Share this page
kada ka bar mu a nan na roƙeka. Daddy wa muke da shi da har za ka barmu a nan? Don Allah kar ka yi haka..." "To cewa na yi ba zan cigaba da ɗaukar nauyinku ba ne da har ki ke wannan kukan?" "Ba zancen ɗaukar nauyinmu ba Daddy. A duk faɗin Gusau kai ne kaɗai muka sani, ta dalilin ka muke zaune a nan..." "Ki bari in mutu tukun Beenafah kafin ki yi ƙoƙarin binneni. Ni kin ji na ce miki kuna da wani bayan ni ne? Daman ina nufin ku zauna a nan kafin na tafi can na yi settling, daga baya idan komai ya daidaitar mini sai in aiko a tafi daku. Tsawon shekara huɗu cikin ta biyar nake ɗauke da nauyinku a kaina; Ciyarwa, shayarwa, sutura, magani, hatta makaranta da na kashe kuɗina na saka ki ƙarshe asara nayi saboda daina zuwa da kikayi, na ɗauki nauyin ciwon mahaifiyarki. Duk da haka ban gaji ba sai da na kwashi maƙudan kuɗi na bayar wurin yi wa jaririn da yake cikin zanin goyo aiki wanda sai bayan na gama wahala ya mutu. To yanzu dan Allah Beenafah duk irin wannan wahalar da na yi daku tsawon lokaci mi zai sa na kasa ci gaba da kulawa da ku? Kar fa ki manta har account na buɗe muku ina tura muku kuɗi a ciki. To ko yanzu ba kasawa na yi ba, kuma ba zan fasa yi muku duk wani taimakon da na saba yi muku ba ko don kasancewarku jinin ɗan uwana. Kawai dai idan na koma can tare da ku a yanzu, wahala ƙara maye mini za ta yi domin rayuwar Abuja ta banbanta da ta Gusau, saboda haka ku yi zamanku a nan, ga gida nan babu mai tashin ku a ciki. Daga baya sai in aiko a tafi daku idan na shirya, kuma In Sha Allah zan ci gaba da tura muku kuɗi kamar yanda na saba..." Tamkar an jefo Ammie daga sama, haka na ganta kwatsam gaban Daddy tana yi mai wani kallon mamaki da al'ajabi na  tsawon lokaci sannan daga ƙarshe ta fashe da kuka a hankali kuma ta koma dariya. Tayi kuka tayi dariya lokaci ɗaya tare da nuna shi da yatsa tana faɗin. "Dr. Bello Wazeer! Alhaji Mudassir Wazeer... Dr. Bello Wazeer... Alhaji Mudassir Wazeer... Bello.. Bello.. Dr.. Bello.." Girgiza kansa yayi yana mai mayarda kallon sa gareni ya ce. "Beenafah ki kamata ki mayar da ita ciki please. Sai kun ji Saƙo in sha Allahu zuwa wata ɗaya." Sake matsawa na yi gaban sa bayan na rirriƙe Ammie cike da magiya ina wani irin kuka mai cike da ƙunci na ce. "Daddy dan Allah dan darajar Allah karka yi mana haka. Daddy ko yanzu da kake tare damu ya muka ƙare ballantana ace ka yi mana nisa? Daddy Bahrain... Bah...."            ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀 *AMEENA IBRAHIM*      *OUM-AMEER* *Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewabooks:@Aminatuibrahimbawa* *PAGE 5* "Kin ga Beenafah.....zuwa anjima idan masu shaguna sun buɗe ki je ki ciro dubu ɗari biyu ne na tura muku. Kin ga yanda hidima dai ta taru ta yi mini yawa, saboda haka sai ku yi maneji tukun mu gani. Kuɗin magani kuma zan yi Magana da Dr. Basheer ko nawa ne zan biya. Sannan ga card ɗina nan, idan kuna da wata matsala za ki iya kirana kai tsaye." Wai aka ce idan gaskiya ta yi maka ya wa, sai ma ta hana maka yin magana. Muna ji muna gani Daddy ya shiga motar sa Driver ya tayar suka fita. A dai-dai kan corner su ka ci karo da Aunty Husaina tana cikin keke-napep. Cikin mamaki da nuna tsan-tsan ɓacin rai Daddy ya fito a mota ya kalle ta yayinda take fitowa itama ya ce. "Miye abin da ya dawo dake? Ina ita Mummyn taku take?" "Eyyah! I'm sorry Daddy. Wallahi I forgot something ne wanda ba zan iya barin shi a nan ba, kuma Mummy ta rantse tace ba zamu dawo ba sai dai a saukeni na hawo Napep idan na ɗauki abin da zan ɗauka kai sai ka dawo da ni." "Ta ya har kika yi sake kika bar wani abu mai muhimmanci duk tsawon kwanakinda ku ka ɗauka kuna shiri." "Daddy ka yi haƙuri, ni ma bansan ya akayi na manta ba..." "To miye ne wai shi ɗin da kika baro?" Cikin nuna magiya ta ce. "Something I can't tell, please dan Allah ka yi haƙuri na ɗauko." Jinjina kansa ya yi alamar gamsuwa da zancen ta ya ce. " OK to,shiga mu tafi." Suna isa ƙofar gidan ya umarci drivern na sa akan ya parker a nan su jira ta ta shiga ta fito. A inda Daddy ya barmu muna nan a wurin ba mu matsa ko'ina ba munata famar kukan rashin sanin makama akan wannan bahagon al'amarin da ya sake shigowa rayuwarmu ya yi mata karan tsaye. Shigowar Aunty Husaina ita ce ta yi sanadiyyar jan hankalina na zuba mata idanuna waɗanda su ka rine akan azabar kuka. Har yanzu ban cire rai da tsammanin cewa Daddy zai iya canza ƙudurinsa na barinmu a nan ba, domin bamu da wani da zamu kira namu duk a faɗin Gusau bayan shi. Rungumeni ta yi sosai a jikinta itama ta fashe da kukanda yake ciciyar zuciyarta tsawon lokaci sannan daga ƙarshe ta janye tana mai riƙo da kafaɗuna murya a raunane ta ce. "Ki yi haƙuri Beenafah! Wallahi Allah shi ne wanda yasan abin da yake cikin zuciyata. Sam ba na jin daɗi kuma ba na farin ciki da irin halin ƙunci da wahalar rayuwar da kuke ciki. Ba ni da wani iko ba ni da wani zarafi fa ce in tanyaku da addu'a. Mummy ita ce wacce ta haifeni amma na sani Sam! Ba ta kyautawa. Yanzu ki ɗauko mini account number ɗinku zan tura miki da kuɗinda na cire daren jiya a account ɗin Daddy, sai ku samu wata sana'ar da za ku riƙa yi domin kada abubuwan rayuwa su gagareku." Ban iya na motsa daga inda nake ba har sai da ta maimaita mini kusan sau uku sannan na je na ɗauko takardar da numbern account ɗin ke a rubuce na kawo mata. Bayan kusan mintuna uku sun shuɗe sai ta kalleni ta ce. "Na tura miki dubu ɗari biyar Beenafah, Allah ya ci gaba da tsare ki daga dukkan sharri ko wane iri ne, Allah ya baiwa Ammie lafiya. Ki kula da rayuwar Bahrain Beenafah." Wurin Ammie ta ƙarasa ta rungumeta sosai tana kuka na tsawon mintuna sannan daga ƙarshe ta janye ta ce. " Ke ɗin Uwa ce mai nagarta da kuma sanin yakamata Ammie, I learned so many things daga gareki tun ban iya banbance tsakanin fari da baƙi ba. I love you so much Ammie, har abadan abada kina zuciyata. Allah ubangiji ya baki lafiya mai amfani ya kuma ƙara miki tsawon rai mai albarka." Faɗin irin halin da zuciyata ke ciki ma ɓata baki ne. Da ana fatan mutuwa idan an shiga matsala da a yau na yi fatan Allah ya ɗauki ranmu ni da Ammie da kuma Bahrain ko don mu huta da duniyar baki ɗaya. to amma kuma sanin cewa hakan baya daga cikin ɗabi'ar musulmi na ƙwarai,Sai na sake fashewa da kuka,haka na dinga mutuwa ina dawowa tsawon lokaci sannan daga ƙarshe na kama Ammie wacce ba zance ga halin da take ciki ba a yanzu muka koma ciki, domin dai ko hawayen naga daga ƙarshe babu su akan fuskarta,Allah kaɗai yasan abin da yake zuciyarta. Misalin sha biyu na rana ina nan zaune na buga uban tagumi abin duniya duk ya bi ya isheni. Ammie ma tana kwance kurum ban san abin da take nazari ba sai na jiyo sallama kamar muryar Biba. Jiki ba ƙwari na lallaɓa na fito, ashe kuwa ita ɗin ce dai. Da mamaki na kalle ta na ce. "Ke ma Biba ba za'a je Abujar dake ba ne?" Fuska tuƙun-tuƙun ta girgiza kanta ta ce. "A'a, da ni za'a koma. Na tsaya ne sai da na jira dangin Mummyn su ka zo su ka kwashe komai kab na amfanin gidan wanda zai lalace, sannan kuma na tsaya na ƙara gyara mata komai kamar yanda ta ce. Yanzu zamu tafi a mota tare da drivern Humaida." Ƙaramar waya ta ciro daga ƙugunta tare da charger ta damƙa mini a hannuna ta ce. " Wannan wayata ce Beenafah, ki riƙe ta a hannun ki... " " Biba idan kika ba ni wayar ke fa? Miye za ki cewa Mummy? Sannan ni mi ma zan yi da waya?" "Zan faɗamata cewa wurin zuwa gidan iyayena ta faɗi a hanya. Beenafah ku yi haƙuri da rayuwa, ni ɗinnan ba kowa ba ce fa ce 'ƴar aiki, kina ji hatta iyayena ta ce idan har wata alaƙa ta sake shiga tsakanin ku da su to daga ranar ta koreni daga aiki, kuma ke ma ba za ki so hakan ta faru ba, domin ni ce nike ɗauke da su da wannan albashin da ake biyana. Abu ɗaya nake da shi da zan iya taimaka miki. Yanzu ki ɗauko hijabinki ki zo mu tafi.. " Ɗan Jim na yi ina nazarin maganar ta cewa na ɗauko hijabina... " Kar ki damu, nan ne maƙota ba ni sa." Ina cikin tunani sai ga Bahrain ya dawo daga islamiyya. Ƙoƙarin saita kaina na yi ina wani murmushin ƙarfin hali, na kalli Bahrain ɗin wanda ya yi ni sa da yin magana da Biba na ce. " Bahrain! Ka zauna da Ammie ina dawowa yanzu." Ɗakin ya shiga ya watse littafan sa yana nuna mata karatunda aka yi mu su yau, daga nan ni kuma muka fice tare da Biba. Wani babban gida ta kaini wanda yake bayan Layinmu. Ɓangare biyu ne, a ciki sai muka nufi ɓangaren dama. Mun kai kusan minti goma a zaune sannan sai ga wata mata ta sauko daga saman stairs a hankali ta ƙara so ta zauna. Saukowa Biba ta yi daga kan kujera ta zauna a ƙasa, hakan yasa ni ma na bi ta muka gaishe ta. Bayan ta amsa ta kalli Biba sai kuma ta kalleni ta ce. "Biba, wannan fa?" Kwantar da murya Biba ta yi sosai ta ce. "Aunty Labiba gidan da nake aiki ne suka tashi za su koma Abuja, to kuma da ni kaɗai za su tafi. Shi ne na kawo miki marainiyar Allah ko kina da wani aikin da za ta riƙa yi miki. Yarinya ce mai natsuwa da hankali, daga ita sai mahaifiyarta da kuma ƙaninta suke rayuwa. Idan Allah yasa akwai dama dan Allah a ba ta wuri." Shiru ta yi tsawon lokaci tana ƙare mini kallo har sai da cikin raina na ji na tsargu, sannan daga baya ta sauke ajiyar zuciya tare da jinjina kai ta ce. " Biba kin san fa tun wancan matsalar da aka samu na daina yin mai aiki, ko Hajjo ma zuwa take tana komawa..." "Dan Allah ki yi haƙuri ki shiga lamarin yarinyar nan, wallahi ita ba kamar sauran masu aikin da kika taɓa yi ba ne..." "Haka ki ke cewa kullum ai.." "Wallahi Aunty Labiba wannan ba haka take ba. Dan Allah..." " Na ji Biba, amma dai kin san ni ba na son aikin kwana... " " A'a, ai ba aikin kwana bane, suna da gidan su, nan ne baya ba nisa, kina iya ma daga zaran ta kambala aikin ta koma gida abin ta." Sake jinjina kanta ta yi sannan ta ce mini. "Ya ya Sunan ki?" A hankali na furta mata. "Beenafah." "Kin iya shara da goge-goge?" Biba ce ta karɓe zancen da faɗin. "Ai idan wannan ne kam ba matsala...." "Biba ba ke na tambaya ba." Matar ta faɗi hakan ta na mai tsatstsareni da ido. Ganin haka yasa na gyaɗa kai na a hankali na ce. "Na iya." "Ok. Zuwa kwana uku sai ki zo da safe kafin nan In Sha Allah na yi magana da babansu." "Allah ya kaimu, na gode sosai Allah ya saka da alheri." Daga haka muka yi sallama muka fito wanda muna tafe Biba na ƙara mini haske akan rayuwar Hajiya Labiba. Muna isa ƙofar gida muka taradda Ilyas yana jiran Biba wato drivern Humaida. " Biba ina ki ka je haka? Tun ɗa zu Hajiya ke kirana ta ce mini tayi ta kiran wayarki kashe, ban faɗa mata cewa kina tare da Beenafah ba kamar yanda kika roƙa, da ta matsa ma ƙarshe ce mata na yi na shiga kina banɗaki, saboda haka ki amshi wayata ki yi magana da ita kamar yanda ta bayar da umarni." Salin-alin na yi shigewata gida don kada ma na tsaya ƙarshe na ƙare da jin abin da zai baƙanta mini raina. Biba kuwa, tana karɓar wayar Hajiya Zaliha ta hau ta da faɗa tamkar za ta cinyeta ɗanye Nama, wai gidan ubanwa ta kai wayar ta. Ta na faɗa mata cewa wai wayar ɓata ta yi ta hau ƙundumomata zagi da cin mutunci wai tunda ba ta san zafin kuɗi ba dole ta sake baki ta yasar da waya, to wallahi ita babu ruwanta sai dai ta sake saya mata wata a cikin albashinta na wannan watan domin ba za ta ɗauki asara ba.  Bayan ta gama ci mata  mutunci tace ta yi maza ta hau mota su tafi.   Ina zaune ina ba Ammie magani Bahrain ya kalleni ya ce. "Aunty Beena wai da gaske su Humaida sun koma Abuja?" Ban san lokacin da na waigo na kalle shi ba domin tambayar ta shi ta zo mini ne a ba za ta. "Aunty Beena tambayarki fa nake." Lumshe idanuna na yi sannan na buɗe a hankali ina mai jinjina kaina na ce. "Eh." "To mu fa Aunty Beena?" "Mu za mu je daga baya ne Bahrain, Kaga Ammie na zuwa asibiti, idan muka koma can zai yi mana ni sa sosai har ya kasance ba zamu iya zuwa ba..." "But Aunty Beena ko a Abujar ma akwai hospital mana..." "Bahrain! Akwai dalili mai ƙarfi da yasa ba zamu tafi yanzu ba sai nan gaba kaɗan, ta inda aka hau bishiya dole ta nan ake sauka saboda haka sai Ammie ta gama karɓar magani sannan za mu tafi. Ba na son yawan tambaya Bahrain ka sa ni." Jinjina kai ya yi ya ce. " Allah ya ba ki haƙuri. Ammie idan ki ka yi bacci ki ka tashi zan ƙara karanta miki karatuna ki ji idan na yi daidai." A hankali ta gyaɗa kanta ta ce. " Allah ya kai mu to, kuma yasa ka iya ɗin."                            ***   Tun da Biba ta ba ni wanna wayar wadda ba simcard a ciki sai Memory only wan da yake cike da abubuwa, waƙoƙi, complete ƙur'an, tafseer-tafseer da sauran su. Hakan yasa Kullum yanzu cikin shan karatu muke, ƙira'a mai daɗi da sanya nutsuwar ruhi, ko kuma wani lokacin tafseer na malamai daban-daban. Kwana biyu da tafiyar su Daddy Abuja, muna zaune misalin ƙarfe huɗu na yamma ina tuƙa mana tuwo Ammie na zaune a gefena ta yi shiru wanda ban san mi take nazari ba. Kwatsam ta buga ihu tare da miƙewa a tsaye jiki na rawa tana ta famar girgiza kai tana kuka sosai tana faɗin. "NO.. NO......This is not happening...Abuja!...Abuja..Yes! Abuja, dole za mu je Abuja muma ko Beenafah?....." Ƙoƙarin ni ke in riƙeta amma na kasa, domin a wannan karon sosai jikinta ya shiga tsima tana kakkarwa, kafin na yi aune har ta runtuma da gudu ta nufi ƙofar gate,kuma cikin rashin sa'a ni da kaina yau na bar ƙofar a buɗe, shiyasa tana zuwa ta fice da gudu tana ta famar faɗin Abuja a bakinta.             ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀 *ADABI WRITER'S ASSOCIATION* *AMEENA IBRAHIM*      *OUM-AMEER* *Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewabooks:@Aminatuibrahimbawa* *FREE-BOOK* *PAGE 6*   Tamkar wadda wani mummunan abu ke farautar ranta, haka ta dinga falfala gudu ina ta faman bin ta. Duk inda ta jefa ƙafarta nan ni ma nake jefa ta wa. Ga unguwar tamu tsit! ba mutane tamkar an yi ruwa an ɗauke, wanda tun azal haka ta gada.   Kuka nake ina kiran sunanta da kuma neman agajin mutane duk da cewa ban ga ko tsun-tsu ya wulga ba. Daman daga ka fito titin gidanmu ka nauso kaɗan za ka tarar da corner mai shimfiɗe da wata kwaltar wacce ta miƙe ta ɗauki hanyar  babban titi baki ɗaya. Ina karyo kan corner ɗin, caraf! Idona ya sauka akan Ammie wacce wata mota ta kaɗe ta fit ɗaya ta yi ta mulmula akan titin sanadiyyar buguwar da ta yi. Kan ta na yi ina mai sake kwaɗa ihun da duk wani mahaluƙin da ya ji ni sai ya tausaya mini, lokaci guda muka isa gareta ni da wani mai Keke-napep tare da Mata guda ukun da ya ɗauko a cikin Napep ɗin ta sa. A gigice na rungumota jikina ina wani irin gurnanin Kuka na tashin hankali da ruɗewa. "Ammie... Ammie..! Ammie dan Allah ki tashi.... Ammie please don't do this to me, Wallahi idan kika yi haka baki yi mana adalci ba... Ammie.." Cike da tausayi mai Napep ɗin ya ce. "Baiwar Allah ki kwantar da hankalinki akwai sauran numfashi a tare da ita, gashi.. Duba ki gani..." Cikin gigita na ɗago na kalle shi tare da Matan da ke tare dashi na ce. "Kalli Jini yanda yake fitowa ta hanci da bakinta bawan Allah.. Daman ga shi ba ta da lafiya, wallahi ba ta da lafiya...." "Allah sarki! Ki yi haƙuri in sha Allah za ta tashi..." Kallon gefen da Matan ke tsaye ya yi yana mai saka hannayensa ƙarƙashin ƙeyar kanta ya ce. "Malamai dan Allah ku taimaka mu saka ta a napep ɗinnan mu kai ta asibiti ka da mu tsaya ɓata lokaci." A tare mukayi nasarar sanyata wanda nice na fara shiga sannan aka shigo da ita na rungumeta zuwa jikina. "Kunga yan da Allah ya yi ikon sa ko? Dan Allah ku yi haƙuri, ku je ku samu wani ya ƙarasa da ku inda za ku tafin." "Ba komai, Allah ya bata lafiya." Matan su ka amsa lokaci ɗaya suna ma su juyawa su ka wuce. Mutumin da ya kaɗe Ammiena duk budurin da muke yana zaune a motarsa wanda nasan yana ciki hankalinsa kwance yana kallon mu, sai dai mu ba ma iya ganin sa kasancewar motar tasa duk tinted ce, gaba ɗaya ba ka iya hango komai sai tsananin duhu sai dai shi dake ciki yake iya hango na waje. Sosai na ƙurawa motar ido ina kallonta da mamakin da ya kusan sumar dani. Bayan ya ga mai Napep ɗin ya tayar ya hau hanya shima sai a sannan na hangosa a dai-dai lokacin ya tayar da motar ya wuce abin sa. "Baiwar Allah wace asibiti zan kai ku?" Wannan tambayar ita ce ta sanyani dawowa daga duniyar tunanin da na abka inda zuciyata ta dugunzuma zuwa ga motar da ta kaɗe mini Ammie na har ta ɓacewa ganina.... "Baiwar Allah na ce wace Asibitin zan kai ku?" " Daman a Sokoto muke ganin likita duk farkon wata domin tana da matsalar ƙwaƙwalwa..." "To ai yanzu kinga halin da take ciki dole tana da buƙatar agajin gaggawa, idan ki ka ce za ki nufi Sokoto da ita a yanzu koda a motar gida kuke ai akwai hatsari da kuma barazana ga lafiyarta, kingadai  yan da ta ke ta faman zubda Jini." Cike da gamsuwa da bayaninsa na jinjina kaina na ce. " To ka kaimu Jan-bulo. Daman can ne farkon inda muka fara jinyarta a lokacin baya wanda daga nanne aka yi referring ɗinmu zuwa Sokoto."                      *** Federal Medical Centre, Gusau, Zamfara state, Nigeria. Har muka isa asibitin hawayena ba su daina tarara ba, ina yi ina hango makomarmu ni da Bahrain idan yau Ammie ita ma ta faɗi ta mutu. Muna zuwa ba ɓata lokaci muka shige Accident and Emergency unit da ita. Bayan sun gama ɗaukar dukkan bayananmu nan take su ka shiga ba ta taimakon gaggawa. Bayan kusan hour biyu sun shuɗe sai ga wani likitan ya fito ya miƙo mana takarda ya ce muje mu biya sannan kuma naje na ɗauko katinta wanda na ce mun taɓa jinya nan a baya. Cikin nuna damuwa mai napep ya ce. "Likita da fatan tana lafiya." Jinjina kai likitan ya yi da murmushi a fuskar sa ya ce. "Da sauƙi In sha Allah." Kallon sa ya mayar gare ni ya ce. "Alhamdulillah! Daman ɗa zu, ina ƙoƙarin karya corner ne sai kawai ta fito ta gabana ni kuma cikin sauri na yi ƙoƙarin na kauce mata, sai wancan mutumin shima ya karya kan motar sa ba shiri, maimakon ta tsaya a inda take sai ta sake komawa hannun sa shi kuma yana ta ƙoƙari amma bai yi nasarar kauce mata ba, domin a tsiyace yake da mugun gudun da ba zai iya tsayawa a lokaci ɗaya ba. To kin san halin mutane a yau, musamman masu kuɗin nan, abu kaɗan suke jira, tun da naga bai fito ba na fahimci cewa sam bashi da niyyar ya taimaka shiyasa ban ma nufesa ba. Yanzu ga wannan... " Ya ƙarashe maganar yana mai sanya hannu a cikin aljihun wandonsa ya ciro kuɗi ya ƙirga sannan ya miƙo mini yana faɗin. " Ki yi haƙuri dubu biyar ce ba yawa, wallahi cinikin kenan da na yi. Amma ki ɗauko wayarki ki kira babanki ko kuma mu tafi na kai ki gida ki taho da wani, kada na barki a nan ke kaɗai." Girgiza kaina na yi ina ta faman share hawayena na ce. "Ka barshi kawai ai ba laifinka ba ne, ko a hakan ma mun gode sosai Allah ya biya. Ko ba ka bamu komai ba ka fiye mini wanda ya kaɗe ta ya tsaya yana jiran mutuwarta, da wannan taimakon har abada ba zan manta da kai ba. Ina da waya amma ba layi a ciki, sannan kuma a yanzu gaskiya ni ce kaɗai zan iya zaunawa da ita kafin na samu kiran en uwanmu su zo." "Allah sarki! To muje na kai ki gidan ki ɗauko abin da za ki ɗauko sai na dawo dake." Sosai na lumshe idanuna a cikin Napep ɗin ina ta lissafin rayuwa har muka iso dai-dai inda aka kaɗe Ammie, daga nan ya tambayeni cewa ina ne gidanmu, sai na nuna masa. Ina shiga na tarar da Bahrain zaune ya haɗe kai da gwiwa yanata faman kuka. Yana ganina ya taho da gudu ya ƙanƙameni sosai yana faɗin. "Aunty Beena na ji tsoro sosai, na dawo ke da Ammie ba kwa nan, gidan su Humaida ma ba kowa, mai gadi ma baya nan..." Ni ma ɗin rungume sa na yi, cikin rarrashi na ce. "Ka yi haƙuri Bahrain...Ka yi haƙuri. Muna asibiti Ammie ba lafiya, ka dai san yanayin jikinta ba sai na faɗa maka ba. Abin da nake so da kai a koda yaushe ka zama jarumi sannan ka ƙwarara kan ka domin mu samu ciwon Ammie ya warke baki ɗaya.....Mu je na ɗauko katinta da ATM card sai mu tafi asibiti." " To Aunty Beenafah, ina mata addu'a Allah ubangiji ya bata lafiya. Ai ko a Islamiyya kullum sai na cewa Ra'is ya sanya mahaifiyata a addu'a ba tada lafiya." "Yauwa yaron kir ki. Zo... Zo mu tafi ana jiranmu a waje." Ciki na shiga na ɗauko mana duk wani abin da nasan za mu buƙata domin in dai zaman asibiti ne na riga da na saba a yanzu. Wuri na ɗauko na kwashe tuwon sannan na juye miya daban na mayar da komai ciki sannan na janyo ƙofa domin dai ba mu taɓa rufe gidan ba tunda muke. Ko gate ɗin ma haka muka barshi bayan na sakaya muka shiga napep ɗin muka koma asibiti. Muna shiga aka sake bamu wata takarda again gashi ko ta farkon da akace muje mu biya bamu biya ba. Wurin biyan kuɗin mukaje wanda nan take aka caji kuɗi kusan dubu ashirin da takwas da ɗari bakwai, ƙuri! mai Napep ɗin ya yi yana kallona domin da alama ya razana. "Karka damu akwai kuɗi a tare dani zan biya, ko tsaya mana da ka yi kawai na gode sosai." Bayan mun biya mukaje muka karɓi magani muka koma still tana ciki ba'a fito da ita ba. Muna nan aka shige da case folder ɗinta, sai a sannan na ce

Chapter 3 of 67