sosai, ga shi dai shi ne ƙanin Mama amma kirkinsa ba zai faɗu ba".......... Yana danna waya ya amsa da. "Dama ai ba zaki haɗa kirkinsa dana Mama ba, amma Innata ta fisa kirki ai, dan baki santa bane"......... "Haka kowa yake cewa, lokacin da Kawu Badamasi yake kawo mana ziyara ai yana faɗa, ya ce Innarka mutuniyar kirki ce sosai, ni kam na ce kai baka ɗaukota dan kai ban da rashin ji ba abin da ka iya".
Ya wani wurga mun wani irin kallo kafin ya ce. "Zo gabana ki maimaita"....... Ina murmushi na ce. "Waɗan nan idanun naka na rashin kunya daga gani ba irin na Inna bane, kai kasan daga ina ka samosu, ji yadda kake wani kallona da su"...... Ya kafeni da kallon ƙasan ido, can kuma ya ce. "Ai da na ɗauko Inna da na ji daɗi, dan duk duniyar yanzu ba wanda ya kaita kyau, ni kam da babana nike kama, kuma irin idonsa na ɗauko, me zaki sake cewa?".
Na sa hannu na toshe ɗan bakina, ina murmushi na ce. "Me kuma zan sake cewa ban da in ce idanunka kyawawa ne sosai, amma dai nasan sharri ka yi wa baba dan kada in zagi idanunka shiyasa zaka ce da shi kake kama"........ "Zan kira kawu Badamasi in baku ku gaisa, ki gwada tambayarsa da waye nike kama zai faɗa maki".
Da sauri na ce. "Ni dai kada ka haɗamu please, bana son yin magana da kowa yanzu, ai ka yarda da Baba kake kama, amma Baba ya fika kyau ne dai, kai da Sulaiman ka fi kama"........ Ya yi mamakin jin na kira Abbie da asalin sunansa, yana ta ƙoƙarin kiran number Kawun nasa amma bata shiga, da alama sharrin network na kauye.
Sai ya ce. "Abbie ya fi kama da baba, ni kuma na fi kama da bappa, ki duba hotunansu bappa zaki ce na faɗa maki"........... Na ce. "To ai da baba da bappa duk kamanninsu ɗaya ne, ni bana banbancesu ko a hoton nema, kuma shiyasa ma kai kama da Sulaiman ɗin ai, saboda duk kamar dangin su Baba ɗaya ne".
Ya jinjina kai alamar haka ne, sai ya ajiye wayansa a gefe tun da ya kwata har ya gaji number bata shiga. Yana ajiyewa na kallesu game da cewa. "Bani wayata bari je ɗaki, call nike son yi, tun safe ban yi waya da Hajiyarmu ba, nasan ta yi ta kirana kuma nasan hankalinta zai tashi sosai da sosai"......... Ya nuna mun wayar a can karshen bed ɗinsa tare da cewa. "Hau ki ɗauka".
Ban kawo komai a raina ba na haye gadon zan ɗauka. Ai ina hayewa ya damki waist ɗina tare da kwantar dani, ya mirgina ya mun runfa da faffaɗar kirjinsa. Da gudu Muhammad ya haye kan bayansa yana faɗin. "Daddy let's start"........ Abba ya ce. "One minute my boy, close your eyes let me show your mammy something"........ Da sauri ya sanya ƴan tafukansa ya rufe fuskansa yana murmushi.
Na tamke fuska sosai game da cewa. "Abba me hakan?"....... Ya ɗan sauke ajiyar zuciya, tamkar zai cinyeni da ido, ya ɗan ƙara kwantowa kaina kaɗan, muryansa can ƙasa yana ɗan sarkewa ya ce..........
labarin A'isha zai dinga zuwa maku labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi.
FATEEMA ZAHRA MUSA
A-K-A
QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥
LABARIN AISHA.🥹💔
PART 32
Na tamke fuska sosai game da cewa. "Abba me hakan?"....... Ya ɗan sauke ajiyar zuciya, tamkar zai cinyeni da ido, ya ɗan ƙara kwantowa kaina kaɗan, muryansa can ƙasa yana ɗan sarkewa ya ce. "Please ki yi shiru na two mins kawai".
Na dallah mashi harara tare da fara ƙoƙarin turesa, a fusace na ce. "Baka da hankali ne wai? A kan me zaka kwanta a kaina?"............... "Please". Ya faɗa can ƙasan maƙoshi.
Mutsu-mutsu na fara yi ina ƙoƙarin kwace kaina, yasa hannunsa ɗaya ya damki hannayena dukka biyu da nike ƙoƙarin turesa da su ɗin, ya haɗesu ya rikesu ta saman kaina, sannan ya ce. "Natsu in faɗa maki wani abin"........ Ina binsa da wani mugun kallo na ce. "Tashi a kaina". ..... "Idan baki natsu kin ji me zan ce ba ba zan tashi ba gaskiya".
Da naga da gaske yake yi sai na natsu, ina hura kumatu na ce. "To me zaka faɗa mun"....... Ya ɗan jujjuya ido tamkar mai tunanin wani abin, sai kuma ya matso da face ɗinsa dab nawa sosai. "A kunne zan faɗa maki dan kada takwarana ya ji". Ya faɗa har da kashe mun ido ɗaya.
Ina hararansa ban yi magana ba. Nisawa yai tare da kara matso da fuskansa dab ni, a daidai kunnena ya tsai da bakinsa, cikin wani irin salo ya ce. "Kin san me soyayya take nufi?" Ya faɗa tare da zame hannunsa daga riƙon da yaiwa hannayena, sannan ya kai hannun nasa da ya zame gefen kumatuna, ya ɗan shafa zuwa kaina. Lumshe idanunsa yai tare da sake cewa. "Kin san me romance yake nufi?". A wannan karon yai maganar tare da dawo da bakinsa ya sumbaci gefen kumatuna yana sake lumshe idanu.
Ai iya karfina nasa na turesa ina faɗin. "Abba, ka sha wani abin ne yau? Baka da hankali ne? Ni fa Auntynka ce, matar yayanka". Cikin masifa nike maganar. Da karfi na sake turesa ina huci, coz ban taɓa tunanin haka daga garesa ba.
Hannayena dukka biyu ya haɗe ya rike da hannunsa ɗaya kamar ɗazu, ya tamke fuska tamau, cike da bada umarni ya ce. "Daga yau kada ki sake haɗa kanki da Abbie, ke ba matarsa bace, ke matata ce, bama shi ba, idan kika sake kiran wani namiji a ɗan bakin nan naki ko?"...... Ya kai ɗayan hannunsa ya matse lips ɗina da ɗan karfi. "Sai na fasa bakin nan in kika sake haɗa kanki da wani namijin, ke tawa ce ni kaɗai".
Ji na yi numfashina na ƙoƙarin ɗaukewa, na ji na yi suman kwance, what? Ni tashi kuma? Kai karya ne wlh. Tirjiya na fara yi ina miƙewa da karfi, dan na dage sai na kwace kaina, amma ko motsa kaina kwakkwaran motsi na gagara yi, shin ɗin ba na wasa bane, hannu ɗaya ya rikeni na kasa kwacewa.
Slowly ya zame hannunsa daga kan lips ɗina, ya kai bakinsa ya sumbaci lips ɗin nawa tare da cewa. "Sorry my wife, kishinki yasa na matse abu mafi daraja kuma wanda na fi kauna sama da komai a tattare dake, ban so ace ba lips ɗina ne zasu fara isa gare shi ba, amin afuwa tawan". A kunne ya raɗa mun.
Muhammad dake kwance a bayansa ya ƙankame wuyansa ne ya ce. "Daddy, should I open my eyes?"......... Abba ya ce. "No my boy, ban gama bawa mammy abin daɗi ba, wait small". Muhammad ya ce. "Daddy zaka bani abin daɗin nima?"......... Ya jinjina mashi kai game da cewa. "Sosai my boy, barin gama da mammynka ka ji?"
Ya ce okey daddy. Abba ya sake manna bakinsa a kunnena, yai ƙasa da murya wajen cewa. "Kada ki yi fushi dani kuma kada ki hukuntani tawan, tuba nike, duk kece silar zautar dani, kome na yi duk kece sula"........... Wani irin hawayen takaici ne ya cika mun ido tab, cikin tsananin bakinciki na ce. "Tashi a kaina Abba!"...... "Zan tashi, amma dan ALLAH tawan, kada ki yi fushi kuma kada ki hukuntani, tabbas nasan ban kyauta ba, amma koma menene kece sula".
Na wani tamke fuska sosai game da cewa. "Abba me hakan?"....... Ya ɗan sauke ajiyar zuciya, tamkar zai cinyeni da ido, ya ɗan ƙara kwantowa kaina kaɗan, muryansa can ƙasa yana ɗan sarkewa ya ce. "So, kauna da kuma zallar cikar buri......... Da sauri na wani rintse idanuna da karfi alamar bana son jin komai daga garesa, hakan yasa ya ɗagani game da komawa gefe.
Da sauri na miƙe, cike da taƙaici na kallesa game da cewa. "Kada ka sake ce mun matarka, ni Auntynka ce, kuma yanzu ka sakeni, dan ba haka muka yi da kai ba"............. Yana ƙoƙarin dawo da Muhammad ta gabansa ya ce. "Ki yi hakuri my wife, kome ya faru kece sula, soyayyarki ke neman zautar dani, kiyi hakuri sati ɗayan ya cika".
"Abba ni kake so?". In a harsh way na faɗa. Yai shiru, dan yana tsoron ALLAH yana tsoron in ki karɓar soyayyansa, bai ma san me ya shiga kansa da ya sanar dani sirrin dake ransa ba, shauƙi da ƙishi ne suka ɗebesa.
"Abba na tsaneka, ka yaudareni, ka cuceni". Na faɗa ina miƙewa tsaye, da gudu na nufi kofa. Sai dai ko da na je kofar a rufe take ruff, na juyo cike da takaici na ce ya buɗe mun kofar nan. Jikinsa ya yi mugun sanyi sosai, ya taso ya zo ya buɗe mun. Da gudu ya fita waje, ɗakina na shiga, na sha kuka tamkar wacce aka cewa iyayenta sun mutu, wannan dare gabaɗaya kuka na kwana yi, Abba bai zo in da nike ba saboda ya san na yi fushi matuƙa, ko ya zo sake lalacewa abubuwa zasu yi dan ina kan dokin zuciya, ya san halina sarai, dan haka ya kwana cikin kunci shi ma.
Tun daga wannan rana muka fara zaman doya da manja da shi, ina son barin gidan ya hanani, ba irin magiyar da ban mashi ba amma ya hana a buɗe mun gate, ya dawo mun da wayata, amma na gagara iya faɗawa iyayena abin dake faruwa, ba'a awa biyu mai kyau Hajiyarmu da daddy basu nemeni a waya ba, amma kodayaushe ina mata karyar ina lafiya, kuma kullum sai ta tambaye shin ban sake haɗuwa da Abba ba ko? Dan ta tsani mu sake haɗuwa! Na ce mata e, tun da ranar ban sake haɗuwa da shi ba, alhalin ina gidansa kuma wai matsayin matarsa, na shiga ukuna na rasa yadda zan fuskanci iyayena da wannan magana.
Na yi kuka har ban san adadi ba, Abba ya yi rarrashin duniya naki sauraransa, idan ina ɗaki ya shigo zan gudu toilet in rufe ƙofa, na ƙi yarda mu sake haɗa inuwa guda, abinci ma bana ci sai na ji yunwa na neman halaka sai in ɗan tsakura, shi kuma kullum sai ya kawo mun abinci ɗaki, haka kuma zai zo ya tattare kayansa ban ci ba. Ya hana mun zuwa makaranta, yau satinmu guda muna cikin wannan matsala, haka kuma sati ban je makaranta ba, class ya wuceni sosai, dan ma bamu jima da buɗewa bawani lecture ake yi sosai ba.
Ya damu sosai, ya rame matuka, ga tafiya dake gabansa a sati biyu masu zuwa zai je Brazil buga wani wasa, amma ya gagara samun kaina bare ya ce zai yi tafiya dani, ya shiga damuwa matuƙa, kullum yana manne da Muhammad. Ya dinga tunanin mafita amma mafita tai mashi wuyar samuwa. Haka dai muka shafe kwanaki bakwai a wannan gida. Ranar kwana na bakwai ɗin ne na kira Ibrahim, dan hakurina ya kare, na ce mashi yana Germany har yanzu ne, ya ce mun yeah bai koma ba.
Sai na ce ina son barin gidan Abba ya hanani, ya taimaka mun in fita daga wannan gida. Aikuwa ya ga dama ce ta samu da zai sameni, sai ya ce. "Zan zo gidan da ƴan'sanda, zan faɗa masu ɗaukoki yai ba da izininki ba, ya tilasta maki zama a gidan, kinga daga nan ƴan'sanda zasu ɗaukeki su fitar dake gida". Da yake burina kawai in bar gidan, sai na aminta da shawarar Ibrahim, na ce ya zo da su, dan har ga ALLAH na gaji.
Da yamma around 4 ina waya da Yah Abbas dake ce mun jibi jirginsa zai ɗaga, zai zo ya dubani, yanzu kusan watanni uku da sati biyu kenan daga gida ba'a zo dubani ba, dama after 3 months suke zuwa dubani, ni kuwa na kusa watanni biyu yanzu a gidan Abba, duk gida ba'a sani ba dan basu kawo mun ziyara ba.
Muna tsaka da waya na ji jiniyar motar ƴan'sanda, ai da gudu na miƙe na fito ina cewa Yah Abba zan kirasa anjuma. Na katse kiran, waje na yo, ina sanye da doguwar rigar lace ɗinkin bubu grown, na yafa ɗankwalin lace ɗin instead of ɗaurawa. Fitowata ya yi daidai da shigowar jami'an cikin gidan bayan sun nunawa guards na gidan ID card ɗinsu, a tsakiyar harabar gidan na tsaya, da sauri Ibrahim dake tare da jami'an ya nufoni.
Daga bayana unexpected na ji an ce. "Meyafito dake wajen nan?"..... Da sauri na juya. Ya tamke fuska tamau tamkar hadari. Na wani watsa mashi harara, dan gabaɗaya haushinsa nike ji, a dake na ce. "Ban sani ba".
"Wuce ki koma ciki tun kafin ranki ya ɓaci". Ya faɗa babu alamar wasa a tattare da shi, ya zura hannayensa dukka a cikin aljihun tracksuit ɗin jikinsa, ya rame sosai bawan ALLAH.
Nai banza da shi tare da juyawa ga Ibrahim da ya isoni yanzu, shi kuma yana sanye da jeans and t-shirt bakake. Ibrahim zai mun magana Abba ya ce. "Idan ka kuskura kai wa matata magana sai na sanya an datse harshenka, ke kuma zo ki wuce ciki".
A daidai lokacin Jami'an suka iso wajen, hakika Ibrahim ya ji shakkar Abba, dan Abba akwai bala'in kwarjini da mugun cika ido, and Ibrahim ya tsorata tun lokacin da na ce mashi gidan Abba nike, ya tambayeni a ina Abba ya samu kuɗin gina wannan gida? Naki faɗa mashi, domin fitar da sirrin wani ba ɗabiata bace, na ce mashi nima ban sani ba.
Jami'an na isowa in da muke Ibrahim ya nuna masu Abba game da cewa. "Ga shi nan".......... Ɗaya daga cikin jami'an ya ce. "Irin wannan katafaren ginin tabbas mafia da kidnapping yake yi"....... Na zazzaro idanu a kansu, sai kuma na juyo na kalli Ibrahim, ya sakar mun murmushi game da cewa. "Yanzu zasu yi maganinsa, zamu bar gidan nan tare dake".
Muryata na rawa na ce. "Ibrahim, a kan me zaka ce Abba na satar mutane? Meyasa zaka ce shi ɗan mafia ne kuma dan kidnapping? Kasan hukuncin hakan a ƙasar nan kuwa? Kashesa kai tsaye ta hanyar rataya fa zasu yi fa"....... Ibrahim ya ce. "Ai saceki ya yi ko? Tun da zuwa yai ya ajiyeki ba da son ranki ba, me banbancin hakan da satar mutane?".
Kai na girgiza da sauri tare da juyawa na kalli jami'an, already sun isa in da Abba yake, suna kokarin sanya mashi handcuff a hannu. Muryata na rawa na ce. "Sir laifin me ya yi da zaku kama shi?"...... Ibrahim ya ce. "Wai ke me ya dameki ne? Ba fita daga hannunsa kike da buƙata ba? To ki zo mu tafi kin samu freedom, shi kuma dole su hukunta shi na ajiyeki da yai ba da son ranki ba".
Jami'an suka ce. "An ce mana ya satoki ta tilasta, ya ajiye ki a nan, zamu tafi da shi ne domin bincike"....... Na haɗe rai sosai, cikin masifa na ce. "Kai kaga nai maka kama da wanda aka sato ne? To da kafata na zo cikin gidan nan, dallah ku sake shi ban son shirme". Ni da kaina ban san yaushe na samu kwarin gwiwar zazzagawa jami'ai wannan masifa ba.
Suka kalli Ibrahim suka ce. "Ba satota ya yi ba kenan?..... Ibrahim ya ce. "Aesh meyasa zaki kare shi kuma?"....... Na juyo na kalli Ibrahim, cikin faɗa na ce. "Saboda baka da hankali sai in bari su tafi da shi, ka sani na sani yadda mutanen nan suka tsani bakaken fata, sai sun kara mashi hadda sharri ma dan su kashesa, ai ni ba haka muka yi da kai ba, mun yi da kai ne kawai dan su zo su fitar dani ba wai su kama shi ba, kai ko baka san Abba a matsayinka na bakin fata a ƙasar nan ba zaka iya tare mashi faɗa ba idan ka ga zai shiga irin wannan gagarumin tuhuma na satar mutane?".
Wani irin sanyayyar ajiyar zuciya Abba ya sauke, ashe dai duk faɗar da muke yi yana rai a cewarsa. Ni kuma na karesa ne saboda nasan hukuncin kisa kai tsaye zasu yanke mashi, saboda dokokinsu yana da matuƙar karfi, sannan shi bakin fata ne wanda dama ba sonmu suke yi ba, dan haka ko dan tsanar da sukai wa baki sai sun azabtar da Abba.
Jami'in ya ce. "Yanzu dai Madam ba satoki aka yi ba kenan?"....... Ina kara ɗaure fuska na ce. "Ba satoni aka yi ba, hasalima yayana ne, zaku iya tafiyanku"........ Suka dai tsaya suka yi binciken cewa ba barazana Abba ya mun yasa na nuna na sato aka yi ba, da suka gane bisa radin kaina na faɗa, sai suka baiwa Abba hakuri, suka juya suka fita.
Abba ya kashewa ɗaya daga cikin jami'an ido, abin da ban sani ba shi ne nan ya ce su yi kamar zasu kama shi yana son gwada wani abin, coz da suka isa in da yake tambayarsa suka yi cewa a matsayinsa na shahararren ɗan kwallo me ya shigar dashi case na ɗauko yarinya ba da son ranta ba, ashe sun ma san shi, ni da Ibrahim ne muke haukarmu a gefe. Shi ne Abban ya faɗa cewa ni fa matarsa ce, faɗa ce ta cikin gida, soyayyarsa ce ke rawa a iska, ya gagara gane ina son shi ko a'a, kuma wancan guy ɗin da ya kirasu shi ne yake ƙoƙarin shiga tsakanin soyayyarsa da matansa, dan haka yana son su gwada kama shi bari ya tabbatar ina son shi ne ko bana son shi, and baya son su kama Ibrahim, su kyalesa. Shi ma Abban ya ce su kyale Ibrahim ɗin ne domin Ibrahim bakin fata ne, idan Abba ya barsa a hannunsu sai ya gwammaci mutuwa, shiyasa Abba ɗin ya taimaka mashi.
Amma Ibrahim bai sani ba yana wani faɗin rai.......... Yanzu Abba ya gama gane cewa ina tsananin son shi nima, amma kuma naki yardanwa zuciyata ina son shi, ba ƙaramin daɗi ya ji ba, ya kara yi wa jami'an jinjina bayan ya faki idona, suka ɗaga mashi gera suna mashi sallama. Wannan shi ne power of money Abba ya gwada mana, watau ni da Ibrahim fa bamu san Abba ba zai kamu a kasar nan ba, ashe shirmenmu kawai muke yi.
Jami'an na tafiya Abba ya ce. "My wife, zoki wuce ciki". Yana magana yana nufomu, a dake ya faɗa babu wasa a tattare da shi. Ibrahim ya ce. "Kinga irinta ai, kin tsaya wai mu tausaya mashi, ga shi mun taimaka mashi kuma yana neman yi maka shirme".
Abba ya daka mun tsawar in wuce ciki kada raina ya ɓaci. Ka ji tsayayye kuma cikakken namiji, ai yana haɗe rai na ji tsoronsa yakamani, duk tsiwata na natsu, yana daka mun tsawa na juya zan koma ciki kenan Ibrahim ya kama hannuna game da cewa. "Kuma sai ki tafi........."
Maganansa ya tsana ne sakamakon ɗauke mashi fuska da mari da Abba ya yi, cike da izza Abba ya ce. "Ƙazami irinka har ka isa kama hannun matata?".......... Ibrahim yai kukan kura ya damƙi wuyan rigar Abba da karfi bayan ya sake hannuna, ya fara zagin Abba yana cewa zai dakesa.
Aikuwa Abba yai mashi wani duka ɗaya a baki sai da bakin nasa ta fashe, sannan ya ɓanɓare hannun Ibrahim ɗin daga wuyan rigansa, ya ture Ibrahim ɗin da hannu ɗaya da karfi. Ya tafi gabaɗaya ya faɗi ƙasa. Wani irin ihu ya dakata tare da miƙewa, yai kukan kura yai kan Abba dake tsaye tamkar wani zaki.
Da sauri na shiga tsakaninsu ina faɗin su bari ni bana so. Abba ya janyeni gefe gudun kada Ibrahim ya taɓa mashi jikina. Hankalina yai bala'in tashi, jikina har yana rawa. Ibrahim ya zo da nufin ya shake wuyan Abba. Abba yasa kafa ya takesa a kirji sai da yai baya-baya ya faɗi ƙasa. Ya sake miƙewa yai kan Abba.
Da sauri na fata jan hannu Abba ina faɗin su bari, Abba yai ƙoƙarin kwace hannunsa, dan ya yi alƙawarin idan Ibrahim ya nufosa yanzu dukan da zai mashi ba zai sake tashi ba.
Da karfi na dinga jan hannun Abba ina cewa ya zo mu koma ciki, ni na yarda zan zauna a nan, amma dan ALLAH su dakatar da faɗar nan. Da na da gaske ba dakatawa zasu yi ba, sai na ce. "Ina dai a kaina kuke wannan faɗar dukka? To duk ku dakata, ba faɗa ta hannu da hannu zaku yi ba, ba faɗa ta dukiya zaku yi, daga rana irin ta yau zan sanya maku sharaɗina wanda duk wanda ya ci da shi zan rayu"...... Ibrahim ya dakata daga yunkurin isa ga Abba, suka zuba mun ido suna saurarona.
Na goge hawayen dake zubowa a kan ƙuncina, sannan na ce. "Sharaɗina shi ne duk wanda ya ɗauko mun ɗana Hassan daga hannun mahaifinsa ya dawo mun da shi gareni, tabbas shi ne abokin rayuwata!".
Ibrahim ya ce. "Nine abokin rayuwanki ba wani banza mai neman soyayya ta karfin tsiya ba, tabbas nine zan mallakeki, ki jira dawowata da Hassan!". Yana kai karshen maganar ya ɗauki wayansa da ya faɗi ƙasa, sannan ya wuce da sauri ya nufi gate.
Abba ya nufoni, a dab gabana ya tsana, hawaye na cigaba da tsere a kan ƙuncina, yai ƙasa da murya wajen cewa. "Nagode da zaɓina a matsayin abokin rayuwa tawan". Yana kai karshen maganar ya ja hannuna muka nufi cikin gida. Muna shiga parlo na kwace hannuna na nufi ɗakina ina sake fashewa da kuka.
Shi ma ɗakinsa ya nufa zuciyarsa cike tab da tunanin yadda zai yi ya samu kaina, ya za'ayi yau ɗin nan ina kasance a ɗakinsa, dan shi ya rigada ya yanke cewa shi ne abokin rayuwata, coz ko yana zaune a nan Germany zai iya sanyawa a ɗauko mashi Hassan, ba abin da Abbie ya isa yi bare kuma ya tsara next week da kansa zai taka har Nigeria ya je ya ɗaukosa, shiyasa ya ce mun ya gode da zaɓansa a matsayin abokin rayuwa da na yi, yasan shi zai ci wasan tum da Ibrahim dai ba shi da hanyar kaiwa ga Hassan bare har ya karɓosa.
Haka ya kwanta a kan gadonsa yana ta tunanin yadda za'ayi yau ɗin nan mu kwana ɗaki ɗaya domin ya rarrasheni, ya ga na rame sosai, na sanya damuwa a raina, so duk ya ji wani irin ba daɗi a ransa. Yana kwance har aka kira sallar magrib bai tunano mafita ba, haka ya miƙe ya nufi toilet, ya ɗauro alwala, sannan ya cire tracksuit na jikinsa ya sanya jallabiya.
Ya fito ya nufi masallaci, a nan yai sallar magrib da ishai kafin ya fito dan ya dawo gida. A hanyansa na dawowa daga masallacin ne ya tuna ina tsananin tsoron mage, aikuwa ya ce yasan maganina, yau dole a ɗakinsa zan kwana koma a jikinsa, dan a irin tsoron magena tsab zan shige jikinsa ban san na yi ba. Umarni ya baiwa driver ɗinsa da ya kai shi su sayi mage guda uku, driver ya so tambayarsa me zai yi da mage, amma bai ga fuska ba, dan haka ya wuce da shi in da ake sayar dasu.
Ya sayi manya sosai farare tas, gasu da gashi sosai a jiki, ya sayi guda uku cuff, sannan suka nufo gida. Bai fitar da su a kejinsu ba, sai bayan ya tabbatar na yi sallar ishai, ya kai mun abinci da kansa, a lokacin na ɗan sake, sai na ci ɗan kaɗan, ya tattare sauran ya fito da shi. Yana fita ɗakin na miƙe na shiga wanka, Muhammad na ɗakin Zahra dan ta gaje yaron nan, yanzu a wajenta yake wuni, so ni kaɗai ce a ɗakin. Aikuwa ya kawo mun mage guda ɗaya ya ajiye a ƙarƙashin gado bayan ya fitar da shi daga keji, sannan ya kai ɗaya ɗakin Zahra, ya bar ɗaya a parlo.
Zahra da shegen son mage ita kam, kun san larabawa da mage na 5&6, aikuwa tuni ta karɓi magen, ya ce kada ta kuskura ko da sunan wasa ta faɗa mun shi ya kawo
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 27 Chapter of 38