and share fisabilillahi.
LABARIN AISHA.🥹💔
PART 11
Tun da muka kama hannayar Kano waya muke ta yi da Abba da yarana, yana ta murna ya faɗa mun sunansa ne a sahun farko na waɗan da zasu shiga gasar kwallon kafa ta jaha, ya ji daɗi sosai, ni kuwa ina kara jan kunnensa kan maganar karatu.
Da na kammala waya da shi na kira Safiyya, muka dasa da hira, tana ta bani labarin yadda suke zuba love ɗinsu da Abba, duk ta rikice a kansa, har sambatu take mun, wai ya iya soyayya, ya iya kalamai masu narka zuciya, aikuwa muna gama waya da ita na kirasa, yana ɗauka na ce.
"Nawan, shi ne ka rikita mun ƴar uwa ko? Ka birkita mata lissafi, ƙasa yarinya sai sambatu take yi, yanzu kai ni yaushe ma ka iya dukka wannan abin e ɗan ƙanina?".
Yana kitchen a lokacin wai yana mun girki, su Hassan suna ta tara mashi ciwon kai, sai ya gyara nan ya koma kitchen su sake watsa komai, duk ya zare ya zama kamar mahaukaci, da ludayin miya a hannu yake yawo, ya ɗaura wayar a kan sink na kitchen tare da sanyata a H-free kafin ya ce. "Please Aunty da gaske ta rikice a kaina? Haka ta ce maki na iya love?".
"Baka yarda dani bane?". Na faɗa ina ɗan murmushi........ Yana ɗauko kayan miya a fridge ya amsa da. "Na yarda dake sosai, amma naga ni fa ko magana dani Safiyya bata son yi, sai in mata dogon note sai ta ce mun okey ko tom, in na matsa mata ta yi magana sai ta ce mun lallaima kam, idan na nuna zan yi fushi sai ta ce mun baga shi nan na ce maka kai na mata ne, ragon namiji amma ka ce kai jarumi ne, jaruman maza basa fushi a wajen neman abin da zai sanyasu farinciki, gabaɗaya Aunty na rasa yadda zan yi da Safiyya, kuma zan ganta a online, in yi magana ba zata amsa ba sai ya jima, idan na kirata ba zata ɗauka ba wai bata son call kawai in mata dropping message a Whatsapp, muryanta wannan ina son ji amma ta hanani, ni ban ma san ya zan yi ba". Ya kai karshen maganar tamkar zai saka mun kuka.
Aikuwa tun da ya fara jawabi nike dariya, saboda iskancin Safiyya yawa ne da shi, a nan ta zo tana haukace mun a kansa, shi kuma tana can bata ma wani sauraronsa ashe...... Sai na ce ina zuwa. Ban jira amsarsa ba na katse kiran na kira Safiyya, na danna recoding kafin in ce mata. "Ke saboda baki da kirki ne kike walaƙanta mun ƙanina ko? Ki zo nan kina haukace mun kan kina son shi, amma shi nan ko maganar arziki baki mashi ko?".
Tana dariya sosai ta amsa da. "Kai Aunty kai rabin raina, wlh ina son shi, sosaima, ai kin san in bana son shi ba zan rikice haka ba, kawai fa wai jan aji nike mashi, dan na yi imani da duk abin da mutum ya samu a sauki sai ya walaƙanta wannan abin, amma idan ya sha wahala ya samesa, da daraja yake rikesa gam".
Wannan magana ta Safiyya ta tuna mun halin da nike ciki, lallai ta yi gaskiya, wlh duk abin da mutum ya samesa a sauƙaƙe sai ya walaƙanta wannan abin, amma duk abin da mutum ya sha bakar wahala kafin ya same shi, wani irin daraja na musamman yake baiwa wannan abin, lallai Abbie da ya sha bakar wahala kafin ya same ni, da bai walaƙantani hakan ba, amma da yake a ɓagas ya sameni, ko kayan lefe bai mun ba, daddyna ya mun komai kamar ba lafiya ba, a sauƙaƙe ya sameni shiyasa yake walaƙanta ni.
Da farko na yi niyyar turawa Abba recoding na call da muka yi dan ya ji tana son shi ya daina damuwa, amma da ta yi wannan magana sai na fasa tura mashi, na goyi bayan ta yi ta mashi wasa da hankali, ta barshi har sai ya san muhimmancinta sosai, sannan ta bada kai.
Muka yi sallama da ita na ajiye wayata cike da tunanin yadda zanyi da Abbie kan maganar gold, ga tunanin Ibrahim a gefe, ni kaɗai in saka wannan in kwance wancan, na saƙa mafita sun kai 50 ina warwarewa dan ban ɗauki ko ɗaya ba, ga shi yaya ya ce kada in kuskura in yi faɗa da Abbie in dai ina son dukiyata ta fito, in na yi faɗa da shi a wannan lokaci to fa na rasa dukiyata ne.
Mata masu faɗa da mijinsu a lokacin da zai kara aure wannan topic naku ne, ko kin yi faɗa ko baki yi ba idan ya ɗauko auren nan sai ya dire, to shiyasa na shirya maku wannan topic musamman dan ku san meyakamata ku yi a wannan lokaci, ku waye, ku nunawa maza kun canza, ku daure, akwai ciwo, amma ku daure, A'isha zata koya maku yadda zaku yi da mazanku a lokacin karo aure har ku ci ribar da baku taɓa zata ba, mu je zuwa.
A haka muka isa Kano around 4 na rana, har gida driver ya kaini, a tsakar gida na isko Abba da su Hassan suna jirana, ya masu wanka suna sanye da kaftan iri ɗaya da nashi, sun yi kyau sosai. Motarmu na tsayawa su Hassan suka yi kaina da gudu, na fito ina murmushi, Abba ma sai murmushi yake yi, yana satar kallona.
Ya matso ya karɓi Muhammad dake ta binsu da kallo yana murmushi shi ma, yasan ƴan uwansa yaron kirki, ya yi kewansu shi ma ashe, ya karɓi Muhammad tare da cewa. "Aunty kinga kyan da kika kara kuwa? Wow, gidan daddy ya karɓeki sosai, ashe dai tawan zata yi ƙiba".
Gaskiya na kara kyau kam, na ciko sosai, dan wlh tun da na je gida ban tuna da wani damuwan da nike ciki, farinciki da ƴan uwana kawai nike, bana aikin komai sai dai a dafa a bani in ci, in ci wanda nike so in Sha wanda nike so, ai dole in yi ƙiba, hankali ya kwanta, na kara kyau da haske sosai, jikina ya kara fresh.
Ina murmushin na ce. "To ai kai ne a nan baka iya rike mace ba, kaga da na je gidanmu yadda na kara kyau, amma kai sam a gidan nan baka iya kula dani ba".
Ya yi wani irin murmushin da daga gani bai kai zuciyansa ba, da alama dai maganar ta taɓa shi, dan gaskiya yayansa bai iya kula da mace ba, ba ci, ba sha, ni nike yi wa kaina komai, and yasan da haka, ai kunga dole ya ji ba daɗi. Na fahimci maganar ta taɓa shi, sai na wuce gaba na barsa tsaye a wajen, na shiga cikin parlo, driver ɗin hajiyarmu ya juya zuwa Kaduna.
Abba ya kama su Hassan da akwatina suka bi bayana, yana shigowa na ce. "Eyee, ɗan ƙanina, idan na ce maka mata maza ko na mata sai ka ɓata rai ka ce ba haka ba, yanzu dubi yadda ka gyara gidan nan, ji wani kamshin turaren wuta mai kwantar da hankali dake tashi, amma a haka kace mun kai ba na mata bane? Da karfina fa nike tafiya duk garin da naga dama saboda nasan ina da kai, tamkar matar gida haka kake kula da su Hassan, ka yi girki ka yi shara, nawan gaskiya Safiyya kai na mata ne, kuma mata maza, Sofi ta yi dacen husband material".
Ya ɗan haɗe rai, can ƙasa ya ce. "Ba don ke ba kina tunanin akwai wacce nike yi wa shara ne? Tambayi Mama zata faɗa maki, ke kaɗai nike yi wa wannan, kuma ke ɗin ma ai saboda ke Aunty ta ce".......... Na wani kallesa, coz ba abin da yai niyyar faɗa ba kenan, tun daga farkon maganar ya canza abin dake ransa, a karshe ma ya so cewa da kika samu ina maki ai dole ki mun walaƙanci, amma saboda shi yana tauna magana kafin ya faɗeta sai ya canza abin dake ransa.
Ya sake yin ƙasa da murya wajen cewa. "Ni Aunty ki daina ce mun na mata kuma mata maza, ita ma Safiyya da take ce mun hakan ALLAH ba kyaleta zan yi ba, zan gwada mata ba yadda take tunani bane". A ɗan shagwaɓe yai maganar, yana tsaye a bakin kofar shigowa parlo yaki karisowa ciki, su Hassan sun shigo sun haye kujera sun fara abin da suka saba na wasanni kamar ƴaƴan mage, while ni ma ina zaune a kan kujera, shi dai yana tsaye rike da akwatina da kuma Muhammad.
Na fahimci wani abu biyu, baya son kalmar nan na mata da nike ce mashi, and yana jin haushi idan ya mun aiki in dinga tsokanarsa ina kara danganta shi da mata, sai ya ji dama bai yi aikin ba.
Cikin zolaya na ce. "Haba nawan, to ayi hakuri a shigo a zauna, duk saboda fushin nan ce maka mata maza ne kaki karisowa ciki?". Ya girgiza mun kai alamar a'a ba saboda hakan bane. Na ce. "To saboda menene?"......... Ya amsa da babu komai.
Na zuba mashi ido ina son fahimtar shi, shi kuma ya sunkuyar da kai ƙasa, sai kuma ya ɗan ɗago yana mannawa Muhammad kiss a baki yana ɗan murmushi, slowly ya ɗan wurga eyesball ɗinsa a kaina, sai muka haɗa ido, ya ɗauke kallonsa tamkar mara gaskiya. Ni kam ina ta mamakinsa, coz Abba ya canza, duk da cewa tun ranar da muka yi wancan maganar ya canza mun, yana gudun mu haɗa ido saboda kunya, amma kwana biyun nan canjin ya yawaita, tun da na bashi number Safiyya, har zuwa muka je Kaduna canjin ya yawaita, sai yanzu kuma da na dawo naga sabon halin da ban san shi da shi ba.
"Nawan". Na ambaci sunansa a natse. Shi ma ya amsa a natse amma bai ɗago ba, yana dai ta sumbatar Muhammad a kumatu yana mashi wasa........ "Meya canza mun kai ne?". Na faɗa cike da mamaki.
Ya ɗan saci kallona, sai kuma yai saurin ɗauke kai, yana ɗan jujjuya eyesball ɗinsa a kan Muhammad kafin ya ce. "Babu abin da ya canzani Auntyna, yanzu please ki je ki yi wanka sai ki zo ga abinci na shirya maki".
Da yake ina gajiye sai ban tasa shi gaba lallai sai ya faɗa mun me yake damunsa ba, na miƙe na nufosa ina faɗin. "To bani akwatina in je in yi wanka"...... Ga mamakina sai naga ya ɗan ja baya game da sake mun akwatin a wajen. Na kallesa da kyau kafin in ce. "Abba lafiyarka kuwa?".
Kai kawai ya gyaɗa mun alamar yeah lafiya yake, amma bai yi magana ba, ya sake ja da baya har zuwa kamar zai fita waje. Na ja akwatina, dan in tabbatar da cewa ni yake gudu na yi kamar zan sake matsawa kusa da shi, da sauri ya sake ɗan ja da baya, mamakinsa kamar zai kasheni, amma na ja akwatin zan wuce da nufin in nai wanka muka ci abinci zan natsu a tsanake in tambayesa me yake damunsa.
Na juya zan shiga ɗakina muryansa can ƙasa ta katseni da cewa. "Please Aunty ko kin yi wanka kada ki sake saka turaren nan da kika saka yanzu"....... Na dakata da tafiya game da wurga mashi kallon meyasa?
Ya ɗan sunkuyar da kai tare da cewa. "Am..... In.... Dama warinsa yana tayar mun da zuciya"........ Ban san lokacin da na ce. "Ciki ne da kai". Ba....... Ya girgiza kai alamar a'a. Na wani dallah mashi harara kafin in ce. "Sai na saka tun da ba naka bane?".
Cikin marairace murya ya ce. "Please my Aunty, dan girman ALLAH ki tausaya mun kada ki saka, please tawan, ki ji tausayina, dan ALLAH ki jefar da turaren ma kawai"..
Yau ga Ikon GOD, watau saboda turaren ma yake guduna kenan? Ko me yake nufi, coz ƙananun shekaruna basu iya sakawa na gane nufinsa ba, ni na tafi duniyar tunanin meyasa turaren yake mashi wari? Nasan turarena mai muguwar tsada ce, ga kamshi mai kwantar da hankali, idan ƙasa ko ka bar waje sai ya ɗauki lokaci wajen yana kamshi, na hajiyarmu ce ma na ɗauko, amma wai ya ce wari take mashi, sai na ɗauki hakan matsayin rainin wayau nema, na ja akwatina na shige ciki na barsa tsaye ban sake yin magana ba.
Ai ina shiga ciki ya shigo cikin parlon da sauri, ya zauna a kan kujera tare da rungume Muhammad a kirjinsa, ya wani sauke nannauyar ajiyar zuciya, watau ɗazun saboda ina parlon ne yaki shigowa, ko meyasa yake guduna yanzu kuma? Oho mashi dai. Ya ɗan lumshe idanunsa kuma yana shaƙar kamshin da na bari a parlon, na jikina da bai gama washewa ba, shi da ya ce turaren na mashi wari, amma ya zauna yana shaƙa yana lumshe ido.
Abba sai shirin ALLAH, amma fa a nawa tunanin, ban san cewa nice sai shirin ALLAH ba, coz Abba ba muharramina bane, ƙanin mijina ne, in da aka fara samo matsala tsakanina da Abba ko in ce wasannin da muke yi har ta ɗan yi yawa shi ne, Abba ya zo rayuwarmu tun ina da shekaru 15 a duniya, lokacin kuruciya da yarinta ne kawai a kaina.
Daga nan muka shaku muke wasanni tamkar ni da yayana Abbas a gida, Yayana Abbas nike bi a wajen haihuwa, shiyasa da na samu Abba a nan na mayar da shi gurbin Abbas a cikin zuciyata, ɗan uwa na jini na ɗauki Abba, shi ma lokacin akwai yarinta a kansa, haka zamu yi ta wasa, har tayani ɗaure gashin kaina mai uban yawan nan yake yi, coz babu wani babban mutum a tare damu bare ya taɓa gwada mana hakan ba daidai bane, a gaban Abbie ma muna wasan ƙanin miji da Abba, amma baya ce mana komai, yanzu da muka ɗan ƙara girma ne ma muka rage wasu abubuwa, Abba ya ja baya dani sosai, saboda ya fini shekaru, ya fini hankali sosai, and shi namiji ne, yanzu ya daina tayani ɗaure gashin kaina, ya daina crossing line ɗinsa sosai, dan ma mun rigada mun saba ne yasa har yanzu dai muke waɗan nan wasanni duk da mun rage.
Tun lokacin da Abba ya girma yasan da cewa akwai feeling a jikinsa, ya daina wasu abubuwan dani, da har goyani yake, duk sai ya daina waɗan nan, coz kamar Abbie yake, akwai ilimin addini, ni kuma ilimin addinina ba sosai cancan ba sai haddar Alqur'ani mai girma, to tun da Abba ya fahimci namiji yake, and ni kuma yarinta yai yawa a kaina, sai ya canza mana salon wasan ƙanin mijin cikin dabara, duk wasu goyo da wassani ya sanya a hankali muka daina su, yana da hankali sosai. Wannan shi ne daga in da muka faro wasan ƙanin mijinmu, tun yarinta ne, abin ya bi jiki, shaƙuwarmu ta zarce yacce kuke tunani, coz na fi shaƙuwa da Abba kan Abbie.
---------------------
Ya jima zaune a parlon har lokacin da na fito, yana jin motsin fitowata ya ɗan zubawa curtain na wajen kofata idanu. Na fito sanye da atampa riga da sket mai kyau, ɗinkin ya zauna a jikina sosai, a Kaduna aka mun ɗinki, sabbi ne, na yi kyau sosai, na yafa ɗankwalin kayan a kaina ban ɗaura ba.
Ina fitowa muka haɗa ido ya ɗauke kallonsa daga kaina, a ransa ya ce. "Na ƙosa in bar gidan nan, na ƙosa in tafi gasar nan"...... A fili kuma can ƙasa ya furta. "Thank you my Aunty". Ya faɗa tare da miƙewa ya kwantar da Muhammad.
Na wani kallesa ina tunanin me na ce mun thank you dan ban sanya turaren ba?. Ganin zan baiwa kaina wahala wajen tunani yasa na ce ohon mashi ma dai, na wuce wajen dining area, Abba na ajiye Muhammad ya fasa mashi ihu wai ba zai yarda ba, dole Abba ya dawo ya ɗaukesa muka ranƙaya saman table.
Abba ya miƙa mun shi yana faɗin. "Karɓi abinki, zai fara mun kuka, ban iyawa"....... Na wani kallesa kafin in ce. "Kai ba na mata bane? A aikin matan da ka iya babu reno ne? Maza karɓi kayanka, a banza ake zama uban ne?!"......... Ya ɗan cukule fuska bai yi magana ba kuma bai karɓi Muhammad ɗin ba, ya ɗauko plate ya hau zuba mana abinci, ya sanyawa su Hassan ya bawa kowa nasa suka hau ci cike da murna, sannan ya zuba mun nawa, ya ɗan turo mun gabana tare da ɗan ɗago kai ya saci kallona, ina kallon duk wani motsinsa, coz mamakin sabon halinsa nike yi.
Ya zuba abincinsa ya zauna ya hau ci, da ya ga ina ta kallonsa ban fara cin nawa abincin ba sai ya miƙe tare da ɗaukar plate ɗinsa ya bar wajen ba tare da ya kalleni ba. Ya Salam, sai ji na yi duniya na ƙoƙarin juya mun, abinku da ba haka muka saba da shi ba, sai nike ganin kamar shima zai juya mun baya ne yadda family ɗinsa suka juya mun baya, haba wani irin kuka na ji ya zo mun.
Da gudu na miƙe, a danginsu duk shi kaɗai nike samun farinciki a gunsa idan muna tare, ace shima ya fara juya mun baya? Ina zan tsunduma rayuwata in ji sanyi. Da gudu na shiga ɗakina, dan ina da saurin kuka sosai, ina zuwa na kwanta a gado game da kwantar da Muhammad a gefena, na hau rera kuka tamkar wacce aka cewa ubanta ya mutu, abin ya mun ciwo, bamu saba yin haka da shi ba, ban taɓa in yi magana ya mun banzan ba tare da na mashi laifin komai ba.
Na yi nisa cikin kukan da nike yi sai ji na yi ya kama hannun ɗaya yana faɗin. "Please Aunty ki yi hakuri".
Haba kamar jira nike, na miƙe zaune na fara zazzaga mashi masifa, ta in da nike shiga ba ta nan nike fita ba, na ce shikenan shi ma zai juya mun baya, yana goyan bayan zuciyata buga. Ya yi shiru yana saurarata, sai da na kammala masifata iya son raina, sannan a natse game da sake hannuna da ya kama ya ce. "Ko da sunan wasa ban taɓa tunanin in juna maki baya ba, har abada hakan ba zai faru ba, wlh nima ban san me ya shiga kaina ba kawai na ji bana son zama kusa dake, amma ba wai dan na juya maki baya ko wani abin ba, ina tare dake, in duk dangina zasu gujeki, wlh Aunty ba zan taɓa gudunki ba, ki yarda dani". Da iya gaskiyansa ya faɗa.
A daidai lokacin muka ji buɗe gate wanda mun san Abbie ne.
Abba ya ce. "Please ki goge hawayenki ga mijinki nan, kada ya zo ya ce na saka mashi mata kuka"........ Ai da sauri na goge hawaye na, bansan lokacin da na sauƙo ƙasan bed ɗin ba, kirjina na bugawa da karfi saboda nasan diramar da zamu kwasa da Abbie kan gold, tuni na mance da rikici muke yi da Abba.
Waje muka fito tare da Abba, ina fitowa Abbie na shigowa parlo manne da waya a kunne yana faɗin. "Gaskiya gobe zan zo, ba zan iya jira har nan da kwanaki uku ba, kin san tsananin buri da muradin ganinki da nike da shi a raina kuwa? Dole gobe zan zo......"......... Maganarsa ta dakata ne a lokacin da yai four eyes da ni ina tsaye a bakin kofar ɗakina ina kallonsa, Abba na tsaye a tsakiyar parlo.............✍️
labarin A'isha zai dinga zuwa maku dama wasu labaran masu gajeran zango dan faɗakarwa da ilmantarwa cikin hikima da basira................ Danne like and share fisabilillahi.
QUEEN OF SURPRISE.✍️🔥
LABARIN AISHA.🥹💔
PART 12
Abbie na shigowa parlo manne da waya a kunne yana faɗin. "Gaskiya gobe zan zo, ba zan iya jira har nan da kwanaki uku ba, kin san tsananin buri da muradin ganinki da nike da shi a raina kuwa? Dole gobe zan zo......"......... Maganarsa ta dakata ne a lokacin da yai four eyes da ni ina tsaye a bakin kofar ɗakina, Abba na tsaye a tsakiyar parlo. Zame wayar daga kunnensa Abbie yai tare da zamu yi waya anjuma.
Ya kalleni kafin ya kalli Abba, nima na mai da kallona kan Abba wanda shi ma ni yake kallo, duk kunyata da Abba yake ji yanzu sai da ya kalleni ido cikin ido ya mun alamar da kada na yi kuka dan girman ALLAH, kuma kada na nunawa Abbie kamar na ji me ya ce.
Takaici yasa na ɗauke kallona daga kan Abban ma, coz sai na ji ya mugun bani haushi, kenan yana bin bayan yayansa, ta ya za'ayi komai sai ya ce in yi hakuri, ni ba mutum bace? Bani da zuciya a kirji nane? Ko sai zuciyar tawa ta fashe ne?.
Abbie da ya hau naɗe tabar kunya da hauka ne ya fara faɗar yaushe na dawo, kuma waye ya dawo dani? Sannan meyasa ban faɗa mashi ina hanya ba?. Mamakin ɗan tahalikin nan ne yakamani, wai masifa ya tsaya yake yi, kai ya ALLAH, wasu mazan basu da kunya basa tsoron ALLAH.
Ai sai na tsaya ƙasake ina kallonsa, tamkar wacce aka sassaƙa na tsaya gum. Ya gama surfen ruwan bala'insa sannan ya wuce cikin ɗakin, daga ni har Abba babu wanda ya ce mashi ƙala. Ƙafafuwana gagara ɗaukata suka yi, na durkushe ƙasa a wajen, na kifa kaina da cinyiyina, wlh yanzu kukan ma gabaɗaya taki zuwa mun, sai kawai na ji zuciyata kamar tana bushewa ne.
Abba ya matso kusa dani ya fara bani hakuri, amma na yi banza da shi, daga karshe na miƙe na bi bayan Abbie ɗakinsa, na samesa zaune a gefen gado ya buga uban tagumi, sai na zauna a gefensa, cikin sanyin murya na ce. "Habibi yau da kanka kake mun faɗa haka? Abin da baka taɓa ba? Ka manta da cewa habibiyarka ce? Lallai in kuwa haka ne na maka laifi sosai, to ina mai baka hakuri, amma dai nasan wani ne ya taɓa mun kai a kasuwa yasa kake wannan faɗan". Ba wai kalamaina sun kai har zuciya bane, kawai daurewa nike.
A tunaninsa ban ji me yake cewa Zainab ba ne yasa na ce haka, dan ya san halina da shegen kishi, a tunaninsa idan na ji me yake cewa Zainab za'a samu matsala babba. Aikuwa jin me na ce yasa ya sauke ajiyar zuciya, ya wani juyo muna fuskantar juna, a natse ya ce. "Sorry my wife, ban kyauta ba yadda na hauki da faɗa, amma komai ya wuce kin ji?".
Na ce ba komai ya yafe mun shi ma. Ya amsa da ya yafe mun, sai ya ɗauko wayansa, kamar ya mance ina zaune a wajen ne ya cire password sabon da yasa ɗin a gabana, sannan ya shiga kan wata number, ya danna message, rubutu yai na minti biyu, ban ga me ya rubuta ba, bayan ya tura sai ya ajiye wayar tare da dawo da kallonsa a kaina, ya ce. "To ya kika baro su Mammy da su Daddy?".
"Suna nan lafiya". Na amsa ina ƙaƙalo murmushi. Ya ɗan yi shiru, sai kuma ya sake cewa. "Ya hanya? Tun yaushe kika dawo? And meyasa baki faɗa mun zaki dawo ba?".
Na amsa da. "Hanya Alhamdllh, tun ɗazun na dawo, to my habibi ni da gidan mijina, tsananin kewarka da begen in zo in ganka ne fa yasa na shiga zumuɗin dawowa har na mance ban faɗa maka ba"....... Ya wani saki murmushi, da alama ya ji daɗin kalaman, sai ya ce. "Hope kin dawo mana da gold ɗinmu to?".
Na girgiza kai alamar a'a cike da fargabar abin da zai biyo baya. Ai take yai kicin-kicin da fuska, zai fara faɗa na ce. "Gold ɗin yana ɗakin Yah Abbas ne, kuma baya kasar, su daddy sun yi tunanin zai dawo kafin in dawo ne shiyasa suka ce kafin in dawo zasu bani, ashe Yah Abbas kam ba yanzu zai dawo ba, wai sai wata na gaba da zamu shiga, kaga ai ba'a kasar yake karatu ba, nima na ji takaicin abin".
Abbie ya ce. "To
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 38