Share this page
gidan Yarima..." "To muje mana.... ina nufin mu taka da ƙafa nasan inda za mu bi yanda zai fi miki sauƙin ganewa." "Wallahi short cut ɗin sunyi lungu da yawa..." "sai in yi ta rakaki har ki gane." Murmushi na yi cikin jindaɗi na ce. "Ai ko na gode, Allah ya biya." Tafiye muke muna fira sai gashi ba jimawa mun isa ƙofar gidan. A bakin gate ɗin ya tsaya ya kalleni ya ce. "Ki kula kin ji ko?" "In sha Allahu Ya Jafaru, na gode sosai...." "Da ƙarfe nawa zan dawo?" "Ummm! To ka dawo zuwa ƙarfe biyu haka." " shi ke nan, Allah ya kaimu." Gaishe da masu gadinda ke zaune na yi suka amsa sannan na saka kai na shige ciki. A gate na biyu kuwa, ina tura ƙaramar ƙofar sai ga wani murtuƙaƙƙen Soja ya ta so wanda babu alamun rahama a fuskar sa ya kalleni ya ce. "Who are you?" Zaro ido na yi hankali tashe, tuni baki na ya fara rawa domin ban san ma mi zan ce masa ba. "I said, wacece ke?" Ƙasa na yi da idona na ce. "Jiya aka ɗaukeni a aiki.." "And??" Mai motar da ya zo ya tsaya shi ne wanda ya ceceni daga hannun dodon da ya tsareni a wannan lokacin, duk da cewa ban san sunan shi ba amma kuma na shaida shi, shi ne wannan na jiya mijin wannan matar da muka iske ni da Aunty Labiba da wani kalar kaki a jikin shi wanda ban san ko na miye ba. Ko yau ma sai da na gaishe shi amma kuma ban ji ya amsa ba kamar dai jiya,sojan kawai ya kira can kusa da shi ya yi mi shi magana wanda ban san mi yace mishi ba, ni dai kawai na ji ya ce mini in wuce. Tsaye na yi ina nazarin kuma ta ina zan shiga, shin ta ƙofar baya ta jiya ko kuma ta inda muka shiga da Aunty Labiba. Wasu maza na gani guda biyu sun gifto ɗauke da wasu kayayyaki a hannunsa suna tafe suna magana. Ganin yanda nake ta rarraba ido yasa ɗaya daga cikin su ya ce mini. "Malama ya dai?" Gidan na nuna ina faɗin. "Nan gidan zan shiga." Ƙara kallona ya yi daga sama har ƙasa sannan ya ce. "Zo ki bi ga hanya nan." Zagawa na yi ta bayan su na wuce ciki. Bakin Kitchen na tarar da su da ƙatuwar MP suna ta shan waƙa suna ta dare-dare hankalin su kwance. Cike da murna suka tarbeni tamkar sunyi shekaru da sanina musamman Haula da Munira. Bayan na samu wuri na zauna Munira ta kalleni ta ce. "Keee! Ai ko mun manta yau dutyn Tayo ne wallahi, ya akayi ya barki kika shigo? Ko ya kira Hajiya ne a waya?" Jinjina kai na yi na ce. "Ai kuwa dai ƙila shi ne kam ya tsareni,har ya fara yi mini tambayayo sai ga mutumin nan na jiya ya zo da mota..." "Ya Emraan ko? Naga ɗazu Haula ta kai mi shi break fast, kamar Kaduna zai koma wurin aikin sa....Ta shi kije ki gaida Hajiya ki dawo." Miƙewa na yi ina faɗin. "Ɗan rakani mana.." Dariya Haula ta yi ta ce. "Naga sai wani ɗari-ɗari kike Beenafah. Ki saki jikinki gidannan bamu da wata damuwa. Ga ƙofa can je ki shiga, tana nan parlour in dai ba yanzu ta tashi ba." A hankali na taka steps ɗin na tura babbar ƙofar na shiga har parlourn inda na tarar da ita zaune ita kaɗai taci uban gayu cikin dakakken leshi wanda ya jiƙe sosai da ruwan kuɗi sanye da farin glasses a idanunta sai baza uban ƙamshi take mai daɗin gaske tana zaune a dining table tana cin Abinci. Duƙawa na yi cike da girmamawa na ce. " Mama Ina kwana?" Ajiye spoon ɗin hannunta ta yi ta ce. "Ya ma sunan ki?" "Beenafah." "Beenafah. Kin tashi lafiya? Ya jikin Maman ki?" Cike da mamaki na ce. "Alhamdulillah. Mai jiki da sauƙi sosai." Daga haka na miƙe na juyo da nufin fitowa sai ta sake kiran sunana na waigo ina mai amsa ta. "Ungo Maganin nan ki kaiwa Ziza please, yanzu sai za ta ce ta neme shi ta rasa alhali na gano ta bata son shan magani." Hannu biyu na saka na karɓa ina faɗin. "A ina ne?" Wata ƙofar ta nuna mini a hankali na taka naje na yi nocking, banji an amsa ba hakan yasa na tura kaɗan ina mai tura kaina ciki. Cikin rashin sa'a ko mukayi ido biyu da ita tana zaune a ƙasa tayi rashe-rashe da plate a gabanta cike da slize fruit. " Lafiya?" Ta tambayeni tana mai tsatstsareni da ido wanda har sai da naji wani tsoro ya kamani. "Ma..Magani Mama tace na kawo miki." "Mama! Wace ce Mama?" Kallonta na yi na ce. "Hajiya!" "OK to, Hajiya za ki ce ba Mama ba, zo ki ajiye min a nan na gode." A hankali na tako na zo inda tace na ajiye mata  na juya da nufin ficewa na ji tana faɗin. "Call Munira for me please.." Waigowa na yi na ce. "Na'am." "Cewa na yi ki kira mini Munira, tun ɗazu na ce mata zan aike ta kuma bata dawo ba... Ko kuma ungu keys...." Ta jefo mini tana faɗin. "Ki ce taje ta ɗauko mini kayan da nace mata a gida. Sannan akwai wa su Keys a bedside drawer na ɗakin Sama ta ɗauko ta rufe mini part ɗin Emraan ta kawo mini Keys gaba ɗaya" Ɗauka na yi ina faɗin to sannan na fito na zo na tarar da su na bata sannan na yi mata bayani. Ɗaki ta shige ta ɗauko hijabi tana faɗin muje ki rakani. Kallonta na yi nace. "Ban yi aikina ba fa Munira.." Dariya ta yi mini ta ce. "Aiki kam na gama sai dai na gobe idan Allah ya kai mana rai. Ki riƙa zuwa Ƙarfe shida da rabi...Ina nufin zuwa dai bakwai na safe kin iso, Hajiya bata son ma sha ɗaya tayi ba'a gama gyara mata gida ba sai dai idan akwai wani ƙwaƙwƙwaran dalili..." Ina jinjina kaina alamar gamsuwa na ce. "To in sha Allahu gobe da wuri zan fito, ai na za ta bata son sammako." Kallona ta yi ta ce. "Muje mana.." Girgiza kaina na yi ina murmushi na ce. "A'a, kije ki daw..." Hannuna taja da ƙarfi muka yi gaba tana faɗin. "Wallahi sai kin rakani to kuma kin ji na rantse." Dole bani da bakin magana haka na yi shiru na bita sai gamu a harabar parking lot tana ƙwala kiran wani wai shi Nuhu. Muna nan a tsaye sai ga shi yazo ya kalle mu ya ce. "Ya akayi Munira?" "Gidan Aunty Ziza za ka kaimu mu ɗauko mata kaya." "OK." Juyawa ya yi yaje ya janyo wata mota a hankali yazo ya tsaya a gabanmu ta buɗe muka shiga. Tafiya muke a hankali tana mini fira da cewa. "Aunty Ziza kenan, shekara ɗaya yanzu da aurenta ita da Yaa Emraan, er Kebbi State ce amma dai an ce wai ba'a nan ta girma ba, a can kudu ne wurin wan babanta, amma kuma tana da matuƙar kirki da sauƙin kai..." Ni dai kawai ina sauraren ta ne ba tare da na amsa ba mata ba. Sai da muka yi tafiya mai nisa sosai sai gamu wata unguwa wacce Munira ta ce mini wai sunanta Tudun wada. Wajen wani katafaren gida ya yi parking tare da danna horn, jim kaɗan sai ga wani ya zo ya buɗe, yana ganin Munira da drivernsu ya koma ya buɗe gate muka shiga. Masha Allah, gidan ya haɗu iya haɗuwa. Muna shiga babban parlourn gidan, tace in zo mu haura sama na ce mata a'a taje dai ta fito ina jiranta. Ina nan zaune ina ta bai wa idona abinci har ta kambala mata uzurinta sannan ta fito muka koma gida.   Muna shiga sai gata ta fito cikin shiri da alama itama fita za ta yi. Kallona ta yi ina mai ɗauke da kayan ta sai kuma ta kalli Munira ta ce. "Tare kuka je?" Cikin ɗan shakku Munira ta gyaɗa kanta ta ce. "Eh..." "To waye ya ce kije da ita? Da zuwan yarinya jiya-jiya sai ki ɗauke ta ki kai mini gidana, kin san halin ta ne?" Shiru muka yi dukkanmu jin yanda take faɗa kamar wacce akace na aikata mata wani zunubi. Sai dai kuma ni, ko a silifas ɗina ban kawo ta ba, domin wani gefen tana da gaskiya, baƙuwa dani bai cancanci ace na shiga gidanta bada izini ba. Sai da ta dasa Aya sannan Munira ta ce. "Ki yi haƙuri Aunty Ziza ba za'a koma ba..." Anshe Keys ɗinta ta yi tana mai wani buga uban tsaki ta taka ta yi wurin inda motar ta take ajiye ta kira drivern Hajiya ya zo suka fita. Hannuna Munira taja tana mai buga tsaki ta ce. "Muje dan Allah, kin san zuciyar mai ciki a wuya take, Sai ka ce wani gidan ƙwarai." Ni dai shiru kawai na yi bance komai ba har muka shige ɗaki muka zauna. Abinci na tarar an jere da yawa a ƙasan ɗakin. Kallona Haula ta yi ta ce. " Sai yanzu? Ku zo muci abinci please ni ina jin yunwa.. " Da mamaki a fuskata na ce. " Abinci? Tun yanzu kuke cin abinci rana?" "A'a. Wallahi fa abincin safe ne wai, sai yanzu za mu karya in faɗa miki." Lafiyayyen breakfast ne kamar wanda na gani a parlourn Hajiya, a raina na ce lallai kuna jin daɗinku kuna sha'aninku. Duk yanda na so zamewa dole sai da suka matsa mini muka ci. Daga nan suka yi ta fira ni kuma ina kwance ina sauraren su. Haka dai na yi wunin ranar a gantale ba wani aikinda na yi taƙamaime har ƙarfe biyu na rana. Ina shirin tafiya gida Haula taje da kanta ta zubo mini abinci da ma sauran abincin karin safe da yawa ta bani tana faɗin. "Jiya Aunty Labiba ta kiramu da dare tace an baki abinci da za ki wuce muka ce a'a, shi ne ta yi faɗa. Kuma mantawa dai akayi domin kullum abinci sai dai ayi ta shanyawa a rana ana yin ƙanzo, ki yi haƙuri." "Haba ba komai, Na gode sai gobenku." Ko yau ma sai da suka sake rakani har ƙofar gidan sannan suka koma. A nan na tarar Yaa Jafaru na jirana wanda ni wallahi kwata-kwata na manta da shi. A tare muka sake takawa har gida.         ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀 *ADABI WRITER'S ASSOCIATION* *AMEENA IBRAHIM*      *OUM-AMEER* *Wattpad:@Ummu-Ameer* *ArewaPen:@Oumameer2671* *FREE-BOOK* *PAGE 18*   Washe gari kam da wuri na fito tun Bakwai saura wanda nasan a lokacin ma Ya Jafaru bai isa fitowa ba. Koda na isa gidan iyaka bakwai da mintota,kuma ina zuwa kowane gate aka barni na shige ba tare da wata damuwa ba. Daga Haula sai wata tsohuwa kawai na tarar a bakin Kitchen ɗin suna fere doya da Irish potato a lokaci ɗaya. Bayan mun gaisa Haula ta kalleni da murmushinta tana mai nuna mini tsohuwar da take gefen ta ce. "Wannan ita ce Inna Kuluwa, idan ana zancen gargiya to itace a samana, idan kuma ana zancen abincin zamani to ni ce nan a sama.." Maganar ta ta dariya ta bani wanda har ban san lokacin da na dara ba sannan na ce. "Allah sarki. Allah ya ƙara basira." "Amin. Kije ciki Munira na can." Yau kam tare muka yi komai ni da ita wanda ko da goma ta buga da mintuna mun kambala komai wanda gidan babu abinda yake idan ba tashin ƙamshi ba. Wa su manyan kwalabe ne Munira ta ɗauko wanda babu komai a ciki sai turaruka masu mashahurin ƙamshi da daɗaɗa rai wanda ko alama ba su yi kala da na yankinmu ba, bayan an gama kunna na burner ta ɗauko air fresheners Wanda su ma ɗin da ga jin yanda suke ƙamshi kasan cewa na musamman ne. Bayan mun kambala muka dawo bakin kitchen muka zauna inda a nan ne Haula ta ɗora mini dubu ɗaya a jikina tana faɗin. "Ga kuɗin satin ki nan.." Cike da mamaki na jimƙe kuɗin a hannuna sannan na ce. "Kuɗin Satina kuma?" "Eh, duk ranar kasuwa, yau Monday kenan ana bamu dubu ɗaya na cin kasuwa daga Yaya." Jinjina kaina na yi na ce. "Allah sarki! Mun gode sosai Allah ya saka da alheri ya ƙara buɗi na alheri." "Amin. Na san yanzu Hajiya ta fito, kije ki gaisheda ita." "Tau, in sha Allahu yanzu kuwa." Miƙewa na yi kamar dai jiya na je na gaishe ta na dawo muka zauna muka ci abincin kari mai rai da motsi wanda ban an kare ba sai wani alamun bacci-bacci da naji yana neman ya sace ni. A hankali na ɗan gincira yayin da su kuma suka ci gaba da aikin surutun na su kamar yanda suka saba. Ina nan bacci ya fara figata na ji Munira na tashina cewa wai na tashi mu shiga Kitchen, Aunty Ziza tace Haula ta yi mata Cake yanzu ta kai mata da zafin shi take so ta ci. Tunani na fara ina za'a yi Cake ɗin tunda Hajjo tana yi a gidan Aunty Labiba ina gani, da kayan wuta ake yin sa, to su kuma naga na su kitchen ɗin na itace ce da manyan Murahu waɗanda da su suke girki. Sai dai kuma, tunanina ne ya yanke ganin mun shiga cikin gidan inda suka ja ni wani katafaren Kitchen wanda yake zaman ɗaki biyu na wata macen ta saboda girma da kuma faɗinsa. Ido, baki, hanci, su na buɗe a lokaci ɗaya ina kallon Aljannar Duniya 'Ya salam!' Wannan kitchen ɗin ya ƙawatu sosai da kayayyakin zamani kala da kala. A hankali Idona ya fara sauka akan double door Samsung smart fridge mai touch screen display Wanda ke nuna time, weather da Kuma recipe tips. A gefen fridge ɗin kuma, akwai built in microwave da Kuma Oven da aka saka cikin bangon kitchen ɗin. Sai kuma Six burner electric cooker Mai digital heat control da Kuma smoke extractor. A saman Cooker ɗin akwai hanging rack da ke Cike da shining copper pots and pans an jejjeresu Kamar wasu kayan kwalliya. A jikin faffaɗan windown Kitchen kuwa, sink ne mai automatic sensor tap. A gefe Kuma, akwai dishwasher, da cabinet drawers masu soft close system. Komai a kitchen ɗin nan is beautiful. Wani store dake ta ciki Haula ta shiga ta ɗauko dukkan kayan buƙata sannan ta fito ba ɓata lokaci muka hau aiki wanda muna yi suna ta faman surutunsu da suka saba, ni dai kawai ina taya su aikin ina sauraren su har muka kambala. Bayan ta gama tsara shi a cikin wani haɗaɗɗen bowl na tangaran kawai sai ta miƙo mini tana faɗin. "Ungo Beenafah, dan Allah ki miƙa mata,nasan tana can tana ta aikin jira, ni zan iyarda haɗa mata Mango juice ɗinne sai na kawo mata." Kallon Munira na yi wacce ta duƙufa sosai wurin gyara wurin da muka yi aikin wanda hakan yasa dole dai ni ɗin zan je na kai mata ko bana so. Ban san abinda yasa ba, tun abinda tayi mini jiya yasa na ji a raina cewa ina shakkarta. A parlourn da na fara tarar da ita farkon zuwana gidan a nan na tarar da ita tare da wasu mata guda biyu, en gayu ne suma kamar ita, suna zaune suna fira a hankali ba tare da hayaniya ba. Bayan na yi musu sallama na gaishe su a hankali na taka naje inda take zaune tayi rashe-rashe a ƙasa na ajiye mata bowl ɗin a gabanta na ce. "Gashi in ji Haula tace na kawo miki.." Daman tun da na shigo na nazarci fuskarta yanda ta yi wani canja lokaci ɗaya tamkar ba ita ce ke dariya ba. Fuska a haɗe sosai ta ce mini. "Ina ita Haulatun take?" "Tana Kitchen za ta haɗo miki lemun da kika ce ne..." Shiru ta yi mini ba tare da tanka ba na tsawon lokaci, wanda daga ƙarshe na miƙe don kaina da nufin tafiya amma kuma sai ta tsayar dani ba tare da ma ta kalleni ba. Zaunawa na yi na tsawon lokaci wanda har a cikin raina sai da na ji cewar na tsargu sannan daga baya sai ga Haula ta shigo ɗauke da Smoothie wanda ko daga kallonsa kaɗai kasan zai yi taste a baki. Tunda ta shigo take kallona ɗauke da mamaki a fuskarta har ta ajiye. Bayan ta ajiye lemun ne ta ce mini. "Beenafah miye kike a nan tun ɗazu?" Kallonda na jefawa Aunty Ziza shi ya tabbatar mata da cewa ba don kaina nake zaune a nan ba ita ce ta tsayar dani, sai gashi mun tsinci muryarta tana faɗin. "Ni ce na tsayar da ita. Je ki kira Munira ku zo." Tashi tayi cikin en wasu daƙiƙun da ba su gaza goma ba sai ga su sun dawo a tare sun durƙusa a gabanta. "Daman bayan ku biyun nan ana barin duk wanda ya ga damar shigowa ya shigo har nan kai tsaye ban sani ba??" Kallona suka yi dukkan su a lokaci ɗaya, domin ba su yi expecting wannan tambayar ta ta ba at all, Sannan daga ƙarshe Haula ta girgiza kanta ta ce. "A'a." "To miyasa kuka ba wannan yarinyar dama take shigowa? Jiya ma ba nan ba, har ɗakina ta iskoni kai tsaye ba wani neman izini ta shiga,why?" Sai da Haula ta ƙara Kallona a karo na biyu sannan ta mayarda kallonta gareta ta ce. "Aunty Labiba ce ta bada damar hakan, ta ce mu ɗauke ta tamkar mu babu wani banbanci, sannan kamar yanda muke da damar shigowa nan a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso itama haka za ta iya shigowa." Wani irin taɓe baki tayi tare da jan siririn tsaki ta kalle ta tace. " Bar mini Smoothie ɗin, amma ki wuce da Cake ɗin bana ra'ayi. Sannan kuma ku kawowa baƙina abin Ci da Sha." Tamkar an zare mini lakka, haka na janyo ƙafafuna a matuƙar sanyaye na yo waje ina mai samun bakin dakalin kitchen na zauna yayinda lokaci ɗaya na ji wata irin kunya da baƙin ciki sun lulluɓeni. Hannun Haula na ji akan kafaɗata ta dafani, cikin sigar rarrashi ta ce mini. "Ki yi haƙuri dan Allah! kada ki bari wannan abun ya yi tasiri a zuciyar ki, Aunty Ziza mace ce mai sauƙin kai wallahi, na rasa yau miye ya hau kanta." Munira itama ta ce. "Sosai wallahi,Aunty Ziza ba ta da matsala ko kaɗan, ni ina ga har da cikin nan yake sakata yin wasu abubuwan..." Cike da jin wani irin zafi a zuciyata idona tab da ruwan hawaye na kalle su a raunane na ce. "To amma miyasa za ta ce ba za ta ci Cake ɗin ba? Saboda ni ce na kai mata? Tana ƙyamata ko?" "Ke Haba! Waye zai kalle ki yace kina da ƙazanta? Dan Allah ki daina ma wannan maganar ba zancen ƙyama ba ne. Duk kwanakin nan fa muma haka take mana. Ko jiya haka ta tada Haula around 11pm ta ce ta yi mata tsire, wallahi muna kitchen har kusan 1am amma da ta kai mata bata ci ko ƙwaya ɗaya ba wai ƙamshin currynda tayi amfani da shi bai yi mata ba. Haka ta fito da shi Hajiya ta ɗauka sannan muka dawo ɗakin nan muna ta mita wanda daga ƙarshe muka cinye muna dariya..." Jinjina kai Haula tayi ta ce. " Ƙwarai kuwa, wallahi daren jiya ta ƙular dani ba kaɗan ba, amma kuma na yi mata uzuri saboda yanayin da take ciki a yanzu. Ke ma ki yi haƙuri kar hakan ya dame ki." Murmushi ne ya suɓuce min da na tuna cewa wai Aunty Labiba tace nima zan iya shiga duk inda nake so a gidan, hakan yasa na gyaɗa musu kaina na ce. " Ba komai, ya wuce..." "Yauwa. Bari na kaiwa Hajiya na ta idan zata ci, sannan in kaiwa baƙin Aunty Ziza Abincin in dawo mu cinye kayanmu...Munira ke kuma ki ɗiba ki kaiwa su Inna Kuluwa. Ke kuma ki tashi ki ɗauko mana abincinmu a kitchen kafin mu dawo." Tashi nayi na je na ɗauko abincin na dawo na shiga toilet na yo alwala na zo na yi sallah sannan na zauna zaman jiran su. Bayan mun ci abincin mun kambala  muka zauna suka yi ta firar da suka saba wanda sam na lura basa gajiya ba ma kamar Munira wacce bakinta sam baya gajiya da zuba surutu kamar wata jikar Aku. Misalin ƙarfe biyu Haula ta miƙe tana kallon agogon ɗakin tana faɗin. "Bari in tashi, naga ƙarfe biyu tayi,nasan yanzu za ki dame mu da faɗin gida za ki." Ɗan murmusawa na yi kawai ban ce mata komai ba har taje ta dawo ɗauke da wata ƙaramar Bacco ta ajiye mini a gefena tana faɗin. "Gashi.....Na saka miki komai a leda idan kinje sai ki zube, zai fi miki sauƙin ɗaɗɗakar kuular nan koda yaushe." Miƙewa na yi na ce. "Na gode sosai, sai anjimanku." Tare muka fito mu uku suka rakoni, a harabar gida muka ga wani ya janyo Mota da alama fita zai yi shima. Da gudu Munira taje ta tsayar da shi tana faɗin. "Oga Sule sai Ina?" Ƙara yin ƙasa da glass ɗin motar ya yi ya kallemu ya ce. "Hajiya ce ta aikeni, idan kuma zan dawo ma sai na biya Eatry ɗin Hajiya Ziza, itama zan ɗauko saƙo a can." "Eyyah! To dan Allah ka ajiye Beenafah a titinsu dan Allah." Kallona ya yi don ya ƙara tabbatarwa tunda already yasan Ita Munirar da kuma Haula sannan ya ce. "Allah yasa hanya ta ce?" "Kabi ta wurin titin su Aunty Labiba sai ka ajiyeta ko shabanke ne dan Allah, Hayin Malam Ibrahim za ta je." Shiru ya yi yana ɗan nazari sannan daga ƙarshe ya ce in shiga. Ɗan waro ido na yi ina mai ƙirƙirar wani murmushin dole na ce. "Ai da ma kun barshi, zan iya tafiya da ƙafat.." Hannuna Munira ta ja tana faɗin. "Dan Allah shiga malama. Waye baya son sauƙi a rayuwa? Sai ki yi ta wani ɗari-ɗari. Oga Sule ba shi da wata matsala shi ne drivern Hajiya." Daga haka ta buɗe gaban motar ta turani ta rufe ya ja muka fito. Muna isowa bakin gate bayan ya fito sai gashi mun yi ido biyu da Ya Jafaru,daman shi kuma Oga Sulen ya tsaya yin magana da mutanen da ke zaune bakin gate ɗin. Kallon shi na yi na ce. " Yi haƙuri dan Allah ga Yayana nan ya zo zamu tafi a tare." Waigowa ya yi ya ce. "To ba damuwa, Allah ya tsare hanya." A hankali na buɗe motar na fito na tako zuwa inda yake tsaye. Ganin na yi ya wani haɗe rai yace mini. "Waye kuma wannan Beenafah?" Ya ƙarashe maganar yana mai bin Oga Sule da kallo wanda ni ma ɗin shi na kalla sannan na waigo na ce. "A nan gidan yake, hanya aka ce ya rage mini." Cikin nuna jin haushi ya ce. "Kamar ya ya rage miki hanya? Bayan kin san dai dole zan zo na raka ki...." "To amma Ya Jafaru ai da ma ka daina wahalar da kanka, domin yanzu na san hanya, ko ɗa zu da kaina na zo a ƙafa..." "Au! Haka ma za ki ce wato?" "To ya zan ce maka? Daman ai don ban san hanya ba ne, yanxu kuwa tun da na gane ba sai ka ci gaba da wahalar da kanka ba.....Naga sai wani ɓata rai kake, miye aka maka?" "Mts! Ba komai. Muje.." Ya ƙarashe maganar yana mai karɓa Baccon hannuna. Sai da mukayi nisa sosai ba tare da kowa ya sake magana ba, wanda hakan ba ƙaramin mamaki ya bani ba,domin muddin muna tare da shi to fa bakinsa baya taɓa yin shiru. Amma yau sai gashi yayi shiru kamar ba shi ba. Sai da muka kusa kai gida sannan ya kalleni ya ce. "Ki daina saurin yarda da mutane Beenafah, musamman irin waɗannan." Gyaɗa masa kaina na yi na ce. "In sha Allah zan kiyaye." "Sannan kuma na zo miki da wani albishir...." Tun kafin ya iyarda rufe bakinsa na washe haƙorana na ce. "Masha Allah Ya Jafaru, miye wannan?" "Na samu Admission a ABU Zaria...sannan kuma babban abin farin cikin shi ne; course ɗinda na fara ne na samu gurbi da shi." Cikin nuna zallar farin cikina na ce.

Chapter 13 of 67