Share this page
mai napep ya aramin wayarsa na kira likitanta. Ina kiran sa yana jin ni ce ya kashe ya kira ni back. Bayan mun gaisa na shaida masa halin da muke ciki da kuma cewa da suka yi na kawo mu su card ɗinta. Umarni ya ba ni da cewa na je na kai musu waya ya yi musu magana ko kuma na ba su numbernsa su kira sa. Ba ɓata lokaci na yi duk abin da ya ce wanda su da kan su suka karɓi numbern ta shi su ka kirasa. Misalin ƙarfe goma sha ɗaya na dare aka fito da ita zuwa Psychiatric Unit da ke cikin asibitin. Gida aka sake turani na ɗauko magungunanta na dawo. Sai a wannan lokacin Ashiru mai Napep ya yi mini sallama ya tafi gida. Still a daren ranar nan sai da aka sake bani takarda na je na biya kuɗin wani maganin kusan dubu talatin, na karɓo a pharmacy na kawo musu. Sai da muka kwana huɗu a asibitin sannan Ammie ta farka,sai dai kuma, farkawa marar daɗi cikin mummunan yanayi wanda ya sakani kuka, kuka fiye da wanda nayi a baya. Domin sabbatu ta shiga yi ba sama da ƙasa, ta ƙarfin tsiya ta shiga neman cisge aikin da akayi mata a hannun damanta  sanadiyyar karaya da ta samu. Cikin tsananin ɗaga murya da ƙaraji na shiga ihun kiran likita domin ba zan iya ɗagawa na barta ba. Halin da Ammie ta shiga a wannan lokacin haƙiƙa ya sakamu cikin tashin hankali da gigita. Hali ne wanda ko maƙiyanta ya kalle ta sai ya tausaya mata. Nan take likitoci suka shigo suka rufu akanta, bayan sun gama dubata ba jimawa bacci ya ɗauke ta da alama allurar bacci suka yi mata. Mun share kusan sati Ammie tana cikin wannan halin wanda har ta kai ta kawo ma bana son ta farka gudun kada ta tashi ta nemi fama ciwon ta. Ga damuwar Bahrain ta wani fannin tana matuƙar sosa mini zuciya, bana son ganin sa cikin halin da yake. Dukkan tsanani yana tare da sauƙi. A hankali a kwana a tashi muka shiga cikin sati na biyu wanda Alhamdulillah! Jikinta ya fara sauƙi ciwon ta shima da sauƙi sosai domin a yanzu ta daina farkawa cikin firgici da tsoro ko kuma sabbatu. Sai dai idan ta farka tayi shiru bata cewa komai ba. Yau ma koda ta farka, a lokacin ina zaune gefenta na ƙura mata ido kawai ina kallonta yayin da Bahrain ke can waje akan tabarma da waya a hannunsa yana sauraren karatu. "Allah sarki Ammiena! kin farka?" Na furta mata hakan ganin yanda ta ƙureni da kallo. Sai da ta ɗauki tsawon lokaci tana kallona kamar yanda ta saba sannan daga ƙarshe ta gyaɗa kanta a hankali ta mayarda idanunta ta rufe sai hawaye. Cikin sauti marar tashi ta ce. " Bani ruwa Beenafah.." Da sauri na buɗe locker na ɗauko ruwan gora na bata tasha a hankali na mayar a locker sannan na kalle ta cike da wani sabon tausayin ta na ce. "Sannu Ammie, Allah ya baki lafiya, Allah yasa wannan ciwon ya zamto kaffara. Kada ki zafafa tunani kin ji Ammie,Bari na kira likita." Ina fitowa na kalli Bahrain na ce. "Bahrain ka je Ammie ta farka, zan je na kira likita yanzu."                              *** Sati Uku mukayi a asibitin, wanda mun kashe kuɗi sun kai dubu ɗari huɗu da wani abu. sai sayen magani muke, yau wannan gobe wannan. Amma Alhamdulillah! Abu mafi muhimmanci shine, ta samu sauƙi sosai wanda wannan shi ne babban burinmu. Yaya Ashiru, wanda ya zamto Yayana a yanzu domin ya tsaya mana a lokacin da ban yi tsammani ba. Da shi muke duk wannan zirga-zirgar, ko sau ɗaya bai taɓa nuna mana ya gaji ba, kuma duk wani abin da ya kamata ace naje nayi shi yake tsayawa tsayin daka ya yi mana shi, hakan yasa na ji sa wani mutum na daban a cikin duniyata.                          *** Ranar Monday da safe likita ya kirani office ɗinsa ya bani takardar sallama tare da takardar refferal zuwa asibitin Sokoto inda muka saba jinya. Amma ya ce zamu iya zuwa gida mu shirya zuwa kwana biyu sai mu tafi, domin condition ɗinta ya yi sauƙi sosai In Sha Allahu babu wata damuwa. Yaya Ashiru shine wanda ya zo ya kaimu gida da kansa. A daren da muka koma gida ne naje shagon Baba mai shago na bashi katin Daddy na ce ya ɗauki numbern wayarsa ya kira shi ya ce mi shi Beenafah ce. Na fi minti talatin a tsaye bai kira ba, daga ƙarshe na ba shi ɗari biyu na ce ya saka kati ya kira mini shi. Sake kiransa ya yi ya miƙomin wayar na kara a kunnena, ƙirjina na dukan uku-uku na yi masa sallama.             ✍️  *OUM-AMEER*  ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀 *ADABI WRITER'S ASSOCIATION* *AMEENA IBRAHIM*      *OUM-AMEER* *Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewabooks:@Aminatuibrahimbawa* *FREE-BOOK* *PAGE 7* "Daddy ina wuni." Jin ya yi shiru yasa na ce. "Beenafah ce Daddy.." Daga can ɓangaren Daddyn cikin nuna kamar alamun mamaki ya ce. "Beenafah?" "Eh Daddy ni ce. Daman Ciwon Ammie ne ya tashi har ta fito titi aka haɗa da tsausayi sai mota ta bigeta, to munfi sati uku a asibitin Janbulo kuma jibi zamu wuce Sokoto domin tana cikin halin jinya sosai har karaya ta samu a hannunta na dama...." "Allah sarki! Allah ya ba ta lafiya." "Amin. To Daddy daman..." Da sauri ya tare numfashina da faɗin. "Dan Allah ki dakata mini Beenafah! Kin fi kowa sanin ina wurin aikina yanzu haka, yakamata ki riƙa sanin lokutan kirana, mts!" Daga haka ya yanke kiran ba tare da ma ya tsaya ya saurari maganata ba. Bayan na tabbatar ba ƙara kira zai yi ba yasa na miƙawa Baba mai shago wayarsa a saɓule ina mai tsiyayar da ruwan hawaye masu cike da ɗaci da baƙin cikin daddy na juya na koma gida. Ina shiga na tarar da Malaman islamiyyarmu su huɗu tare da ɗalibansu rututu suna yi wa Ammie addu'a. Zaunawa na yi nima tare da su har aka kambala addu'ar, sannan na gaishe da Malaman na kuma yi musu godiya. Wallahi har cikin raina na ji daɗin ganin su da kuma ƙaunar da suka nuna a garemu. Hakan sai ya mantar dani baƙin cikin daddy da na dawo da shi daga shagon da naje. Bayan mun rako su, a bakin gate Ra'is ya kalleni ya ce. "Beenafah shikenan dai da gaske kin yafe Islamiyyar ko?" Girgiza kaina na yi ina murmushin ƙarfin hali na ce. "Ba haka ba ne Ra'is, nima ina son islamiyya amma kuma dole ce tasa na barta, idan ina da rabo watarana zan dawo." "To Allah ya taimaka, Allah ya bata lafiya. Kuma dan Allah ina roƙo; Bahrain yana daga cikin yara masu hazaƙa da muke alfahari da su, a daina wasa da makarantarsa, idan yazo sati biyu cikakke sai an samu tsawon kwanaki bai zo ba, kinga hakan dole zai yi affecting ɗinsa, domin da zaran an wuce shi an wuce shi ba za'a dawo baya saboda shi ba." Jinjina kaina na yi a raina ina jin ba daɗi na ce. " Haka ne Ra'is, wallahi duk abinda ka faɗa gaskiya ne, to amma ko yanzu ina ƙara baka haƙuri domin uzuri ne wanda ban san ya zan yi ba,amma In Sha Allahu za'a gyara." " To Allah ya bada iko. Allah ya bata lafiya mai albarka." "Amin Ra'is, na gode sosai Allah ya saka da alheri." Akan hanyarmu ta dawo daga rakiyar su na cewa Bahrain. "Kai ne ka ce su zo duba Ammie?" Girgiza kai ya yi yana riƙe da hannuna ya ce. "A'a. Ina zuwa Ustaz ya ce mini miyasa na daina zuwa kwana biyu, shine na ce mishi muna asibiti an kwantar da Ammienmu ba lafiya,shikenan ya ce na wuce na zauna, to ana tashi sai ya kirani ya ce mini za su taho tare dani duba Ammie." "Allah sarki! Allah ya saka musu da alheri." "Amin aunty Beena. Ustaz ya ce addu'a waraka ce, indai aka dogara ga Allah akayi ta addu'a ciwo kowane iri ne za'a warke..." "Wannan haka yake Bahrain, Ustaz gaskiya ya faɗa, muna kan addu'ar akodayaushe, Allah yasa mu dace amin." Haƙiƙa koda na taso ni ɗin na kasance mai ƙwazo sosai ta kowanne fanni, da hakan na kafe manyan burika guda biyu a cikin raina wanda both Ammie da Abbie suke kan wannan burin su ma. Sai dai kana naka Allah yana na shi iko,ta dalilin rayuwar da muka tsinci kanmu a ciki dare ɗaya,yasa dole na haƙura da nawa mafarkin domin ba zan bar mahaifiyata ita kaɗai ba na fita makaranta, amma kuma na ɗauki alƙawarin bai wa Bahrain cikakkiyar kulawa da goyon baya akan islamiyya da bokonsa, mafarkina da ban samu damar cikawa ba sai ya cika mini shi inda rai da rabo. Ɗan wanda na samu Allah yasa masa albarka ya hore mana hanyar kulawa da na Bahrain.                                           *** Washe gari Ina zaune a bakin famfo misalin ƙarfe goma sha ɗaya na safe ina wanki na ji ana ta bubbuga ƙofar gate ɗinmu. Cikin mamaki na je ina tambayar waye ne. "Ashiru ne..." Kafin ma ya iyarda rufe bakin sa cikin farin ciki na je na buɗe. Turus na yi ina kallon taron bataliyar da yake tare da su. Murmushi ya yi ya ce. Shima dai murmushi ya sakar mini tare da kallon su ya ce. "Iyayena ne da ƙannaina Beenafah. Cewa suka yi suna so su zo su ga Ammie da jiki." Cikin nuna zallar farin ciki na ce. "Allah sarki! Sannunku da zuwa....Ku shigo ciki dan Allah." Tare muka shiga har ciki inda Ammie ke kwance akan katifa saman varendar, ga waya a gefe sautin karatun alƙur'ani yana ta tashi mai taushi da sanya nutsuwa. Daman a nan na fito da ita kusa da ni domin na riƙa hango ta da kyau kada na barta a ɗaki ita kaɗai. Tunda muka dawo daga asibiti bacci ya ƙaurace mini domin dole nayi kaffa-kaffa kada ta yi ƙoƙarin fama ciwon hannun ta da akayi ɗori. Cikin ikon Allah kuma, tunda muka dawo daga asibitin, lafiya ƙalau take babu alamun motsawar yanayin ta har yanzu, ko don sanadiyyar zafin ciwon da take ciki ne oho! Koda yake kuma babu abin da ya gagari Ubangiji, Allah na gode maka, Allah ka ƙara bata lafiya da nutsuwar ruhi amin. Tabarma na shiga na ɗauko musu na baza ta a gaban su na ce su zauna. A hankali na taimakawa Ammie ta tashi ta zauna sannan na gaishe da su, bayan mun gaisa na kalli Ammie na ce. "Ammie waɗannan iyayen Yaya Ashiru ne da ƙannensa suka zo duba ki." "Allah sarki! Sannun ku da zuwa.." A tare duk suka amsa suka gaggaisa sannan ɗayar dattijuwar dake gefen Yaya Ashiru wacce da alama ita ce mahaifiyarsa domin sun yi kama sosai ta ce. "Sannu Hajiya! Ya jiki? Ashe kuma wasu ƙaddarori ke ta faruwa?" "Wallahi kuwa. Jiki mun gode Allah." "Ubangiji Allah ya baki lafiya yasa kaffara ne." "Amin. Na gode Allah ya saka da alheri." Ɗayar ce ta karɓa da cewa. "Ai Ashiru yayi mana bayanin duk abin da ya faru, abin takaici abin baƙin ciki mutumin da ya kaɗeta ko dai ya fito a mota yace Allah ya sawaƙa bai yi ba. A lokacin da ya kaɗeta dama tafiyarsa ya yi da abin ba zai dame mutane ba da ace wai sai da ya tsaya ya ga an sakata a Napep tsabar iskanci sannan ya juya ya wuce,wannan wane irin rashin imani ne?" Take na ji takaicin mutumin nan ya dawomin sabo a raina, wanda bayan su Daddy da wasu tsirarrun mutane; shine mutum na gaba da tsana a rayuwata. "To ya za'a yi! Tunani da hankalin mutane ya banbanta, kowa da irin yanda Allah ya halicce sa. Abu mafi muhimmanci shine tana raye bata mutu ba, Fatanmu shine Allah ya bata lafiya." Cewar Yaya Ashiru yana mai ƙureni da kallo ganin yanda lokaci ɗaya yanayina ya canza. Ni kuma jin wannan furucin yasa na ɗan saki raina na kalli yaran da ke wurin wanda ciki har da sa'annina da ma waɗanda suka girme mini na ce. " Yanzu Yaya Ashiru waɗannan duk gidanku ɗaya da su?" Dariya suka yi dukkan su sannan daga baya ya gyaɗa kan shi ya ce. "Ƙannina ne! kin gansu su tara cif,akwai biyu da sukayi aure, bayan su kuma akwai Maza uku mata biyu waɗanda su ne yayyuna. Wa su kinga Mamansu nan, wa su kuma kinga ta su  Maman nan. Kuma ita wannan...Umma muke ce mata." Cewa da maman su, sai kuma ya nuna ɗayar ya ce. " Ita kuma wannan, Ayya muke kiranta." Murmushi na yi ina jinjina kaina na ce. "Masha Allah. Ban taɓa ganin irin wannan familyn ba." Cike da mamaki ɗaya daga cikin ƙannen nasa ta ce. "Ba ki taɓa gani ba?" Bakin gaskiyata na gyaɗa mata kaina na ce. "Da gaske nake miki. Duk familyn da nake gani,Mama da Baba, mostly yara uku, yara biyu, highest yara biyar haka..." "To amma..." Da sauri Yaya Ashiru ya katseta da faɗin. "Fa'iza ya isa haka, ku tashi mu tafi na mayar daku na koma wurin aikina." "Ni kuma tambayata ɗaya ce, dan Allah duk wannan gashin da nake gani naki ne?" Cewar wata ƙaramar yarinya wacce iyakarta may be sa'ar Bahrain. Dariya muka sake fashewa da ita dukkanmu sannan na saka hannu ina ƙara janyo zaren gashin kan nawa na gyaɗa mata kaina na ce. "Eh, gashina ne mana. Kema ai kina da shi..." Lokaci ɗaya Yaya Ashiru ya miƙe yana faɗin. "Ji wata tambayar shirme dan Allah? Ku tashi mu tafi please." Jinjina kai Ayya tayi ta ce. "Haka ne kam, ku tashi mu tafi. Allah ya ƙara bi da lafiya." "Amin Yah Allah mun gode sosai, Allah ya saka da alheri ya bar zumunci. Allah ya mayar daku gida lafiya." "Amin yah Allah Hajiya." Daga haka suka miƙe suna ta yiwa Ammie addu'a na rako su har bakin gate. Kallona Yaya Ashiru ya yi bayan sun wuce bakin Napep ɗin ya ce. "Yaushe za ku tafi asibitin? Kin san fa an ce ku gaggauta tafiya." Jinjina kaina na yi na ce. "Haka ne, in sha Allah zuwa jibi zamu tafi kamar yanda suka ce." "To Allah ya kai mu, In Sha Allahu zan zo zuwa ƙarfe shida na asuba na kai ku tashar." "Na gode sosai Yaya Ashiru Allah ya saka da alheri ya bar zumunci." "Ba komai Beenafah, Allah ya bata lafiya." Bayan na dawo daga rakiyar su na zauna inda nake na ci gaba da Wankina ina ƙara girmama kirkin Yaya Ashiru da familynshi. Daman ashe akwai family irin haka mai yawa da suke rayuwa so simple. Ga shi dai haɗuwa ɗaya tasa tamkar mun yi shekara da sanin juna.                             ***     Daren da ana gobe zamu tafi Sokoto Sai misalin ƙarfe tara na fita na je wurin Baba mai shago na ce ya kira mini Daddy sanin cewa wannan lokacin shi ne lokacin da na saba samunsa a gida,sai dai kiran duniya an yi amma yaƙi ya ɗauka kuma bai kira ba har kusan tara da arba'in na dare. Tsintar muryar Baba mai Shago na yi yana faɗin. "Beenafah ya ƙi ya ɗaga wayar nan fa. Ya kamata ki koma gida hakanan,ki faɗamin koda ya kira daga baya mi zan faɗa masa?" Jiki sanyaye na ce. "Kawai ka ce mishi Beenafah ce  ta so ta yi magana da shi kuma ta koma gida." Daga haka na juya jiki a mace na fara tafiya, ina kan hanya ina tafe ina lissafi, abubuwa duk sun isheni, lissafin kuɗi na shiga kamar wata zararra, gaba ɗaya kuɗinda ke account ɗinmu sun tafi, har so na yi na ce ayi mini checking balance amma tsoro hanani. Ga term ya yi na biyan kuɗi both islamiyya da boko dole zan yiwa Bahrain registration kamar yanda nayi last term, ko yanzu idan har Daddy bai tallafa mana ba, kuɗin nan sai mun wayi gari ba ko sisi, dole mu tattala su mu shiga yin sana'a da su kamar yan da Aunty Husaina ta shawarceni.... Ina cikin tunane-tunane ban ankara ba kawai na ji habshin Kare da gudu ya biyo ni, ba shiri na shiga falfalawa ina mai fashewa da kuka domin na tsani kare a rayuwata, ina tsoronsa sosai ko ganin sa idan nayi hankalina ta shi yake. Ina hango wa su mutane bakin wani gate da alama masu gadi ne, suna zaune a benci na nufe su ba shiri, wurin na tsallaka lambatu zuruf na faɗa ciki gwiwata ta bugu haka ɗan yatsan ƙafata. Take ɗaya daga cikin su ya ɗaga sandarsa ya kori Karen sannan suka yo kaina a tare mai sandar ya miƙa mini hannu na fito ina ta kuka suna ta faman yi mini sannu. "Ke ko yarinya ina za ki je da daren nan?" Cikin sheshsheka na ce. "Gi...gig..gida zan tafi." "To ina ne gidan na ku?" "Wan can titin na baya." "To muje." Ba musu na shiga gaba shi kuma ya bi ni a baya bai tsaya ba sai da muka kai ƙofar gida ya ga na shiga sannan ya koma. Tsayawa na yi na yaga gefen ɗankwalina na ɗaure babban yatsan ƙafata da ya kwaile yana zubar jini, sannan na duba gwiwata ta dama wadda naga itama ta goge sosai. Bakin famfo na je na wanke fuskata na goge da hijabina sannan na shiga gidan, ina gudun kada Ammie ko Bahrain wani ya ga yanayina kuma ban so hankalin su ya tashi. Gaba ɗaya daren ranar ban yi wani baccin kirki ba kasancewar raunukana da suka kwana suna mini azabar zogi da raɗaɗi, sai da na lalaɓo Rub na shafa nasha maganin ciwon jiki sannan na ɗan samu sauƙi.                                 *** Katamfe Extension, FCT Abuja, Nigeria.    Daddy yana zaune a cikin sabon gidansa da ya saya ya sake renovating kira ya shigo wayarsa, kamar ya san cewa Beenafah za ta sake kiransa da wannan numbern sai ya yi saving ɗinta.  Yana ganin sunan da ya yi saving da ita ya buga tsaki ya mayar ya ajiye. "Alhaji, Hafiz ya ce mini ya yi ta kiran ka amma ba ka ɗaga ba, lafiya kuwa?" Cewar Mummy dake shigowa ɗakin yanzu ɗauke da trayn slize fruit a hannunta. A hankali ta ajiye saman glass center table ɗinda yake gabansa sannan ta samu wuri cike da ƙasaita ta zauna a kusa da shi. Ajiyar zuciya ya sauke sannan ya ce. "Wallahi ban lura ba, da yake Beenafah ce ta tasani a gaba da kira shine na ajiye wayar, to ina ga lokaci ɗaya kiran ya shigo da na ta." Wani irin ɓata rai ta yi ta ce. "Ita kuma da kullum kwanan duniya ba ta gajiya da ɗorawa mutum lalura, kamar gare su babu ta yanke cibi. Shegiyar yarinya kawai. Mts!" "To yanzu dai ai an kai ƙarshe, bata ganni ba, waya kuma sai idan na ga damar yin picking zanyi. Miye Hafiz ɗin ya ce?" "A'a, cewa ya yi yanata jiranka baka aika masa da kuɗin ba tun jiya." "Kash! Wallahi kinga kuwa na manta ne, amma gobe In Sha Allah zan tura masa." "Allah ya kaimu." Suna nan a zaune suna fira sai ga su Husaina sunyi sallama sun shigo,bayan sun gaishe da su suka samu wuri suka zauna. Kallon su Daddy ya yi ya ce. "Ya na ganku duk kunyi wani iri? Any problem?... Uhm! Hassana, miye matsalar?" Ɗan yatsina fuska Hassana ta yi cike da mulki ta ce. "Ni Daddy problem ɗina ɗaya ne, ni dai bana son driver yana kai mu school, na fi so a bamu mota mu riƙa zuwa da kanmu, wallahi most of our friends duk da Mota suke zuwa da kansu..." "Drivern yana da matsala ne?" "Eh Daddy, baya zuwa da wuri, ko yau har kusan magrib muna hanya, ga shi wani irin baƙauye da shi Daddy, ni wallahi yana kofsa mana..." Mummy itama dai taɓe bakin ta yi ta ce. "To Allah na tuba daman wanda ya girma a ƙauye bai taɓa zuwa gari irin Abuja ba ai dole ya yi ƙauyanci wallahi. Ni fa, ko Biba don dai ta iya aiki ne kuma Humaida na sonta kawai yasa na ke zaune da ita, amma da ba don haka ba wallahi banga dalilin da zai hana na koreta ba. Saboda haka, Alhaji kawai ka yi musu yanda suke so su ma su shiga cikin tsara su kece rai ni kamar ko yaushe." " To shikenan, gobe idan Allah ya kaimu zan ce ya damƙa mu ku key a hannun ku... " Cikin shagwaɓewa Hassanar ta ce. " Haba Daddy dan Allah! Nile University fa! ... Ni gaskiya wannan motar ta yi mana local da yawa sai dai a saya mana sabuwa er yayi.." "To kar ki damu in sha Allahu gobe-goben nan za'a kawo muku sabuwa...." Daga haka ya mayarda kallon shi gun Husaina wacce tayi tuƙun-tuƙun da rai tun ɗa zu ya ce. "Husainata ya dai? Ko ke wannan tsarin bai miki ba?" Girgiza kanta ta yi cikin yanayin ta na ko in kula ta ce. "Ba komai Daddy, ni duk wannan baya gabana, fatana shine Allah ya bamu sa'a. Duk yan da akayi dai-dai ne." Tsaki Mummy ta ja tare da girgiza kai ta ce. "Shashasha kawai, marar wayau." Daga haka suka koma firar su hankali kwance suna nishaɗi.                        ***   Ƙarfe shida na safe a ƙofar gidanmu ta yi wa Yaya Ashiru kamar yanda ya yi alƙawari. Hankali a tashe ya kalleni ganin yanda nake ɗingishi ya ce. "Beenafah lafiya? Miye ya sameki a ƙafar?" Murmushi na yi na ce. "Wallahi tsautsayi ne, jiya da dare ina tafiya ban lura ba na faɗa lambatu." "Dan Allah ki riƙa kulawa kinji ko? Allah ya ƙara tsarewa." "Amin, na gode." Bayan mun isa Tashar, da kan shi ya shiga layi ya amso mana ticket ɗin motar da zamu hau. Bayan ya bani a hannuna ya kalle ni ya ce. "To amma Beenafah miyasa za ku tafi da Bahrain? Karatun sa fa yana samun cikas sanadin wannan uzururrukan? Sannan yanzu ba'a san odar dawowar ku ba" "Hmm! To Yaya Ashiru ya zan yi? Dole na tafi da shi domin bani da inda zan bar shi..." Kai tsaye ya ce. "Wannan karon ki bar shi a hannuna mana, sai na kai shi gida wurin su Umma.." Da sauri na girgiza kaina na ce. "A'a. Gaskiya ba zan iya ba..." Cikin nuna zallar mamaki ya ce. "Beenafah ba  ki yarda dani ba ne?" Ɗan guntun murmushi na saki sannan na girgiza kaina na ce. "Ba haka bane Yaya Ashiru.." "To idan ba haka bane miye ne? Ki bani shi, na yi miki alƙawarin kai shi islamiyya kullum tare da boko. Na kai shi na dawo da shi har ku dawo. Dan Allah ki yarda dani." "Ka yi haƙuri Yaya Ashiru, amma ba zan iya barin Bahrain ako'ina ba." Ajiyar zuciya ya sauke sannan yace. "Shikenan. Allah ya tsare ya kai ku lafiya yasa kuma a dace." "Amin. Na gode sosai." "Ina wayar hannunki?" Cirowa na yi na miƙa mishi. Nan  naga ya buɗe wayarsa ya ciro simcard ya saka ya kunna sannan ya miƙo mini ya ce. "Ɗayan MTN ɗina ne na saka muku, zan kira ki In Sha Allahu." "Na gode sosai Yaya Ashiru, na gode." Kallon Bahrain ya yi ya ce. "Bahrain! Allah ya tsare ka ji ko? Allah ya bai wa Ammie Lafiya." "Amin Yaya Ashiru, sai na dawo."   Har ya juya zai tafi, a hankali na kira sunan sa ya juyo idanuwana cike da ruwan hawaye na ce. "Na gode Yaya Ashiru.." Da murmushi a fuskar sa ya kalle ni ya ce. "Ke! Miye kuma abun kuka a nan? Ki tabbata kin ajiye wayar a kusa dake zan kiraki." "To Yayana na gode, ina gaida Umma da Ayya, da Fa'iza..." Dariya ya fara mini yana gyaɗa kai, jin nayi shiru ya sanya shi cewa. "En hen! Da Fa'iza... Da wa kuma?" Dariyar nima nayi na ce. "Da wacce ta tambayeni cewa gashina ne.. Da ma sauran da ban sani ba."

Chapter 4 of 67