Share this page
tafiya ne suka daina zuwa, amma yanzu tunda ta dawo zaki riƙa ganin su kodayaushe, to idan baki ƙwarara kanki ba haka kowa zai rainaki wanda kullum kwanan duniya kika zo sai kin yi kuka. Ki daina kuka, ko abu kika yi ba daidai ba kice kawai mutum ya yi haƙuri amma ki daina kuka. Ɗauki ki kai masa please, idan ya sake miki faɗa ki ce ya yi haƙuri..." A hankali na ɗauko na dawo parlourn na shigo ɗauke da wata sallamar a bakina, wata irin sassanyar ajiyar zuciya na sauke ganin shi tare da Aunty Labiba suna zaune. Sai da na dire trayn a gabansa sannan na kalli Aunty Labiba na ce. " Aunty Sannu da zuwa." Murmushi ta yi tana mai jinjina kai ta ce mini. "Yauwa Beenafah sannu. Ya kike? Ina fata ba wata damuwa?" Jinjina kaina na yi ina mai ƙara yin ƙasa da idona kawai ba tare da nayi magana ba. "Kin yi shiru baki ce komai ba, kuma naga idon ki yayi kamar kin yi kuka, miye ya faru?" Lemun ya ɗauka ya tsiyaya ya kalleni sannan ya komar da kallon sa ga Aunty Labiba hankalinsa kwance ya ce. "Na yi mamaki da kika ce wannan matar tawa ta yi zama gidanki amma kuma ba ta iya bada lemu ba.." "Ka yi haƙuri.." Na faɗa ina mai ƙara sadda kaina ƙasa sosai. Muryar Aunty Labiba na ji ta kira sunana. Ɗagowa na yi na kalle ta ba tare da nace komai ba, ta ce mini. "Ta shi kije abin ki kinji ko." Tashi na yi na wuce ɗakinmu direct na kwanta akan katifa ni kaɗai ina kuka har bacci ya ɗauke ni ban sani ba. Labiba kuwa, Kallon Emraan ta yi wanda ke shan lemun sa hankali kwance ta ce. "Emraan! Please idan ma kana takura yarinyar nan ne dan Allah ka daina...ko ranar da kace na kawo maka matar aure,I take that as a joke kamar yanda ka saba wani lokacin, but repeating ɗinsa da kayi yanzu na sake kiranta matarka, I don't like it,hakan kuskure ne...." Ajiye aikinda yake a wayar ya yi ya watsa idanunsa a kanta ba tare da ya ce komai ba. Ita kuma ganin yanda yake mata wani kallon mai nuni da yana buƙatar ƙarin haske yasa ta jinjina masa kanta ta ce. " Yeah, I'm serious Emraan. Idan kana faɗin haka duk da cewa wasa kake, Ziza won't be happy, and za ka sa Ita yarinyar ta riƙa takura tana shigewa gashi a duk lokacinda ta ganka,and bana so hakan ta faru, I want her to feel at home Kamar yan da su Munira suke." "OK." Kalmar da ya furta kenan tare da kauda idanunsa ya ɗauki wayarsa ya ci gaba da abin da yake. "When are you people leaving?" Ba tare da ya kalle ta ba ya ce. "I think in the next two weeks haka...because sai na je Kwara State na dawo wurin wani aiki." "Ok...Allah ya tsare ya bada sa'a." "Nadee ta matsa akan za ta zo, na ce ta bar shi har mu dawo ta ce a'a, please talk to her, Ko don karatun su Dija.." "Mun yi magana a ɗazu, na ce mata ko ni ba zan tafi ba, saboda haka ta bari sai idan Allah ya sauketa." Miƙewa ta yi tana faɗin. "Bari na tashi mu tafi, yau kasan ƙurarren lokaci ne kuma ina so muje gidan Hajiyarsu Babansu. Yau kacokam na kashe musu school.." Sai yanzu ya ɗago ya kalle ta yace. "To akan me?" "Sun matsa suna so suga Beenafah, and can gidansu Babansu kuma ana kawo lefen Lailah." Murmushi ya yi ya ce. "Lailar da kuka hana a bani ita ko? Saboda kunga bani da kuɗi..." Dariya ta fashe da ita tace. "Auntynka Hajiya Marwanatu dai ta san yanda tayi har ta hana a baka ita ni ba ruwana. Kuma ma ai muddin kaga ana so ayi aure ya zo bai faru ba to Allah ya riga ya rubuta tun can babu zanen ƙaddarar aure a tsakanin su mutum biyu ɗin." "To Allah yasa alheri, zuwa dare dai idan kin dawo zan shigo, domin gobe zan wuce." "OK, sai ka zo."                           *****     Tagwaye masu kama da juna tamkar an tsaga kara, waɗanda ake kira (Identical Twins or Monozygotic) suna fitowa ne daga ƙwai ɗaya na ƙwayar halittar mahaifiya (single Ovum) da kuma ƙwai ɗaya na ƙwayar halittar mahaifi (Single sperm). Bayan an samu ciki, a lokacin haɗin halittar ɗan Adam, idan waɗannan Eggs ɗin guda biyu suka haɗu da juna, maimakon samun ɗa ɗaya da ake yi walau ɗa namiji ko ɗiya mace kamar yanda aka saba, sai a samu ya rabu gida biyu maimakon gida ɗaya a farkon ciki, sai su zamo yara guda biyu wanda komai na su zai kasance iri ɗaya saboda sun fito daga ƙwayar halitta guda, shiyasa suke da DNA ɗaya, genetic material ɗaya, hatta placenta ma ɗaya (Uwa), hakan yasa suke matuƙar kama sosai tamkar an tsaga kara, ko kuma kamar ka samu lemu ne na fata ko kuma Kankana ka raba gida biyu, komai zai kasance iri ɗaya, shiyasa ake shan wahala wurin bambanta su idan ba shaƙiƙansu ba. Sannan su identical twins yana da matuƙar wahala a samu jinsi biyu a ciki,misali; basa zuwa a namiji da mace, 99% ɗin su, ko dai su zo a maza guda biyu ko kuma su zo a mata guda biyu masu matuƙar kama da juna. Tagwaye waɗanda ba su kama da juna kuma waɗanda ake kira (Non-identical twins or Dizygotic) su tun a farkon samun cikin, Ƙwai biyu ake samu daga ƙwayar halittar mahaifiya (Two Ovum) sannan ƙwai biyu daga ƙwayar halittar mahaifi (Two Sperm). A lokacin halittar ciki, lokaci ɗaya suke zuwa gida biyu-biyu daga kowane ɓangare, sai a samu a yi fertilizing two eggs ɗin by different sperms cell. Ta dalilin hakan ne yasa ake samun tagwaye waɗanda ba su kama da juna sam, idan ka gansu akace maka tagwaye ne zaka gardama saboda komai na su ya bambanta, domin kowa yana da DNA ɗin shi daban, Genetic material ma daban, Sannan placenta ma biyu kowa da na shi (Uwa), sannan a na iya samun su jinsi biyu, na miji da mace, ko kuma maza biyu,ko kuma mata biyu, sannan za'a iya samun su wani fari wani kuma baƙi, ko kuma dukkan su su zama baƙaƙe ko kuma dukkan su su zama farare saɓanin identical da suke zuwa da kala ɗaya, Haka; yanayin murya, magana, tafiya, girma sai ka ga sun bambanta da juna. Da wannan dalilin ne mafi yawan iyaye masu Identical twins waɗanda ke kama da juna suke kwaɗayi da burin aurawa yaran su twins ɗin masu kama da su domin ƙara ƙarfafa su da kuma ganin sai abin yafi tafiya a tsari da burgewa. Tagwayen gidan Alhaji Mansur Anka identical twins ne masu kama da juna kamar yanda su Hassana suke kama da juna. Yau, ta kasance Asabar ce wanda kowa yake gida domin hutawa kamar yanda dokar ƙasa ta tanada. Tun da suka wayi gari Mummy take kai kawo ita da 'ƴan aikin gidan domin shirye-shiryen manyan baƙinsu wato Ameer da Ammar waɗanda za su auri su Hassy idan Allah yasa sun samu fahimtar juna kamar yanda Mummy ta ci buri. Daddy ne ya zo mata da zancen,amma kuma yanzu, tayi uwa ta yi makarɓiya domin ta fi shi son abun wanda har yake matuƙar bai wa su Hassana mamaki. An gyara babban parlourn baƙin su, bayan an yi dafe-dafen abinci kuma sai da ta sake yin order aka kawo daga waje. Ko kafin ƙarfe huɗu na yamma ta cika, an gama shirya komai da komai. Ɗinki na musamman ta kawo musu ta ce su saka wanda ya yi matuƙar yi musu kyau tamkar yau ne ranar auren. Komai na su ya yi iri ɗaya hatta ƙamshin turarensu iri ɗaya. Misalin ƙarfe biyar suka fito zuwa parlourn wanda a nan suka tarar da su Ammar ɗin suna jiran su. Suna shigowa ɗaya daga ciki ya miƙe yana ta wani blushing ya kalli ɗan uwansa ya ce. "Ka san dai yanda muka yi da kai? Saboda haka ka jira babba ya fara.." Murmushi na zaunen ya yi masa tare da gyaɗa masa kansa ya ce. "To na jira Yaya. Allah ya tabbatar mana da alheri." Kallon su ya yi ya ce. "Ni ne Ameer... Ina Ameera? Ina nufin ina Yaya Babba.." Dariya Husaina ta yi tana nuna Hassana ta ce. "Ga Ameerar a nan to..." Washe baki ya yi yana gyaɗa kansa yace. "Alhamdulillah! Zo ki zauna a kusa dani... Kema ƙanwata kije ga gefen Ammar can ki zauna.." Yanzu kam na zaunen dariya yayi har ana ɗan jiyo sautinsa sannan ya ce. "Wai kai dan Allah ko'ina sai ka nuna halinka na son girma?" "Eh, ai ko'ina akwai babba, inda babu babba wurin banza ne." Zaunawa suka yi kamar abin arziki suka gaggaisa da juna bayan sun gaisa Ammar dake gefen Husaina ya ce. "Kamar yanda kika ji tun farko ɗan uwana, abokina kuma aminina ya faɗa, shi ne Hassan ni ne Husaini, wanda ake kiransa da Ameer ni kuma Ammar. Kasuwancinmu ɗaya, wurin aikinmu ɗaya, in fact Komai namu ɗaya ne hatta wurin kwananmu har yanzu ɗaya ne..." Ɗan taɓe baki Hassana ta yi ta ce. " Ni kuma abin bai wani burgeni ba, mutum biyu a duniya ɗaya, idan akace komai na su ya zama iri ɗaya abun zai yi wani iri. Ko kai baka lura da hakan ba?" Jinjina kai Ameer ya yi yana kallonta ya ce. " while! Daman ba lallai a haɗuwarka da mutum ta farat ɗaya ba kaji tsarinsa ya burgeka. Amma na san in sha Allah, with time za ki ji hakan ya yi miki." "And don't mind her, Kawai itama tana wasa ne. Ita ce Hassana ni Husaina, kamar yanda kuke, muma haka muke. Komai namu iri ɗaya ake mana tun har yanzu..." Jinjina kai ya yi ya ce. "Allah ya tabbatar mana da alheri." Nan dai suka yi ta tattaunawa wanda duk ƙarfin firar tsakanin su ne da Husaina yayin da Hassana ta kame kan kujera tana ta charting tamkar ba da ita ake zancen ba. Mummy kuwa, ta jima a jikin windown ɗakinta tana aikin kallon masu ba su tsaron da suka zo da su wato bodyguards. Ga sunan sun kame a cikin kaki sun tsaya tamkar bishiyar kwa-kwa wanda ko giyar wake kake sha baka isa ka kawo musu wargi ba. Tana cikin kallon su taji motsin shigowar su Hassana sun dawo. Waigowa ta yi cike da zumuɗi ta ce. "Ya ya?" Wani irin ɓata rai Hassana ta yi ta ce. "Mummy ba haske.... Me I don't like the guy... Ni ina zan kai wannan munin na shi da mugun baƙi kamar gawayi, ga guntanci kamar batir, haba! Da me ace akwai bambanci tsakaninsa da ɗan uwansa da zan iya haƙuri hakanan mu juya, to amma duk su ne... Ni gaskiya ba kalar namijin da nake mafarki ba ne Mumm..." Kafin ma ta ƙarasa rufe bakinta Mummy ta kai mata wata uwar jimƙa a hannu ta ja ta da ƙarfi zuwa jikin windown ta nuna mata da hannu ɗaya ta ce. " Kalli nan!" Ta nuna mata jerin gwanon jibga-jibgan motocin su cike da zafin rai ta ce. " Waɗannan ake bautawa ba soyayya ba.... Wallahi tallahi idan kika ce za ki bijire mini Hassana zan yi matuƙar baki mamaki."          ✍️  *OUM-AMEER*  ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀 *ADABI WRITER'S ASSOCIATION* *AMEENA IBRAHIM*      *OUM-AMEER* *Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671* *FREE-BOOK* *PAGE 20*   Tun ina jin ɗar-ɗar idan ina aiki akan ko zan ƙara ganin sa har na zo na saki jikina domin ban sake ganin sa ba, ko Aunty Ziza karan kanta na daina ganin ta kwana biyu. Hakan yasa na saki jikina na manta da su. Da Wata ya cika kuwa, dubu hamsin haka Haula ta damƙa mini a hannuna tare da kayayyaki, sannan ga shi duk bayan kwanaki sai sun bani dubu biyu dubu biyar haka su ce mini baƙi akayi suka raba kuɗi. Hakan yasa har yanzu ni na kasa bambancewa akan; shin su en siyasa ne ko kuma dai? Domin yawan mutanen da suke shigowa gidan har sun zarce misali, sai dai mafi yawansu ba kowa ke ƙarasowa har cikin gidan Hajiya ba sai hamshaƙai da mafi yawan dangin su masu zuwa. Ba ni ba, hatta Ammie ta yi matuƙar jin daɗin wannan sabon albashi da muka samu wanda mun ɗauki manyan buruka mun ɗora akai muna ƙara hasaso gobe mai haske. Ga shi dai bama siyen ko allura a cikin kuɗin, abinci ma kullum na dawo sai an ɗibarwa su Fakiha sannan su Yaya Hamza ma yanzu har Ammie ta saba kullum sai ta aje musu, sabulun wanki, sabulun wanka, kamar dai lokacinda nake gidan Aunty Labiba, sannan a wannan karon na har da sababbin dogayen riguna masu sauƙi a ka ɗinka hardani wanda nawa sun fi na su yawa har da hijabai da undies ma su yawa suka ce mini wai Hajiya ta bayar a ɗinka mana wanda ba ni da abin cewa sai godiya, amma kam Aunty Labiba da Iyayenta sun yi mana abinda Allah kaɗai zai iya biyan su wanda ina musu fatan Aljanna maɗaukakiya. A ranar da na kawo kuɗin ba ɓata lokaci muka yanke cewa daga zaran na rakata asibiti mun dawo ranar Monday zan je islamiyyar su Bahrain na yi register na ci gaba da zuwa. A yammacin ranar na je na siyo uniform na bai wa Ya Jafaru ya ɗinke mini. A daren ranar da ƙyar na samu bacci ya yi nasarar ɗaukeni akan ɗokin zuwa makarantar da na yi shekaru ban je ba. Babu babban abin da nake ƙara godewa Allah a kai face ci gaban da muka ƙara samu na ciwon Ammie, duk muka je asibiti sai mun samu kyakkyawan labarin cewa ciwon ta ya na ƙara sauƙaƙa, haka ma yanzu magani wanda muke siye duk wata bai fi na dubu bakwai ba. Lallai dukkan tsanani yana tare da sauƙi Alhamdulillah. Bayan mun dawo daga asibitin ma ban wani ci abincin kirki ba saboda ɗoki, ƙarfe biyu da rabi na yi na rana muka bi hanya ni da Bahrain da Ya Jafaru wanda komai zan ce ba zai daina bibiyata ba. Ammie ma har cire kunya ta yi tai masa magana amma bai ji ba. Bayan mun kusa isa makarantar na kalle shi na ce. "To sai ka koma haka ko Ya Jafaru? Ko kuma har cikin makarantar za ka rakani?" Murmushi ya yi mini tare da tallafe hannayensa akan ƙirjinsa ya ce. "Dole dai a nan zan tsaya ko bana so Beenafah. Allah ubangiji yasa kin shiga a sa'a, Allah ya baki ilmi mai amfani da kuma tarin albarka. Allah yasa yan da nake rakaki duk inda za ki je da ƙafa watarana ya nuna mini na ɗaukoki a abun hawanmu muna tafe muna farin ciki..." Ba tare da kawo komai a raina ba na ce. " Ameeeennnn! Ya Jafaru, sai na dawo." Nan ya tsaya yana ta ɗaga mini hannu har na shige cikin gate ɗin. Ina zuwa na wuce office ɗin shugaban makarantar wanda daman na saba da shi ta dalilin Bahrain. Bincike suka mini kamar yanda dokar makarantar ta tanada, na yi iya abinda zan iya wanda dole wani abin na manta sa tunda na share tsawon lokaci rabona da makarantar domin ni ko ƙur'ani ban gama saukewa ba ko da na bar zuwa amma dai bai fi hizib bakwai ba da ya rage mini, hakan yasa bayan gama mini bincike suka jefa ni a aji uku. Haka na ci gaba da tafiya, idan gari ya waye zanje na yi aikina zuwa ƙarfe biyu in dawo in wuce islamiyya tare da Bahrain. Komai ya dawo mini sabo tamkar a mafarki. Gidan su Hajiya ma na samu natsuwa da kwanciyar hankali sosai domin har na manta da wata matsala a gidan.                     **** Royal Crest University of Arts and Management (RCUAM) Sydney, New South Wales, Australia. Tun kwana uku da suka wuce Daddy ya shirya zuwan sa makarantar su Hafiz, yana sauka ƙasar direct ya wuce makarantar, department ɗinda Hafiz yake wanda ko Mummy bai sanarwa cewa zai zo ba, kawai dai ya faɗa mata cewa zai yi tafiya zuwa ƙasar waje amma bata san cewa makarantar Hafiz zai zo ba. Yana isa ya tarar da wata Mata a reception suka fara musayar kalmomi da turanci, ya ce. "Good morning ma'am. Ni ne Alhaji Mudassir Wazeer, mahaifin Hafiz Mudassir Wazeer, ɗalibin da ke karatu a wannan makarantar, na zo ne daga Nigeria." Murmushi matar ta yi tare da jinjina kai da ɗan nuna alamun mamaki akan fuskarta ta ce. " Oh! Gaskiya wannan tafiya ce mai nisa sir, sannu da zuwa, da fatan komai lafiya?" Daddy ya ce. "Not really. Na zo ne na musamman in ga academic officer ko kuma kowane lecturer daga department ɗin su, I need to confirm something personally." Jinjina kanta ta yi tana mai ɗaga wayarta ta kira wani lecturer mai suna Mr. Collins. Bayan ta gama mi shi bayani direct tasa aka kai shi office ɗinsa dake can hawa na huɗu. Bayan ya shiga sun gaisa ba ɓata lokaci ya zayyana masa buƙatarsa kamar yanda yayiwa receptionist ɗin sai Mr. Collins ɗin ya ce. "Of course sir, Hafiz yana daga cikin manyan ɗalibanmu ma su hazaƙa da muke tutiya da su, he's very brilliant in class, active in presentations. Ko a last semester he got a GPA of 4.12. Gaskiya ba shi da wata matsala." Cikin wani irin farin ciki Daddy ya ɗaga hannu sama ya ce. " Alhamdulillah!, that's my boy." Wata takarda Mr. Collins ɗin ya ɗauko ya buɗe sannan ya kira waya yana connecting computer ɗinda ke gabansa ya saka numbern Hafiz sai gashi hotonshi da bayanan shi sun bayyana har da result ɗin shi na tsawon shekara biyu, da kuma bayanan shekaru biyu da suka rage masa da zai kambala nan gaba. Sannan kuma ya faɗa masa cewa, ai sai dai ya fara wani course wanda shekara ɗaya ne da watanni sannan yanzu daga baya ya ɗora da wannan. Da sauri Daddy ya miƙa masa hannu yana murmushi ya ce. "Thank you so much Mr. Collins, ina matuƙar alfahari da ɗana, yanzu na tabbatar cewa ba kuɗin banza nake kashe masa ba. Daman rashin tura mini result ɗin ne ya ɗaga mini hankali tun farko." Daga haka ya yi sallama da shi ya fito, Yana fitowa wajen Campus ɗin ya ɗaga waya ya kira Hafiz domin ya zo su gaisa amma kuma a lokacin shi Hafiz ɗin suna da shiga wata test. Bayan ya zauna zaman jiran shi ƙarshe kuma cikin rashin sa'a suka wuce wurin wani Debate a wata ƙasar, kuma sai nan da wasu kwana uku za su dawo. Haka ya juyo ya dawo gida cike da alfahari ya cewa mummy. "Makarantar su Hafiz na je." Cikin nuna mamaki ta ce. "Makarantar su Hafiz kuma Alhaji?" Jinjina kansa ya yi ya ce. "ƙwarai, hankalina ne bai kwanta ba, shiyasa na shirya naje na bincika da kaina, kuma ki ji yaron nan Hajiya Zaliha, ashe yana can yana performing ni ne ban fahimce shi ba." "Haba! Ni ma wallahi na yi mamaki ace wai duk irin basira da ƙoƙarin Hafiz kace wai kana zarginsa..." "Eh, abun da yasa kika ga na ƙara ɗaukar zafi; Alhaji Mansur ya yi mini alƙawarin ba shi babban matsayi a kamfanin sa dake Lagos. Kinga ba zan yi sanya da hakan ba." Cike da farin cikin jin wannan kalamin Mummy ta ce. "Kaga daga ya samu wurin shikenan, ga kuma en biyu da za su auri 'ƴa' ƴan sa..." "To ai shi ne Hajiya, amma kuma kin ce mini Hassana tana neman to botsare wa wannan maganar..." Lokaci ɗaya annurin fuskarta ya ɓace ta wani girgiza kai ta ce. "Ai wallahi tallahi! Bijirewa wannan maganar tamkar ta ɗauki hannuwanta ne ta ɗora su saman tukubar tsire mai tsananin tururi da zafi." "Noo! Kar ki damu, munyi magana da ita kuma ta amince..." "To wallahi ni dama an gaggauta yin auren nan kawai, in ya so can su iyarda karatun na su tun da haka abin ya zamo.." Miƙewa ya yi yana faɗin. "Ai tunda har ta amince ba wata damuwa, gwanda a bar su su ƙarasa karatun na su zai fi.... Bari na je, yau ni zan ɗauko Princess ɗina da kaina,na yi missing ɗin ta sosai kwana biyu. (Humaida)."                         **** Ashiru kuwa, abu wasa-wasa tun su Umma na ɗaukar al'amarin kamar na wasa, kullum cikin yi masa faɗa suke suna ganin laifin sa har suka dawo rarrashi ganin kamar abin na nema ya zamo masa da cikas a cikin rayuwar sa. Daga baya ma sai ya kamu da ciwo wanda sai da aka dawo da shi gida, ana ta magani. Ayya kullum kwanan duniya ta kasa yarda da cewa wai su Beenafah mutane ne, duk wanda ya zo duban Ashiru ce masa take gamo ya yi da Aljanu suka shafe sa. Shiyasa kullum cikin yi masa hayaƙi da turaren Aljanun suke, duk inda Ayya ta ji ana bada taimakon iska sai ta je ta karɓo masa, shi kuma duk abin nan ji yake kamar zai yi kuka idan suna faɗin wai da Aljanu ya yi gamo,wanda shi yasan Sam ba haka bane kawai dai ƙaddarar sa ce tazo a haka. Da haka suka samu Allah ya taimake su ya warware, da rarrashi da komai ya koma Kano, daman kuma gashi Yayan nasa ya buɗe masa nasa shagon wata bakwai da suka wuce domin yana da farin jinin kasuwa da kuma basirar iya mu'amala da mutane wanda tunda ya koma bai dawo ba sai yanzu da ya rage saura kwana biyar auren ƙanwar sa da take bin sa Zulfa'u. Yana shigowa gidan ya tarar duk 'ƴan uwansu da danginsa sun taru ana ta hada-hada. Kallon su wata abokiyar wasar sa ta yi tana dariya ta ce. "Yayan Aljana an samu isowa?" Wata uwar harara ya maka mata tare da buga uban tsaki ya ce. "Bana son rainin wayau Sabila..." Ayya dake zaune bisa ƙofa tana duba tabarmi da kayan tarkacenda su Fa'iza suka siyo daga kasuwa ta kalle shi ta ce. "To ai ba ƙarya kika yi ba Sabila ƙyale shi, gaskiya ce baya so...Wallahi idan kika ga yarinyar nan Sabila za ki ce ita ce ta halicci kanta, saboda tsabar kyau, ko gashin kanta kaɗai abun tuhuma ne wanda hatta Nufaisa sai da ta kasa haƙuri duk yarintarta sai da abin ya bata mamaki har yasa ta tambayeta cewa duk gashin ta ne..." Fa'iza dake tsaye gefen Ayya ta ce. " Ki ji fa Ayya.. Wai bata taɓa ganin iyali mai yawa irin namu b... " Da mugun ɓacin rai ya ɗaga hannu domin kifa mata mari sai dai kuma cikin rashin sa'a ya kuskure. Ai kuwa, da gudu ta runtuma ɗakin umma ba shiri tana haki. Juyawa ya yi ransa a zafafe ba tare da ya gama gaisawa  da mutane ba ya koma ɗakinsa ya yi kwanciyar sa. Kallon Sabila Ayya tayi wacce tuni ta cika ta batse, cikin rarrashi ta ce. "Sabila... Ashiru yana da wata irin tsinanniyar zuciya, ki daina yi masa zancen yarinyar nan indai kina so a samu a shawo kansa a kanki. Domin mu idan son samunmu ne ma zuwa wata kaka mai zuwa kawai ayi a huta ku wuce can tare da shi, ke kuma sai kinsan yanda za'a yi da rarrashi da komai kisa ya manta yarinyar. Wannan bala'i da mi ya yi kama... " Jiki sanyaye Sabilar ta kalli Ayya ta ce. " Ayya kin san sha'anin Aljanu fa akwai ruɗarwa, kada ma ace ta aure shi ne... " " Kaii! Don Allah bari ma yi mini wanga batu na banza...ko ta aure shi ai bata fi ƙarfin Allah ba, wallahi tallahi da ayoyin Allah za'a halakata kuma dole ta fi ce ta ƙyaleshi." Haka dai suka yi ta firar, Ayya na ƙara ƙwararawa Sabila gwiwa akan Ashiru.             ✍️  *OUM-AMEER*  ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀 *ADABI WRITER'S ASSOCIATION* *AMEENA IBRAHIM*      *OUM-AMEER* *Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671* *FREE-BOOK* *PAGE 21*   Yau tun da na shigo babban gate na tarar da yawan motocin da ke harabar wurin sun ƙaru

Chapter 15 of 67