da wahala na laulayi da naƙuda har lokacin da ta haife shi kuma....kuma ga shi ma a lokacin haihuwar ta sa ne ta mutu...Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! A yanzu ina amfanin rayuwar sa? Shekaru arba'in da wani abu a duniya amma bai taɓa yi mata addu'a ba! Shi ɗin kwana nawa ne ya rage masa a duniyar? Kai co!'
Wani irin firgigit na yi cikin tashin hankali na miƙe zaune jin ƙarar sautin kuka a saman kaina.
Zaune na gansa a gabana yasa hannayensa ya dafe kansa tamkar wanda saƙon mutuwar sa ya riske sa a yanzu.
Cikin zafin nama na janyo hannayensa ina jin wani sabon tausayinsa na ƙara yi wa zuciyata, murya a raunane na ce.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un! Ka yi haƙuri! Dan Allah ka yi haƙuri Yaya Muhammad! Ka tuna fa kai musulmi ne wanda ya yi imani da ƙaddara....halin da kake ciki yana ɗaga hankalina yana sa ina jin raɗaɗi da ƙuna a cikin zuciyata.....Dukkan wata rayuwa tana tafiya ne tare da jarabawa wanda duk wata dukiya, mulki, talauci ko sarauta wallahi ba su isa su hana abinda Ya rubuta maka ya same ka ba.... Shin ka ɗauka cewa kai ka ɗai ne allon ƙaddara ya taɓa birkitawa haka? Ba kai ka ɗai bane Yaa Muhammad....... "
Daga hana na zuro Ƙafafuwana ƙasa na sauka na je banɗaki na yo alwala na zo na gabatar da sallahr Asuba, ina kambalawa ban tsaya doguwar addu'a ba na miƙe na je na kwanta jikin sa a hankali na ce.
" Ka yi haƙuri....Idan kana kuka, ji nake kamar zuciyata za ta fashe akan ƙunci da takaicin jin cewa na gaza wurin kulawa da kai. Ka riƙa tunawa cewa mutane da yawa a duniya suna cikin jarrabawowin da idan ka ji labarin wani sai ka ji cewa kai duk da haka a Aljanna ka ke. Ka yi haƙuri, Allah da kansa ya cewa manzon Allah (S.A.W); Ka yi haƙuri, haƙuri mai kyau. Kuma sai ya yi haƙurin ya ci riba mai girma. To saboda haka, ina so ka yi koyi da masoyinmu, shugabanmu annabin Rahma (S.A.W) ka yi haƙuri kuma ka mayarda al'amarinka ga Allah, in sha Allahu ya isar maka...Sannan kai fa ɗin nan jajirtaccen Yaya ne kuma Uba, idan ba ka ƙwarara kanka ba ta ya ya za ka iya ƙwarara waɗanda suka ɗauke ka jigo kuma tsayayyen Uba a gare su....."
Haka na yi ta faɗa masa kalamai ma su daɗi da sanyaya rai har Allah ya ɗorani a kansa na ji yayi shiru.
Muna nan a haka daga ni har shi babu wanda ya sake runtsawa har misalin ƙarfe bakwai da wani abu sannan ya miƙe a hankali ya zameni yana faɗin.
" Ta shi ki je ki shirya za mu fita."
Saukowa na yi a hankali na wuce ɗakina na yi wanka na fito na mulke jikina da mayukan da ya kawo masu daɗin ƙamshi da sanya nutsuwa, sannan na ɗauko sabuwar bra na buɗe na zaɓa size ɗina saka, daman tun da muka iso da na yi wanka na cire wadda na zo da ita ban sake sakawa ba sai yanzu, Allah na tuba breast ɗin nawa ma gudawa nawa ne? Akwai su amma ba lallai ina buƙatar bra ɗin ba tun da ba wani girma ne da su sosai ba kuma ga su a tsaye....bayan na saka na saka pant da wani cotton under skirt mai azabar laushi da kyau sannan na shirya cikin wata rantsatsiyar Abaya C-green wacce ta yi matuƙar amsar jikina. Bayan na kambala na sake buɗe wasu turarrukan bayan wanda na buɗe jiya na tuttulasu a jikina domin da alama yana masifar son ƙamshi... Ko da yake waye baya son ƙamshi ma a duniyar nan? Amma dai shi ɗin na musamman ne domin turaruka ne wanda ban taɓa sani ma da akwai su ba a faɗin duniyar nan ba.
Fitowa na yi naje na karɓo abin kari na dawo ɗakinsa inda na cimma sa shima ya shirya cikin manyan kayansa na wani rantsatstsen yadi fari ƙal da hula da takalmi ya fito shar da shi wanda muna haɗa ido lokaci ɗaya na ji zuciyata ta tsinke ba shiri na yi ƙasa da kaina domin ba ƙaramin ƙwarjini ya mini ba sosai haibarsa ta cika idona.
Zaunawa ya yi akan Sofa wanda da alama zaman yana da nasaba da shigowar da na yi ganina ɗauke da tray. Wani ƙaramin glass table na janyo na ɗora a kai a hankali na ɗan kalle sa na ce.
"Bismillahi!"
Kafin ya yi maganar da ke bakinsa don da alamar kallon da yake mini yana da ra'aya yasa na miƙa hannu na ɗauki ɗayan Tea cup ɗin na shanye Sannan na ɗauki spoon na ɗan tsakuri sauce ɗin Indomien da aka haɗata da nama da kuma veggies na kai bakina. Jin yanda ta yi daɗi yasa na zage ina ta kaiwa a hankali wanda tun ɗazu shima yana shan Tea ɗin da toast bread yana kallona. Bayan ya cinye one piece na toast bread ɗin ya ci yam ball ƙwaya biyu sannan ya ɗauki bottle water ya buɗe yasha sannan ya ajiye ya kalleni karon farko ya jinjina kansa da ɗan murmushi a hankali ya ce.
"Thank you."
Daga haka ya miƙe ya shige banɗaki.
Nima dai bayan na gama na tashi na fice da kayan sannan na koma ɗakina na wanke bakina na ɗan ƙara gyara hulata da ke ta zamewa sannan na gyara rolling ɗinda na yi na fito muka haɗe a parlour muna nufi hanyar fita wanda yana gaba ina bayan sa har muka isa mota. Nan muka tarar da guides ɗinsa tsaye tamkar wasu saƙagai suna ta kwasar gaisuwa da muka fito sannan suka buɗe mana muka shiga.
Shiru ne ya ratsa tsakaninmu wanda yana kallon wata 'ƴar computer da ke gaban sa yana aiki ni kuma ina kallon waje har muka isa Nigerian Immigration Service (VIP Channel) muna shiga wani office muka nufi wani table inda aka rubuta VIP Consular Desk inda muka tarar da wani managern sa na reshen kamfaninsa Golden pathways dake nan Abuja Abdul-Kareem wanda suke kira da Mr. Kareem har ya riga mu zuwa yana zaune yana tattaunawa da Jami'in.
Cike da girmamawa suka gaisa wanda ni dai ban yunƙurin gaishe su ba, domin idan akwai buƙatar hakan wata ƙil da yace na gaishe su a fahimtata.
Bayan sun gama gaisawa ne ya faɗa mishi cewa an cike application form na E-passport da bayanan biometric yanzu thumbprint zan yi da kuma ɗaukar hoton fuskata. Ya faɗa masa cewa an biya service fee Sannan ya miƙo masa receipt mai ɗauke da official stamp. Sannan ya ce an duba identity document, birth certificate da letter of sponsorship daga Golden pathways Wanda ya nuna dalilin tafiyar na business and residency a Dubai.
Nan suka ci gaba da tattaunawa, bayan na gama komai da ake buƙata sai ga wani ya shigo ya miƙawa Mr. Kareem ɗin letter to authorization daga kamfanin Dubai branch tare da e-visa confirmation da aka fitar ta Hanyar MISA/Government liaison na kamfaninsa na Golden pathways.
Bayan mun kambala muka fito muka je offishin Customs for Checks-up wanda a nan ma already Mr. Kareem ya gama komai, nan aka bamu wasu takardu muka cike tare sannan na yi signing shi ma ya yi, sai kuma health clearance letter da ya karɓo daga prestige Clinic a matsayin proof of fitness for traveling. Nan suka sake yi min general health screening da Komai da komai sannan daga ƙarshe aka bamu travelling declaration. Bayan mun kambala sai misalin 2pm muka koma gida.
Haka muka rayu tsawon wasu kwana yana ta min shirye-shiyen ni dai iya ka ta ido sai idan an ce in yi sannan zan yi. Haka muke zaune kamar wa su kurame domin sai abu ɗaɗɗaya ne yake sa muna yin magana da juna. Amma kuma a tare muke bacci baya taɓa barina ni kaɗai kuma ko zaune muke wani lokacin yafi son ya jini ina cikin jikin sa koda kuwa magana bata haɗamu ba. Idan ka ji maganata to waya nake da su Ammie amma shi tunda muka taho banga ya yi magana a waya ko ta second ɗaya ba, wannan wayar number ɗaya ce a cikinta ta Ammie wanda ban sani ba ko yana da wata wayar daban da yake magana da su Aunty Labiba.
Yau ma muna tashi bayan mun yi sallah ya shirya ya fita ko karyawa bai yi ba kuma bai dawo gidan ba sai misalin ƙarfe biyar na yamma. Yana shigowa karo na farko kenan da na buɗe baki na ce.
"Sannu da zuwa!"
Jinjina kansa ya yi yana ɗan murmushi ƙasa-ƙasa ya ce.
"Na barki ke ɗaya ko? I'm sorry...."
Nima murmushin na mayar masa, cike da ƙarfin hali na ce.
"Ya kamata ka ci abinci..."
Hannuna ya janyo yana faɗin.
"Thank you...but I'm sorry,kan hanya muke a yanzu, idan mun samu dama sai muci a hanya. Ya yi miki?"
Jinjina kaina na yi na ce.
"Ba laifi. Duk yanda ka yi dai-dai ne."
"Ok to! Bari in ɗan yi wanka, kema idan kina buƙata ki je ki shirya kafin na fito...."
Girgiza kaina na yi na ce.
"Ban ji ma da yin wanka ba...za ka iya zuwa ka fito...."
Ɗan tsagaitawa na yi kaɗan har ya juya sannan na ce.
"Ina so in yi magana da Aunty Labiba..."
Wata irin faɗuwar gaba ya ji lokaci ɗaya jin kalmar sunan Labiba... Labibar sa, ƙanwar sa mai son ganin farin cikinsa. Ita ɗin bayan Hajiyarsa tana da wani irin matsayi ne a zuciyar sa. Tana da matuƙar kirki da hankalin da har abada ba zai daina alfahari da ita ba. A lokacin da ya cika 40years ya shirya buki a Dubai inda ya gayyace kowa da kowa aka yi shagali sannan ya bata Kambu (award) ya naɗata jakadiyar wanzar da zaman lafiya na kamfanin sa na GOLDEN PATHWAYS (Peace Ambassador).
'A yanzu ko a wanne irin hali take ciki bayan ya baro ta? Yanda za su nun karaya su ji kunya akan al'amarin Hajiya shi ne abin da baya son gani a rayuwar sa. Ya zai yi idan Labiba ta durƙusa a gabansa da kuka a idonta wai da sunan ba shi haƙuri...! 'Kai duniya! Wallahi Hajiya ta cutar damu. Ta rusa mana gida ta rusa mana farin ciki. Emraan,' ƴar rigimarsa Nadeeyah sannan masoyiyar er Auta Hairiyya.' Ya tuna ranar auren da ta tuma ta ɗane bayan sa wai bari ta ƙara shanye daɗin bayan Daddy kafin yaran da Mummy NANA za ta haifa musu su yi mata cin layi.....
Ganin yan da hawaye suka cicciko idonsa yasa na yi saurin girgiza kaina na ce.
"Ka yi haƙuri idan maganata ba ta yi maka daɗi ba.."
Janyoni ya yi a hankali ya yi kissing forehead ɗina lightly Sannan ya wuce ɗakinsa ya buɗe bedside drawer ya ɗauko wayar da yake magana da su ya kunnata ya cire mata passwords gabaɗaya ya miƙa mini sannan ya juya ya koma ciki.
Tun da ya miƙo min messages suka shiga shigowa ɗaya bayan ɗaya sun kai guda talatin wanda babu suna guda ɗaya da na gane a ciki.
Ban buɗe ba domin ba hurumina ba ne. Contact na shiga ina neman sunan Labiba amma kuma ban gani ba. Hakan yasa dole na haƙura. Koda ya fito batun ƙarfe shida ake. Hakan yasa a gaggauce ya kalleni ya ce.
"Zamu iya tafiya.?"
Jakar hannun sa na karɓa ina jinjina masa kaina alamar eh.
Bayan mun shiga mota mun zauna na miƙa masa wayar ina faɗin.
"Banga numbern ta Aunty Labiba ba..."
"Ok."
Abin ya ce kenan tare da karɓa wayar ya ajiye ta a gefen sa wanda sai da muka isa Airport ɗin ne sannan ya kama hannuna ya sanya wayar yace na zauna a motar yana dawowa yanzu.
Bayan ya fita na danna wayar sai naga an rubuta 'my peace' akan wata number, hakan yasa na danna kiranta wacce da alama ita ce ya kamo mini.
Ringing ɗaya zuwa biyu na ji muryar Aunty Labiba cike da kuka ta ce.
"Yayah..!!"
Wata irin doka wa ƙirjina ya yi. hankalina a tashe na ce.
"Aunty Labiba..."
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali itama ta ce.
"Beenafah...! Beenafah ina Yaya?"
"Ga shi can ya fita yanzu, ina zaune a mota ne ina jiran sa, ya ce min yana zuwa yanzu....."
Ajiyar zuciya ta sauke a hankali ta jinjina kai tamkar ina a gabanta ta ce.
"OK."
Shiru ne ya ratsa tsakaninmu wanda a tunanina yanda na rasa abun faɗa itama haka ne a wurin ta. Da ƙyar na ƙaƙalo wata maganar can ƙasan maƙoshina ina mai jin wa su siraran hawaye na jin cewa ban kyauta ba a raina a hankali na furta mata cewa.
"Ku yi haƙuri Aunty Labiba ku yafe mini! Idan har na zama sanadin rugujewar farin cikinku dan Allah ina neman gafararku...."
"Haba Beenafah! Dan Allah ki daina ma wannan maganar...babu abin da kika aikata. Ina matuƙar alfahari dake. Ki kula min da Yayana sosai kin ji ko,shi ɗin tamkar mahaifi yake a gare ni wani ɓangaren. Na san ki, ke ɗin jaruma ce ta gaske, na yarda da cewa za ki iya. Dan Allah kada ki bari ya shiga wani ƙunci, na ba ki amanar sa. Shi ɗin bai san kowa ba idan ba mu ba, idan baya tare damu aikinsa shi ne abokin rayuwar sa, amma yanxu ke ɗin kin maye gurbin komai da kowa...Allah ya ba ki ikon kulawa da shi... In sha Allahu komai zai yi daidai watarana."
Tun ina iya sarrafa sautin kukana har ta kai ga na kasa riƙe kaina, sosai nake kuka ina jinjina kaina tamkar ina a gabanta na ce.
"In Sha Allahu Aunty Labiba..."
Daga haka ta yanke kiran. Wallahi na ji tausayinta sosai har cikin zuciyata. Sai nake jin cewa kamar abin da na yi ban kyauta ba, dama na bari ya sake nin da yanzu hakan ba ta faru ba. Na jima kusan 30mnt sannan ya dawo. Da sauri na goge fuskata ina mai ƙirƙiro murmushi don kada ya fahimci cewa na yi kuka. Shigowa motar ya yi a nutse ya kalleni ya ce.
"Ina fata kina lafiya?"
Jinjina kaina na yi ina mai kawar da kallona gefe na ce.
"Alhamdulillah! Da fatan kaima haka?"
"I'm fine..."
A hankali motocin suka fara tafiya zuwa can cikin sannan muka fito a tare muka wuce. Muna isa wurin wata glass window Haroun ya miƙa wata takarda ya ce.
"She has been cleared under diplomatic Company sponsorship....Manifest will be forwarded to King Khalid private Terminal."
Jinjina kai Officer ɗin ya yi sannan ya miƙo masa takardar clearance muka wuce muka sake shiga motocin. Private Aviation Terminal (Fixed Base Operator) muka nufa inda aka buɗe mana wani gate zuwa tarmac wanda yake private ne ma'ana wuri ne na musamman for special people only. Hannunsa riƙe da nawa muka iso wani haɗaɗɗen lounge mai private check-in counter muka zauna.
Bayan mun yi sallar Magrib da Isha, Iyakar mu 15mnt muka tashi muka wuce wurin wani private jet na musamman da aka rubutawa The 'Golden Falcon X9 MAA' (Muhammad Attahiru Araam). A bakin stairs ɗin hawa jirgin wata flight attendant ta miƙo min hannu tana murmushi ta ce.
"Welcome Ma'am.."
Murmushin na mayar mata na ce.
"thank you."
Daga nan ya jinjina kai yana mai ƙara maƙalƙale hannuna a nasa ya ce.
"Kada ki damu, tare zamu shiga ni da ita....."
Sai da jami'an tsaron sa suka fara shigewa su huɗu sannan su Sharath suka shige sannan mu da kuma wasu guides ɗin sa biyu.
A wani private suite muka shige inda luxurious club seat muka zauna Wanda yake ɗauke da komai na jindaɗi da more rayuwa.
Kallona ya yi a hankali ya jinjina kansa ya ce.
"Wannan jirgi na ne, when ever you wish,he will take you around the world...yanzu zamu tafi inda nake zaune da kasuwanci na a United Arab Emirates, that's Dubai.."
Murmushi kawai na yi masa ina ƙara jinjina girman abin a raina. Wato shi ɗin wai har jirgi yake da shi. No wonder Hajiya da su Hairi suka maida tafiya ba a bakin komai ba.
A hankali bayan an gama komai jirgin ya fara tafiya yayin da na lumshe idanuna na nutsu ina addu'a har ya gama daidaita a sararin samaniya. Nan aka gabatar mana da light meal muka ci Sannan bayan mun kambala ya rungumeni shiru ba tare da ya yi magana ba.
Bayan tafiya mai tsawo wanda har na yi bacci na tashi sai gashi mun isa ƙasar cikin amincin Ubangiji.
Flight attendant ɗin nan ta ɗazu ita ce ta sake dawowa ta kawo min Immigration forms na UAE mai ɗauke da landing cards da declaration slip. Nan ya karɓa ya rubuta sunana, passport number, da kuma full address ɗin gidansa da yake zaune a ciki. Muna saukowa muka fito sai ga welcoming delegates daga Golden Pathways Dubai sun tsaya a bouquet da murmushi cike da girmama suka shiga yi mana sannu da zuwa.
A yau babu abin da nake idan ba murmushi ba, duk da cewa wannan tafiyar ba ita ce tafiyata ta farko a jirgi ba, ta bar min wani tarihi na musamman. Daman kuma shekara nawa da hawana jirgin? Komai ganin sa nake tamkar a mafarkina ne yake faruwa. Ga shi duk inda muka saka ƙafa hannuna na maƙale a cikin nasa lokaci bayan lokaci yana tambayata da fatan ina lafiya.
Nan muka shiga motoci exact irin waɗancan da muka hau a Nigeria zuwa gida.
*********
Aunty Aysha kuwa, sai da ta share wata ɗaya gidan Ammie sannan ta shirya daga can ta wuce gidan Hassana. Sosai ta yi farin cikin yanda ta tarar da ita domin Alhamdulillah tana zaune cikin rufin asiri bama kamar yanda suka tsamma ta ba, duk da dai idan da ace Mummy za ta zo to tabbas babu abin da zai hana zuciyarta bugawa akan baƙin ciki, domin gidan ƙofa ƙarama ko gate babu.
Daman Aunty Aysha ta faɗawa Uncle Isma'ila cewa ta samu labarin Ammie,yana jin wannan labarin ya nemi da ta faɗa masa inda take ta ce mishi tayi alƙawari ba za ta faɗa ba. Kawai ta faɗa mai ne idan har zai iya ya faɗamata saƙon sa ita kuma ta yiwa alƙawarin za ta mayarwa Ammie.
Hakan yasa ya tura kuɗin direct babu ya ce ta bata kuma ta roƙa masa gafarar ta.
Bayan ta faɗawa Ammien, murmushi kawai ta yi tana tuna yanda ya wulaƙansu a ranar da suka dawo daga asibiti sannan ta ce mata ta turawa Malam Habibu 5M Babansu Ya Jafaru ya ja kasuwa, sannan idan taje gidan Hassana ta bata 6M ɗin itama ta dogara da kanta kada taje can watarana rayuwa ta yi wahala su Mummy su kasa taimaka mata.
Mamaki ne ya kama Aunty Aysha na cewa wai ga baki ɗaya ta rabe kuɗin kuma ta faɗawa Uncle Isma'ila cewa ta yafe masa duk abin da ya samu sama da kuma duk laifin da ya mata.
Hakuri ta bai wa Aunty Ayshar ta ce, duk abinda zai sa ta tuna da zamanta a gidan Daddy Mudassiru to bata ƙaunar sa har abada. Kuma ma ai sadaka ta yi ba wani abu ba.
Baba da mamakin Fakiha Mota suka ɗauka sukutum har Sokoto wurin yi mata godiya har da kukansu.
Ga shi daman har da Jafaru suka je da Ya hamza. Ya so ganin Beenafah koda sau ɗaya ya tayata murna amma cikin rashin sa'a akace sun wuce inda Mijinta yake aiki. Yanda ya ji haka ya faɗawa Ashiru wanda yanzu sosai suke abota da juna wanda da kanshi yake bai wa Ammie labarin Ashirun na cewa tun da ya ji labarin auren Beenafah bayan ya gama jimaminsa ya koma Kano ya ci gaba da kasuwancinsa tare da mantawa da wasu abubuwan amma dai ta kasa mantawa da Beenafah.
Hassana kuwa, yi ta yi tamkar za ta yi hauka akan kuɗin da Ammie ta aika mata. Kuka sosai take da hawayenta tana tuna irin gudummawar da ta bada wurin wulaƙanta Ammie da Beenafah. Hatta Bahrain tasha dukan sa haka kawai ba tare da ya yi mata laifin komai ba. Yanzu ga shi ta turo mata kunyarta ta aiko mata da kuɗinda ko mutuwa za ta yi tasan Mummy da Daddy ba za su iya bata ba.
Nan ta ɗauki 4M ta baiwa Salman ɗin ta je ya buɗe private clinic ya zuba magunguna ita ma sai ta shiga juya 2M ɗin su gani.
Suna kan kassafa kuɗin kawai Aunty Aysha ta fashe da kuka tana kallon Salman ɗin ta ce.
"Haƙiƙa ka bani tausayi daga kai har ita, amma kuma ƙwarin gwiwa da jarumtar da ka nuna sun burgeni kuma na ƙara ji a raina cewa ka dace da ƙanwata. Haɗuwarku ne da taimakon Allah yasa ta shirya daga munanan halayen da take. Allah ya baku zaman lafiya ya baku zuriya ɗayyaba sannan ya sa albarka a cikin kasuwancin ku."
Rungumeta Hassana ta yi tana ta wani kuka cike da nadama ta ce.
" Aunty Aysha ku yafe mini dan Allah....yanzu haka ina ɗauke da juna biyu na 6weeks...A yanzu daga ke sai su Hajiya Ermama kawai nike da, ke ce uwata.... Dan Allah ki yi min alƙawarin cewa idan na haihu za ki zo..."
"Insha Allahu na yi alƙawari Hassana.... Ina roƙon ubangiji ya bani ikon cika wannan alƙawarin. Ki kula da kanki kuma ki kula da shan magungunan ciki kin ji ko musamman na ƙarin jini da abinci mai lafiya don gujewa matsala.. Kuma duk abin da kike so kada ki ji shakka kawai ki kirani kin ji ko..."
" In Sha Allahu Aunty Aysha. Na gode sosai Allah ya saka da alheri ya bar zumunci."
Kwana ɗaya ta yi wanda duk sai da suka zaga dangin Salman da ita ta gansu suka gaisa sannan ta juya ta koma Abuja ba tare da sanin Su Mummy ba ta hau jirgi ta yi tafiyar ta London.
********
Daddy kuwa, daman unguwar da Ammie suka bari ta gusau, can yaje tamkar wani taɓaɓɓe yana ta bin mutane duk wanda ya haɗu da shi yana tambayar sa wai ko yasan Hajiya Mulaifa sannan da kuma wanda ya auri Beenafah.
Ya daɗe yana wahala bai samu bayanin komai ba. Sai daga ƙarshe Allah ya taimake shi ya samu wani yaron da ya ce ya san su amma kuma sai idan za su yi jinga ya biyasa shi kuma zai kawo masa Ammie da Beenafah da ma mijin da ta aura.
Kullum yanzu cikin bauta masa yake yana tura masa kudaɗe, ko a katin waya kawai a yini yana tura masa na 10k banda dubu dari biyu dubu dari wai duk na hawa abun hawa ne kafin ma su gama yanke abin zai ba shi.
Bayan ya tabbar masa cewa idan ya samosu zai faɗa masa sannan ya tura masa da kudadensa shi kuma ya zo ya kawo masa su.
Yana kan hanya ya fito daga Kaduna wurin ɗaurin auren ɗiyar abokinsa zai koma Abuja ya kira shi. Wuri ya samu jiki na rawa ya yi parking ya fito ya kira shi back yana faɗin.
"Ado ka samo su ne?"
"Eh Alhaji...aiki ya cika. Ka turo da kaya nima in turo maka su..."
Bai ankare ba ya ji saukar Itace an rabka masa a bayan ƙeyar kansa. Ɗaya daga cikin mutanen da suka Parker mota ne su uku suka buɗe gabanta suna gyara.
Haka Daddy ya zube luuu! Yana kiran.
" Innalillahi wa inna ilaihi raji'un.! An samo min Mulaifa... Dan Allah ku bari a kawo min tsinanniyar matar nan.."
Wani irin wawan naushin ne ya sake kai masa sai ga Daddy ya sume. Cikin uxuri suka karɓe Key ɗin motar tare da lalabe wayoyin sa da duk abunda yake da suka ajiye masa key ɗin kwaraɓaɓɓiyar motar su suka shige tasa motar suka tsere suka bar shi nan kwance a dajin.
*********
Gefen Hajiya kuwa, duniya ta yi mata zafi kowa ya guje ta akan abinda ta aikata. Hairi ma da ta rage mai goyon bayanta ta shirya ta koma makaranta.
Hatta su Hajiya Samiya da ta sanar da su cewa asirinta ya tonu ko kaɗan ba su yi gigin sake tahowa inda take ba, domin sun sani ko Emraan ya ɗaure su sai sun kusa
All Chapters
Chapter 1
Chapter 2
Chapter 3
Chapter 4
Chapter 5
Chapter 6
Chapter 7
Chapter 8
Chapter 9
Chapter 10
Chapter 11
Chapter 12
Chapter 13
Chapter 14
Chapter 15
Chapter 16
Chapter 17
Chapter 18
Chapter 19
Chapter 20
Chapter 21
Chapter 22
Chapter 23
Chapter 24
Chapter 25
Chapter 26
Chapter 27
Chapter 28
Chapter 29
Chapter 30
Chapter 31
Chapter 32
Chapter 33
Chapter 34
Chapter 35
Chapter 36
Chapter 37
Chapter 38
Chapter 39
Chapter 40
Chapter 41
Chapter 42
Chapter 43
Chapter 44
Chapter 45
Chapter 46
Chapter 47
Chapter 48
Chapter 49
Chapter 50
Chapter 51
Chapter 52
Chapter 53
Chapter 54
Chapter 55
Chapter 56
Chapter 57
Chapter 58
Chapter 59
Chapter 60
Chapter 61
Chapter 62
Chapter 63
Chapter 64
Chapter 65
Chapter 66
Chapter 67
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 33 Chapter of 67