Share this page
Kowa tamkar zai fasa mini dodon kunnen daren jiya. Ɗazu ma Su Aunty Ziza sun kira ina wurin wanka." "Wanne suna ne kike so a raɗa musu Bibi?" Dariya na yi na ce. "Suna kam, ai ba zai wuce Dr. Bello da Alhaji Attahiru ba..." Cikin tsantsar farin ciki baki har kunne ya ce. "Allah Bibi?" "Sosai ma. Sai mu riƙa cewa, Arhaam and Aryaan..." Jinjina kai ya yi yana ta wani irin murmushi ya ce. "Wannan ɗin ma sound very sweet. Kina da tunani mai kyau a koda yaushe. Shiyasa bana taɓa dana sanin neman shawararki, domin duk abin da za ki faɗa mini mai kyau ne." "Allah ya raya su ya shirya mana da su, yasa duniyar musulunci ta yi alfahari da su, ya bamu ikon kula da tarbiyyarsu da duk wani nauyinsu." "amin.." "Ina miki gaisuwar Daddy. Allah ya ji ƙansa da rahama ya gafarta masa." "Amin. Thank you so much...Ahm! Wai nikam a ina kake kwana?" Wata dariyar ya yi sannan ya ce. "Hotel mana." Cikin nuna rashin jin daɗi na ce. "Hotel fa? Miyasa ba za ka riƙa kwana a nan gidan ba?" Yanzu kam dariya ya ke sosai yana jinjina kansa ba tare da ya ɗauke idonsa a kaina ba. Ɓata fuska na yi na ce. "Ni dai bana so! Ka wai a ba wa mutum amsar tambaya amma sai a riƙa masa dariya. Ni gaskiya bana so." "To Bibi abun ne ya bani dariya. Ta ya zan iya kwana a nan? Ai ko ke kina mini faɗa kice mijin ki bai da tunani..." "To ai ni hotel ɗin ne ya mini wani iri." "Uhm! Da gaske? To ki bari duk ranar da Allah ya nuna mana zamu koma sai na kaiki inda nake kwana ki gani." Sallamar Bahrain muka ji, bayan na yi masa izinin shigowa, ya shigo tare da Ya Hamza. Abinci suka girke a gaban sa sannan suka gaishe da shi cike da mutuntawa. Kallon Ya Hamza na yi ina dariya na ce. " Ga Ya Hamza nan da na ce maka yaƙi siyo mini Fara a ranar." "Wallahy ranka ya daɗe ba haka akayi ba..." "Ba wani nan...ai cewa kayi na faɗawa duk wanda zan faɗawa ba za ka siyo ba..." Dariya Bahrain ya yi ya ce. "Aunty Beena ki faɗi gaskiya, a ranar fa dare ya yi sosai." Dariya muka yi dukkanmu sannan daga ƙarshe Ya Mohaa ya ce. "Duk abin da take so komai dare a tabbatar an kawo mata shi, wannan doka ta ce daga yau ɗin nan." "An gama ranka ya daɗe." Bayan sun fita na kalle shi ina dariya na ce. "Thank you." "Kina farin ciki sosai a gidan nan..na lura da hakan." "Uhm! Kuma ina farin ciki a gidan ku shima idan na je ai..." "To ni kinji na ce wani abun ne?" Dariya na yi ina girgiza kai na nace. "Ni ma ai ba wani abu na ce ba. Ka ci abinci ka ji. Na san cewa baka ci abinci ba." Murmushi kawai yayi sannan ya ɗan tsakuri abincin kaɗan yaci. Bayan ya kambala yake faɗamini cewa Jadda za ta zo ita da Taimiyyah, Mummy Razia da Zayn. Ana gab kiran sallahr magariba ya fice sannan Su Mama su shigo. ******** Sai da aka ƙara sati ya zama sati biyu kafin suna, domin na samu na ƙara warwarewa sannan kuma ma su zuwa daga nesa suma su samu lokaci isasshshe na zuwa. A hankali gidan ya fara ɗaukar mutane baƙi, wanda Su Aunty Labiba da su Aunty Husaina su ne na kusa da suka fara isowa ana saura kwana uku. Sai su Jadda da kuma Ammah da iyalanta gabaɗaya wanda har Abiyh ba'a bari ba. Ammie ta yi farin ciki ganin yanda gidanta ya cika da en uwanta da abokan arziki. Babban abun farin ciki ma har da iyayenta wanda kowa kira take tana faɗin ya zo ya ga danginta da iyayenta. Hidima aka shiga shiryawa ta musamman wacce mutane da dama basu taɓa gani ko jin labarin irinta ba. Dayaa ya saka ni a farin ciki, ya saka ni a matsayin da na ji cewa tabbas ni ɗin na cancanta a kirani da Matar Engineer Muhammad Attahiru Araam, yasa na ji ni ɗin Uwa ce wacce ta haifi Mazajen gaske guda biyu. Dangina, iyayena, da abokan arziki sun faranta rai na wanda sai da na zubar da ƙwalla na yi kirari ga Ubangiji akan wannan ni'imarda ya mini. A daren suna, ina zaune a ɗaki tare da su Aunty Labiba tana wanke mini lallena wanda sai yanzu aka samu ya yi sai ga Farisa ta zo tace wai ana kirana a waje. Kallonta na yi na ce. "Waye ne yake kirana Farisa?" "Ya Jafaru ne, ya ce wai yana so ya miki barka, gobe tun asuba zai koma makaranta." Wani irin ɓata rai na yi na ce. "Yana ina?" "Yana waje wurin mota." "Ina Fakiha?" "Ya Fakiha kamar tana gidan Mama Asma'u ta bi Aunty Huda ba jimawa." Ajiyar zuciya na sauke sannan na kalli Hairi na ce. "Muje ki rakani waje." A tare muka fito, baiwar Allah ma tana fama da ɗan laulayinta amma haka na ce sai ta rakani. A parlour na togace na tsaya ganin yanda Su Ammah suka cika parlourn an haɗe kowa da kowa sai fira ake ana ta nishaɗi bakin Ammie har kunne. Kallon Hairiyyah na yi na ce. "Hairi. Kin san miyasa na yanke hukunci cewa a nan zan haihu wurin Ammie?" Girgiza kanta ta yi alamar a'a. Jinjina kaina na yi ina share guntun Hawayena na ce. "Lokacin da ta haifeni, ta haifi Bahrain, ta haifi Sajjad. Babu ɗan uwanta da ta taɓa gani wurin tayata murna. Amma a yau, sanadiyyar su Arhaam...ga shi kowa na ta ya zo tayata murna. Sannan na yi hakan ne domin darajarta ta ƙara ɗaguwa a wurin Mijinta da dangin Mijinta. Kin san sharrin shaiɗan da zuciya, bana so a samu wani watarana ya goranta mata cewa ba ta da dangi, a asibitin mahaukata ya haɗu da ita wurin jinya ya tausaya mata ya aureta...kinga ganin iyayenta da danginta shi ya tabbatar musu da cewa ita ma ɗin mutum ce er dangi kamar kowa. Sai ga shi kuma hasashe na ya tafi a daidai, domin Ammie tana cikin farin ciki sosai." "Wallahy haka ne Mummy! Ammie tana cikin farin ciki domin ko jiya ni dai ban san sun yi bacci ba, a haka da kika gansu suna fira suna dariya, a haka suka kwana, Annie ma ta kasa matsawa daga inda take." Shigowar Raihab da Bahrain ce ta katse mana firar. Ina dariya na kallesa na ce. " Best friend wai daman ka zo?" Dariya ya yi ya ce. " Na zo mana ƙawata. Ina twins ɗina?" "Suna ciki. Bahrain ka shiga da shi, wurin su Sis Noura,duk su Aunty Aysha suna ciki." Na furta ina mai ɗaga ƙafata domin zuwa yin abinda ya fito dani. Ji na yi ya ce. "Ina za ki je haka, na ga ƙarfe goma har da rabi na dare..." "Mts! Wallahy wai wani ne yake so ya mini barka..." Hannuna ya ja yana faɗin. "Dare ya yi gaskiya, ki ce ya miki a waya. Ko kuma ya dawo gobe. Muje ciki....idan Abiyh ya ganki waje yanzu zai miki faɗa." Ciki muka koma kamar yanda ya zaɓa, koda muka shiga duk Aunty Ziza sun watse sun tafi wurin kwana, ɗakin ya rage daga Sis Noura, Aunty Husaina da kuma Suwara. Aunty Husaina ma tana ganin mun shigo ta tashi ta mana sai da safe. Wayata Suwara ta shiga miƙa mini tana faɗin. "Ya Hammodi fa sai kira yake tun ɗazu." Murmushi na yi na ce. "Ai wallahy na san ba zai taɓa iya wa ba..." Dariya Sis Noura ta yi tana faɗin. "Ya akayi ne?" "ɗazu ne da ya kirani around Magrib ya ce mini ba zai ƙara kira ba sai gobe, domin yaga ina ji da baƙi. Shi ne wai yanzu mai miss calls har bakwai." Zaunawa muka yi ya ɗauki Aryaan a hannunsa yana ta murmushi yana musu addu'a. Bayan ya gama muka ɓude sabuwar chapter fira yana faɗin wai Qatar na can yana jiran tsammanin zuwana. Idan na je sai na musu wata shida. Muna nan sai ga su Aunty Labiba ita da Aunty Hassana wacce ke ɗaɗɗake da cikin itama da Aunty Ziza muka ci gaba da fira har misalin ƙarfe ɗaya sannan kowa ya watse ya rage ɗakin daga ni sai Aunty Labiba da kuma Sis Noura. Kayana da zan yi amfani da su gobe ni da Su Aryaan suka shirya mini tsab, sannan aka rurrufe sauran Bahrain da Ya Hamza suka kwashe suka kai Part ɗin Abbu aka rufe. ****** Jafaru kuwa, Tun daga Zaria ya baro jiki na rawa ya biyo su Mama kamar da gaske yace zai zo ya mata barka daga nan kuma ya ga iyayen Ammie ya mata barka da arziki. Maimakon ya biyo ayarin su Mama ya shigo gidan ya yi barkar sai bai yi ba. Domin gari ya shige ya faɗa musu cewa wai shi kunya yake ji. Sai dai da dare idan duhu ya sauka mutane sun rage tukunna zai shigo. To koda daren ya yi yazo da robar lemun shi a aljihu wacce ya baɗeta da maganin tun a bakin shagon da ya siya. Bayan ya shigo ya tarar mutane ne ta ko'ina, sannan daman babansu ya koma tunda yamma, Mamansu kuma koda ya kira ta ta ce mishi tana gidan Mummy Sameera wurin aiki sai gobe da safe za ta dawo. To Ammien ma daƙyar ya samu ganinta koshi ko tsayuwar minti ɗaya ba ta yi da shi ba aka janye ta. Haka ya dawo waje ya kira Hamza yace ya zo ya shigar da shi gidan. Sai kuma akayi rashin sa'a Hamzan baya nan tun ɗazu Abbu ya kira shi gidan Mama Asma'u ya aike shi. Ya rasa yanda zai yi ya samu a kira masa Beenafahr, wanda ƙirjinshi ma bugawa yake domin har yanzu bai gama yankewa a ransa abinda zai faɗa mata ba, ballantana har ya samu ta karɓi lemun tasha. Ga Kwallin nan ya ramɓadoshi tamkar wani ɗan Gaida (ƙyanda). Yana nan takaicin Hamza ya gama cika masa zuciya sai ga Farisa da Humaida Allah ya jefo masa. Nan ya tsara mata abinda za ta faɗa mata. Tana zuwa ba jimawa sai ga ta ta dawo tace masa tace tana zuwa. Farin ciki ne ya kama shi tamkar zai taka rawa. Shi kenan yanxu da ta kalle shi tasha wannan lemun daga gidan iyayenta sai gidan shi. Shi ke nan za su zamto mata da miji na har abada idan ta rabu da wancan matsiyacin. Yana nan a tsaye daga yaji motsi sai ya waiga, abu kamar wasa sai ga shi har ya jima sosai bata fito ba. Ganin har sha ɗaya ta gota da wani abu yasa ya gama tabbatarwa a ransa cewa ba za ta zo ba. Tamkar ƙirjinsa zai tsage haka ya dinga ji domin gabaɗaya daga wannan daren ya gama tunanin cewa mafarkinsa ya rushe. Haka ya lallaɓa ya koma ɗakin Hamza ya kwanta baƙin ciki duk ya bi ya dame sa. ****** Washegari, da wuri mai make-up ta iso ta cancareni da kwalliya kamar ka sace ka gudu. Munsha wanka, gida ya ɗibi sai ti sai sai shagali ake wanda babu abinda zan ce sai sambarka. Sai misalin ƙarfe biyar Ya Mohaa ya shigo gidan fuskar nan cike da annuri. Hotuna aka fara mana dani da shi wanda shi ne ya buƙaci hakan, sannan ya yi ta kiran Su Ammah ya ce su zo ya ɗauki hoto da su na tarihi. Magana ake ta family, duk wani girma ko wani matsayi ajiye shi ake ayi farin ciki domin, wannan ranar ta kasance rana mafi girma da daraja a wurinmu domin ta kafa tarihin da har abada ba zamu manta da shi ba. Hajiya Batula ta yi matuƙar farin ciki yau har da kukanta, ganin yanda ya riƙe hannun ta yana nunawa kowa ita a matsayin mahaifiyarsa, wanda ba ita ɗin ba, hatta su Aunty Labiba sun tsinci kansu a cikin wani irin sabon farin ciki. Dangin Dr. Basheer ma sun nuna mini matuƙar ƙauna da kara wacce sai da na yi ƙwalla, ganin yanda suka zo har mutanen Bunza suma ba'a bar su a baya ba. Haka aka yi taro lafiya, aka ci aka sha, akayi zumunci sannan aka watse lami lafiya. Misalin ƙarfe goma ina ɗaki daga ni sai Sis Noura ina cire kaya sai ga Bahrain ya yi sallama. Tsayar da shi na yi sai da na gama canjawa sannan na ce ya shigo yana ta wani rawar jiki yana nuna min waya ya ce. "Aunty Beena zo ki ga yanda Mijin ki ke ta posting a handles ɗinsa. Wallahy Aunty Beena mutumin nan yana cikin farin ciki...kalli rubutunsa...Ko'ina kika zaga sai maganar nan ake.." Karɓa na yi na kalla yayin da na ji wani daɗi ya ƙume zuciyata. Murmushi kawai na ke ba tare da nace komai ba. Muna nan sai ga Ya Hashim ya shigo. Kallon sa na yi na ce. " Ya Hashi sai yanxu? Gaskiya na yi fushi." Dariya ya yi ya ce. " I'm sorry please Maman en biyu, busy nake sosai sai yanzu na samu kaina." "To ba komai Yayana. Naga saƙon ka a wurin Mama, na gode sosai Allah ya saka da alheri ya bar zumunci." Humaida ce ta shigo ɗauke da leda a hannunta tace. "Aunty Beenafah ga shi nan in ji Ammie ta ce wai wata ce ta kawo miki. Pampers ne a ciki.." Kallonta na yi nace. "Wace ce?" "Oho, ni ma bata faɗamin sunan ba haka kawai ta ce." "Ok kice na gode." Tana fita Ya Hashi ya kalleni ya ce. "Beenafah wannan ɗin ƙanwarki ce ko?" Kallon sa na yi, sai kuma na yi murmushi na ce. "Eh, ya akayi?" "Ina son auren ta....da gaske nake miki. Za ku bani?" Wani irin kallo Bahrain da ke zaune ya yi masa tamkar zai fashe da kuka ya ce. "Gaskiya Ya Hashi ni ban amince ba. Humaida ba ta da kunya ba ta da kirki ko kaɗan...ni gaskiya a'a...ga uban girman kai da jin cewa ita wata ce." Dariya muka yi ganin yanda da gaske ya haƙiƙance yanata masifa yana kushe ta wanda ni sam a cikin raina ban ji daɗin hakan ba. " To ai ni Ji da kan ma shi ne abinda ya ja ra'ayina na ji duk duniya babu wacce nake so sai ita.." Cikin ƙufula ya ce. " Ya Hashi kasan kuwa wace ce Humaida? To er yarinya ce ma ƙarama bari ganinta da wannan jikin, ko secondary ba ta ƙarasa kambalawa ba. " " To ai ni irinta nake so, Kaga tana gama zana SSE sai mu yi aurenmu." Tashi ya yi ya fice yayin da muka dinga masa dariya na wannan wautar tasa. Yanzu da Allah yasa su Aunty Aysha suna ɗakin da yasa na ji kunya. Allah ka shirya Bahrain ka canja masa rayuwa. Yana da wani hali na riƙo, idan aka masa abu yakan saka shi a rai ya kasa mantawa. Kallon sa na yi na ce. "In Sha Allahu karka damu, zan gayawa Ammie sai ta gayawa Aunty Aysha kai kuma sai ka sanar da gidanku." "Na gode Beenafah." "Haba! Ai ni ce da godiya, Allah ya saka da alheri." ******* Koda sati ya zagayo gidan ya koma shiru domin kowa ya koma gida. Daga ni sai Ammie da su Arhaam muka dawo rayuwa da sauran mutanen gidan, wanda ba ta yi ƙasa a gwiwa ba ita da su Ya Hamza su Mama, kullum cikin kulawa take damu take ba dare ba rana. Ya Mohaa ma ana kammala hidiman ya juya ya koma gida wanda wata ɗaya yace mini zai yi ya dawo. Haka muka ci gaba da rainon twins ɗina cike da soyayya. Sai da muka yi wata huɗu cif sannan muka fara shirye-shiryen tafiya. A satin da za a mayar dani ne muka shirya muka je Bunza muka gaishe da Hajiya na yi mata sallama muka kwana ɗaya muka dawo. Mummy Sameera kullum cikin yi mini sabon karatu take. Ga shi ta yi min shiri na musamman sannan ta haɗamin kayan amfani masu kyau masu nagarta da inganci ta bani. Gankn irin yanda ta loda mini kayan ne yasa na yi mata wani kallon nace. "Mummy Sameera Ya Mohaa fa wallahy shegen wayo ne da shi da biyar diddiƙi. Yanzu sai ki ga ya tasa ni a gaba da tambaya." Baki da hanci ta buɗe tana kallona sannan daga ƙarshe ta yi murmushi ta ce. "To sai ki ɓoye ta yanda ba zai gani ba..." "Hmm! Ni wallahy baki san halin sa ba ne Mummy Sameera..." "To idan ya tambaya ki ce masa kayan gyaran jiki ne.. Haba! Ke kullum dai gaki dai gaki! Dan Allah ki canza rayuwa. Allah ma yasa ni duk abinda na kwashe tsawon lokaci ina karanta miki baki watsar ba." Dariya na yi na ce. "A'a wallahy! Komai na haddace sa kamar yanda kika faɗamin mummy ta." "To Allah yasa. Duk kin gama shanye waɗannan da na kawo satin can?" "Na shanye su, tambayi Ammie ki ji." "To shi ke nan. Allah ya ƙara zaunar dake gidan ki lafiya ya baku farin ciki ya raya muku yaranku." "Amin Mummy na gode sosai." Da dare ya yi, tare muka je gidan Mama Asma'u ni da Ammie na yi mata godiya da kuma bankwana washegari ranar friday muka wuce Gusau tare da Ya Hashim, Ya Hamza da kuma Bahrain. Gidanmu na Abbienmu muka sauka, bayan mun huta washegari muka shirya muka je gaisuwa gidan su Mummy Zaliha. Koda muka shiga tana zaune saman Veranda da carbi a hannunta, ya yin da Aunty Husaina ke zaune tana haɗa musu Tea da alama sai yanxu za su karya. Sai Aunty Hassana dake zaune gefen mummyn tana Shayar da Babyn da ta haifa wata ɗaya da ya wuce. Agogon wayata na duba bayan mun kai zaune. 11:13am, kuma sai yanxu za su yi kari. Gaisawa muka shiga yi wanda babu abin da idon Mummy ke tarararwa sai ruwan hawaye. Cike da tausayi Ammie ta ce. "Hajiya Zaliha ya ƙarin haƙurin Alhaji?" "Hmm! Haƙuri sai ma'aiki, mun gode Allah." "Allah ya gafarta mi shi yasa ya huta." "Amin amin. Na gode Hajiya Mulaifa. Babu abinda zan ce sai godiya. Ina kuma ƙara neman afuwa. Duk da abunda ya faru, ga shi kin manta har kin goya bayan cewa ɗan mijin ki ya aura Humaida..sannan ga katafaren shagon Electronics an buɗewa Hafiz kika ce ya ci gaba da kulawa dani. Mun gode mun gode.." "Haba ba komai,Allah ya sanya alheri da albarka yasa ace gwamma da akayi. Allah kuma yasa mu cika da kyau da imani." Tasowa Aunty Husaina ta yi ta karɓi Aryaan daga hannun Bahrain tana dariya ta ce. "Ah ahh! Barakallah masha Allah! Amma dai kam ba only breast milk ba? Wannan nauyi haka Masha Allah..." Dariya ta fashe da ita ganin yanda ya ke ta dariya yana wani tsalle tamkar wani doki. "Allah sarki! Daɗi yake ji yaga Mamansa...ko?" Ta ƙarasa maganar tana mai jan kumatunsa. Murmushi Ammie ta yi ta ce. "Waɗannan sarakan cin abincin ina Nono zai ishesu. Harda Madara ake basu..." "Kai Ammie...." "Wallahy kuwa, yini suke shan Nono da cin abinci idan dare ya yi ma haka. Shiyasa ga su nan sun yi barakallah kamar waɗanda suka shekara.." "Kai Ammie kyauwu kika gani. Kuma nasan har kin fara jin kewa, domin za su miki tawaye." "Allah ya tsare hanya. Ina nan ai kujera nake, ina zaune za'a dawo a same ni. Hassana kawo min jikar tawa na gani mana." Da sauri na miƙa hannu na karɓeta ina dariya na ce. "Ni ce nan uwar ta, saboda ni zan fara ɗaukanta ba ke ba." Dariya suka kwashe da ita sannan Ammie ta ce. "Ba komai. Ni ko cewa akayi ba zan ɗauke ta sai in tsaya daga gefe in yi addu'a." Fira muka sha sosai wanda har Ya Hafiz sai da ya dawo gidan muka zauna kamar komai bai taɓa faruwa a tsakaninmu ba. Sai da aka yi mana abinci muka ci wanda Mummy ta ji daɗin hakan sosai, sannan misalin ƙarfe uku muka shiga gidan su Fakiha. Koda muka shiga an gama shirya gida an tsara komai ana jiran masu kawo lefen Fakihar idan an yi sallar Asr. Cikin farin Mama ta karɓe su Arhaam ta goya ɗaya a bayanta ta rungume ɗaya tana faɗin burinta ya cika. Cikin jindaɗin yanda Mamar ta ba ta muhimmanci Ammien ta ce. "Wato dai lefen nan sai da kika hana a kawo shi ɗin sai idan ina nan?" Zaunawa tayi a ƙasa yayin da Ammie ke kan kujera a zaune tana facing ɗinta ta ce. "Hajiya Nana Hauwa! Wallahy tallahy ni a duk duniyar nan dai a yanxu...bani da tamkar ki. Hajiya kika bai wa Mijina Million huɗu...million huɗu fa a zamanin nan, kika ɗauki ɗana kika mayar na ki, ki ka riƙesa matsayi ɗaya da Bahrain kuka saka shi a makaranta...kalle shi..kalle shi ki ga yanda ya canja ya dawo ɗan gayu da shi ga kuma tarbiyya..auren Fakiha ya tashi kin zunguro mana manyan kuɗaɗe kin ce gashi nan mu saya mata kayan ɗaki...mu da ko dubu ɗari ta kanmu bamu da ita, amma ta sanadinki, rayuwa sai dai muce Alhamdulillah!" Girgiza kanta tayi tare da zubo da hawaye ta ce. " Hajiya Wallahy ba ki san yanda nake jin ki a raina ba. Allah dai ya ƙara mana lafiya ya kuma ya ƙara mana tsawon rai mai amfani. Amma auren Fakiha ko shekara goma za'a yi, na gama yankewa sai ranar da kika zo za a yi shi." "Allah sarki! To ai gani na zo. Allah ya kaimu ranar auren lafiya." "Amin." "Ta so mu je kiga kayayyakin da aka haɗa musu..." A tare suka fice suka barni daga ni sai Fakiha, bayan su ma su Ya Hamza sun fita. Kallonta na yi na sheƙe da dariya na ce. "Amarya Amarya...kin ga kyaunki kuwa?" Itama dariyar tayi tana mai matsowa kusa dani ta shafa fata ta tana faɗin. "Ai kece amarya. Ji yanda jikinki ke ta wani sheƙi yana walwali...ko ni nan da za a yiwa auren wani sati kin fini haɗuwa. Wata dariyar na ƙara yi harda buga ƙafa sannan na ce. "Ke! Billahillazy raba kanki da ni. Na ƙuna bani tarar ƙauri,a tsime nike nan ciki da waje in gaya miki. Giwa ta Mohaa Uwargida mai Capacity. harkar ba irin taku ba ce ku en yara, magana ake ta matan aure uwayen gida..." Dariya ce ta ƙwace mata tare da yin mini wani kallon mamaki ta ce. "Beenafah! Haka kika dawo ashe?" "Af! Tsaya kallon ruwa kwaɗo ya miki ƙafa. Mummy Sameera ta fi wata tana gyara ni tamkar wani bakanike a cikin garage...." "To ai ni kin goge mini harda yau Beenafah. Na rantse da Allah daman wanda ya ke shiru-shiru idan ya tashi burgewa ya fi burgaggen kan famfo haukacewa..." "Oho dai! Kema nan watarana haka za ki yi. Ina nan ina lissafi yau saura kwana biyu mu dawo haka..ki bari zan ɗiba miki turaruka In Sha Allahu idan na buɗe kayana.." Na faɗa ina mai ɗaga mata ystsuna guda biyu da na yi twisting. Shigowar su Hafsa ita ce ta katse mana firar, sannan muka tashi muka yi sallar Asr ɗin. Bayan mun kambala muna zaune muka ji ana ta keta guɗa ana ta arerewa ana farin ciki masu kawo lefe sun zo. Muna nan gida saida aka gama sallar Isha bayan an kammala komai sannan muka koma gida. Washegari kuma muka shirya muka tafi gidan su Yaya Ashiru kamar yanda na roƙi Ammie tun muna Sokoto. Koda muka shiga gidan yana nan a gyare tsab kamar yanda suka saba. Gidan ba kowa da alama yaran suna makaranta kasancewar Lahadi ce. Ayya ce ta fara fitowa sannan Umma. Yanda suka tarbemu ne ya bamu mamaki baki ɗayanmu. Cikin farin ciki suka baza mana tabarma a bakin bishiyar mangoron wacce ke ta kaɗa iska mai sanyi da daɗi. Bayan mun gama gaisawa Ayya ta ce. "Allah sarki! Hajiya ashe haka abubuwa suka yi ta kasancewa ko?" Ɗan murmusawa Ammie ta yi tace. "Wallahy fa! Al'amarin Allah kenan?" "Masha Allah! Beenafah ke ce mai tagwaye? Naga kansu ɗaya, kamar su ɗaya." Cewar Umma tana mai miƙo hannu ta karɓi Arhaam daga hannun Ammie wacce itace ta amsa mata da cewa Eh. "Allah sarki!

Chapter 60 of 67