zafi a kan wannan al'amari, and sun yi wa su Sulaiman dukka kuɗin goro, ba zasu yarda Muhammad na daban bane". Na riko hannun Aunty Maryam ina rokonta da ta taimaka ta tayani baiwa Hajiyarmu hakuri, su yarda da Abba. Auntyna ta mun alƙawarin tayani, sannan ta ce in kira mata shi in haɗasu a waya. Da sauri na ɗauko wayata na kira, bugu ɗaya ya katse, dan shi ma a lokacin ya ɗauko wayansa zai kirani kenan sai ga kirana. Tun a nan Aunty Maryam ta jinjinawa Abba, yadda bai ɗauki kirana ba ya katse ya kirani, wannan shi ne namiji. Yana kirana na sanya wayan a H-free. Muryansa a sanyayye ya ce. "Assalamu alaiki my wife"...... Na ɗan saci kallon Aunty Maryam, duk kunya ta kamani, dama na so ne wai in saka shi a free dan ta ji irin yadda yake kula dani, sai kuma na ji kunya. Ina ƴan kame-kame na amsa da. "Wa'alaikassalam, ina wuni". "Lfylou Alhamdllh, kin wuni lafiya ina yarana?"....... "Suna wajen Safiyya"...... Ya ɗan yi shiru, can kuma ya ce. "Ina begen ganinki matata, ashe haka muka yi sabo, ashe ba zan iya nisa dake sosai ba, akwai wahala my wife, anya zan iya wannan tafiya in barki kuwa? Kin san da ya na kawo dare kuwa? Na ga lokaci baya mun sauri da baki tare dani, duk na shiga damuwa sosai". Gabaɗaya kunya takamani sai na ce. "Nawan dama Aunty Maryam ce ta ce in kira mata kai ku gaisa, gata nan". Ina gama faɗar hakan na miƙa mata wayar tare da miƙewa na nufi fita waje. Naki tsayawa in ji me suka tattauna. Ina fitowa na samu Hajiyarmu a parlo, in da take na nufa, a gabanta na durkusa na sake bata hakuri, ta dinga mun faɗa kafin ta ce babu komai, shikenan komai ya wuce. Na mike jiki ba kwari na isa dining area ɗinmu. Na zuba abinci na hau ci, a nan Aunty Maryam ta zo ta sameni, nan fa ta fara tayani santin Abba, wai he's so nice, sai kuma ta ce. "Aisha ashe haka yake da arziki? Kin san na yi searching a kansa yanzu, ya salam, ɗan kwallon dake tashe yanzu, manyan team yake bugawa"........... Aunty Maryam fa tana da son sharholiya abinta, aikuwa ta ji daɗin ganin Abba na da kuɗi, ta ƙara zugani wai duk wuya kada in kuskura ko da sunan wasa in ce zan rabu da shi, dan ya haɗu, na amsa mata da In Sha ALLAH. A gaskiya Aunty Maryam ta taka muhimmiyar rawa wajen ganin ta gyara alaƙar Abba da su Hajiya, and ta taimawa Abba sosai, saboda kullum tana kara ingiza zuciyata, tana nuna mun irin daɗin rayuwar da zan samu a wajensa, hakan yasa na kara jin duk wuya duk daɗi ba zan taɓa rabuwa da Abba ba, Aunty Maryam ta kwaɗaita mun zama da shi sosai da sosai. Intakaice maku haka na yi kwanaki uku a gida kullum cikin neman mana mafita, muna kwana waya da Abba, ya yi ta zuba mun rigimar ya gaji da nisa dani, haka nike ta bashi hakuri, ba'a awa ɗaya bai kirani ba, kodayaushe cikin neman mafita muke yi, na ɓoyewa iyayena ina cikin tsarkina kuma ina sallah, a ɓoye nike sallahta, Aunty Maryam ce kawai ta sani. A rana ta huɗu da dawowana gida ne na samu Hajiyarmu da Aunty Maryam a ɗaki suna zaune, Aunty Maryam tana ta faman nunawa Hajiya kirkin Abba. A gaban gadon Hajiyarmu na durkusa, cikin girmamawa na ce. "Barka da hutawa Hajiya". Ta amsa fuska ba yabo ba fallasa, hakan yasa na ji daɗi, kuma na kara samun kwarin gwiwar isar da saƙon da nike tafe da shi. Cikin girmamawa na ce. "Hajiya dama magana nike son mu yi". Ta ce. "Ina sauraronki"........ Kirjina na bugawa da karfi-karfi, na dinga maimaita lailaha illallah anta subhanaka inni kuntu minazzalumin, da kyar na saita natsuwata, na tattaro sauran kwarin gwiwar da Aunty Maryam ta dinga bani na ce. "Kiyi hakuri Hajiyarmu, ranar da na ce kada Abba ya sakeni ina cikin period karya nike, hasalima bana al'ada saboda cikinsa dake jikina, na ji tsoron ki rabani da shi ne yasa na ce haka, amma dan ALLAH ki yi hakuri ki yafe mun"........ Kirjina na bugawa da karfi na faɗa. Na zauna na gama tunanin duniyar nan na rasa samo mafitar da zai sanya su bar mana aurenmu, shi ne na ga kamar idan na ce masu ina da cikin Abba zasu hakura. Hajiyarmu ta dinga salati tana sake maimaitawa, sai kuma ta yi shiru bata ce komai dangane da cikin ba. Na matso na rike hannunta, cikin tausasawa da girmamawa na ce. "Duk abin da kike yi saboda farincikina kike yi nasani, ki yarda dani Hajiya, wlh ban taɓa daidai da second ɗaya in yi burin ɓata maki rai ba a duniya, kuskure aka samu, kuma na karɓi laifina, ina baki hakuri sosai, dan ALLAH Hajiya kada ki ɓata rai, in kina fushi dani ina zan tsunduma kaina in ji daɗi? Idan kina fushi dani fa fushin ALLAH zai hau kaina, ke uwa ce ta gari a garemu, kullum kina iyaka bakin ƙoƙarinki wajen ganin kin inganta rayuwarmu, mun san da hakan, muna matuƙar alfahari dake matsayin uwa, dan ALLAH ki yafe mun mahaifiyata farincikina, na maki alƙawarin ba zan sake maimaita makamancin wannan kuskure ba". Da yake tun da nike da ita ban taɓa saɓa maganarta ba, kuma tsakanin uwa da ƴa sai ta kama hannuna, a sanyayye ta ce. "Cikin naki wata nawa ne?"...... Na ji tsoron kada ta ce a zubar, dan in bai kai wata huɗu ba a yadda ta tsani dangin Abbie tsab zata ce a zubar Abba ya sakeni, idan kuma na ce ya kai wata huɗu to ina yake? Duk da cewa basu san yaushe muka yi aure ba amma dai ciki wata huɗu ba zai ɓuya ba, ga cikina a shafe can ina naga wajen nuna ciki wata huɗu a wajen?. Nan fa fargaba ta kamani, na shiga zazzare ido, Aunty Maryam dake gefen Hajiya ne ta ce. "Ba ɗazun kin ce mun baki san cikin naki wata nawa bane?"........ Da sauri na ɗago na kalli Aunty Maryam, saboda nasan ban yi maganar ciki da ita ba, ashe ta yi ne dan ta bani mafita, tamkar tasan abin dake raina kenan rashin mafita. Ina ɗago ido muka haɗa ido da ita sai ta kashe mun ido ɗaya. Wani irin daɗi ne ya maimaiye zuciyata, na ce. "E, ban san wata nawa bane". Hajiya ta ce. "To shi ne baki faɗa mana da wuri ba kika bari kike zama cikin damuwa? To maza ki je ki shirya Maryam ku je asibiti a gwadata muga cikin wata nawa ne?". ... Aunty Maryam ta shawo kan Hajiyarmu, ta nuna mata ai gara aure da na je na aikata zina ko wani abin da ba shikenan ba. Na ƙanƙame hannun Hajiyata, daɗi tamkar ba zan mutu ba, cikin girmamawa na ce. "Hajiyarmu to kin yafe mun?"...... Ta amsa da. "Tun kafin ki dawo kasar nan na yafe maki, ban ƙullaceki ba, mijinki shi ne matsalata, amma ku je ku gwada cikin ku dawo sai mu san matakin da zamu ɗauka nan gaba". Kirjina na bugawa sosai, dan nasan in dai cikin bai kai wata huɗu ba, ba'a busa mashi rai ba kenan, to tsab Hajiyarmu zata ce a zubar da shi, jikina ya ɗan yi sanyi, na mata godiya na miƙe na fita, Aunty Maryam ta miƙe ta biyo bayana. A ɗaki ta iskoni zaune ina danna waya, Safiyya dai tana can tana fama da Muhammad and Hassan da Abba ya dawo dashi tun kafin yai tafiya. A kusa dani Aunty Maryam ta zauna game da cewa. "Da gaske ne kina da ciki?". Cike da murna ta faɗa. Na amsa da. "A'a Auntyna, bani da cikin komai kawai neman mafita ne". Aunty Maryam ta ce. "Aikuwa kin yi ƙoƙari kuma kin yi farar dabara, tashi mu je asibiti da sunan asibiti mu wuce kasuwa hai, mu je mu sayi kayan gyara in zo in fara gyaraki, gidan mijinki sai kin koma ba fashi In Sha ALLAH"...... Sosai Aunty Maryam ta faranta mun rai, na ji daɗi sosai, na rungumeta ina dariya. Ta ɗan bugeni a baya tana faɗin. "Mara kunya, ko kunyata bakya ji ko?".... Ina dariya ban yi magana ba, na raba jikinmu game da jawo wayata, na fara dannawa. Ina shiga media na ga news a kan shahararren super heron nan na kwallon kafa Muhammad Abba Hussain a wannan wasa da suka buga ko kaɗan basu samu nasara sosai ba, dan ana zargin ɗan wasan tamkar bashi da lafiya ya shiga fili, bai iya buga ball ɗin yadda yakamata ba, ya ja an shasu wasa, sai faɗa mutane suke yi, masoyansa na ƙoƙarin karesa da cewa ai mashi uzuri kila bashi da lafiya ne, su basu san damuwar mutum ba sai bakaken maganganu suka iya saboda hasada. Ba ƙaramin tashi hankalina yai ba ganin wannan matsala ta yi affecting ɗin Abba sosai, har ya fara rasa wasan shi. Ai da sauri na miƙe na shige toilet, na ce da Aunty Maryam ina zuwa. Ina shiga na kirasa, sai da kiran ya yanke sannan ya kirani video call. Ganin video call ya sanyani murmushi, coz ni kaina na yi kewar fuskansa, tun kwanaki biyu da suka wuce. Ina ɗauka muka haɗa ido na sakar mashi murmushi. Ya ɗan zazzare mun manyan idanun nan nasa, yana kwance a kan wani haɗɗaɗen gado, ya yi kwanciyar ruff da ciki, ya sanya pillow a kirjinsa, sai ya kwantar da kansa a kan pillow ɗin. Babu riga a jikinsa sai single. Ganin na yi murmushi ne yasa shi zare mun ido, muryansa can ƙasa cike da damuwa ya ce. "Alhamdllh da ALLAH yasa yau na kiraki kina murmushi my wife, hakan ya fi komai kwantar mun da hankali, akwai wani labari ne da ya sanya tauraruwata murmushi haka?"........... A ɗan shagwaɓe na ce. "Nawan kalli yacce ka rame fa, ka je ka sanya damuwa a ranka ko?". Ya amsa da. "To ya zan yi my beb, ba zan iya rabuwa dake bane, ina cikin damuwa matuƙa"......... "Shi ne har kake ƙoƙarin sanyawa mu rasa wasan wannan zangon ko?"....... Uhm ya ce bai iya sake magana ba. Na ce. "To albishirinka"........ Ya ɗan jujjuya idanunsa gefe da gefe zuwa sama kafin ya ce. "Goro"........ Nan na kwashi duk abin dake faruwa na faɗa mashi, a karshe na ce. "In Sha ALLAH Hajiyarmu zata kyalemu, daddyna kam dama ya sauƙo, ina son ta sauƙo sosai ne sai in kira kawu na kauye in faɗa mashi ya zo, idan Hajiyarmu bata sauƙo ta hakura ba in na kira kawu ya zo da ita da daddy duk faɗa zai masu, kaga kenan zata ce okey na kai su ƙara saboda basu isa dani ba kenan, na je na yi aure basu sani ba, sun zo sune faman gwada mun kuskurena shi ne zan kaisu ƙara wajen Kawu, and kaga kawu akwai faɗa, yana zuwa da faɗa zai rufesu, kenan kaga matsala ce zata ƙaru, amma da zarar sun sauƙo zuciyarsu ta yi sanyi, sai in kira kawu ya zo ya faɗa masu shi ya ɗaura mana aure, kaga daga nan zasu kara samun natsuwa, zasu gane ba gaban kaina na yi ba". Tun da na fara magana ya tsare ɗan bakina da kallo har na kai karshe, wani irin farinciki ne ya lulluɓe zuciyansa, amma ya gagara yin magana, coz yana jin wani irin zazzafar feeling a kaina, musamman yadda ya ga fuska ina cikin farinciki, sai ya ji na kashe mashi jiki........ Na ɗan ɗaga mashi gera. "Nawan, lafiya kuwa?"...... Ya ɗan girgiza mun kai, da kyar ya buɗi baki, muryansa na sarkewa, can ƙasa ya ce. "ALLAH yai maki albarka, nagode sosai da irin soyayyar da kike nuna mun, ALLAH yasa Hajiyarmu ta fahimcemu, ta yafe mana, ta karɓemu dukka matsayin ƴaƴa". Na amsa da Amin, sannan na ce. "Zamu je asibiti ni da Aunty Maryam amma batu na gaskiya kasuwa zamu je sayan kayan gyaran jiki"........ Ya ɗan waro mun idanunsa waje, kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce. "Me zaki yi da kayan gyaran jiki?". Na ɗan hararesa kafin in ce. "Zan gyarawa mijina jikina mana, dan ya ji daɗinsa sosai"...... Ya ɗan juya idanunsa, sai kuma ya ce. "My beb, kina tsananin shagwaɓani sosai fa"............ "Ka yi addu'ar in dawo gidanka, zaka ga shagwaɓawa sosai". Ya ɗage mun gera guda. "Da gaske tawan?". ...... Na jinjina kai alamar haka. Godiya yai wa ALLAH SUBHANAHU WATA'ALA kafin ya ce. "My beb zoki hau bayana yanzu ki mun tausa"....... Yana faɗar hakan na fahimci yana duniyar sama jannaty, sai na ce. "My honey ka bari sai mun dawo mu cigaba da waya ka ji?". Ya ɗan shagwaɓe mun fuska. "Anya kuwa zan bari ki fita?"....... Na ce. "To yaushe zaka dawo?"......... "Kina son in dawo ne?"...... Na gyaɗa mashi kai alamar e..... "Cikin satin da zamu shiga, saura mana wasa biyu, kin yi kewata ko?"...... Na ce. "Sosai ma na yi kewarka". Ya gyara kwanciyansa, ya kara jawo pillow jikinsa sosai sannan ya ce. "Me kika fi kewa a tattare dani beb?"....... Na sanya hannu na rufe fuskata ina ɗan murmushi kafin in ce. "Komai ina kewa, amma na fi kewar takurawa bakina da kake yi"........ Ya ganoni, watau ina kewar kiss ɗinsa, saboda kunya ta jinin fulani yasa ba zan ce hakan ba. Ya kai yatsansa manuniya a kan soft lips ɗinsa, ya ɗan shafi lips ɗin cikin salo mai jan hankali, in a romantic voice ya ce. "Matso in baki abin da kika fi kewa ɗin". Ya kai karshe game da fito da tongue ɗinsa ya lashi lips ɗin nasa. Gabaɗaya ji na yi ya jefani cikin wani yanayi, da sauri na ce. "Uhm, uhm, ni kam sai anjuma". Ban jira amsar shi ba na katse kiran. Ina kashewa na fito, Aunty Maryam bata ɗakin, ta tafi shiryawa. Da sauri nima na hau shiryawa. Ina kammala shirina cikin lace ɗinkin pencil sket and half gown sai ga Aunty Maryam ta shigo. Ta dinga yabon kyauna, sai ta ce ba zata bari kyan nan ya tafi a banza ba, in kawo waya ta mun hotuna in turawa Abba. Ba musu na ɗauko wayata, ina kunna wutar screen ɗin sai naga alert na kuɗi tun 15 mins ago, kuɗi ne 5M daga account ɗin Abba, na yi shiru ina tunanin ni yaushe na tambayesa kuɗi?. Sai na shiga Whatsapp dan in mashi magana, sai na ga ya ajiye mun saƙo. A dawo kasu lafiya, kuma a sayi kayan masu kyau sosai, idan akwai abin da kike buƙata please ki kirani kai tsaye kin ji tawan?. Cike da mamaki, duk na ruɗe na ce da Aunty Maryam. "Aunty ki ga abin da Abba ya turo mun na kuɗin sayan kayan gyara"..... ALLAH sarki, ba'a taɓa mun kwatan wannan kyauta ba, Abbie sai dai in bashi ba dai ya bani ba bawan ALLAHN nan, na ji matuƙar daɗin kyautar Abba a gareni. Aunty Maryam ma ta dinga yaba mashi tana tayani godiya, ta ji daɗi, har da ce mun ga miji kam nan, ba wancan sha-sha-shan da sai dai ke ki bashi ba. Ni kam murmushi kawai nike ta faman yi, na ƙarisa shirina na, muka fito, sai da muka shiga wajen Hajiyarmu muka mata sallama, ta ɗauki 20k ta basu, sai Aunty Maryam ta faɗa mata ai Abba ya tura mun 5M na zuwa asibitin, Hajiya ta yi jim, kamar tana son yin magana, sai kuma ta yi shiru, but mood ɗinta ya ɗan canza, ta ɗauke kai daga kallonmu, Aunty Maryam ta ja hannun muka fito. A parlo muka isko su Sofi da yaranta suna ta faman sakata magana, ta baiwa Hassan wayanta yana danne-danne, Muhammad na jikinta tana mashi wasa, gabaɗaya kunyar kallon Sofi nike ji, haka muka wuce ban mata magana ba. Muka fito harabar gida, Aunty Maryam ta karɓi wayata ta ɗaukeni hotuna masu kyau, sannan muka kira driver ɗin Hajiyarmu, shi ya fito da mota muka shiga ciki, muna shiga ciki na turawa Abba hotunan nawa dukka. Ba'afi mintuna biyu da tura mashi ba sai ga kiransa, a lokacin mun fito gida driver zai kama hanya. Kamar ba zan ɗauka ba saboda video call ne, ina jin kunyar Aunty Maryam. Amma sai na daure na ɗauka. Ina ɗauka ya zuba mun ido sosai. Nai ƙasa da murya sosai wajen cewa. "Ya aka yi?". Yana kwance yadda muka yi magana ɗazun bai motsa ba. Da wata iriyar romantic voice ya ce. "Ɗan cire mun mayafin nan in ganki da kyau".......... Da sauri na wurga eyesball ɗina kan Aunty Maryam, ko kaɗan hankalinta baya kaina, tana faman rubuta kayan gyaran da zamu saya. Tamkar mai raɗa na ce mashi............. Jama'a ya za'a kare? Idan su Aisha suka dawo suka ce ciki watanni 2 ko 3 Hajiyarmu ta ce a zubar me zai biyo baya? Me kuke tunani? Abba zai dawo kwana kusa, me zai faru?. labarin A'isha zai dinga zuwa maku labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi. FATEEMA ZAHRA MUSA A-K-A QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥 LABARIN AISHA.🥹💔 PART 40 Follow my TikTok account 👇 https://www.tiktok.com/@princess_teema1?_r=1&_t=ZS-92AoEpYYmwP Follow my Channel account 👇 https://whatsapp.com/channel/0029VaMOfZZI7BeKXPU9gK2S Tamkar mai raɗa na ce mashi. "Aunty Maryam fa na jinka nawan, ka ganta a zaune"......... Ya ɗan zare mun ido, sai kuma ya kara kwantar da kansa luff a kan pillow ɗin yana ta faman kallona bai sake yin magana ba. Na ce. "Barci kake ji ne?". Ya girgiza mun kai alamar a'a. "To me yake damunka?" Ya nunani da yatsansa, ya motsa lips ɗinsa ba tare da fitar wani sauti ba ya ce. "Kece damuwata, ke nike buƙata, please ki mallaka mun kanki mana tawan"..... Na ja dogon numfashi game da saukewa a hankali kafin in ce. "Ni mallakinka ce already, na mallaka maka kaina my honey"...... Ya lumshe idanunsa, wani irin daɗi na ratsa mashi zuciya, ya gagara yin magana saboda halin da yake a ciki. Nisawa na ɗan yi tare da cewa. "Sai mun dawo kawai". Ban jira amsan shi ba na katse kiran, ina ɗan murmushi na dawo da kallona kan Aunty Maryam. "Aunty, me kike yi ne?". Ba tare da ta kalleni ba ta amsa da. "Rubuta abubuwan da zamu saya"...... Na matso na kwantar da kaina a saman shoulder ɗinta, motar yai shiru ina sauraron wa'azin dake tashi a motar har muka isa kasuwa. Sayayya sosai muka dinga yi, driver ɗin Hajiyarmu ya faka motar a garage na kasuwar muka shiga ciki, mun sayi abubuwa sosai da sosai kafin mu fito, kaya niƙi-niƙi. Na ce da Aunty Maryam ta ɗauki ko nawa take so a cikin kuɗin da Abba ya turo mun, ta ce bata son komai, na dinga matsa mata, amma taƙi ɗauka. Haka muka gama sayan kayan dukka muka kamo hanyar gida. Tun daga wannan rana Aunty Maryam ta fara mun gyara mai shegen kyau, ta hanani yin video call da Abba, wai bata son ya ga aikin da take yi, sai dai ya kirani normal call mu yi tahira, amma video call kam babu. Hajiyarmu ta saka mun ido kan tsakanina da Abba, duk wani motsin da muke yi na waya da shi tana ankare da mu, sai in kwana ina waya da shi, duk tana sane. And duk abin da muke yi da Aunty Maryam na gyaran jiki Hajiyarmu na ta faman binmu da kallo, ta tambayi cikina wata nawa ne Aunty Maryam ta ce mata watanni biyu, dan bamu isa cewa watanni huɗu ba, saboda cikin babu alamansa. Hajiyarmu ta yi shiru bata sake yi mana magana ba, suka tattauna da daddy da babban yayanmu, ban san me suka tattauna a kaina ba, ni dai basu sake mun magana ba, ni ma ban sake tambayar jin me ake ciki ba. Kullum ina waya da mijina, ina kwarara mashi gwiwa kan ya zage ya buga wasan nan da kyau ya dawo mu ga juna, Aunty Maryam ta zage sai gyarani take yi, ta mun gyaran fata kala uku, ta mun haɗin gyaran fata gabaɗaya, ta kuma mun haɗin laushi da sheki, sai haɗin cire dattin fata da sabuntata, shi Aunty Maryam ta fara yi mun, sai da ta cire mun dattin fatata kafin ta fara gyara mun shi. Haɗin cire dattin fata Aunty Maryam ta haɗa abubuwa kamar haka. Garin coffee 2 cokali, sugar mai kyau 2 cokali, man kwakwa 2 cokali, ɗan ƙamshi kamar lavender kaɗan, ta haɗesu ta kwaɓa ta shafe mun a jikina, sai ya bushe nike murjesa a hankali ina ciresa, yana cire dattin fata sosai, idan na kammala murjesa sai in je in yi wanka, sau uku a sati ta mun wannan kafin mu fara asalin gyara. Bayan na yi wannan da daddare kafin in kwanta sai ta mun face & body scrub da kuma mask. Abubuwan da take haɗawa sune kamar haka, garin oat 2 spoon, zuma 1 spoon, madarar ruwa 1 cokali, lemon tsami ruwan guda ɗaya kawai ya isa, sai ta haɗe shi waje guda ya haɗu sosai, sannan ta shafe mun a ko'ina a jikina, after 10 to 15 mins sai in shiga wanka, wannan haɗi yana cire matattun ƙwayoyin fata da duhu tabbbai da sauransu, yana bala'in gyara fata sosai. To idan na yi wanka already ta haɗa mun man da zan dinga shafawa wanda ta haɗa shi kamar haka. Man zaitun, olive oil kenan, man almond, coconut oil, garin turmeric ɗan kaɗan, sai ki sanya orange zest dan man yai kamshi sai ta haɗa mun a kwalba, duk inna fito daga wanka shi nike shafawa kafin kwanciya barci. Yana gyaran fata, yana haskakata kuma yana cire layi-layi da duk wasu tabo!. Sannan da safe tana haɗa mun garin lalle, da kwai kaɗan,

Chapter 33 of 38