Share this page
zan fi jin daɗi a yanzu musamman da bansan ya za su karɓeni ba a wannan karon tunda wata ƙila gani suke kamar ni ce na hana ya aura er su. Da shigarmu gidan, abun da zuciyata take rayamin shi na tarar ko Ince ya ma zarce yanda na hasasa, domin idan ba Suwara da Taimiyya ba...babu wanda ya yi mini tarbon arxiki har su Aunt Fattoom. Babu abunda yafi bani al'ajabi da mamaki kamar yanda Jadda ta yi mini. Tamkar wata baƙuwar suka fara gani haka suka tarbeni a wulaƙance a yatsine. Musamman Jadda, domin a yanda nake gaisheta ma ko alamar arzikin ta tsaya ta kalleni ban samu ba. Da farko na ɗauka yanayin baƙi ne da ya cika gidan yasa wata ƙila bata ganeni ba, sai daga baya da naga tana ta zuwa tana dawowa ne yasa na sake cewa. "Jadda na fa iso tun ɗazu.." A ɗan tsawace ta yi mini wani kallon sannan ta ce. "To Beenafah zan raba kaina gida goma ne? Ko ba ki ga ina ji da baƙi ba ne? Ki jira ina zuwa tunda dai ke baƙuwa ba ce a gidan nan." Wallahy a yanda na ɗimauta na gigita da mamaki sai da naji ɗan cikina ya hautsina tamkar zan sako fitsari haka na ji. Mutanen da suka cika parkourn sai kallona suke tamkar na nutsa cikin ƙasa haka naji, ga yunwa daman ga fitsari ina ji ga gajiya. Sannan tun ɗazu su Suwara sun wuce ban ƙara ganin giftawar su ba. Wani irin matsanancin kuka ne yaso ƙwace mini amma dole na dake domin ina jin tsoron kada na yi kukan kuma ya zamto matsala. Bayan ƙara zaman kusan mintuna talatin babu wanda ya kula ni yasa na miƙe har ina dafe kaina tsabar yanda na ke ji na lallaɓa na fita zuwa gidana. Ina shiga na rufe da Key na je da sauri na yi fitsarin da ya addabeni sannan na fito jiki na rawa na kira Suhaib na ce dan Allah yasa a kawo mini abinci domin tun da na shigo gajiya ta rufeni na kasa fita wurin Jadda, amma idan na ci abinci na yi wanka na huta, zan fito In Sha Allah. Ina nan ba jimawa sai ga Taimiyya ta ƙwanƙwaso mini. Tambaya ta take hankalinta a tashe akan cewa miye yake damuna ganin kamar nasha kuka na ce mata ba komai, kawai gajiya ce. Daga haka ta juyo domin ta ce mini aiki take ana jiranta. Haka na koma na je naci abincin sannan naji na fara dawowa hayyacina. Salloli nayi sannan na rarrafa na watsa ruwa wanda a lokacin ƙarfe tara na dare ake magana na samu wuri kawai na kwanta. Wani irin kuka ne ya ƙwace mini mai tsananin na rashin taƙamaimen ma abunda yake damuna. Tambayar kaina na fara da cewa ni nai musu? Minai musu da har na cancanci wannan wulaƙancin? Ko ba su kulani domin komai ba suna kula ni ko don cikin jikansu da yake jikina. Har yanxu babu wanda ya biyo sawuna...Jadda taƙi ta zo taƙi ta aiko a bincika lafiyata, ya na zo, na ci abinci ko banci ba? Ina nan na ji wayata na ringin, ina dubawa naga kiran Suhaib ne yake ce mini wai ga Jaddi a bakin ƙofata yana son Magana da ni. Ta shi na yi da ƙyar na rarrafa na je na buɗe sai gashi a tsaye yana mini murmushi. Kayayyaki ne a hannun sa, ganin hakan yasa na janye ya shigo daga ciki muka zauna a parlour. "Beenafah an zo lafiya?" Sosai na shiga ƙoƙarin ɓoye hawayena ina murmushin Ƙarya na jinjina kai na na ce. "Lafiya ƙalau Grandpa..." "To miyasa kike na ke kaɗai? Ba za ki shiga can ba ne? Kamar zai fi ko? Domin kada ki zauna ke ɗaya." Jinjina kaina na yi na ce. "In Sha Allahu daga zaran na kambala abin da nake zan je Grandpa.." "To masha Allahu. Kinga kayan fruit nan na kawo miki su, har gona naje da kaina na ɗebo su daga bishiyarsu domin ki ke kaɗai. Sannan wannan...." Ya ɗago wata kwalba yana nuna mini ya ce. "Za ki riƙa shan murfi ɗaya a kullum kin ji ko?" Sosai na ji duk wani baƙin cikin da suka ƙunsa mini ya washe yanda Jaddi ya nuna tsantsar kulawarsa a gare ni. Ya jima yana mini addu'a sannan daga ƙarshe ya miƙe da nufin tafiya. Har ya kai ƙofa sai kuma ya juyo yana murmushi ya ce. " Af! Kin ga kuwa na manta, Na sa an gyara miki Rooftop ɗin ki, naga kina son wurin, hakan yasa na saka aka shirya miki shi, idan kina so za ki iya tafiya ki zauna." Yanzu kam har da guntun hawayena wurin yi masa godiya. Yana fita sai ga kiran Dayaa ya shigo. Ɗauka na yi muka gaisa ya shiga yi mini tambayoyi akan yanda tafiyata ta kasance da kuma yanda na ji zaman gidan na wuni ɗaya. Murmushi kawai nake ina ce masa komai lafiya lau amma ba don komai ɗin yana lafiya ba. Sosai ya damu yana ta tambayata abin da yake damuna na ce masa gajiya ce. Yanzu haka ina so ma na kwanta. Da haka na samu ya ƙyaleni tare da yi mini fatan tashi lafiya. Wato abinda na ɗauka a wannan tafiyar tawa;Mutane a kullum kwanan duniya ƙara baka darasi suke. Domin su Jadda sun bani darasin da har na koma ga Allah ba zan manta ba. Wato dole sai sun ƙuntata mini tunanin cewa ni ce na hana auren Mijina da er su Noura. Haƙiƙa na yi nadama, na yi nadamar wannan zuwan da nayi, kuma har abada ba zan daina nadama da baƙin ciki ba. Wato duk abin da na yi gudu ban tsere masa ba. Dani da babu ni duk ɗaya,babu wanda yake damuwa da shin na fito ko kuma ban fito ba. Gidan ya cika sosai da sosai mutane ta ko'ina. Ni kaɗai ke kwana a gidana domin su Suwara suna can suna gararinsu na 'ƴammata. Jadda ta koma mini wata mace ta daban, domin Jaddar da na zo na tarar a wancan zuwan ba ita ba ce a yanzu. Na kasa gayawa mijina halinda nake ciki. Kullum sai dai in yi masa Ƙaryar cewa ina lafiya kuma komai yana tafiya daidai, amma ba don komai ɗin yana lafiya ba. Tamkar wacce take cikin ƙungurmin daji tana neman agaji yanayin da na tsinci kaina kenan a ciki. Na ƙagu na ƙosa ranar bukin ta zo inga su Aunty Nadee ko zan samu na ji sanyi a raina. Hatta abinci wannan sai idan na kira na ce a kawo mini. Wallahy na san idan na faɗa masa halin da nake ciki nasan cewa shi da su har abada. Amma ba zan yi hakan ba, dole na yi haƙuri, Allah yana sane dani, kuma ma ai ba nan zan tabbata ba, ana gama bukin Dayaa zai zo nan mu wuce gida idan ya kawo Hairi ɗakinta. Da wannan idan na tuna sai in ji er nutsuwa ta shigeni. Shiyasa akoda yaushe nake kan yin waya da su Ammie su Aunty Labiba duk da cewa babu wanda na faɗawa halin da nake ciki. Bukukuwansu kawai suke ta yi masu cike da ƙayatar wa. Yau koda na wayi gari, a farin ciki nake, domin an tabbatar mini cewa Su Aunty Nadeeyah suna hanya. Hakan yasa na shirya da wuri amma dai ina cikin gidana ban fita har sai da na ji cewa sun iso. A wani babban parlour ne na musamman aka saukar da su wanda yake can cikin wani mansion ɗin da ake buɗe saboda su. Kusan sanƙamewa na yi a tsaye ganin cewa wai harda Ammie suka zo. Daman ita amma suka ɓoye mini babu wanda ya faɗa mini? Shigowar Jadda shi ne abinda ya yanke mini hanzarina na tsaya a nan inda nake tsaye ba tare da motsa ba. Tana kallon inda nake sai kuma ta mayarda kallonta wurin su Ammie wanda ita ce mutum ta farko da idonta ya fara sauka a kanta. "NANA MARYAM? ba cewa kika yi ba za ki samu zuwa ba? Saboda wannan shashashar mai son kanta ta hana Hammodi ya auri Noura shi ne kika yi fushi Nana maryam??" Waigowa ta yi sai kuma ta dawo da kallonta gare ni cike da tsana ta ce. "Ke ɗin kin cika mai son kanki Beenafah! Ke fa macece.. Kisa kanki a takalmin Noura. Idan kice mijin ki ya mutu aka ce ga ɗan uwanki zai aure ki domin ya tallafeki keda marayun 'ƴa'ƴan ki amma matar shi ta ce bata amince da ya aureki ba ya za ki ji dan Allah? Kin cika muguwa azzaluma marar tausayi Beenafah...sam ba ki kyauta mana ba..." Aunt Fattoom dake tsaye a bayanta cike da shock ta ce. "Jadda Wannan fa ba Nana Maryam ba ce ki duba ki gani? Nana Maryam ta fi wannan jiki...sannan su ne fa dangin Emraan da akace za su zo...ga Nadeeyah ai kin gane ta.." Da gudu ni kam naje na faɗa Jikin Ammie ina mai fashewa da wani irin mugun kuka jin irin munanan kalaman da ta yarfa mini. Lokaci ɗaya dukkan ilahirin jikinta ya ɗauki rawa, ta hau nuna Ammie da yatsa tana rawar baki alamar magana ta ke son furtawa amma kuma hakan bai samu ba, domin ganin kawai muka yi ta zube ƙasa somammiya. ✍️ *OUM-AMEER* ✍️ *GANIN IDO* 🥀🥀 *ADABI WRITER'S ASSOCIATION* *AMEENA IBRAHIM* *OUM-AMEER* *Wattpad:@Ummu-Ameer* *Arewapen:@Oumameer2671* *FREE-BOOK* *PAGE 55* Bayan Jaddan ta farfaɗo ne da gudu Aunt Fattoom ta fita, ba jimawa sai ga ta tare da wata tsohuwa wacce kamanninta sak Jadda tamkar an tsaga Kara. Kallon Jadda tayi wacce ta soke kanta a ƙasa ta ke ta rusa uban kuka,  hankalinta a ɗimauce ta ce. "Samaahat! Da gaske ne abinda Fattoom ta faɗo mini?? Da gaske ne?" Yatsanta kawai ta iya ɗagawa a raunane ta nuno saitin inda muke tsatstsaye tun ɗazu mun zubawa sarautar Allah ido, daga mu har su Mummy Na'Imatu su Aunty Nadeeyah, al'ajabi ya ishemu ya sha mana kai. Musamman ganin irin uban kukan da take rusawa. Direction ɗin yatsan Jaddan ta biyo jikinta yana wani irin ciccira sosai ta zo ta tsaya gaban Ammie. "NANA HAUWA?? Nana Hauwa da gaske ke ce? Daman ina da rabon sake ganinki a duniyar nan? Dan Allah ki mini magana....ki mini magana dan Allah.." Wani irin matsanancin kuka ne ta sake fashewa da shi, kukan da duk mai zuciya a ƙirji matuƙar yana da tausayi sai ya ji wani abu idan ya ji yanda take kukan tsabar yanda ta gigice. Kallon kallo muka fara wanda kowa sai bin ta yake da ido domin mun ji wani abu na daban wanda ya ruɗa mana zuciya, musamman Ammie wacce aka kira wai da NANA HAUWA bayan ta ji ɗazu an kira wata da NANA MARYAM. Tasowa Jadda ta yi ta zo ta ɗago Tsohuwar tana kallonta cike da tausayi ta kira sunanta ta ce. "Sumaiha! In Sha Allahu ta'ala! Ko kokonto babu, wannan ita ce Nana Hauwarmu. Itace, ABUBAKAR SIDDEEQEE ya ɗauka cewa wai shi yana da wayo, ya ɗauka cewa wai shi yana da dabara, ya manta cewa Ubangiji shi ne wanda yake da iko akan komai. Sai dai kuma...Allah ba azzaluman sarki ba ne! Yana tunanin ke ce wacce ya cutar, sai ga shi ya shiga jarabawar da ya kasa jurewa." Ƙara matsowa tayi dab da Ammie ta saka hannu ta shafo fuskarta wanda dukkan su sai da suka ji wani abu mai kamar shock ya shige su a lokaci ɗaya. " Tabbas gaskiya kika faɗa Samaahat, bana buƙatar kowace shaida domin wannan 'ƴa ta ce Nana Hauwa!!!" Wani irin zazzare ido muka fara jin wata iriyar magana kuma mai ban mamaki. Ammie ba ta tsaya komai ba kawai ta rungumeta tare da fashewa da wani irin matsanancin kuka. Duk da cewa bata da tabbacin cewa da gaske ne ko a'a. Kukan da tsohuwar ke yi ya daki zuciyarta ba kaɗan ba. Tsaye muke kamar wasu shashashu inda su kuma suka hau kiraye-kirayen wayo yi. ********* Auren da za'a ɗaura gobe juma'a, dole aka ɗage shi zuwa ranar Monday daga nan ɓangaren Emraan, wanda shi kam na Suhaib ba'a fasa shi ba. Tsawon kwana biyu kenan na kasa matsawa daga jikin Ammiena kamar yanda itama ta kasa matsawa daga jikin mahaifiyarta kamar yanda tsohuwar tayi iƙirari duk da cewa har yanxu ba mu ji wata gamshashshiyar hujja ba. Hmmm! Allah sarki! Uwa kenan!. Daman tun a jiya, Noura da mahaifiyarta suka iso wanda tabbas kallo ɗaya za ka yi mata da Ammie Kaga kamanninsu tsantsa, dole duk wanda ya gansu ya ruɗe ya kasa bambance su da juna Indai ba kasan su sosai ba. Duk da cewa Ammie ta ga wannan ƙwaƙwƙwarar shaidar...har yanxu a zuciyarta ta kasa yarda muddin ba sheikh ta gani a gaban ta ya tabbatar mata ba. Nikam na yi kuka sosai tare da neman su gafara domin sai da suka haɗu ne na gane kuskurena, da ace na ɗauki maganar Dayaa tun a ranar da ya kirani da yanxu sun jima da ganawa da juna. Amma sai nake gani da kuma tunanin cewa kada na ɗaga musu hankali a banza alhali babu abinda suka haɗa. Zaman jiran isowar Sheik muke da kuma ainahin mahaifinta wanda aka ce sun iso kaɗan ya rage su ƙara so. Fitsarin da ya matsamin ne yasa na miƙe ina kallon Ammie na ce mata zan je na yi fitsari. Jadda na ganin na miƙe ta taso itama ta biyoni tana faɗin na yi a hankali kada na zame, amma dai bari ma ta rakani. Wani uban tsaki na ja a raina, ina faɗin ai duk neman gindin zama ne, idan ba shi ba, ni yarinya ce da za ta ce kada na zame? Tun can bata san cewa kada na zame ba sai yanzu? Zamewa ta nawa kuma? Ai gwanda ma ace na zame na faɗin wallahy ya fiye mini alheri da irin azabar da suka ɗanɗana mini kwana biyu. Ina shiga gidana na datse ta ciki, sannan na wuce na yo fitsarina na fito. Wayata na ɗauko na kira Dayaa muka sha fira wacce bana gajiya da saurarensa sannan daga ƙarshe muka yi sallama yana faɗamin cewa ana kan shirya Hairiyya ɗin gobe Lahadi za su taso zuwa nan ɗin In Sha Allah. Ina hango tsayuwarta, na juya naje ta ƙofar kitchen na buɗe na fice, ta baya na zagaya na shige na barta a nan. Shiga ta ba'a fi minti uku ba sai ga su sun shigo. Wani irin ɓari jikin Ammie ya ɗauka ganin da gaske kuwa Sheikh ne da wannan mahaukacin wanda yake zuwa a matsayin babanta. Duk da cewa baya cikin wannan shigar da ya saba ta mahaukata,yana shirye cikin shigar Larabawa waɗanda suka jiƙe da kuɗi da kuma jindaɗi, ga shi kuma da medicated glass, duk hakan bai hana mata gane shi ba, tabbas a yau ta shaida shi. Shi ne wannan. Kukanta ne ya tsananta wanda tama rasa ina za ta dafa. Da kanshi ya iso har inda take, sai dai kafin ya ƙarasa Isa, wannan tsohuwar wacce muka ji Jadda ta kira da Sumaiha ce ta tare gaban shi cike da zafi a kalamanta ta ce. "Kada ka taɓa mini 'ƴata SIDDEEQEE!!!" Ta shi Ammie ta yi taje ta faɗa jikin Sheikh tana kuka ta ce. "Sheikh...Wai miye yake faruwa? Su waye waɗan nan ɗin? Na rantse da Allah ba don na ganka a tare da su ba, tabbas ba zan taɓa aminta da duk abinda za su faɗa mini ba." Jinjina kai Sheikh ya yi sannan ya dafa kafaɗunta yana mai zubar da ƙwalla ya ce. "Mulaifa! Tabbas wannan shi ne mahaifinki. Shi ne wanda ya kawo ki gare ni. Ya dawo bayan kin ɓata daga gareni Mulaifa. Ya ce mini ya kwanta matsananciyar jinya ne lokaci mai tsawo, shiyasa bai dawo ba, bayan ma ya warke akwai wasu dalilai da suka hana shi dawowa sai a wannan lokacin. Kin gan shi ko? Abubakar Siddeeqee ne ashe wanda aka fi sani da Siddeeqee a ƙasar Qatar. Sam shigar da yake a wannan lokacin ta hana mini na shaida shi...Na yi kuka, na yi addu'a da neman Allah ya bayyana mini ke domin in damƙa ki hannun mahaifinki. Kullum sai na roƙi Allah akan ya ƙara mini tsawon rai domin na ga na mayar da amanar da aka bani. Sai dai, a neman ki da na yi ta yi ƙarshe Yayan Mijin ki shi ne wanda ya tabbatar mini da cewa kun mutu a haɗarin mota daga ke har 'ƴa' ƴan ki...Mulaifa! Ki gafarceni. Ban san abinda ya faru da rayuwarki ba, amma tabbas laifina ne dana haɗa ki aure da mutumin da ban sani ba..." Waigawa yayi Wurin Wanda aka kira da Siddeeqee ya kamo hannun sa ya jona dana Ammie ya ce. " Ga amanar da ka bani a yau na sake dawo maka da ita, ina neman afuwarka da yafiyarka akan gazawata..." Sosai yake kuka yana girgiza kai cike da nadama ya ce. "Ya sheikh wallahy babu inda ka gaza. Ni ne nan na gaza, ni ne nan na biye wa zuciya na aikata abin da ya dawo ya dame ni daga baya, na kasa bacci, na kasa ci, na kasa sha. Komai na duniya ya juye mini sama ƙasa Nana Hauwa...haƙiƙa ni ne nan mahaifinki. Wannan kuma ita ce SUMAIHA, ita ce mahaifiyarki da ke da Nana Maryam. Mun yi aure da ita dalilin SAMI wanda shi ne mijin twin sister ɗinta SAMAAHA. Kasuwanci ya haɗamu daga nan sai abota ta ƙullu a tsakaninmu. Yana neman Samaaha da aure nima ya nema mini Sumaiha. Sai da suka shekara goma da aure cif, bisa wani ƙaƙƙarfan dalili sannan muka yi aure mu kuma. daga nan na ɗauke ta zuwa Qatar inda can ne ƙasata inda nake zaune tare da familyna. Sumaiha ta kasance Mace mai tsananin zafin kai da zafin zuciya. Al'adunmu da rayuwar matanmu a Qatar tasha babban da rayuwar al'adun mutanen Sudan. Musamman da mahaifiyata ta kasance jinin sarauta. Dalilin da ya hana mini aure tsawon shekaru goma shi ne ƙin amincewar mahaifiyata da auren Sumaiha, hakan yasa na ce na haƙura da aure matuƙar ba ita ɗin zan aura ba. Sai da taga da gaske na yi shekara goma bayan sun buga sun buga dole daga ƙarshe ta haƙura na auro ta ɗin." " Bamu shekara ɗaya da aure ba ta ce tana so ta ci gaba da kasuwancinta wanda take yi a nan Sudan ɗin. Na san abu ne mai matuƙar wahala mahaifiyata ta amince, domin harakar kasuwanci ta fita kasuwa mu a garemu na Maza ne kawai ba da mata ba. Matayenmu muna matuƙar ba su muhimmanci da kuma kulle su a cikin gida domin a nan suka fi cancanta, koda fita ta kama ayi, to dole a lulluɓe ko'ina hatta fuska da tafukan ƙafa wacce fitar dole sai idan ta kama babu yanda za'a yi, musamman a zamaninmu abun yafi tsanani sosai. Da Sumaiha ta zo, duk ba ta damu da wannan ba. Ba sa jituwa Sam da mahaifiyata da 'ƴan uwana tunda ta fahimci cewa ba sa sonta. Alhali ba son ta ne ba sa yi ba, halayenta ne basaso. Na sha zaunar da ita na nuna mata cewa, idan har ka je Gari ka isko mutane kowa yana da Bindi (Tail) to kai ma ka yi ƙoƙari ka ɗaura naka domin kada ka fita daban. Amma Sam taƙi ta saurare ni. Itama sai excuses take kawo mini na cewa ba dole sai ta kasance yanda dangina suke ba matuƙar dai ina son zama da ita da gaske. A haka nake daurewa ina rarrashinta ina bata haƙuri a koda yaushe ina goya mata baya saboda ina tsananin ƙaunarta. To a lokacin da ta zo mini da zancen kasuwanci, sai na shaidawa iyayena wanda suka ce sam ba su amince ba, musamman mahaifiyata, abu kamar wasa abubuwa suka yi tsamari sosai wanda na yi ta roƙon Sumaiha akan ta haƙura. Haka ta nuna taurin kai ta hau kasuwanci wanda ni ne dai wanda na ke ji da aikina in kuma ji da kasuwancinta. A haka muka yi ta tafiya wanda ko magana wannan sai ta ga dama take yin ta da mahaifiyata." "A haka har Allah ya bata juna biyu ta haifi yara mata guda biyu wanda muka saka musu Nana Maryam da Nana Hauwa. Mahaifiyata sam taƙi amincewa ta kalli inda yaran suke ballantana ta ɗauka tace Allah ya yi albarka. Hakan ya yi matuƙar yi wa Sumaiha zafi da raɗaɗi wanda nima ɗin karan kaina ban ji daɗi ba, domin hatta sauran en uwana babu wanda ya zo inda take ita da waɗannan jariran. Ban san cewa tsananin ƙiyayya ya girmama a tsakanin iyalina da dangina ba sai a wannan lokacin. Muna nan dai a haka. Abubuwa basu ƙara lalace mana ba, sai da Sumaiha ta zo Sudan ta koma ta tace za ta buɗe shago a kasuwa. Hmm! Nana Hauwa...Matsalar mahafiyarku a wannan lokacin! Ba ta taɓa yarda cewa tana aikata kuskure ba, ita kullum gani take duk abinda take akan daidai take. Da wannan nima na nuna rashin amincewa ta. Na ɗauka cewa duk tsawon lokacin da muka ɗauka ina goyon bayan ta idan nace ban amince ba za ta yarda ta kuma amince kasancewata na Mijinta kuma shugabanta. Amma a haka ta hau shuka min rashin mutunci ta ce ita sam sai ta aikata. Wasa-wasa abubuwa suka ƙi daɗi a tsakaninmu, tashin hankali da rashin zaman lafiya suka zamto abin yin mu wanda muka kwashe tsawon shekaru biyu a haka. A ranar da ta je kasuwa ta sayi Shago da gaske, a ranar na ce mata sai dai ta zaɓa ko ni ko kasuwancinta. Kai tsaye saboda zafin kai da taurin zuciya ta ce mini ta zaɓi kasuwancinta ba tare da tunani ba." Girgixa kan shi ya yi tare da haɗiye wani wahalallen yawu ya cire glass ɗinsa ya share guntun hawayensa ya na kallon Ammie ya ce. " A ranar na ƙaryata soyayya Nana Hauwa! A ranar na cire duk wani abu da na taɓa jin ya taɓa burgeni a soyayya daga zuciyata. Domin haka ta zage a wannan ranar ta ci mutuncina da na mahaifiyata tana faɗin wai duk tsawon shekarun da mukayi bata taɓa jin farin cika ba. Kullum cikin ƙunci take da baƙin ciki. Haka ta dinga kuka ina roƙonta akan kada ta tafi. Amma ta saka ƙafa za ta fita, tana riƙe da hannunki dana Nana Maryam, sai na yi nasarar kama hannun ki na riƙe ki. Duk da cewa na janye ki daga hannunta...ko sau ɗaya bata juyo ta kalle ni ba, da ta kai ƙofa ne na ji nima bata da wani matsayi ko wata martaba a idona da zuciyata, hakan yasa na ɗaga bakina na furta mata kalmar saki. Da hakan ma bata juyo ba, kawai ta wuce ta barni dake. Ko kallon ƙarshe bata ƙara juyowa ta yi miki ba...." Durƙushe Sumaiha ɗin ta yi a inda take tsaye tana ta wani irin kuka tamkar za ta shiɗe. Tsawon shekarun da ta yi da rabuwa da shi babu watarana da za ta zo ba tare da zubda hawayen nadama ba. Girgiza kansa ya yi cike da takaici ya ce. " Ku kalle ta wai kuka take a yanxu! Ta ɗauka cewar duk abinda tayi akan daidaita take. Haka ta bar ni dake tayi tafiyar ta, mahaifiyata kuma, itama tsananin ƙiyayyar da take yiwa mahaifiyarku har da en uwa na, tsanar tana nan bata matsa ko'ina ba. Na ɗauka da Sumaiha ta tafi za su manta da komai su riƙeki da amana. Amma suka shiga azabtar dake tamkar kece Sumaiha ɗin, tamkar basu haɗa wata dangantakar jini dake ba haka suka riƙeki. Ƙarshe da na gaji da ganin yanda kike cutuwa, sannan ba zan iya zuwa Oumdurman ba saboda gani nake idan na mayar da ke wurin ta na nuna gazawa, hakan yasa na yanke shawarar damƙawa sheikh ke tun wata da'awa da yazo a Qatar, bayan ya gama gabatar da darussa na tsawon wata ɗaya tare da manyan maluma, haka na shirya cikin wata shigar

Chapter 56 of 67