Share this page
abu, ko kuma ta ke shirya wani abun. Ta kan zo nan ta zauna ta yi ta rubuce-rubuce wanda Kakanku shi ne ya zamto babban abokinta kuma amininta a wannan lokacin. Domin duk abin ta kawo zai duba shi cikin hikima da basira wanda koda ya kasance abin da ta kawo bai yi ba...cikin lallami da fahimta yake cire abun daga rayuwarta...." Mun jima ko a bakin ruwan muna shan labarurruka sannan daga ƙarshe muka wuce wani babban masallaci muka yi Asr da magrib sannan muka wuce wani gidan cin abinci na musamman. Bayan mun kambala muka shiga garin inda muka yi ta yaba kyawun garin musamman da ya kasance akwai fitilu masu kyau waɗanda suka ƙarawa garin ƙwarjini da kyawun kallo. Wannan rana ta yau ta shiga cikin tarihin kowane ɗaya daga cikinmu domin mun samu ilimi, nishaɗi da kuma ƙarin sanin daraja da girman gwagwarmayar Mace. Ba dole sai ka fara da mai yawa ba, kaɗan idan Allah yasa albarka ya isheka mabuɗin rayuwa domin mai ƙarami shi ke da Babba watarana. Muna isa gidan bayan mun fito mota ya damƙe hannuna sannan naga ya kira Aunty Labiba. Cike da ladabi ta zo ta tsaya a gaban shi ta ce. "Gani Daddy..." Jinjina kansa ya yi in a calm voice ya ce. "Je ki kawo mata kayan ta....duk abin da kika san na ta ne ki haɗo mata. Wannan building ɗin na gefen dama a nan za ki kawo." "OK." Juyawa ta yi ta wuce ciki ta tattaro kayana wanda su dai su Nadeeyah kawai Sun zura ido suna kallon ikon Allah har ta kambala ta fi ce. Har ta shigo ta ajiye kayan na kasa ɗago idanuna na kalle ta. A hankali tayi mana sai da safe sannan ta sa kai ta wuce. Kayan jikin sa ya rage sannan ya shige banɗakin ya yo wanka ya yo alwala ya fito. Ganin ina nan inda nake na kasa yin wata huɓɓasa ya kalle ni yace. "Ki je kiyi wanka...Akwai gajiya sosai." Cire kayan jikina na yi na ɗaura towel, ba tare da kawo komai a raina ba na wuce kai tsaye na yo wankan sannan na zo nayi sallar Isha da muka ɗauko nauyin ta. Bayan na kambala na buɗe kayana inda nan na tarar har da sabbin turarukan jiki da wasu mata suka kawo mana jiya ta haɗa ta kawo min. Kayan nawa na shiga dubawa ina neman kayan baccin da zan saka. Ƙirjina ne ya buga ganin irin lalataccin kayan da ya sako min. Idan ban manta ba shi ne wanda ya zaɓomin komai na sakawa ya Shirya mini box ɗina, Kuma tun da muka zo ni ban nemi kayan bacci ba domin a gajiye nake kwantawa kuma ta wani fannin ina jin kunya sosai wanda har bana Iya sake wa da yawa....Lallai Ya Mohaan nan sai yau na ƙara tabbatarwa da cewa ɗan garari ne! to yanzu sabi da Allah muda muka zo ziyara mi zan yi da wannan kayan? Muryarshi na ji a bayana yana faɗin. "Har yanzu ba ki gama shiryawa ba ne Bibi?" Waigowa na yi tare da yin narai-narai da ido a darare na ce. "To ai ni banga kayan sakawa a nan ba.." Takowa ya yi zuwa gaban kayan ya tsaya ya ɗauko min wata ficiciyar riga mai hannun vex wadda bata da mara ba da tsirara ya ce. "Ga wannan.." Ai tuni na ƙarasa ruɗewa na ce. "Wannan ɗin fa kalli yanda take..." Ido a ƙanƙance ya ce. "Na gani.." "Dayaa ba fa gidanmu ba ne.." Rigar ya ƙara miƙa hannu ya ɗauko kai tsaye ya zura ta a wuyana yana faɗin. "Waya ya faɗa miki ba gidanmu ba ne Bibi? Ba ki ga wannan building ɗin mu kaɗai ne a cikin sa ba kacokam. Nan ɗin shima gidanmu ne kada ki sake cewa ba gidanmu ba ne..." Yana gama maganar ya zare towel ɗin nawa ya barni daga ni sai wannan ficiciyar rigar wacce ta sa na ji duk na koma wata iri daban. Ni fa gabaɗaya ma wallahy a rikice nake da yanayin sa na yau domin nasan ban isa na hana masa kaina a irin yanda naga wutar fitina na wani irin tururi a ƙwayar idanunsa ba. "Bibi..." Ya yi whispering sunana cikin wani irin yanayin da sai da na ji tsikar jikina ta ɗaga. "Shin ba ki ji ko kaɗan cewa kin yi kewata ba? Na kasa bacci, na kasa yin wani kataɓus...kewar ki kawai ke ɗawainiya dani Bibi...a yanzu bana jin ina iya ɗaukar kwana biyu ba tare da kina gefena ba idan zan yi bacci." Cikin wani irin yanayi mai wuyar fassarawa ya shiga birkitani tare da haɗe bakinmu wuri ɗaya ya shiga aika min da zafafan saƙunan da suka gaskata maganar sa da ya gama ta cewar yana matuƙar jin kewata. Jin ƙafafunmu sun kasa riƙe nauyinmu muna neman faɗuwa yasa ya jani muka faɗa kan gadon muka Lula wata duniyar da muka kwana biyu bamu leƙa ba, musamman shi da ya ji kamar yau ne ya fara sani na. Duk yanda na so in nuna juriya a wannan karon na kasa, domin ba ƙaramar wuya na sha ba wacce ta saka ni dole na fashe masa da kuka. Bayan ya gama da ƙyar ya yi nasarar rungumeni a ƙirjinsa da rarrashi da komai ya samu bacci ya kwasheni sannan ya samu ya rarrafa yaje yayi wanka. Da wani irin mugun zazzaɓi na farka wanda a yan da nake ji ko kaina ba zan iya ɗagawa ba. Hakan yasa na fashe masa da kuka wanda ba shiri ya bar abin da yake yayo kai na. Cike da takaici na shiga tambayar kaina wannan wane irin ƙalafuci ne? A garin mutane na wuni ina zirga-zirga amma ya kasa ɗaga mini ƙafa. Koya a jiya ya tabbatar cewa lafiyata ƙalau, to amma yau ta ya ya zan iya fuskantarsu bayan na kwana tare da shi da sunan rashin lafiya. "Bibi..." Cikin rashin kuzari na ture hannun sa cikin kukan na ce. "Ni wallahy ka ƙyaleni..."           ✍️  *OUM-AMEER*  ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀 *ADABI WRITER'S ASSOCIATION* *AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER* *Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671* *FREE-BOOK* *PAGE 45* Murmushi kawai ya yi tare da amfani da ƙarfinsa ya riƙe hannayena sannan ya janyoni jikin sa yana mai bani warm hug. Laɓɓansa ya kai saitin kunnena cikin sigar lallashi ya shiga furtamin wasu kalamai masu daɗi da taushin da ban san lokacin da na haɗiye sauran kuka na ba na kwanta laƙwas a jikin sa ina saurarensa har ya yi nasarar lallameni na manta da laifinda ya mini wanda har yasa bana jin haushinsa sai dai yanayin jikina ina jin ba daɗi akan zazzaɓin da nake ji. Miƙewa ya yi a hakanli ya ɗagoni muka wuce toilet ya barni nan nayi wanka na gasa jikina da kyau sannan na yi alwala na fito. Ina sallah na ji ana ƙwanƙwasa babbar ƙofar shigowa gidan gabaɗaya. Jallabiya ya zura ya tashi ya fita ba jimawa sai gashi ya dawo hannayensa ɗauke da abincin kari. Bayan na kambala sallar ya miƙomin alƙurni na karɓa na buɗe na karanta cikakkun shafuka biyu sannan na rufe na je na ajiye masa. Sai da na gama shiryawa cikin doguwar riga da gyalenta na saka hula bayan na gama ɗaure gashin kaina, sannan na tsaya jikin mirror na ƙura ido ina kallon sa. Wannan mijin nawa a yanzu ya ƙware a tafiya dani, shi ne zai takalo fushina da kansa kuma daga ƙarshe shi ne wanda zai rarrasheni yasa na manta da duk wani ɓacin ran da yake zuciyata. Son sa nake...tabbas ina son sa sosai wanda duk abin da nake ji daga zaran na gansa nutsuwata ma nemanta nake na rasa. Na jima ina kallon sa wanda shi sam bai ma lura dani ba akan yanda ya duƙufa yana aikin da na san baya rasa nasaba da kamfaninsa na Golden pathways Wanda kullum cikin aiki yake ba dare ba rana. Da murmushina da kullewar idanunsa cikin nawa lokaci ɗaya ya kasance. Ai ba shiri na saukar da kaina a ƙasa cike da kunya ina neman yanda zan kare kaina idan ma ya tuhumeni da laifin kallonsa ina murmushi. Kamar kuwa na sani. Rufe system ɗin ya yi ya ture duk wasu kayan aikinda suke gabansa ya taso ya zo gabana ya tsaya tare da riƙa gefen veil ɗina yana leƙa fuskata yana murmushi ya ce. "Masha Allah...daga ganin wannan kallon da kike min kina murmushi na san cewa an yafe min laifin da na yi ko Bibina?" Shiru nayi tare ƙara saukarda idona ƙasa sosai ina wasa da yatsun hannuna lokaci ɗaya ina jin wani abu yana mini yawo a ƙirjina. "Mu je muci abinci?" Ya ambata cikin sigar tambaya. Jinjina masa kaina na yi sannan na taka muka je muka zauna. Kaɗan na ci abincin domin har yanzu bana jin daɗi ina jin zazzaɓi. Kamar yasan abin da nake tunani domin magani na ga ya ɗauko ya bani, karɓa na yi na sha sannan na kwanta a jikin sa na lumshe idanuna kamar mai bacci. Bayan ya kambala cin abincin ya tattara kayan ya kira Jadda sai gashi ta turo Taimiyyah ta tsaya can daga parlour ya bata kayan sannan ya rufe ƙofar ya dawo. Wayata ya ɗauko ya miƙomin yana faɗin na kira Ammie domin ta kira bana kusa. Ina karɓa na kirata tare da yi mata sallama sannan na gaisheta. Duk yanda na yi iya yina wurin ganin na sai ta kaina sai da Ammie ta tambayeni cewa mi yake damuna. Murmushi na yi kai tsaye na ce. "Ammie yau na tashi bana jin daɗi ne, amma dai na sha magani, jikin ma ya sauka." Cikin nuna kulawa daga can ɓangarenta ta ce. "Kin tabbata?" "In Sha Allahu Ammie. Ina su Mummy Sameera? Na ji duk wurin ya cika da surutu, ina kike haka?" "Wallahy kin ganmu nan ana ta shiri wai Kebbi zamu je Huda ta haihu..." Murmushi na yi na ce. "Allah sarki! Aunty Huda ta gidan Mama Asma'u ko?" "Ita fa. Ta haihu ta samu ɗan ta namiji kwana biyar da suka wuce." "Allah sarki! Allah ya raya ya bata lafiya. Duk da su Mama da su Mummy Sameera za ku je?" "A a. Kin san haihuwa ta uku ce yanzu ta yi, to shi ne Abbun ku yace ta shirya tun da haihuwa ta uku ce ba wani abu ba ne don taje ai za ta ji daɗi idan taga mahaifiyarta a kusa da ita. Shi ne fa ta rantse ta ce ba inda za ta je ai tun da ni gani yanzu ina nan ni ce uwar ta, saboda haka sai dai in je ita ba za ta je ba..." Cikin jin farin cikin cewa yanzu Ammie na tana zaune cikin jin daɗi da walwala ba kamar can baya ba yasa na yi murmushin da har tana iya jiyo sautina don in ƙara tabbatarwa da kunnena na ce. " Lafiya ƙalau kike zaune ko Ammie na?" Jinjina kai ta yi tamkar ina a gabanta ta ce. "Alhamdulillah Beenafah! Lafiya ƙalau nake zaune da Dr., matarsa, yaransa da kuma danginsa. Kowa lafiya ƙalau muke zaune dasu. Hajiya Asma'u ta mutuntani wanda babu abin da zance sai dai Allah ya ƙara mana hak'uri." "Amin amin yah Allah Ammie." "Kunyi magana da Aysha kuwa?" Girgiza kaina na yi na ce. "A'a. Mun kwana biyu bamu gaisa ba gaskiya.." "To ki kira ta ki ƙara yi mata ya jikin Daddyn ku domin jikin nasa har yanxu ta ce sai a hankali." "Tau ya yi Ammie In sha Allahu zan kira ta. Allah ya tsare ya kaiku lafiya....Ammie Bahrain fa? Kwana biyu ya daina cewa a bashi mu gaisa" Sautin dariyarta na ji tana faɗin. "Ai yanzu ɗana ya fara zama babban yaro. Yana gidan Hajiya Asma'u, tun shekaranjiya da Hashi ya zo su ka tafi tare. Hamza ne kaɗai a gidan nan." Jinjina kai na nayi na ce. "Hmmm! To ya yi Ammie, ai bari na kira mama Asma'un mu gaisa daga nan in ce ta bani shi in ji muryar babban yaro. Ina gaishe da Ya Hamza." "Tau ya yi, In Sha Allahu za su ji, ki gaishe da Su Jadda da su Labiba." "In Sha Allahu za su ji, ai jibi ma zamu koma." "Ok! Allah ya nuna mana." "Amin. Sai an jima." Bayan na kashe na kamo numbern Mama Asma'u na gaishe ta sannan muka gaisa da su Bahrain, sannan na kira Mummy Sameera itama wacce in dai gidan lecture ce ta zaman aure da kula da miji to Mummy Sameera ba ta da tsara. Yanzu ma wannan kiran da na yi mata domin mu gaisa sai da ta tutseni da sabon karatun da ni dai kawai sauraren ta nake,domin ko wancan allon ban gama biye wa ba ballantana in wanke a yi min wani sabon karatun. Inda ma Allah ya taimakeni shi ne, Dayaa gabaɗaya aikinsa yake hankalinsa baya kai na ballantana ya saka ni a gaba da tambayoyi. Bayan mun kambala daga ƙarshe na kira Aunty Aysha muka gaisa na yi mata ya jikin Daddyn kamar yan da Ammie ta ce domin wallahy darajar ta yaci da Aunty Aysha da babu abin da zai sa wai ni Beenafah na kira da sunan jin labarin lafiyar Daddy. Allah ya tsari gatari na da saran shuka wallahy. Allah ma yasa ya mutu ni ina ruwana. Mugu azzalumi wanda bai ƙware a komai ba sai zalunci. "Subhanallah! Bibi..miye kuma aka miki na kuka?" "Ba komai." Kalmomin da na furta masa kenan, a raina kuma tambayar kaina nake cewa wai ashe kuka nake tunawa da irin zaluncin da Daddy ya yi a gare mu. Wata irin tambayar sa ce ta nemi hargitse tunani jin yan da ta jefo ta bagatatan da cewa. "Miye abin da Mummy Sameera take faɗa miki naga kin nutsu sai murmushi kike?" A ruɗe na ɗago na kallesa na ce. "Na'am...Uhm! Ba fa komai. Kawai nasiha ce ta ke ƙara mini..." "Nasiha Bibi? To akan me kenan?" Hmm! Wai tashin service. To ni ko Karen hauka ya ci je ni an faɗa masa zan iya faɗin karatun da ta gama biya mini a yanzu? Ba zai ma faru ba. Mutumin nan ya iya bin diddigi kamar wani ɗan jarida wallahy. "Bibi..." Cike da neman agajin ya ƙyaleni da wannan biyar diddigin nasa na rausayar da kaina gefe tare da karyar da murya na ce. "eyyah ba fa komai....ni dai wallahy bacci ma nake ji." Jinjina kai ya yi yana murmushi ya juya ya koma kawai yaci gaba da abinda yake. Ina ganin ya tafi na tashi naje na kwanta kawai na ci gaba da bacci wanda ban farka ba sai kusan ƙarfe huɗu na yamma sannan na tashi na yi sallar Asr sai ga shi ya dawo shi ma daga masallaci. Abinci na fara ci sannan muka shirya muka fita Zuwa wurin su Jadda. Ina shiga bayan mun gaisa da Jadda na wani haɗe rai na ganin irin kallon da su Suwara ke mini wanda naga alamar idan na yi musu saku-saku za su kawo mini wargi. Haka muka zauna da su wanda hatta Hairi sai da ta shiga taitayinta dani, bayan ya dawo masallaci tare da su Ya Emraan ba kunya ya kirani muka koma ɓangarenmu muka ci abincin dare sannan muka fito muka hau matattakala zuwa Rooftop ɗin su Jadda. Ban san lokacin da wani kyakkyawan murmushi ya suɓuce min ba domin wurin ba ƙaramin burgeni ya yi ba. An ƙawata shi da shimfiɗu, kujeru da fitilu na alfarma. Wato ashe shiyasa suke ruffing irin wannan domin su riƙa hawo wa suna nishaɗi da dare. "Wurin ya yi miki kyau ko?" "Sosai wallahy, wurin ya burge." Na faɗa ina mai wucewa da sauri na shiga tsakiyar su Taimiyyah da suka zauna akan wata kewayayyar shimfiɗa da aka saka mata wata fitila a tsakiya gwanin burgewa. Baki na tsalma a firar da suke muka ci gaba da firar muna dariya, daman dai babu abin da yayi min wani laifin da nake fushi, ni na yi fushi don kaina yanzu kuma na dawo na sake kamar bani ba. Wuri Ya Mohaa ya samu gefen Jaddi ya zauna akan kujera suna fuskantar juna ya gaishe sa sannan ya gaishe da Jadda da su Uncle Mu'aƙƙib. "Miyasa kuke rufin gidajen ku a nan da wannan sigar? Koda yake yanzu ma ga dalili ɗaya na gani tunda gamu a sama muna farin ciki..." Miƙewa Suwara ta yi ta taje ta tsaya wurin Ya Emraan wanda shi ne ya yi tambayar. Yanda ya saka hannayensa ya riƙe zagayayyen ƙarfen da ya zamto garkuwa ga filin wurin ya tsaya yana kallon faɗin birnin itama haka ta yi sannan ta zuba ido tana kallon shi fuskar nan cike da annuri ta ce. "Dalilin da yasa muke ruffing irin wannan shi ne; wannan ƙasar tamu ta kasance tana da zafi sosai saboda yashi da muke da shi da dai sauran dalilai..hakan yasa muke ginin ƙasa sannan mu rufe da ita ko muyi yaɓe ko kuma mu shafe da siminti kamar dai yanda Kaga namu yake, domin mu samu sauƙin zafi." Jinjina kansa ya yi tare da sakar mata murmushi kamar yanda take masa ya ce. " Uhmm! Da kyau. Gaskiya tsarin gidajen ku akwai burgewa sosai." " Aunty Suwara Ya Emraan fa yana da mata har da yaro. Naga kin zaƙe sosai..." Cewar Hairi wacce tun bayan da Suwara ta bar wurin ta je wurin Ya Emraan kunnen, idonta da baki da hanci ke kansu. Waigowa ta yi cike da alfahari ta kalleta sai kuma ta waiga gun Ya Emraan ɗin ta kalle shi tun daga sama har ƙasa ta yi wani murmushin gefen baki sannan ta ce. " Na sani. Amma ai ba haramun ba ne. Ba ki ji ko a cikin Alƙur'an mai girma Allah maɗaukakin sarki da biyu ya ce a fara ba, sannan uku, sannan huɗu. Sai kuma daga ƙarshe yace sai idan kunji tsoron cewa ba za ku iya adalci ba to sai ku zauna da guda ɗaya jallin jal." Sosai Ya Mohaa ya mayar da hankalinsa a kansu yana wani irin murmushi a ransa yana ayyana cewa idan har hakan ya kasance gaskiya to haƙiƙa sai ya fi kowa farin ciki. Domin zumuncinsu tabbas zai ƙara ƙarfi. Dariya muka fashe da ita cike da nishaɗi Hairi ta sake cewa. " Idan kuwa haka ne, to lallai ki bini sau da ƙafa ki mini biyayya domin nice nan babbar Aminiyar sa, ƙawarsa mai bashi shawara." "Masha Allahu! Ku ce sabon zumunci dai zai sake ƙulluwa a tsakaninmu..." Gabaɗaya lokaci ɗaya kallonmu ya koma gun Ya Mohaa jin irin kalaman da Jadda ta gama faɗa a yanxu. Ganin yan da kowa ya tsura ido yana kallonsa Har da Ya Emraan ɗin wanda saƙon idanuwansa kaɗai sun gama tabbatar masa da gamsar da shi cewa shima ɗin yana ƙaunar Suwara da gaske. Hannayensa ya ɗaga sama yana murmushi ya girgiza kansa ya ce. "Ban isa na ce a'a ba ai. If you do love her...i will be more happier than anyone here..Allah ya tabbatar mana da alherinsa." Cike da wani irin jin alfaharin kalaman yayansa ya yi murmushi mai kyau ya kalle sa da su Jadda ya ce. "Thank you for understanding..." Suwara kuwa, tafin hannayenta ta saka ta rufe fuskarta wai ita taji kunya, daga nan ta gangara ta sauka ta wuce ɗaki. Fira muka ci gaba da yi kowa ya baje ra'ayin zuciyar sa muna ta nishaɗi tamkar waɗanda suka ɗauki  shekaru da sanin juna. Ba ma wanda yake ƙara bani mamaki kamar Ya Mohaa, na lura da shi yana da matuƙar sakin jiki a cikin ahlinsa tamkar ba wani mai babban matsayi wanda ake girmamawa ba. "Taimiyyah Please ki kawo mana abin taɓa wa.." Cewar Jadda tana mai kallon gefen da muke zaune. Kafin Taimiyyah ta miƙe har Hairiyyah ta miƙe tsaye tana dariya ta ce. "Jadda ni ce wacce zan kawo...And ko yayi muku daɗi ko bai yi ba, sai kun sha domin ni ce nan wacce zan haɗa komai da hannuna, daman ai na fara koya ko Aunty Labiba?" Dariya muka fashe da ita sannan Aunty Labiba ta jinjina kanta ta ce. "Na san kin fara koya, but the true is,hannunki bai bi ba..." Ya Mohaa na dariya ya ɗaga hannu sama ya ce. "I will be the first one to taste everything...kuma ko bai yi daɗi ba, since favorite ce ta dafa, to dole kowa ya ci ya sha...Har Jaddi ban ɗauke masa ba." Dariya muka yi wanda hakan ba ƙaramin ƙara hura mata kai ya yi ba ta gangara da sauri zuwa ƙasa. Kitchen ɗin ta fara zuwa ta dudduba wanda ashe bata sani ba, dare da rana cikin aiki suke, musamman shayi da duk wani abu kayan ruwa da fulawa baya yanke musu a kitchen ɗin. Wata ƙila don gidan yana gidan mutane ne yasa haka oho. Bayan ta ɗauko tray da taimakon wata daga cikin masu aikin kitchen ta jera Coffee, tsire da kayan snacks ta ɗauka tana dariya ta fito ta nufi rooftop ɗin. Tana tafe tana lissafin yan da za ta shirga musu cewa ita ta ce ita haɗa komai ba kawai ta ji ta yi karo da mutum wanda da ace bai yi saurin saka zafin nama ya riƙe tray ɗin ba, tabbas da babu abin da zai hana masa tarwatsewa a jikinsa. Cike da tashin hankali ta rufe bakinta da hannayenta tana zaro ido ta bar shi da tray a hannu tana faɗin. "pp...Please I'm sorry...I'm sorry please!" Tag ɗin shi da ya sance ya faɗo ƙasa ne ta yi saurin duƙawa ta ɗauko tare da glancing ta kalla rubutamin da ke jiki 'IG SUHAIB M. SAMI'. Miƙa masa ta yi still da damuwar abin da ya faru ta ce. "Please I'm sorry!" A hankali taga motsawar kyawawan lips ɗinsa yana faɗin. "And ta ya ya kike so na karɓa bayan kin barni da kayan ki a hannuna??" Jin Hausa raɗau a bakin sa ya ƙara ruɗata ba shiri ta miƙa hannun ta karɓa Tray ɗin sannan shi kuma ya karɓi Tag ɗinsa ba tare da ya ƙara kallon inda take ba ya haura ya wuce sama. Jikin gini ta faɗa yaraf! tana mai jin yanda zuciyarta ke wani irin tsalle kamar za ta shiɗe tsabar yan da ta gigice wanda ta tabbatar da ace wannan trayn ya zube akan wannan haɗaɗɗen Kakin nasa babu abin da zai hana sa kifa mata mari. Bayan ta ɗauki tsawon lokaci a haka, daga ƙarshe ta lumshe idanun ta tare da sauke wata irin sassanyar ajiyar zuciya ta yi wani murmushi tana mai daidaita nutsuwarta sannan ta kama hanya ta haura sama. Tana hawa idonta ya sauka a kansa inda yake zaune kusa da Ya Mohaa da Emraan suna magana suna murmushi. Ajiyewa ta yi tare da samun wuri ta zauna tamkar wacce ruwa ya cinye. Lokaci zuwa lokaci take ɗaga ido tana kallonsa sannan daga ƙarshe ta kalli Taimiyya ta ce. "Wane ne wannan naga ya shigo yanzu?" Waigawa ta yi ta kalli Suhaib ɗin sannan ta dawo da Kallonta gare ta tana jinjina kai ta ce. "Ahiy wai? Nan gidan yake shima, yaron Uncle Mu'aƙƙib ne. Yana wurin aiki ne shiyasa kika ga tun da kuka zo baku gan shi ba. Akwai Raihab da, su su Zayn...duk a wannan familyn suke wanda duk suna wurin aikin su, but da sannu In Sha Allahu watarana za ku san su gabaɗaya." Kiran da Ya Mohaa ya yi mata ne yasa ta miƙe jiki ba ƙwari ta matsa inda suke zaune. " Favorite...wannan Suhaib kenan. Ke kaɗai ce ba ki gaisa da shi ba." Kallonta ya yi a tsanake sannan ya jinjina kansa yana murmushi ya ce. " Akwai dai kam nutsuwa da hankali." Bata san lokacin da ta sake waro ido ta kalle shi ba, jin wata iriyar magana mai harshen damo da ya yi. Ji ta yi ranta ya ɓaci da shi hakan yasa bata san lokacin da hawaye suka wanke mata fuska ba. A ruɗe Ya Mohaa ya janyo ta yana faɗin. " Lafiya? Miye ya faru?" Tambayar da kusan kowa ya jefa mata kenan lokaci ɗaya wanda hakan shi ne abin da ya ƙara tunzura ta ta fara kuka har da sauti. Cikin wata irin muryar sangarta wacce ta ƙware da ita ta ce. "Zan hauro ne fa ban lura da shi ba na kusa kifa trayn da na ɗauko a

Chapter 43 of 67